Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka fito

A nan suka haɗu da Laɗifa itama zuwan ta kenan, ta isa wurin su cikin farin ciki suka rungume juna da MEEMA

Idris da ke kulle mota yace, "to saura Ni baza ayi hugg ɗina bane?"

Hararan sa Laɗifa tayi tana cewa, "haka kawai ƙato da kai ba miji na ba, na ƙi ɗin." Sai kuma ta kalli MEEMA tace, "let's go." Ta riƙo hannun ta suka shige ciki suka bar Idris na kwaɗa mata kira. But ta ƙi tsaya wa suka shige ciki. Dayake Office ɗin su ɗaya ne can suka shiga suka zauna suna ɗan taɓa hira

Sai ga Idris ɗin ya shigo yana cewa, "wato ke ina kiran ki kika yi banza da Ni Ko? Kin ganki; ki fa mayar da hankali a kan aikin da oga ya sanya ki don na kula tunda na kawo miki Abokiyar hira kike wasa yanzu."

"A'a yaya kai ne dai kake ganin haka but ina aiki na yanda ya kamata wlh."

"Ok on that talk of ours we are going to meet the Senator tomorrow, he has given us an appointment tomorrow, but I have a place to go tomorrow, there is work for me to go to Zaria, now you and MEEMA will visit his house tomorrow, I hope you can?"

"Don't worry Bro, we'll go together."

"Ok let me go I have a job, kiyi sauri da Allah ki gama wancan aikin ki zo mu fara ɗaura videon Nan." Yafaɗa Yana kallon Laɗifan

"Ok." Tace da shi tana janyo computern ta gaban ta

Shi kuma ya fice ya bar su.

            There they were at work and MEEMA raised her head looking at Ladifa and said, "Where are we going tomorrow I don't understand?"

Laɗifa tace, "There is someone who is seeking the Senate seat in this city, we have been wanting to interview him on this television station for a long time, but we have not had the opportunity yet until this time, he is a great man because everyone wants to meet him. But now we have a way to go tomorrow. We going to interview him."

"Ok God Lead us." Cewar MEEMAN tana mayar da hankalin ta kan abin da take yi.


                By 02:00pm. Suka je suka yi sallah, Idris ya ɗauke su zuwa wani restaurant da babu nisa da wurin suka ci abinci, sai hira suke yi gunun sha'awa suna dariya har suka dawo. Zuwa ƙarfe 03:00pm. Suka tashi, Laɗifa ta sauke MEEMA a gida tunda Idris Yana da aiki ba yanzu zai koma gida ba. Sallama suka yi Bayan ta sauke ta taja motan ta ta tafi

Ita kuma MEEMA tayi Nocking aka buɗe mata ta shiga ciki, lokacin da ta isa parlour babu kowa sai Zabba'u wacce ta buɗe mata ƙofa tana mata sannu da aiki

"Where is Grandma?" Ta tambaye ta tana kallon ta

"She is in her room praying."

"Ok." Tace tana wuce wa. Sai da ta shiga ɗaki ta watsa ruwa a jikin ta ta sanya wata ƙaramar riga na shan iska wacce tsawon ta be wuci iya ƙasan gwiwan ta ba, kalan ta kalan ruwan Powder ne, sannan ta fito ta wuce ɗakin Hajiya. Sai dai a lokacin babu ita a ciki shiyasa ta fito Parlour ta tarar da ita tana karatun Hisnul Muslim. Wajen ta ta nufa tayi hugging din ta tana sakar mata kiss a bayan hannun ta tare da faɗin, "Weldon Grandma."

Murmushi tayi mata tana shafa kanta da cewa, "it works hope you enjoy the project?"

"Alhamdulillah." Tafaɗa itama tana mayar mata murmushin

"Ok go eat and come back for a chat."

Amsa mata tayi tana miƙe wa ta nufi kichen. Tana shiga ta ga Zabba'u a bakin madafa tana juya miya, ta isa wurin ta tana murmushi tace, "you are always cooking, you are not tired?"

Dariya Zabba'u tayi tace, "How can I get tired of cooking after a woman is known for cooking? You too should come in and teach you because cooking is for women. What are you looking for?"

Taɓe baki tayi tana sake duban kichen ɗin tace, "nothing. I came to see what you are doing."

Murmushi Zabba'un tayi tana ci gaba da juya miyan. Sai kuma tace, "your food is on the dainning table go and get it."

