Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sajjad, Ni wlh gaba ɗaya na tsani yarinyan nan gaskiya Abba a hana sa auren ta.."

Kafin ta ƙarisa maganar ma Sajjad ya bige mata baki, "ke ki kama kanki Allah zan tattaka ki ina wasa dake ne?" Yayi maganar yana wani zazzare mata idanu

Ita kuma kuka ta saka ta hau shura ƙafafu

Abba yace, "meye kuma na dukan ta My son?"

"Abba baka ji me take cewa bane? Idan ba ta son ta ai Ni ina son ta, Kuma wlh idan ta sake zan fasa bakin ne". Ya ƙare maganar da tashi ya wuce ɗakin sa

"Ke ma kiyi hakuri da Allah ba fa wani dukan ki yayi ba kina wani ɓare wa mutane baki". Inji Umma tana kallon ta

Tashi Murjanan tayi tana bubbuga ƙafafu ta wuce ɗaki tana cewa, "ai dama kun fi son shi wlh, kuma bazan yarda ba sai na rama".

Tana shiga ɗakin MEEMA dake kwance a kan gado tayi saurin ɗago wa saboda a tunanin ta ko Sajjad ne, ganin ba shi bane sai ta mayar da kanta ta ci gaba da waya da Esha da ta kira ta suna gaisa wa

Dogon tsaki Murjanan ta ja tana wuce wa Toilet, tana fito wa ta haye saman gadon tana sake jan tsaki kamar wacce tsaka ta haifa, "dole ne ma a raba mana ɗaki don bazai yiwu in riƙa kwana da ita ba, shegiya kawai da wani fuska sai kace na mage".

MEEMA na jin ta sai dai dayake bata san me take cewa ba wayan ta kawai take yi, sai da duk ta kira su Ummu Hani da Zamiya suka gaisa kafin ta ajiye wayan tayi addu'a ta shafa ta gyara kwanciyar ta, rufe idanuwan ta tayi zuciyar ta duk babu daɗi, bata jin ko wani irin farin ciki a cikin ta, tana ji baza ta iya zama a gidan nan ba Sajjad na mata abun da ya ga dama, sosai take jin tsoron kar ya zo yayi mata wani abun, shiyasa take ta saƙa da warwaran hanyar da zata ɓullo, ko kaɗan zaman gidan ba ya mata daɗi tunda ta fahimci kamar ba ƙaunar zaman ta suke yi ba, musamman ma Murjana da Umma da suke mata wani kallo, ga kuma Sajjad dake son takurata, tana ga idan babu hali dole zata koma can Riyadh, gwara ta zauna a can zai fi mata, amma kuma abu ɗaya ke hana ta tafiya saboda wasiyyan mahaifin ta, umarni ya bata ta koma wajen mahaifiyar ta ta zauna da ita, but ko kaɗan ba ta ƙaunar sake tozali da Ummeen ta har ta koma ga mahalicci, ta tsane ta sosai a zuciya shiyasa ta ga gwara ta zo wajen dangin Mahaifin nata ta zauna tunda zaman ta a can ne be son tayi ita kaɗai, sai dai a yanzu ɗin tana ganin dole ta nemi layin Ishaq ta ba shi haƙuri ya taho nan ya aure ta ta bi shi, hakan shi ne maslaha a rayuwar ta don baza ta iya zama a cikin Nigeria ba, har yanzu ƙasan be mata daɗi ba, but idan ta auri Ishaq sun koma can hakan ba yana nufin ta ƙi bin umarnin Abee ɗin ta bane. Share hawayen fuskar ta da tun ɗazu suka soma sintiri tayi tana gyara kwanciyar ta, ƙanƙame jikin ta tayi tana sake jin kewar Abee na ratsa mata zuciya, da ace yana da rai da ba haka ba, komi nata na farin ciki ya ruguje, ba ta tunanin akwai ranan da zata sake farin ciki da walwala babu Abee ɗin ta, Abee shi ne farin cikin ta kuma ya tafi ya barta, rayuwar ta gaba ɗaya ta ruguje tun tafiyan Ummee, shiyasa gaba ɗaya laifin alhakin mutuwar Abee take ɗaura shi a kanta, ita ta kashe mata Abee ɗin ta da a yanzu suna tare cikin ƙaunar junan su, baza ta taɓa yafe mata ba. Daƙyar a daren barci ya ɗauki MEEMA tare da mafarkai kala-kala.

