Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama jakar sai yazo ya janye hannun jakar daga hannuna. "ba zata dauka ba" ya fada yana kallon Mufida" ta tabe taki ta fara yi masa shagwaba. "Ni baka damu dani ba Yaya Doctor, ni zan dauka ni kadai kenan"

Ya danyi dariya yace "haba sweety kema kinsan kece favorite sister dina duk duniya amma ki duba yanayin jikinki da nata ba daya bane, in ta dauki wannan kayan kafin taje hostel din ku ai ta karya kafa ko hannu" sai naji haushin yadda yayi min kallon karama, duk da nasan Mufida ta fini ki ba amma ni ma ai ba karamar da har za'a yi kwatance dani ba ce ba nace "zan iya fa, dazu ma mun dauki wasu kayan, kullum ai muna daukan kaya" Mufida tace "da daukan ruwa, bucket din penti muke dauka kullum" nace "dazu ma shi muka dauka. Am stronger than I look"

Yayi murmushi "show me" na bude ido "what?" Yace "ƙarfin" na cigaba da kallon sa cikin rashin fahimta sai ya daga hannunsa ya nuna min kwanjin sa, ai kuwa na gani duk da ta cikin riga ne, nayi saurin dauke kaina ina jin tsigar jikina tana tashi, yayi dariya. "Ga nawa, show me yours" Mufida tace "wow, Yaya Doctor tsara kaga nawa nima" ta tattare hijab din ta tayi yadda yayi da hannun sa tare da daddagewa lallai wai sai kwanji ya fito, yayi dariya yana dan dukan hannunta kadan "ji wani kwanji kamar na kadangare" ta turo baki yace "ai kina dashi ma, kawarki ita irin na sauro ne da ita" na bata rai "sauro? Sauro ai bashi dashi" yace "that's exactly what am saying, baki dashi" nace da sauri "ina da shi mana" ya gyara hannunsa tare da jingina da jikin mota yace "then show me"

Muryar Mama muka ji "wai baku tafi kai kayan ba har yanzu?" Mufida ta daga murya, "Mama Yaya Doctor ne ya hana mu dauka" ya bude ido "Mama sharri take yi min" ta murguda masa baki shi kuma yayi mata alamar zai zaneta da hannunsa. Muka kuma yin kokarin dauka sai ya janye jakar yana kallona yace "am serious fa, in dai ina gurin nan ba zaki dauki kayan nan ba. Baku da laborers haka da zasu shigar muku dasu?" Mufida tace "akwai su amma sai an basu kudi" ya zaro kudi a aljihunsa idonsa a kaina ba tare daya kirga ba ya mika mata, tayi saurin karba tana dan tsallen murna sannan ta fara waige waigen neman mai daukan kaya.

Ya rankwafo da kansa yana kallon cikin fuska ta, muka hada ido nayi saurin kallon gefe, sai ya zagaya da fuskar sa ta gefen da nake kallo, muka sake hada ido sai na rufe idona, ya danyi murmushi mai sauti yace, muryarsa can kasa yadda na tabbatar ko da hankalin mufida yana kan mu ba zata ji abinda yace ba "smile, please". na sake rintse idona ina jin muryar sa a jikina tana zuwa har inda banyi tunanin murya tana iya zuwa ba, ina jin yakin da ake yi a tsakanin ƙwaƙwalwa ta da kuma zuciyata, zuciyata which already belongs to him tana son yin obeying din umarninsa, yayinda ƙwaƙwalwa ta take kokarin cigaba da maintening dignity dina. "Smile, ko da dan kadan ne, ko da iyakacin lips dinki ne, ko da bai gama zagaya kyakykyawar fuskar ki ba"

Na sake juya fuskata gefe, zuciyata tana so ta cigaba da zama a wajen tana sauraron muryar sa yayin da ƙwaƙwalwa ta take gayamin "run!" Yace "bude idonki ki kalle ni, ko ba zakiyi murmushi ba ki kalle ni kawai kafin ki tafi, dan Allah" na juya masa bayana sannan na bude ido na naga Mufida tana bawa masu shigar da kaya sako, sannan na kuma jin alamar ana kallona daga side din da yan gidan su suke, na kalli gurin and I saw Mama, idonta a kaina da kuma wani irin yanayi a fuskarta. Daga bayana naji yace "in baki kalle ni kinyi min murmushi ba, zan iya kwana a asibiti a yau"

