Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kula da ita sosai dan kusan babu abinda ta nema ta rasa, daga ita a gidan sai mijinta da yar autarta, Jamila.

Jamila kyakykyawar budurwa ce yar gayu mai ji da yammatanci, a lokacin tana shekarar ta ta karshe a jami'ar Bayero, tunda muka je gidan muke ta kallon ta cike da sha'awa ni da Farhan, komai na yaya Jamila burge mu yake yi, yadda take kwalliya da dressing, yadda take magana ana yi ana jefa turanci a ciki da tafiya kamar ana tausayin kasa, a ranmu sai muke ji ina ma dai mune muka samu wayewa irin tata. Sai dai kuma a cikin kwana biyun da mukayi a gidan su muka lura da irin tsananin soyayyar da yake tsakanin yaya Jamila da wayarta. Ko da yaushe tana hannunta tana daddanna wa tana murmushi, ko ita da waye oho. Cikin dare kuwa har mu farka fitsari tana cike da waya a kunne tana hira kasa kasa yadda mu da muke daki daya gado daya bama fahimtar abinda take cewa. Bamu tashi tabbatar da zargin mu a kanta ba sai da muka ga ta chanchada kwalliya ta gayawa gwoggo cewa zasu fita unguwa da wani friend dinta, irin yadda tayi maganar kamar mai sanarwa ba wai neman izni ba sannan ta fice ba tare da ta jira amsa ba, har sai da muka yi bacci sannan ta dawo ta kwanta tare da cigaba da magana a cikin wayarta tana dariya kasa kasa. "Yes, I really enjoyed myself" ta fada a hankali. Sai muka kalli juna ni da Farhan sannan muka gyada wa juna kai alamar duk irin tunani daya muke yi. Sai na kwanta ina tunani a raina "shin irin wannan wayewar da irin wannan rayuwar Abba yake gudar mana shi yasa yake takura mu? In haka ne shima yana da tasa gaskiyar kenan.

Gidan Aunty Afia (Mami) shine gida na karshe da muka je. Tun a hanya nake ta zumudin ganinta, ina balain son ta har cikin raina ita da yayanta, Aira da Aarif. Aira kusan sa'a ta ce, Aarif kuma da kadan ya girmi Amira. Ni a idona gani nake kamar Mami da yaran ta sunfi kowa kyau a duniya amma sai inji mutane suna cewa wai kamar mu daya da Aira wai kamar an tsaga kara ni kuma dariya nake yi in aka fadi haka.

Tun daga gate mai gadi ya karbi kayan mu yana mana sannu da zuwa, ya sanni kuma yasan dangantaka ta da gidan. Mijin Aunty mai kudi ne, gidan su kato mai cike da duk abinda suke bukata. Muna shiga na tafi da gudu jikinta na rungume ta ina jin hawaye yana taruwa a idona, ta rungume ni ta na shafa bayana tana dariya, sai kuma ta dago fuskata tana kalla tace "sai yau babanki ya ga damar barin ki ki zo ki ganni ko? Kema so yake ya mayar dake kamar Ayesha ko? So yake ki zama daddawar cikin daki ko? To Allah ya fishi" nayi dariya ina goge hawaye na, "kai Aunty Abba ne fa" tace "Abban ki ne ai ba nawa ba. Tun da ya raba yaruwata da kowa nata sai shi kadai ai nima ba zan raga masa ko inji nauyin sa ba. Wannan ne yasa baya son kuke zuwa gurina" na yi kokarin kawar da maganar ta hanyar fara neman yanuwana. "Aira! Arif!" Tayi dariya suna islamiyya, zasu dawo ai su same ku" sai a lokacin Farhan ta samu ta gaishe ta, ta amsa mata babu yabo babu fallasa sannan ta kira masu aiki ta bada umarnin suyi entertaining din mu. Muna cin abinci su Aira suka dawo nan take muka cika gidan da hayaniya da murnar ganin juna.

