Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin ajiye ta? Ai a daren nan zamu kaɗa shegiya ta tafi.."

Kawu Zubairu yayi saurin taran numfashin sa da cewa, "to gadon mu fa? Haka zata tafi da dukiyan nasa bayan shi muke wa sintiri tun ba yanzu ba?"

"Gaskiya nima abun da na gani kenan?" Inji Umma da ta saka musu baki

Kawu Ali yace, "to ai dole sai mun amsa kason mu kafin ta bar mana gida". Sai ya juya yana kallon MEEMA da kanta ke saman cinyoyin ta tana ci gaba da kuka yace, "so since he died now where is our inheritance? Where is your father's property then we will share?"

Ɗago kai tayi tana kallon su, sai kuma tace, "Abee owned everything for me before he died, and now he has returned all his property to my name."

Wani ashar Kawu Ali ya fesar ya buɗe jajayen idanuwan sa zai yi mata magana sai Kawu Zubairu ya dakatar da shi

"Ka ga Yaya bar ta don Allah, na nemo mana mafita, ai maganar ma gado bata taso ba, kaf dukiyar sa ya zama namu wlh kuma dole sai mun amshe sa, amma yanzu idan kace zaka nuna mata halin da muke ciki zata iya tafiya wajen uwar ta ta bar mu, yanzu samun hanyar da zamu yi mu mallaki komi ya zama namu shi ne mafita, in yaso daga baya sai mu kore ta ta tafi, ka san tayi karatu tana da ilmi dole sai mun nuna mata siyasa komi ya dawo hannun mu".

Shiru Kawu Ali yayi yana tunani

Umma tace, "Abban Sajjad maganar Zubairu fa a kan gaskiya take, yanzu ai ko kace zaka amshi komi bazai yiwu ba, ta yiwu ma babu komi a hannun ta dole zata zauna damu har sai kun mallaki komi ya zama naku kafin ku kore ta".

Sai da Kawu Alin ya kalli Murjana yace, "ke ja ta ɗakin ki ku tafi ki nuna mata komi don a can zata zauna".

Tashi tayi tana kallon MEEMAN cikin yatsina tace mata, "she got up and they went".

Hakan yasa ta kalli su Kawu Alin ta ƙi ta tashi

Shi kuma yace, "she get up and followed her to her room."

Sannan ne ta tashi ta ja kayan ta tabi bayan ta suka wuce ɗakin Murjanan

"Yauwa to na yarda da shawaran ku hakan za'a yi, yanzu dai dole zamu ja ta a jiki domin mu mayar da duk ƙadarorin ta ya zama namu".

"Eh Yaya hakan za'a yi". Inji Kawu Zubairu

"To shikenan mu bar maganar yanzu sai zuwa gobe sai mu ci gaba da tattaunawa ko zamu ɓullo hanyar da ya kamata".

Da haka suka rufe maganar Kawu Zubairu yayi musu sallama ya tafi. Su kuma suka wuce ɗakin su.








                 *WASHE GARI*

            Sai tara da rabi MEEMA ta farka daga barcin da ya ɗauke ta tun sallan asuba da tayi ta koma. Ta jima a zaune a saman gadon bata iya tashi ba tana ta faman tunanin da ya zame mata jiki, da kuma yadda Rayuwar ta zata koma a nan gaba a inda bata saba ba. Sai daga baya ta miƙe sabida yunwan dake ƙwaƙulan ta don babu wanda ya zo ya tashe ta, daga ita sai farar riga me tsantsi da guntun wandon sa ta shiga bayi tayi brush sannan ta fita parlour'n ko ɗan kwali, sai dai ta kama gashin nata ta tufke shi a tsakiyar kan.


          Babu kowa a parlour'n sai wani kyakykyawar saurayi bafulatani fari sol, don da gani kaf gidan ya fi su kyawu domin shi zak Fulani ne babu silƙi, tamkar dai Mahaifin MEEMA ya haife sa saboda kamanceceniyar da suke yi, don shi ya fi kama dashi a kan su Kawu Ali. Yana zaune ne a kan sofa ya saka ear phone a kunnen sa, daga shi sai gajeren wando ko riga babu, kan nan nasa ya sha askin zamani wanda ƴan iska suke yi, ya bar tulin gashi sosai a tsakiyar kan wanda ko kitso za'a iya yi tsaban tsawon sa, wata macen ma baza ta nuna masa yawan gashi ba. Waƙa yake bi na Turanci duk ya kure parlour'n da muryan sa

