Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikin gidan ce. Tunda ta ɗaura ido a kan MEEMAN ta tsaya kallon ta, sai da ta gama ƙare mata kallon kafin tace, "baiwar Allah daga ina?"

Ita MEEMA yanda bakin ta yayi mata nauyi shiyasa ta kasa yin magana illa zuba mata idon itama da tayi tana bin ta da kallo. Koda tayi mata maganar bata fahimci abun da tace ba amma hakan yasa ta buɗe baki a hankali tace, "May I come in?"

Jin tayi turanci kuma bata gane ba kasancewar yanda take furta words ɗin sai Matar ta sake cewa, "to Ni gaskiya ba na jin ki ina zuwa". Sai ta juya ciki tana ce ma Hajiya dake zaune a kan wheelchair ɗin ta, "wata budurwa ce ta zo Hajiya, amma gaskiya ba na jin yaren nata, turanci ne ko wani yaren ne oho don maganar nata wani iri wlh, Idan kika ganta kamar ba ƴar nan bace, sanye da kayan Larabawa ta zo".

Hajiya dariya tayi da cewa, "Kai Zabba'u kin cika Zabbo ta, wlh kin ci sunan ki. Idan ban dake memakon ki zauna kina min kwatancen ta ai gwara ki ce mata ta shigo kin bar ta a waje kuma".

"To kuma fa haka ne Hajiya, to amma kin san yanda duniya babu gaskiya shiyasa gwara in soma sanar muku don wlh ban yarda da ita ba Ni daga kallon ta, sak bata yi kama da ƴar nan ba, yaren nata ma fa ban fahimci me tace ba don ba turanci bane ai da zan gane ko ya ya ne tunda ina jin kaɗan-kaɗan."

"Ki dai zauna kiyi ta rattaba zance da Allah kin bar baiwar Allah a waje". Hajiya tafaɗa tana jan guntun tsaki

Hakan yasa Zabba'un ta wuce da sauri bayan ta ce, "to kiyi haƙuri Hajiya kar ranki ya ɓaci, bari in CE ta shigo to". Tana zuwa bakin ƙofan tace da MEEMA, "shigo baiwar Allah".

MEEMA da bata fahimci me tace ba ko motsi bata yi ba sai kallon ta da take yi

Sai Zabba'un ta sake maimaita mata da gwarancin turancin ta tana sanar mata, "ta shigo ciki".

A hankali ta taka ta shiga ciki idanun ta suna faɗa wa kan Hajiya wanda itama ta kafe ƙofar da kallo

Da sauri ta furta, "Zulaiha ke ce?"

Har gaban ta ta tako ta tsaya ba tare da ta furta komi ba illa son hana fitowar hawayen ta da suke maƙale a kwarmin idanun ta

"Ya ki Jika ta, taho.. taho wuri na". Hajiya ta furta cike da rawan baki tsaban murnar ganin MEEMAN

Yanda take ya fico ta da hannun ta ne yasa ta isa gare ta a hankali tana duƙa wa a gaban ta

Hannayen ta ta kama cike da farin ciki kamar zata yi kuka tace, "Will I ever see you again? How did you get here? Who brought you? Where is your father?"

Bata iya amsa mata ko kalma ɗaya ba duk da a ranta ta ɗan ji sanyi da yanayin karɓar da tayi mata, sannan kuma farin cikin da ta ga ya bayyana a fuskar ta yasa ta gane tana murna da zuwan ta. Shiyasa ta matsa sosai ta rungume ta hawayen idanun ta suna sauka kamar an kunna su

Sosai itama Hajiyan ta sake ƙanƙame ta a lokacin tana kuka da sambatu

Ita dai Zabba'u baki ta kama kawai tana kallon su. A lokaci ɗaya kuma sai ƙwaƙwalwan ta ta bata ƙila yarinyan Ummee ce, domin ta san da cewar tana da ɗiya kasancewar wani lokacin tana yawan jin suna ambatar ta, sai dai a zahiri bata taɓa ganin ta koda a hoto ne duk da ta daɗe a gidan tun kafin Ummee ta dawo Nigeria, shiyasa tayi tunanin ita ce ɗiyar Ummee duk da ba wai kama suke yi ba, amma Idan ka kalle ta tabbas zaka gane jinin ta ne.

