Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kan kujera ta nufa ta zauna tana ajiye numfashi

"Har kin dawo?" Cewar Momyn still tana kallon ta

"Eh." Ta bata amsa a taƙaice. Sai kuma tace, "Momy da zan fita naga wasu ƴan jarida sun shigo nan gidan."

"Nan gidan kuma?" Tafaɗa Momy mamaki cike a fuskar ta

Shima Abdul ya ƙara da cewa, "kina nufin ƴan jarida suka shigo gidan nan? To waye ya gayyato su?"

Tsaki ta ja da cewa, "waye kuwa ban da Yaya Umar. Wajen shi suka ce sun zo."

Momy tace, "Mata ne ko maza?"

"Mata ne su biyu suka zo, Ni ban ma ga sun yi kama da ƴan jarida ba gaskiya."

Momy tace, "ba na tunanin Umar Faruk zai gayyato su nan gidan duk da dai ban sani ba, amma kin san zaɓe ya kusa nan da kwana huɗu dole dama zasu takura masa, but mun yi maganar da shi kuma na san bazai ƙetare magana ta ba, babu wani amfanin yin hira da ƴan jarida bare har su tako wannan gidan."

"Gaskiya ne Momy, Ni ina ga wankin hula yana so ya kai mu ga dare." Abdul yafaɗa fuskar sa babu walwala ko ɗigo. "Momy i hate this Guy wlh! na gaji na gaji da ganin shi kiyi wani abu don Allah, Nima fa Ina so na fara watayawa a ƙasar, don Allah jibe yanda ya jajibo wani siyasa saboda iyayi don ya ga uban shi yayi, so nake yi Ni in gan Ni a matsayin sa Momy amma ba shi ba, Ni ya kamata nayi suna ba shi ba Momy. Sannan a kan wannan siyasan kowa zai san waye shi and kowa zai san arziƙi mu muke ci a gidan nan. Wannan ai tonon asiri ne."

Ajiyan zuciya Momy ta sauke tana kallon shi tace, "kayi haƙuri Abdul da sannu burin mu zai cika, da sannu komi zai kasance namu, Ni fata na ba na so muyi wani abun da zai ja hankalin police a gidan nan, ka san yanda muka kashe Nusaiba a gidan nan, mun bata guba ta ci daƙyar muka samu muka tsallake zargin ta, ba don mun biya ASP kuɗi me yawa ba ba na tunanin zai goge hujjojin da ya samu a kan gaskiyar guban da aka bata, so dole sai da dabara burin mu zai cika a kan Umar Faruk, muna da sauran lokaci da zamu aiwatar da shirin mu, yau saura kwana huɗu ayi zaɓe, kafin lokacin dole zamu cika burin mu a kan shi, sai dai wani ba shi ba."

Duk kan su murmushi ne ya suɓuce a fuskar su

Yayinda Luwaira wacce fuskar ta babu walwala ta buɗe baki da ninyan yin magana sai suka ji Nocking a bakin ƙofa

Shiru duk suka yi ko wanne yana kallon ƙofan. Sai da aka sake Nocking ɗin ne kafin a tare Momy da Abdul suka amsa, "yes. Waye ya shigo."

Hafsah da Yusra ne suka fara shigo wa kafin shi ya biyo bayan su. Kamar yanda ya saba yayi shigan shi na manyan kaya, farar shadda wacce sai maiƙo take yi tsaban sabunta da ɗaukan guga, tamkar wani ango sabida kyawun da yayi, gaba ɗaya turaren sa ya cika parlour'n da ƙamshi. Da gudu yaran suka isa wurin Momy suna rungume ta. Yayinda shi kuma ya taho a cikin ƙasaitan sa ya sami wuri a kan kujera ya zauna

Momy sai rungume yaran take yi tana musu maraba da zuwa fuska a washe

While Abdul yace, "to ku taho nan mana yara na, Momy kaɗai kuka sani ne?"

Da gudu suka dawo jikin shi suna kiran sunan shi da, "Uncle Abdul."

Ya rungume su yana cewa, "yauwa babies ɗina."

Umar Faruk da ke murmushi sabida yanda suke nuna wa yaran shi ƙauna sai ya mayar da idon shi kan Momy yace, "dama zan fita ne ina da meeting sai zuwa dare zan dawo, kuma ba na so su zauna su kaɗai, idan na dawo komin dare zan zo in ɗauke su."