MEEMA dake tsaye a bakin ƙofan tunda ta fito ta hange shi sai ta tsaya cak tana bin sa da kallo, tayi five minutes a tsaye a wurin tana faman kallon sa kafin kuma a hankali ta tako ta soma dosan cikin parlour'n zata wuce zuwa kan dainning table da ta hango

Gab ta iso kusa da wajen nasa ne ya ankare da ita, da sauri ya ɗaga idanu yana kallon ta, be san sanda ya miƙe tsaye a kan ƙafafuwan sa ba yana sake ware ido a kanta

Itama idanun ta na a cikin nasa ta kasa ɗauke nata a kanshi, sai dai ko kaɗan fuskar ta babu alamun walwala haka take kallon sa. Sai da ta kusa wuce wa kafin ta janye nata idanun ta nufi saman dainning

Har sai da ta zauna before ya kawar da kansa ya nufi ɗakin Umman sa yana kwaɗa mata kira kamar zai tsaga gidan

Kafin ya kai har ta fito da sauri tana faɗin, "lafiya Sajjad wannan wani irin kiran mafarauta kake min? Me ya faru ne?"

"Umma wace ce wannan? A ina kuka samo ta?"

Sai da ta bi inda yake nuna mata da kallo ta hangi MEEMA a zaune har ta soma haɗa tea ko kallon inda suke bata yi ba, sai ta ja tsaki don ta manta da ita a gidan sai yanzu da ta ganta, tace dashi, "jiya ta zo ai lokacin kayi barci, yarinyan Uncle ɗin ku ne na Riyadh".

"What..! You mean Zulaiha ce wannan?" Yafaɗa yana sake nuna inda MEEMAN take a zaune

"Eh ita ce. Ka bari idan Abban ku ya dawo sai yayi maka bayani Ni yanzu ina aiki". Tafaɗa tana juya wa ciki ta bar sa a wurin

Shi kuma juya wa yayi ya isa inda MEEMAN take

Sai da ya ja kujera ya zauna kafin ta ɗago tana kallon sa da manyan idanuwan ta

Washe baki yayi yana bata hannu yace, "Hi Zulaiha I'm Sajjad your brother".

Sai ta bi hannun nasa da kallo tana tsayar da taunan bread ɗin da take yi

Murmushi ya sake yi yana tura mata hannun yace, "I'm your brother fa? I was so surprised to see you here, I never thought of that, are you so good. The truth you very beautiful. "

Miƙe wa kawai tayi ta juya ta bar wurin

Shi kuma sai ya saki baki yana bin ta da kallo kamar zai zubar da yawu, har wani lanɗe baki yake yi. "Wow gaskiya tana da kyau. Wai dama haka take yarinyan? Amma gaskiya an cuce Ni da ba'a nuna min ita ba sai yanzu. Wow.. wow". Yake ta faɗi yana shafa ƙeyan sa, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin Umman nasa, ya same ta tana gyaran gado sai ya zauna a kan drowan gadon yana cewa, "Umma wlh yarinyan kyakykyawa ce sosai har kama take yi dani, amma a nan gidan zata zauna ko?"

Ɗago wa tayi tana hararan sa kafin tace, "Ni fa Sajjad ka rabu da Ni da wannan halin naka, ka kiyaye Ni wlh".

"Haba Common Momcy yawa ne, ki share kawai Ni fa yarinyan ta shiga raina ne wlh, I like her so much, kuma kin ga ƙanwa ta ce wani abu ne idan nayi tambaya game da ita?"

"To ka je ka tambaye ta mana ina ruwa na a ciki?"

"To ai Umma ta ƙi kula Ni ne, yarinyan tana da matuƙar class ta haɗu Allah fa ina gaya miki".

"Hohoho Sajjad baza ka rabu da Ni ba ko?"

"Sorry Momcycy na rabu dake." Ya faɗa yana tashi tsaye tare da sara mata, sai kuma ya matso kusa da ita yana cewa, "but Umma Ina Murjana sai in tambaye ta?"

"Ta je school".

