Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko kuma su fitsare su daina jin magana su daina bin umarnin sa suyi tunanin dai dai suke da maza suma.

Sai dai deep inside him yana son suyi karatun su mori ilimin su, wannan ya saka duk wanda zai aura wa yarsa yana yin yarjejeniya da su cewa zasu barsu suyi karatu bayan aure, har alkawari yake yi cewa shi zai dauki nauyin kudin karatun burinsa dai kawai a bari din, amma cikin ikon Allah kaf surukan nasa babu wanda ya cika masa wannan burin, daga an shiga sai ciki, sai reno sai wani cikin, sai kuma ace an tara yaya karatu ba zai yiwu ba. Aunty Hudallah ce kawai tayi diploma a Legal, shikenan kuma bata kara komai ba.

Abba yakan yi mita akan haka wasu lokutan, amma bai taba samun surukan nasa yayi musu mitar ko kuma ya tilasta musu suyi abinda yake so ba, saboda ya riga ya saka a ransa cewa duk wanda ya auri yarsa kuma ya rike ta bai sako masa ita ba to ba karamin rufa masa asiri yayi ba.

"Dakin miji shine babban rufin asirin mace. Duk abinda kuke so na daga kudi ko wani abu ku zo ku same ni in dai ina da shi zanyi muku, amma duk wata matsala data shafi mazajen ku ku barta a cikin ku, bana son ji, ko iyayen ku mata kar ku gaya wa sirrin auren ku. Ku je ku sasanta a tsakanin ku ba tare da kowa yaji ba, wannan shine halin mace ta gari".

Wannan ita ce nasihar da mukan ji yana yiwa yayyen mu mata idan sunzo gaishe shi. Wani lokacin idan yana cikin fada yakan ce

"Duk wadda taki bin mijinta a cikin ku babu ni babu ita. Duk wadda ta yi yaji wai dan tana ganin mijinta yayi mata wani abu na rashin kyautawa to ta tafi gidan wani ba gida na ba. Duk wadda ta kashe aurenta to ta nemi wani uban bani ba. Duk wadda ta jawo min magana ta zubar min da mutunci Allah ya isa tsakani na da ita"

Wannan maganar, hatta mu da bamu yi aure ba a lokacin, mun rike ta tamkar karatu a kan mu....

Har yanzu ina iya tuno yarintar mu da irin cin zalina da yaya Muslim ya ringa yi har sai da ya kasance ko tsakar gida bana iya fitowa dan inya kama gashina ya murde sai nayi kamar zanyi fitsari a wando, sai da yaya Tahir ya ritsa shi yayi masa duka sannan na samu sa'ida amma duk da haka in dai baya kusa in ya ganni sai ya dake ni, daga nan kuma sai rigima ta balle tsakanin Umma da Hajiya.

In short, abinda nake so in nuna muku shine gidan mu babu zaman lafiya, babu soyayya a tsakanin mu da yanuwan mu, akwai yan ubanci sosai a tsakanin mu da yan uwan mu.

But there is one exception.......

Ni da Farhan tamkar tagwaye ne, babu yadda iyayen mu mata basuyi ba dan su raba tsakanin mu tun muna kanana amma basu samu nasara ba, Farhan ce babbar kawata, ita ce kuma babbar aminiya ta tun kafin in san menene kalmar aminiya, na dai san duk sanda muka hadu sai ma bata labarin duk abinda ya faru a lokacin da bama tare ita ma kuma sai ta bani. Kasancewar kwana bakwai ne kawai tsakani na da ita ya saka ajin mu daya aboko da islamiyya, wannan yasa dole iyayen mu mata suka barmu muke tafiya tare, in mun dawo gida ma tare muke karatu, ina kaunar Farhan sosai dan har cikin zuciyata bana jin suna da banbanci ita da Amira.

Bayan kammala primary school din mu ne sai Farhan taci jarabawar da muka rubuta ta day science ta kano, ni kuma na fadi, lamarin da har yau Umma ta kan alakanta shi da kasancewar kanin Hajiya a cikin masu ruwa da tsaki a gurin marking jarabawar "ita ta saka aka kayar dake, babu wata faduwa da kika yi, bata so ki je ne" wannan rikicin ya saka Abba ya yi ta cuku cuku har ya samo min admission a GSSS Taura, ta hanyar principal din makarantar wadda suke da dangantaka a matsayin su na masu aiki iri daya.

