Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

    Yanda MEEMA take ihu zaka ce an yanka ta ne saboda abinda bata taɓa ji bane ya faru a rayuwar ta, tunda uwar ta ta zuƙuna ta haife ta ba'a taɓa marin ta ba, shiyasa duk ta gama gigicewa ta rasa gabas da yamma

Abee kuwa tuni ya soma kuka saboda ganin abin da Zubairu ya yiwa ɗiyar sa, idan da ace yana da ƙafafun tashi wlh babu abinda zai hana shi be rama mata ba saboda yanda zuciyar sa take tafarfasa, cikin rawan murya da kuka daƙyar ya soma maganar cikin gurɓataccen hausan sa yace, "Yaya Zubairu meyasa ka maran min Ummy? Meyasa.. meyasa? Me tayi muku? Don Allah kar ku kashe min ita na roƙe ku".

Yanda Abee ke yi ne sai duk suka saki baki suna kallon shi

"Ikon Allah yanzu kai Faruk don an yi mata wannan ɗan marin shi ne kake kuka ka tayar da hankalin ka haka? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. tabbas  maganar da ake faɗa ya tabbata, ashe bayan rashin auren da ka ƙi kay mata take yawon karuwanci kai ma bin ta kake yi wato? Ita shafaffiya da mai baza a taɓa ta ba tunda kana samun abinda kake so ko?..."

"Enough Yaya... Enough...?" Yayi maganar cikin rawan baki sosai wanda daƙyar ya iya faɗi tsaban tashin hankalin dake cin sa da jin abinda ɗan uwansa yake faɗa

Yaya Ali da yayi maganar sai ya sake cewa, "dalla rufe mana baki ko zaka ce ƙarya ne bayan ga shi mun gani? Shiyasa Allah ya kama ka ga ka nan a kwance babu ƙafafu ciwon Cancer ya kama ka, to, wlh kaɗan ma ka gani muddin baka canza alƙibla ba, ka gudu ka bar ƙasan ka ka zo nan ka ɗauki al'adun wasu, sannan ka koya wa ɗiyar ka karuwanci ga ta nan taƙi aure ganɗamemiya da ita, ƙannin ƙannin bayan ta mun aurar da su amma kai kaƙi, shiyasa ma matar ka ta gudu ta barka tunda muna da labarin komi, abin ma da yasa ka gan mu a nan don mun ji labarin ciwon ka ne, kar duniya ta tsine mana a matsayin mu na ƴan uwan ka muka zo mu taimake ka, zaka bamu wannan mara kunyan yarinyan taka mu je can mu aurar da ita ko ka rage nauyi a kanka".

Duk maganganun nan da Yaya Ali yake yi gaba ɗaya Abee ya tsaya yana sauraron sa inda hawayen fuskar sa ke sake kwaranya kamar an kunna famfo, domin ya ma kasa magana

MEEMA da sai yanzu ta gama dawowa hayyacin ta, sai ta tashi da gudu ta faɗa jikin Abee ɗin ta ta sake sakin kuka me tsuma rai, sosai take kuka tana kiran sunan sa, so take yi ta ce mishi ya dena kuka amma bakin ta ya ƙi furta wa illa kukan da take yi

Shi kuwa sosai jikin sa ke rawa yana hawaye babu daman taɓa ta, domin gaba ɗaya jikin sa ba ya aiki

Zubairu yace, "ka gani ko Yaya Ali, tun bamu je ko ina ba suna son su nuna mana halin karuwancin". Sai ya kalli MEEMA ya daka mata tsawa da cewa, "tashi ki je ki haɗo kayan ki mu tafi".

Ita duk bama tasan me suke magana a kai ba, ko kaɗan taƙi ɗagowa a jikin Abee illa kukan ta dake ƙara yawaita

Abee daƙyar yace dasu, "babu inda ɗiya ta zata bi ku wlh, na gode da taimakon naku Yaya zaku iya tafiya".

A zuciye Yaya Ali yace, "haka kace ko? Mu yi tattaki tun daga uwa duniya amma kaƙi bin umarnin mu? To shikenan Allah ya gani mun sauke haƙƙin ka tunda haka ka zaɓa. Taho mu je Zubairu yau zamu koma gida".

Haka suka fice gaba ɗayan su a fusace.


        Sai lokacin MEEMA ta ɗago kai tana kallon Abee ɗin da idanuwan ta da suka kaɗa suka yi jazur tace, "What are they saying Abee? Please tell me."

"No Ummy stop talking ok?"