Momy cike da fara'a tace, "ok babu damuwa my son. Ka kula da hanya ka san zaɓe ya kusa, kar ka soma ka fita kai kaɗai ka je da masu tsaron ka Please my son. Allah ya kiyaye ya dawo min da kai gida lafiya, Allah ya bada sa'ar abun da aka je nema kaji ko?"

Cike da jin daɗi wanda ya nuna a fuskar shi yace, "Amin Momy. Sai na dawo." Ya ƙare maganar da tashi tsaye. Idanun sa a kan Luwaira yace, "Luwaira babu addu'a kamar muna faɗa?"

Murmushi tayi tace, "haba yaya ko zan yi faɗa da kowa ai bazan yi da kai ba. Ina jiran Momy ta gama nata ne Nima inyi maka nawa special."

Murmushi yayi da cewa, "no ba na tunanin naki ne special ke dai kar ki ɓige da daɗin baki. Na Momy na ne special. Yanzu dai yi min naki in tafi."

Daga Momy har ita dariya suka yi

Momy tace, "yauwa ɗan albarka ashe dai ka gano ta."

Murmushi yayi kaɗai

Luwaira tace, "to Yaya Allah ya tsare ya kare hanya."

"Amin my dear sister. Ban manta da maganar ki ba idan na dawo zamu tattauna ko zuwa gobe."

Washe baki tayi tace, "to Yaya."

Daga nan fita yayi bayan ya sake yiwa yaran shi Ba-bye.



                 Yana fita Momy ta kira Talatu me aikin ta tace, "kwashe su ki wuce da su ɗakin ki ku zauna tare."

"To Hajiya." Tafaɗa tana jan hannun yaran

Sai Hafsah ta ɓata fuska tace, "Ni bazan je ba wajen Uncle Abdul zan zauna, ai yace zai kai mu shan Ice cream."

"No Hafsa ki je wajen ta ai ba yanzu zan fita ba, yanzu akwai abin da zan yi zuwa anjima sai mu je ko?" Yafaɗa hakan da murmushi a fuskar sa yana riƙe da kumatun ta da hannayen sa biyu

Murmushi tayi masa sannan ta bi bayan Talatun da ke riƙe da Yusra suka wuce

Tafiyan su Luwaira ta ja dogon tsaki tace, "wlh Momy na tsani yaran nan sosai kamar yanda na tsani uwar su. Ni ban ga amfanin su ba, kamata yayi su ma a aika su inda uwar su ta tafi."

"To abin hauka ne ashe? Ki bar maganar yaran nan ƙananan alhaki, idan mun gama da uban su zamu dawo kan su. Shirin mu kawai na plan A. Yanzu zamu mayar da hankali, idan haƙan mu be cidda ruwa ba zamu sauya wani shawaran. Abdul kai yanzu ya kamata ka samo mana waɗanda zasu yi aikin nan, in two days komi zai kammala ba na son a wuce wannan ranan."

"An gama Momy. Bari in je akwai inda zan je yanzu. Idan na dawo zamu yi magana."

"To."

Daga haka ya tashi ya fice

Luwaira kuma ta dawo kusa da Momyn tana ɓata fuska da cewa. "Ni Momy meyasa baza ku amince da nawa plan ɗin bane? Gaskiya ba na jin zan haƙura da shi cikin sauƙi haka. Ku taimaka min Momy."

"Ban san shirmen banza ke Luwaira. Wai meyasa kike haka ne sai mun kai magana ki dawo damu baya? Gwara ma idan zaki cire wannan shirmen naki a zuciya ki cire shi tun wuri, baza ki taɓa auren Umar Faruk ba, ke ma kin san da haka kar ki sake zuwar min da wannan maganar. Dalla tashi ki ban wuri."

Zumɓura baki tayi tana ƙunƙunai kafin ta tashi ta wuce

Ita kuma ta ja dogon tsaki tana bin ta da mugun kallo. "Idan ba iskanci irin naki ba ko mu mun amince shi zai amince ne? Ba na tunanin zai taɓa auren ki tunda yana kallon ki a matsayin ƙanwar shi ce. Kina so ki mayar da mu baya naga alama zamu dena saka ki a aikin mu, duk wannan abin da nake yi ina yi ne duk don ku amma ke ta banzan shirmen ki kike yi, to sai dai ki mutu kuwa don baza ki taɓa auren shi ba." Haka Momyn ta ci gaba da faɗa ita kaɗai duk da ita Luwaira tuni ta wuce ɗaki abun ta.
[14/10, 9:55 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏻‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
















                             *NO_23*

          Yau SATURDAY ranan da aka tashi da zaɓe na senetoci shiyasa ko ina ana hutu makarantu da wajen aiki. Su MEEMA ma yau suna gida suna hutu, shiyasa bata tashi barci ba sai ƙarfe 11:09am. Ta farka. Wanka ta soma yi ta saka doguwar riga fara me taushi da zanen followers a jiki. Ta fito Parlour ta sami su Hajiya zaune har da Ummee suna taɓa hira. Zama tayi a gefen Hajiya bayan tayi kissing ɗin hannun ta kamar yanda ɗabi'ar ta kenan gaisuwar ta

Hajiya tace, "Hope you are well?"

