Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

not coming until today, please be patient. May God have mercy on Abee and forgive him". Zamiya tafaɗa idanuwan ta a kan MEEMA da ta riƙe mata hannu

Murmushin yaƙe MEEMAN tayi kafin tace, "no problem, thank you very much for your coming".

Cike da fuskar tausayi Zamiyan tace, "Are you alright now? But you are not going to be alone in this house, are you? You should go back to Ummee."

"We've already told her, if she doesn't come back she will follow ME to our house." Ummu Hani Said

Kallon su kawai MEEMAN take yi, sai dai gaba ɗaya a ranta damuwa ne ke damun ta, duk da har yanzu basu san asalin abinda yasa Ummeen ta ta tafi ta bar su ba, ta sanar musu cewa, "Ummee sun rabu da Abee ne". Dalilin da yasa ta tafi ta bar su kenan, domin ba ta fatan su san real labarin, tana ga kowa ya ji dole ne zai yi tirr da mahaifiyar ta, abun kunya ne ma a gare ta ace an san Ummeen ta ta tafi ta bar su. Shiyasa kawai da suka matsanta mata sai tace musu, "dama tana da ninyar zuwa Nigeria wajen ta".

A ranan a gidan suka wuni kafin suka wuce suka bar ta da Zamiya don a wajen ta zata zauna. Zaman Zamiyan na kwana biyu yasa ta ɗan sake jikin ta sosai saboda tana jan ta da surutu tare da mata abinda zai ɗebe mata kewa, shiyasa da zata tafi tayi kewar ta sosai har ƙwalla tayi.


            Zuwa kwana biyu duk ta gama haɗa kan komi na Abee ɗin ta, lauyan Abee shi yayi mata jagora ta haɗa takardun ƙadarorin shi da ya mayar da sunan ta, dama already duk dukiyan sa ya mayar mata a account ɗin ta kafin ya rasu, lauyan ta saka ya samo masu siyan companies ɗin suka taya, da fari ta so siyar da su duka ne sai kuma ta sauya shawara aka yi cinikin ɗaya, ɗayan kuma ta danƙa shi a wurin Lauyan Abee zai riƙa kula mata dashi sai kuɗaɗen su riƙa shiga account ɗin ta.




             A ranan da zata tafi Nigeria kuka sosai ta sha, haka ma house Girl ɗin su da duk masu aikin gidan, babban Trolly ta cika da kayan ta da sauran abubuwan amfanin ta, har computers ɗin ta dana Abee duk ta haɗa ta tarkata, sai kuma ɗan ƙaramin Back Shima da ta cika iyakan abubuwan da ta kwashe a gidan, gidan kuma ta danƙa a hannun su don ta kasa siyarwa, za su ci gaba da kula dashi tana tura musu albashin su ta account

Gaba ɗayan su da drever suka raka ta har airport ta hau jirgin da zai wuce Nigeria. Seat ɗin ta na line 3 ne, ita ce a ciki shiyasa tunda ta zauna ta kafa kanta a window ta mayar da idanuwan ta ta rufe. Har jirgin ya cika ana ta maganar a saka belt while bata motsa ba

Wanda yake gefen ta da ya gama saka nashi a karo na farko sai ya kalli inda take, kamar bazai yi magana ba domin har ya kawar da kansa sai kuma ya sake kallon ta yace, "excuse me". Bata ji sa ba har sai da ya saka hannu ya buga jikin kujeran nata kafin tayi firgigit tana kallon sa idanun su cikin na juna. Janye nasa yayi yana ɗan lumshe su kafin ya buɗe, ba tare da ya kalle ta ba yace, "put on your belt".

Sai a lokacin ta janye nata idanun tana kallon jikin ta, sai kuma ta saka hannayen ta a kasalance ta saka belt ɗin ta sake kafa kanta a window, sai dai a wannan lokacin bata rufe idanuwan ta ba waje kawai take kallo, bata sake motsa wa ba har sanda aka zo tambayar su abinda suke so a kawo musu. Ko juyo wa bata yi ba ta girgiza kanta alamun ba ta son komi

Wanda ke gefen ta shima be amshi komi ba, jarida kawai yace, "a kawo masa." ya kara a fuskar sa yana karanta wa. Shima ɗin be sake motsa wa ba har jirgin nasu yayi landing a garin Abuja.



