Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


*Happy New Year 2021*
Allah yasa mun shiga a sa'a ameen

*💔 JIDDA 💔*

*By*

*Maman Maama*

Bismillahir Rahmanir Rahim

Assalamu alaikum masoyana da masoyan littattafai na. Kamar yadda nayi alkawari tun kafin in fara *Tagwaye* cewa zanyi su su biyu da *Jidda* to alhamdulillah an kammala Tagwaye ga kuma Jidda nan yazo muku, ina kuma fatan zaku karbe shi kamar yadda kuka karbi Tagwaye koma fiye da haka.

Dan dai idan nace *Jidda* is a must read for every woman zai zamanto kamar naso kaina da yawa ne, amma gaskiya in baki karanta *Jidda* ba zan iya cewa an barki a baya. It is going to be a hit, that I promise you.

Tafiyar *Jidda* da banbanci da sauran littattafai na, banbancin kuwa shine about 70% na labarin Jidda is based on true life events, musamman daga farkon sa zuwa tsakiyar sa, karshen sa ne kawai zai zama fiction yadda zai fi kayatar da ku. I gave this book my all, na rubuta shine from the very depth of my heart. Sometimes ina murmushi, while other times ina share hawaye, so get ready to do both.

Littafin Jidda na siyarwa ne kamar yadda na riga na fada tun kafin fara Tagwaye. Da farko nayi niyyar sai na gama gabaki daya zan fara posting, but I found out cewa ba zan iya ba, without your motivation I lost my courage, wannan ya tabbatar min idan babu readers babu *Maman Maama* dan haka zamu fara a haka.

Sai dai ba za'a ke samun posting kullum ba saboda alhamdulillah kullum responsibilities suna kara yi min yawa ne, I guess wannan shine girman ko? Lol. Za'a ke fashin kwana dai dai, misali in akayi Saturday ba za'a yi Sunday ba sai Monday. Yes, nasan wadansu ba zasu iya jira ba and I advise them to wait sai anyi nisa ko kuma ma su bari a gama sai su karbi document. Please in kinsan ba zaki iya jira ba kar ki biya, don't pay and be pressuring me please. Fashin kwana dai dai so that you will have well arranged and well edited episodes insha Allah. I assure you that ba zakuyi dana sanin siyan Jidda ba, it is going to be one of your best dan for me *Jidda* already ya kere wa saura a zuciya ta.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067801020

Please banda kira, WhatsApp only

Again dai ina tunawa nasu siyan online novels cewa copyright (hakkin mallaka) na marubuciya ce, ita kadai take da right din copying da kuma sharing littafin ta, duk wanda yayi hakan bayan ita to ya shiga hakkin ta kuma duk munsan cewa Allah baya yafe hakkin wani har sai shi ya yafe da kansa.

Allah yasa mu gane ameen.

Akwai 18 free pages insha Allah

Asha karatu lfy

*Episode One........The Beginning and the End of Me*

Free page

A duk lokacin dana duba rayuwata, kamar in inaso in bada labarina, na rasa dalilin da yasa bana iya farawa ta farko na, bana iya farawa ta lokacin da aka haife ni ko kuma ince lokacin da na bude idona na ganni a duniya. A kowanne lokaci in na duba bayana ina farawa ne da ranar dana fara ganinsa, a gurina wannan ranar, wannan hour din, wannan minute din da kuma wannan second din da idanuwan sa suka shiga cikin nawa a lokacin ne rayuwata ta fara. A lokacin ne kuma rayuwata ta kare.

Ranar visiting day ce a makarantar yammata ta garin Taura dake jahar Jigawa. Kasancewar yan ss3 ne kadai a makarantar suna zaman extension wanda ake yi lokacin zana jarabawar karshe ta secondary ya saka makarantar take shiru ba kamar sauran ranakun visiting ba.

Ni da babbar kawata a lokacin, Mufida, munyi duk abinda yake al'ada ta dalibai dan wannan ranar, munyi wanki da guga da kitso, sannan muka tashi da wuri mukayi wanka muka yi kwalliya dai dai irin wacce ake barin dalibai suyi sannan muka fita class area tare da sauran ɗalibai dan jiran tsammani, duk da dai muna saka ran tabbas za'a zo mana visiting daga gidajen mu dan ba'a taba fashin zuwa mana ba sai dai in da kwakwkwaran dalili.