Ba tare da na sake magana ko na waiwaya na kalle shi ba na bi bayan mai daukar kaya, duk da cewa zuciyata tana kokawa, tana so ta sake kallon cikin idanunsa, Mufida ta biyo bayana da bakaken ledoji biyu a hannunta, ta miko min daya "ai dai wannan ba zaki karye ba in kika dauka ko?" Duk mukayi dariya a tare, duk da ni tawa dariyar bata kai ciki ba, all I wanted a lokacin is to look into his eyes again. Ina jinta tana min hira, bansan ma me take cewa ba har muka danyi nisa kadan sannan kuma ina jin idanuwan sa still a kaina, I can even swear cewa magana yake yi da zuciyarsa, addu'a yake yi in sake waigawa. And I did.

Na dan dakata da takuna, ina jin kamar ba zan iya kara taku daya ba har sai na kalle shi, sannan na juya na kalli inda yake tsaye har yanzu a jikin mota, kuma kamar yadda nayi tsammani, idanuwan sa a kaina. Yayi murmushi sannan ya daga min hannu, and I smiled back and wave back. And then my life begins and ended.


*💔 Jidda 💔*

*By*

*Maman Maama*

*Episode Two : Matters of the Hearts*

Free Episode

Ita zuciya, annabi yace wata tsoka ce a jikin mutum wadda idan ta gyaru to dukkan sauran jiki ya gyaru idan kuma ta baci to dukkan sassan jiki ya baci kenan. Idan muka yi amfani da wannan maganar zamu iya nada zuciya a matsayin sarauniyar gabaki dayan jikin mutum, wadda kuma a lokuta da dama tana gudanar da mulkinta ne bisa son kai da son zuciya (lol) musamman in aka samu cewa shi mamallakin zuciyar baya iya juyata ya sakar mata ragama tana yin abinda ta ke so, to ina kuma ga ni? Ni da zuciyar tawa gabaki daya na riga na danka wa wanda bai ma nemi in bashi din ba, bai ma kuma san cewa na bashi din ba.

Tun ranar dana fara ganin sa, ranar visiting day, ban kuma jin cewa na dawo dai dai Jidda ta yadda nake kafin idanuna su shiga cikin nasa ba. Sau da yawa nakan samu kaina ido biyu bayan karfe biyun dare ta wuce, kuma ba wai akan sallaya ina sallah ba ba kuma wai da littafi a gaba na ina karatun jarabawar da aka kawo ni makaranta dan in karanta ba, a'a, na kan samu kaina ne a zaune akan gado na na jingina baya na da pillow staring into nothing and smiling.

In kuma nayi yaki da zuciyar tawa na samu na dauki littafi na kunna fitila da niyyar karatu to bayan wasu mintuna kadan zan iya samun kaina ina zana abinda zan iya tunawa na daga fuskarsa a bayan littafin da ya kamata ace karantawa nake yi. Idan kuwa class muka tafi da niyyar sauraron extra lessons din da coppers din makarantar sukan shirya mana kusan kullum dan shirin taryar jarabawar waec din da take gaban mu, to na kan samu kaina da rafka tagumi da hannu bibbiyu, idanuna tsaf a kan malamin, faffadan murmushi akan fuskata amma kuma sam babu abinda nake ji ko gani a abinda yake yi kuma yake fada, sau da yawa fuskar yayan kawata na kan gani a fuskar mai koya mana karatun, da kuma muryarsa yana cewa "smile, please".

Those were the good days....

On the bad days kuma ji nakan yi duniya tayi min zafi, in ji na tsani kaina for feeling what I was feeling, inyi kokarin tursasawa kaina daina jin abinda nake ji din amma sai inji kamar kara hura wutar abin nake yi a zuciyata. Nakan zauna inyi kuka a bayan idon kowa. Dama ni kuka babban abokina ne. Babu abinda nake so illa in sake ganin sa, ko in sake jin muryar sa, ko kuma at least in ji ko da labarin sa ne, ko da hirar sa ne ayi min. Sai dai kuma duk da halin da zuciya ta take ciki ba zan iya karya kambu na na yarinyar da tafi duk sauran yammata aji a set din mu ba, ba zan iya gayawa Mufida feelings dina a kan yayanta ba. Wannan zub da class ne right?