              Sai da aka soma fita tukun MEEMA ta ɗago kanta ta kalli wanda ke kusa da ita da yake ƙoƙarin tashi zai ciro jakan sa, murya a matuƙar sanyaye tace, "Afuwan uridu an as aluk".

Ɗago idanuwan sa yayi ya zuba mata su ba tare da yayi magana ba

Hakan ne yasa ta ɗan dafe goshin ta kuma sai ta maimaita masa da harshen turanci, "Please I want to ask you".

Ɗauke kansa kawai yayi ya mayar kan jakan sa, sai da ya sauko kafin yace da ita, "I hear you".

Ran MEEMA babu daɗi tace, "We come to Yola?"

Be san sanda ya kalle ta ba jin abinda tace, ƙare mata kallo kawai yake yi yana nazartan ta

Ita kuma ganin kallon da yake mata sai ta ɓata fuska tana tura baki tare da ɗauke kai

Hakan yasa ya waro idanu waje still idanun sa a kanta, be furta komi ba ya ɗauki kayan sa ya wuce

Da kallo tabi bayan sa zuciyar ta cike da haushi, sai kawai taja tsaki tana miƙe wa itama ta soma ciro nata kayan ta fita a jirgin. Tun da ta saka ƙafafuwan ta a waje take bin duk inda Allah ya kai idanuwan ta da kallo, wannan shi ne rana ta farko da ta taɓa zuwa Nigeria a rayuwar ta, duk da ta sha jin labarin ƙasar wajen mahaifin ta amma bata taɓa mayar da hankali a kan wai tana son ta ga ya ƙasar take ba koda a hoto ne, ko kuma tazo ta gani a matsayin ƙasar iyayen ta, in fact ma ita ko sau ɗaya bata taɓa jin ƙaunar ƙasar ba, amma yau sai gata a cikin ta, shiyasa ta zama kamar village Girl sabida yanda take kallon mutanen ciki, daƙyar take ma iya tafiya tsaban kalle-kalle har tuntuɓe take ci. Bata san ina zata nufa ba shiyasa ta tsaya a tsakiyar airport ɗin tana ta ganin yanda mutane ke zirga-zirga, duk da dare ne amma gaba ɗaya wajen ya haske da ƙwan fitila. Sai da ta ji ƙafafuwan ta sun soma gajiya kafin ta tasar wa ƙofan da ta ga ana fita. Yawanci ganin mutane take yi sai hawa mota suke yi suna tafiya, sai kuma wasu suna wuce wa wajen ƴan taxi suna hawa, da yanda kuma masu taxi ɗin suke biyo fasinja suna tambayar inda za su je. Hakan yasa itama ta nufi can ɗin kanta tsaye tana jan kayan ta daƙyar

Ɗaya na hango ta ya taho da sauri yace da ita, "tafiya zata yi?"

Bata san me yace ba shiyasa tace mishi, "I'm going to Yola".

"Yola kuma Hajiya? Ai babu inda zaki samu motan Yola a nan, gwara ma ki kama hanya ki san inda dare yayi miki". Ya wuce abin sa yana ci gaba da tare fasinja

Tsaye tayi a wurin kawai don bata fahimci inda zancen nasa ya nufa ba



Wani yana hango ta shima ya zo ya hau tambayar ta inda zata je

The same amsar da ta bawa wancan shi ta ba shi

Shi da yake ya iya turanci sai ya sanar mata, "babu motan Yola a nan, saboda yanzu dare yayi baza ta samu ba sai gobe".

Jin hakan yasa ta roƙe sa a kan,
"Take her to Yola. She will give him whatever it is."

Cikin turancin yace mata, "Madam nan fa Abuja kike ba Yola ba, tafiyan da zamu yi awanni taya zan ɗauke ki a wannan tsohon daren? yanzu fa ƙarfe 09:00pm".

Bata kai ga yin magana ba mutumin da suka zauna tare a jirgi ya iso wajen. Kallon me motan yayi fuskar shi babu walwala yace, "mu je ka kai Ni barikin sojoji".

"Ok to". Me taxi ɗin ya amsa mishi da sauri yana amsar Jakar sa ya wuce mota shi kuma ya bi bayan sa. Bayan ya saka mishi kayan a cikin Boot sai ya dawo wurin MEEMA da ke tsaye kamar status a wurin ta kasa motsa wa yace da ita cikin turanci, "ta faɗa inda zata je ya sauke ta sabida motoci sun ƙare, idan ba haka ba zata sha wahalan samun abun hawa idan ta bar wurin".