Makarantar daga senior ta fara,amma sai akayi sa'a a shekarar suka dauki jenior section da niyyar zasu raine su, naci sa'a na fada cikin wannan tsarin. Abba ya so ta bashi space din mutum biyu sai ya hada ni ni da Farhan amma bai samu ba, dole ya hakura aka kaini ni kadai aka bar Farhan a Day Science.

Zan iya tunawa da ranar da aka kaini ina ta kukan rabuwa da gida da kuma rabuwa da Farhan sai aka kawo wata itama daga Kano itama tana kuka, aka hada mu seat daya malamar da take ajin tace mun zama kawaye tunda muna kuka. Sai kuwa gashi kawancen namu ya dore, kusan halayyar mu daya da ita da kankantar jiki, da yanayin mu. Sunan ta Halima Usmam Kollere, bafulatana ce, nima kuma da yake mutane da yawa basa gane kabila ta sai ake min kallon fulani dan haka kawancen mu ya dace sosai.

Babban abinda nafi tunowa a tare da Halima shine yayanta kuma saurayinta Sadauki. I doubt in ta ma san soyayya a lokacin, dan ni dai ban sani ba, abinda kawai na sani shine duk sanda kuka zauna sai ta baku labarin Sadauki, kalma biyu uku in tayi to ta hudun sunan Sadauki ce. Babu wanda ya san Halima ba tare da yasan sadaukin ta ba. I can remember in yazo mata visiting har satar jiki muke yi muje muyi ta leken su muna dariya.

Sai dai.......muna gama jss munyi hutu mun dawo Halima bata dawo ba, muka yi ta cigiyar ta sai wani malami da yake abokin baban ta ya gaya mana babanta ya rasu sannan kuma anyi mata aure, wannan labarin ya girgiza mu sosai, mun kuma yi takaicin rabuwa da ita da kuma alhinin mutuwar mahaifin ta, sai kuma muka yi mata murnar auren saurayin ta da take mutuwar so. Sadauki.......

Bayan munyi hutu har gidan su naje, saboda na taba karbar address dinta sanda muna tare, amma sai na tarar da gidan a rufe, na tambaya a makota aka gaya min mai gidan ya rasu su kuma sun tashi daga gidan. Wannan shine rabuwata da *Diyam*

Bayan mun rabu da Halima, bayan mun shiga ss1 ne aka kawo Mufida, ita tayi replacing Halima a gurina. Zainab Muhammad Gidado ƴa ce a gurin attajiri Alhaji Muhammad Gidado Fata, mutumin daya shahara ya kuma yi suna akan sana'ar sa ta siyan fata, sarrafa ta tare da fitar da ita zuwa kasashen waje da siyar da ita a can. Sana'ar sa ta karbe shi kuma yayi arziki da ita.

Yayansa Bakwai, Yaya Mubaraka itace babba, sai Umar Faruq, sai Muhibbat, Muhsina, sannan Mufida auta a gurin mahaifiyarsu Hajiya Maimunatu da suke kira da Mama, sai kuma twins din amaryar Alhaji Afnan da Affan.

Umar Faruq kyakykyawan saurayi ne da yake ji da kansa a fannin kudi, ilimi, gata, asali, background mai kyau da kuma uwa uba kyau. Bafulatani ne shi ta bangaren uwa da uba baki daya, kuma matsayin da yake dashi na babban da na Alhaji Mahmud ya saka iyayen suka dage wajen ganin sun bashi ilimi mai kyau har xuwa matsayin cikakken likita, wanda ya samu a cikin wannan shekarar, sannan kuma suka dora shi akan son kannensa tare da fatan ko babu ransu shi din zai zama mai rike yanuwansa ya zame musu uwa da uba.

Sun kuma yi nasara, dan Umar ya samu duk abinda suke so ya samu, sannan kuma yana tsananin son yanuwan nasa kamar yadda suka yi fata. Dan tun yanzu da yake a matsayin matashi kuma suke still da ransu da lafiyar su a duniya ya riga ya karbe kuma ya tsaya akan dukkan al'amuran da suka shafi yanuwan sa, dasu kansu ma, wannan abin shi ne ya sake polishing tauraruwar sa a idon mahaifan sa tare da dukkan sauran wadanda suka san shi.

