Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

her body is fine."

Murguɗa masa baki Laɗifan tayi da cewa, "baza ta tashi ba, a nan zata zauna, kai ka tafi kai kaɗai."

"Kina ji ko Umma? Yarinyar nan naki ta raina Ni wlh zan fasa mata baki."

Umma tace, "ai kun fi kusa wlh babu ruwana."

Hakan yasa Laɗifa tayi masa gwalo

Yayi ƙwafa shi kuma yana kaɗa mata yatsa alamun, "zai riƙe ta."

Da haka dai suka zauna suna ta shirmen su, duk da Laɗifa ba ta jin daɗin jikin ta sai da ta biye mishi don Idris akwai wasa, ko ba ka so idan ya saka ka a gaba sai ka biye mishi

Daga baya ya tashi yace, "za su tafi." Suka yi musu sallama suka fice. Kai tsaye wajen aiki suka koma.




✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

Zuwan Uncle Hashim da ya tarar da yanda suke ta cin ma Hajiya mutunci ai sai ya hau su da faɗa. Dama ga shi akwai fushi nan da nan ya zuciya yace Jalila, "ta ɗauko mishi bindigan shi duk sai ya harbe su."

Yanda suka ga Uncle Hashim ɗin yake yi ne tamkar be da Kai, sun san tsab zai iya harbe su kamar yanda yace, hakan yasa suka ɗibi jiki suka fice daga waje suna ta zage-zage a kan, "sai an basu gadon su." Daƙyar suka bar gidan

Hajiya tace, "ku ne matsiyata, gado ne za'a raba a kawo muku naku har inda kuke, MEEMA kuma babu inda zata koma a nan zata zauna." Nan ta saka Uncle Hashim ɗin da zancen, "idan MEEMA ta dawo yayi magana da ita a kan dukiyar Mahaifin nata".

"Ai Hajiya ki bar zancen waɗannan matsiyatan, gadon ne baza a raba ba inga wanda zai sake tako mana gida yace zai ci mana mutunci, ƴan iska matsiyata."

Hajiya tace, "a'a dole ne a raba ko don mamacin, kana ganin yanda suke tada jijiyan wuya duk wannan fitinan a kan Faruk zai ƙare, gwara a raba ko zai samu salama a cikin ƙabarin shi, inyaso ko can Riyadh ɗin ne sai ku je tare a san abun yi."

Kansa kawai ya gyaɗa ya haura sama da sauri domin har yanzu a cikin fushi yake, bindigan na hannun shi tunda Jalilan ta kawo mishi, Da da farko ta ƙi kawo wa ne tana tsoron abun da zai biyo baya, sai da ya hau ta da faɗa sannan ta kawo a lokacin su kuma su Kawu Ali tuni sun fice a gidan.

Su Hajiya suna falo suna mayar da zancen duk kan su sai cece kuce suke yi suna tsine wa su Kawu Ali musamman yanda Ummee take ta faɗar mugun halin su, abubuwan da suke musu tun Faruk yana da rai, dama ba shi suke ƙauna ba dukiyar shi suke so, ga shi kuma yanzu sun biyo sahu har suna iƙirarin zasu aurawa ɗan su MEEMA ne.









✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

*TWO DAYS AGO*

"Ke ɗaga kanki mana, wai lafiyan ki ƙalau? Na kula tunda muka zo school ɗin nan kike cikin damuwa karatun ma be dame ki ba yau". Cewar Abida wacce ke zaune a kan deks tana taunan chewing gum idanun ta a kan Luwaira. Ganin ta ƙi ɗago kai yasa ta bugi bayan ta tana cewa, "wai Ni kike wa wulaƙanci Luwaira? Ina magana kin yi banza da Ni."

Sai a lokacin ta ɗago kan nata ta zuba wa Abidan idanu. Fuskar ta babu walwala tace, "me kike so in CE miki? Abida ba na son takura don Allah ki bar Ni in huta."