Hotel kawai ta iya furta wa a laɓɓan ta

Shi ne yace, "to su je". Taimaka mata yayi da kayan suka wuce, ya sanya mata a Boot

Ita kuma ta wuce ta buɗe baya zata shiga. Ganin mutumin hakimce a bayan motan sai ta ja ta tsaya ta ƙi shiga

"Madame, enter. We are in a hurry."

Maganar da me taxin yayi ne ya ankarar da shi na cikin motan ma, don a lokacin wayan sa yake duba wa ko ɗago kai be yi ba. Idanu suka haɗa dashi sai yayi saurin ɗauke nasa

While itama hakan ne, rufe motan tayi ta koma gaba ta shige

Me taxi ya ja motan suka tafi

Babu me motsi a cikin motan har sanda suka isa wani kyakykyawan Hotel ya tsayar da motan, sannan ya kalle ta yace, "Madam here is ok?"

"Is that Hotel?" Ta tambaye sa tana kallon sa

"Yes, it's a hotel. Look at the name there."

"Ok" kawai tace tana shirin fita

"Your money is two hundred Madam".

Shaf ta manta shiyasa ta dakata tana juyo wa ta kalle sa, cikin sanyin murya tace, "give me your account number".

"Account number? Two hundred You paid for my account? I don't have it. Just give me Cash."

"Sorry I don't know how much money you are using, and I don't have money now in my hand, I will pay you through my account".

Zai yi magana suka ji muryan mutumin nan na baya yana cewa, "wai zaman me kake yi ne? Ka sallame ta mu tafi."

Dayake ita bata ji me yace ba tunda da Hausa yayi

Shi kuma me taxin yace, "kayi haƙuri don Allah haƙƙi na zata bani".

"Mu je zan biya". Cewar sa ba tare da ya ɗago kai daga latsa wayan da yake yi ba bcoz hasashen sa ya ba shi kamar ita baƙuwa ce a ƙasar, domin yanayin ta da shigan da tayi ya nuna ba ƴar nan bace

"Ok madam let's go take your Trollys off, he said he'll pay your bill".

"WHO?"

"This is in the car."

Kallon sa tayi ta ga hankalin sa na kan waya ne. Bata ce komi ba ta buɗe motan ta fice, Sai da ta fita ne kuma ta leƙo kaɗan tace dashi, "shukran".

Be yi ninyan ɗago wa ya kalle ta ba, amma jin yanda sassanyan muryan nata ya daki kunnen sa hakan yasa ya ji kwaɗayin sake tozali da ita

Ai kuwa idanuwan nasu suka shige cikin na juna. Ita ta soma janye nata idanun tana juya wa ta tafi domin already shi me taxi ya gama ciro mata kayan ta

Shiga motan yayi ya ja suka bar wurin

A hankali ta ja kayan nata ta nufi Hotel ɗin. Ta samu masu aikin don basu tashi ba, faɗa musu tayi, "she needs a room".

Babu ɓata lokaci suka yi mata bayanin dokokin Hotel ɗin tare da bata takarda ta cike bayan ta biya su kuɗin ta account, sannan suka bata keey ɗin ɗakin bayan ɗaya tayi mata jagora har zuwa bakin ƙofan ɗakin