Sun jima a haka kafin Hajiyan ta sake ɗago ta tana me riƙe mata hannu da cewa, "Zulaiha, will we see you again? Your mother do not came to check on you, and I was sick and had legs, and your uncle was not in the country to go and check on you and your father, I hope he feels better?"

Fashe wa tayi da kuka tana girgiza mata kai tace, "My father is dead. He is dead.. He is dead." Yanda kukan ya ci ƙarfin ta ta kasa ƙarisa zancen nata dole tayi shiru tana sake rungume ta a wannan lokacin tana kuka sosai

Salati kawai Hajiya take yi tana bubbuga bayan ta. Sun jima a haka kafin ta ɗago ta taci gaba da rarrashin ta, sannan ta kalli Zabba'u da har yanzu tana wurin tana ta kallon su, tace da ita, "ki kawo mata ruwa ta sha sannan ki kira min Zulaiha a ɗaki".

"To Hajiya". Ta amsa ta tana wuce wa wurin Fridge ɗin da sauri

Ita kuma Hajiya hannu ta sanya tana share mata hawayen fuskar ta tana ci gaba da rarrashin ta, sannan ta ɗago ta ta zaunar da ita kan sofa dake jingine da wheelchair ɗin ta. Da Zabba'u ta kawo ruwan ita da kanta ta amsa ta bata ta sha tana sake shafa mata fuska cike da rarrashi

Zabba'u da ta wuce kiran Ummee bata kai ga hawa benen ba ita Ummeen ta fito daga saman zata sauko, kyawu da zubi da tsari gami da haɗuwa da tsaban iya kwalliya shi zaka soma gani a tattare da ita, a kallon farko baza ka taɓa ce mata ta haura shekaru arba'in ba, but tsaban kyawun jikin ta da ɗaukan wanka irin nata sai kayi tunanin ƴar shakara talatin ne, sam bata da jikin manyanta. Tana sanye da lesi me uban tsada da tsantsan kyawu, gaba ɗaya hannayen ta da wuyan ta duk ta zuba sarƙa da awarwaron Gwal sai walwali suke yi, fuskar nan nata ya ɗau Powder duk da ba kwalliya ne a fuskar ba, yanda take tafiya zaka tabbatar da babban mace ce me aji sosai. Tun daga saman benen idanun ta suka sauka a kan MEEMA, sai dai bata gasgata itan bace kasancewar ba ta ganin fuskar ta sosai. Hakan yasa ta ɗan ƙara sauri wajen sauko wa tana son ƙaryata idanun ta. Sai dai bata gama ƙarisowa ba suka haɗa ido da MEEMAN wanda a lokaci ɗaya ta tsaya cak daga inda take tsaye.
[10/10, 3:46 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* 🧝🏻‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



               *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._


















                             *NO_19*

             Wasu sabbin hawaye ne suka wanke mata fuska saboda arba da tayi da fuskar mahaifiyar ta a yau, kimanin shekaru biyar da watanni kenan rabon da ta sake tozali da ita. yanda idanuwan ta suke mata zafi ne yasa ta mayar da idanun nata ta rufe ruf tana sauke numfashi daƙyar

While itama Ummee tuni hawayen ne suka cika mata idanu, sai dai ta kasa samun ƙwarin gwiwan da zata iya tunkaran MEEMAN a halin yanzu, gaba ɗaya ta kasa motsa wa a inda take

Inda Hajiya tace da ita, "ki ƙariso mana kin tsaya a wurin, ko zuwan nata ma baki yi murna da shi bane?"

Girgiza kanta ta soma yi still hawaye na zuba a face ɗin ta, sai a lokacin ta samu damar taka wa ta iso gaban MEEMAN zata sanya hannu ta taɓa ta tare da furta, "My daughter..."

Saurin janye jikin ta tayi tana tashi da sauri, ido cikin ido take kallon ta cike da wani irin yanayi da fushi a tattare da ita tace, "Don't touch me again! I am not your daughter because I will never be your daughter." Sai ta juya ga Hajiya cike da rawan murya a wannan lokacin tace, "She is not my mother. If she touches me again I will leave this house. I will enter the world wherever I am and, I will not stay here."

Gaba ɗayan su shiru suka yi suna sauraron kukan ta da a yanzu take yi da ƙarfi wanda ke fita da ɓacin rai da tuƙuƙin baƙin cikin da ya kasance da ita tsawon shekaru

Hajiya ce tayi ƙarfin halin kiran sunan Zabba'u tana bata umarnin, "ta kai MEEMAN ɗakin kusa da nata".