Gyaɗa masa kanta tayi inda sosai hawayen ta suke tsiyaya

Girgiza mata kai yayi yana cewa, "Stop crying please I don't want to see your tears flow. Please Ummy".

Hannayen ta ta saka tana share hawayen, sai kuma ta saka hannun tana shafa inda Zubairu ya mare ta, wurin sosai ya kumbura yayi ja har yatsun sa sun fito, sai ta sake shigewa jikin Abee ɗin tana ɓoye fuskar ta jin wasu sabbin hawayen sun sake zubo mata

Be ce mata komi ba illa a haka suka ci gaba da zama, yana jin yanda take fitar da numfashi da shashsheƙa na tsawon lokaci kafin kuma yaji fitar numfashin nata ya sauya, hakan yasa ya gane ta samu barci, shima lumshe idanun sa yayi yana me jin hawaye sun cika mishi ido, ba komi ya tuna ba sai rayuwar su na baya, da yanda ada suke tsantsan cikin farin ciki ako da yaushe, sai dai kuma lokaci ɗaya Allah ya jarabbe shi da wahalhalun ciwukan nan, Cancer da ciwon sugar, yayi jinya na ɗan wasu watanni a asibiti inda lokaci ɗaya kuma side ɗin jikin sa ya dena aiki gaba ɗaya, mafarin kenan da suka sake rasa gaba ɗaya farin cikin su

Daga baya likitocin sun sallame shi domin sun ce, "jinyan sa sai dai a gida, saboda zai daɗe be warke ba, kuma hakan zai cinye musu kuɗi sosai ga wahalhalun zirga-zirga na asibiti," dole aka mayar dashi gida likita na kula da shi

Tashi ɗaya mahaifiyar MEEMA ta nuna gajiyawar ta da mishi hidima na yau da kullum a matsayin shi na majinyaci wanda be iya taɓuka wa kansa komi

A wani ranan da baza su taɓa manta wa ba MEEMA ta tafi school, sai dawowa tayi ta tarar da Ummeen ta ta tafi. Wanda sanadiyar tafiyan nata ne ciwo ya sake yin tsanani ga Mahaifin ta, domin ada yana iya magana sosai amma daga baya ya dena magana gaba ɗaya

MEEMA ta sha kuka wanda hakan ya saka har sai da tayi jinya tsaban ruɗu da tashin hankalin da take ciki, tana ganin lokaci ɗaya Allah ya jarabbe su da matsaloli kala-kala har hakan yayi sanadin tafiyan mahaifiyar ta, ta kasa yarda mahaifiyar ta zata yi musu haka ita da mahaifin ta, duk rayuwar da suka gina tsawon shekaru amma lokaci ɗaya ta rushe musu, meyasa baza tayi haƙuri na ɗan lokaci Abee ya samu lafiya ba? Meyasa zata nuna gajiyawa da laluran Abee ɗin ta? Ashe dama ba son su take yi ba da har zata iya tsallake su tabar su a wannan duniyar? Haƙiƙa abin ya taɓa ta wanda lokaci ɗaya gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi ta sauya mata, wanda tana ji kamar gwara mutuwar ta da wannan rayuwar, sai lokaci ɗaya MEEMA ta sauya sabida ƙunci da raɗaɗin da Ummeen ta ta sanya mata, ga kuma uwa uba wanda tafi ƙauna yana kwance tamkar matacce, hakan na nufin ta rasa kowa nata kenan? Ada ita me son fara'a ce matuƙa, ga surutu kamar aku don idan ta soma zuba ba ta jin bari, shiyasa wannan halin nata sai ya zamana kowa nata ne, idan har ta zauna a wuri dole sai ka santa, mahaifin ta ya koya mata sangarta da shagwaɓa domin ita bata san bari ba, hakan yasa ta taso yarinya me kazar-kazar da son Wasa har girman ta, tana jin ta tamkar dai yarinya ƙarama ce, ga dolanci irin na ƴan fari kuma gata Auta. Ga kuma yanda iyayen ta suka ɓata ta da gata. Lokaci ɗaya sai kuma komi ya juya mata baya, ta dawo tamkar Miskila.. ba ta dariya bare murmushi kullum gani take yi rayuwar ta mafarki ne akwai ranan da zata farka shiyasa ko yaushe cikin tunani take da damuwa, idan ka ganta tana murmushi to tabbas tana gaban Abee ɗin ta ne domin saka shi farin ciki.