Murɗa ƙofan tayi ta shige ciki, a bakin ƙofan ta tsaya ganin ɗakin da duhu, sai ta laluba jakar ta ta ɗauko wayan ta ta haska, a nan ta samo inda abun kunna glof ɗin ɗakin yake ta kunna, ta mayar da ƙofan ta rufe. A hankali ta taka ta isa kan sofa ta zauna tana me bin ko ina da kallo yayinda fuskar ta take a cikin tsantsan damuwa. Tunda ta zauna bata iya motsa wa a wurin ba domin kwantar da kanta tayi a kan kujeran ta mayar da idanuwan ta ta rufe, a haka ta zauna na tsawon wani lokaci. Daƙyar ta iya tashi ta rage after dress ɗin ta ta koma ta ƙudundune a kan sofa ɗin, yanda take ji gaba ɗaya jikin ta babu daɗi har zazzaɓi yake son kama ta, hakan yasa ta kasa taɓuka komi, ga shi kuma barcin ya ƙi zuwan mata don tsananin damuwa da tunani sun yi mata yawa, gaba ɗaya kewar Abee ɗin ta ya cika mata zuciya har hawaye take tsiyayar wa. Ta raba daren a haka bata iya kataɓus ba kuma ta kasa barci, sai daga baya ta tashi ta shiga Toilet tayi alwala ta soma gabatar da sallolin da ake bin ta. Bayan ta idar ta ɗaura da nafila tare da nema wa Abee ɗin ta rahamar Allah. Sai da aka kira sallan subahi kafin ta dakatar da nafilolin da take yi ta gabatar da sallan subahi ɗin. Tana idar wa wani nannauyan barci ya kwashe ta a wurin. Bata farka ba sai taran safe, lokacin daƙyar ta iya tashi a wurin saboda tsaban yanda jikin ta yayi mata nauyi da tsami, daƙyar take iya ɗaga ƙafafuwan ta haka ta isa cikin Toilet ta fito ta zauna a kan kujera, idanuwan ta duk sun gama sauya kala sun kumbura sosai daƙyar take iya buɗe su, da gani ka san damuwa ce da rashin barci ishashshe ya mayar da ita haka. Ta fi mintuna talatin a zaune a kujeran ta kasa motsi.

               Sai wajen ƙarfe Goma kafin tayi odan abin da zata ci aka kawo mata. Dama har da yunwa ya galabaitar da ita amma sabida rashin daɗin bakin ta yasa ta kasa saka komi a cikin nata tun jiya. Daƙyar a yanzu ɗin ma tayi Breakfast ɗin, ko kaɗan abincin be mata daɗi ba dole ta koma tayi odan tea ta Sha sosai sannan ta tashi ta shiga Toilet, wanka tayi ta fito tayi shirin ta, riga da wando ta saka a ciki, sannan ta ɗaura after dress blue color, tayi rolling kanta da ɗankwalin Abayar babu abinda ake gani nata sai kyakykyawar cuty face ɗin ta da ta sake yin haske sosai tayi fayau kamar mara lafiya, komi bata saka a fuskar nata ba ta tattara kayan ta ta fito. Kai tsaye wajen reception ta wuce ta mayar musu da keey ɗin sannan tayi musu sallama ta fice. Har ta fita hotel ɗin baki ɗaya sai kuma ta juya ta dawo ta tambayi ɗaya daga cikin masu aikin tace mata, "She needs to go to Yola, please tell her where to find a car to take her?"

"Ok but don't say I'm full of questions, aren't you a native of this country? Because of your temperament and the way you speak English you are not Nigerian." Cewar receptionist ɗin cikin fara'a

Gyaɗa mata kai MEEMAN tayi ba tare da ta furta komi ba

Murmushi ita kuma tayi tace, "Yes I can understand. You are really beautiful. "

"Thank you". Tace da ita itama tana murmusawa

"Okay, I'll help you get there Bus Stop and get a car there."

"Ok no problem".

Ita kuma matar fita tayi ta shiga cikin hotel ɗin, babu jima wa ta dawo ita da wani na miji. Sai ta nuna masa MEEMA tace, "ita zaka kai Tasha, sai ku yi magana da ita zata biya ka". Sannan kuma ta kalli MEEMAN tace, "This will take you".

Godiya MEEMAN tayi mata sannan suka fice ita da saurayin. A cikin keke napep ɗin sa suka wuce ya kaita tasha. Shi ta roƙa ya taimake ta ya sama mata motan da zai kaita Yola. Taxi ya samo mata tace, "she will pay in full and be taken alone".

Me taxi da ya ji zunzurutun kuɗin da zata biya shiyasa ya amince zai kaita ita kaɗai

Haka shima me napep ɗin ta biya sa kuɗi me yawa sannan suka tafi

Sai da tace, "It has started to change where it will change Nigeria's Money".

Bayan sun je shi ya amsa ya canzo mata kafin suka tasar wa hanyar Yola, tafiya suke sosai don tsula gudu kawai yake yi. Duk da haka sai magriba suka shiga cikin Adamawa

Me taxi ɗin tambayar ta yayi, "inda zai wuce da ita ya sauke ta?"