Kanta ta gyaɗa tana juya wa bata ce komi ba ta fice. Sai da ta ɗibi abincin sannan ta koma kusa da Hajiya ta zauna tana ci tana kallon ta

While ita kuma tana ta karatun ta

Bayan ta gama ta ɗauki Plate ɗin zuwa kichen

Lokacin Ummee itama ta dawo gidan, gaisa wa da Hajiya tayi ta haye sama.


                 The following day.
Har gida Laɗifa ta zo ta ɗauke ta suka wuce G.R.A where they will go to the Senator's house to find out about him being that the election is near, they want to post his interview on their television channel

Koda suka isa bakin Gate ɗin gidan an hana su shiga

Laɗifa ce ta fito a motan ta isa wajen Gate man ɗin tace, "Malam don Allah ka faɗa masa ƴan jarida ne daga Light T.v suke son hira da shi ya san da zuwan mu Please."

"Ok sai ku jira in sanar a ciki idan ya san da zuwan naku."

"Ok thanks." Tafaɗa tana kallon shi

While shi kuma ya shige ciki

Shiru-shiru kusan mintuna goma babu me gadi. Laɗifa da ke waje har yanzu sai kai komo take yi tana faman jan tsaki

Sai daga baya sai ga shi ya fito yace mata, "su shigo."

Hakan yasa ta koma wajen motan ta sanar wa MEEMA da ke zaune a ciki tana latsa wayan ta. Fitowa tayi da Laptop a hannun ta suka jera zuwa cikin gidan

Babban gida ne me Part-part da yawa. A can daga nesa akwai wani babban gini don shi kaɗai ne upstairs a gidan. Duk inda ka gifta masu aiki ne suke yawo suna ta faman aikin su, tsarin ginin sosai zai tafi da kai saboda tsantsan haɗuwar shi, daga gani ka san mamallakin gidan me kuɗi ne sosai. Sai da suka zagaya round about da ke tsakiyar gidan kafin suka isa wannan dogon ginin. Dayake suna biye da wani house men ne yana musu jogara zuwa wajen ogan nasu

Kafin su kai ga isa ginin ne sai ga wata tsaleleliyar budurwa wacce a ƙalla baza ta fi 24years ba, ta ɗau wanka a cikin ƙananan kaya tamkar baza ta taka ƙasa ba, tana tafe tana amsa call ta fito a ɗaya daga cikin sashin gidan. Tana matsowa wajen su ne while su ma hakan. Sai da suka yo gab da juna sannan ta ɗaga kai ta kalle su. Kallon kallo suka yi gaba ɗayan su yayinda ta ƙi ɗauke nata idanun a kan MEEMA wacce ita tuni ta ɗauke nata tun kallon da tayi mata daga nesa. Har sun gota ta kuma sai ta kira House Men ɗin tana yafico shi da hannu

Hakan yasa ya dakata daga yin musu jagoran da yake yi ya nufe ta da sauri ya duƙa a gaban ta

Magana take mishi tana nuna su MEEMA da yatsa

Shi kuma yana bata amsar tambayar ta. Sai kuma ya tashi a bisa umarnin ta ya nufi su MEEMA ya sanar musu, "kuyi haƙuri Ƙanwar Yallaɓoi tace baza ku samu ganin shi ba."

"To saboda mene?" Inji Laɗifa cike da haushi

"Haka tace in sanar muku."

Kallon inda budurwan ke tsaye tayi. Tana nan har yanzu da waya a kunnen ta idanun ta na kallon wani wurin. Hakan yasa Laɗifa ta kalle shi tace, "kai mu je ka kai mu."

"To." Yafaɗa da sauri yana yin gaba

MEEMA da bata san ma me suke faɗa ba ganin Laɗifa tayi gaba yasa itama ta bi bayan ta tana jan gajeren tsaki, kasancewar akwai rana sosai duk tafiyan nan da suka yi daga bakin Gate zuwa nan duk ta gama takura, har wani gumi ne yake tsatstsafo mata sabida yanayin shigan kayan ta

Budurwan da itama ta biyo bayan su cikin ɗaga murya tace, "Hi.. Hi.."