       Shima da yaci gaba da samun kulawa domin tuni an kawo Nurse tana kula dashi ita take mishi komi, sai kuma likitan dake duba shi. a sannu a sannu ga shi har yana iya yin magana, shima daƙyar domin wani lokacin ba ya iya yi duk da yana son Yi

Babu abinda ya fi komi saka MEEMA farin ciki illa ganin Mahaifin nata ya soma magana, hakan na nufin wata rana zai warke ya tashi kamar yanda yake a baya. Kuma za su ci gaba da rayuwar su ta farin ciki ko da babu Mahaifiyar ta a tare da su. Idan ta tuna hakan shi ne take jin salama a rayuwar ta

Da farko ta dena zuwa school, sai da mahaifin ta ya soma samun sauƙi sannan ya matsa mata a kan, "ta koma". Yanzu haka tana degree ɗin ta ne a fannin Mas.Com. kuma tana zangon ƙarshe domin watanni ya rage mata. She's 26years all.


         Abee shi ɗaya ne wajen mahaifiyar sa, asalin su ƴan Yola ne Fulanin can. Mahaifiyar shi ita ce ta farko wajen mahaifin su Alh. Ahmad Riskuwa. Matan sa biyu da Maman Faruk sunan ta Zulaiha da kuma Jammatu, amma suna kiran ta da Jamma

Bayan Shekaru me tsawo da Zulaiha bata haihu ba sai iyayen Ahmad suka sanya shi ya ƙaro aure ya auri Jamma, ita kuma daga zuwan ta ta haifi Yaya Ali, bayan shi ta jima kafin ta sake haihuwa, inda ta sami cikin Zubairu

Ashe itama Zulaiha tana da cikin amma babu wanda ya sani. Sai da Jamma ta haifi Zubairu kafin cikin Zulaiha ya bayyana. Aikuwa ta sha habaici wajen su Jamma da ƴan uwan Ahmad, sai dai bata biye musu ba tunda Allah ya bata nata ba juya bace ita kamar yanda suka ce ɗin

Zubairu na da watanni huɗu aka haifi Faruk

Zo ku ga murna wajen Ahmad domin ji yake yi kamar ba'a taɓa haihuwar masa ba sai yanzu, domin ƙaunar da yake yiwa Zulaiha ya wuce kwatance, shiyasa dangin shi suke jin haushin ta sosai, sai kuma suka sami dama wajen rashin haihuwar ta suka saka shi ya ƙaro aure.


     Tun tasowan yaran Ahmad ya rigada ya bambanta su, domin ba ya iya ɓoye soyayyar shi ga Faruk. Wannan dalilin ne Jamma da yaran ta suka tsani Faruk sosai, ko kaɗan ba ya jin daɗin zama dasu illa wajen mahaifin sa da Mahaifiyar sa

Ana haka Jamma ta soma biye-biye wajen bokaye domin ta raba Faruk da soyayyar mahaifin shi, inda kuma ta sanya wa Zulaiha ciwo lokaci ɗaya ta mutu

Mutuwar nata shi ya jawo Ahmad ya samu ciwon zuciya, inda yayi jinya me tsayi kafin ya rasu.

     Faruk ya taso cikin maraici da uƙuban rayuwa, wanda ya gummaci mutuwar sa da rayuwar sa. Sai dai Allah shi ne me rayawa shiyasa har ya kai girman sa. A lokacin da mahaifin sa ya rasu ya gama secondary School ɗin sa, koda ya mutu kuma an ƙi ba shi gadon shi bare yaci gaba da karatu, sai ya koma aikin ƙarfi tare da taimakon dangin mahaifiyar shi da suka rage mishi, a haka yake rayuwa yake samun abin saka wa a bakin sa, domin be da wani amfani a gidan su tunda har koran sa ma sun yi, sai daga baya ne da ƴan uwan Maman shi suka nema masa ƴancin sa shi ne suka bar shi yana kwana a zauren gidan

Rayuwa taci gaba inda har su Yaya Ali suka gama karatun su suka sami aikin yi

A lokacin ne Allah ya taimaki Faruk ya haɗu da wani uban gida me kuɗin gaske yana mishi gadi, tsawon lokacin da ya ɗauka yana mishi aiki wanda ya yaba da hankalin sa, sai ya ɗauke sa ya tafi dashi can Riyadh kasancewar a can matar sa da ɗiyar sa ɗaya suke zaune, a nan kuma Nigeria kasuwanci yake yi yana da Company, nan Faruk yake mishi gadi. Ya mayar dashi can ne sabida ya riƙa taimaka mishi a can tunda ya yaba da hankalin sa, ga kuma tausayi da yake ba shi domin ya san komi cikin rayuwar sa tunda ya taɓa tambayar shi, shiyasa ya yanke shawaran kai shi can Riyadh ya kula masa da dukiyar sa sannan kuma ya saka shi makaranta, tunda yayi alƙawarin sai ƴan uwan sa sun yi alfahari dashi, sai sun dawo suna dana-sanin koran sa da suka yi.