A nan ta sanar dashi address ɗin gidan su Abee ɗin ta, da sunan me gidan, kasancewar gidan yayi suna domin Kakan sa Alh. Riskuwa shi ya fara zama a anguwan nasu, shiyasa zai yi wuya idan ka je ɓarayin a kasa gane gidan nasa, kaf anguwan babu wanda be san gidan Alh. Riskuwa bafulatani ba duk da a yanzu ɗin jikokin sa da tattaɓa kunnen sa suke zaune.



         Duk da haka me Taxi ɗin ya sha wahala yana tambayar gidan kafin ya samu wanda ya san anguwan ma, dayake ba ta ɓarayin suka sauka ba. Sun kai bakin gidan wajen ƙarfe 09:12pm na dare. A nan ya sauke ta ta biya shi kuɗin sa. Sai godiya yake mata saboda kuɗin da ta ba shi masu yawa ne, haka ya ja motan nasa ya tafi

Ita kuma tana tsaye tana bin anguwan da kallo ko ina tsit kake ji babu kowa, don har wasu sun kulle gidajen su, dare yayi sosai sai dai akwai hasken farin wata. MEEMA bata saba tsintan kanta a irin wannan rayuwan ba shiyasa duk ta tsure jikin ta har rawa yake yi, daƙyar ta iya ƙarisa wa bakin Gate ɗin gidan ta hau buga wa tana yi tana kalle-kallen bayan ta.



           Ta jima a wurin tana buga wa kafin me gadin ya fito da goran sandan sa yana haske-haske da tocilan hannun sa, a fuskar MEEMA ya sauke yana dalle ta da cewa, "kee lafiya daga ina?"

Hannu ta sanya ta rufe fuskar ta tana kau da kai, bata iya magana ba domin bata san ma me yake cewa ba

Shi kuma ƙara dage wa yayi yana haska ta don a tsorace yake da ganin ta, musamman kyawun nata da ganin ta fara fatt da yayi. Daure wa yayi kawai yana sake tambayar ta, "daga inda take kuma wa take nema?"

"Please remove this item on my face". Tayi maganar tana ɗan goce wa

Dayake shi kuma ya iya turancin sai ya kawar yana sauya harshe ya sake tambayar ta, "Where are you from, Ma'am? Please leave there before I hit you."

"It was here that I was told the house of Uncle Aliyu my father's Brother to his place I came." She spoke looking at him

Me gadin sake haska ta yayi sosai har yana leƙe kafin yace, "You mean you come his home?"

"Yes".

"So stop here let me go and let them know". Yafaɗa yana garƙame Gate ɗin ya wuce

Ita kuma jingina tayi da jikin Gate ɗin tana ta kalle-kalle

Har sanda ya dawo shi da Kawu Zubairu yana cewa, "ina take ne?"

"Tana waje". Inji me gadin. Da sauri ya buɗe masa Gate ɗin suka fita suna haske ta da tocila


"Zulaiha". Cewar Kawu Zubairu yana sake haska ta da kyau don sake gasgata idanun nasa.


 



_bakwa yin Comments. Gaskiya zan dena tunda ba kwa so._
[08/10, 2:57 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                         💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍




*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*




               *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._



*KAN MATSALAR KASANCEWA A TSAYE ANA SALLAH*
      _Rahamar Allah tana isowa, mun samo labarin wani shahararren mai kawo hadisai da ake kira Abu Ishak Subaihi wanda ya rasu yana da shekara ɗari. A kan ji shi yana cewa, "Kash! Wannan rauni na zurfin shekaru ya hana mini more ma doguwar sallah. Yanzu a raka'o'ina biyu Baƙara da Al-imrana kaɗai nake iya karantawa." Su kuwa surorin nan biyu sun kai kamar ɗaya bisa takwas na Alƙur'anin gaba ɗayan su._
_Shi kuwa Hafiz Ibni Ƙayyam yayi nazarin irin fa'idojin da ake samu daga sallah ne ya jero su da cewa, "sallah tana tabbatar mana da samun abincin yau da kullum, ta kawo lafiya, ta kore cututtuka, ta ƙarfafa zuciya gami da faranta ta, ta kawo haske ga fuska, ta sabunta jiki, ta kawar da lalaci, ta haskaka zuciya, ta daɗaɗa ta, ta rage mata jin nauyi kana ta yiwa mutum albishir da rahmar Allah. Tana kasancewa garkuwa ga azabar Allah, tana tsare mu daga shaiɗan ta kuma kusanta mu da Ubangiji. A taƙaice dai; sallah lamuni ne na duk wani abin so kuma garkuwa ce ga duk wani abin ƙi na zuci ko na jiki a wannan duniya ko lahira." Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin ya Allah._














                            *NO_12*

              Bata iya magana ba sai kallon sa da take yi

"What happened to bring you here? Where is your father?"
Ya sake jero mata waɗannan tambayoyin

Wannan karon ma bata ba shi amsa ba

Dole ya kalli Me gadin yace da shi, "ya ɗauko mata kayan nata ya shigo da su," sannan yace mata, "she follow him".