Ɓata fuska yayi sai kuma ya juya ya fice. Har ya zauna a kan kujeran Parlour'n yana ta kallon ɗakin Murjanan, sai kuma ya tashi ya wuce ɗakin ya tura ƙofa ya shige

MEEMA dake ƙoƙarin cire rigan jikin ta zata ɗaura tawul ta shiga wanka, sai ganin sa kawai tayi a tsakiyar ɗakin, ƙara ta saka lokaci ɗaya ta ja rigan tayi sama da shi

Shi kuwa daskare wa yayi a wurin tsaban ganin kyakykyawar halittan ta da yayi, idanun sa kawai suke motsi a kanta

A lokacin da gudu Umma ta shigo ɗakin tana tambayar, "lafiya?" Saboda ihun da MEEMAN tayi har ɗakin ta. A kan Sajjad ɗin ta sauke ido sai kuma ta kalli MEEMAN, "ke lafiya mene ne?"

Ita dai tana tsaye ta maƙure a jikin bango tana kallon su don bata san me tace ba

Sai Umman ta ja tsaki tana cewa, "wannan ai shashanci ne kawai ki zo kina cika mana gida da ƙara. Kai kuma uban me kayi mata ne da zata fasa min dodon kunne?"

Daƙyar yake iya sauke numfashi, sai da ya ɗan ja fasali kamar ya dawo a cikin hayyacin sa kafin yace, "Babu Umma. Shigo wa ta kenan nima".

Dogon tsaki ta ja tana juya wa kawai ta fice

Shi kuma sai ya mayar da idanun sa kan ta kafin ya taka izuwa wurin ta

Hakan yasa tayi saurin haye wa gadon tana sake ware idanuwan ta kamar za su faɗo ƙasa a kansa, hannayen ta kuma suna a kan ƙirjin ta sai sake matse su take yi tana ƙanƙame jikin ta. Ganin da tayi ya ƙi dakata wa daga inda yake yana neman hayo wa gadon cikin ruɗe wa tace, "what are you doing here? Please get out."



Dariya ya saki yana ci je leɓe, sai kuma ya saka hannu zai riƙo ta yace, "Common Babe nayi zaton ke wayayyiya ce, ki riƙa abu kamar na classics big Girls mana, just I will hugg you because I really Love you".
[10/10, 3:38 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                         💎💎💎

*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏼‍


*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*




             *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._













                            *NO_13*

                  Da sauri ta sauka daga kan gadon ganin da tayi ya kusa taɓa ta. Fuskar ta babu walwala cikin ruɗu da tashin hankali tace, "what will you do for me? What is my connection with you? Please get rid of Me."

Tsaya wa yayi yana kallon ta domin yanda ta buɗe baki ala dole tana masifa sosai ta sake burge sa, ji yake yi kamar ya je ya rungume ta ya tsotse mata bakin da ya fi ɗauke masa hankali, sai kawai ya shafa kansa yana killer smile yace, "Babe I love you so much, I am so impressed by everything you do. Please I want us to be friends..."

"No I don't want to. I said go out". Ta katse sa a cikin tsawa

"Ok, calm down. I'll be out." Sai ya juya yayi bakin ƙofa har yana waigen ta, yana zuwa dai-dai bakin ƙofan ya dakata yana juya wa sosai ya kafe ta da ido yana haɗiyar yawu, har da wani lanɗe baki sai faman shafa kansa yake yi wanda alamu ya nuna ɗabi'an sa ne hakan. Ya ja wani soconni a wurin kafin ya juya ya fice

Wani irin ajiyan zuciya ta sauke har tana dafe ƙirjin ta ta zauna a bakin gadon, sosai zuciyar ta ke gudu kamar zata faso ƙirjin ta tsaban tsoro, a haƙiƙanin gaskiya ta tsorata da shi sosai domin abun da be taɓa faruwa da ita bane. Zumbur ta tashi kamar ta tuna da wani abu ta nufi ƙofa ta murza keey sannan ta dawo ta sake zama. Ta daɗe a wurin tana faman saƙa da warwara a ranta kafin ta tashi jiki a saɓule ta ci gaba da zame kayan nata, sannan ta ɗaura tawol ta shiga Toilet, wanka tayi ta fito ta wuce bakin dressing mirror, tsaya wa tayi kawai tana kallon kanta a mirror  har a lokacin fuskar ta babu wani ɗigon walwala, ƙare wa kanta kallo take ta yi har na tsawon lokaci kafin ta ja numfashi tana wuce wa wajen Trolly ɗin ta ta buɗe, kayan da zata saka ta ɗauko, sannan ta ciro cream lotions ɗin ta da take amfani da su ta shafa ta mayar, ta saka kayan riga da skert masu tsananin kyau, rigan me ruwan madara ne me taushi sosai tana da zane-zane a jiki wanda sai ka kula da kyau zaka iya hango wa kasancewar da kalan ruwan madaran aka yi, gajeren hannu ne da ita sai kwalliya da aka yi da zare dack brown color da kuma milk ɗin, sai skert ɗin sa Robber brown color da ta sanya har wajen cikin ta, sai ta ɗaura belt ɗin sa Shima Brown but light, gyara gashin ta tayi ta kama da ribom, bata saka komi a kanta ba ta ɗauki computern Abee da nata ta haye kan gadon, buɗe wa tayi ta soma aiki akai.