      Wannan ne mafarin da yasa Faruk ya dawo Riyadh da zama har yayi karatu ya sami aikin yi, inda lokaci ɗaya Allah ya buɗa mishi yayi kudin kanshi, a lokacin har ya auri ɗiyar uban gidan nasa tunda soyayya me ƙarfi ta shiga tsakanin su, sai dai Allah be taɓa basu haihuwa ba shekara da shekaru

    Shekara goma suna zaune da Abiha kafin Allah ya ɗauki ranta, inda ta rasu har lokacin bata taɓa ko da ɓarin wata bane, shi kuma Faruk yaƙi yin aure domin kawai farin cikin ta, yana ganin be kyauta ba muddin yayi mata kishiya saboda gudummawar da mahaifin ta ya ba shi a rayuwa, domin a lokacin ma Mahaifin nata tuni ya daɗe da rasuwa sai mahaifiyar ta, ita kuma ta koma can dangin ta har ta sake aure.


        Mutuwar Abiha ya taɓa Faruk sosai, inda ya jima be sake aure ba, a lokacin ne ya yanke shawaran zuwa Nigeria neman ƴan uwan sa tunda ya rasa kowa nasa a nan, zuwan sa ya tarar da su ma su Yaya Ali sun sami ci gaba sosai, tunda duk kansu suna aiki da albashi me tsoka, inda suka rushe gidan su suka yi na zamani ko wanne da nashi part ɗin tare da matan su da yaran su

Abubuwa da dama sun sauya mishi domin an yi rashi kala-kala, inda Jamma tuni ta daɗe da rasuwa itama, sai kuma wasu daga cikin dangin Maman shi na kusa.


    Su Yaya Ali sun yi matuƙar mamakin ganin Faruk ya sauya yayi kuɗi sosai, domin ko hausan ma tuni ya ɓace a bakin sa sai ɗaiɗai. Sai hassada ya cika zuciyar su ganin ya fi su

Sai dai shi be duba wannan ba illa alkhairin da yake ta musu. Duk yabi ya zagaye dangi ya gaishe su. Inda da ya tashi tafiya sai su Yaya Ali suka ce basu san zancen ba, wai, "a dole sai ya dawo Nigeria ya zauna da su".

Shi kuma yace musu, "bazai iya ba tunda ya baro dukiyan sa da komi nashi a can," domin a lokacin har Company biyu ne dashi a can. Haka suna ji suna gani ya tafi ya bar su domin a tunanin su za su iya juya shi, sai dai yayi musu alƙawarin zai riƙa dawowa yana ganin su.


     Allah da ikon sa a faɗi tashin nan da yake yi na ziryan zuwa Nigeria duba ƴan uwan sa sai suka ci karo da mahaifiyar MEEMA, sunan ta Zulaiha ƴar Kaduna ce. Inda lokaci ɗaya soyayyar ta ta shiga Abee kuma be yi ƙasa a gwiwa ba ya sanar mata, duk da a lokacin yana da shekaru sosai ba kamar ita yarinya jagal ba, amma kuma kasancewar sa me kuɗi yana samun jin daɗi sai girman nasa ya ɓoye, tamkar yaro ɗan shekara 35.

    Babu abinda ya ƙara faranta mishi rai jin sunan ta Zulaiha sunan mahaifiyar shi, shiyasa ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata, inda suka yi soyayya na ɗan ƙanƙanin lokaci domin shi yace, "ba wasa ne ya kawo shi ba, Auren yake so da sauri".

     An so ayi fitina sanda ya kai labarin wajen ƴan uwan sa, domin su a lokacin har sun yanke shawaran za su zaɓa mishi mata, sam suka ce, "basu yarda ya auri Zulaiha ba".

Amma shi kuma yace, "atabam ita yake so".

Dole ba don sun so ba suka bar shi ya aure ta.


    An yi auren lafiya an gama lafiya inda ya ajiye ta a gidan sa na can Riyadh, kamar jira ake yi tana shiga ta samu cikin MEEMA, zo ku ga murna wajen Faruk, tun a ciki ya ɗauki son duniya ya ɗaurawa ɗiyar sa.