Ba iyayen Umar ba hatta yan'uwa, makota, da abokan arziki suna yabawa da halayyar sa musamman yadda yake faran faran da mutane da kuma yadda yake girmama manya. Sukan yiwa ƴaƴansu fada da cewa "me yasa ba zaka zama kamar Umar Fata ba? Yaron kirki mai ganin girman mutane, shi ko yar sigarin nan ma ta matasa shi baya sha"

Abu daya ya rage wa Umar yazama perfect son, shine aure.....


******************************************


Ina ta tunanin mafita a kan sabuwar rayuwa da zan fuskanta a haka har muka je gida

Gidan mu yana nan a unguwar gandun albasa dake garin Kano. Gaban gidan railer ne doguwa tun daga farkon gidan har karshe. A cikin ta ne Abba yake ajiye motar sa tunda bashi da garage. Idan ka shiga cikin ta akwai kofa biyu, daya double door ce wadda zata shiga da kai cikin sitting room din Abba, a nan ne yake zama da bakin sa anan ne kuma duk wani bako namiji yake sauka, a cikin sitting room din akwai dakuna guda biyu da kuma toilet, a dakunan samarin gidan suke zaune duk da dai yanzu tun bayan bikin yaya Muntari saura su uku, Tahir, Muslim, da Abbah.

Sannan a cikin railer da akwai karamar kofa wadda zata shiga da kai cikin corridor shi kuma zai shiga da kai tsakar gida, tsakar gidan bashi da girma sosai, kana shiga dakuna biyu ne suke facing dinka, ɗakunan Hajiya da Umma, kowacce ciki da falo madaidaita, sai kuma dogon filin da muke cewa ventilation a bayan dakunan nasu inda anan ne muke shanya kayan wankin mu. Kowacce tana da toilet a cikin falon ta.

Sai kuma daki daya daga barin hagu wanda shine dakin yammata, Farhan ce kadai a ciki yanzu sai ni da nake da niyyar zama tare da ita. A barin dama kuma kitchen ne, sai kuma toilet din tsakar gida a kusa da kofar shigowa.

A gaban toilet din benen Abba ne wanda ya hau zuwa saman dakunan su Umma. Shima ciki da falo neda kuma katuwar baranda da yake zama mostly da yamma har zuwa dare, lokacin zafi ma anan yake kwana. Da azumi ma anan yake shan ruwa.......

Da damuwa a raina na shiga gidan mu, sai dai ina shiga ganin ummata ya wanke duk wasu traces na bacin rai da suke cikin rai na, naji zuciyata tayi fari kal, naji cewa kowanne problem ma mai sauki ne ashe in dai har kana da uwa a duniya, ko bata yi maka maganin sa ba ganin ta kawai ya isa ya warkar da dukkan damuwa.

Abinci mai rai da lafiya na tarar an shirya min, shinkafa da miyar kifi da salad kamar yadda nake so, Farhan tayi min dan malele da manja da yaji da tumatir da albasa. Ga kuma sobo mai sanyi an hada min. Sai ma na rasa wanda zanci ina ganin kamar sunyi min yawa amma dana faraci sai na lura ashe akwai yunwa sosai a tare da ni, musamman da Farhan da Amira suka saka hannu sai mukayi ta zurawa muna hira har bamu san mun cinye ba.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*💔 Jidda 💔*

*By*

*Maman Maama*

*Episode Four : Musa*

Bayan mun gama ne naje nayi wanka na chanja kaya zuwa atamfa riga da skirt da dankwali, suna ta yabawa da sabon kitsona ni kuma ina complain din zafi yake min, sai Umma ta ce inje in gaishe da Hajiya sannan in shiga makota duk in gaishe su kafin Abba ya dawo.

A dakin Hajiya na tarar da ita tare da Mammy babbar yar mama Sa'a, lokacin sunyi Junior candy shine tazo zata kwana biyu a gidan.

