Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

want to marry her if there is no problem, because.." sai ya ɗan ja numfashi kafin yace, "because she entered my soul. I love her!"

Farin ciki ne ya bayyana a fuskar Uncle Hashim, cike da tsantsan farin ciki yace, "da gaske kake yi Aboki na?"

"Yes." Yafaɗa yana gyaɗa mishi kai

"Oh I can't tell you how happy I feel in my heart, naji daɗin abun da ka faɗa, insha Allahu zan shige maka gaba a kan samun ta, ina bayan ka dude because you fit so well."

Murmushi kaɗai Umar Faruk yake yi be sake cewa komi ba, shi kansa a zuciyar sa farin ciki ne yake ɗawainiya da shi, yana ga hukuncin da ya yanke hakan shi ne dai-dai, zuciyar sa zata fi aminta da ita a kan ta zame mishi Abokiyar rayuwa, ya san hakan zai faranta ran Momy idan yau aka ce ya je mata da zancen ya samu matar aure duk da be da tabbacin ita MEEMAN zata amince, but yana sa ran hakan

Uncle Hashim yace, "Let's go back inside and wait for her to come back sai ku gaisa."

Daga nan gidan suka koma. A nan Uncle Hashim yake sanar wa su Hajiya abun da ke faruwa

Babu wanda be nuna murnan sa ba musamman ma Ummee da ta fi kowa farin ciki, tabbas ta ga dacewar ɗiyarta da Umar Faruk saboda shi Mutum ne me matuƙar kirki, ko ba komi hakan zai kusanta ta da ɗiyarta tunda zata yi aure a nan, kuma tana fatan ta ga auren ta yanzu tunda ta kai girman da ya kamata tayi aure domin rayuwar mu a nan daban da can inda ta tashi, 26/27years ai ya wuce ace har yanzu tana zaune babu aure.





               ******

       Koda MEEMA ta dawo babu wanda yayi mata maganar sai Uncle Hashim, sai yace mata, "she prepares and eat and a visitor comes to her."

Dayake lokacin yana parlour'n sama an kai shi ya zauna zaman jiran ta

"A visitor came over me?" She asked in surprise

"Yes daughter. Get ready and go find him."

Ɓata fuska tayi tace, "then Uncle why did you come of me?"

Dafe goshin sa yayi kafin ya kalle ta yace, "daughter please leave your questions and go to him, he will tell you what he has come to do."

Daƙyar ya shawo kanta da tambayoyin da ta tsare shi da su. Ta ci abinci sannan tayi wanka ta saka doguwar riga kamar yadda ya zame mata jiki, Abaya ce ja da kwalliyan Stones a gaban. Sai tayi Rolling da mayafin

Har zata fita sai Jalila ta shigo ɗakin ta ganta, tace, "Where are you going to go without a make up?"

Ido ta zuba mata fuskar ta da mamaki

Sai ta kamo hannunta ta zaunar da ita a gaban mirror ta soma mata shafe-shafe

Bata ce mata komi ba illa bin ta da take yi da ido. Sai da taga abun ya wuce gona da iri domin ita ta tsani kwalliya sosai a fuskar ta, "no Aunt I don't want. Leave me alone."

Murmushi ita kuma tayi tana kallon ta tace, "You're so beautiful."

Ɗan tura baki tayi tana kawar da kai

Ita kuma dariya tayi mata ta kamo hannun ta suka fice. Sai da suka fito ta saki hannun nata tace, "Go upstairs he waiting for you". Daga haka ta juya ta wuce Parlour inda su Hajiya ke zaune

Ita kuma kamar baza ta tafi ba sai kuma ta taka a hankali ta soma hawa matattaƙalan benen, tana zuwa bakin ƙofan da zata shiga parlour'n ta ja ta tsaya, tunani kawai take yi, "Then who came to her?" Bata da me amsa mata tambayar ta hakan yasa ta tura ƙofan ta shige. Sosai gaban ta ya faɗi kawai arba da shi da tayi zaune a saman kujera. Sai ta sake waro ido tana sake duban shi kamar wata status a wurin

Haka zalika shima kallon ta yake yi yana aiyana tsantsan kyawun da Allah ya bata, musamman yanzu da ya ganta da Powder a fuska ta saka kwalli a fararen manyan idanun ta, hakan ya ƙara fito da zallan kyan ta domin be taɓa ganin fuskar ta da kwalliya ba. Yanda ya ga ta tsaya ta ƙi takowa ne sai ya tashi tsam ya isa gaban ta

Idanun ta ƙirr a kanshi har yanzu tana mamakin ganin shi kuma tana son tabbatar da cewa, "Is he her guest?"