"Alhamdulillah." Ta amsa ta tana kallon ta

Zabba'u tace, "Weldon you slept. Today is a holiday."

Murmushi tayi mata

"Go to Breakfast there and lie down." According to Hajiya

Hakan yasa ta tashi ta wuce kan dainning ɗin

Ummee da ke aiki a computer ta ɗago tana kallon Hajiya tace, "Hajiya zamu fita da MEEMA zuwa kasuwa, kiyi mata magana sai mu je tayi shopping abun da take so, and Ina so in je gidan Hajja Salma sai mu je tare su gaisa, dama tayi min complain bata san ta ba."

"To ke meyasa baza ki faɗa mata ba sai Ni? Ki sanar mata idan zata bi ki sai ku je."

Ummee tace, "ok." Sannan ta ci gaba da aikin ta.


              Bayan MEEMA ta gama Breakfast ɗin ne ta dawo parlour'n ta zauna

Ummee looked at her and said, "We are going to go shopping. If there is anything you need, we will go and buy it."

"No I don't need anything." Tafaɗa ba tare da ta kalli Ummeen ba

"Why do you say that? I know you need MEEMA, you will follow me to go because I want to go to my friend's house and greeting".

Shiru MEEMAN tayi bata ce komi ba

Hakan yasa Ummee tayi tunanin ko ta amince ne, sai ta ci gaba da aikin gaban ta

Hajiya tana ji bata tanka ba hiran su suke yi ita da Zabba'u

While MEEMA tana latsa wayan ta

Can Ummee bayan ta gama abin da take yi ta tashi tana kallon MEEMAN tace, "Go get ready and we'll go out."

"I will not go anywhere." Tafaɗa a wannan lokacin tana kallon ta

Shiru Ummeen tayi kamar zata yi magana kuma sai ta juya ta haye sama

Hajiya kallon MEEMAN tayi tace, "Why are you like that?"

Da ido ta bi ta ba tare da ta fahimce ta ba

"Don't do that to your mother. She's your mother. You shouldn't argue with her. Get up and follow her."

Girgiza kanta ta soma yi har hawaye sun cika mata ido. "No, I'm not going. I'm not happy if I follow her." Tafaɗa tana miƙe wa ta wuce ɗaki da sauri

Da kallo suka bi ta har ta ƙule

Zabba'u tace, "wai Ni Hajiya mene ne ya haɗa su ne take yiwa Hajiya ƙarama haka? Kawai fitan da zasu yi ne tare shi ne take cewa baza ta je ba hakan be dace ba."

"To ai duk yanda kika gani da laifin Zulaiha. Sannan kinga rayuwar su da na nan ba ɗaya bane. Dole sai kin taimaka min wajen mun fahimtar da ita muhimmancin uwa, yanzu tana kallon mahaifiyar ta ce a maƙiyiyar ta kuma kin san hakan be dace ba tunda uwa uwa ce. Ni kaina ba na so ta ci gaba da nuna wa mahaifiyar ta tsana."

"To Allah ya kyauta Hajiya, ai a sannu zata saba komi zai wuce tunda yanzu suna tare a gida ɗaya". Cewar Zabba'un tana tashi tsaye zata wuce kichen. Sai kuma suka ji Nocking hakan yasa ta wuce bakin ƙofan ta buɗe. Zaro ido tayi tana kallon Matar da ke tsaye riƙe da hannun ƙaramin yaro da bazai gaza shekaru bakwai ba. Washe baki tayi tana kiran sunan ta. Sai kuma ta juya tana cewa, "Hajiya Jalila ce ita da Habeeb."

Jalila murmushi tayi ta shigo tana cewa, "ina Hajiyar tawa? Yau na kawo miki Mijin ki."

Dariya Hajiya tayi da cewa, "maraba lale yau dai muna da babban baƙi kenan?"