              Abun da Sajjad yayi mata shiyasa ko kaɗan ba ta sha'awar sake fita, shiyasa tayi zaman ta a nan tana ta faman aiki a computer, sai da aka kira sallan azahar kafin ta tashi ta gabatar sannan ta sake zama ta ci gaba har sanda Murjana ta dawo ta hau buga mata ƙofa. Da sauri ta rufe computern ta mayar a cikin Trolly ɗin ta sannan ta wuce ta buɗe mata. Su biyu ta gani a bakin ƙofan ita da wata sa'ar Murjanan har kayan school ɗin su iri ɗaya ne

Ita Murjana tsaki ta banka tana hararan ta ta wuce ciki

While ita kuma ɗayan washe baki tayi tsaban farin ciki kawai ta rungume MEEMA, sai kuma ta sake ta tana faɗin, "Oyoyo sister. Ni ƴar uwan ki ce suna na Habibah, Habibah Zubairu,
I am your uncle Zubairu's daughter, I am happy to see you". Ta ƙare maganar tana bata hannu

MEEMA bata gama fahimtan maganar nata ba sabida kasancewar ta haɗa da Hausa, amma sai ta miƙa mata hannu itama tana ƙirƙirar murmushi tace, "me too".

Shigowa ɗakin Habiban tayi tana riƙo hannun MEEMAN ta ja ta suka zauna a kan gado tace, "yanzu da zamu dawo school Murjana take sanar min da zuwan ki, shi ne nace bari in zo in ganki".

MEEMA kallon ta kawai take yi, sai kuma ta murmusa tace, "sorry i don't understand, what did you say?"

"Oh don't you understand Hausa?" Habiban tayi magana tana ware idanu da mamaki

Still MEEMA tana murmushi ta gyaɗa mata kai

"Ok sorry I don't know, but do you want to teach you our language?"

Shiru MEEMAN tayi bata iya ce mata komi ba

Sai ita kuma tayi murmushi tana riƙo hannun ta ta haɗa da nata kafin tace, "I will pass our Part, I will come back to see you later, because even in my soul I like you".

"I like you too". Tafaɗa itama sosai a wannan lokacin tana murmusa wa

Tashi tayi Habiban ta ɗaga mata hannu ta fice

Da kallo ta bi bayan ta har ta ɓace wa ganin ta, a ranta sosai ta ji sanyi haɗuwar ta da Habiba zata samu wacce za suna magana ba kamar Murjana da ko kallon ta ba ta yi, ko magana ta ƙi yin mata

Yanzu ma tuni ta fice a ɗakin tunda ta sauya kaya. Tana fita parlor Sajjad ya tare ta da maganar MEEMA, shi ne abin ya bata haushi ta ja tsaki tana cewa, "wai Yaya meye haɗin ka da ita ne da kake son sanin wani abu a kanta? Gaskiya yarinyan bata yi min ba bcoz tana da jijji da kai, ko don ta ga tana da kyau ne?".

Dungure mata kai yayi yace, "kina dai baƙin ciki ne bayan haka meye a jikin ta da zaki ce bata miki ba? Ni kuma ina son ta".

Tura baki tayi ta wuce ta zauna a saman dainning ta soma haɗa lunch

Sai ya biyo ta yana cewa, "Common Sister ki sanar dani abun da na tambaye ki kinji? Haba My sister".

Sai da ta taɓe baki kafin tace, "Wai Mahaifin ta ne ya rasu shi ne ta zo nan".

"Wow da gaske?" Yafaɗa yana buga tsalle

Da kallo ta bi sa kafin tace, "lafiya Yaya meye na murnan?"

"Uhmm daɗi nake ji sosai a raina, kenan ta dawo nan da zama? Kin ga shikenan zan same ta".