Can nesa muka samu benchi muka zauna, dan ba'a bari dalibi yaje gurin sai an kira shi sai su headgirl da kuma prefect on duty. Kasancewa ta health prefect kuma kasancewar ba duty na bane ranar yasa nayi zamana muna hira excitedly da Mufida. "Yaya Mukhtar yace min zaizo, yace tare da matarsa Aunty Halima ma zasu zo" Mufida tace "hmm. Ni bansan ma dawa dawa za'a zo min ba. Nasan dai Mama confirmed zata zo"

Kiran sunana da mukaji anayi ya saka mukayi saurin juyawa cike da mamaki. Na kalli agogon fatar da yake hannuna, few minutes after ten, nooo there must be a mistake dan nasan yan gidan mu ko wanka basu gama yi ba balle girki balle har su dauko hanya daga kano balle su zo. "Hauwa'u Habib" aka sake kirana. Na mike ina kallon Baba mai kiran alkhairi da yake tsaye da takarda a hannunsa "Baba? Hauwa'u Habib da gaske?"

Ya nuna min takardar, "karanta da kanki in kina ganin ban iya karatu ba" na girgiza kai na "akwai Hauwa Muhammad Habib, ko dai ita ce akayi mistake, ni ba yanzu zasu zo ba sai yamma suke zuwa" yayi gaba yana cewa "sai kije can ki gani ai, in bake din bace ba sai ki dawo ki kira waccan din" na gyada kai tare da binsa da sauri ina yiwa Mufida signal cewa ina zuwa, yana ta zabga sauri, ni kuma in akwai abinda ban iya ba to sauri ne, generally ma ni komai nawa a sanyaye nake yinsa tun daga magana har tafiya har komai. Da wahala kaji ni na daga murya.

A gaban staffroom, inda few iyayen yara suka fara zuwa kuma mostly maza ne suka fara zuwa na hango motar Abban mu, nan take jikina yayi sanyi, shikenan ta faru ta kare anyiwa mai dami daya sata, shikenan Abba shi kadai yazo. A lokacin na ganshi ya fito daga staffroom yana duba agogon sa sannan ya dago kai briefly ya kalle ni yace "kiyi sauri mana! Kina tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, sauri nake yi daurin aure ne dani a gumel shi yasa banzo da iyayenki ba"

Na durkusa a gabansa "Abba sannu da zuwa, ina kwana?" Bai amsa ba ya cigaba da magana "kiyi sauri ki dauki sakon ki in wuce, already ma na makara har goma ta wuce. Umman ki ce ta tsayar dani wai sai ta soya miki miya" ya karasa yana zagaya wa baya tare da bude booth, na bishi can na sake gaishe shi "Abba ina kwana?" Ya fito da kwalin indomie da bagko ya ajiye sannan yace "lafiya lau, ya karatun? Komai dai lafiya ko? Babu wata matsala ko?"

Na gyada kai na automatically hawaye yana zubowa. Ya tsaya yana kallona, "kuka kuma? Wato kin fi son uwarki akai na ko? Shine kike kuka dan ni nazo uwarki bata zo ba ko?" Nayi saurin girgiza kai ina share hawayena. Wasu kuma sababbi suna replacing dinsu. Yace "kinga, sauri nake yi yanzu shi yasa ban taho dasu ba, kuma suna can suna rigimar tasu da suka saba. Ki bari in na koma gida, in mun sami albashi, sai in hado su da wani a cikin yayyenki ya kawo su ki gansu"

Na sake share hawayen ina gyada kai, sannan nace "Abba ina Farhan?" Ya danyi murmushi yace "tana can tana kuka wai sai ta biyo ni, rigimammiyar yarinya kawai, duk halinku ai iri daya ne" sai kuma ya fara shafa aljihun sa "kinga na manta ma ta bani takarda in baki. Yar banza, ko me ta rubuta a ciki?"

Ya dauko wata farar takarda daga aljihunsa ya miko min na karba ina dan murmushi kadan sai kuma hawaye suka biyo murmushin, ina ta burin ganin ummana da yanuwana, shi Abba ma yana daga can karshe a list din wadanda nake son gani.

Ya sake mayar da hannun sa aljihu ya dauko 1000 ya miko min. "Kun kusa kammala wa ai, in kika lallaba kayan nan da kuma kudin nan zasu ishe ki. Sai ki dage da karatu dan naga kamar kinfi yanuwanki son karatun, gashi nan kaf yan uwanki mata babu wacce take morar karatun ta duk sun biye wa mazajensu sunyi zamansu suna zuba yaya. In kika dage kika ci ssce sai ki wuce kiyi nursing, ko Allah zai saka in mori kudina a kanki"

Na gyada kai "insha Allah Abba" wayarsa ta fara kara, ya bude mota "kinga har an fara kirana a waya. Na tafi, in sunzo to....in kuma basu zo ba sai kun gama jarabawa" na ja baya ina daga masa hannu, bai ma lura ba yana magana a wayarsa har sai da ya juya mota sannan ya daga min hannu briefly ya wuce.