[10/10, 3:40 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎

*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*




                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._




            *TUNATAR WA*
_Kamar yadda sallah take ibada ce ta ruhu, haka nan muka lura cewa wajen yin ta jikin yakan sami babban ƙarsashi saboda motsa shi da ake yi. Ƙwararrun masana wasannin motsa jiki sun yaba da abubuwan da sallah ta ƙunsa, harkokin nan daban-daban waɗanda ake nanata su a cikin raka'o'in Sallah. Wadannan harkoki ba su barin wata gaɓa a jikin mutum mai Sallah sai sun motsa ta. Watau dai, yadda musulmi suke samun ibada ta ruhu a cikin sallah, haka nan ma suna samun amfani babba na motsa jiki._
         _lada da fa'ida da mai yin Sallah zai samu kenan. Ina hukuncin wanda ya yi watsi da ita, ya ƙi bari ta zame masa garkuwa?_
         _Duk wanda ya juya wa sallah baya ya guje wa Musulunci, ya saɓi Ubangijin sa. Ya karya dokokin imanin sa, ya kuma kama hanyar halaka. Duk ayyukan sa na ƙwarai sun ɓalɓalce don kuwa ya kauce wa umarnin Ubangiji game da Sallah - duk wanda ya saɓa ma Allah tamkar ya ce ba shi ne ma, domin kuwa ai da ya amsa cewa akwai Allah ai ba shakka da ya bi umarnin sa, kamar dai yadda yace, a cikin Alƙur'ani mai tsarki:_
        *"Kuma ku tsayar da Sallah. Lalle sallah tana hanawa daga alfasha da abin ƙi"* _Suratul Ankabut, aya ta 45._
Allah yasa mu dace.



















                             *NO_16*

             *WASHE GARI*
          MEEMA na cikin barci ta ji ana shafa mata face, tana buɗe idanuwan ta suka faɗa cikin na Sajjad dake durƙushe a gaban gadon ya tsira mata idanu, da sauri ta sake zaro idanun nata don sake gasgata shi ɗin ne a lokaci ɗaya tana me tashi zaune

"Good morning my love." Yayi maganar yana mata murmushin sa me kyau

Bata iya amsa wa ba kuma bata cire idanun ta a kan sa ba, sai ma tamke kyakykyawar fuskar ta da tayi tana mishi mugun kallo

Tashi yayi ya zauna a gefen ta, kana ya saka hannun sa zai riƙe nata

Tayi saurin daka masa tsawa tana janye hannayen nata, "don't touch me again".

"Why dear?" Yayi maganar kamar zai yi kuka

Tashi tayi daga kan gadon tayi hanyar Toilet ta shige

Da kallo ya bi ta kamar zai haɗiye ta tsaban yanda tayi masa kyau a cikin guntun rigan barcin nata, ko kaɗan ya kasa ɗauke ido a ƙofan har sanda ta fito

Ganin sa a zaune har yanzu sai ta ɗauke kai kawai tana sake haɗe fuska, wajen Trolly ɗin ta ta nufa ta ciro towel da abubuwan da zata buƙata ta sake shige wa Toilet ɗin

Sajjad buga tagumi kawai yayi still idanun sa a kan ƙofan ya ƙi ko gezau. A lokacin da ta fito ai sandare wa yayi ganin ta daga ita sai towel, gaba ɗaya santala-santalan cinyoyin ta a waje suke

Ita kanta bata yi tunanin zata sake ganin sa ba kasancewar ta ɓata lokaci a cikin Toilet ɗin, da sauri ta ja ta tsaya tana kallon sa cike da haushi, "I will prepare. Please Get out."

