Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan akayi bikin sai anyi hutu zamu hadu, ban gane wacce Ummi suke nufi ba kuma ban tambaya ba.

Umar ya sake lekowa. Ya tsaya kawai a bakin kofa ya saka hannu a aljihu yana kallon mu. Hajiya ta taba ni "tashi maza ku tafi yana jiran ki, kinsan unguwar ku da nisa" ina mikewa ta kwalla wa Mufida kira tace tazo ta karbi kayan hannuna sannan ta dauko mana abinci a kitchen mu tafi dashi tunda bamu yi dinner ba. Mufida ta fara buga kafa tana shagwaba, "Mama ita ta dauko mana da kanta" Aunty tayi dariya "yayarki ce dai yanzu ko kin ki ko kinso" ta juyo tana harara ta ni kuma na yi mata gwalo sannan na sake yiwa su Mama sallama na fita.

Yana cikin mota a zaune, sai na tsaya a jikin motar ban shiga ba, na sauke glass yana kallona amma bai yi magana ba, nace "Mufida nake jira, zata kawo min kaya inji Mama" sai ya dage glass din. Sai naji ni bana son wannan shirun nasa, fushi yake yi dani na sani. Na hadiye yawun tsoro.

Mufida ta fito tare da Muhsina, suka saka mana kayan a mota sannan mukayi sallama na bude gaba na shiga na rufe.

Bai ce min komai ba ya tayar da motar muka fita muka hau titi, na juya ina kallon sa ta hasken street light ina jujjuya hannuna nace "kayi hakuri" ya juyo yana kallo na "hakurin me fa?" Na mayar da kaina kasa, "naga kamar kayi fushi ne" yace "fushin me zanyi?" Nace "akan abinda nayi" yace "me kika yi" na ji kamar zanyi kuka "dana boye maka gaskiya" yace "gaskiyar me fa?" Na fara yarfa hannu na "aika san maganar da nake yi wallahi kawai so kake ka nuna baka sani ba"

Yace "so nake inji kin fadi laifin ki da bakin ki. Kin kuma amsa cewa kin yi laifi kin yarda kuma cewa baki kyauta min ba" nace "to ai na yarda ban kyauta din ba shi yasa na baka hakuri ai, kuma ina sake baka hakuri. Allah ya baka hakuri" yayi shiru yana kallon gabansa.

Na fara share hawaye na "sau nawa zan baka hakuri ne to wai ba zaka hakura ba?" Ya juyo yana kallona yana jin sautin kuka a muryata. Sai ya danyi murmushi yace "cry cry Baby. Zan hakura mana, amma ba yanzu ba. Ask me again tomorrow morning zaki ji nace miki na hakura"

Na gane abinda yake fada, sai kuma naji damuwar rashin yin hakurin sa ya tafi tsoro kuma ya dawo min. Na jawo kafafuwa na kan kujera na nannade su a cikin skirt dina na kwanta a jikin kofar mota na rufe ido na.

Ina jin motar ta tsaya, na bude ido na na gan mu a kofar wani guri da ban gane ba, sai kuma na lura kamar gurin sayar da gasassun kaji ne, ya bude ya fita bayan mintuna kadan ya dawo da leda ya saka a seat din baya. Kamshi ya cika motar gabakidaya amma ni sai naji kamar hawa min kai kamshin yake, sam banji ina son cin kazar ba, dan gabakidaya bani da appetite.

Ya tayar da motar muka dauki hanyar gida, yayi horn mai gadi ya bude muka shiga yayi packing ya kashe motar. Na dago kai ina kallon sa, ina jin alamar kamar zazzaɓi yana neman rufe ni nace "in na roke ka nace ka hakura da wannan abin zaka hakura?" Sai naga yayi dariya har yana dafe kansa, na bata rai ina jin haushin dariyar sa yace "my dear sweet Jidda. No. Ko kin bani hakuri ba zan hakura ba saboda babu laifin da kika yi min. Ni wannan abin da kike yi ma in baki sani ba shi yake kara min son abin"

Na harare shi ina magana kasa kasa "kayi dariyar ka ka gama, tunda bai kashe kowa ba nima ba zai kashe ni ba" ya juyo sosai sannan ya kama hannayena biyu ya damke a cikin nasa yace

"look at me Jidda. Trust me, ina neman alfarmar kamar yadda kika danka min zuciyarta ki daure ki danka min kijinki shima and I will not hurt either of them. I will not hurt you Jidda. I promise I will never hurt you"

Na lumshe idona na bude. Ya dawo da hannayenmu a tare zuwa fuskata yana goge dan guntun hawaye daya fito a kasan idona.