"Why did you stop here?" He spoke slowly looking at her

Hakan yasa ta ɗan ƙyafta idanuwan ta tana kawar da su, sai kuma ta sake ɗagowa ta kalle shi, ganin sun haɗa ido ta sake ɗauke kai

Shi kuma murmushi yayi yace, "Let's go and sit down." Sannan yayi gaba

Hakan yasa ta taka tabi bayan shi kamar an tsamo ta a ruwa coz yanda take tafiyar. Slowly she sat down in the chair looking at him, sai ta haɗa hannayen ta a saman cinyoyin ta ta dunƙule su wuri ɗaya tana sauraron bugun zuciyar ta da sauyin yanayin da ke baƙuntan ta

Shiru ne ya biyo bayan zaman nata. Shi kansa be san ta ina zai fara ba shiyasa kawai ya kafa mata ido yana kallon ta, sai da ya ɗau kamar mintuna biyar yana mulmula baki da tunanin ta inda zai fara kafin ya ɗan ja numfashi yana sake tsayar da idanun sa ƙyam a kanta ya soma kiran sunan ta

Hakan yasa ta ɗago dara-daran idanuwan ta ta sauke a kanshi wanda fuskar ta har ta soma tsatstsafo da zufa sakamakon halin da take a ciki

"I know you will be surprised to come to your place even though I know your Uncle has informed you." Sai ya sake jan numfashi ya ci gaba da faɗin, "MEEMA is nothing come to you but a word of love. I am currently in love with you That's why I let you know. I hope you will be the mother of my children if you don't mind." Still sai ya kira sunan ta

Kiran sunan ta da yayi a ƙarshen maganar nasa yasa ta lumshe idanuwan ta tana sake tamke hannun ta sosai

"I love you MEEMA! please trust me As your beloved please."

Sosai maganar nasa ya shige ta har cikin zuciya, sai dai ta kasa ko motsin kirki domin har zuciyar ta ta dena aiki a halin yanzu, maganganun nasa kaɗai ke kai kawo a cikin kunnuwan ta suna sake mata yawo tamkar yana sake maimaita mata. Bata san sanda ya iso gaban ta ba sai kawai ganin shi tayi durƙushe a gefen ta. Da sauri ta ɗaga kai ta zuba masa idanun ta wanda hakan yasa suka shige cikin nashi. Kasa ɗauke kai tayi domin yanda take jin wani baƙon yanayi na shigan ta sabida haɗa idanun da suka yi

Karantan yanayin ta yake yi na ɗan soconni kafin yace, "I want to hear your answer if there is no concern please."

Tsit tayi ta ƙi yin magana domin bata san me zata ce ba

"Okay I'll give you time to think, but you know I'm a big man I need your answer in a little while because I hope soon we will be husband and wife." Sai ya tashi tsaye yana tusa hannayen shi a aljihun wandon shi. Kamar zai yi magana a yanda ya kafa mata idanun shi, sai kuma ya fuszar da iska ya juya ya ɗan yi taku biyu kafin ya kalle ta yace, "I will go, good bye." Sannan ya juya ya fice.