Kwana dayan da mukayi a gidan sai naji kamar second daya ne, nan da nan wai har dare yayi kuma har gari ya waye. Duk da cewa ba wani baccin kirki mukayi ba dan kusan raba dare mukayi da Aunty tana bani labarin yanuwanmu da yadda take so watarana Abba ya bar mu muje mu gansu. "insecurity ne yake damun babanku, shi kansa yasan Aysha ba sa'ar auren sa bace ba amma ta dage lallai sai shi, to tsoro yake yi kuma kar takoma cikin dangin tata guje shi, kuma kuma yana tsoron kar kuje can idon ku ya bude ku fi karfinsa, wannan shine matsalar sa. Amma kinga yanzu in kika yi aure ai kin tashi daga ikonsa kin koma ikon mijinki kuma zaki ke zumunci damu yadda kike so insha Allah. Wai in tambaye ki mana, akwai wani ne yanzu da yake zuwa gurinki?"

Nayi shiru ina tunani, Musa dai bana son sa kuma bana jin ya kamata in gayawa Aunty labarin sa, Umar kuma ban ma san menene matsaya a tsakanin mu ba. Na girgiza kai "babu kowa Aunty" ta gyada kai "to Allah ya kawo nagari. Ni in a so nane ma nafi son kiyi aure a dangin mu dan mu karfafa zumuncin mu, amma babu wanda yasan ki a can ballantana ya ce yana son ki"

A ranar da muka dawo gida, bayan mun gama murna da gaishe gaishe sai na ja Amira gefe "ke! Sanda ba ma nan babu wanda yazo nemana?" Tace "a cikin gida ko a waje?" na sosa kai "a ko'ina ma" tayi dariya "wai Musa? Zuwansa biyu fa, ana biyun Umma tace inje in gaya masa ranar da zaku dawo dan kar yayi ta zarya" naji raina ya fara baci duk da babu abinda Musa yayi na bacin rai.

"Bayan shi babu wanda ya zo?" Ta girgiza kanta. "Babu kuma wanda ya kira Umma yana nemana?" Ta kuma girgiza kai "ni dai bansan kowa ba, sai dai in Umma zaki tambaya ko an kira sanda bana nan" nayi saurin cewa "a'a, shikenan" sai kuma na wayance dan bana son tayi ta yi min tambayoyi "kinsan number dinta na bawa kawayena a makaranta, to ina tunanin ko wasu daga ciki sun kira ta ne."

Amma duk da wannan interview din da nayi wa Amira ban hakura ba sai da nayi ta duba call history din Umma wai ko ya kira bata dauka ba kuma bata bi ba, sai dai babu wadansu missed calls daga unknown number, kuma babu daga number din Mufida. Na ajiye wayar tare da yin ajjiyar zuciya. "Ya fasa" na fada wa kai na, "dama karya yake yi" na maimaita. Sai dai kuma zuciya ta taki amincewa da wannan musamman idan na tuna da abinda na gani a idonsa, it looked so real.

Da dare ina tsakar gida Umma ta kira ni ta gaya min cewa Mufida ta kira ni yanzu, da sauri na karbi wayar "Allah sarki Mufida, bara in kira ta mu gaisa" sai dai a wani bangare na raina ina fatan ba Mufidan bace ba. Ina kira kuwa ta dauka, muka yi ta hira tana bani labarin hutun da suke yi a Lagos gabakidayan su, amma ko a cikin magana bata ambaci ko da sunan yaya Doctor ba nima kuma ban tambayeta ba.

Sai dai washegari da yamma ina wanke wanke sai ga dan aike. "Wai ana sallama da Jidda" naji raina ya baci, naki bashi amsa ma saboda takaici sai da Umma ta leko tace "kaje kace tana zuwa" ta kalle ni "baki ji ana magana bane ba? Yaron nan zuwansa biyu ba kya nan kuma ni nace masa ya dawo yau kafin nan kin dawo" na mike bance komai ba na wanke hannu na ina lissafin abinda zanyi masa idan na fita. Hade rai zanyi yayi hirar sa shi kadai, haka zan ke masa a haka har ya hakura ya rabu dani.