Ya na kallona cikin ido yace "I can't do it in ranki baya so, in hawaye yana fita daga idonki. Duk matsuwar da nayi da ke Jidda in baki ce kin amince ba ba zan miki komai ba. Zan cigaba da kallon ki ina lallabaki har sai kin ce min kin amince. That's how much I love you"

Na cire idona daga nasa na sauke su kasa, sannan a hankali naji tsoron dake raina ya ragu, gyada kai na "na amince"

Yayi alƙawarin cewa he will not hurt me, but he did, it hurts alot at first har sai da nayi tunanin ajali na ne yazo and then he took away the pain with the pleasures ta yadda har sai da nayi tunanin babu wani sauran pain a duniya. Nayi tunanin babu sauran komai a duniya sai abinda muke yi, na kuma yi tunanin babu sauran kowa a duniya sai shi.

A ranar ya mallaki jikina ya mayar da shi nasa, kamar yadda ya mallaki zuciyata ya mayar da ita tasa.

Wannan dare ne da bazan taba mantawa dashi ba a tsahon rayuwata.....

Ban san sanda muka yi bacci ba, amma nasan nayi dogon bacci dan ban farka ba sai da rana ta fito sosai. Shima kuma feeling din cewa rana ta fito ne da kuma feeling din ana kallona ne ya tashe ni.

Na bude idona a hankali, sannan na sauke su a cikin nasa. Yana kwance a kusa dani, kansa a kan pillow na, fuskarsa kusa da tawa, sannan idonsa akai na. Ina bude ido na yayi min murmushi. Zan iya rantsewa ban taba ganin murmushi akan fuskar sa mai kyawun da yakai na ranar ba.

Na jawo hannayena da sauri na rufe fuskata nima ina murmushi, sai ya rankafo yayi kissing goshina sannan ya saka hannu yana gyara min gashina daya baje akan pillow yace "tun dazu nake ta so in gyara gashin nan, hannuna har kaikayi yake yi amma bana son in tashe ki because you looked so beautiful when sleeping and I love you so much. Maybe a little bit too much. Ina so ki sani cewa daren jiya is the best night of my life so far, ban sani ba ko akwai wani daren da zanfi so fiye dashi nan gaba, in ma akwai inajin daren da zaki haifa min kyakykyawar baby irin ki ne" ya fada yana shafa karan hanci na sannan ya goga nasa akan nawa.

"Na gode Jidda. You gave my everything that I have ever dreamt of. Duk abinda nake so kuma nake da burin samu na samu anan wajen. Ina fatan Allah ya biya ki da aljanna ni kuma ya bani ikon faranta miki kamar yadda kika faranta min. Nagode"

Ya dauke hannayena dana rufe idona dasu sannan yayi kissing idanuwan da suke a rufe. Na bude su ina kallon sa, ina jin sonsa yana kokarin yiwa zuciyata yawa nace "godiyar me kake yi ne wai? Me na baka da zaka gode min? Dama ai naka ne. Abin ka ne da nake ajjiye maka kuma kazo ka karbi abinka. My heart and my body are yours, na Umar ne shi kadai"

Ya dora goshinsa akan nawa, hancinsa akan nawa ya rufe idonsa sannan a hankali shima yace "my heart and my body are yours. Na Jidda ne ita kadai"

And then he kissed me.

Hasken ranar daya matso kan fuskokin mu ne yasa na janye fuskata daga tasa tare da kare hasken da hannuna. "Rana ta fito ba muyi sallah ba" na fara kokarin mikewa sai dai wani suka da naji a kasana ce ta sakani komawa in kwanta tare da yin yar karamar kara. Sai yanzu na tuna da pain din da naji jiya, har yanzu yana nan sai ma tsami da gurin yayi yanzu. Ga karin cinyoyi na da suke ciwo kamar wadda nayi tsallen kwado, sannan ga cikina kamar anyi min yasa, bayan abinci ma kamar harda hanjina aka hada aka kwashe.