                Ta kasa motsa wa a wurin tun fitan nashi. Idanun ta kawai ke motsi a jikin ta, sosai ta shiga wani yanayi da bayyana mata kalaman soyayya da yayi, ba wai don bata saba ji ba, hasali ma baza ta iya cewa kai tsaye ba ta ƙaunar shi ba sabida abubuwan da take ji a game dashi, amma kuma tana da wanda zuciyar ta take ƙauna har yanzu, "ISHAQ." zuciyarta ta furta mata. Har yanzu shi ne a zuciyar ta, tana son shi matuƙa kuma shi take da burin ta aura, but bata san meyasa ba tana jin wani irin shauƙi tare da marari a zuciyar ta wanda take ji tamkar shi ne ya fi dacewa da ita, bata san meyasa ya tsaya mata a rai ba musamman yanzu da ya gama bayyana mata abun da take ji kamar tana buƙatar jin sa a bakin sa. Yanda zuciyar ta take bugawa a halin yanzu sabida tunanin da suka cinkushe mata yasa ta tashi da sauri ta nufi ƙasa ta shige ɗakin ta. Kan gado ta faɗa tana mayar da idanun ta ruf ta rufe. Ta jima a haka bata sake yin motsi ba kuma bata ba wa zuciyar ta damar yin wani tunani ba, har sanda Uncle Hashim ya shigo ɗakin bayan Nocking ɗin da yayi mata. Tashi tayi zaune tana kallon sa

Shi kuma ya zo ya zauna a gefen ta kana yace, "MEEMA I want to talk about something understands." Sai ya saka hannu ya kamo hannayen ta biyu ya haɗa da nashi. Cikin ido yake kallon ta yace, "I know you heard what my friend brought to you. He loves you very much and wants to marry you. What did you say?"

Shiru tayi tana sauke kai ƙasa

Sai ya saka hannu ya kamo fuskar nata ta yanda zata sake facing ɗin shi yace, "Tell me. Do you like him? I want an answer from your mouth."

Nan ma she kept quiet because she had nothing to say

Sai yace, "MEEMA let me know what's on your mind, no one will restrict you ok? Do you like my Friend?"

"Uncle, I have the one I want.." she said calmly.

"Who is he?" Ya katse mata maganar yana kallon ta

"ISHAQ. I still love Ishaq very much. But I still haven't got his phone, every time I call But his phone did not ring." Sai ga hawaye sun soma zubowa a fuskar ta, nan da nan ta soma shashsheƙan kuka

Mamaki ne ya kama shi, sai ya riƙo kafaɗun ta yace, "Why you crying Daughter? What happened to you? Or because you can't find him on the phone?"

Girgiza kanta tayi, sai kuma ta kwanto da kanta a jikin sa cikin shashsheƙan kukan da a yanzu ya ƙaru tace, "Uncle I love him but I know he broke up with me."

Kasa magana yayi illa shafa mata kafaɗa da yake yi alamun rarrashi. Can sai ya ɗago kanta yana kallon ta yace, "Now you don't like my friend but Ishaq?"

Shiru tayi tana runtse idanun ta

Shi kuma sai ya bi cuty face ɗin ta da kallo a ransa yana nazartan yanayin ta, tabbas idan ba hasashe yake ba he sees his friend's love in her eyes amma kuma tana son dannewa sabida wani. Don haka dole ya san abun yi bazai bari abokin shi ya rasa ta ba, sun fi dace wa da juna koda be san wancan ba. Hannayen ta da ya saki ya sake riƙo wa yanzu tare da kiran sunan ta

Sai ta buɗe idanun ta da suka soma sanja kala ta zuba mishi

"Tell me about your boyfriend. What do you have in common? Did you fight?"

Sai da ta ja majina kafin ta buɗe baki a cikin raunin murya tace, "I started to break up with him, but when I came to this country I told him to follow me and ask to marry me, but since I came I have not got his number again, I informed my friend to go home and check on him.." sai ta tsagaita sabida yanda muryan ta ya harɗe sakamakon shashsheƙan da take yi. Kana taci gaba da faɗin, "but he refused to listen to her. He refused to let them speak."

"MEEMA raise your head and look at me".

Babu musu ta ɗago kanta tana kallon shi

"I will tell you the truth now that he is separated from you, he cannot follow you here and marry you, you also know the truth, forget him. keep my friend as your life partner, he loves you. Umar Farouk is very kind has a good attitude, He was once married but his wife died, and she bore him two children Hafsah and Yusra, he loved them very much, and now he lives with his father's wife and children in their house. I promise you you will be happy, he will take care of you." Sai ya sake kiran sunan ta a hankali, be bari ta amsa ba yaci gaba da cewa, "my daughter. Please accept my friend's love. Please allow him to show you his love for you. If you do not like him you may part with him in the future, but now I beg you give him a chance ok?"