Taɓe baki tayi tana wani yatsina da taunan chewing gum ɗin bakin ta, sai da ta dage ta ɗirka ƙwai ta fasa shi tuss a kusa da fuskar Luwairan kafin tace, "kin san hali na, idan har baki kula Ni ba wlh na dinga damun ki kenan, bazai yiwu ace tun ɗazu muna tare dake kin bar Ni ina ta zuba Ni kaɗai ba, sannan kin wani luƙume kai a benci kamar wata kunkuru ki ce bazan tanka ba. Dalla ki faɗa min damuwar ki Ni fa ƙawar ki ce."

Tsaki Luwaira ta ja, ta san halin Abida shiyasa ta buɗi baki tace, "baza ki gane ba koda nayi miki bayani Abida..."

Katse ta tayi da faɗin, "ba dai ki fahimtar da Ni bane ta yanda zan gane, idan kika faɗa min damuwar ki ai zan gane."

"Hmm matsala ce ta soyayya Abida. Ban taɓa sanar da ke ba amma tunda kin matsa zan sanar miki, na san zaki kalle Ni da wani irin kallo sabida abinda zaki ji ya fito a baki na. Soyayyar Umar Faruk ne yake son kashe Ni, duk yanda na so na jure amma abin ya faskara na kasa."

"To ban gane ba. Wani Umar Faruk ɗin? Ko kin yi sabon saurayi ne?" Abidan ta tambaye ta tana tsare ta da ido

Ita kuma sai ta girgiza mata kai, sai da ta ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu kafin tace, "Yayana Umar Faruk wanda kika sani, wanda muke gida ɗaya da shi; shi nake nufi."

"Kutmar..." Ta saki wani zagi tana duro wa daga saman deks ɗin da take, sai kuma ta koma ta zauna a kan kujera tana facing ɗin Luwairan tace, "ke kar ki haukata Ni mana da yawa, yayan ki dai Yayan ki wanda na sani? Senator Umar Faruk na gidan ku; shi kike so? To ta ya hakan zai yiwu bayan na san Yayan ki ne?"

Kanta Luwaira ta sauke ƙasa tace, "Ba Yayana bane, Umar Faruk ba Momy ta haife shi ba, hasali ma Momyn mu ita ce take auran mahaifin shi ta zo da mu gidan nan, sannan bayan ya rasu mahaifin shi sai ta riƙe Umar Faruk a wurin ta tamkar ɗan da ta haifa, bamu da wani alaƙa da Umar Faruk bayan wannan da nake faɗa miki."

"Tab ɗijam... Gaskiya ban taɓa tunanin ba Momy bane ta haife shi duba da yanda take tsananin ƙaunar sa da nuna masa kulawa, duk da a yawancin lokuta ina mamakin yanda shi ya fita daban da ku, sai dai kasancewar na ga hoton Mahaifin shi shiyasa naga kamanceceniyar su tare, hakan yasa nayi tunanin shi ɗin ya biyo Mahaifin ku ne, ashe duk wannan abun shi ba ɗan Momy bane?"

Gyaɗa mata kai tayi ta ƙara da cewa, "haka ne. Amma kuma maganar gaskiya sai dai Momy ba ta ƙaunar na aure shi."

"To a kan me? Meyasa hakan bayan duk abinda na miji me ji da kanshi ya kai har ya zarta a so shi? A ko yaushe ina ma kaina kallon ban kai ajin da Umar Faruk zai so ni ba, bayan haka da tuni na afka a ƙaunar shi, sai dai ina ganin tabbas zan sha wahala duba da yanda rayuwar shi take, ba na tunanin zai iya so na domin babu ƙofan bayyana hakan, amma ke kuna gida ɗaya da shi kuma kin fi kowa sanin yanda yake ji da ke amma ki kasa sanar mishi, tun yaushe ma kike fama da dakon son shi?"

Luwaira tace, "tun da muka dawo gidan su da zama, kamar yanda nace miki Momy ba ta ƙaunata da shi saboda wani dalili wanda sirrin mu ne bazan iya faɗa miki ba."