"Oops, sorry baby"

Sai kuma yayi dariya. Na juya na harare shi "dariya ma kake yi min ko?" Ya daina dariyar sannan yayi fuskar tausayi "sorry dear, ni ne ko? Ki bar ni da ni zan yi maganin ni. Bulala nawa kike so nayi wa ni?" Na fara matso hawaye duk da bana gaskiya bane ba. Ya mike "sorry sorry, don't start with the crying please. I am going to take care of you" ya sauka daga kan gadon, nayi sauri na rufe idona saboda lura da nayi ashe babu komai a jikinsa, amma na kasa cire image din daga raina.

Ya shiga toilet sai kuma ya fito "babu ruwan zafi a toilet din nan ashe. Bara in duba toilet dinki" na dan bude idona kadan sai kuma na sake mayarwa na rufe. "Please ka saka wani abun a jikin ka" ina jin shi yana dariya sannan ya fadi wani abu da banji sosai ba sannan naji ya bude kofa ya fita.

Na sauke ajjiyar zuciya na bude ido na ina kallon hotonsa da yake dakin, sanye da kayan su na doctors da stretescope a wuyan sa, fuskarsa dauke da murmushi. Nima nayi murmushin ina ji kamar babu wadda ta kaini dace da miji a duniya.

Ina jin motsin sa na mayar da idona na rufe, yace "can din ma babu, but na kunna yanzu. Bara in kunna anan ma. Let me get you something to eat kafin ruwan yayi" na dan bude ido naga ya saka jallabiya, sai ya kunna heater sannan ya sake fita. Few minutes ya dawo da tray a hannunsa ya ajiye sannan ya fara kokarin tashina zaune ni kuma nayi ta zuba masa shagwaba, sai da ya hada min pillows da kuma jikinsa na jingina sannan na tashi ya bani cup din tea daya hada min mai kauri na karba na shanye tas, ya daga hannu "to kin shanye tea din da me zaki ci bread din kuma?" Na langwabe "wani zaka hada min".

Ya dauki cup din "an gama ranki ya dade" sai ya koma ya hado wani ya dawo, sannan ya dauki bread ya shafa min butter na kuma cinye na sake shanye tea din. Ya dauke tray din ya fita dashi sai gashi da apple ya kawo min,shima nace ba zanci ba sai ya yayyanka min, ya koma ya dauko wuka da plate ya zauna yana yanka min ina ci har na cinye.

Sai da na gama sannan nace "banyi brush ba fa" yace "kar ki damu, nayi miki already"

Toilet ya koma ya hada min ruwa sannan ya dawo yana tattare hannun rigarsa da murmushi a fuskarsa. "Yauwa, lokacin yiwa baby wanka yayi" na bude ido "wa za'a yi wa wankan?" Ya kashe min ido, "wai da" kafin in sake magana ya yaye bargon, nayi kokarin tashi da sauri sai kuma nayi kara ina rike waist dina da naji shima ashe ciwon yake yi.

Dole na hakura ina ji ina gani ya dauke ni zuwa toilet, ya saka ni a cikin ruwan zafin da naji kamar ya zuba jajjagaggen attaruhu a ciki, na rike shi kam ina jin ruwan yana shiga kofar da da take a rufe sai jiya aka bude ta, jikina har karkarwa yake yi shi kuma yana ta jera min sannu, a hankali kuma sai na fara jin dadin ruwan sai na sake shi na koma na kwanta. Ina jinsa ya fita.

Ban jima sosai ba saboda sallah da nake ta tunanin banyi ba. Na tsarkake jiki na sannan nayi wanka na tsarki dana sabulu. Na dauko toothbrush dinsa, a raina ina tuna ranar da yace zamu yi sharing toothbrush da toilet, nayi murmushi sannan na saka paste nayi brush sannan na daura towel dinsa na dafa bango na fita.

