Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce nagani da kaina kuma na tabbatar" sai ta saka hannu a jakarta kamar mai neman wani abu yayin da mu kuma muke jira ta fito da evidence dinta na kiran Umar da mugun suna. Sai ta dauko wayar ta tayi danne danne sannan ta mika wa Umma "shine wannan ko?" Umma ta karba tana dubawa, Hajiya kuma ta matsa itama tana lekawa yayinda ni kuma kunnuwa na suka jiyo min wakar video din dana yi bacci ina kalla.

Umma bata taba ganin Faruq ido da ido ba amma ta ga video din jiya dan haka tace "eh shine, me ya faru wai?" Gwoggo Habibah tace

*"to saurayin Jamila ne, shine wanda Jamila zata aura"*

Gidan yayi shiru, komai ya tsaya including bugun zuciya ta, a kunnuwa na sai naji kamar har tik tok din agogon bangon dakin mu tsayawa yayi.

Umma tace "wacce Jamila kike magana gwaggon yara?" Gwoggo Habibah tace "wacce Jamila ce kuwa zata sakani tahowa gidan nan da sassafe kuma ta saka ni zubar hawaye banda Jamila taku ta waje na?" Hajiya tace "shi zata aura fa kika ce? To ita kuma Jidda fa?"

Tace "shine abinda nazo a bincika aji, wacce yake so da gaske a cikin su? Wacce zai aura a cikin su? Kar mu bashi kofar da zai raba mana zumuncin mu dan na fahimci shi ba dan arziki bane ba" Umma tace "kiyi mana cikakken bayani dan Allah. Tun yaushe suke tare da Jamila? Kuma ma ai mu bamu san an bayar da Jamila ba. Menene gaskiyar lamari?"

Tace "ba'a bashi ita ba saboda kunsan babansu sai sun gama degree yake yi musu aure, amma sama da shekara uku suke tare da ita tun kafin ya tafi India karo karatu, shi kuma yasa tayi masa alkawarin zata jira shi kuma ba zata kula kowa ba sai shi" ta share wasu hawayen.

"Tunda tayi masa alkawarin nan shikenan ta daina kula kowa, bata da wani saurayi sai shi kuma ta gama yankewa in ance ta fito da miji shi zata fitar, jiya ma fa da daddare suna tare, kawai sai data dawo gida ta ga wannan video Tahir ya dora a matsayin mijin da Jidda zata aura"

Naji duniya ta tana juyawa, numfashi na yana sama sama, zuciyata tana bugawa da karfi a kirjina iska tana kin shiga kofofin hancina, na tabbatar cewa attack zan samu, na dafe bango sannan na zame na zauna tare da rufe ido na amma kunnuwa na still suna jiyo min maganganun su Umma a tsakar gida.

"Amma dai wannan yaron ba mutumin kirki bane ba, dole kuwa a fasa auren nan dan ba zai zo ya raba zumunci a tsakanin yaran nan ba. Wata kila dama duk su biyun ba auren su zaiyi ba" Hajiya ta cigaba da sababi tana kokarin wuce gwoggo Habibah ta hau sama gurin Abba yayin da Umma ta samu guri akan baranda ta zauna tare da dafe kanta.

Kafin Hajiya ta kai kashen stairs din Abba ya fito yana gyara babbar rigarsa, daga alama wani daurin auren zashi ko kuma wani guri mai muhimmanci. Bai kula da zancen da Hajiya ta tare shi da shi ba ya wuce ta ya sauko yana kallon Habibah. Ta mike tsaye "yaya, kaji abinda yaron nan yayi mana ko? Yaudarar yaran nan yake yi ashe, ya za'a yi ya hada su duk su biyu yace yana so kuma kowacce bata san da zaman kowacce a zuciyarsa ba. Wacce irin yaudara ce wannan. Jamila jiya yadda taga rana haka ta ga dare saboda takaicin abin nan kwana tayi tana kuka yanzu kafin in fito ma zazzaɓi ya rufe ta ruf kuma....." Ya daga mata hannu.

"Duk naji maganar da kuke yi tun ina sama. Amma in tambaye ku, shin yaron nan ba namiji bane ba shi? Shin ba mata hudu aka halasta masa ya aura ba? A bayanin da kika yi na fahimci cewa shi yana son Jamila kuma yana so ya aure ta amma ku kunfi son boko akan aure sai kuka ce sai ta gama makaranta, shi kuma yana son aure yanzun, shine ya hadu da Jidda ba tare da ya san cewa yan'uwa bane ba har aka bashi ita kuma zai aure ta, watakila a ransa duk su biyun yake niyyar hadawa, watakila nufinsa in ya auri Jidda yanzu ita kuma Jamila in ta gama makaranta sai ya kara da ita, ni duk banga yaudara ko mugun hali a cikin wannan ba, ai ba sai lallai ya gayawa daya daga cikin su cewa akwai wata daban a cikin zuciyarsa ba ko dan gudun irin wannan halin naku na mata. Allah ya kyauta. Ni zan fita sai na dawo" daga haka ya saka kai ya fice.