Na wanke hannuna da fuskata sannan naje daki na dauko hijab dina na fito, Umma ta bini da kallo sannan tace "ki koma ki shafa mai a kafarki duk tayi jirwaye, sannan kuma ki saka powder a fuskar ki da dan man lebe" na juya still ba tare da na ce komai ba na koma nayi abinda tace ba dan raina yaso ba, na tsaya ina kallon fuska ta a madubi ina hango kamar da ake cewa muna yi da Layla. Nayi ta gwada fuskokin bacin rai iri iri ina lura da yadda suke chanja min kamanni, so nake in samu wadda zata saka inyi muni dan in naje inyi masa yaga muni na yace ya fasa.

Ina tsaye naji kiran Umma, na fita da sauri ina lura da kallon da take min tana noticing ko nayi abinda tace, ina shiga sitting room na goge lipstick din dana shafa har da tabbatar wa cewa ya bata gefen baki na dan inyi muni. Na dan gyara sitting room din na kunna fitila da fanka sannan na bude kofar waje na fita da niyyar kiran Musa.

Sai dai me?.....

Na gane motar sa kamar yadda na gane tsayuwar sa, ya juya bayan sa yana daddanna wayar sa. Gaba na ya fadi "Umar" zuciya ta ta kira sunansa. Kamar tashi zuciyar taji kiran da tawa tayi masa sai ya juyo da sauri ya saka idonsa a cikin nawa. For a brief second babu wanda yayi magana a cikin mu, but I can feel my heart talking to his sai-dai bana jin amsar da tashin take bayarwa. "You!" Na fada a hankali. "You are here" ya juyo sosai tare da saka wayar hannun sa a aljihunsa ba tare da ya dauke idonsa daga cikin nawa ba. Sannan ya rungume hannunsa a kirjinsa yana sakar min lallausan murmushin sa. "Ni din nan da kike gani, murucin kan dutse ne ni ban fito ba sai dana shirya" na dan bata rai cikin rashin fahimtar maganar sa. "Muruci kuma? Wanne irin shiri? Ban gane ba?" Ya taho zuwa gabana ya tsaya, towering over me yadda sai da na daga kaina sannan na ke kallon fuskar sa, fuskar da bana so in daina kalla kamar yadda shima yake rarraba idanuwan sa akan tawa fuskar kamar mai son haddace suffar duk abinda yake cikin ta.

Nayi saurin sunkuyar da kaina dan tunawa da nayi da abinda nayi a fuskar tawa, na wayance da yin tari sannan na rufe bakina da gefen hijab dina ina kokarin goge lipstick din da nayi messing a gurin.

Nayi taku biyu baya tare da nuna masa kofar sitting room din. "Bismillah" nace "sannu da zuwa" na sake fada tare da yin gaba da sauri. Zuciya ta tana tsalle a kirjina.

A tsakiyar falon na tsaya har ya shigo na dan nuna masa kujera a farkon falon sannan na zauna a kujerar karshe "ina wuni" na gaishe shi kaina a kasa, bai amsa ba yace "ya ilahi yarinyar nan kin wahalar da ni. Kinsan kuwa ta yadda nayi nazo gidan nan?" Nace "driving kayi daga gadon kaya zuwa gandu. Babu nisa ai sosai" ya bude baki "wato kin san ma gidan mu kenan. Ya ilahi! Duk wannan wahalar da nasha ashe ke kinsan gidan mu? Yarinyar can karya take yi min kenan" nayi shiru ina lissafi, ni ban fahimci abinda yake so yace ba, nace "wacce wahala kake magana akai?" Ya gyara zama yace "kin san kuwa ta yadda akayi na samu address dinki? Wai ku dama mata haka kuke friendship dinku? Ace babbar kawar ki bata da number din ki kuma bata san gidan ku ba?" Nayi shiru ina accessing maganar, ya cigaba "ashe wai Mufida bata da contact dinki, idan da ace nasan hakan da bazan taba barinki ki fita daga mota ta a ranar nan ba, a cikin kwanakin nan sau uku ina komawa taura makarantar ku wai ko zasu gaya min address dinki amma suka ki gaya min, har bribe na bawa principal dinku ta karbe kuma taki gaya min, sai shekaran jiya suka bani address din wani tsohon malamin ku Malam Abdulrashid, to jiya naje wajensa shima ya gama jirgani ya kuma gama yi min dogayen tambayoyinsu irin na tsofaffin malamai sannan ya bani address din"