Na gaishe da Hajiya, ta amsa babu yabo babu fallasa "an gama jarabawa ko? Allah ya bada sa'a. Saura aure kuma ko? Sai dai ke naga kamar har yanzu babu wani tsayayye, to Allah yayi zabin alkhairi"

Farhan da take zaune a kan hannun kujerar da nake kai tace "ameen" tana kallo na da dariya, ni kuma na harare ta cikin wasa. Hajiya ta kalle ta tace "ke kam dai ai na roki baban ku ya bar min ke kiyi makarantar nan dai kema, kuma insha Allahu Allah zai dora ni a kansa tunda dai ke ce auta ai ba zai hana ba, ballantana yadda kike da kokarin nan dan Alhaji Kabiru ya gaya min ana saka ran zaki ci jarabawa sosai".

Farhan tace "insha Allah zan ci Hajiya. Kuyi tayi mana addu'a ni da Jidda mu tafi jami'a tare" Hajiya ta rike baki "Jidda kuma? Ke ma kinsan Jidda aure za'a yi mata musamman yadda tayi girman nan haka. Ita ma umman ta ai zata so taga nata jikokin tunda a kanta zata fara samu, su zo suyi ta danne ta itama" ta karasa tana ture Mammy da ta dora kanta akan cinyarta tana danne danne a yar karamar wayar da take hannunta.

Muka yi dariya gabaki daya, ta mike zaune tana bata rai sannan ta kalle ni sama sama tace "sannu da zuwa. An gama school. Congratulations" "thank you" nima na bata amsa a takaice. In da sabo na saba da rashin kunyar Mammy amma bana taba kulata saboda gudun karin raini a tsakanin mu.

Farhan ta karbe wayar hannun Mammy "marar kunya. Bani inga abinda kike aikatawa a wayar. Haka kawai mu manyan yammata ba'a bamu waya ba sai ke yar ficiciya da ke, wani in ya gani sai ya dauka ubanki wani abu ne a Kano" ta fada tana duba screen din yar karamar wayar data karba daga hannun Mammy. Ina kallon Hajiya tana hararar Farhan a fakaice, dan babu abinda ta tsana irin a fadi aibun wani nata a gaban mu ko wani wanda ya shafe mu, kullum nunawa take yi tamkar yayanta sunfi kowa komai bayan mun san ba haka bane ba.

Dariyar da Farhan tayi ce ta dawo da hankalin mu kanta, ta nuna min wayar "kinga, wai facebook take yi, dan Allah ji wani hoto da ta saka ita a dole yammata ce" na karba ina kallo, taci kwalliya an sha jambaki da uban gilashi, ga maza nan sun dage sai comment suke yi mata "WOW" "wow" "wow" sai kace wata jiniyar motar asibiti. Na rike baki nima ina dariya. Ta taso ta warce wayarta daga hannuna tana kunkuni ta shige cikin daki.

Farhan tace "kar dai ki zage mu, marar kunya, kin san ni yanzu sai in fasa miki baki wallahi, kuma wannan hoton kamar a kunnen uwarki, gwara tasan me kike yi da wayar". Ganin Hajiya har yanzu tana ta harare harare yasa na mike tare da cewa "bara inje in gaishe da Abba naji kamar ya shigo" tace "okay, wannan maganar sai kin tashi mayi" nayi murmushi, tatsuniyar gizo dai bata wuce ta koki, ba zai wuce zancen wani sabon saurayi ba ko something like that. Tun muna yra Farhan ce yar soyayyar cikin mu, kullum zancen ta baya wuce na samari ko aure ko wani abu mai kama da haka.

Ina fita na tsaya ina kallon saman Abba, kofar falon sa a bude take nasan yana ciki amma gabana faduwa kawai yake yi dan ban san da wadda zai tarye ni ba. Haka muke ni da Farhan kullum fargabar zuwa gaishe shi da safe muke yi, in mun tafi a hanya kuwa munyi ta tunani ko akwai wani laifi da mukayi wanda ba'a yi mana fada a kansa ba. In kuwa dama mun san munyi laifi har kirkirar ciwon karya muke yi mu kwanta a daki mu ki zuwa gaishe shi amma har dakin ya kan biyo mu yayi mana fadan ko da kuwa muna karkarwar zazzabi ne.