Dole suka ja suka tsaya gaba ɗayan su jin muryan ta a sama wanda yake nuni dasu take yi

"Me nace maka? Ina zaka kai su bayan nace maka baza su samu ganin shi ba?" Tayi maganar a ɗaurewar fuska tana kallon House Men ɗin

Kafin yayi magana sai Laɗifa ta riga shi da faɗin, "kiyi hakuri ba wajen ki muka zo ba, shi wanda muka zo wajen shi shi ne yace a shigo damu don haka baza mu koma ba." Sai ta ja hannun MEEMA suka yi ciki ba tare da ta sake bi ta kan ɗan rakiyan ba

Ita kuma ƙwafa tayi tana bin su da kallo har suka ƙule mata, sannan ta ja dogon tsaki ta wuce zuwa wajen motan ta ta shiga tabar gidan.



       A dogon ginin Laɗifa ta ja tunga ta tsaya domin a ranta tana da tabbacin nan ne ya kamata su shiga. Sai ta soma Nocking ƙofan

MEEMA da ke kallon ta tace, "but who is that? What is she asking us?"

"Forgot her. I think she's also a housewife, or his younger sister oho."Cewar Laɗifa still tana ci gaba da Nocking ɗin

Babu jima wa aka buɗe musu. House maid ne ya buɗe yana kallon su da tambayar, "wanda suke nema?"

Laɗifa tayi mashi bayanin abin da suka zo yi

Yace, "ok ku shigo". Ya shigar da su har cikin ƙaton parlour'n ya basu wurin zama. Sannan ya kawo musu drinks sai ya wuce kiran musu me gidan. Be jima ba ya dawo yace musu, "su biyo shi."

Kallon MEEMA Laɗifa tayi tace mata, "let's go."

Tashi tayi ta bi bayan ta suka shiga wani ƙayataccen parlour'n sai dai shi be kai wancan girma ba, amma ya fi haɗuwa sosai da sosai

Wata matashiyar yarinya wacce a shekaru baza ta fi 8yers ba ke zaune a parlour'n tana buga Game a t.v, Remote ɗin na hannun ta tana sarrafa wa. Daga ita sai siririn wando da vest a jikinta, ganin su yasa ta tsayar da abun da take yi tana faman kallon su

Shi kuma house maid ɗin yace musu, "su zauna."

Zama suka yi while Laɗifa sai baza idanu take yi a parlour'n kasancewar yayi mugun tafiya da ita, babu shakka kuɗi na inda suke, baza ka taɓa cewa a duniya kake ba idan ka ji ka a cikin parlour'n nan saboda tsantsan tsaruwar shi. Sosai haɗuwar sa ya tafi da ruhin Laɗifa kasancewar bata taɓa tozali da irin tsararren gidan nan ba

While MEEMA kuwa kasancewar ta taso a wanda ya fi shi sau miliyan shiyasa bata tsaya kallo ba domin babu abinda ya birge ta sai wani hoto da ta ƙyalla ido ta hanga. Hakan yasa ta sake ɗago kai ta sauke a kan yarinyan da ke zaune tana bin su da kallo sannan ta sake mayar wa a kan hoton. Yarinyar ce a cikin hoton ita da wata wacce bata kai ta Shekaru ba, sun rungume mutumin da ke a cikin hoton duk kan su suna dariya, tsananin kaman da suke yi da shi dole ka gane mahaifin su ne, babban Mutum ne domin ya sha manyan kaya me ruwan madara, riga da wando da malin-malin ɗin shi, a ƙalla bazai wuce shekaru 37years ba, amma tsaban kwarjinin shi da tsantsan kyawun shi dole sai ya cika maka ido. Shiru tayi tana kallon fuskar mutumin tana son zurfafa tunanin ta, sai muryan yarinyar ya dawo da ita a cikin hayyacin ta. Hakan yasa ta mayar da kallon ta wajen ta

Faɗa yarinyar take yiwa hause Maid ɗin a kan shigowar su MEEMA cikin parlour'n

Shi kuma yake sanar mata, "Mahaifin ta ne yace a kawo su wurin."

Sai ta ja dogon tsaki tana ɗaukan Remote ɗin taci gaba da Game ɗin ta bata sake magana ba bare tabi ta kansu

While me aikin tuni ya fice

Su kuma suka zauna jigum babu wanda ya sake bi ta kansu. Har MEEMA ta gaji ta juyo da kallon ta ga Laɗifa tana cewa, "I'm so tired I'm leaving."

Hannu Laɗifa ta saka ta riƙe nata tana marairaice fuska da cewa, "Please let us wait a little longer, since we have come so far we will sit and wait."