Tun da ya fara maganar nake murmushi, ina jin dadin yadda yayi going through wannan dan ya zo gurina sannan kuma ina kara tabbatar wa kaina cewa zargin da Mufida take yi masa ba gaskiya bane ba. Ya lura da murmushin fuskata yace "dariya ma kike yi min ko?" Na girgiza kaina da sauri ina kara fadada murmushi na. Yace "babu komai. Ko yanzu na fanshe duk wahalar da nasha, wannan murmushin kadai ya biya ni duk abinda nayi har da kari. And I can do it all over again for it, for the smile"

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Episode Six : The Sweetest Thing*

Na dan boye fuskata kadan a jikin kujera, yayi murmushi mai sauti sannan ya taso ya kuma dawowa kujerar kusa da tawa yace "amma gayamin, dan Allah wai Mufida bata san gidan nan ba? Kuma wai da gaske bata da number din da za'a same ki? Ni fa jikina yana bani wasa tayi min da hankali. Tana sane ta wahalar dani a banza"

Na dan juyo ina kallon sa ina tunanin ta yadda zan kare kawata. Wata idea ta zo min sai na sunkuyar da kaina nace "jiya ma munyi waya da ita. Suna can Lagos ko?" ya hada yatsunsa suka yi kara yace "I knew it. Yarinyar can ta shiga uku a hannu na, sai na yayyanka naman ta na cinye duk sanda na kama ta. Nace "kawar tawa? Besides, shi abu mai daraja ai dama sai an sha wahala ake samun sa ko? Duk abinda aka samu cikin sauki to anfi saurin wulakanta shi"

Ya rufe fuskarsa da hannu daya yana dariya a cikin kirjinsa sannan ya bude idonsa yana kallo na, ni kuma na rufe tawa fuskar sai yace "na gane, sai yanzu na gane komai. Issoryt. Wato kun hada kai ne dan ku ja min aji ko? Duk abinda nake ciki ashe kina sane ko? I like it, ina fatan dai naci test din?" Nace "ai ba test bane ba, screening ne dan muga how far you can go. Kayi passing first phase saura phase na biyu"

Na mike tsaye, shima ya mike da sauri "dan Allah, kar kice gida zaki koma. Ki barni na cigaba da ganin ki" nace "ganin kama da nayi yanzu a matsayin mai laifi nake. Ba'a gani na sai an samu izni daga Abba na. Ka neme shi, ka ganshi, kayi masa bayanin dalilin da yasa kake son ganin yarsa sannan in ya amince maka sai ka dawo' na juya zan shiga gida naji ya kira sunana "Jidda" na tsaya amma ban juyo ba, naji ya tako xuwa bayana ta tsaya sannan yace "zan je inga Abban mu, sannan zanyi iyakacin kokari na dan in samu karbuwa a gurinsa sannan zan dawo in sake ganin murmushin ki da license dina a hannu na"

Sai da na kai bakin kofa sannan na juyo, muka hada ido yayi min murmushi na mayar masa sannan na shige cikin gida.

Daren ranar is one of my happiest. Dan har sai da Farhan ta gaji da jin hirar Umar ta rufe kunnuwan ta da pillow. Duk da haka kuma ban fasa bata labarin sa ba har sai dana tabbatar tayi bacci sannan na kwanta nima na rufe ido na, fuskarsa ta bayyana gare ni, nayi murmushi, tabbas nasan yau dole ne ma ya shigo cikin mafarki na.

Two days after that, da yamma muna tsakar gida muna cin abinci tare da Farhan da Amira sai Hajiya ta leko daga barandar Abba ta kira ni, na amsa tace in zo inji Abba. Gaba na ya fadi na juya ina kallon Farhan, itama ni take kallo tace "me kika yi?" Na bude hannu "nima ban sani ba" Amira tace "an kira ki a court dole kinyi wani abu da sanin ki ko ba da sanin ki ba ko kuma wani yayi wani abu a gabanki zaki bayar da shaida" na hadiye abincin bakina mukut cikin tsoro sannan na wanke hannu na na hau saman ina karanto duk adduoin da suke cikin kaina, na tarar dashi yana cin abinci, Hajiya tana gefen sa tana yi masa fifita.

