Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta take yi tana kwashe su

Yayinda shi kuma yana kwance a saman gado idanuwan sa a rufe, da alamu ba wasu rauni ya ji ba sai dai a kansa da aka naɗe mishi da bandage, sai kuma ƙafar shi ɗaya ta dama da itama duk an saka mishi bandage a ciwukan da ya ji, sai kuma ƙaramar yatsar shi itama ta hannun dama wacce aka saka mishi drip

Shigowar su yasa su Momy suka bi su da kallo suna amsa sallaman nasu. Kasancewar Momy ta gane su musamman ma ganin Uncle Hashim da tayi yasa ta washe baki tana tashi tsaye tare da musu lale marhaban

Shima Abdul tashi yayi ya bai wa Ummee kujeran sa

Sannan aka gaisa cike da mutunci. Su Hajiya suka yi musu, "ya me jiki?"

Momy ta amsa da faɗin, "alhmadulillah. Ya samu barci ne  mu ma tunda muka zo be farka ba."

"Allah Sarki! Allah ya ba shi lafiya. Wlh hankali na ya tashi da jin labarin hatsarin shiyasa muka taho gaba ɗaya." Cewar Hajiya cike da damuwa

Momy tace, "wlh kuwa. Ai abun ne da tashin hankali. Nima ya zo ya gaishe Ni a jiyan yake ce min zai fita meeting, wlh a Raina sai da naji ban amince da fitar nashi ba, amma kuma tunda ya zama dole babu yanda zan yi, be fi mintuna goma ba aka kira mu aka sanar mana yayi hatsari, kuma motar tashi ce kaɗai ta kwace ma drever'n, Allah yasa akwai mutane tare dashi aka yi saurin taimakon shi tunda hatsarin ba sosai bane, ai mun auna arziƙi." Ta ƙare maganar tana sake share hawayen fuskar ta

Haƙuri duk suke bata. Hajiya na sake tausan ta

Sai kuma ɗakin ya ɗan yi jugum

A lokacin ne Umar Faruk ya buɗe idanun sa

Hakan yasa Uncle Hashim da ke tsaye ya koma gefen gadon ya zauna yana kallon shi

A hankali yake bin mutanen ɗakin da kallo yana yi yana ɗan lumshe idanun sa

Uncle Hashim ya soma mishi sannu kafin sauran su soma gaishe shi da jiki

Kanshi kaɗai yake ɗaga musu yayinda ya sauke idon shi a kan MEEMA wacce ta tsaya a can baya ta zuba mishi ido

But yana kallon ta sai ta ɗauke nata idon daga kallon shi tana ɗan gyara tsayuwar ta kasancewar ta soma gajiya, ɗan ɗago kai ta sake yi ta sauke a kanshi ta ga har yanzu ya kasa ɗauke ido a kanta, sai ta janye nata tana sauke kai ƙasa tare da wasa da yatsun hannayen ta. Ta kula yana da yawan kallo a yanda ta fahimta, kaifin idanun shi yake sa take gane ita yake kallo, hakan ke haifar mata da faɗuwar gaba me tsanani, sosai gaban ta ke bugawa wanda yasa ta kasa tsayuwa wuri ɗaya tana ɗan jujjuya jiki

Momy wacce ta lura da kallon da yake yiwa MEEMA yasa ta mayar da kallon ta gare ta, sai yanzu tayi mata kallon ƙurilla domin tun shigowar ta baza tace akwai ta a cikin ɗakin ba ma, duba da yanda ta ja can baya ta tsaya. Hakan yasa ta ɗan washe baki tana cewa, "ita kuma wannan kyakykyawar yarinyar fa daga ina?"

Zabba'u tayi saurin bata amsa da faɗin, "ai ɗiyar Hajiya ƙarama ce, sunan ta MEEMA."

"Allah Sarki! Masha Allah yarinyar kyakykyawa da ita."

Duk murmushi suka yi

While Abdul da shima sai yanzu ya kula da ita, tunda ya kafa mata ido ya kasa ɗauke wa, sai ƙare wa halittan ta kallo yake yi daga sama har ƙasa tamkar idanun sa za su fito waje har buɗe baki yayi

Uncle Hashim da shima yana kula da kallon da Umar Faruk yake bin MEEMA da shi, sai yayi murmushi yana matso da fuskar sa gefen sa, ya ɗan raɗa masa maganar, "sai na tsole idon idan baka dena kallon ta ba, ko dama ba jinya kake yi ba?"