Shiru ne ya biyo bayan zancen nata, yayinda Abidan ta kafe ta da idanu tana tunani a ranta. Sai can kuma ta ja numfashi da cewa, "to yanzu ya zaki yi? Idan har kin amince Ni zan taimaka miki, ya kamata ace ke ce kika mallaki babban ƙadaran nan ba wata ba, dama ce a gare ki, Umar Faruk ya wuce duk yanda kike zato, idan da zaki san yanda ƴan mata suke rushing a kanshi zaki sha mamaki tunda na san ke kanki sheda ce, amma babu inda zancen shi be zagaya ba a duk faɗin garin nan, ba na son kiyi rashin shi ƙawata, duk yanda za'a yi ki mallake shi domin kun dace wlh, idan ba haka ba zaki mutu a ƙaunar shi, ke ya kamata ki fahimtar da shi halin da kike ciki, kar ki wani biye ta Momy duk da ban san dalilan ta ba, amma ina mamakin ta ya ya take son hana auren ku duk da tarin ƙaunar da take nuna mishi."

Shiru Luwaira tayi, a zuciyar ta tana son ta bayyana mata sirrin su na son ganin bayan Umar Faruk domin su mallake komi nashi, amma kuma tana tsoro, shiyasa ta sauke numfashi tace, "zan faɗa miki dalili amma ba yanzu ba."

Gyaɗa kanta kawai tayi kafin tace, "fine. Allah ya Kaimu lokacin, yanzu tashi mu je mu samu wani abu mu ci yunwa nake ji, duk chewing gum ɗin nan ya gama ƙwaƙwule min ɗan hanji."

Tashi Luwaira tayi ta ɗauki jakan ta suka fice. Sai da suka je suka ci abinci sannan suka dawo aji, dayake lecture ɗaya suke dashi ana gamawa suka yi gida. Kowa drever'n gidan su ya zo ya ɗauke ta.

Luwaira na koma wa gida ta shiga Parlour ta tarar da Momy zaune ita da su Hafsah. Da gudu yaran suka isa wajen ta suka rungume ta suna mata Oyoyo

Murmushin ƙarfin hali ta sakar musu tana rungume su duka. Daga nan ta ja su zuwa kan sofa ta zauna ta ɗaura Yusra a jikin ta

Cikin murna Hafsah tace, "Aunty Dadyn mu ya dawo, an dawo da shi daga asibiti yanzu."

"Da gaske?" Tafaɗa cike da farin ciki a zuciyar ta jin abinda Hafsan tace

"Eh Aunty. Amma bamu je mun gan shi ba har yanzu."

"Ok ku tashi mu je yanzu sai in Kai ku wurin shi."

Yanda Luwairan take rawan jiki ne yasa Momy ta bi ta da harara. Sai dai kasancewar bata kalle ta ba bata san ma tana yi ba. Har suka fice sannan tayi ƙwafa tana ɗauke kai daga kallon bakin ƙofan da suka fice.



Kai tsaye Part ɗin Umar Faruk suka wuce. Babu kowa a babban parlour'n don haka suka wuce ƙaramin parlour'n

Ai kuwa yana zaune a saman sofa daga shi sai baƙar Singlet a jikin sa da dogon wando Robber kamar na sanyi itama baƙa, ƙasan wandon da mazugi wanda ya bai wa wandon damar tsuke masa ƙafa. Gaban sa kuma computer ne yana dannawa a hankali idanun sa ƙirr a kai. Jin motsin su yasa ya ɗaga kai ya dube su, ganin su yasa ya saki yalwataccen murmushi wanda ke ƙara fito da zallan kyawun sa da kamalan sa. Nan da nan ya buɗe hannayen sa suka zo suka faɗa jikin sa ko wannen su na kiran sunan, "Dadyyyy."