 

Kanta ta jinjina mishi a hankali hawayen cikin idanun ta suna sake zubo wa
   

Sai ya saka hannu ya ɗauke mata yana murmushi yace, "Why are you crying Daughter? Because my friend told you he loves you is because you're all in trouble?"

Fuskar ta ta kwaɓe a yanzu ɗin tana shirin yin kuka tace, "laà Uncle."

"To what's wrong?"

Shiru tayi masa tana sauke kai ƙasa

Sai ya ɗaura hannun sa ɗaya a kanta yace, "I give him your Number you will always look for him. Let me go." Sai ya mike ya fice ya barta a wurin ko motsin kirki ta gaza yi.
[14/10, 10:04 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

















                             *NO_28*

                 Ya fi mintuna biyar a cikin motan be fito ba koda yayi parcking ɗin motan a cikin gida

Securities ɗin sa duk sun zo sun mamaye wurin har ɗaya ya buɗe masa ƙofan motan suna miƙa mishi gaisuwa

Sai dai ya ɗaga musu hannu be ce komi ba. Ɗan numfashi ya ja kafin ya ziro dogayen ƙafafuwan sa ya fito a motan, sannan ya taka ya wuce ya nufi Part ɗin Momy. Nocking yayi da sallama ya shiga ciki

Da gudu Hafsah da Yusra suka yo kanshi ganin mahaifin nasu suna murna

Nan da nan ya haɗa su ya rungume cike da fara'a yana ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya yana ajiye wa. Kana kuma ya riƙe musu hannu zuwa kan kujeran yana tambayar su Momy

Kafin ma su ba shi amsar sai ga ta ta fito a ɗaki tana washe baki tace, "ah ah my son ka dawo?"

"Wlh kuwa Momy. Ina wuni?"

"Lafiya lau. Nayi mamaki da aka ce min ka fita, kuma ga shi har yammaci tayi baka dawo ba duk hankali na ya tashi, yanzu nake cewa Luwaira ta kira min kai a wayanta tunda nawa ya ƙi shiga."

Murmusawa yayi yace, "ayya Momy kiyi haƙuri na tayar miki da hankali. It's something I do and it's important that I go out."

"Masha Allah tunda Babu abunda ya same ka ka dawo gida Lafiya, abun da nake ji dama kenan shiyasa duk na tashi hankali na." Sai kuma ta kalli su Yusra tace, "an ga Dady ana ta murna ko?"

"Momy dama akwai maganar da zamu yi. Maganar aure na insha Allahu yanzu na samu wacce nake so zan aura."

Sosai maganar ta zo wa Momy a bazata, wani irin sarawa ƙirjin ta yayi wanda ya hana ta magana, sai da ta ɗan ja seconni kafin ta buɗe baki cike da murnan da iyakan shi fuska tace, "Masha Allah Son, yau ka faranta min abun da na jima ina fatan ji daga bakin ka, ai hakan ya fi shi ne zai ƙara kankaro maka mutunci ka zama babban mutum. Aina yarinyar take?"

Yana murmushi yace, "yarinyar Aunty ce ai, ƴar Yayar Hashim Aboki na."

"Oh ko wannan yarinyar wacce muka haɗu a asibiti?"

"Eh ita Momy."

Murmushin yaƙe tayi tace, "Masha Allah sosai kuka dace kuma, ai yarinyan naga kamar babu ruwan ta, yanzu kuma zumunci zai ƙara ƙulluwa kenan kai da Hashim? Abun gunun sha'awa wlh tunda zai baka yar shi ai haka ake so."

Shi dai murmushi kaɗai yayi

Tace, "alhmadulillah ai komi yanzu ya zo da sauƙi tunda ka samu Matar Aure, ko su Hafsa zasu ji daɗi ai idan aka ce sun sami Mahaifiya. Allah yasa ayi damu."

"Amin Momy. Abdul be shigo nan bane?"

"Eh ina tunanin ma ba ya gidan, amma na san bazai jima ba zai shigo tunda dare ya fara."

Miƙe wa yayi yace, "zai tafi." Sannan yayi mata sallama suka fice da yaran.


              Kai tsaye Part ɗin shi ya nufa, ya saka yaran suyi alwala sannan shima yayi, sai da ya tabbatar sun tayar da Sallan ya bar su a nan falo ya wuce masjid ɗin da ke a cikin gidan.