Hakan yasa ya saki kyakykyawar murmushin sa yana ɗan lumshe idanun kamar zai rufe su sai ya juyo su ga kallon Uncle Hashim ɗin, be ce komi ba illa murmushin da yake saki, sai kuma ya ɗan karkata kai ya kalli Habeeb da ke jikin Jalila ya yafico shi da hannu

Hakan yasa yaron ya iso wurin shi

Yayi mishi murmushi da cewa, "har da kai kaima ka zo duba ni?"

"Eh Uncle. Ya jikin ka?."

"Alhamdulillah my boy. Kai ma ya naka jikin?"

"Ai naji sauƙi." Yafaɗa yana ɗaura hannun sa a kai

Zabba'u tace, "ai ya ji sauƙi sosai in dai Habeeb ne."

"Eyya shima be da lafiya ne ashe? Allah ya sawwaka ɗan yaro na, taho mu gaisa ko." Cewar Momy fuskar ta cike da fara'a

Daga Hajiya har su Ummee amsa mata suka yi da, "Ameen Ameen."

Iso wa yayi wajen ta, ta ɗaura shi a cinyan ta tana tambayar shi

Daga haka ɗakin yayi shiru illa sauraron surutun da Habeeb yake yi tare da Momy.

             Ita kuwa MEEMA duk ta gama gajiya, gaba ɗaya fuskar ta ta sauya tamkar zata yi kuka sabida rashin sabo

Ta gefen ido duk Umar Faruk yana kallon ta, a ransa kuwa dariya ta ba shi yana mamakin sangarta irin nata domin ya kula tsayuwar nata ne ya dame ta take shirin kuka. Sai dai ya kasa yanda zai yi yayi mata magana bare yace, "ta zauna." Wanda hakan ne a cikin zuciyar sa

Shima Abdul ya kula da yanayin ta hakan yasa ya buɗe baki da ninyan yin mata magana

Sai Uncle Hashim yace, "Daughter, you are tired? Come here and sit down and let me out."

Murmushin yaƙe ta ɗan saki sai dai bata ce komi ba ganin inda yake nuna mata ta zauna ɗin, ma'ana a saman gadon shiyasa ta kasa motsa wa

Hajiya tace, "ai mu ma ba daɗe wa zamu yi ba, But before we leave, go and sit down since you are tired."

Kanta ta ɗan gyaɗa ta nufi wajen ta ɗofana mazaunan ta a inda Uncle Hashim ya matsa mata, hakan yasa har jikin ta ke gogan juna da cinyan Umar Faruk. A tare suka lumshe idanun su ko wanne yana jin wani abu ya tsirga mishi; wanda ita ta kasa jure wa dole ta sake jan jikin ta ta matsa gefe sosai ta yanda baza su haɗe ba.


           A haka dai suka zauna jigum sai su Hajiya da suke ɗan taɓa hira. Sai da wasu mutane da suka zo gaishe da Umar Faruk ɗin suka shigo sannan su Hajiya suka yi musu sallama suka fice a ɗakin. Manyan Mutane ne kusan su goma ƴan siyasa suka zo gaishe da shi.


          Uncle Hashim da MEEMA a mota ɗaya suka koma. Dayake zai sauke ta a wajen aiki. Yana zuwa ya sauke ta ya wuce tunda akwai inda zai je

Tunda ta shiga ciki suka gaisa da waɗanda ta ci karo da su ta wuce Office ɗin su. Sai dai tana shiga babu kowa sai ta tsaya ba tare da ta zauna ba. Tana shirin juya wa zuwa Office ɗin Idris sai wata me suna A'isha wacce itama aiki take yi a gidan t.vn, ita ta hange ta ta ƙariso wurin ta tana cewa, "Hi MEEMA".

"Hi." Ta amsa mata tana kallon ta

Murmushi A'isha tayi tace, "Today I thought you would not come, and Laɗifa did not come, and you is ok?"

"Fine. I went somewhere."

Isowar Idris wajen shi yasa A'isha ta yiwa MEEMA sallama ta wuce

Yana isowa suka gaisa yake tambayar ta, "Where are you going? I've just come to pick you up but your gate Man says you're all out."

"We went to the hospital."

"Subhanallah.. Who is sick?"

Shiru tayi, sai kuma tace, "This man we went to his house me and Laɗifa and interviewed, amm... Senate."

"Ok Senator Umar Faruk Aliyu, You went to him?"

Gyaɗa masa kai tayi da faɗin, "na'am."