           Bayan wasu watanni aka haifi MEEMA kyakykyawa ƙin kowa ƙin wanda ya rasa, sak mahaifin ta bafulanan usuli don basu da maraba, inda ya mayar mata da sunan mahaifiyar sa Zulaiha, sannan kuma sunan Ummeen ta itama. Shiyasa suke kiran ta da MEEMA tun tasowar ta, kuma da haka take amfani dashi a school wato *MEEMA FAROUK.*

        Ta taso cikin gata sosai fiye da tunanin mutum, bata san babu ba ko hantara har sai sanda ta soma girma ta fara gane ƴan uwan Abee ɗin ta dake zuwa gidan sun takurawa iyayen ta, har ita kanta basu bari ba domin sun dinga dungure mata kai kenan, kuma duk idan sun zo sai sun saka iyayen ta kuka saboda baƙaƙen maganganun su, shiyasa tuni Abee ya dena zuwa Nigeria gaba ɗaya

Inda akwai wani lokacin da suka yi faɗa baram-baram yace, "kar su sake zuwa mishi gida". Wannan dalilin ne yasa suka dena zuwa gaba ɗaya, sai dai idan suna neman kuɗi me yawa a wurin sa sai su zo dole sai ya basu. Idan ba kuɗi ba kuwa babu abinda ke kawo su. Da haka suka sami salama.


     Duk da iyayen MEEMA ƴan Nigeria ne amma bata taɓa koyan Hausa ba, ba wai don sun ƙi koya mata bane, a'a sai dai don ba ya birge ta Yaren, bata damu ko kaɗan ta koya ba, kuma su ma basu cika yi ba tunda shi Abee har hausan ma ya ɓace a bakin sa sai kaɗan, idan kuma yana yi tamkar yana yare, ba kowa ke iya ganewa ba. Iyakan Turanci da Larabci suke yi.


     Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin su.





                     ✳️✳️✳️✳️✳️

        Shigowar Nurse Zara ne ya sanya Abee ya buɗe idanun sa da suka kaɗa suka yi jazur

Da sauri ta ƙarisa wajen sa tana mishi sannu

Be iya amsa wa ba sai da ya ja lokaci kafin a hankali yace da ita cikin larabci, "ko zata iya ɗaukar MEEMA ta kaita ɗaki ba tare da ta tashi ba?"

Dariya ma maganar taso bata, taya zata iya ɗaukar ganɗamemiyar budurwan da ta girme ta ta kai ta ɗaki kuma ba tare da ta tashi ba? Duk da dai ta fi ta jiki amma dai ta san MEEMA ta girme ta. Sai tayi saurin girgiza mishi kai itama ta mayar masa cikin harshen larabcin, "baza ta iya ba".

Sai yace mata, "ta tafi".

Haka ta fice tana rufo musu ɗakin.



       Dole ya bar MEEMA a kan jikin sa taci gaba da barcin ta yana faman kallon kyakykyawar fuskar ta wanda ya kasance irin nasa sak. Murmushi ne tare da hawaye ya saki lokaci ɗaya. Babu abinda yake ƙauna sama da MEEMA a duniyar nan, ba don haka ba da tuni ya roƙi Allah ya ɗauki ransa saboda ƙuncin da ke cikin ransa, amma kuma tunawa da ita a rayuwar sa yana saka shi jin sanyi a ransa, wanda yake fatan samun lafiya nan gaba domin yaci gaba da rayuwa da ita a duniyar sa. Duk da ya san dole wata rana zata yi aure ta bar shi, kuma har a zuciyar sa yana son ganin kafin ya mutu ya danƙa ta wajen wanda zai zame mata jigo a rayuwar ta, ma'ana mijin ta, ba ya fata ya mutu ya bar ta hannun ƴan uwan sa, tun yanzu ma sun zo amsar ta wanda ya san duk saboda kuɗin sa ne, suna ga kamar zai mutu a yanzu shiyasa za su ɗauke ta don su mallaki komi nata. Ba ya fatan hakan ya faru dole ne yayi wani abu a kai, amma taya? Ta ina zai faro wajen samar mata abokin Rayuwa? Ta ina zai saka ta ta yarda tayi aure bayan tace, "muddin yana numfashi a duniya to babu ita babu aure a rayuwar ta! Baza ta taɓa tafiya ta bar shi ba har sai idan ya samu lafiya ne". A koda yaushe wannan kalaman nata take yawan sanar masa. Be san ta ina zai fara shawo kanta ta amince da ƙudirin sa ba.