Baya dakin amma naga alamar ya gyara bed din, duk da dai kana gani zaka fahimci cewa wanda yayi gyaran gadon bai iya ba, bani da kaya a dakinsa dan haka na tafi dakina na lallaba na saka riga da hijab nayi sallah ina jin guilty feeling a raina na rashin sallah da wuri.

Bayan na idar na tashi na shirya cikin riga da wando masu fadi wadanda basu takura jikina ba amma sunyi min kyau sosai kuma sun fitar da shape dina sosai. Na gyara gashina na daure shi a keyata sannan na gyara fuskata lighly. Na bude kofa na fita palo duk da cewa da kyar nake daga kafata amma tunani na Umar, ko ya ci abinci?

Ina shiga palon yana shigowa shima daga waje, da leda a hannunsa, yazo ya kamani "wa yace ki tashi ne wai. Ke fa patient dina ce yanzu" ya zaunar dani akan kujera sannan ya dauko robar ruwa ya bude min ya kuma dauko ledar daya shigo da ita ya ballo min magungunan da suke ciki. Ina gama sha ya kwantar dani akan kujera tare da saka min pillow, shi kuma ya zauna a gabana yana shafa fuskata.

"Don't worry, zaki yi bacci idan kika farka kuma zaki ji ciwon duk ya tafi. Kar ki manta, you have a doctor waiting on you dan haka baki da wani problem"

Na lumshe idona ina masa murmushi, realising cewa harda maganin bacci ya hada min ban sani ba. Ko minti daya banyi ba kuwa baccin ya dauke ni

Cikin baccin naji kamar muryar Farhan tana magana da Umar, na dan bude idona kadan sai na ganta a tsaye tare da Amira, nayi kokarin tashi amma kaina yayi min nauyi sai na mika mata hannu "Farhan" ta karaso inda nake ta rike hannuna

"Amarya. Kar dai baki da lafiya ne, mu da muka zo ziyara" bance komai ba Umar yace "eh bata jin dadi. But tasha magani kuma na bata maganin bacci dan ta huta sosai. Ku barta tayi baccin in ta tashi zata ji dadi sosai" daga nan na koma bacci na.

Sanda na kuma farkawa wajen karfe biyu, naga Amira tana zaune da remote a hannunta tana kallo, na dafe kaina tare da kokarin tashi zaune ina cije lebe da tunanin zanji ciwo a kasa na amma sai naji babu kamar yadda nayi tsammani, sai dan ciwon jiki kadan da kuma wani feeling na yaji yaji a kasan.

Amira ta gaishe ni tayi min sannu sannan naga Farhan ta fito daga kitchen, ita ma tayi min sannu sai na tashi na shiga toilet nayi alwala nazo nayi sallah ta. Ina idarwa Farhan ta zubo mana abinci muka hadu muka ci, tana ta yi min labarin gida da abubuwan da suke latest a gidan "Abba ya bawa yaya shamsu da yaya Aminu kudi zasu shiga kasuwanci da sunan sa, duk wata zasu ke kawo masa abinda aka samu na riba" na gyada kai cikin fahimta. Sai dai ina fatan bai yi mistake ba, saboda su din masu iyali ne kuma naji ance ba'a trusting namiji mai iyali da kudi, amma bance komai akan hakan ba dan bana son Farhan tayi min mummunar fassara.

Ni kuma na bata labarin yanuwan Umar da suka zo min ziyara da kuma zuwan mu gidan su. Ta matso kusa dani tana yi min rada "to wannan rashin lafiyar fa? Anya kuwa ta gaskiya ce?" Ta karasa tana kashe min ido, na dake ta a kafada ina dariya sai tace "dan Allah bani labari, ya kika ji? Da ciwo sosai" she looked concern sai na tuna da nima nawa tsoron.