"Ai ba mu kaɗai bane har da Abban shi." Inji Jalilan tana zama

Kafin ma suyi magana sai ga shi ya shigo

Hajiya bata san sanda tayi yunƙurin tashi daga kujeran da take zaune ba. Sai dai kasancewar ta kasa dole ta zauna tana bin ɗan nata da kallo

Shi kuma da sauri ya iso yana kiran sunan ta. Ai rungume ta yayi tsaban murna sai ga hawaye

Itama haka hawayen ta fara bakin ta na rawa tace, "Hashimu ashe zan sake ganin ka? Kai ne dai ka dawo?"

Ɗago kansa yayi yana murmushi da hawaye a tare yace, "Hajiya Allah yayi mun dawo. Yau dai gani ga Hajiyata." Sai ya sake rungume ta

Zabba'u kuwa baki har kunne, ai sai ta ruga zuwa sama don sanar wa da Ummee. A tare suka dawo Ummee kamar zata kifa tsaban sauri

Shi kuma yana ganin ta sai ya tashi ya nufe ta yana faɗin, "Aunty."

Hannayen sa ta riƙe cike da tsantsan farin ciki tace, "na kasa yarda da aka ce min kai ne ashe dai kai ɗin ne? Gaba ɗaya ka manta damu?"

"Haba Aunty Kar ki CE haka, kin san aiki. Inda muka je gaba ɗaya babu network muna daji, jiya na sauka muka taho yau." Yafaɗa yana koma wa ya zauna

Itama zama tayi sannan aka sake gaisa wa

Zabba'u tuni ta cika musu gaba da drinks

Hayaniyan su ne ya fito da MEEMA dake ɗaki

Uncle Hashim shi ya fara hango ta, sai ya waro ido yana faɗin, "wa nake gani kamar MEEMA?" Sai kuma ya kira sunan ta

Hakan yasa ta dawo da idon ta kanshi. Sai kuma ta nufe shi itama tana kiran sunan shi

Cike da farin ciki ya tashi ya rungume ta yana cewa, "When did you come back here? Are you already here?"

Hajiya ce ta ba shi amsa tana faɗa mishi dalilin dawowar ta

Hannun ta ya riƙe suka koma suka zauna. Cike da tausayin ta yayi mata ta'aziyyar mahaifin ta

Kasa magana tayi saboda yanda idanuwan ta suka cika da hawaye

Yace, "Be patient my daughter. Pray for him because he is the only one who needs it. May God forgive us for his loss."

Duk suka amsa da, "Amin." Ban da MEEMAN da har yanzu ta kasa magana

Hajiya kallon Habeeb tayi da ya maƙale a jikin mahaifiyar shi tace, "kai kuma baza kazo bane mu gaisa? Ko har ka manta da Ni ne tunda dama ka rabu da zuwa gaishe Ni?"

Tashi yayi ya iso wurin ta

Ta kama shi tana shafa kanshi tace, "Miji na yau dai ga ka a gida, ga kuma Baba ya dawo ko sai murna?"

Murmushi yayi yana gyaɗa mata kai

"Ai yau tunda muka tashi da safe yake murna zai zo wajen Kaka, dayake ya tashi da zazzaɓi a jikin sa amma hakan be hana shi murna ba, zaman mota ne yasa duk yayi yaushi kafin mu zo amma da kuzarin shi muka zo don ya dame Ni har yanzu ba'a kawo ba?" Cewar Jalila tana murmushi

Dariya duk suka yi

Hajiya tace, "ayya ashe mijin nawa babu lafiya ne? Ai ko be kamata a bar shi haka ba. Zabba'u ki samo mishi magani sai a ba shi, amma kafin nan ki dama mishi ko Custard ne sai a ba shi kafin a gama girki."

"To Hajiya." Tafaɗa tana yinƙura wa ta tashi

Su kuma hira suka ɗan fara taɓa wa

While Uncle Hashim kallon MEEMA yayi suka sakar wa juna murmushi. Sai ya saka hannu ya riƙe nata hannun yana cewa, "My baby has grown, how did you grow up so much? I miss you so much."

Dariyan farin ciki ta saki wanda zai tabbatar maka da cewa tabbas tana a cikin farin ciki sosai. Dayake sun saba da shi, a lokacin da tana yarinya kusan ko yaushe yana yawan ziyartan su can Riyadh musamman domin ta, tunda dai aka ƙara mishi matsayi a wurin aiki ne ya dena zuwa amma duk da haka suna waya sosai, sai kuma tafiyan nan da yayi ya jima dole ta dena jin wayan shi, duk da bata yi tunanin ko aiki ne yasa ta dena samun shi a waya ba sai dawowar ta da Hajiya ta sanar mata. Kanta ta ɗaura a saman kafaɗan shi tace, "I miss you so much, Uncle!"