        Lumshe idanun sa kawai yayi yana haɗiyar wani yawu me ɗaci.
[08/10, 2:53 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                   💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*




               *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._




*SAKAMAKON SALLAH 1*
          _Mun sani cewa a shika-shikan musulunci ɗin nan guda biyar bayan imani sai tsayar da sallah. Abdullahi Ibnu Mas'ud ya ce, "Na taɓa tambayar Manzon Allah cewa wane aiki na ɗan Adam Allah ya fi so?" Sai Annabi ya ce, "sallah". Na sake cewa, "daga ita fa?" Sai Annabi ya ce, "kyautata wa iyaye". Na sake cewa, "daga wannan fa?" Sai ya ce, "sai jihadi."_
       _Manzon Allah ya taɓa ce ma Abu Zarrin, "in Mutum yayi Sallah domin neman yardar Allah, duk zunuban sa za su zube Kamar yadda ganye yake zubewa daga itace," Abin lura a nan shi ne sallah tana kawar da ƙananan zunubai. Manyan kam sai an tuba. Amma in Allah ya ga dama yana iya yafe sagiran da kaba'iran don sallar da mutum yayi. Amma kuma, ko can ba ayi ma musulmin ƙwarai kallon zai riƙa kuntuka kaba'ir, manyan laifuka. Ban da ma haka duk mai Sallah yakan yi istigfari ne, a ƙarshe ya roƙi Ubangiji ya gafarta masa zunuban sa, manya da ƙanana._
          _Abu Sa'id Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce, "ya taɓa jin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na cewa: "ko wace ɗaya daga cikin sallolin nan biyar tana kankare zunuban da suke tsakanin ta da wadda ta gabace ta." Bari mu kawo misali da wani wanda aikin sa yake sa yayi butu-butu da ƙura. Akwai ƙoramu guda biyar suna gudana tsakanin gidan sa da inda yake aikin. In ya tashi zuwa gidan yakan yi wanka a kowace ƙorama. To, haka fa sakamakon yin sallolin nan biyar yake. Ana yafe duk wasu kurakurai da zunubai da suke tsakanin salloli biyu saboda istigfari da tuba da ake a kowace sallah._
        _Manzon Allah yakan riƙa kawo mana ire-iren misalan nan ne don ya nuna mana irin ƙarfin da sallah take da shi wajen kawar da zunubai. Idan mun yi watsi da jin tausayi na Ubangiji, ba za mu kuka da kowa ba sai kan mu._
        _Ba shakka ɗan Adam mai yin kurakurai ne. Muna iya yin ayyuka da dama wa'danda za su saɓa ma Ubangiji, mu kuma gamu da hushin sa da horon sa. Amma kuma mu duba irin jin ƙan da Ubangijin mu yake mamaye mu da shi. Ya nuna mana yadda za mu sadu da rahmar sa da jin ƙan sa. Abin takaici ne ƙwarai a ce mun bari wannan baiwa ta wuce mu, bamu kama ta mun riƙe da hannu bibbiyu ba. Rahmar Allah kusa take ƙwarai ga mai Sallah. Sallah falala ce daga Allah ya zo, ya gusar da abin da yake damun zuciya. Haka aka san Manzon Allah da Sahabban sa suke yi._
_Ɗan Adam yana yin Sallah tun safe har ya zuwa sallar isha'i da fatar dacewa da rahmar Allah. Bayan isha'in mutane sun kasu gida uku. Akwai waɗanda suke su gare su daren hanya ce ta samun lada da tubarraki. Waɗannan su ne masu raba dare suna bautar Allah, lokacin da wasu suke ta shara Barci. Su kam lada suke samu daga Ubangijin su. To, sai kuma mutanen da suke mayar da daren wani kaya mai nauyi da masifa gare su saboda yin ka-ce-na-ce cikin miyagun ayyuka da talatainin dare. Ba abin da daren yake kawo musu sai baƙin ciki. Sai kuma kashi na uku wanda ya ƙunshi masu hayewa gado kawai bayan sun gama isha'i. Su kam ba yabo ba fallasa. Irin su sun kauce wa hadisin Manzon Allah da yake cewa, "ku dimanci yin Sallah a gidajen ku ko baiwar Allah da rahmar Allah su iso gare ku." Allah yasa mu dace duniya lahira._














                    *NO_

Please Login or Register in order to submit comment