                 *******

          Momy kasa motsa wa tayi a wurin tun fitan shi gaba ɗaya hankalin ta ya tashi

Fitowar Luwaira daga ɗaki ne ta zauna tana tambayar ta da cewa, "Momy kamar na ji muryan Yaya Umar a nan ina Toilet. Ya dawo ne?"

Kallon ta Momyn tayi bata iya ce mata komi ba domin hankalin ta ya fita a jikin ta tunani ya sha mata kai

Sai da ta sake magana ne tana tambayar ta, "Wai Momy lafiya kika yi shiru?"

"Babu lafiya Luwaira. Ina Abdul kira min wayan shi yayi maza-maza ya zo?"

Yanda ta ga hankalin ta ya tashi ne yasa ta tashi da sauri ta nufi ɗaki ta ɗauko wayan nata ba tare da ta sake furta komi ba, sai da ta kira shi kafin ta sake kallon ta tace, "Momy wai lafiya ki sanar min don Allah?"

"Ki bari Abdul ya zo".


             Babu jima wa sai ga Abdul ɗin ya shigo tunda dama ya iso gida. Koda ya shigo ya gansu a haka shima tambyar ya soma jeho wa

A nan Momy ta sanar musu da zancen da Umar Faruk ya faɗa mata

Luwaira kasa cewa komi tayi saboda tashin hankali

"Momy wacce yarinyar kika ce zai aura?"

"Wannan yarinyar da suka zo gaishe shi a asibiti da su Hajiyan Hashim."

Saurin tashi tsaye yayi ya furta, "Whattt..?"

Kallon sa Momy tayi tana karantan yanayin sa ganin yanda gaba ɗaya tsananin tashin hankali ya nuna a fuskar sa. Kafin ma tayi magana sai ji suka yi Luwaira ta faɗi ƙasa a sume. Tuni Momy tayi kanta ita da Talatu wacce ta fito daga ɗakin ta ta hangi me ke faruwa

Shi kuwa Abdul a halin da yake ciki yana ga ya fi ta shiga tashin hankali, shiyasa be bi ta kansu ba ya juya ya fice da sauri ya nufi Part ɗin shi. Yana shiga ya faɗa kan kujera yana mayar da numfashi, sai kuma ya kama kanshi zuciyar sa tana tafarfasa kamar zata faso ƙirjin sa, kawai maganar Momyn ne ke dawo mishi a kwanya, taya zai bari ya rasa yarinyan nan bayan ya rigada ya kamu da ƙaunar ta? Ya za'a yi ma ace Umar Faruk ne zai aure ta? Haba bazai yiwu ba.. sai kuma ya tashi tsaye ya nufi cikin bedroom ɗin shi kamar zai tashi sama.

               Ruwa talatu ta ɗibo aka zuba mata kafin ta farfaɗo

Ganin sambatun da take yi ne sai Momy ta kalli Talatu tace, "je ki kiyi aikin ki."

Hakan yasa ta tashi ta wuce har tana jiyowa tana kallon su, sai kuma ta taɓe baki a ranta tace, "babban magana. Akwai tashin hankali kenan."

Momy kuwa tana ganin Talatu ta shige sai ta kalli Luwairan tace, "ke ki yiwa mutane shiru kina hauka ne zaki tona mana Asiri?"

Kuka ta fashe da shi tana cewa, "Haba Momy ke kin san a halin da nake ciki ne? Wlh ji nake yi kamar zuciyata zata faso ƙirji na saboda zancen ki, bazan iya jure wa ba wlh, bazan iya bari wata ta shigo gidan nan a matsayin Matar Umar Faruk ba, Ni ce zan aure shi, idan har ban aure shi ba to babu shi babu wani auren, sai dai duk abinda za'a yi ayi bazan bari ba." Sai ta sake kece wa da kuka

Dole Momy ta koma rarrashin ta tace, "ki tashi ki wuce ɗaki kiyi sallah, zamu yi maganar daga baya domin nima bazan bari wata ta shigo gidan nan ba gwara ke ki aure shi."

"Da gaske Momy?" Tafaɗa da sauri jin abinda Momyn tace

"Ki tashi nace ki wuce ban son iskanci."