"Ok I heard, right now I want to go and talk to him about the accident, now go to the office and rest when I finish my work so we can go together and talk to him. From there we go to greet Laɗifa and She is not feeling well."

Fuskar ta ne ya sauya tana ɗan sake buɗe manyan idanuwan ta tace, "really? I don't know, i didn't call her, easily her body?"

Ɗan numfashi ya ja kafin yace, "Calm down, insha'Allah. Her body is fine, but I just called her and she couldn't pick up the phone. Her mother informed me of her condition. Go inside and finish your work and we'll go."

Ɓata fuska tayi hawaye na ciko mata a idanu tace, "I can't work now until I see her condition. I'm scared."

Murmushi yayi a ransa yace, "MEEMA rigima! tana jin ta kamar wata yarinya ce." Sosai ya kula akwai dolanci da sangarta irin na ƴaƴan masu kuɗi a tattare da ita, irin waɗan da aka shagwaɓa ɗin nan sosai. komi nata tana yin sa ne tamkar wata ƙaramar yarinya, ba ta kunyar ta yiwa ko waye taɓara ko kuma tayi masa kuka, bata da wahalan kuka ko a gaban waye ne. "Fine. Let's go to my office and pass from there."

Kanta ta ɗaga mishi tana bin Bayan shi. Daga can bayan ya gama abinda zai yi suka fito suka wuce asibitin da aka kwantar da Senator Umar Faruk.







✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

          A can kuwa gida lokacin da su Hajiya suka koma. Me gadi na buɗe musu ƙofa Ummee ta tura hancin motan ciki. Tunda suka shiga suka ga wata jan mota wanda sun tabbatar ba na gidan bane

Me gadi na rufe Gate ɗin ya iso wurin su da gudu. A lokacin duk sun fito suna ƙoƙarin fito da Hajiya. Ya gaishe su yana cewa, "Hajiya dama baƙi ne suka zo nan gidan. Ga su can a cikin mota."

"Baƙi kuma?" Da Hajiya da Ummee suka haɗa baki wajen faɗa

"Eh wlh. Nayi yunƙurin tsayar da su daga waje amma sun ƙi tsaya wa, dole suka saka Ni na buɗe musu ƙofa suka shigo. Bari inyi musu magana sai su zo." Ya ƙare maganar yana wuce wa wajen motan da hanzari

Bayan yayi musu magana ne sai suka fito daga motan

Ai Ummee na ganin su ta gane su, Kawu Ali ne da Kawu Zubairu

Hajiya kuma sai da suka iso gab da ita itama ta shaida fuskar su

Su suka fara gaishe da Hajiya kafin itama ta saki fuska ta amsa su tana musu lale marhaban

Ita Ummee ta kasa musu magana sai kallon su da take yi, domin ta san halin su tunda ta gansu a nan ba alheri ne ya kawo su ba, baza ta manta sanda suke zuwa can Riyadh suke cin musu mutunci ba ita da Faruk da ɗiyar su. Sanadi har da rashin ƙaunar da suke nuna mata yasa ta bi ruɗin ƙawaye ta bar mijin ta a halin laluran da yake tsananin buƙatar ta ta taho nan. Daƙyar ta buɗe baki a yanzu ɗin ta gaishe su

Duk amsa wa suka yi fuska a ɗaure suna wani ciccin magani

Ita dai taɓe baki kawai tayi tayi gaba abin ta

 Hajiya ce ta ce musu, "su shiga ciki."

Sannan ne suka bi bayan su suka shiga Parlour. Sai da suka zauna aka ƙara gaisa wa

Kafin Kawu Ali ya soma magana da faɗin, "ba wani abu ya kawo mu nan ba sai maganar Zulaiha. To mu mun zo ne mu tafi da ita kawai babu wani kace nace duk da dai wulaƙancin da ɗana ya fuskanta zuwan shi nan, yarinyar nan ta ci mana mutunci ba kaɗan ba amma duk da haka muka biyo baya saboda a matsayin mu na dolen ta, ba don haka ba wlh babu yanda za'a yi mu tako ƙafar mu mu taho nan. Don haka sai ku bamu ita mu tafi da ita abun da ya kawo mu kenan."

Hajiya da ta zuba musu ido tana kallon su jin yayi shiru sai tace, "to Aliyu kake ko wa? Zancen gaskiya baku yiwa yarinyar nan adalci ba, ita a yanda ta faɗa mana so Kuka yi kuyi mata aure ba tare da amincewar ta ba, hasali ma bata san da zancen ba sai da biki ya zo. Hakan ai ba kyautuwa bane..."