Ita kuma Luwaira hannayenta ta naɗe a ƙirji tana bin su da kallo tare da sakin murmushin da be kai har zuci ba, domin a zuciyar ta ji take yi kamar ta je ta ture su ita ta shiga faffaɗan ƙirjin sa da koda yaushe yake mata gizau a cikin mafarkin ta, bata da wani buri sama da ace an wayi gari ta mallaki wannan basaraken namijin me tsananin haiba da kwarjini gami da nagarta. Tabbas duk wanda ya sami Umar Faruk ya gama dace da duniya domin duk inda na miji ya kai da ji da kanshi ya kai, kyawu nasaba gami da kuɗi duk ya haɗa, ga uwa uba tsantsan ilmi da tawali'u da son ibada. Shiyasa sosai take baƙin ciki da kishi da yaran shi duk idan ta gansu maƙale dashi, ko kaɗan ba ta iya sukunin zuciya sai dai dauriya da take azawa kanta wajen ta ga ta ɓoye abin da ke cin ranta... Maganar da yayi mata shi ya dawo da ita dogon tunanin da ta afka wanda yasa har guntun murmushin da ke fuskar ta ya gushe bata sani ba, da sauri ta gyara kanta tana sake yalwata fuskar ta da wani ƙirƙirarren murmushin tace, "na'am Yaya."

"Ya naga kin tsaya a nan? Come and sit."

Zuwa tayi ta zauna a kan sofa wanda ke kallon nashi still tana murmushi

Sai ya ɗan ƙura mata ido tare da cewa, "me ke damun ki naga kamar kina da damuwa ko? Please faɗa min abinda ke damun ki domin ba na son ganin ki a cikin damuwa, ko kaɗan ba na jin daɗi."

"Oh Yaya babu komi wlh, babu abinda ke damuwa." Tafaɗa maganar tana sosa kai tare da sake faɗaɗa fuskarta da fara'a

Numfashi ya ja tunda shi dama ba Mutum bane me son takurawa makusantan shi. "Well. But kiyi haƙuri har yanzu ban cika miki alƙawarin ki ba. Ki ƙara haƙuri da Ni kinga yanzu nauyi ya hau kaina Ni kaina yanzu bani da lokacin kai na, amma insha Allahu i promise you wannan week ɗin motan ki zata shigo."

"Allah yaya babu komi na san ai baka manta da Ni ba, Allah ya kai mu rai da lafiya."

Murmushi yayi yace, "Amin." Sai kuma ya mayar da kallon sa kan Yusra wacce ta langaɓe masa a jiki yace, "Ya dai my Baby?"

Tura baki tayi gaba tace, "Dady yunwa."

"Yunwa kuma Baby?" Yafaɗa yana ware ido

Ta gyaɗa mishi kai

"To baku ci abinci bane? Hafsah baku ci komi bane da kuka dawo school ɗin?"

Hafsah tace, "mun ci Dady, Momy ta saka Talatu ta girka mana kus-kus amma ita bata ci ba."

Fuskarsa ne ta nuna alamun damuwa, sai dai yayi shiru be ce komi ba

Hakan da Luwaira ta gani ne sai tayi saurin cewa, "Yaya bari in dafa mata a nan tunda yunwa take ji. Me zaki ci in dafa miki?" Ta ƙare maganar da kallon Yusran tana mata murmushi

"Indomie zan ci."

"Nima zan ci Dady ta dafa har da Ni." Cewar Hafsah cikin sauri


"To kuna so ku mayar da ƙanwata kukun ku ne? Basu takura miki ba ko sister?" Yayi maganar yana kallon fuskar ta

Murmushi ita kuma tayi tace, "haba dai a'a wlh, ai babu damuwa, bari in je in dafa musu."

"Ok thanks my Sister. Nima ban san meyasa Kukun su har yanzu be dawo bane, ina tunanin zan sama musu wani."