Shiga suka yi gidan suka wuce Part ɗin Kawu Ali. Sai da yayi Nocking kafin ɗiyar sa Murjana da suke zaune da Umma a parlour'n suna kallo ta zo ta buɗe masa jin muryan Kawu Zubairun

"Lafiya me ke faruwa? Wace ce wannan kuma?" Inji Umma domin itama ta taso ta biyo Murjanan a baya a tunanin ta ko babu lafiya ne

Shi kuma yace mata, "baki gane ta bane? Zulaiha ce ƴar wurin Faruk".

"Faruk.. Faruk dai ɗan uwan ku na Riyadh?" Ta ambata tana sake ƙare wa MEEMAN kallo

"Eh shi. Kira min Yayan nawa sai ki sanar masa do Allah".

"To shikenan bari in shiga in Kira sa".

"Ke kuma ki zo ki zauna kin wani tsaya a tsaye". Inji kawu Zubairun yana kallon MEEMAN dake tsaye har yanzu a bakin ƙofa. Ganin bata motsa ba sai ya tuna ai ba ta jin Hausa sai ya kuma maimaita mata da turanci

Hakan yasa ta tako a hankali tana bin ko ina da kallo ta zo ta ɗofana mazaunan ta a kujeran

Itama Murjana zama tayi tana ƙare mata kallo kafin kuma ta kalli Kawu Zubairun tace, "wai Kawu wannan ɗin ita ce yarinyan Uncle Faruk ɗin?"

"Eh ita ce mana baki ga sun yi kama da uban nata bane?"

Taɓe baki tayi tana sake ƙare wa MEEMAN kallo don bata taɓa sanin ta ba, a kaf gidan ma babu wanda ya san ta illa labarin ta da suke ji, sai kuma su Kawu Ali da suke zuwa can ɗin shi ne suka santa.



              "Ina Zulaihan take?" Inji Kawu Ali da ya fito da sauri daga ɗaki Umma na take masa baya. Ganin ta yasa yace, "ashe dai ba ƙarya Jamila take min ba itan ce da gaske, ikon Allah". Yafaɗa yana zama gefen Kawu Zubairu idanuwan sa a kan MEEMAN, kafin kuma ya juya yana tambayar Kawu Zubairu, "a ina ya samo ta?"

"Nima wlh Ina tsaye a bakin ƙofan sashi na na hangi Gali Yana taho wa, shi ne nake tambayar sa lafiya ina zai je? Yake sanar min wai baƙuwa ce ta zo kuma wurin ka ta zo shi ne zai zo ya sanar maka, Ni kuma nace mu je in ganta".

Kawu Ali yace, "to ke wa ya nuna miki gidan namu? Waye ma ya kawo ki ƙasar? Ina uban naki?"

"Kaima ka san ba ta jin ka tunda ba iya Hausa tayi ba". Cewar Kawu Zubairun

Shi shaf ya ma manta sai ya juya harshen yana sake tambayar ta

"My Abee is Dead".

"He died?" Suka faɗa a tare cikin wani irin farin ciki da ya kasa ɓoyuwa a fuskar su

Ita kuwa bata ma fahimci yanayin nasu ba sai gyaɗa kanta da tayi cikin muryan kuka take cewa, "yes he died and left Me". A nan take sanar musu da komi da mutuwar nasa da kuma wasiyyar da ya bata ta dawo Nigeria ta zauna

"Ka gani ko Zubairu ai Allah ba azzalumin bawan sa bane, tunda Ni na gansa a haka dama na san zai wula nan ba da jima wa ba, muka so mu taimake shi mu tafi da ita amma ya ƙi furr har shegiyar yarinyan nan tana mana rashin kunya, sai ga shi dai mu ne dolen ta ga shi ta dawo wurin mu, to uban wa yace mishi muna da

Please Login or Register in order to submit comment