Sai na girgiza mata kai, "ba irin ciwon da muke tunani bane ba fa, da ciwo dai amma ba sosai can ba. Ba irin wanda muke karantawa a novels bane ba, ba'a suma kuma ba'a wani fitar da jini kamar an yanka rago" mukayi dariya tare sannan ta kara matsowa "bani labari mana" na harare ta "ke zancen manya ne fa. Duk abinda kike so kiji zaki sani ne wata rana, duk kuma bayanin da zan miki ba zaki fahimta ba sai yazo kanki"

Ta tabe baki sai ta fara bani labarin irin damuwar da take ciki yan kwanakin nan da bana gida, kowa ya saka mata ido, dangi kowa zai tafi sai yace "ke yaushe ne naki bikin?" Ko kuma "saura ke, ai da an sani ma hada ku akayi aka huta" Abba kuma yakan ce "hada sun naso inyi ai, ita kuma taki fito da mijin"

Ta juya hannu, "ni makaranta ma nake so ya barni in shiga wallahi. Ga result dina yana da kyau, gashi bana komai a gida, ban san me yasa ba zai barni in yi karatu ba kafin Allah ya kawo mijin".

Sai nayi ta lalashinta da bata shawarar da nake ganin zata bulle mata "hakuri". Muka tashi muka gyara gurin muka tafi kitchen, tare da ita mukayi ta duba kitchen appliances din wadansu ma bamu san yadda ake amfani da su ba sai mu karanta manual, muna fitowa ta tambaye ni "amma dining table din nan ba Abba ne ya siya ba ko?" Nace "eh. Daddyn su Aira ne ya siya min a matsayin gudummawa" ta shafa shi "yayi kyau sosai".

Bayan mun zauna sai na tambayeta "Umar fita yayi ne?" Ta girgiza kai "kamar daki naga ya shiga" na mike da sauri "wayyo Allah. Yana can yana jin yunwa. Yanzu haka ko breakfast bai yi ba" ta bini da kallo "soyayya manja, na dauka ai da aka kar tsami kwarnafin ya kwanta" na harare ta "sai ma tashi da ya sake yi"

Har dare su Farhan suna nan, sun kawo min kayana da na bari a gida sannan suka bude lefena suka zabi abinda suke so, wasu na basu wasu kuma na hana su. Sai da muka ci abincin dare tare sannan Umar yace in dauko hijab dina mu kaisu gida. Ai kuwa har da rawar murna nayi zanga Umma ta tunda ban saka ran ganin ta kusa ba.

Muna zuwa gida na shiga da sauri na na rungume ta sannan na gaishe ta, itama tayi mamakin zuwa na kuma daga dukkan alama taji dadin ganin nawa dan sai bina take yi da kallo da murmushi a fuskar ta, yan samarin ta duk basa nan, sai na bada sakon lallai suma suje suga dakina. Ta saka ni na je na gaishe da Hajiya, ta amsa min babu yabo babu fallasa sannan tace "wannan wanne irin aure ne ko sati ba'a yi ba har an fara zarya a gida? Ko akwai wata matsala ne" na girgiza kaina kawai sannan nayi mata sallama na fita.

Na hau saman Abba da dokin son ganinsa amma ina shiga sai yace "ke! Me kike yi a gidan nan?" Na durkusa "Abba tare da.......tare da shi muka zo muka kawo su Amira" ya kama fada "su amiran basu da kafa ba zasu iya tahowa da kansu ba? Yaran yanxu kun dauki aure kamar wani wasan yara, ki tashi maza ki koma gidan ki kuma kar ki sake zuwa gidan nan idan ba da wani kwakwkwaran dalili ba"

Na mike jiki n a sanyaye, sai dana sauka sannan na tuna ko gaishe shi banyi ba. Ina shiga dakin Umma kafin in zauna ya leko ta baranda " Jidda? kin tafi ko har yanzu kina nan?" Na mike da sauri ina jin kwalla tana zuwa idona, Umma tace "kar kiyi, kar ki sake ki fita kina kina kuka. Ba kim gan mu ba sai menene kuma?" Na dauki jakata nayi mata sallama na fita kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki.

Ina fita waje Umar ya bini da kallo "har kin fito?" Na dauke kai na bance komai ba sai shima yayi shiru ya tayar da motar muka tafi gida.

Sati uku bayan bikin mu hutun Umar ya kare, kuma kusan a lokacin nima muka koma school na shiga shekara ta biyu. A cikin wadannan kwanakin ba soyewa ba in ma kone wa ne duk mun kone kan mu a gida, wannan yasa komawa aikin da school ya dan zame mana da wahala saboda sabawa da junan mu da muka yi.