Numfashi ya sauke sabida jin daddaɗan muryan ta a kunnen sa, yanda yake ji a jikin sa bazai iya magana ba shiyasa a hankali ya taka ya fice a ɗakin har yana sake waigen ta, ji yake yi kamar ya koma ya haɗa jikin su wuri ɗaya tsaban feelings ɗin da yake ji

Ita kuma yana fita ta ja dogon tsaki ta nufi kayan ta, gaba ɗaya zuciyar ta ba ta mata daɗi har ta gama shirin ta cikin wata doguwar riga fara ne wuyan love, rigan Robber ce gaba ɗaya ta bi ta lafe mata duk ta fito mata da shafe ɗin jikin ta, dayake akwai ɗan guntun Hijab ɗin sa maroon color da aka yi design da less a ƙasan, shi ta saka ya tsaya mata a iyakan kafaɗa, da agogon ta da flet shoes ɗin da ta sanya duk na kayan ne white color, tayi kyau sosai duk da fuskar ta babu abun da ta sanya, wayan ta dake ajiye ta ɗauka ta fita Parlour

Babu kowa sai Sajjad dake zaune. Yana ganin ta ya tashi tsaye idanuwan sa kamar za su faɗo a kanta, tsaban kyan da tayi masa tamkar ya je ya haɗiye ta haka yake ji, sosai MEEMA take da mugun kyau shiyasa gaba ɗaya ta zauta shi ya koma kamar wani soko a kanta, shiyasa ko barcin kirki ba ya iya samu sabida rashin kula sa da take yi, ba zai iya haƙura da ita ba a rayuwar sa, tabbas idan ya rasa ta mutuwa zai yi domin be taɓa ƙaunar wata mace ba sai ita, duk da yana da tarin ƴan mata domin Sajjad na mata ne but sai dai ya gara su be san cewa akwai ranan da wata mace zata shiga zuciyar sa kamar yanda MEEMA tayi ba... Idanuwan sa ya lumshe sanda ta gifta sa ta wuce ƙamshin daddaɗan turaren ta na Arab ya bugi hancin sa. Ya buɗe su yana bin bayan ta da kallo har ta zauna a saman dainning. Wani irin numfashi ya ja nan da nan idanun sa suka soma kaɗa wa, bazai iya jure wa ba dole ya nufi inda take shima ya ja kujera ya zauna, kamar zai yi kuka tsaban yanda yake kallon ta yace, "Zulaiha".

Kallon sa tayi sanda ta kai tea Cup bakin ta, ido cikin ido suke kallon juna sai dai fuskar ta a tamke yake tun zaman sa a wurin ta sake haɗe wa

"I love You, why don't you love me?"

Kawar da kanta tayi bata iya cewa komi ba taci gaba da shan tea ɗin, sosai yake tururi but haka take kaiwa baki tana kurɓa a hankali

Sai shima yayi shirun ya sanya mata idanu zuciyar sa babu daɗi

Wayan ta ta ɗauka ta soma latsa wa still tana kurɓan tea ɗin, Numban Ishaq ta rubuta sannan tayi dealing but switch off, tsaki ta ja tana ajiye Cup ɗin ta tashi tsaye ta wuce

Har ta kusa shiga ɗaki Umma da ta fito a nata ɗakin ta kwaɗa mata kira

Hakan yasa ta tsaya tana kallon ta, sai kuma ta buɗi baki a hankali tace, "Morning Mom".

"Kar ki koma ɗakin nan ki zo ki gyara mana parlour, sannan ki shiga kichen ki ɗaura mana girki".

Ita dai MEEMA tsaya wa tayi tana kallon ta bata ce uffan ba tunda bata san me tace ba

Sajjad da ya taho wurin ya kalli Umman yace, "Umma wani girki kuma? Haba Umma daga zuwan nata tana baƙuwa sai ki saka ta aiki? Ni gaskiya baza a saka min mata aiki ba".

"Sajjad ka fita ido na tun kafin in nuna maka fushi na, idan bata yi aikin ba haka zata zauna mana a gida sai dai muyi mu bata taci tayi kashi kamar wata uwar mu?" Sai kuma ta juya ga MEEMAN tace, "ke ko baki ji abinda nace bane kin tsaya kin wani kafa min idanu kamar wacce zata haɗiye Ni?"

Sajjad yace, "to ai bata san me kike cewa ba ko kin manta ba ta jin Hausa ne?"

"Ohh! To sai ka sanar mata da abun da nace".

Juya wa MEEMAN tayi kawai zata shige ɗaki

Umman tayi saurin janyo ta tace, "babu inda zaki shiga dan uban ki, na ce ka sanar mata ko?" Ta ƙare maganar da daka wa Sajjad ɗin tsawa

"Umma yawa fa kike yi wlh, haba don Allah baki ga yanda take bane taya zata iya wani aiki? Kema daga gani kin san ƴar hutu ce baza ta iya waɗannan aikin ba Gaskiya, don Allah Umma kiyi hakuri ki barta".