Na sunkuya na dauki kwalin da hannu daya, na kuma dauki bagkon da daya hannun na fara tafiya a hankali zuwa hanyar hostel. Tun daga nesa Mufida ta hango ni, ta mike da sauri ta zo ta karbi kwalin hannuna "wai da gaske yan gidanku ne? Har sun tafi?" Maimakon in bata amsa sai sababbin hawaye suka biyo kuncina, ta ja bakinta tayi shiru muka cigaba da tafiya tare dan tasan in ta cigaba da jan maganar zan cigaba da kuka ne kuma daga nan in ba sa'a naci ba zan iya samun attack na asthma.

Sai da muka je har daki muka zauna a kwanar mu sannan nace mata "Abba ne yazo shi kadai" na bata labari in brief na abinda ya faru. Ta bani hakuri tana kokarin yi min hira dan in manta sannan ta fara fito da kayan da aka kawo min tana sakawa a lokar kayan abincin mu. Ta dauko food flask guda biyu, daga maikon jikin dayan munsan miya ce a ciki, ta bude dayan sai ga taliya.

Na danyi murmushi, Allah sarki Umma, na tabbatar shinkafa tayi niyyar dafa min dan tasan nafi son ta amma azalzalar Abba ya saka ta dafa taliya, nasan bai ma gaya mata cewa ba zai zo dasu ba sai da safe zata ga ya fito yace ta kawo sako zai taho. Na dauko takardar da Farhan ta rubuto min na bude na fara karantawa

Dear Sister
Abba yace ba zai zo damu ba, zanyi miki dan malele ma bai barni nayi ba yace ba zai jira ba. Kiyi hakuri insha Allah zan roki yaya Mukhtar ya kawo mu ni da Aunty Halima da Mammy da Amira. Akwai labari sosai, in gaya miki nayi sabon kamu a cikin invigilators din mu. Sai nazo zan baki labarin sa.
Kar kiyi kuka.
Farhan

Murmushi nake yi ina karatawa amma ina zuwa gurin kar kiyi kuka sai na fara kukan, na rufe fuskata da takardar ina kuka ina missing yaruwata. Na rasa dalilin da yasa ita take day school ni kuma nake boarding duk da cewa set din mu daya da komai.

Mufida ta zuba abinci muka ci sannan ta zuba wa duk yan dakin aka kai musu, muka yi alwala mukayi sallah sannan muka sake gyara fuskar mu muka koma class area dan yanzu ne aka fara zuwa sosai. Bamu dade da komawa ba kuwa ai gashi anzo kiran Mufida "Zainab Muhammad Gidado" ta mike da sauri tana murna, "dama wallahi motar can data shigo sai da jikina ya bani sune, irin motar Yaya Doctor" na dan yi murmushin takaici, wato yau sai dai inga kowa da yanuwansa banda ni. Ta ja hannuna "taho muje mana" na makale "kin san Malam Yakubu yana can, kar ya dizga ni a gaban mutane yace naje kwadayin jar miya" tayi dariya "dalla can, ke tsoro ne da ke, akwai mutane da yawa a gurin ba zai gane cewa ba'a kira ki ba"

Na dan sake yin jim, ni mutum ce mai bin doka da ka'ida tun ina yarinya, ina da rules akan kaina kuma ina da su akan wasu, sannan ina iyakacin kokari na na ganin ban yi stepping boundary ba ko wanne iri ne, uwa uba, ina matukar gudun wulakanci. Na kuma girgiza kaina. Ta jani da karfi "me zakiyi to in kin zauna din, sai dai kiyi ta kallon mutane suna shiga da fita? Ko kuma so kike ki koma daki kiyi ta kuka?"

Tana maganar tana ja na ina tirjewa kamar uwa da rigimammiyar yarta, na san she meant no harm, tana so ta rage min jimamin rashin zuwan yan gidan mu. A haka muka je gurin da ta hango motar gidan su, muna zuwa gurin ta sake ni ta tafi gurin mahaifiyarta da gudu ta rungume ta "mamana oyoyo" sai kuma ta gaishe da amaryar babansu "sannu da zuwa Aunty" sannan ta juya kan sisters dinta biyu da aka zo dasu, Muhibbat da Muhsina, suka rungume juna, sai naji ina kewar nawa yanuwan, da yanzu muna nan muna hira abin mu, da yanzu Farhan ta bani labaran da ta ce zata bani na sabon saurayin da tayi.