Nayi bismillah sannan na hau benen a hankali cikin nutsuwa naje kofar falon nayi sallama sannan na saurara, daga can ciki naji ya amsa min. Na daga labule na shiga na ganshi a zaune akan kujera da table a gabansa da takardu a kan table din, da alama aikin makaranta ne ya taho da shi gida. Na dan karasa gabansa kadan na durkusa na gaishe shi. Ya dago kai yana kallona yace "Hauwa'u an dawo gida ko? Ya jarabawar taku?" Na danyi murmushi "alhamdulillah Abba" yace "good, Allah ya bada sa'a. Kuka ya kare ko?" Na sake murmushi bance komai ba sai ya kuma mayar da hankalinsa kan takardun gabansa.

Hakan yasa nayi yunkurin mikewa ina jin dadin ba'a yi min fadan komai ba, sai naji yace "dakata tukuna" gaba na ya fadi amma automatically na koma na zauna ina jiran me zai ce sai ya fara magana.

"To alhamdulillah. Kin kammala secondary school dinki. Allah yayi miki albarka"

Nace "ameen"

Ya cigaba "zan so ace kin cigaba da karatun ki har ki zama wata aba a rayuwa, amma kuma zan so ace kinyi hakan ne a gidan mijinki ba'a gidan nan ba. Saboda haka nayi wa yanuwanki kuma kema haka zanyi miki. Kai ko da ba haka nayi musu ba ke hakan zanyi miki saboda idanuwan mutane sunfi yawa a kanki a kan akan su. Wannan idon na jama'a shine dalilin da yasa ban matsa akan sai na samo miki makarantar day kamar yaruwarki ba, saboda na fahimci cewa tafiyar ki makarantar kwana shi zaifi kwantar min da hankali a kanki,ba ruwa na da tunanin ina kike ko tare da wa kike me kuma yake gaya miki. Abinda yasa nafi damuwa da ke akan yaruwar ki saboda banbancin halitta da yake tsakanin ke da sauran mutanen mu, zaki fi jan hankalin mutane musamman maza saboda suna ganin ki daban da sauran mata."

To yanzu kuma gashi kin gama kin dawo, kin kara komai da zai ja hankali kanki ɗin, amma kuma ina tunanin kin kara hankali. Wannan yasa nake miki wannan maganar. Ba wai ina gaya miki ki fito da miji inyi miki aure ne ba a'a ina gaya miki na baki iznin yin samari, kuma hakan da na fada ba wai yana nufin na baki izni kiyi ta kula ko waye yayi miki magana a hanya ba, duk wanda yayi miki magana cewa yana so ya nemi auren ki to ki turo min shi gurina first in fara ganin sa in san ko shi waye sannan in bashi iznin fara neman ki ko kuma in naga bashi da nagarta in hana shi, kar ki yarda in ganki tare da wani wanda ban san da zamansa ba, kar ki yarda in ganki tare da wanda na hana ki ganin sa. Idan lokacin da nake son yi miki aure yayi zan gaya miki ki fitar a cikin wadanda suke zuwa gurin ki. In kin bi abinda nace zamu dai dai ta in kuma baki bi ba to zamu bata ni da ke"

Na gyada kai da sauri a raina ina lissafin abinda yake nufi da batawar, na dauka ya gama sai kuma naji yace "kinsan yaron nan Musa?" Na daga kai ina kallon sa, sannan nace cikin rashin fahimta "wanne?" Yace "dan gidan Malam Magaji na bakin layin nan" na fahimci wanne Musa yake nufi, yayan kawar mu Sakina, tabbas na san shi ina ganin sa a hanya ko kuma in mun shiga gidan su ni da Farhan mun biya wa Sakina zuwa islamiyya.

Na gyada kai kirjina yana bugawa nace "na san shi Abba" yace "good, yaron kirki ne mai girmama mutane da addini, wani lokacin ma shi yake kiran sallah a masallacin mu idan ladan baya kusa. Satin daya gabata Malam Magaji ya same ni ya gaya min cewa Musa ya aiko shi ya gaya min yana son a bashi iznin neman auren ki"

Na dago kai da sauri ina girgiza kai, yace "ba cewa nayi na bashi ba, duk yayana mata babu wadda nayi wa auren dole kuma kema ba zanyi miki ba, na bashi izni zai ke zuwa wajen ki, idan kun daidaita to shikenan idan kuma baku daidaita ba kuma Allah ya kawo wani nagari sai muyi masa fatan alkhairi"

Nayi ajjiyar zuciya ina jin sanyi a raina, lallai ma wannan musan, ko a fuska bai taba nuna min wani abu ba, babu abinda yake hada mu sai gaisuwa a hanya in mun hadu ko a gidan su, gaisuwar ma wani lokacin Farhan ce take yi ni sai inyi kamar ban gan shi ba.