"Iyeeeee Sajjad Ni kake faɗa wa haka don uban ka? Wato ta zauna sai dai Ni nayi ita tana luƙume a ɗaki saboda ita ƴar hutu? To nan ba gidan uban ta bane wlh idan har tana son zaman ta a gidan nan dole ne sai ta yi min bauta". Ta ƙare maganar tana jan hannun MEEMAN da cewa, "ai dole ki gane idan na tasa ki gaba".

Da sauri Sajjad ya riƙe Umman yana cewa, "don Allah Umma ki sake ta wai meye haka ne? Ni zan yi aikin a madadin ta ki sake ta".

While MEEMA kallon su kawai take yi zuciyar ta kamar ta fito tsaban baƙin ciki, ganin Umman ta ƙi sakar ta sai ta ƙwace hannun ta idanuwan ta har sun soma cika da hawaye, bata ce komi ba ta juya ta shige ɗakin

Nan Umma ta yunƙura zata bi bayan ta tana kiran sunan ta

But Sajjad ƙiri-ƙiri ya tare ta ya hana ta wuce wa, "haba Umma haba Umma ki ƙyale ta".

A fusace tace, "to bari uban naka ya dawo barin gidan nan zata yi". Sai ta wuce fuuu ta nufi kichen

Shi kuma ɗakin Murjanan ya wuce zai shiga, sai dai MEEMAN ta garƙame ƙofan da keey, dole ya haƙura ya wuce nasa ɗakin.


                  MEEMA bata buɗe ɗakin ba har sanda ta ji muryan Murjana kafin ta zo ta buɗe mata ta juya ta koma

Da kallo Murjana ta bi bayan ta tana ƙare wa rigan jikin ta kallo, har ta shiga ciki ta kasa ɗauke ido a kan rigan domin yanda take matuƙar son irin rigan a rayuwar ta, sai dai har yanzu bata mallake sa ba don har kasuwa suka je a lokacin ita da Habiba but basu samu ba, dole suka haƙura tunda a lokacin sun so suyi ankon ta ne sanda za'a yi auren Amina. Cire kayan ta tayi ta sanya riga da skert na atamfa kafin ta fice ɗakin. Can sai ga ta ta shigo a lokacin MEEMA ta buɗe Trolly ɗin ta ta ciro computern ta ta koma ta zauna. Tsaki ta ja tana ɗauke kai daga kallon ta

Ita kuma MEEMAN sai a lokacin ma ta ɗago da idanun ta ta dube ta, kawar da kai tayi ta ci gaba da abin da take yi

While Murjana tuni ta sake fice wa tunda dama wayan ta ta dawo ɗauka

Fitan ta babu daɗe wa Habibah ta shigo tana kiran sunan MEEMAN fuskar ta ɗauke da fara'a

Itama ganin ta yasa ta tsayar da abinda take yi tana murmusawa

"Sister I miss you so much, I can't bear to say let me come and see you." Tayi maganar bayan ta zauna a gefen MEEMA ta riƙe hannun ta

Sitll da murmushi a fuskar ta tace, "me too".

"But your dress looks good on me, and it looks great on you. You are so beautiful."

Kallon ta kawai tayi bata ce komi ba illa murmusa wa da take yi

"Aren't you working? Because we're going to our Part today stay for us there, I'll be happy with that".

Jinjina kanta tayi kafin tace, "ok I will go". Ta ƙare maganar da rufe computern tana ɗauka ta tashi ta mayar a cikin Trolly ɗin ta, sai ta zaro irin rigan dake jikin ta sak sai dai shi blue color ne, ta kalli Habiban dake zaune tace, "take it's for you".

"Wow! Thank you so much. Thanks again". Tafaɗa cikin farin ciki bayan da ta taso ta amsa rigan

"Don't worry there is no gratitude between us." Itama MEEMAN tafaɗa cikin murmushi kana ta mayar da Trollyn ta rufe sannan ta tashi tana kallon ta tace, "ok let's go".