Na zauna nesa dasu kadan nace "Abba gani" sai da ya jima yana kallona, jin Hajiya bata ce komai ba na san cewa bata san dalilin kiran ba dan da ta sani da tuni ta fara fada tun kafin Abba ya fara, sai daya gama kallona sannan yace "waye Umar?" na dago kai da sauri, jikina ya fara rawa kamar marar gaskiya nace "na'am?" Ya maimaita "waye Umar nace, wanda kika tura office dina" na sunkuyar da kai na fara wasa da band din hannuna ina murmushi cikin jin kunyar su, this is serious, wato har yaje kenan, lallai da gaske yake kuma wannan ya kuma samar masa space mai kyau a zuciyata.

Jin nayi shiru ya saka Hajiya tace "saurayin ta ne ko?" Yace "eh haka yace min, amma so nake in san a inda suka hadu dashi, yace min a gadon kaya gidan su yake, ita kuma bata da kowa a can, a ina ya ganta?" Hajiya tace "zai wuce a waya?" Ya ajiye chokalin hannunsa yace "waya? Yaushe Jidda tayi waya ban sani ba, waye ya siya mata?" Tace "a'a ba waya ce da ita ba, amma ai suna ɗaukar wayoyin mu suna amfani dasu, zata iya yiyuwa wayar Umman ta ta dauka tayi wannan chatting din nasu na zamani anan suka hadu, kasan yaran yanzu sai addu'a"

Na bude ido ina mamakin yadda za'a yi min sharri ina zaune da raina, nace "a'a Abba ba haka bane ba, yayan Mufida ne fa, yayan kawata ne" ya mayar da hankalinsa kaina yace "yayan kawarki? Yaushe kika je gidan su kawar taki har ya ganki? Ni dai ban san lokacin da kika tambaye ni cewa zaki je gidan su kawarki ba" na sunkuyar da kai na, "a makaranta ne, ranar da muka gama makaranta yaje daukan ta ni kuma na raka ta mota, shine .......shine......kuma sai yazo nan shekaran jiya sai nace yaje ya same ka"

Ya gyada kai yace "haka ya gaya min. Inaso ne in tabbatar. Malamin ku ne Abdulrashid ya raka shi gurina kuma naga kamar da gaske yake, ba yaro bane ba dan cikakken likita ne ma a yanzu, na kuma ya ba da hankalin sa da kuma asalin sa, nace ya cigaba da zuwa gurin ki, in Allah ya hada kan ku kuma kin zabe shi shikenan. Tashi ki je"

Na mike da sauri a raina ina tunanin godiya ya kamata inji masa ko kuma godiyar zata zama kamar rashin kunya? Ban dai gode ba na fita baki har kunne cikin farin cikin da yasa ban damu da maganar da naji Hajiya tana yi ba "likita? Anya kuwa likita bai yi mata girma ba?" Abba yace "a ina kika taba ganin namiji yayi wa mace girma?"

Ban ji sauran maganar ba na sauka da sauri, nasan halin Abba in dai yace abu to ba Hajiya ba ko wacece ba zata chanja shi ba. Ganin fuskata yasa Farhan ta fara murna ita ma duk da bata san abinda ya saka ni murna ba muka rungume juna muna dariya sannan tace "what are we celebrating?" Nace "Umar yaje gurin Abba kuma Abba ya amince" ta kama kumatu na "inye, mun samu lisence sai soyewa kenan" na kama nata kumatun "harda soye soye ma kuwa"

Umma data fito daga dakinta ta bimu da kallo "me za'a soya?" Amira da take jin mu tace "wai wani Umar ne zasu soya shi" muka kwashe da dariya sannan na shige dakinmu da gudu ina jin Farhan tana yiwa Umma bayanin saurayi na ne Umar din "yayan Mufida ne" banji amsar da Umma ta bayar ba saboda na toshe kunnena ina murmushi mai hade da dariya.

A ranar, bai jira sai washegari ba a ranar yazo da dare. Umma tana daure tuwo a leda a tsakar gida ni kuma ina karasa mata miya a cikin kitchen a ka shigo ana sallama dani. Yaron yace "wai ana kiran Jidda inji Umar" nayi kamar banji ba amma na kasa faking murmushin daya sauka akan fuskata. Umma tace "tana zuwa"

Sai kuma ta kira Abbah da ya shiga dakin ta yana kallo tace "kaje waje akwai bako a waje ka gyara sitting room kace masa ya shiga" yace "waye yazo Umma?" Bata ce komai ba sai ta kalle ni, yace "au ho Musa ne ashe, mun hadu jiya ai yana ta jin kunya ta" na juyo na harare shi a raina ina cewa "ba Musa ba sai dai kakan Musa" yayi dariyar ganin yadda na bata rai yace "Allah ya baki hakuri yar malamin makaranta matar malamin makaranta kuma kanwar malamin makaranta, kina tafiya chalk yana zuba"

Duk muka yi dariya har Umma, na dauko ludayin miya na bishi da sauri ya bude kofar sitting room ya shiga, na koma kitchen Umma tace "miko kananan flask a zuba masa tuwo" na mika mata, Amira da take kwance akan sallaya tana game da wayar Umma tace "Umma ni zan kai masa, sai in ganshi in ga ko ya dace da yayata"

Aka zuba masa tuwon semo miyar zogale ta fita zata kai masa ni kuma na fito na wanke jikina a bakin pampo na shiga dakin mu na cire doguwar rigar jikina na saka riga da skirt din atampa nayi daurin dankwali na mai kyau na shafa powder na saka kwalli sannan na saka turare kadan yadda ba zai yi yawa ba na kuma yafa mayafi na na fito, ina fitowa Umma ta harare ni, sum sum na koma na cire mayafin na saka hijab na sake fitowa.

A lokacin Amira ta dawo daga kai abinci bakin ta har kunne "Umma baki ganshi ba wallahi ya hadu sosai. Yace min nima ina da kyau kamar Jidda amma ita tafi ni kyau wai. Ya tambaye ni mu wane yare ne na gaya masa" Umma ta kai mata duka, "to mai bakin aku, waye ya tambaye ki" ta matsa gefe tana dariya sannan ta fito da kudi daga cikin hijab dinta yan dari dari sababbi bansan ko guda nawa bane ba, a daidai lokacin da Farhan ta fito daga dakin Hajiya, ganin kudin ya sa tayi kan Amira da gudu suka shiga dakin Umma, nayi musu dariya kawai na tafi sitting room.

Ina shiga na mayar da kofar shiga cikin gida na rufe, a raina ina fatan bai ji maganar da Amira tayi yanzu a ciki ba, na juyo a kalleshi. Yana zaune akan kujerar da take bakin kofar fita waje, kananan kaya ne yau a jikin sa rigar mai gajeren hannu wadda ta fito da damatsen sa tare da bayyana siffarsa ta cikakken namiji, kansa babu hula sai gyararren gashin kansa.

Ya mike tsaye yana kallona kamar yadda nima nake kallon sa. Na zauna a kujerar karshe nace "sannu da zuwa Yaya Doctor" yayi murmushi bai amsa ba sannan ya taho zuwa inda nake kamar yadda yayi ranar nan amma maimakon ya zauna a kan kujerar kusa dani kamar yadda yayi ranar nan sai ya zauna a gabana a kasa kusa da kafafuwa na yana kallona.

"Gani na dawo Jidda. Naje na karbo license din ganin ki a gurin Abba kuma ya amince min. Saura kuma menene kike bukata? Say it, whatever it is, and it will be done"

Na girgiza kai na a hankali nace "nothing, for now" yace "sai nan gaba? Har yanzu ba'a gama yi min jarabawar ba?" Nace "ba fa exam bace ba..." Yace "it felt like exam, sanda ina gaban Abba I felt like ina cikin exam hall ne banbanci kawai shine babu question paper babu kuma answer sheet" ya danyi dariya "kamar oral exams, nine student Abba shine supervisor" nace "tunda kace kana son ƴar malamin makaranta dole yayi maka exam" yace "da gaske? Sake fada inji?" Nace "me?" Yace "ina sonki" ba tare da tunanin komai ba nace "kana so na" ya lumshe ido ya bude yace "ke kuma me kika ce?"

Sai na fahimci trap yake neman hada min, na rufe ido na cikin kunya na kasa magana,

Please Login or Register in order to submit comment