Dole ta tashi tana faman hawaye ta wuce ɗakin ta

Ita kuma Momy kasa tashi tayi saboda ruɗu da tashin hankalin da yake cin ranta, duk ta rasa abun yi, daga baya kuma ta miƙe ta wuce ɗakin ta.







                ✳️✳️✳️✳️✳️

               Sai da aka yi sallan isha'i sannan ya dawo gida. Da ya shiga parlour'n su Hafsah suna zaune suna kallo. Yana shigowa suka zo suka ƙanƙame shi suna kiran sunan shi. Ya kama su suka zauna yana cewa, "My babies har Kun idar da sallan?"

"Eh Dady." Suka haɗa baki wajen faɗa

Shafa kansu yayi ya dubi wajen dainning. Sai kuma yace, "ok to ku tashi mu je ku ci abinci."

Tashi suka yi suka nufi wajen dainning ɗin. Bayan sun zauna ya zuba wa kowa abinda yake so kafin suka soma ci

Shima abincin yake ci amma hankalin shi na kan wayan shi, laluba Numban MEEMA da Uncle Hashim ya turo mishi yayi, sai da yayi saving kafin ya danna kira. Lumshe idanun sa yayi ya buɗe sanda ya ji wayan ta soma Ring, sai dai har ta tsinke ba'a ɗaga ba sai ya sake kira, nan ma shiru dole ya haƙura ya mayar da hankalin sa kan abincin sa. But ko kaɗan ya gaza ci sosai saboda tunanuka da suka yi masa yawa, surutun da su Hafsah suke mishi ma kaɗan-kaɗan yake amsa musu tunda hankalin shi ba ya wurin. Sai da suka gama yace, "su wuce ɗaki yana zuwa." Daga baya ya bi bayan su ya ciro musu kayan barci suka saka sannan yace, "su hau gadon su kwanta." Yayi musu addu'a ya fice ya koma ɗakin sa

Shima sai da ya shiga yayi wanka ya saka kayan barci sannan ya hau kan gadon shi. Kansa ya ɗaura a dantsen hannun shi yayi shiru, ya jima a haka sai kuma ya ja numfashi ya karkace kai ya ƙura wa wayan sa ido da ke ajiye a saman gadon. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma ya saka hannun sa ya ɗauka ya sake laluba Numban MEEMA ya kira ta.





✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

              A lokacin shigowar MEEMA kenan ɗaki, ta gama shirin ta tana ƙoƙarin kwanciya ta ji Ring ɗin wayan ta da ta ajiye a saman mirror tun kafin fitan ta. Zuwa tayi ta ɗauka sai kiran ya tsinke, nan ta ga an yi mata three missed calls, ɗan jim tayi bata kai ga yin wani tunani ba wani kiran ya sake shigo wa. Sai ta nufi bakin gadon  ta zauna kana ta latsa wayan tayi peacking ta saka a kunne.

             Wani ajiyan zuciya me ƙarfi ya saki jin anyi peacking call ɗin. Sai da ya ɗan gyara kwanciyar sa kafin ya kai wayan kunne yana sallama

Sassanyan muryan sa da ta bugi kunnen ta ne yasa ta ɗan lumshe idanu tana buɗe su. Sai da ta ja seconni kafin ta amsa sallaman in a very low voice

Shiru ne ya gifta na ɗan wani lokaci

Kasancewar MEEMA bata san shi bane; ko kaɗan bata kawo shi ne ya kira ta ba duk da muryan nasa yayi mata kama da wanda ta taɓa ji, jin shiru sai ta ciro wayan ta duba ta ga yana tafiya sannan ta mayar ta sake faɗin, "hello who's online?"

Lumshe idanu yayi saboda jin yanda muryan nata ya ratsa shi har cikin jiki da ɓargon shi, sai da ya gyara kwanciyar sa daƙyar ya buɗe baki wanda muryan nasa har shaƙewa tayi ya kirayi sunan ta

Hakan yasa tayi shiru tana tunani a ranta, a nan ne tunanin sa ya faɗo mata wadda ta tabbatar da tabbas shi ne. Bata amsa ba

Please Login or Register in order to submit comment