           Suna fita Habibah da ta hangi Murjana zaune a kan dainning, da gudu ta isa wurin ta tana shaida mata kyautar rigan da MEEMA ta bata

Yayinda MEEMAN ke tsaye a wurin da ta barta bata motsa ba tana kallon su, sai dai a yanzu ɗin murmushin fuskar ta ya gushe

Ita Murjana taɓe baki tayi cike da isa tace, "ai yayi miki kyau tunda kin je kin roƙe ta kin zubar mana da mutunci, ke dai wlh Habibah baki yi ba a rayuwa". Sai ta ja tsaki tana banka mata harara ta mayar da hankalin ta kan abincin ta

Habibah da ta saki baki tana kallon ta sai tace, "to fa! Gaskiya Murjana akwai gyara a lamarin ki, har yanzu baza ki dena wannan ɗabi'an naki ba bayan kin san da cewa ita ƴar uwan ki ce, to Ni meye ma a wuri na don na roƙe ta ai kin san Ni ba irin ki bace domin ba Ni da girman kai".

"To kar dai ki gaya min magana don Allah ki tashi min akai".

Tsaki kawai Habiban ta ja tana juya wa ta wuce wurin MEEMAN da har yanzu idanuwan nata a kan su suke, bata iya mata magana ba sai jan hannun ta da tayi suka fice.




           Suna fita Murjanan ta tashi da sauri ta nufi ƙofan ta leƙa su, ganin da tayi sun bi hanyar Part ɗin su Habiban sai ta koma ta rufe ƙofan ta wuce ɗakin ta da sauri, tana shiga ta nufi wajen Trollyn MEEMAN ta saka hannu zata buɗe.
[10/10, 3:41 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎

*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED ND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*




                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
















                             *NO_17*

               Koda tayi ƙoƙarin buɗe wa ya ƙi buɗuwa dole sai ta saka code, hakan yasa ta saka sunan Zulaiha but ya ƙi buɗe wa, sai da ta tsaya tayi tunani kafin ta tuna sunan da ake kiran MEEMA da shi, shima ta saka ya ƙi, ta saka sunan mahaifin ta Faruk nan ma ya ƙi buɗe wa, ta saka sunan Daddy domin a tunanin ta haka MEEMAN take kiran sunan Mahaifin ta but nan ma ya ƙi. The same ƙaramin jakan shima da akwai code, cike da jin haushi ta tashi ta fice sabida rashin cikan burin ta, amma dai a sannu a sannu zata riƙa sanya mata idanu domin ta gane Numban da take sanya wa.







✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

             Suna shiga Part ɗin su Habiban babu kowa a parlour'n, sai tace mata, "she just seat there and called her mother." koda ta je tana Toilet tana wanka shiyasa ta dawo tana mata murmushi tace, "Come, let's go to my room."

Tashi MEEMAN tayi ta bi bayan ta suka shiga ɗakin Habiban

Nuna mata kan gadon ta tayi tace mata, "set". Sannan ta fice ta ɗauko mata Fresh Yo me sanyi ta haɗo da Cup, zuba mata tayi ta miƙa mata tace, "take drink".

Murmushi MEEMAN tayi mata ta sanya hannu ta amsa tana me furta, "shukran". Kafin ta sanya a baki ta ɗan kurɓa kaɗan

Habibah cike da fara'a tace, "You can also teach me Arabic because I really like it."

"Ok insha Allah If you want I will teach you".

"Thanks. But I want you to tell me about your country. In the past we wanted to come but Baba refused to bring us."

Murmushi kaɗai MEEMAN tayi bata ce komi ba

Habiban na shirin magana sai ga Inna ta tura ƙofan ta shigo, kallon su tayi fuska a ɗaure tace, "uban me wannan yarinyan ta zo min a nan? Ke kika kawo ta ko Habibah ban miki kashedi ki fita harkan ta ba?"

Tura baki Habiban tayi tace, "kai Inna Wai me tayi muku ne da kuka tsane ta? Ni dai ina son ta tunda ƴar uwata ce kuma idan aka tsaga jini na dole sai an ga nata a ciki.."