Hakan yasa ta iso da sauri ta ja Trolley ɗin bayan ta ɗauki ƙaramin

Hajiya ta yiwa MEEMAN bayanin, "she follow her."

Bata ce komi ba ta bi bayan Zabba'un har ɗakin da zata kaita, a downstairs ne ɗakin bayan ka wuce dogon corridor zaka hangi ɗakuna guda biyar a jere, ɗaya daga ciki ta shigar da MEEMAN. Dayake ɗakin babu datti tunda a koda yaushe ana gyara wa, tana ajiye mata jakan ta ta fito ta bar ta.





                    ********

             "To kin gani abun da nake gudan miki kenan tuntuni Zulaiha, son zuciya da ruɗin ƙawaye yasa kin aikata mummunan aikin da zai ja miki dana-sani a rayuwa, yanzu ke baki ji kunya ba da kiran ta da kika yi a matsayin ɗiyar ki? Kin san kina son ta meyasa kika yanke wannan hukuncin? Dama na sha sanar miki akwai ranan da zaki yi nadama, tunda kika tafi kika bar su baki sake waiwayan su ba, sannan ni ba ƙafa ba bare in je in ga lafiyan su, wanda kuma zai je ɗin yanzu kusan shekaru shida kenan basu dawo ba, bamu da tabbacin yana raye a halin yanzu ko ba ya raye, wata huɗu kenan da wayan Hashim ba ta shiga, ba don haka ba da shi ne zai riƙa zuwa yana duba mana a halin da suke ciki. Ni na tabbata Faruk ya tafi da baƙin cikin ki a zuciya domin kin cutar da shi sosai, ya koma ga Allah ya bar ki a duniyar da kike ganin ya fi miki shi, mutum me ƙaunar ki amma kika kasa zama ki tallafi rayuwar sa da ɗiyar sa, wannan wani irin zuciya ce da ke Zulaiha? Anya kina da ɓurɓushin imani?"

"Wlh Hajiya nayi matuƙar nadaman abin da na aikata, na san zuciya ta bata yi min adalci ba da har na yanke hukuncin barin su, amma wlh ina matuƙar nadama da abun da nayi musamman ma a yau..." Kukan da ya ci ƙarfin ta yasa a dole tayi shiru

Hajiya tace, "hmm kaɗan ma kika gani, yanzu ga shi kin koya wa ɗiyar ki tsanar ki a zuciya, ba na tunanin a yanzu kina da wani sauran mutunci a idanun ta, wacce ta tafi ta bar ƴar ta tsawon lokaci babu waiwaya ai ba na tunanin akwai wani sauran soyayya, gwara ma ki tashi min a nan tun kafin raina ya ɓaci, kuma ban amince ki takura mata ba domin muddin ta bar gidan nan a sanadin ki wlh sai nayi mummunan saɓa miki Zulaiha". Daga haka Hajiyan ta kwaɗa wa Zabba'u kira. Tana zuwa tace mata, "ta mayar da ita ɗaki."

Haka ta ja ta suka wuce ɗakin Hajiyar suka bar Ummee a wurin tana ta faman share hawaye. Zuciyar ta sosai take mata tuƙuƙi da baƙin ciki sabida fama abun da ke cikin ta. Ta jima a wurin ta rasa me ke mata daɗi, daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakin da aka sauke MEEMAN

Tunda ta shiga ɗakin MEEMA ta sauke ido a kanta sai tayi saurin kawar da su tana sake haɗe rai sosai

Ita kuma a hankali ta taka izuwa bakin gadon da take zaune, kasa zama tayi illa tsaya wa da tayi tana kallon ta yayinda idanuwan ta har yanzu suna da danshin hawaye. A hankali ta soma magana a cikin harshen turanci. "I know I was wrong with you and your father, and I do not know how to apologize to you. I was a mother who loved herself more than anyone else. I followed the deceptions and advice of my friends. I made a big mistake that I now know..." sai tayi shiru sabida kukan da ya taho mata sosai a yanzu ɗin. Daƙyar ta iya buɗe baki da zummar taci gaba

Sai MEEMAN ta dakatar da ita wajen ɗaga mata hannu da cewa, "enough..! I do not want to hear your words in my ears, you are a tyrant in my place, you do not love me and you do not love my Abee, if you had faith you would never do that to us, how can I call you mother? Do you think that is appropriate? Tell me, do you think that is appropriate?" Ta ƙare zancen da wani irin ihu tana kuka sosai. Sai kuma ta haɗe hannayen ta wuri ɗaya tana haɗa su da fuskar ta tace, "please leave this place before my heart beats, I do not love you and I don't want to see you around me!"