Wannan tunanin ya sa na tafi gurinta da niyyar in bugi cikinta ko zam samu abinda nake so, sai dai kuma matsalar daya ita ce tun ranar da na ganshi din sai ya zamanto tamkar anyi min chanjin babbar kawa ta Mufida ne da wata mai kama da ita amma ba mai halinta ba. Mufida yarinya ce mai shegen surutu, fadi ba'a tambaye ka ba, da son iyawa. Yana daya daga cikin abinda take so shine ta tara mutane tayi ta basu labarin gidan su da yan gidan su, kusan kaf set din mu babu wanda bai san yan gidan su Mufida ba, babu wanda bai san Yaya Doctor ba, amma tun ranar da yazo din sai ya zamana kamar ta saka sealtape ta like bakinta.

Na jawo kujera ta kusa da tata, nayi gyaran murya, ta dago daga karatun da take yi tayi min murmushi, nace "na gaji da karatu wallahi, kaina ya toshe" ta dafa goshinta tace "same here, kawai yi nake yi kar kuce bana yi" ta karashe maganar tana dariya. Nace "ni kaina ma ciwo yake yi" tace "ke ce fa health prefect, nasan ba zaki rasa magani a jakarki ba" nace "haka ne. Daga naji ciwo nake shan abina" na danyi shiru sai kuma nace "kuma a gida ai kunji dadin ku, gaku da Dr a gida, daga kun fara ciwo ba sai kunje asibiti ba sai kawai ya duba ku" ta dan yamutsa fuska "eh fa. Haka ne" Sai ta ja kujerar ta baya ta mike, "bara in dan zagaya insha fresh air ko kaina zai dan bude" na bi bayanta da kallo. She has been acting like that tun ranar visiting, what's up?

Haka na cigaba da jinyar zuciyata ni kadai, telling my self that the feelings will go away, but they never did, har yara suka dawo daga hutu muka kuma fara WAEC. Paper din mu ta farko bayan mun gama practicals ita ce geography, muka shiga muka fito ba tare dana tabuka komai na kirki a ciki ba, ni kaina nasan ko ni za'a bawa marking din paper ta ba xan bawa kaina credit ba indai ina so inga annabi. A cikin hall din na yanke shawarar cewa in dai ina son kaina da arziki kuma ina son inga abin kirki a result dina har in samu tafiya nursing school din da naji Abba ya ambata to kuwa dole in tattara Dr Umar Faruq dashi da idanuwan sa da murmushin sa in ajiye su a gefe. But how ......

Ina yin sallar na tafi gurin wata yar ajin mu Ramlah. Ramlah yar soyayya ce, dan tun muna jss take da samari kuma take zaunar damu ta bamu labaran su, dan haka sai nake ganin kamar duk ta fi mu experience akan wannan harkar kuma maybe tana da shawarar da zata bani. But still I was not ready to open up in yarda cewa ina son wanda bai san ina yi ba.

A dakin su na same ta a kwanar ta tana kwadon kanzo da yaji manja da yaji da albasa sai kamshi yake yi. Na kwanta akan gadon ta ita kuma tana karasa hadawa nace "malamar soyayya nazo daukan darasi" ta bude baki "kar dai ki gaya min finally wani yayi awon gaba da zuciyar beauty queen din mu" da haka yawanci suke tsokana ta. Na bata fuska "neva, sai dai inyi awon gaba da zuciyar wani" na fada a raina ina hoping ina ma dai haka ne, ina ma dai nice na tafi da zuciyarsa ba shine ya tafi da tawa ba?