"Now I know you graduated?"

Gyaɗa masa kai tayi

"Now you are getting married. However I thought I would come back and find out you are married and I will see your children walking." Ya ƙare maganar yana kwatanta wa da hannun sa

Duk dariya suka yi har su Hajiya da suke hiran su daban

Yayinda ita kuma ta shagwaɓe fuska da cewa. "Uncle I am still a young girl."

"Really?"

Tura masa baki tayi

Murmushi yayi yana sanya hannu ya ɗan bugi goshin ta

Tace, "oshhh! Uncle it's hot."

"You still don't change my daughter."

"I also see that she is still unchanged." Cewar Jalila tana murmushi

Hajiya tace, "Now that you're back, you're going to get marry her."

"No. I'm not going to get married now. I haven't finished my studies yet. I'm just starting to work and I'll be long before I get married." Tafaɗa tana kallon shi

"Well daughter no matter what you say, what you want is what I want too." Shima yayi maganar idanun shi a kanta yana mata murmushi

Itama murmushin tayi tana sake mayar da kanta a jikin shi

Jalila tashi tayi tana cewa, "Hajiya bari in Kai kayan mu ɗaki." Ta wuce ta ja Trollyn tayi sama

A lokacin ne Zabba'u ta dawo da Custard ɗin ta gama dama mishi. Ta zauna tana cewa, "to zo ga shi na gama dama maka ka sha."

Taso wa Habeeb ɗin yayi daga jikin Hajiya ya taho wurin ta. Ita take ba shi da kanta bayan ta zaunar da shi a cinyan ta.



                Da haka dai suka kasance a ranan suna tare suna ta hira. Sallah kaɗai ke tayar da su a wurin. Sai da aka gama abinci suka haɗu gaba ɗaya suka ci a saman dainning sannan suka dawo Parlour suka dasa hira.










✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

          "Har yanzu Allah be bamu Sa'a a kan wannan yaron ba, na rasa meyasa har yanzu yake tsallake shirin mu. Yanzu wai ya zamu yi ne?"

"Momy ba fa matsalar mu bane, kin san kwana biyun nan ba ya zama dole baza mu samu damar aiwatar da komi ba, kuma kinga yau gidan cike da jama'a duk masu taya shi murnar samun kujeran nan ne, dole mu jira har sanda komi zai yi sauƙi."

Tsaki ta ja tana tashi ta soma zagaye. Can kuma ta juyo tana kallon Abdul tace, "yanzu ina Umar Faruk ɗin?"

"Na bar shi da wasu Mutane a waje, ya ce yanzu zai shigo idan suka gama."

"To ka tashi ka je kar yazo ya tarar da mu a nan."

Tashi yayi ya fice.



          Babu jima wa sai ga Umar Faruk ya shigo parlour'n da sallama

Momy saurin sauya fuskar ta tayi tana murmushi tace, "ah ah my son ƙariko mana ka zauna."

Taho wa yayi ya zauna a kujeran da ke facing ɗin nata

"Yanzu Abdul ya fita yake sanar min da daddaɗan labari. Ashe har an sanar da zaɓen ne?"

Murmushi yayi da cewa, "A'a Momy akwai saura, mu namu ba'a tabbatar ba dai. Zuwa anjima muke tunanin komi zai kammala."

"To ai dai tunda kaji haka insha Allahu kai ne da Nasara, na san yaro na bazai wuce shi ne da Nasara ba da yardan Allah. Kai na Mutane ne kamar yanda mahaifin ka shima na Mutane ne, ina da tabbacin kai ne zaka lashe zaɓen nan."