"Wai kana nufin da gaske son ta kake Yi?"

"Sosai ma. Kuma auren ta zan yi domin dai-dai kala ta ce ita, macen da nake fatan samu kenan, Abba na dawo wa zan sanar mishi ayi-ayi a aura min ita".

Dariya Murjana tayi tace, "daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi Yaya? Tab ɗijim zan ga inda draman nan zata ƙare, akwai kallo a gidan nan wlh". Ta ƙare maganar tana sake fashe wa da dariya

"Ke fa baki da kunya na lura, amma bari in je in dawo kafin Abba ya dawo zaki ga me zan yi". Ya tashi ya fice

Ita kuma sai dariya take yi, daƙyar ta dakatar da shi ta soma cin abincin.



              A lokacin ne MEEMA ta fito ta nufi wajen dainning ɗin

Da kallo Murjana take bin ta har ta ƙariso ta ja kujera ta zauna. Sai ta ja tsaki tana ɗauke kai ta ci gaba da cin abincin nata

Ita kuma MEEMA kallo ɗaya tayi mata itama ta cire nata idanun a kanta ta soma serving kanta. Duk da tana jin yunwa but daƙyar ta iya yin spoon uku ta ture abincin, hannu ta sanya ta janyo Flaks ɗin dake wurin ta zuba ruwan Lipton ɗin a cikin Cup, ganin babu kayan haɗa tea ɗin a wurin sai ta ɗauka haka nan ta soma sha ko sigar babu a ciki

Murjana dake kallon ta ta ƙasan ido sai ta taɓe baki a fili ta furta, "sanabe gai da uwar miji a kasuwa. Zaki saki ciki ki riƙa cin abinci ne tunda nan ba can bane, ƴar wahala".

Dayake MEEMAN ba jin ta take yi ba shiyasa ko ɗago wa bata yi ba bare ta kalle ta, har ta kurɓe ruwan lipton ɗin ta tashi zata koma ɗaki

A time ɗin ne Habiba ta shigo ita da Inna Mahaifiyar ta, dayake itama ta shigo domin ta ga MEEMAN ce tunda Kawu Zubairu ya sanar mata

"Yauwa Inna kin ganta". Cewar Habibah cikin farin ciki tana me ƙarisa wa kusa da MEEMAN ta riƙe mata hannu. Sai kuma ta juya ga MEEMA tana ce mata, "she's her mother".

Hakan yasa ta ɗan saki fuska tana gaishe ta

Inna kuwa sai ƙare wa MEEMAN kallo take yi tana faman yamutsa fuska da taɓe baki, domin itama irin waɗannan jarababbun matan nan ne, don har ta fi Umma iya shege

Sai da Habiba tace mata, "Inna gaishe ki fa take Yi?"

"To Ina na sani tunda ba iya Yaren nayi ba?". Sai kuma ta ja tsaki ta wuce tana tambayar Murjana, "Ina Umman ta?" Hango ta da tayi zaune a saman dainning

"Tana ɗaki". Ta bata amsa a taƙaice

Hakan yasa ta wuce ciki

Habiba itama tuni ta bi MEEMA cikin ɗaki.



             Inna na shiga ɗakin Umma ta ganta zaune tace, "ashe kina ciki na shigo ban gan ki ba?"

"Eh ina ciki Halima. Aiki na gama kuma na zauna ban fita ba".

Inna zama tayi a gefen ta kafin suka gaisa kana tace, "Wai Jamila haka zaki zauna da yarinyan nan a gidan ki. Me ya kai ki amsar ta?"

"Wace yarinyar?" Umma ta tambaya tana kallon ta

"Wannan Yarinyan mana na wajen Faruku".

"Ohh wlh Ni manta wa nake yi da ita a gidan, to ya na iya tunda ba dauwama zata yi ba, su ma su Abban Sajjad ɗin ai suna shirin koran ta ne bayan komi ya dawo hannun su".

"Ai gwara haka don wlh bata da wurin zama a wannan gidan haka kawai, Ni kinga Habibah ne ma naga tana wani murna da zuwan ta, Ni fa bazan lamun ta hakan ba wlh sai in saɓa mata".

Umma tace, "ai Ni dayake Murjana babu ruwan ta kinga ko shiga safgarta bata yi ba".