Bata ajiye numfashi ba Kawu Zubairu ya tada jijiyan wuya da cewa, "to ke a ganin ki Hajiya har sai an tambaye ta sannan zamu iya mata aure? Muna da ƴancin da zamu iya aurar da ita ga duk wanda muke so, sannan shi wannan yaron ɗan mu ne haka itama ƴar mu ce, ganin babu ran mahaifin ta yasa muke so mu rufa mata asiri mu aurar da ita ga ɗan mu kamar yanda ya ce yana so, amma mu ma ba'a son ran mu bane tunda babu yanda za'a yi muna ji muna gani mu ɗaura wa ɗan mu yarinyar da ta gama gantale wa ta kasa auruwa, yarinyar da kaɗan ya girme mata don mun yanke wannan hukuncin shi ne zai zama abun magana? Ai idan ba'a gode mana ba baza ayi Allah wadai da mu ba."

Sosai maganganun Kawu Zubairu ya ɓata wa Hajiya rai

Ba ita kaɗai ba har Ummee wacce tana ji tana gani ana son aibata mata ɗiya. Shiyasa tayi saurin cewa, "maganar gaskiya Yaya bazai yiwu ace ku zo har cikin gidan mu kuna gaya wa Mahaifiya ta da ɗiya ta magana ba, idan na jure a baya wancan nayi shiru ne domin ɗan uwan ku, amma yanzu babu wanda zai zo har gidan mu ya ci mana fuska, ita MEEMA ai ɗiya ta ce kuma ta dawo hannu na baku da halin amsar ta, ita da kanta ta zaɓi nan don haka babu wanda a cikin ku zai tafi min da yarinya wani wuri."

"Auu iyeeeee! Wuyan ki ya isa yanka Zulai mu kike faɗa wa haka?" Cewar Kawu Ali a zafafe

Hajiya tace, "gaskiya ce ta faɗa, babu inda zaku je mata da ɗiya tunda ba arziki ne da ku ba."

Kawu Ali yace, "to wlh baku isa ba, dole sai mun tafi da ita tunda mu ne ya zama wajibi ta zauna da mu, idan ba haka ba wlh babu inda zamu je ƙafar mu ƙafar ta, har ku kun isa? Matsiyatan banza matsiyatan hofi! ɗan uwan mu ya bar dukiya dole ai ku ɗauke ta, meye bamu da labari a kai, nan ita uwar ta ta tafi ta bar su sai yanzu da kuka san ya mutu shi ne kuke da bakin cewa zaku riƙe ta, to zan gani, wlh tallahi sai dai kotu ta raba mu da ku."

"Yo kuce kuɗi kuka biyo ba yarinya ba? Akwai wasu matsiyata ne bayan ku? Tunda ba mutunci ne daku ba ku fice min a gida tun kafin ku ga abin da zai faru da ku, ƴan iska mara sa mutunci." Inji Hajiya itama a zafafe kamar zata tashi tsaban rigima

Nan fa sai cacan baki ya kaure wanda dole su Jalila ita da Zabba'u suka fito tunda su basu a wurin

Yanda suka taru suke ta cin ma ƴar tsohuwa mutunci ne yasa Ummee itama take tare mata

Jikin Jalila na rawa ta nufi ɗaki ɗauko waya ta kira Uncle Hashim ganin abun nasu ba na ƙare bane. Tana kiran shi ya ɗauka ta sanar mishi da halin da ake ciki

Kankace me ya kashe wayan da faɗin, "ga yi nan zuwa yanzu-yanzu."








✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

            Idris na Isa hospital ɗin ya faka motan suka fito suka shiga ciki. Sai dai koda suka je shiga ɗakin securities ɗin shi sun hana su shiga duk da Idris ya nuna I.D card ɗin shi

Da ya dame su da naci ne sai ɗaya security ɗin ya shiga ya sanar wa da Umar Faruk ɗin. Babu jima wa ya dawo ya sanar musu, "ba ya buƙatar hira da su."

Fitowar security ɗin ne ya bar ƙofan a buɗe wanda ya bai wa Umar Faruk damar hango kayan MEEMA, baƙin Abayar da ta sanya tabbas shi ne ya hango tunda dashi ta zo ɗazu. Sai leƙa kai yake yi sai dai ya kasa yin magana domin ya san ko ya ɗaga murya baza su ji ba, bare shi ba me son hayaniya bane. Yana kallo har suka tafi sai ya ɗan yarfa kai gefe yana mayar da idanun sa ya lumshe su. Allah yasa sai ga security ɗin ya shigo da sauri ya buɗe ido yana kallon sa ya sanar mishi, "yayi maza ya kira mishi Macen tazo."