Bata ce komi ba ta ɗauke kai ta mayar ga T.vn da yarinyar take yin Game. Sai kawai ta shagaltu da kallon Game ɗin domin tunawa tayi da itama sanda take gida, a lokacin da Abee ɗin ta yake lafiya, tare suke buga Game ɗin suna farin ciki da nishaɗi, kasancewar ta me matuƙar son game shiyasa ba sa rabo da buga wa tare, kala-kala take da su domin har ɗakin Games ne da ita... Hawaye ta ji sun cika mata idanu ta kai hannu ta share waɗanda suka silalo mata a kunci tana ɗan jan majina kaɗan.
















_Barka da wannan rana me albarka. Ina ma ɗaukacin masoya na murna da zagayowar wannan rana ta juma'a. Allah ya sada mu da albarkatun ta yasa mu dace duniya da lahira. Ayi weekends lafiya._
[14/10, 9:54 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```(WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

















                             *NO_22*

                  Yanda aka shanya su a wurin ne yasa ran MEEMA ya ɓaci ta miƙe tana kallon Laɗifa fuska babu walwala tace, "Please get up and go. I'm very tired."

Bata kai ga yin magana ba sai wata yarinyar ta fito a guje tana kiran sunan, "Aunty Hafsah.. Aunty Hafsah." Tafaɗa kan kujeran da ƴar uwan ta ke zaune

"What's wrong?" Ta tambaye ta tana ajiye Remote ɗin hannun ta

Ita yarinyar tuni ta mayar da kallon ta kan su MEEMA tana kallon su. Sai kuma ta nuna su da yatsa tana cewa, "Aunty waɗannan fa su wane ne?"

"Oho ki tambaye su ga su nan."

"Baby come I want to ask you." Cewar Laɗifa tana ma ƙaramar murmushi

Hakan yasa ta taso izuwa wurin ta

Sai ta riƙe mata hannu still tana mata murmushi tace, "what's your name?"

"My name is Yusra."

"Ok Yusra ko zaki kira mana mahaifin ki?"

Gyaɗa mata kai tayi kana ta juya da gudu ta hau upstairs

Tafiyan ta yasa Laɗifa ta kalli MEEMA tace, "Sister, sit down. Now she will be called for us, Let's wait a little longer."

Ɗauke kai tayi bata ce komi ba kuma ta ƙi zama

Babu jima wa sai ga Yusran sun fito ita da mahaifin nata. Daga shi sai jallabiya fara sol da waya a kunnen sa yana amsa call

Har suka sauko ƙasa Laɗifa idanun ta na kanshi, sosai take tasbihi da tsantsan kyawun da Allah ya yi masa

While MEEMA itama tunda ta kalle su sau ɗaya sai ta sami wuri ta zauna

Har ya iso wajen hankalin sa be kai ga su Laɗifa ba, sai da ya zauna a ɗaya daga cikin manya-manyan kujerun parlour'n sannan ya sauke fararen idanun sa a kan su

Hafsah da Yusra tuni sun haye kan shi

While shi kuma yana ci gaba da wayan shi, sai dai tunda ya ɗaura idanun sa a kan MEEMA ya ƙi ɗauke wa. Hannun sa ɗaya na a saman giran sa yana murza wa hakan yasa baza ka gane ita yake kallo ba

Ita kuma a jikin ta taji ana kallon ta shiyasa ta sake ɗaga kai a karo na biyu ta kai duban ta gare shi. Hakan yasa idanuwan su suka shige cikin na juna. Ko soconni bata ɗauka ba ta cire nata idanun tana jin gaban ta na faɗuwa matsananciya, tabbas tana ji kamar ta san wannan fuskar, a jikin ta tana jin kamar ta taɓa ganin sa

Shima haka a wajen sa. Shiyasa ya kasa cire idon sa a kanta yana son tuna inda ya san fuskar ta. Be ɗauke idanun nasa ba har sanda ya tuno ta kuwa. Ya tuna sanda ya je Umrah ya hayo jirgi daga Riyadh, ita ce wacce suka zauna a jirgi tare zuwa Abuja. A lokacin ya dawo da dare babu wanda ya sani shiyasa ya wuce gidan Abokin shi Hashim a barikin sojoji ya kwana. Tabbas ita ce. Hakan yasa ya lumshe idanuwan sa yana me sake buɗe wa a kanta, sallama yayi da wanda suke wayan ya mayar da kallon shi sosai a kan su har Laɗifa yace, "ku ne kuke nema na?"