Ta hawo kan gadon tana ajiye kwanon kanzon a tsakanin mu da cup din ruwa a gefe. To bani labari, waye shi kuma me ya faru tsakanin ku? Ina so in san komai" na sake gyara fuska ta, ba zan zubar da ajina ba fa. Nace "babu kowa fa na gaya miki. Kawai dai kinga mun kusa gama school, ina son in san yadda zan facing rayuwa outside these walls" ta gyada kai cikin gamsuwa. "A Beauty queen like you will have a swarm of flies after her kina fita daga school din nan"

Nayi dariya muka fara cin abincin tare sannan nace "flies kuma?" Tace "yeah, mostly flies ne, few of them will be honey bees, amma ke kadai zaki iya tantancewa kuma kiyi filtering out flies din" na sake cewa "okay, ta yaya zan danne zuciyata ko da naga wanda naji ina so" ta kalle ni da alamar tambaya, "ban gane ba" nace "ta yaya zanyi unloving wanda already nake loving" ta bude ido sannan tayi dariya "I knew it, yadda kika rame yadda kika kara yin silent akwai wani a kasa, ko kuma a sama zance ne?" Ta sake dariya. Na bata rai "babu kowa fa na gaya miki"

Ta daga hannu, "tunda kin ce haka mu bar shi a hakan. No, bana jin zaki iya unloving wanda kike loving, sai dai ko idan lokaci ya ja sosai kun rabu ba kwa tare to zaki iya rage son sa kiji cewa it doesn't matter that much. Ko kuma idan yayi miki wani abu mai tsananin ciwo a zuciya, bacin rai zai iya danne soyayyar sa amma shima bance zaki daina son sa ba" ta cigaba da cin abincin ta, yayin da ni kuma nake ta juya spoon din data bani a hannuna, sannan tace "yadda kike ji a ranki zai ragu, with time zaki saba da feeling din kuma zaki koyi controlling din sa, kar ki damu"

Bance mata komai ba, amma tunani na ya tafi kan cewa ban samu amsa ta ba. Kamar ta san tunanin da nake yi sai tace "in the mean time, dole ki ajiye komai a gefe kiyi facing karatun ki" na ajiye cokalin nace "ta yaya zanyi hakan?" Ta ajiye itama nata cokalin tana kallo na tace "ta hanyar concentrating on abinda zai faru idan baki yi hakan ba" nace "me zai faru?" Tace "zaki fadi exams of cause, in ba ki da result mai kyau baki da damar cigaba da karatu, in baki cigaba da karatu ba kuwa babu abinda zaki yi a rayuwa. Worst case scenario Abba zai samar miki miji, dan abokinsa ko kuma abokin nasa ya aura miki. Wanda kika ki karatu a akan nasa ko labarin sa ba zaki sake ji ba. That will be the end of your love story"

Na gyada kai ina relating, yayata Hudallah da akayi bikinta last year kusan abinda ya faru da ita kenan, wanda take so ya gudu yaki auren ta, Abba ya saka ta fitar da miji ta rasa yadda zata yi shi kuma baya barin ƴaƴan sa su dade a gida rana daya yazo yace ya samo mata miji, dan tsohon abokinsa, five months later tana dakin mijinta, shekara ta zagayo da baby a kan cinyarta. Naji cikina yayi karar tsoro.

Ta cigaba da magana "idan kika yi karatu kuma kika ci exams dinki, kina da chance da zaki tafi school kiyi ilimi, ki kara warewa ki kara class ki kara kyau ki kara shekaru. Add these to your beauty, wannan wanda kike so din zai iya lasar takalmin ki dan ki bashi minti daya yayi magana da ke" na gyada kai, already ina hango Dr Umar yana bina a baya kamar jela ni kuma ina ja masa aji son raina, yes, wannan tunanin kadai ya isa ya saka in maida hankali na kan karatu na.

And it did.....

Ban ce na daina tunanin Umar ba amma tunanin nasa sai ya zama shi yake kara min kaimi wajen ganin naci exams dina dan in same shi.

Farhan bata zo ba kamar yadda tayi min alkawari a letter din da ta rubuto min, haka zalika su umma basu zo ba kamar yadda Abba yayi min alkawari, sai dai da muka yi waya a wayar wani copper da ya kan bamu waya a boye mu kira gida, sun bani hakuri cewa basu samu dama bane ba, ni kuma nasan ba wai dama ce basu samu ba tunda dai babu abinda suke yi a gidan, babu aiki babu sana'a, nasan dai Abba ne bai bar su suzo ba, zai ce ne bashi da kudi ko kuma yace za'a shagwaba ni ko kuma wani excuse din da shi kadai zai fahimci ma'anar sa.