"Daughter..."

"Please out". Tafaɗa cikin tsawa yayinda take kallon ta a wannan lokacin ido cikin ido hawaye na zuban mata

Shiru Ummeen tayi ta kasa motsa wa, sai kuma a hankali ta juya ta fice har tana sake waigo ta

Ita kuwa tuni ta kifa kanta a saman gadon ta soma rusa kuka sosai, ji take yi kamar ta haɗiye zuciya ta mutu tsaban baƙin ciki, why Ummee zata yi mata haka? Anya ita uwa ce a gare ta da har ta zaɓi rabuwa da su? Ba ta tunanin akwai wata uwa makamanciyar nata uwar, shin wani hujja ne da take da shi da har zata tsallake tabar su alhalin suna matuƙar buƙatar ta? Tana ga rashin lafiyan Abee ɗin ta ba hujja bace da zata aikata musu haka, abun da take gani kawai Ummeen ta bata da imani, rashin imanin ta ne yasa ta aikata musu wannan abun, to, don me itama zata ɗauke ta a matsayin uwa? No hakan bazai taɓa yiwuwa ba domin tun sanda ta tsallake ta bar su itama ta cire ta daga zuciyar ta, a yanzu ita ba mahaifiyar ta bace, bata da kowa a yanzu sai ita kaɗai, a ko yaushe kuma hakan zata riƙa ɗauka... ta jima a nan zaune tana ta sharɓan kuka wanda har kanta ya soma mata zugin ciwo kafin ta shafa wa kanta lafiya ta haƙura, kiran sallan da ta ji ana yi shi ya ankarar da ita bata yi sallolin dake kanta ba, don haka ta tashi ta shiga Toilet ta ɗauro alwala ta ciri hijabin ta ta soma rama sallolin ta

Tana cikin yi ne Zabba'u ta shigo ɗakin, ganin tana sallah sai ta juya, babu jima wa kuma sai ta dawo da ƙaton faranti a hannun ta ta ajiye mata ta fice

Ita kuma ta jima tana sallan, sai da ta haɗa da shafa'i da wutri sannan ta sallame sallan, ta zauna yin addu'o'i na tsawon lokaci kafin ta shafa, yunwan dake addabar ta shi ya sanya ta jawo farantin ta zuba abincin dake cikin coolar a cikin ƙaramin Plate, haka tayi ta tusa abincin a baki ba don yana mata daɗi ba, duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana cin abincin ko rabin Plate ɗin bata yi ba ta ture ta tashi tsaye. Wanka ta shiga tayi kafin ta sanya kayan barcin ta tabi lafiyar gado. A lokacin wajen ƙarfe 11:30pm. Na dare ne, sosai tunani suka bijiro mata a zuciya wadda yasa ta kasa barcin sai daƙyar ya sure ta daga baya. Tunda ta tashi da asuba tayi sallah ta sake komawa kasancewar akwai barcin sosai a idanun ta, bata farka ba har sai sha biyu saura domin Hajiya ta hana a taso ta har sai idan ita ce ta tashi, ta san tabbas akwai gajiya a tattare da ita. Koda ta tashi sai da tayi wanka ta shirya a cikin riga da skert na wani jan yadi me flowers da aka yi da kalan maroon color. Rigan tana da igiya ta baya wanda ta ɗaure shi, sai kuma gaban rigan a buɗe yake sai dai an saka raga-raga kalan maroon, shi kuma skert ɗin ya buɗe sosai tun daga saman ƙugun ta har ƙasa, sun mata cif sun fito mata da kyakykyawar surar jikin ta da Allah ya bata, while ta tufke gashin ta a ƙeya ta sanya ɗan kwalin kayan tayi Rolling da shi wanda ya saukar mata iya kafaɗun ta, exactly ta fito a tsantsan Balarabiyar ta. Koda ta gama shirya wa bata fita ba sai tayi zaman ta a kan gado, wayan ta dake kashe tun daren jiya ta ɗauka ta kunna, da saƙonni ta soma cin karo wanda ta fahimci Sajjad ne ya turo mata, domin kasancewar shi ya bata Simcard ɗin that's why ya mallaki Numban, a ko yaushe yana kiran ta but tunda ta san shi ne bata sake ɗauka ba, yanzu ɗin ma bata duba ko ɗaya ba illa zare layin da tayi ta karya shi biyu ta jefar. Miƙe wa tayi ta bar wayan a wurin ta zira room slippers ɗin ta da ta ciro su daga Trolley ɗinta ta fita. Ta cikin corridorn da ta san an biyo da ita ta nan ta fita sai ga ta a tsararren parlour'n gidan