Na danyi kokarin gaishe da maman su Mufida amma duk hankalin su yana kan yarsu, sai naja baya na tsaya ina kallon su feeling awkward, feeling like a trespasser. Har na fara tunanin juyawa in koma sai Mufida ta gabatar dani "Mama ga Jidda fa, Jiddan da nake gaya muku" Mama ta juyo tayi assessing dina tun daga sama zuwa kasa, sannan kuma sai naga tayi murmushi da alama zuciyarta ta yarda da abinda idonta ya gani "a'a Jidda yan makaranta, ya karatu?" Na durkusa nayi gaisuwa ta biyu duk suka amsa min da sakakkiyar fuska, sannan muka shinfida tabarmar da suka zo da ita muka zauna suna ta hira ina dan saka baki kadan a inda naga sun sako dani. A dan lokacin na lura da wani abu, Maman su Mufida tana matukar son ƴaƴan ta kuma bata boyewa, kuma na lura auntyn su tana da kirki.

Ni dai ina zaune daga dan gefe kadan ina ta wasa da zaren tabarma da hannuna, ba wai rashin sabo da su ne ya saka na kasa sakewa ba. A'a, wani irin abu nake ji tun da nazo gurin, wani irin feeling na kamar ana kallona, wani irin kallo mai kaifin da nake jin kamar yana ratsa kayan jikina ya huda skin dina da tsoka ta da kashi na ya zarce har cikin zuciyata. Wannan yasa nayi ta gyara zama ina kuma gyara hijab dina amma na kasa jin dai dai, kuma na rasa a ina idanuwan da suke kallona suke.

Na kasa sakewa, nayi ta waige waige amma na kasa gane waye yake kallona. Maman su Mufida ce ta gane discomfort dina "Jidda kin ki sakin jikinki kina ta kalle kalle. Ko neman yan gidan ku kike yi?" Sai Mufida ta basu labarin zuwan Abba na, suka yi ta min dariya ni kuma naji kamar zanyi kuka. Aunty tace "kiyi hakuri kinji? Haka suke mazan nan, nima sanda ina makaranta bana son namiji yazo min visiting, boring" na gyada kai, at least ita ta fahimce ni.

Na mike "zan koma ciki Mufida, sai kin taho" ta mike itama "bara in raka ki hanya to" Aunty tace "to kunga, ku tafi da kaya suna mota, shikenan kun huta" ambaton mota ya saka muka juya muka kalli motar a tare. And then I saw him and I saw the eyes.

Yana zaune a cikin mota a seat din driver yayi adjusting mirror dai dai inda nake, daga ganin karkacewar mirror din kasan karkata shi akayi da niyya. Ina juyawa kuwa idona ya fada cikin nasa, bana ganinsa sosai, bana ganin jikinsa tunda ya juya bayansa, ba kuma na ganin fuskarsa gabaki daya tunda girman mirror din yayi wa fuskar kadan, sai dai idonsa kawai na gani wadanda suka sauka a cikin nawa. And I lost myself a cikin su.

That second, that very second da idanuna suka shiga cikin nasa, wannan shine karshen rayuwata, karshen rayuwata a matsayin Jidda amma kuma farkon rayuwata a matsayin tasa. Last bugun da zuciyata tayi kafin in waiga shine last bugawar da tayi for me, the next bugun da tayi is for him, kuma daga lokacin ta cigaba da bugawa for him. Daga wannan last bugun ta tashi daga tawa ta koma tasa, ta daina bin duk wani umarni na sai dai umarnin sa, ta damka mishi mulkinta tun ma kafin ya nemi takara ballantana har ayi zabe. What a selfish heart!

Nayi kokarin cire idanuna daga cikin nasa amma na kasa, naji kamar Mufida tayi magana amma kwakwalwa ta bata iya assessing abinda tace ba balle ta bada ma'ana, sai dai naga motsinta ta tafi inda motar take da sauri. Bakinta yana motsi kamar tana yi masa magana. And he took his eyes away from me for a second, second din da naji kamar hour guda ne, ya danyi mata magana sannan ya kuma dawo min da idanuwansa kaina, tamkar dan da ya dawo gidansu.