Hakan yasa ya fita da sauri ya isa haraban Hospital ɗin

A lokacin har sun shiga mota Idris na ƙoƙarin tayar wa

Sai ya isa wurin da sauri. Ya tsayar da shi yana faɗa mishi saƙon Umar Faruk ɗin. Ganin Idris ɗin zai fito sai yace dashi, "ita kaɗai yake buƙata."

Koma wa yayi ya zauna Idris ɗin yana duban MEEMA wacce take zaune a cikin motan. Bata ma san me suke cewa ba tunda hankalin ta na kan waya tana latsawa. Yace da ita, "MEEMA come out and join Senator Umar Faruk he wants to talk to you."

Duban sa take yi da mamaki but taƙi yin magana sai ɗan ƙara buɗe kyawawan idanuwan ta da tayi

"Yes. He said he should be called you. I think you will talk together." Sai ya miƙa mata recorder ɗin hannun shi yace, "Go with this and discuss."


Ɗan jim.. tayi tana kallon shi, sai kuma ta saka fararen hannayen ta ta amshi recordern ta fice. Bayan security ɗin tabi har zuwa ɗakin da yake ciki. Shi security ɗin ya tsaya a waje ita kuma ta tura ƙofan ta shige a hankali kamar wacce take tsoron shiga.
[14/10, 10:01 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                     💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*



*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

















                      *NO_26*

Tunda ta turo ƙofan ta shigo idanun sa na kanta ya kasa ɗauke su

Ita kuma ganin kallon da yake mata yasa ta kawar da kai tana takowa a hankali zuwa cikin ɗakin, tsayawa tayi ta kasa ƙarisawa illa sauraron bugun zuciyarta da ke ƙara hauhawa take yi

Shi ne yace mata, "Come and sit down here." Ya nuna mata kujeran da ke bakin gadon nashi

Hakan yasa ta ɗan kalle shi sai kuma ta taka izuwa kujeran ta zauna a hankali. Kanta a ƙasa ta kasa ɗagowa

Sai ɗakin yayi shiru illa shi da yake faman kallon ta ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a kanta, be san meyasa ba tunda ya fara ganinta ta tsaya mishi a rai, ba ya gajiya da kallon kyakykyawar fuskar ta hakan yasa be iya control kansa, wani lokacin be ma san yana kallon ta ɗin ba sai daga baya yayi ta mamakin kansa. Yanzun ma daƙyar ya iya buɗe baki yace, "Do you need anything from my place?"

Kanta ta ɗago ta kalle shi a wannan lokacin sosai sai dai fuskar ta babu walwala. Bata iya ce mishi komi ba illa kallon shi da take yi

Shima sai ya tsira mata ido yana kallon cikin idanun ta yayinda yake jin tamkar wani abubuwa suna jansa izuwa cikin nata idanun

Ta kasa jure wa ta ɗauke idanuwan ta tana mayar da su ƙasa. Sai kuma a hankali ta furta, "how your body?"

Yanda muryan ta ya bugi kunnen sa yasa ya lumshe idanun sa sabida daɗin sanyin muryan ta. Ya ɗau lokaci a haka kafin ya ware idon a kanta yana furta, "alhmadulillah. How did you get home?"

"Fine." Tafaɗa a taƙaice. Sai kuma ta ɗan ɗago ta dube shi da cewa, "We want to talk about your accident. If you don't mind I'd like to talk to you?"

Idanun sa cikin nata yace, "I don't want to talk to journalists. I have nothing to tell you. And I see that you want to restrict me."

Jin maganar nasa yasa ta tashi tsaye still tana kallon shi, sai dai bata ce komi ba ta juya ta fice tana mamakin, "to meyasa ya kira ta idan babu abinda zai ce da su?"

Shi kuma ya kasa tsayar da ita yana kallo ta fice domin be san me zai ce mata ba, shi dai ya bi umarnin zuciyar sa ne wacce ta saka shi ya kira ta ba shi da abun ce mata.

Tana isa wajen motan ta buɗe ta shiga

Idris da ke faman jiran ta kallon ta yayi ya tambaye ta, "Did you interview him?"