Daga haka Abba ya sallame ni na taso ina jin wani iri a raina har na fara saukowa daga stairs sai kuma na tsaya ina murmushi ni kadai, tabbas na samu hanyar gane gaskiyar magana akan Umar, in dai har ya kuma dawowa gurina zan gaya masa yaje yaga Abba, in dai ba da gaske yake ba nasan zai gudu, in kuma da gaske yake to shikenan ni na huta da neman wasu samari kuma, dan na riga na gani na yaba kuma na gamsu.

Sai dai kuma da dare bayan mun kammala komai munyi shirin kwanciya sannan na zayyanawa Farhan labarin Umar, yadda muka hadu da yadda nake ji a zuciya ta game da shi, abinda ya gaya min shima da kuma yadda mukayi da Mufida. Sai kuma na bata labarin abinda Abba yace min da shawarar dana yanke akan Umar. "Kinga in ba da gaske yake ba sai yayi tafiyar sa kawai"

Sai kawai naga tayi dariya, na tsaya ina kallon ta dan ni banga abin dariya a cikin magana ta ba, sai da ta gama dariyar ta sannan tace "lallai Jidda kin tabbata yar boarding school wadda bata san abinda yake faruwa a cikin gari ba. Ai in dai dan yaudarar ne kamar yadda kanwarsa uwa daya uba daya ta fada to kuwa zuwa gurin Abba ba zai hana shi yaudarar ki ba. Rikakkun yan yaudara su kan kawo kudin aure ma kuma har zuciyarsu ba da gaske suke ba. Ke dai kawai muyi ta addu'a muna neman zabin Allah tare da neman tsari daga hatsabibai kuma mugayen samari"

Nayi tagumi da hannu daya ina kallon ta, ina jin duk farin ciki na na samun solution yana tafiya. Ta dan baya rai "ke ni har cikin raina ma sai naji bai yi min ba duk da ban ganshi ba. Yadda kike tsara shi sai nake ganin kamar kinyi masa kankanta, irin su manyan yammata suke so wayayyu yan jami'a"

I was so into my problem har na manta da maganar da tun ina makaranta take cewa zata gaya min. Sai da ta tuna min "baki tambaye ni labarin da zan baki ba?" Na juya barin da take ina kallon ta, sai naji kunyar mantawar da nayi, nace "okay, ina ji. Bani labarin new catch din" tayi murmushi mai sautin da ya saka nan take na fahimci cewa ita ma duk a cikin jirgin da nake a nan take ita ma, jirgin soyayya.

"Kinga, sunan sa Sulaiman, lokacin da muna waec shine yake mana invigilation, to shine fa ranar nan mun taso na fito neman mota zan taho gida sai gashi yazo wucewa shine ya dauko ni"

Na bude ido "a motarsa? Baki ji tsoro ba? Da Abba ya gan ku fa?" Tayi murmushi "nima naji tsoro ai, but kawai na daure, kuma dai rabon zamu dai dai ta ne. That was how it started" na dan dake ta kadan ina dariya "to a ina zata yi ending?" Ta juya ido "a inda zaku yi ending ke da Umar din ki" na dauki pillow na na doke ta ita ma ta dauki nata ta rama, muka yi tayi sai da muka gaji dan kanmu sannan muka kwanta muna haki, sai kuma muka cigaba da hira, planning our lives, but Allah shine the greatest of planners duk namu tatsuniya ne.

Kwana na biyar a gida, a cikin kwana biyar din nan Sulaiman yazo, dama already ya samu amincewar Abba, kuma naje mun gaisa da shi ya kuma kwanta min a rai, mutum ne mai faran faran da wasa da dariya.

Malamin makaranta ne shima kamar Abba, sai dai bai kai Abba dadewa a system din ba kuma bai kai Abba matsayi ba. Kuma daga ganinsa ba karami bane ba sai dai yana da karamin jiki kuma yana da kyau dai

Please Login or Register in order to submit comment