"Eh ranka ya daɗe!" Inji Laɗifa cike da murmushi a fuskar ta

"Ok sorry I settled you, there's something I'm doing what's important in it."

Hakan yasa MEEMA ta sake ɗago kai ta kalle shi jin abun da yace, sai suka sake haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta

Shima haka janye nashi idon yayi yana kallon yaran nashi da cewa, "ku ɗan bamu wuri zamu yi magana My Babies."

"Ok Daddy." Suka faɗa a tare suna tashi da gudu suka yi cikin gidan

"Ina sauraron ku. I give you ten minutes to do what brought you here."

"Ok Sir." Laɗifa ta faɗa da sauri tana amsar Laptop ɗin hannun MEEMA ta buɗe

Ita kuma ido kawai ta zuba mata bata ce komi ba.




             Nan ta soma mishi tambayoyi tun daga full name ɗin shi zuwa shigan shi siyasa

A taƙaice dai ba wani amsa mata sosai yake yi ba, wasu ataƙaice yake bata amsa. Daga ƙarshe duba agogon sa yayi yace, "lokaci ya cika. Ina da abun yi." Sai ya tashi ya wuce be jira cewar su ba

Dole su ma suka tashi suka fice a gidan. Sanda suka hau mota Laɗifa take cewa, "I don't think we will ever see him wlh, he is very well connected and it is beautiful, but I honestly didn't like the way he answered our questions."

MEEMA da ta kwantar da kanta a jikin kujeran idanun ta a rufe, tana jin ta but ko magana ta gaza yi sabida ɗan tunanin da ya hau mata kai, so take yi ta tuna inda ta san fuskar nan domin ya tsaya mata a rai. Sai da Laɗifa ta taɓa ta sannan ta ɗago kanta tana kallon ta

"I mean you're silent what do you do?"

"Nothing."

"Ok call Bro Idris and let him know we're done." Laɗifa tafaɗa tana ci gaba da tuƙin

MEEMA bata ce komi ba ta ɗauki waya ta soma neman layin Idris. Sai dai a kashe aka ce

Laɗifa tace, "maybe it is still not in Zaria. We'll try again later."

Da haka suka ƙarisa wajen aikin su.



           Zuwa ƙarfe uku Laɗifa tayi dropping ɗin ta a gida. Lokacin da ta shiga Parlour Hajiya da Zabba'u suna zaune sun yi baja-baja da kaya

"These are your belongings, come and see if they do it for you." Cewar Hajiya bayan MEEMAN ta zauna

Kallon kayan take yi bata ko motsa ba

Zabba'u da ke washe baki tace, "These items are all Hajiya's choice for you. In fact, Hausa clothes will look good on you. God willing, they will please you."

MEEMA kallon Hajiya tayi tace, "Thanks grandma, I am very happy."

"Ok come and see. Look at everything that is not yours and you will be changed."

Kanta ta gyaɗa kafin ta tashi ta iso gaban kayan ta durƙusa tana duba wa

While Zabba'u tana taya ta ɗauko wa

Atamfofi ne da lessi sai materials kala-kala. Sai takalma har da gyale

Ɗago kai MEEMAN tayi tana kallon Hajiyan a marairaice tace, "But how can I use them? I can't."

Dariya suka yi mata

Hajiya tace, "You will learn, no matter what you say you can't. Since you came back to our country you have to learn all our culture."

Murmushi kaɗai tayi tana ci gaba da ɗaga kayan, wasu kuma sai ta kara a jikin ta kafin take ajiye wa

Hajiya tace, "You go with Zabba'u to take your sewing, then choose the style you want. Go eat and rest later and take it to your sewing shop."

"Ok." MEEMA tafaɗa tana tashi ta wuce ɗaki

Yayinda Zabba'u kuma ta haɗa kan kayan ta mayar a cikin leda.


              Koda MEEMA ta shiga ɗaki wanka tayi ta saka riga da wando masu taushi ta fito Parlour. Abinci ta sawo ta zauna a gefen Hajiya tana ci tana sauraron hiran nasu. Sai da ta gama ta wuce ɗaki ta ɗaura after dress baƙi a saman kayan ta tayi Rolling da ɗan kwalin shi kafin ta fito suka fita. Drever ya ɗauke su suna shirin fita itama Ummee ta dawo gidan.