Girgiza masa kai tayi kamar baza tayi magana ba sai kuma ta kalle shi tace, "He says he doesn't need to talk to us."

Mamaki ne bayyane a fuskar sa, sai yace, "But why does he need to see you if not the interview would bother us?"

"I don't know." Tafaɗa a hankali tana kawar da kanta gefe

Shima be ce komi ba ya ja motan suka fice. Sai da ya cilla motan a kan titi kafin ya sanar mata, "their house Laɗifa will pass."

Bata ce masa komi ba har suka kai bakin gidan

Ya taka birki suka fito suka shiga cikin gidan su Laɗifa. Da Umman ta suka soma cin karo a tsakar gida don haka Idris ya gaishe ta. Itama MEEMA ta gaishe ta da Hausan jin Idris ya gaishe ta

Cike da fara'a ta amsa musu tana musu lale marhaban. Kana kuma tayi musu jagora zuwa ɗakin nasu

Suna shiga suka ga Laɗifan a kwance a saman kujera

Ganin su yasa ta tashi zaune da murnan ta tana washe baki, duk da kana kallon ta zaka fahimci tana jin jiki amma hakan be sa ta ƙi nuna farin cikin ta da ganin su ba

Idris da ya ƙware wajen tsokana sai ya kama haɓa yana cewa, "Umma anya yarinyar nan ba ciwon aure ne ke damun ta ba? Dama na faɗa miki ki gaggauta aurar da ita kin ƙi, kullum ita ciwo ba ta shafe sati bata yi ciwo ba."

Dariya Umma tayi

While ita kuma Laɗifa hararan shi tayi tace, "masharranci kawai, kai me ya hana ka auren sai Ni zaka ce nayi? Idan ka gaji da gani na ka aurar da Ni mana." Sai kuma ta kalli MEEMA tace, "Sister come here and sit."

Zama MEEMAN tayi a gefen Laɗifan

Idris da shima ya sami wuri ya zauna sai ya taɓe baki yace, "ai Ni bani da kuɗin miki aure, amma zan sanar wa Baba tunda naga alamu aike na kike yi. Wlh ina faɗa miki yarinya gwara kiyi auren ki kar ki biye ta tawa, Ni yaro ne har yanzu ban isa aure ba idan kika ce sai kin jira Ni ai kuwa zaki yi kwantai a gida don Ni ba take nake yi ba, bar gani na haka na san abun da yake zuciyar ki."

Ɓare baki tayi kamar zata yi kuka tace, "Umma kin gansa ko ki ce ya dena ba na so, nima me zan yi da kai ai kayi min ƙanƙanta."

Zaro ido waje yayi, zai yi magana kuma sai suka haɗa ido da Umman, sai ya kwashe da dariya yace, "Allah arziƙin ki ɗaya akwai Umma da sai na faɗa miki magana Al'ƙur'an."

Umma tace, "ai Ni Idris ba kunyata kake ji ba da kayi maganar ka ma. Hmm Allah ya shirye ka baza ka sauya hali ba wlh."

Dariya kawai yake yi

Laɗifa kuma bata kula shi ba illa riƙe hannun MEEMA da tayi tana kallon Umman nata tace, "Umma wannan ita ce MEEMA wacce nake baki labari ƙawata."

Murmushi tayi Umman tace, "Masha Allah ga ta kyakykyawa, Ashe Zulaiha tana da yarinya kamar ta ban taɓa sani ba wlh. Sannu ƴar nan ga shi ko ruwa ban kawo miki ba, na zauna ina jin shirmen Idris."

Dariya yayi yace, "ai Umma bata san me kike cewa ba. Bari Ni in taimaka in ɗauko mata ruwan." Ya tashi izuwa wurin Fridge ɗin

Ita kuma Umma tace, "au ba ta jin Hausa ne?"

Laɗifa tace, "eh Umma, har yanzu ta kasa koya wlh, kuma kwanaki har na fara koya mata amma ko tunawa ba tayi." Ta ƙare maganar tana dariya

"Allah Sarki." Cewar Umman. "Da sannu zata iya tunda tana tare da mu Hausawa."

Ruwan da Idris ya kawo mata MEEMAN ta amsa ta kurɓa kafin ta ajiye. Cike da sanyin murya tace da Laɗifan, "I'm worried about you, but I'm glad to see you. God get well soon."

Murmushi Laɗifa tayi tace, "Ameen thanks MEEMA."

Idris yace, ,"ai ta warke sosai. Get up and let's go since

Please Login or Register in order to submit comment