"Na san maganin Habiban ai, bari in je wanki nake yi na taso". Cewar Innar tana tashi tsaye

Itama Umman tashi tayi ta bi bayan ta suka fita Parlour suna sake zantawa

Innar ta tambayi Murjana dake zaune a kan sofa a yanzu tana latsa waya, "Ina Habiban?"

"Ta bi wancan yarinyan ciki". Tayi maganar cikin taɓe baki

"Habiba.. Habiba". Inna ta ɗaga murya tana kiran ta

Da sauri ta fito tana faɗin, "Inna gani nan fa ba nisa nayi ba".

Hararan ta tayi tana cewa, "ai na san ba nisan kika yi ba, uban me kike yi a wurin ta?"

"Inna babu komi fa muna hira ne tunda.."

Katse ta tayi tana faɗin, "dalla rufe min baki, idan baki yi wasa ba wlh zan saɓa miki a gidan nan, ina ruwan ki da ita daga zuwan ta zaki fara maƙale mata?"

"Inna ƴar uwa ta ce fa". Tafaɗa tana zaro idanu

"Eh ƴar uwan taki, ba na son alaƙar ku nace, wuce mu je dalla".

Habiba cike da rashin jin daɗin abun da uwar nata tayi mata haka ta bi bayan ta suka fice

"Nima fa wlh yarinyan ba burge Ni tayi ba Umma, idan ba ma zubar da kai ba na Habibah daga zuwan ta ta wani fara maƙale mata, da can suna son mu ne da zata zo mana gida?"

"Nima abun da na gani kenan, ki barta ai mu ma ba dauwama zata yi mana a nan ba, can ta wuce dangin uwar ta ba dai nan ba, don bazan riƙe ɗan riƙo ba wlh".

"To Umma amma fa bazai yiwu ta zauna a haka kullum ki girka ki bata ba babu abinda zata rika yi ƙatuwar budurwa kamar ta, nan ba gidan su bane dole ta riƙa yin aikin gida ko nima zan huta wlh, kinga tunda na fita ke baki gyara parlor'n nan ba ita kuma bata zo tayi miki ba."

Umma tace, "to dama ai na barta ta ɗan kwana biyu ne kafin ta soma mana aiki, wlh ƴar aiki aka kawo mana don bazai yiwu ta ci ta sha a gidan nan ba ta luƙume a ɗaki, ki bar ta zuwa gobe komi na gidan nan dole tayi shi, wannan sanƙamemiyar budurwan da a yanzu tana gidan miji ina zan iya da ita?".





                ******

          MEEMA dake zaune a ɗaki duk maganar da suke yi a kunnen ta ne tun fitan Habibah, sai dai bata fahimci ko eh ba a ciki, tayi jiran ko Habiba zata dawo amma shiru shiyasa ta kwanta tana ɗaukan wayan ta ta soma latsa wa

Murjana ce ta shigo ɗakin ta ganta a haka, ta ɗauke kai tana wani ciccin magani ta wuce ta shiga Toilet. Bata jima ba ta fito tana kallon MEEMAN tace, "ke dalla tashi ki fita zan gyara ɗaki na tunda baki san ki gyara min ba".

Idanu ta zuba mata tana mamakin yadda take hararan ta tana mata tsawa a kai. Shiru kawai tayi tana sake ƙare wa Murjanan kallo, ko a girme zata bata good 5years ko fiye da haka..

        "Keee! Ko ba kya ji ne ki tashi nace ko gadon uban ki ya siya min ne?" A wannan karon ma Murjanan tayi maganar a fusace tana ɗaga murya

Tashi zaune MEEMA tayi tana kallon ta sosai kafin tace, "what do you say I don't hear you?"

"Uban ki nace banza kawai. I said get up and go out".

Ɗauke kai tayi daga kallon ta tana me ɗaukar wayan ta ba tare da ta furta komi ba ta tashi ta fice a ɗakin.. Kai tsaye Parlour ta koma ta zauna tana ɗaura kanta a saman kujeran ta lumshe idanuwan ta

Sajjad ne ya buɗe ƙofan ya shigo yana rera waƙa ear phone a kunnen sa. Idanuwan sa suna sauka a kanta yayi saurin zare ear phone ɗin yana bin ta da kallo kamar zai haɗiye ta tsaban kallo while zuciyar sa cike da farin cikin ganin ta

Ita kuwa tuni ta ɗago tun sanda ta ji muryan nasa itama tana kallon sa, sai dai ta sake haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba.
[10/10, 3:39 PM] نفيسة

Please Login or Register in order to submit comment