Luwaira ita dai tuni ta tashi ta nufi kichen. Hakan yasa Hafsa ta bi ta tana tsalle-tsalle

While Yusra ita kuma ƙara maƙalewa a jikin sa tayi

Shafa kanta yayi kafin ya ci gaba da latsa computern shi, jefi-jefi yana ɗago kai yana mata magana yana hura mata iska a fuska ganin tana wani lumshe idanu

Hakan yasa ta ɗan dawo da kuzarinta ta saki jiki har tana dariya. Ta soma tsalle a jikin sa kamar yanda ta saba

Ɓoyayyen ajiyan zuciya ya sauke ganin ta saki jikin ta sosai. Ya san duk da yunwa ya mayar da ita haka, ko daga kallon ta zaka gane ƙarfin hali kawai take yi saboda Yusra akwai ci ba ta wasa da cikin ta, abu kaɗan ke saka tayi wani yaushi da ita tunda ta kasance me son gazar-gazar. Shiyasa yake matuƙar ƙaunar yarinyan saboda sak mahaifiyar ta ne, har lukutin jikin ta na Nusaiba ne.


















*Nayi iya yi na wajen sanar muku ina buƙatar more comments but har yanzu You don't changes, I'm very tired! from today insha Allah I will not posted again. Nima ina bukatar Comments ɗinku domin shi ke saka Ni naji daɗi a raina har na tabbatar da cewa ana karantawa, ko Thanks ka rubuta min zai tabbatar min kana karantawa, amma yanzu na gane babu masu bukata insha Allahu na dakata daga yau sai kuma sanda Allah ya waiwayo Ni. Bissalam 🙏🏻 Ina ma Real masoyana Barka.*
[14/10, 10:03 PM] نفيسة ام طاهرة: 💎💎💎
*MEEMA FAROUK*
                        💎💎💎


*NA_NAFISA ISMA'IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*🧝🏼‍



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*



                 *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._


















                             *NO_27*

             Bayan Luwaira ta gama dafa musu indomien sai ta zubo ta kawo musu parlour'n. Sannan tayi masa sallama ta fice

Shi kuma yana ta faman aikin shi har suka gama cin abincin suka koma wasa da juna. Daga ƙarshe kuma barci ne ya ɗauki Yusra. Hakan yasa ya tashi ya wuce sama inda ɗakin shi yake ya bar Hafsah tana kallon cartoon. Da shigan shi ɗakin inda yake ajiye towul ɗin shi ya nufa ya zari ɗaya ya wuce cikin Toilet. Wanka yayi ya fito sanye da towul ɗin a jikin sa. Kai tsaye gaban mirror ya nufa ya gyara suman kanshi kana ya wuce wajen sif ɗin kayan shi ya zaro wani farin yadi me tsananin haske da taushi, kayan dai-dai jikin sa suke sun masa kyau ainun tare da ƙara haskaka skin ɗin shi, sai yayi amfani da baƙar hula tare da cover shoes su ma baƙi, sannan ya wuce gaban mirror ya feshe ko ina na jikin shi da turaruka masu tsananin ƙamshi da shiga rai, agogo ya ɗauka ya ɗaura a tsintsiyan hannun sa kafin ya zari wayoyin sa guda biyu ya zuba a aljihun wandon sa ya fice da keey ɗin mota a hannu.

          A lokacin da ya fita falo ya tarar da Hafsah itama tana gyangyaɗi, kai tsaye wajen ta ya nufa ya kira sunan ta. "Baby na KE ma barci kike ji?"

Kanta ta gyaɗa mishi ba tare da tayi magana ba

"To Ni kuma ga shi zan fita. Amma tashi mu je wajen Momy sai ku kwanta a can."

Tashi tayi shi kuma sai ya nufi wajen Yusra ya ɗauke ta ya aza ta a kafaɗan shi, tare da riƙe hannun Hafsan suka fice. Part ɗin Momy ya nufa yayi Nocking a bakin ƙofan kafin ya tura da sallama a bakin sa ya shiga. Babu kowa a parlour'n don haka ya sauke Yusra a saman kujera ya shimfiɗa ta

Yana cikin gyara mata kwanciya ne sai ga Talatu me aikin Momy ta fito daga kichen. Wajen shi ta nufa tana gaishe shi tare da mishi, "ya jiki?"