"Uban ki tayi mana, ki je ki tambayi uban ki sai ya faɗa miki abinda tayi, tun wuri ki sallame ta ta bar min gida tun kafin in saɓa miki wlh, kuma ki zo ki tattara kayan ki ki wuce gidan Amina tunda ke ba kya jin magana, gwara ki je can ki zauna da ita ki riƙa mata aiki. Ki zo ki wuce kar ki sake kuma in dawo in tarar da ita wlh na gaya miki". Bata jira cewar ta ba ta ficewar ta

Gaba ɗaya zuciyar Habiba babu daɗi don har ƙwalla ne suka taru mata a idanu, dole ta mayar da su ta saka wa fuskar ta murmushi saboda kallon da MEEMAN take mata tace, "Don't worry. Inna is talking about the job she did for me."

Gyaɗa mata kai kawai tayi ba tare da tace uffan ba.



           Shiru ne ya ratsa saboda Habibah ta kasa yadda zata yi ta sanar mata, "Let them go". Tun da ita ta kawo ta kuma yanzu idan tace mata, "su tafi." Zata iya gane Innar ta ce ta kore ta

Ita kanta MEEMAN duk da bata yarda da abun da Habiban ta sanar mata ba domin a jikin ta ta ji cewa faɗan da Innar ta yiwa Habibah a kanta ne. Shiyasa ta tashi tana kallon ta tace, "I'm leaving because I have a job. "

"Ok, let's go with you." Habiban tafaɗa tana mata murmushi

Fita suka yi ta kaita har bakin ƙofan su Murjana, bata shiga ba tayi mata sallama ta koma

Ita kuma MEEMAN ta buɗe ta shiga

Umma da Murjana ce a Parlour'n while Umma tana sanar mata da abun da ya faru ɗazu. Shiyasa yanzu da ganin MEEMAN sai Murjana tace mata, "Zulaiha, come here, Ummah she's calling you. "

Tsaya wa tayi tana kallon su, sai kuma ta taka ta isa wurin su ta tsaya ƙiƙam a kansu tana kallon su

Murjana tace, "Umma says she will not guarantee that you will stay in this house. You have to go out to work. It is not possible for you to sit on the room of a girl who is being cooked in your mouth and eat and then go back to bed, you have to do the housework since my mother gave it to you."

"Work?" According to MEEMAN full of surprise on her face

"Yes working or you Don't do it?"

"Na'am I can't". Tayi maganar tana juya wa ta wuce ɗaki. Tana jin Murjanan na zagin ta but bata ko juya ba har ta shige

Umma tace, "wai me tace ne?"

"Cewa tayi wai baza ta iya ba, ki ji fa Umma?"

Ƙwafa Umman tayi tace, "bar Ni da ita bari Abban naku ya dawo ai ya kusa zuwa. Je ki kira min Sajjad a ɗaki".

Tashi tayi ta wuce ɗakin Sajjad ɗin, koda ta je ta ganshi a kwance a saman gado yana ta sharan barci. Hannu ta sanya ta soma tashin shi tana kiran sunan shi

Daƙyar ya buɗe ido ya zuba mata yana kallon ta

"Umma na kiran ka".

Shiru yayi kawai yana kallon ta

Ita kuma ta juya ta fice abin ta, ta koma wajen Umma tana sake zuga ta a kan MEEMAN

A lokacin da Sajjad ya fito shima Abban ya dawo

Sannu da zuwa suka yi masa

Ya amsa yana zama cike da gajiya

Umma ta tashi ta kawo masa ruwa kana ta zauna tana kallon sa tace, "dama yanzu jiran ka nake yi Abban Sajjad, a kan wannan yarinyan da ka kawo ta ka ajiye min babu aikin fari bare na baƙi haka zata zauna min a gida wato? Kuma ɗazu na ce tayi min aiki ƙiri-ƙiri Sajjad yace baza ta yi ba, to Ni ban gane abin da ake nufi da ita ba domin wlh baza ta zauna min a sashi ba ta aikin komi ba sai dai ta ci ta sha abun da ta iya kenan, idan haka ne sai dai ta koma sashin Zubairu gaskiya".

Sajjad da ya buɗe baki ya soma magana Abba ya katse shi da cewa, "kayi shiru Sajjad ban son jin bakin ka. Ke kuma Jamila meye ne na son takura mata don Allah? Mene ne a kan aiki ca nake yi na ce zan kawo miki me aiki but kika ƙi? To ki barta kawai ta zauna tunda ko kin saka ta na tabbata bata iya ba,

Please Login or Register in order to submit comment