A lokacin Hajiya na zaune a Kan wheel chair ɗin ta tana karanta littafin Hisnul Muslim sanye da eyeglasses. Ganin ta yasa ta tsayar da karatun nata tana me yalwata fuskarta da murmushi tare da yiwa MEEMAN alamu da hannun ta alamun ta ƙariso gare ta

A hankali ta taka izuwa wurin ta yayinda ta ɗan saki fuskarta kaɗan. Hannun Hajiyan da ta miƙa mata ta kama tare da ɗan ranƙwafa wa kaɗan ta sumbaci hannun cikin sassanyan muryan ta da a yanzu be fita ko kaɗan ta gaishe ta

Sai da ta riƙo mata kafaɗun ta ta zaunar da ita a saman kujera kafin ta amsa ta cikin tsantsan fara'an da dole zaka gane tana a cikin farin ciki sosai, kana ta tambaye ta yanda ta kwana?

A taƙaice ta bata amsa tana kallon ta

Murya Hajiyan ta ɗaga ta kirayi Zabba'u

Babu jima wa kuwa sai ga ta ta bayyana a gaban Hajiyan, cikin washe baki ta kalli MEEMAN tace, "Barka da safiya ƴar nan".

Kasancewar da hausa tayi bata amsa ta ba

Sai Hajiya tace, "ki riƙa mata magana da turanci ne saboda ba ta jin Hausa. Tukunna ki je ki haɗo mata Breakfast ɗin ta ki kawo mata nan sai ku gaisa daga baya".

"To Hajiya". Ta amsa cikin sauri tana juya wa

Ita kuma Hajiya ta kalli MEEMAN tace, "Now she'll bring you your Breakfast. Hope you stay home?"

Guntun murmushi ta saki tana jinjina mata kai

"Calm down, ok? Whatever you are want ask me directly, insha'Allah you will never touch Zulaiha. I am always with you."

Still kanta ta sake ɗaga mata a lokacin idanun ta suna me ciko wa da hawaye

Murmushi Hajiyan tayi mata, kana kuma ta mayar da kallon ta kan Zabba'u da ta kawo Breakfast ɗin a saman faranti. Still she keeps her eyes on MEEMA asking her, "what she wants?"

"Tea alone is enough". Tafaɗa a hankali cikin muryan ta da har yanzu be washe ba sakamakon kukan da ta sha jiya

Saka Zabba'u tayi ta haɗa mata tea ɗin. Bayan ta gama ta amsa da kanta ta miƙa mata

Ita kuma Zabba'un zama tayi kana ta kalli MEEMAN da har ta soma kai Cup tea ɗin bakin ta, cikin turancin ta na ƴan koyo tace, "Good morning and hope you are fine? Hope you enjoyed the stay?"

Kasancewar har yanzu Cup ɗin na bakin ta, kallon Zabba'un kawai take yi tare da gyaɗa mata kai kawai ta ci gaba da shan tea ɗin

Sai ita Zabba'un ta kalli Hajiya tana muskuta zaman ta tace, "Hajiya wai yanzu ita ɗin dai yarinyan Hajiya Zulaiha ce kenan?"

"Ƙwarai kuwa. Baki ga sun yi kama bane?"

"Eh na gani wlh, ai ban yi tunanin ta kai girman haka ba, Masha Allah gaskiya tana da kyau matuƙa tamkar dai ƴar can ƙasan wlh". Ta ƙare maganar tana washe baki

Ita dai Hajiya bata ce komi ba illa ɗaukan Hisnul Muslim ɗin dake jikin ta taci gaba da karanta wa

"Hajiya nace ba. Amma tana da aure ko?"