Farhan kuma da yaya Mukhtar da Aunty Halima, nasan Hajiya ce zata hana su zuwa. Wannan bani da ko shakka akai.

Lafiya lau muka cigaba da exams din mu, na cigaba da rike kambu na, na cigaba da tabbatar wa cewa Mufida bata san cewa akwai wani abu a zuciya ta a dangane da yayan ta ba. A haka har muka zana final paper din mu. Hausa language. Ranar da ta zama ranar graduation din mu. Ranar kuma da nayi masa gani na biyu a rayuwata. Ranar kuma da ya yi ban ruwa akan shukar daya riga yayi a cikin fadarsa dake zuciyata.

Tun saura sati daya graduation din mu aka fara shirye-shirye, ana ta gabatar da programs na yin bankwana da mu, kowanne club yana shirya wa members dinsa dinner da kuma dan entertainment haka sannan kuma a bayar da gifts, a ciki nima na dan samu rabo na babu laifi. Kyautar da na samu ta farko ita ce ta tsafta kuma dama kusan duk shekara ina samun wannan kyautar, ba wai nafi kowa tsafta bane a set din mu ba, a'a, ni abinda nake ganin ya sa ake bani wannan kyautar bayan tsafta ta wadda na san ina da ita to akwai gayu kuma. Gashi dai ni ba yar masu kudi sosai can ba amma ina da daukar wanka ko da kuwa a cikin uniform ne ballantana a gida. Kuma sanyin jikina sai yake karawa gayun nawa kyau, komai a nutse nake yinsa a tsare. Wannan ya saka aka bani health prefect, sannan kuma yanzu da zamu yi graduation aka sake bani kyautar tsafta.

Bayan ita ma kuma na samu kyautar third overall student, sannan in-coming health prefect ita ma ta bani kyauta kamar yadda yake al'ada ta makarantar. A harkar sports ma an raba kyaututtuka, amma ni ban sami komai ba saboda hardly in yi sport ko ranar sport day ne, sai dai in an matsa min sai inje inyi table tennis, dan ni duk abinda zai saka ni wahala bana son sa.

Amma duk da haka sai aka raba mana wani hand band wanda akayi customising dinsa kowa da sunansa da kuma sunan makaranta da graduation year a jiki, an yi masa ado mai kyau haka kamar saƙa da different colors masu daukan ido. Ana bani nawa na karba ina karantawa "JIDDA. Beauty Queen" sai kuma sauran rubutu, nayi murmushi ina jin a raina ina son abin, na bare shi a ledar sa na saka a hannuna, naga ya danyi min yawa kadan amma a raina nace in naje gida naci abincin gida na huta nasan zanyi kiba kuma zaiyi min dai dai.

Ranar da za mu bar makarantar, paper din mu ta karshe ita ce hausa dan haka ba wani karatu mukayi sosai ba, da daddare ana ta kitson candy da lalle masu hada kaya nayi masu kukan rabuwa da juna nayi nasu kida da table da rawar murna nayi. Ni dai ranar na wuni dakin su Maryam kawata.

Maryam kawata ce, dan zan iya cewa a lokacin bayan Mufida sai ita a layin kawaye na, babban abinda ya hada mu kawance da Maryam shine gayun mu da yake kusan iri daya, amma ita kasancewarta yar talakawa futuk sai ya zama gayun nata ya zama kamar karya dan tana daukar wa kanta abinda yafi karfin ta ne, wannan ya saka tamu tafi zama daya da Mufida, ita kuma yar masu kudi ce sosai amma kuma down to earth, funny, and sweet, sannan kuma tana so na.

Tun safe ina kwance gadon Maryam ina ta cike slum books din da ban zauna na cike ba, masu su suna ta bina suna hada ni da Allah da Annabi, sai a ranar na cike musu wasu kuma na bawa Maryam ta taya ni cike wa dan sunyi min yawa, muna yi muna hirar mu da nishadi.