               Koda ta shiga parlour'n ta tarar da Hajiya. Sannu da gida tayi mata kafin ta tambaye ta, "ina su MEEMA zasu je ta gan su a mota?"

"Kaya ne na ɗaukar mata wajen Dillaliya, ɗazu nace ta kawo min shi ne zasu kai ɗinki."

Gyaɗa kanta tayi, sai kuma tace, "amma Hajiya da kin bari na siyan mata da kai na kar ɗawainiyar yayi miki yawa."

Hajiya tace, "yanzu ma ban hana ki siyan mata naki ba, Ni nayi ra'ayi baza ki hana Ni abun da nayi ninya ba."

"To Hajiya ai ba na faɗa bane abun." Ummee tafaɗa tana murmushi

Shiru Hajiya tayi mata tana mayar da idanun ta kan t.v dake faman aiki shi kaɗai

Ita kuma Ummeen sai ta wuce sama inda ɗakin ta yake. Sai da tayi wanka ta sauya kaya kafin ta fito ta zuba abinci ta dawo Parlour. Tana cikin ci ne sai kuma ta kalli Hajiya da cewa, "Hajiya baki yiwa MEEMA magana a kan ƙadaran mahaifin ta ba, ya kamata a san abun yi sabida be kamata a bar su a can ƙasar babu me kula da komi ba, sannan akwai magada a ciki kamata yayi a sauke mishi nauyi tun yanzu."

Hajiya da ta dawo da kallon ta kan Ummeen tace, "nayi tunanin hakan, sai dai be kamata mu tayar da maganar yanzu ba, mu bari zuwa nan gaba bayan ta sake sakin jiki sosai damu, har yanzu ina ganin damuwa sosai a tattare da MEEMA, har yanzu ba wai ta manta mutuwar mahaifin ta bane, shiyasa duk wani abun da zai saka ta farin ciki nake iyakan ƙoƙari na wajen naga nayi mata. Tunda ke kin gaza a matsayin mahaifiyar ta ki bar ni Ni inyi mata, Ni kaɗai take kallo take jin daɗi a yanzu."

Cike da sanyin jiki Ummee tace, "Amma Hajiya mene ne na gori kuma?"

"A'a ba maganar gori bane gaskiya na faɗa. Yarinyar nan tana cikin damuwa tsantsa, ko fuskar ta kika kalla bata cika yin fara'a ba, wani abun ma tana yi ne kawai domin mu, don haka ba na son ma a cika mata maganar da zai riƙa tuna mata da mahaifin ta."

"To shikenan." Cewar Ummeen tana ajiye Plate ɗin abincin. Sai kuma ta ɗauka ta kai kichen ta haura sama.



            Ba su wani jima ba su MEEMA suka dawo gidan.



            Da dare suna cin abinci a dainning Idris ya shigo gidan. Kai tsaye wajen su ya nufa yana jan kujera ya zauna yace, "nima yau da Ni za'a ci abincin duk da na cika ciki na daga gida."

Hajiya tace, "dama wa ya isa yace ban da kai za'a ci Mijin?"

"A'a gaskiya ban girka da kai ba, ka tashi ka bamu wuri." Inji Zabba'u cike da barkwanci

"Wai kin ji Hajiya in tashi?"

"A'a zauna ka zuba abun da ranka yayi maka, idan ba ka kawo wa taya za su samu su ci?"

"Yauwa Hajjaju na Ni kaɗai, an dai Gwale wasu." Yafaɗa yana dariya

Su ma dariyan suke taya shi ban da MEEMA da ido ta zuba musu tunda ba ta fahimta

Gaishe da su yayi kafin ya mayar da hankalin sa kan MEEMA yana tsokanar ta

Ita dai murmushi kaɗai take mishi har suka gama cin abincin suka koma Parlour

A nan ya ɓata lokaci kafin yayi musu sallama ya tafi. Dama ya zo wajen MEEMA amsar Laptop ne kasancewar ita ta taho da shi lokacin da suka tashi daga aiki tunda nashi ne.








✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

               Horn tayi har kusan biyar kafin me gadi ya buɗe mata ƙofa. Ta shige da motan ta zuwa wajen parcking. Fitowa tayi ta nufi Part ɗin su da ke a cikin gidan

Tana shiga parlour'n Momy da Abdul dake magana suka tsayar da maganar suna kallon ta

Ita kuma kai tsaye

Please Login or Register in order to submit comment