Murmushi yayi mata kamar yanda ya saba ya amsa ta cikin mutuntawa. Kana ya tambaye ta, "ina Momy?"

"Tana ɗaki bari in Kira maka ita."

"A'a ba sai kin kira ta ba, ga su Hafsah nan ki shiga da su ciki suna jin barci ne, idan Momy ta fito ki sanar mata na fita."

"To ranka ya daɗe!" Tafaɗa cikin girmamawa kana ta matso da zummar ɗaukar Yusran

Shi kuma ya shafa kan Hafsah kafin ya juya ya fice. Kai tsaye haraban gidan ya nufa nan da nan securities ɗin sa suka nufo sa suna kai gaisuwa gare shi. Tsayar da su yayi da hannu kana ya wuce gaban wata farar mota ƙirar jib zai buɗe da kanshi, amma sai ɗaya daga cikin security ɗin ya zo da gudu ya buɗe masa. Sai da ya shiga ciki kafin ya kalle shi fuskar sa a sake yace, "ba na son ku biyo baya na."

"Amma ranka ya daɗe!..."

Katse shi yayi da cewa, "ya isa. Haka nake buƙata ba na son ku biyo NI zan iya da kai na ok?"

"Ok Sir. Allah ya tsare." Yafaɗa yana sara mishi. Sannan ya mayar da ƙofan motan ya rufe mishi

Shi kuma ya ja motan a hankali ya fice a gidan.




                       ******

          Momy da ke tsaye a bakin windown ɗakin ta tana kallon duk abin da ke faruwa. Bata saki labulen ba har sanda ta ga fitar Umar Faruk sannan ta ja dogon tsaki tana yarfe labulen. Sai ta koma zagaye ɗakin hannayen ta a goye a baya, gaba ɗaya damuwa ta nuna a fuskar ta kasancewar gani take yi wankin hula na son Kai su ga dare, har yanzu sun kasa cin nasara a kan shi, ga shi abinda suka shirya domin ganin bayan shi hakan be kasance ba, ya tsallake hatsarin da suka shirya mishi yanzu basu san kuma abinda zasu yi ba next? Tunanin Momy duk ya tafi ga matakin da zata ɗauka a kanshi. Ya zata yi? Zuciyar ta tana bijiro mata abubuwa da dama a ranta wanda har yanzu ta kasa yanke ƙwaƙwƙwaran makaman abin da zasu yi. Maganar Abdul ne ya faɗo mata a rai sai ta saki dogon numfashi tana komawa bakin gado ta zauna tare da tsirawa waje ɗaya ido. ita yanzu abinda ke damun ta kar yace zai auro wata ya kawo ta cikin gidan nan kamar yanda take buƙata, duk da ba har zuci take mishi maganar ba amma ba ta son ya sake aure, gaskiya akwai matsala dole ta samo mafita, amma kuma ba ta so ɗiyarta ta aure shi domin dole nan gaba zata rasa shi, "amma kuma idan dogon burin ki zai cika fa?" Wata zuciyar ta tambaye ta haka.




✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

           A hankali yake tuƙin motan cikin ƙware wa, duk da tuƙin yake yi but hankalin shi gaba ɗaya ya tafi ga tunanin abun da ke zuciyar sa, shiyasa lokaci-lokaci yake fuszar da iskan bakin shi yana ɗan dukan sitiyarin motan kaɗan-kaɗan a haka har ya kai gidan Hajiya. Ya danna horn me gadi ya fito

Ganin da yayi Umar Faruk ne sai ya koma ya buɗe mishi Gate ɗin ya shiga da motan

Parking space ya nufa ya faka motan

Da gudu me gadin ya taho ya buɗe mishi ƙofan yana washe baki da faɗin, "Barka da zuwa ranka ya daɗe!"

Murmushi yayi mishi yace, "Yauwa. Kana Lafiya?"

"Alhamdulillah ranka ya daɗe!" Yafaɗa cike da fara'a kamar zai duƙa mishi

Shi kuma fitowa yayi a motan kafin yace, "Allah yasa Captain yana nan?"