Bayan mun gama ta wanke min kaina, muna ta rigima dan ni babu abinda na tsana irin a taba min gashina, sannan bayan tayi towel drying gashin tayi oiling sannan ta fara min kitso inata mita ina cewa tayi min manya ita kuma tace kanana zata yi min, ai kuwa ita kanta sai da jikinta ya gaya mata saboda gashina cika ne dashi in ina kitso kamar ba zai kare ba, jelar ma kuma in tayi rabi sai ta saka band ta daure ta ta barta a haka dan in bata daure ba warwarewa zaiyi.

Haka muka zauna har bayan magrib, taje tayi sallah ta dawo muka cigaba, da yake ni ina off, har ishai muna abu daya, sai ga Mufida tazo ta zauna a gurin mu ita ma sannan da kyar aka gama kitson. Yan ƙanana, kitson da ina jin ban kuma yarda anyi min masu kankantar su ba.

Kusan kwanan zaune mukayi a ranar muna hira, muyi hira muyi kukan murna muyi kukan bakin cikin rabuwa sannan kuma muyi dariyar jin dadi. Da assuba muka kammala hada duk wasu sauran kayayyakin amfanin mu dan kusan komai mun bayar dashi sai few abubuwan da suke da muhimmanci muka dauka. Da sassafe muka kai kayan mu bakin gate din makaranta muka koma ciki sannan muka yi wanka muka shirya a tsanake muka fito daga hostel bayan munyi bankwana da metrons da sauran daliban da muka bari a bayan mu, muka tafi exam hall muka zauna, sai a lokacin ne muka danyi karatu kadan kafin a shigo mana, ana shigowa kuwa muka ajiye komai muka rubuta final paper din mu.

Kowa yana gamawa, daga mai ihu sai mai tsalle sai masu rungume juna suna kukan dadi da kuma na rabuwa, amma ni sai na samu kaina da tunani.

Wannan fa shine kamar wata border a rayuwa ta, kamar with this final paper na ajiye duk wani childhood dina kenan. Na zama cikakkiyar budurwa, kamar yadda nake kallon wadanda suka yi candy a matsayin manyan yammata nima na shiga cikin su kenan yanzu.

And my battle begins......

Neman admission, samari, aure ko karatu, yaushe zaki yi aure, samari yan yaudara da yan iska......duk yanzu zanyi facing dinsu in full scale. Am I ready?

Ni dama haka nake a rayuwata ina da tsoron chanji, na gammace in ta jure halin da nake ciki akan in nemi chanji sai imta jin tsoron irin kalubalen da zan fuskanta a sabon babin da zan bude, but wannan babi ne da dolen dole in bude shi, ba wai shawara ta bace ba, a'a dole ne.

Tunanin cewa aure yana daga cikin abinda wannan sabon babi na rayuwata ya kunsa sai ya dawo min da tunanin sa, though dama ba wai tafiya tunanin yayi ba, but sai naji son ganinsa ya dawo min sabo, sai na ji a raina ina addu'ar ina ma yazo daukan kanwarsa? At least nasan zan raka ta mota ko kadan ne sai in samu damar satar kallon sa ko da kuwa bamuyi magana ba.

Mufida ce ta katse min tunani na ta hanyar zuwa ta dane min jikina tana ihun murna, daga nan komai ya rike ce, muka fara bin malamai muna yi musu sallama su kuma suna yi mana nasiha akan rayuwa, wadanda already aka zo dauka suka fara tafiya. Ana ta exchanging phone numbers musamman a gurin wadanda suke da waya, mu kuma wadanda bamu da ita sai muke bayar da wayar wani da za'a same mu tare, ni dai wayar Umma nake bayarwa.

Muna cikin haka aka zo kiran Mufida, nan take naji cikina ya murda sosai kamar zanje toilet, Muka kama hannun juna muka fito daga hall din tare, a raina ina son in raka ta ko Allah zai saka shine yazo daukanta sai in ganshi, har munyi nisa sai kuma na ja na tsaya ina tambayar kaina ina aji na yake? Ai ba dan Allah nake da niyyar raka tan ba sai

Please Login or Register in order to submit comment