Ɗago wa Hajiyan tayi tana kallon ta da cewa, "ke dai Zabba'u kina da son tsegumi wlh, idan tana da aure ai zaki sani tunda tare muke da ke tsawon shekaru a gidan nan, a baya nasha sanar miki labarin su tun Zulaiha na can, sannan kuma koda ta dawo baki taɓa jin mun ce miki tayi aure ba".

"Haka ne Hajiya. To kiyi haƙuri".

"Idan ban yi haƙuri da ke ba ya zan yi ne Zabba'u? ki tashi dai yanzu ki je ki ɗaura mana sanwan abinci kina gani rana tayi amma kin zauna tsegumi".

Tana washe baki tace, "Hajiya ai na ɗaura miyan har ya kusa soyuwa zan sauke, dama farar shinkafar kaɗai ya rage in girka".

Bata ce mata komi ba ta juya ga kallon MEEMA da har yanzu tana kafe da Cup tea ɗin a bakin ta. Tace da ita, "What do you want to eat?"

Sai a lokacin ta cire Cup ɗin a lokacin ta shanye tass duk da kuwa zafin shi, domin ita ta fi son ta ji tea da zafi-zafin sa, kuma ta shanye sa a hakan ya fi mata a ko yaushe. Ce mata tayi, "She doesn't need anything, that's enough."

"No, Zulaiha, tell me something to be cook for you, because you will not sit still and eat nothing but tea."

She Said, "I will eat whatever is prepared."

"To maza tashi ki girka ki kawo mata". Inji Hajiyar tana kallon Zabba'un

"An gama Hajiya." Ita kuma tafaɗa tana tashi ta wuce

Hajia Looking her said, "I am still not tired of being sorry with you for not coming to see you. Please be patient. Your uncle is not in the country that's why he did not come to you, but forgive us."

Hannu MEEMAN ta sanya ta riƙo nata, fuskar ta a sake sosai a yanzu ɗin tace, "Don't worry my grandmother because you are not criminal. Ummee is a criminal and I am the only one who is angry with her. "

Hajiya tace, "But do not be angry with her because she is your mother, bind yourself to hide what you feel about her in your heart, don't forget she's a mother to you, no matter what she does to you, you should not hate her."

Girgiza kanta MEEMA ta soma yi hawayen idanun ta da suka taru suka soma zubo wa, cikin amon muryan ta me kama da ɓacin rai tace, "No, I will never forgive her for taking me not her daughter, I will never see her as my mother, I have long removed her as my mother. Please grandma I don't like talking about her".

"Well. Since you said I will never speak to you again." Ta ƙare maganar da shafa mata kai tana mata murmushi.




                 Lokacin ne Ummee ta sauko daga sama a cikin shigan ta kamar yanda ta saba, yau ma tayi kwalliya da baƙin less me kyan gaske, duk ta saka sarƙa da awarwaro a hannayen ta, duk da a yanzu ɗin damuwa ce cinkushe a fuskar ta, ga shi idanuwan ta sun yi ja sun kumbura sosai. Koda ta iso gaishe da Hajiya tayi tana samun wuri ta zauna a kan sofan da ke kallon wanda MEEMA ke zaune

Hajiya amsa mata tayi tana kallon ta da cewa, "wai yau baza ki je aiki bane sai yanzu kika fito?"

"Eh Hajiya yau bazan iya fita ba".

"To me ya sami idanun ki suka yi ja haka? Kar dai ace tunanin MEEMA kike yi?"

MEEMA da kanta ke sunkuye tun zuwan Ummeen sai ta ɗago kai ta kalli Hajiyan jin ta kira sunan ta, duk da bata fahimci me suke cewa ba ta gane da ita ake yi

Ita kuma Hajiya murmushi tayi mata tana dafa hannun ta, sai kuma ta mayar da kallon ta ga Ummee da ta ƙura wa MEEMAN ido, tace da ita, "tun wuri ki dena saka wa kanki damuwa tunda komi da ke faruwa ke kika jawa kanki, son zuciyar ki yasa kika aikata hakan, kin baro Ƴar ki da mijin ki kin taho nan, to, meye na saka wa rai damuwa?

Please Login or Register in order to submit comment