"Jidda" naji muryar Mufida ta ratsa tunani na naji kuma hannunta yana girgiza kafada ta, tunanin me kike yi ne haka. Na dan kifta idanuna ina so su taimake ni suyi cooperating su rabu da kallon idonsa su dawo gare ni. Na kalle ta atlast, tace "ki zo ki gaishe da yaya Faruq"

"Faruq" baki na ya motsa ya ambata a hankali, kamar yana aikawa zuciyata sakon sunan sabon mamallakin ta, commander in charge dinta, wanda yayi min juyin mulki a garin da ni kadai nake ciki nake rayuwata sai shi yau daya shigo ya cika ko'ina ya barni a rakube a gefe, with just his eyes.

Ta kama hannuna muka karasa gurin motar tare "yaya Doctor ga kawata Jidda"

"Jidda" naji ya fada a hankali. Na lunshe idona na bude feeling very proud of my name. Ashe haka sunana yake da dadi? Ko dai maganar sa ce mai dadi? Ko muryarsa ce tayi min dadi. Ko ma dai menene yana da alaka dashi, dan ban taba jin irin wannan akan sunana ba sai da ya fito daga bakinsa.

Ya bude kofar motar, sannan ya zuro kafarsa daya waje ya kuma juyo fuskarsa sosai yana facing dina, and he smiled. His lips curving and his eyes softening. Na sake kokarin dauke idona daga fuskarsa amma na kasa, musamman yanzu da na samu access da dukkan fuskarsa not just the eyes.

Farar fatar sa tayi kama da wadda ake cewa "wanke hannu ka taba" irin wadda zaka yi tunanin in ka dangwala hannunka zaka tabo jini. Ko kuma ido na ne ya nuna min hakan? Ko kuma bakar sumar kansa da baki kuma cikakken sajen fuskarsa ne ya kara haskaka fatar ta sa? Cikakken fuskarsa tayi matukar dacewa da kyakykyawan dogon hancinsa. Sai dai duk wadannan a baya suke, babban abinda yafi birgeni a fuskarsa shine idonsa, wanda zan iya spending hours looking at.

Ya fito gabaki daya sannan ya mike tsaye, tsahon sa ya saka sai na daga kai na kafin in cigaba da kallon fuskar tashi, but that will look awkward right? Dole na hakura da kallon na sunkuyar da kaina ina kallon kafafuwana da suke cikin safa a kuma cikin sandals, ba wai dan kafafuwan suna birgeni ba sai dan bani da wani zabi.

"Jidda" ya sake fada, zuciyata ta motsa a cikin kirjina. Mufida ta taba ni "ki gaida yaya Doctor yana yi miki magana" "ina ruwanki" ya fada. "In bata gaishe ni ba ina ruwan ki. Chakwaikwaiwa!" Tayi dariya "kai Yaya, kawai dai ranta a bace yake tun safe, abbanta ne yazo ba ummanta ba shine take ta fushi" ya gyara tsayuwar sa yace "haka ne? I see. Wato ba kwa son maza suyi visiting dinku kunfi son mata ko? Shi yasa ni ma tunda nazo baki ko kalle ni ba sai kika barni da leke ta window ko? Yayi kyau"

Ta kama hannunsa, nabi hannun da kallo ina lura da zobban azurfa guda biyu dasuke jere a middle finger dinsa da manuni, "ha! Yaya, wallahi ban san kana cikin mota ba" ya karbe hannunsa "inafa zaki sani? Kina can kina daddanne min uwa. Kina can kina introducing friend dinki to all but me"

Ta dawo kusa dani ta dafa ni "Jidda kenan. My very best friend" ta nuna shi "Jidda ga yaya Faruq, my favorite brother. One in million" ya sake yin murmushi mai sauti. "Dadin baki ko? To ko kwandala ba zan baki ba" na dan russuna, still kaina yana kasa "ina wuni?" Yayi shiru amma ina jin idonsa a kaina, "bana amsa gaisuwa sai an kalle ni" Mufida tayi dariya "ba ka san Jidda ba, zaka bushe a gurin kafin ta daga kai ta kalle ka" yace "baki san ni bane ba, bayan kallo i bet she is going to smile back at me kafin ta bar gurin nan" ta daga kafada "okay, amma ni nasan kawata ba zata bani kunya ba"

Sai ta zagaya bayan motar ta dauka jakar ghana must go da kuma bagko guda dai dai, da kyar ta fito dasu daga booth din sannan tace "Jidda zo mu dauka mu tafi" yayi saurin cewa "what? Wannan uban kayan zata dauka?" Tace "zamu dauka, da ni da ita" ta fada tana nuna kanta sannan ta nuna ni, na tafi inda take still kaina a kasa na fara kokarin

Please Login or Register in order to submit comment