"Eh yana nan don yanzu ya dawo gidan ma."

"Ok." Yace dashi sannan ya saka hannu a cikin aljihu ya zaro sabbin kuɗi ƴan dubu ɗaya ya ba shi

Nan ya soma mishi godiya kamar zai je ƙasa don duƙa masa

Shi kuma murmushi yayi yace, "kar ka damu ka dena min godiya."

"Ai ranka ya daɗe! Dole ne. Allah ya ƙara buɗi yasa kafi haka, Allah ya tsare ka da duk kan sharrin maƙiya."

"Amin Amin." Ya amsa shi cike da jin daɗi kana ya wuce ya tafi. Kai tsaye ƙofan shiga parlour'n ya nufa yayi Nocking

Babu jima wa sai ga Uncle Hashim ya fito yana waya. Ganin shi yasa ya waro ido waje yana kashe wayan kana ya ba shi hannu tare da cewa. "ah ah patient ɗin mu ne a nan? Ya aka yi haka?"

Murmushi yayi ya miƙa mishi hannun suka cafke kana yace, "Ai naji sauƙi Malam."

Matsa mishi yayi ya shigo sannan ya rufe ƙofan suka shiga Parlour

Zabba'u da Jalila ne zaune a parlour'n. Don haka suka soma gaishe shi Zabba'u na faɗin, "ikon Allah har ka samu sauki da zaka fara yawo Umaru?"

Murmushi yayi yana zama

Shi kuma Uncle Hashim yace, "nima abun da na gani kenan. Yau fa aka sallame ka? Gaskiya zan ɗau mataki a kan masu tsaron ka da har suka bar ka ka fito, i know Momy bata san ka fito ba?"

"Haka ne. "But I'm relieved. I came to greet Hajiya."

"A'a ai baka kyauta ba kuwa. Ina kai ina zuwa gaishe da Hajiya baka da lafiya, itama baza taji daɗi ba, bari in Kira ta." Cewar Zabba'u tana tashi ta wuce

Ita kuma Jalila tuni ta tashi ta kawo mishi drinks ta ajiye mishi

Godiya yayi mata sannan ya tambaye ta, "ina Habeeb?"

"Yana tare da Ummee a ɗakin ta".


           Fitowar Hajiya itama sai da tayi mishi faɗan zuwan nashi

Shi kuma yace, "ya zo gaishe ta ne kawai."

Tace, "haba dai Umar. Kana wasa da lafiyan ka dai, amma mene ne na zuwa gaishe Ni bayan yau aka sallamo ka?"

Uncle Hashim yace, "hm Hajiya bar shi kawai."

Tace, "duk da haka dai mun gode, sai dai ka riƙa kula da lafiyan ka. Ya jikin naka Yanzu?"

"Alhamdulillah Hajiya."

"Masha Allah haka ake so ai. Allah ya daɗa tsare ku ya taimaki rayuwar ku."

"Amin Hajiya." Shi da Uncle Hashim suka amsa

A lokacin Ummee itama ta fito suka gaisa take tambayar shi itama jikin nashi?

Yace, "da sauƙi Aunty."

"To Masha Allah mun ji daɗi Allah ya tsare gaba."

Daga nan ɗan hira suka taɓa kafin suka fita da shi da Uncle Hashim zuwa waje. Sai da suka kai baƙin motan shi sannan ya kalle shi yace, "Your daughter is not here?"

"Oh ko dai wurinta ka zo ne? Tell me the truth?"

Murmushi yayi yace, "No Ina tambaya ne saboda ban ganta ba."

Uncle Hashim yace, "bata dawo daga wajen aiki ba, amma na san yanzu zata shigo tunda three ya kusa."

"Ok." Yace yana ɗan kaɗa keeys ɗin hannun sa

"I still don't trust you Dude, tell me the truth you come to her?"

"Yes. I think about your talk, I

Please Login or Register in order to submit comment