Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikin gidan sun tafi kai rahoto wajen ƴan sanda

A lokacin ne motocin Umar Faruk suka shigo gidan kusan su huɗu, da shi da Momy tare da Abdul suka taho. Bayan an buɗe musu kofofin motan suka fito gaba ɗayan su

Bazan iya misalta muku a halin da Umar Faruk yake ciki ba, duk da yana iya ƙoƙarin sa wajen ɓoye tashin hankalin sa da halin da yake ciki but kyakykyawar fuskar sa sai da ya bayyana damuwar da yake ciki

Haka ma Abdul domin shima zan iya ce muku ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tashin hankali da jin an rasa Masoyiyar sa, sosai yake jin ƙaunar ta a zuciyar sa wanda gaba ɗaya ta mamaye masa zuciya ta hana sa saƙat, duk da har yanzu be taɓa tunkarar ta da zancen soyayyar sa ba, kuma tun ganin ta sau ɗaya be sake ba bare ya bayyana mata halin da yake ciki a ƙaunar ta, babu abun da ya fi ɗaga masa hankali jin cewa Umar Faruk zai aure ta, shiyasa gaba ɗaya a kwana ɗayan nan yake cikin tashin hankali, sai ga shi kuma abun ya daɗu saboda ɓacewar ta

Momy kuwa babu wanda ya fi ta shiga farin ciki da jin wannan labarin, sai dai ko kaɗan bata nuna a fuska ba sai alhini da tashin hankali da ya bayyana a fuskar ta, wanda har ƙwalla sai da ta fitar a gaban Umar Faruk a sanda ya je musu da zancen. Ita da Luwaira tamkar zasu zuba ruwa a ƙasa su sha tsaban farin ciki

Yanzun ma da suka shiga ciki. Umar Farouk shi be iya zama ba tunda ya gaishe su yayi musu jaje ya tambayi Uncle Hashim?

Shi ne Jalila ta sanar mishi a halin da ake ciki

Hakan yasa ya fice ya koma haraban gidan yana riƙe da wayan sa a hannu yana laluba Numban Uncle Hashim ɗin don jin inda yake ya biyo bayan sa

Sai yace mishi, "ga shi nan ma a hanya suna dawo wa."

Hakan yasa ya dakata daga bakin motan sa ya harɗe hannayen sa a ƙirji yayi shiru, idanun sa har kaɗa wa suka yi saboda tsaban tunani, abin da kawai ya zo masa a zuciya kidnapper ne suka sace ta, kuma zai iya kashe ko nawa ne koda dukiyar shi zai ƙare domin a amso ta, yana matuƙar ƙaunar ta sosai a ransa. Soyayyarta ta rigada ta kama mishi zuciya wanda yana jin bazai iya koda kwana ɗaya ne be sake sanya ta a idanu ba

Abdul shima fitowan yayi ya zo ya tsaya a wajen sa fuskar sa duk a dame duk da babu wanda ya san a kan me ya shiga tashin hankali haka

Ita kanta Momy sosai take mamakin yanda ya nuna damuwarsa har ya buƙaci zai biyo su.

                Sanda su Uncle Hashim suka dawo gidan a lokacin ne Umman Laɗifa da ita Laɗifan suka zo gidan su ma, sai da suka gaisa kafin suka shige ciki

Uncle Hashim da Umar Faruk suna tsaye bakin motan shi suna zantawa, inda Uncle Hashim ɗin yake faɗa mishi a halin da ake ciki yanzu

Jan numfashi yayi shi kuma yana kallon sa da cewa, "I think it was the kidnappers who took her. Abin da nake tunani kenan."

"Nima haka nake tunani, duk yanda aka yi su ne suka ɗauke ta, sai dai mu jira har sanda zasu kira mu tunda abun ya faskara, Numban ta ba ta shiga har yanzu da alamu sun salwantar da wayan nata ne." Uncle Hashim Yafaɗa fuska babu fara'a zuciyar sa na suya

Dafa kafaɗan sa yayi yana kallon sa yace, "haka ne. But we must do our best to answer her, bazai yiwu mu bar ta a can ba, bamu san me zai same ta ba".



                 Har aka kira sallan magriba Umar Faruk suna tare da Uncle Hashim

Momy da Abdul tuni sun koma gida tunda suka yi musu jaje

Har zuwa dare babu labari daga wajen ƴan sanda duk da kuwa suna iya bakin kokarin su wajen sun ga sun nemo ta, bare akwai hannun manya musamman da suka ga Umar Faruk ya sake zuwa da kansa, haka sukai ta zirya babu inda basu duba ba har a gidan talabijin ɗin da take aiki an yi sanarwa duk da ba'a saka hoton ta ba, haka ma gidan rediyo duk an kai rahoto

Yanzu kawai jira suke yi su ji an kira su an buƙaci kuɗi tunda sun bar zancen a kan duk yanda aka yi ƴan kidnapped ne suka ɗauke ta.








✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

                Idanuwan ta ne suke buɗe wa suke rufe wa, dishi-dishi sosai take gani wanda hakan yasa ta ɗau lokaci tana rufe idanun ta mayar da su har sanda ta buɗe su tarwai tana kallon cilling ɗin ɗakin. Yanda komi ke juya mata ne ta kasa gane a inda take yanzu ɗin, a hankali komi ya soma dawo mata daga sanda suka fito ita da Laɗifa har sanda wani Mutum ya tura ta a cikin mota, sai kuma sanda ta ji numfashin ta ya ɗauke sakamakon toshe mata hanci da aka yi da handkerchief. Daga nan ne bata sake sanin me ke wakana a duniyar ba sai yanzu da ta farka ta tsinci kanta a wannan ɗakin. Zumbur ta tashi zaune tana ƙara ware manyan idanuwan ta da suka sake shanyewa suna buɗe wa daƙyar a cikin ɗakin da babu komi sai katifan da take kwance a kai, sosai take bin ko ina da kallo tana son ganin ta farka a wannan mummunan mafarkin da take hasashen tabbas mafarki ne, tabbas ba da gaske ne ba. Sai da ta fi mintuna goma a haka tana ƙare wa ɗakin kallo da son ganin ta farka, sai zare idanun ta take yi ko ta ina, sai kuma daga baya ta saka hannu ta soma mitstsike su domin ta kasa yarda har yanzu ɗin ba mafarki bane. Ta shafe fiye da mintuna talatin a wurin bata gasgata kanta ba, sai kuma daga baya da ta gane tabbas gaske ne ba mafarki ba, sace ta aka yi sannan aka kawo ta nan inda babu kowa aka ajiye ta. Sai kawai ta fashe da kuka a lokaci ɗaya tana tashi tsaye da mugun sauri, tsaban tashin hankali jikin ta har rawa yake yi domin ƙafafuwan ta ma sun kasa riƙe ta, inda ta ga ƙofa ta nufa da gudun gaske zuciyar ta na wani irin bugawa tamkar zata tsago ƙirjinta ta fito, fatan ta kawai idan ta taɓa ƙofan ta ganta a waje a bainar jama'a. Tana taɓa ƙofan ya buɗe sai dai ganin ta tayi a wani babban parlour da shima babu komi a ciki sai wani ƙofa da ya kasance kichen ne. Tsoro ne ya sake tabaibaye mata zuciya while idanuwan ta suna tsiyayar da hawaye domin a lokacin kukan nata ya tsaya cak sai hawayen da ke zuba tsaban kiɗima. Da gudu ta isa ɗaya ƙofan da ta tabbatar daga shi sai waje ta fincika da ƙarfi domin ganin ta buɗe, sai dai a rufe ruf ko motsi ba ya yi. Wani irin jijjiga ƙofan ta soma yi a lokaci ɗaya tana sakin wani irin ihu me uban ƙara, sosai ta ɓare bakin ta tana kuka da neman ceto da amon muryan ta da be fita sosai tsaban tashin hankalin da take ciki. Duk yanda ta so ta buɗe ƙofan ta fice ta kasa sai kuka take yi tana neman ceto. Daga ƙarshe kuma sai ta koma bin parlour'n da kallo tana tunanin har yanzu mafarki ne, tabbas zata farka, taya za'a ce ita ce a nan? Ita ce aka kama? To a kan me? Sai kuma ta koma bin ɗayar ƙofan da ta gani ta murɗa ta shige, kichen ne da windown sa a can sama wanda ko tayi ƙoƙarin ficewa ta nan babu hali. Dole ta sake koma wa inda ta fito a cikin ɗakin da ta ganta, can ma windown a sama yake, tana kallo sai ta zame a ƙasa ta kurma ihu tana kiran sunan Uncle Hashim, Hajiya, Ummee.. babu wanda bata kira ba a wanda ta sani but babu wanda ke jin ta. Sai ta faɗa kan katifan ta dinga rera kuka, tun tana yi da ƙarfin ta har ta gaji ta koma zubar da hawaye kaɗai, ta sadakar sace ta aka yi, amma su wane ne? Me tayi musu?. Tsawon lokaci tana a yanda take babu wanda ya zo wajen ta, har duhun magriba ya soma gabato wa yayinda ɗakin ya soma duhu. A lokacin ne ta ji kamar an buɗe Gate an shigo da mota. Sai ta tashi a firgice tana fice wa tayi ƙofan parlour. Jira kawai take yi ta ga wanda zai shigo da readyn da zaran ya shigo ta samu hanyar tsere wa. Wuri-wuri tayi tana neman inda zata samu abun bugu, sai dai a kaf gidan bayan ita babu komi a ciki, da alamu gidan sabo ne domin ko penti babu a cikin gidan. Jin an fara taɓa ƙofan sai gaban ta ya sake tsananta da wani irin bugawa saboda bata san wa zata gani ba, da sauri tayi bayan ƙofan da zaran an buɗe ƙofan hakan zai saka me shigowar bazai ganta ba, idanuwan ta sai tsiyayar da hawaye suke yi sun kasa tsayawa. Shiru taji an dakata ba'a buɗe ba, a hankali take jiyo murya ƙasa-ƙasa domin da alamu kamar mutane biyu ne a wajen, lumshe idanun ta tayi tana ɗaura hannun ta ɗaya a ƙirji saboda wani irin kyarma da jikin ta yake yi ga zuciyar ta da ke ƙara hauhawa tsaban buga wa, komi nata rawa yake yi sosai har hannayen ta, daƙyar take iya riƙe kanta a wurin domin ƙiris take jira ta faɗi ƙasa, tsoro da fargaba sun hana ta tsayawa ƙyam, sai ta sake manne wa a jikin bango saboda jin an sake taɓa ƙofan tare da murɗa wa za'a shigo.


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment