Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "ki fada mana, ina son ki Jidda, ke kuma fa?" Na girgiza kai na, yace "ba zaki fada ba?" Na gyada kai, yace "saboda me?" A hankali nace "kunya nake ji" yayi dariya "in baki shawara? Tunda kunya kike ji ki toshe kunnen ki zaki daina ji" na bude idon ina kallon sa cikin rashin fahimta nace "kunne kuma?" Yace "eh, ba 'jin' kunya kike ba? Ai da kunne ake ji ko? Ki toshe kunnen sai ki daina ji" nayi murmushi "ba wani nan, ba haka bane ba" yace "baki yarda ba? Ki gwada ki gani. Ki toshe kunnen sai ki fada shikenan ni kadai zanji abina"

Na makale wuya, "wayo zaka yi min, naki wayon" yayi dariya "to ki fada min dan Allah" nace "ba yau ba" yace "sai yaushe?" Na juya idona Nace "sai nayi shawara" yayi ajjiyar zuciya yace "duk jan ajin ne haka? Naji na dauka, duk sanda kika zama ready my ears my heart and my every other thing will be ready"

Nayi shiru ban ce komai ba, shima yayi shiru amma ina jin idonsa a kaina sai dai ni na kasa dago kai duk da zuciya ta tana son hakan. Zuwa can naji yace "kafarki tana da kyau Jidda" nayi sauri na kalli kafar da take a ajjiye a gabansa, tsirarar ta babu ko safa balle takalmi, nayi saurin dauke ta na mayar kan kujerar da nake zaune tare da lullube ta da hijab din jiki na.

Yayi dariya "gabaki dayan ki kina da kyau, komai naki mai kyau ne kuma ina son komai naki sosai, yadda kike magana, yadda kike tafiya, yadda kike murmushi da yadda kika yi wannan zaman komai burgeni yake yi, komai yayi min yadda nake so. Ina son ki sosai Jidda, ina jinki a zuciyata irin yadda ban taba jin kowacce mace ba, saboda ban taba ganin irin ki ba and I have seen a lot, have been in a couple of relatonships even, amma tun daga lokacin dana dora idona akanki nasan cewa this is it, kamar irin feeling din da mutum yake ji a lokacin da yazo gida bayan yayi doguwar tafiya"

"A dan lokacin dana sanki Jidda sai nake jin ki a raina kamar ba yanzu ne na sanki ba, kamar dama can muna tare, kamar you have been there with me every step of my life kawai dai bana ganin ki ne, kamar ke ce other side of me din da nake missing, sai yanzu dana ganki sannan na zama complete"

"Auren ki nake so inyi Jidda, that's idan kin amince kuma idan su Abba da Umma sun yarje min. Tun ganin ki na farko na yanke hakan a zuciyata duk da ban san halayyar ki ba a lokacin, kuma a ganin da nayi miki guda uku bayan nan na fara fahimtar wasu daga cikin halayyar ki kuma suma duk sunyi min. Amma na sani cewa ke yarinya ce, yanzu kika gama secondary school kuma bansan lissafin ki da burinki ba. Dan haka dole zan baki lokaci iyakacin yadda kike so ki shirya ki kuma zama ready"

"Daga gobe zuwa nan da shekaru biyar, ni zan jira, duk sanda kike so" na dago ina kallon sa nace "har shekara biyar zaka jira?" Ya dan shafa sumar kansa yace "zan so kar ya kai haka, zanso with all my heart amma sai abinda kike ce, ban sani ba ko kina son ki cigaba da karatu ne kafin aure ko kuma kina so sai kin gama karatun ma gabaki daya kafin kiyi auren ko Abba yana so sai kin fi haka girma da wayo kafin yayi miki aure ban san tsarin ba shi yasa nace shekara biyar din, maximum"

Nayi murmushin jin dadi, yadda yake saka damuwata a cikin lissafin sa yana burge ni sosai "ina son yin karatu gaskiya, ko ban kammala ba ina son zan fara" "angama" yace, "inyi lissafin shekara biyu kenan, kamar level two kenan ko?" Nayi murmushi bance komai ba. Yace "kinyi jamb ne?" Na girgiza kai na, na tuno lokacin da aka yi jamb iyaye suka yi ta zuwa daukan yayansu daga makaranta suna kaisu gida suyi kwana biyu suyi jamb, a ciki har da Mufida, ni kuwa dama ko saka rai banyi ba kuma ko mai kama da Abba ban gani ba.

Ya shafa fuska, "ya salam, sai wata shekarar kenan. Amma wanne course kike so ki karanta" na danyi tunani "ni ban san me zan karanta ba" ya bude baki cikin mamaki "kin gama secondary school baki san me zakiyi a jami'a ba?" Na danji kunyar abin sai nace "uhmm, na dai ji ranar nan a school Abba yana maganar nursing" yace "okay, na fahimta, abinda yasa bai dauko ki kinyi jamb din ba kenan. Amma Allah yasa shi ma bamu makara ba, dan form dinsu da wuri yake karewa"

Ban ce komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing ya saka a kunne "kai ya? Ya garin? Kana can kana jin dadin ka ko?" Yayi dariya, dariyar sa tana kara masa kyau kuma tana yi min kyau sosai, ya cigaba "ka shiga daga ciki ka bar ni da shafa kai. Ya maganar daliban ku ne? Form nake so dan Allah. Kai haba? Gaskiya pull some strings ka samo min. Guda daya kawai nake so but it is very important, kayi min wannan kokarin and I will forever be grateful. Okay. Thanks. Bye bye"

Ya ajiye wayar yace "har anyi an gama, next zuwa zan taho miki da form din school of nursing, sai ki kaiwa abba mu ji abinda zai ce akai"

Naji wani irin dadi a raina, dadin da ba zan iya misalta shi ba irin wanda ban taba jin irinsa ba, kuma wannan abin da Umar yayi min zan iya cewa yana daya daga cikin abubuwan da ba zan taba manta wa dashi ba, daya daga cikin abinda har abada zan zama forever grateful for.

Na fara kokarin yi masa godiya sai ya dakatar dani, shi a ganinsa it was nothing, ni kuma a gurina it was everything.
A kokarin sa na ganin banyi masa godiya ba sai ya fara dauko min labarin brief tarihin sa.

"Sunana Umar Muhammad Gidado Fata, kamar yadda nasan kin sani. Asalina bafulatani ne ta bangaren uwa da uba gabaki daya, mahaifina dan kasuwa ne da yake safarar fatu daga Nigeria zuwa kasashen ketare, mu bakwai ne a gidan mu, Yaya Mubaraka sai ni, sai Muhibbat, sai Muhsina, sai Mufida sannan twins din aunty Aarif da Arfat. An haife ni a garin Lagos, a can kuma muka yi karatu ni da Yaya Mubaraka tun daga primary har secondary, amma farkon shigar mu secondary school ne family suka dawo kano saboda lokacin kannena mata sun fara girma kuma iyayen mu suna tsoron yi musu tarbiyya a can, sai suka taho dasu nan ni kuma aka barni a can tare da Baba, su kuma matan gidan sai suke shifting na wata ɗai ɗai a tsakanin su"

Na fahimci bayanin sa sosai, amma sai na samu kaina da tambayar kaina "shin akwai banbanci a tsakanin tarbiyyar yaya maza da kuma mata? Shin duk abinda yake ba dai dai ba a gurin mace yana chanja suna in ya koma gurin namiji? Me yasa iyayen mu suke ware tarbiyyar maza da ta mata? Me yasa ake takurawa mata da tsoron kar su lalace amma kuma sai a sakarwa maza? Me yasa?

A cikin tunani na naji yana cewa "bayan na gama secondary ne nima na dawo Kano, anan buk nayi mbbs sannan naje India inda nayi specialising a bangaren gynecology. A yanzu shekara ta daya da dawowa kuma ina aiki a AKTH, ina kuma zuwa asibitin Murtala sometimes, sannan akwai wani private clinic na friend dina da nake zuwa shima, mostly weekends. I am twenty eight years old, and very ready for marriage but sai matata ta shirya tukunna"

Briefly nima na dan bashi nawa labarin da kuma siblings dina, sannan nayi masa tayin abincin da ya riga ni zuwa gurin "baka ci abinci ba fa, Umma ce da kanta ta zuba maka tace a kawo maka" ya juya yana kallon tray din yace "dole in ci abinci kuwa ko dan in samu albarkar Umma ta" nayi murmushi ina jin dadin yadda komai nawa yake mayar dashi nasa. "Ki zo ki zuba min mana to.....ko baki san haka mata take yiwa mijinta ba?" Na danji kunya amma na sauko na dauko tray din na dawo dashi kusa dashi sannan na zuba masa tuwon leda daya na zuba masa miya a gefe na tabbatar na zuba masa nama a cikin miyar sannan na ajiye masa a gabansa tare da plate din da aka sako pure water guda uku.

Ya dauki chokalin ya fara chi, loma daya sai ya dago yana kallona "wannan miyar tayi dadi da yawa, ban sani ba kuma ko hakan yana da alaka da hannun daya zuba min?"

Kafin na bashi amsa aka bude kofar aka shigo, yaya Tahir, ya kalle ni sannan ya kalli Umar wanda ya cigaba da cin abincin sa hankali kwance. "Sannu da zuwa yayana" na fada ina jin kunyar sa, yace "yauwa jiddo, sai kuma ya mayar da hankalinsa kan Umar, na kalli Umar nace "ga yaya Tahir nan" sai ya ajiye cokalin hannunsa ya mike tsaye ya mika wa Tahir hannu "sannu da zuwa yayana" ya fada yana kwaikwayon yadda nake magana ta.

Duk suka yi dariya sai kuma suka gaisa, abin mamaki yaya Tahir din da ba mai yawan magana ba sai gashi har da zama suna hirar ball saboda shirt din jikin yaya Tahir akwai hoton dan ball a jiki, ni bam ma san ko waye ba amma dai na fahimci hoton nasa ne ya kawo hirar, suna hirar har Umar ya cinye tuwon sa sannan Tahir ya shiga gida, nayi masa tayin in kara masa sai yace dama rowa ce ta saka na zuba masa guda daya kawai "duk girman nan nawa ace malmala daya kawai za'a bani?"

Naji kunya, "to ai bansan zaka ci ba. Yanzu na sani, in ka dawo guda uku zan saka maka" ya mike yana cewa "to yaushe zan dawo?" Na daga kafada "ko yaushe ma, ni ina gida babu inda nake zuwa" yace "okay gobe in na fita office zan karbo miki form din ki. In an samu goben to a goben zan kawo miki da yamma saboda da daddare ina da wani aiki da zanyi asibiti, in kuma ba'a samu gobe ba sai jibi zan dawo" na gyada kai amma ina jin kamar jibi tayi min nisa, dan a yanzu ma bana son tafiyar da zaiyi dan dai ba zan iya ce masa ya zauna bane ba.

Tare muka fita na raka shi har gaban motarsa, cikin tsokana yace "ko in sace ki ne mu tafi gida na? Kinga babu kowa a layin nan babu wanda yake ganin mu" sai na ja da baya duk da nasan wasa yake ina murmushi, yayi dariya, "wata rana anan za'a zo da motoci a daukar min ke zuwa gidana" sai na juya da sauri na koma ciki, amma sai na kasa shiga na labe a corridor ina leken sa sai da ya shiga mota ya bar layin sannan na shiga ciki.


*Kar ku ce ban gaya muku ba, duk wadda bata sayi littafin nan ba tabbas ta bar dadi*

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only



*Episode Seven: The Ladies' Doctor*

Kamar yadda yayi alƙawari haka ya dawo washegari da yamma ya kawo min form din, sai dai cikin sauri yazo ina karba ya juya ko godiya bai tsaya nayi masa ba. Na shiga gida da takardar a hannuna jikina a sanyaye dan bansan abinda zai biyo baya ba. A cikin daki na samu Umma tana sorting kayan da aka kawo daga gidan wanki, na zauna a bakin gado tare da mika mata takardar. Fuskar ta da alamar tambaya ta karba tana dubawa tare da tambayar "takardar menene?"

Nayi shiru ban amsa ba sai da ta karanta heading din sannan tace "wannan ai kamar form ne na school of nursing" na gyada kai "eh Umma, Umar ne muka yi magana da shi nace ina son nursing sai kawai ya siyo ya kawo min, kuma yace in cike kafin ya dawo zai karba" ta fara girgiza kanta "kinsan babanku ba zai yarda ba, babanku ba zai bari ba, me yasa kika karba?" Naji hawaye ya taho min,

"Umma kawai na gaya mishi ina son karatu ne, kawai na gaya mishi ina son nursing ne, shine ya siyo min. Umma yanzu in ban cike ba in yazo karba me zance masa kuma?" Ta ajiye takardar tare da cigaba da jera kayan da take yi amma daga ganin fuskarta kasan a cikin tunani take, sai ta juyo tana kallo na sannan tace "idan baban ku ya dawo in an jima, in yana zaune shi kadai kije ki same shi ki kai masa takardar ki gaya masa yadda kuka yi da Umar din, sai kiji abinda zai ce, in Allah ya dora mu a kansa sai ki ga ya bari tunda naga kamar yana son Umar din, in kuma bai bari ba sai ki hakura ki gaya wa Umar din gaskiya ba'a barin ku kuyi karatu a gida sai in kunyi aure, in yaso in da gaske yake maganar auren da kuma maganar karatun sai ya bari in kinje gidan sa sai ya saka ki a can".

Na share hawayena tare da gyada kaina, already har na fara karanto adduoin da zaku dora ni akan Abba dan ban san yadda zanyi wa Umar bayanin bama karatu sai a gidan miji ba, it will sound like ina gaya masa aure za'a yi min yayi gaggawar fitowa, ni kuma pride dina bazai barni in fadi haka ba.

Ina daki naji shigowar Abba bayan Sallar magrib, ina ji kuma Hajiya ta hau saman ta kai masa abinci, amma nasan zai sauko yaje masallacin isha itama kuma zata sauko kuma in ya koma sama zai ji labarai ita kuma zata yi kallo a kasa ba zata koma ba kuma sai goma da rabi zuwa sha daya. Wannan lokacin shine target dina.

Sama sama naci abinci, Farhan kuma tana waje tana zance da Sulaiman, ina jin Abba ya dawo ya koma sama sannan naji ya kunna radio, na tashi na shiga daki na dauko form din na saka hijab dina na fita, na jima a tsaye ina karanto adduoi sannan na hau. Yana baranda yana kwance akan karamar katifar da ake shimfida masa anan musamman idan babu nepa, nayi sallama ya amsa sannan na durkusa daga dan nesa da shi kadan.

Ya rage radion sa kadan sannan yace "Hauwa'u? Ya akayi?" Na fara inina "Abba dama.......uhm dama zuwa nayi.....uhm takarda ce dama.....? Ya mike zaune "ki gaya min abinda kike so ki fada, ko kuma ki tashi ki koma in kin shirya sai ki dawo. Wacce takarda kike magana akai?" Nayi sauri na mika masa Form din hannuna inajin hawaye already yana tahowa, na tsani wannan saurin kukan nawa amma hali na ne a jikin rai na yake.

Ya karba yana haska touchlight dinsa a kai, nayi saurin cewa "Umar ne ya kawo min dazu, nima ban san zai kawo ba kawai dai nace masa naji kace kana so inyi nursing shine ya kawo min form" ya dago ya kalle ni sannan ya mayar da kansa ya na karanta takardar, jin yayi shiru kuma bai wurgo min takardar ba ya saka na samu courage din cigaba. "Shine na kawo maka dama in gaya maka, sai in ka yarda kuma kace in cike sannan sai in cike, in kuma kace a'a sai in mayar masa" ya ajiye takardar yace "wannan takardar wahalar samu ne da ita, ya akayi ya samu cikin sauki?"

Nace "akwai abokin sa a gurin, kuma shima kaga kusan duk harkar su ce" ya sake yin shiru yayin da zuciya ta take bugawa. Sai kuma ya gyara zama yace "naga kamar da gaske yake, tunda har sai daya bi ta gurin aboki na sannan yazo gare ni. In har aurenki zai yi da gaske to zabin sa ne kiyi karatu ko a'a, amma ni inaso kiyi din, sai dai nafi son kiyi a gidan mijinki" ya miko min takardar "ki je ki cike ki bashi, sannan in har yayi kokari ya samo miki admission din to ki karba, amma duk sanda nayi niyyar aurar dake kuma aka ce masa ya fito yaki sannan wanda yazo da gaske zai aure ki yace baya so to zaki ajiye karatun duk da ina so kuma kema kina so amma aure yafiye miki komai".

Tunda kunne na ya jiye min cewa ya amince sai ya toshe saboda murna, sauran sharadin ma duk ban ji su ba na fara zuba godiya cikin murna sannan na karbi takardar na sauko da sauri ina hada stairs bibbiyu, ina saukowa Farhan tana shigowa ta dawo daga zance, na rungume ta ina tsalle, Umma da take dakin ta take jiran saukowa ta ta fito da sauri, tana gani na tasan nayi nasara sai ta fara tayani murna "alhamdulillah, Allah na gode maka" Farhan ta rike ni "ke lafiya?" Na dan tsaya da murna ta nace "Farhan, Abba ya amince za'a nema min admission a school of nursing"

Ta karbi takardar da sauri "what?" Nace "da gaske wallahi, Umar ne ya siyo min" Umma ta karba a hannun ta "kawo nan kar ku yaga" Farhan ta mika mata sannan ta fara tayani rawar da nake yi muna zagaye tsakar gida, Hajiya ta fito hannunta rike da charbi "menene naji ana cewa? Hayaniyar menene kuke yi haka?" Farhan tace "Hajiya kinga Jidda saurayinta ya samo mata makarantar karatun nursing, kuma Abba ya barta zata yi"

Sai Hajiya ta saki charbin hannun ta tana karasa fitowa daga dakin ta zuwa kan baranda. "Menene? Karatu? A gidan nan? To wallahi ba'a isa ba, chafdi, wato ni yayana an tauye su an hana su karatu sai da abin yazo kan ƴaƴan shafaffiya da mai sannan za'a bari ayi? To wallahi yadda suma ba suyi ba itama ba zata yi ba. Uban kuturu ma yayi kadan"

Umma wadda kamar jira take yi tayi farat ta bayar da amsa "yana sama, wanda ya bari ayi din yana sama sai kije ki gaya masa uban kuturu ma yayi kadan" Hajiya tace "ai yana jina daga nan ma, ba zai yiwu ba wallahi, na gaji da rashin adalcin da ake nuna min a gidan nan ni da yayana wallahi. In kuwa za'a bar Jidda tayi karatu to kuwa dole ne a samo wa Farhan itama su tafi tare"

Sai muka ja da baya ni da Farhan muna kallon su, dama haka muke yi kullum in suna maganganu irin wadannan kuma ko sun gama ba zamu mayar da baasi a tsakanin mu ba, Abba ya leko ta saman sa yace "nine mai gidan kuma ni nace tayi, idan akwai wanda zai hana yazo ya hana, itama Farhan in wanda zai aureta ya amince tayi to zata yi, amma ni ba zan nema mata ba kamar yadda itama Jidda bani na nema mata ba" daga haka ya koma, muna jinsa ya shige dakinsa ya turo kofa.

Ni dai wannan bai hana min farin ciki na ba. Da safe kuwa da yaya Tahir ya shigo na saka shi a gaba sai da ya taya ni muka cike form din tare, bani da passport photograph ma amma a ranar ya kai ni akayi min two minutes nazo nayi attaching. Da dare da aka zo kirana sai naji dadi na dauko takarda ta na fara shiri, sai da aka ce Musa ne sannan kuma raina ya baci na ajiye takardar na lallaba zuwa soro nace da yaron yaje yace bana nan, na dan jima kadan a gurin sannan na koma nace da Umma har ya tafi wai sauri yake yi.

Umar din da nake jira kuma vai zo ba a ranar sai washegari da yamma sannan aka sake aikowa ana kirana amma this time around ma sai aka kuma cewa inji Musa. Na maze nayi kamar banji ba, niyya ta yau ma inki fita, amma Umma ta matsa min sai naje "babu kyau wulakanta mutum. Ki je ko gaisawa ne kuyi a hankali Allah zai raba ku lafiya. In kuma shine mijinki babu yadda zaki yi" sai naji raina ya kara baci da maganar ta ta karshe duk da nasan cewa gaskiya ne. Amma ina rokon Allah kar ya kaddara min auren wanda bana so, sai dai abinda ban sani ba a lokacin shine wata kaddarar tafi wata tashin hankali.

Ban ma bude masa sitting room ba dan kar ma ya zauna balle yayi tunanin yi min hira, a tsaye na gaishe shi ya amsa yana kallon kofar sitting room din amma na dauke kaina nayi kamar bansan me yake yi ba. "Gani ance kana kirana" ya dan yi jim sannan yace "kin san dalilin kiran naki ai ko?"

Nayi shiru. "Jidda me yasa kike rufe min duk wata kofa da zata sada ni da zuciyar ki ne? Me yasa ba zaki bani dama ba?" Na dan kalle shi "to ba gani na fito ba? In bana so in baka dama ai ba zan fito ba ma ko?" Yace "Kamar yadda baki fito ba ranar nan? Ki ka ce ace ba kya nan?" Nayi shiru ina jin nauyin sa, ashe yasan ina gida a lokacin.

Ya cigaba "yanzu ma jikina yana bani cewa matsa miki aka yi kika fito, dan gashi ko gurin zama kin ƙi ki bani" a raina nace wannan mutumin ko dai dan duba ne? Allah dai ya shiga tsakanin nagari da mugu. Sai nace "ina wani abu ne a cikin gida shi yasa, bana so in dade sosai" ya danyi yar hirarsa shi kadai wadda in za'a yanka ni bansan me yake cewa ba, a karshe ya hakura yayi min sallama ya tafi.

Washegari Umar ya dawo. Wannan karon bayan magrib yazo kuma tun a aiken farko yace ace inji Umar, nayi kokari sosai wajen boye excitement dina, Amira harda riga ni shiryawa wai zata je ta gaishe shi sai da Umma ta hana ta "bana son kwadayi, dan ya baki kudi ranar nan shine zaki koma masa?" Ta hakura ta zauna amma ranta bai so hakan ba. Ni kuma na shirya na saka hijab dina na dauki takarda ta na fita.

Sai da na bude kofar sitting room din sannan na leka waje, yana tsaye a gaban motar sa idonsa yana kallon kofar da yake saka ran zan fito. Muna hada ido yayi min murmushin da naji shi a ko'ina na jikina, ban san sanda na mayar masa ba sannan ba tare da nace komai ba na koma ciki shi kuma ya biyo ni.

Ganin yana zama a kasa ya saka yau na riga shi zama a kasan. Shima ya zauna sannan na gaishe shi. "Ya mutan gida? Ina Amira" "tana ciki" na amsa "ina Farhan? Ita ba zata zo mu gaisa ba?" Nace "zata zo mana, ba ka neme ta bane ba" yace "ita ma Amira ai ban neme taba, dan tana da kirki ne ya saka tazo" nace "wato Farhan bata da kirki kenan ko? To sai na gaya mata" ya daga hannu "kar ki hada ni da ita, dan naga alama a gurinta ne zan kafa gwamnati na. Nayi murmushi "tabbas. Dan ita ce babbar aminiya ta" yace "har Mufida? Sai na gaya mata"

Na danyi dariya "kar ka hada ni da ita, dan naga alama nima ta gurinta zan kafa tawa gwamnatin" yayi dariya sosai sannan yace "tabbas, dan kaf sisters dina nafi ji da ita, but she is a little bit stubborn, abinda na fahimci shine ya karfafa kawancen ku" na rike baki "ni yanzu stubborn ce?" Yace "sosai ma, gashi har yanzu kin ki cewa I love you Umar" na jawo hijab zan rufe fuska yace "na daina tsokanar ki, dan Allah kar ki hana min kallon kyakykyawar fuskar ki mana, dan Allah" ya fada murya kasa kasa yana

Please Login or Register in order to submit comment