Sai dai jin dadin mu shine hanyar mu daya, babu nisa tsakanin office dinsa da school dina dan haka tare mume fita ya ajiye ni shi kuma ya tafi, in na tashi ko bai gama ba kuma ya kan ajjiye aikin ya kaini gida sannan ya dawo, na nuna masa ya ke barina ina tafiya a adaidaita sahu amma yaki yarda. "Menene amfani na idan ban kai ki gida ba? Menene amfanin mota ta idan bata dauke ki ba? Da kin iya mota da sai in ke baki kina tafiya da ita, in yaso ni in na gama sai in nemi abin hawa"

That's the kind of person Umar is to me.......

Duk abinda nake so shi yake yi min, duk abinda ya fahimci ina so ko ban furta ba sai yayi min shi, duk abinda yayi tunanin zan so ko da bai ga alama a fuska ta ba sai yayi kokarin yayi min shi in da har bai fi karfin sa ba.

Gidan mu kullum a cike da kayan ciye ciye, tunda ya lura ina da kwadayi, besides ni nafi son kayan kwadayi ma akan solid abinci, dan haka kullum sai ya samu abinda zai siyo min, ko kuma ha dauke ni mu tafi yawon ciye ciye. Duk wani joint a kano da ake siyar da wani abin kwadayi mun san da zamanshi.

Watanni uku da auren mu ne akayi hutun yan makaranta. A lokacin ne kuma mukayi bakuwa. Ummi.

Ni tun zuwan mu gidan su naji suna zancen Ummi tana makaranta amma ban san wacece ita ba tunda ban taba jin sunan ta a bakin Umar ko a bakin Mufida ba. Sai gasu an kawo su tare da Afnan da Affan wai zasuyi mana hutu anan. Na tarye su sosai, yaran suna ta murna, itama kuma Ummin ta gaishe ni na kuma saka ta kai musu kayan su guest room.

Yarinya ce zan iya cewa kusan sa'ar Amira, koma Amira ta dan girme ta kadan dan ta gaya min a js3 take, Amira kuwa lokacin tana ss1. Abinda ya bani mamaki shine muna zaune tare da su a falo Umar ya shigo,sai kawai naga ta mije ta gudu taje ta rungume shi shi kuma har da dan daga ta sama kadan sannan ya ajiye ta yana dariya "ya naji kin kara nauyi? Me suke baku a school din?"

Sai daya ajiye ta sannan ya tari kannensa. Sai naji hakan bai yi min ba, ai ba karamar yarinya bace ba dan akwai nono a kirjinta dan haka zan iya kiranta da balagaggiya. A lokacin bansan menene alakar su ba shi yasa nayi shiru tukunna.

Daga baya ne Umar yake min bayanin ta "kanwar Aunty ce, tun tana karama Aunty take rikon ta har yanzu kuma a hannun ta take. She is like a sister to us" na gyada kai kawai amma a raina ina jin bana son ta duk kuwa da cewa bata yi min komai ba.

Sun kwana biyu anan, kullum in mun fita zamu barsu a gida kuma zan iya cewa tana taimaka min sosai da aikin gida dan kamar yadda take da shegen surutu haka take da aiki. Amma duk da haka zuciyata bata kwanta da ita ba sai dai ina iyakar kokari na wajen boye mata hakan. Sai kuma na fara tunanin ko kishi nake da ita shi yasa nake jin haushinta?

In dai har Umar yana gida to tana kusa da shi, ko magana zata yi masa sai ta rike hannunsa, ga shagwaba, magana daya ta fara yi masa shagwaba tana girgiza jiki shi kuma yana yi mata dariya.

And then ranar da suka yi sati da weekend na kwanta ina bacci da rana a dakina, na farka nayi sallah sai nace bara in duba Umar ko ya tashi yayi sallah shima dan ya riga ni kwanciya baccin ma.

Sai dai ina shiga dakinsa na gansu tare. Yana kashingide ya jingina bayansa da bed frame ita kuma tari ruf da ciki a tsakiyar gadon tana kada

Please Login or Register in order to submit comment