"Amin Momy." Yafaɗa cike da jin daɗi

Gyara zaman ta tayi tace, "ya maganar mu da muka yi da kai a kan neman matar aure? Kar ka manta fa yanzu kowa idon shi na kanka, kana da wannan babban matsayin amma ace baka da mata wannan be dace ba, dole ka nema wa su Hafsah mahaifiya ko su ma zasu ji daɗin uwa a halin yanzu, Nusaiba ta rigada ta tafi inda kowa zai je baza ta taɓa dawowa ba. Ba na so Mutane suna ma yaro na kallon ƙaramin mutum wanda zai gaza musu. A kullum da wannan batun nake kwana nake tashi kullum ina cikin zullumi da tunani." Ta ƙare maganar nata fuskar ta cike da damuwa

Shiru yayi kansa a ƙasa ya gaza cewa komi

"Umar ka duba magana ta komi ina yi ne domin ka, bazan so ace yau duniya tana zagin min ɗa ba, kai ɗana ne wanda nake ji kamar Ni na zuƙuna na haife ka. Mahaifiyar ka ta haife ka ne kawai amma Ni nafi kowa ƙaunar ka. Ina son ka ba na son abinda zai same ka, ba na iya barci a ɗan kwanakin nan tunda ka kama siyasan nan." Ta ƙare maganar da fashe wa da kuka

Da sauri ya ɗago yana kallon ta jin muryan kukan ta. Sai kuma ya tashi izuwa gaban ta jikin sa har rawa yake yi ya riƙo hannayen ta. "haba don Allah Momy mene ne na kuka kuma? Don Allah ki dena. Duk abun nan da kika ga ina yi; wa nake da shi da zan yi dan shi idan ba ku ba? Bani da kowa sai ku, na rasa kowa nawa amma kun zauna da ni, kin zame min mahaifiya sannan ga ɗan uwa na samu ga kuma ƙanwa duk kin maishe su nawa. Kina nuna min duk ƙaunar da uwa zata nuna wa ƴaƴan ta. Don Allah ki dena kuka na yarda zan yi aure ko domin farin cikin ki ne Momy." Sai yayi shiru saboda jin hawaye sun cika mishi ido. Daƙyar ya furta. "Zan yi auren Momy."

Murmushi tayi tana saka hannu ta riƙe nashi hannayen tace, "Allah ya maka albarka my son, Ni dama buri na inga kana farin ciki ne a rayuwa, tunda Matar ka ta mutu ka gaza yin aure wanda hakan be dace ba, kowa yana maka kallon Mutumin kirki ba na son a soma maka akasin haka tunda yanzu ka ga idanun duniya a kanka suke, kana da babban matsayi a duniya, ina son aci gaba da kallon ka a haka. Tashi ka je Allah yayi maka albarka."

Amsa mata yayi yana miƙe wa tsaye cike da sanyin jiki ya fice. Kai tsaye Part ɗin shi ya wuce ya shiga. Ɗakin yaran shi ya wuce ya duba ya ga suna barci sai ya haye sama inda ɗakin shi yake. Ya shiga ya yiwa kansa masauki a gaban gadon shi. Shiru yayi yana me kama kanshi da hannayen shi biyu. Shi Mutum ne me sanyin hali da rashin son hayaniya, shiyasa ko ya ya ne aka yi wani abu ko ya ɗan samu damuwa a ranshi yanzu sai duk ya rasa kuzarin shi, sai nan da nan kanshi ya soma ciwo har ya rasa sukunin shi, yana da matuƙar sanyin hali da tausayi sosai, abu kaɗan ke ɗaga mishi hankali shiyasa a sanda ya rasa Matar shi tashin hankalin da ya shiga ne ya haddasa mishi ciwon zuciya. Wanda har yanzu fama yake yi da kanshi kullum cikin magani. Ba ya son abubuwan da za suna tuno mishi da matar shi a koda yaushe shiyasa ya kasa ƙara aure yau kimanin shekaru shida kenan. Ta haifi Yusra da kwana ɗaya Allah ya ɗauki ranta sakamakon guban da ta ci a cikin abinci wanda su Momy suka sanya mata.



             Nusaiba ta kasance ɗaliban likitanci yarinya ɗaya tilo a wurin mahaifan ta da suka kasance Malamai, a nan Kaduna suke zaune kuma ba wasu masu kuɗi bane, sai dai suna da rufin asiri sosai. Tun Umar Faruk yana karatu a ƙasar Amurka lokacin ya dawo hutu suka haɗu da ita sanda ya kai ziyara wajen wani abokin shi a makarantar su. Kamun kanta da tsantsan tarbiyyar ta yasa Umar Faruk ya faɗa soyayyar ta, domin Nusaiba ba wata kyakkyawar yarinya bace amma akwai ta da tarbiyya sosai, tun tana ƴar shekara goma tayi saukar alƙur'ani me girma. Kuma a sanda ta girma tana koyar da ɗaliban mahaifin ta a makarantar da ya

Please Login or Register in order to submit comment