Banji sauran maganganun da suka gudana a tsakar gidan ba saboda numfashi na da nake ta kokawa dashi. A idona ina hango fuskar yaya Jamila, kyakykyawa ce itama, ta fini ilimi ta fini shekaru ta fini wayewa, na tuno sanda muka je gidan su yadda take fita gurin saurayi da kuma yadda take kusan raba dare tana waya da saurayi. Was it Umar all along? Ni ba zanyi kishi da yaruwata ba, ni ba zanyi kishi da Jamila ba, dole Umar yazo ya zaba ko ni ko ita.

Sai dai kuma wani barin na zuciyata yana tsoron kar ya zabe ta ya barni. Allah ne kadai yasan me zai faru dani idan hakan ta kasance.

"abinda zaka ce kenan yaya? Yanzu abinda zaka ce kenan? Shi ke nan yaci bulus yayi a banza? Ya yaudari yaya kuma ka bashi auren kanwarta? Ta yaya ma zaka ce zai hada su su biyu? In dai kuwa har ya auri Jidda ai ko maza sun kare a duniya ba zai auri Jamila ba wallahi tunda mu munsan zumunci mun san martabar yanuwan mu. Ba zan taba bari Jamila tayi kishi da yaruwarta ba....."

Ta cigaba da bambami alhalin shi wanda take yi dan shi din ya jima da barin unguwar gabaki daya. Hajiya tana ta kara zuga ta ta sigar bada hakuri. "Kiyi hakuri gwoggon yara. Allah yasa hakan shine yafi alkhairi ga Jamila. Shi kuma tunda halin sa ne tabbas watarana asirin sa zai tonu. Shima kuma tunda ya goya masa baya shima watarana zai ji kunya ai. A juri zuwa rafi dai inji hausawa dan tabbas watarana za'a fasa tulu"

Duk abinda suke yi Umma tana tsaye kawai tayi tagumi da hannu daya, she seemed lost of words, ta rasa bayan wa zata goya ta kuma rasa me zata cewa Habiba. Sai gwoggo Habibah ta mike daga zaunen da take tana gyara mayafi ta tsaya a gabanta tace "ke macece Aisha, shi ba zai fahimta ba amma ke zaki fahimta tunda ance ciwon ya mace na ya mace ne. Kiyi iyakar kokarin ki kar ki bari ayi auren nan ba tare da an nuna masa kuskuren sa ba idan kuwa ba'a yi haka ba to tabbas Allah kadai yasan abinda zai cigaba da aikatawa nan gaba, tunda bashi da kunya bayan auren ma zai iya dawowa yace zai auri Jamilar, wannan kuma zai iya zama sanadiyyar lalacewar zumunci tsakanin yayan mu. Kar ki bari hakan ta faru. Bance kar ayi auren nan ba amma kafin ayi aja masa kunne a nuna masa yayi ba dai dai ba. In kuma ba haka ba tabbas za'a yi nadama nan gaba"

Sai ta sake ta ta fita da sauri tana hada hanya, Hajiya kuma ta bita a baya tana sambatun ban hakuri. Suna fita Farhan wadda duk abinda ake yi tana labe a falon Hajiya inda ta tafi da sassafe dan kallon wani series movie da take gani, ta fito da sauri ta taho dakin da nake dan tasan ina bukatar kafadar da zan dora kaina a kai inyi kuka. Sai dai abinda ta gani data shigo dakin shi ya mantar da ita duk maganganun da taji anayi a tsakar gidan. Ina zaune baya na a jingine da jikin bango ina ta kokawar shigar da iska cikin hunhu na. Na hada gumi kashirban.

Ta karaso inda nake da sassarfa tana tayani dafa kirjina da nake jin sa kamar a kan garwashin wuta sannan ta kwalla kira "Umma!" Urgency din kiran ya saka Umma ta shigo dakin kusan a guje, "Jidda!" Ta fada tana durkusa wa a gaba na itama sannan kuma sai ta mike da sauri ta kuma fita daga dakin, daga dukkan alama inhaler ta ta tafi dauko min. Sai dai ni kaina bansan inda take ba dan na dade rabon da in samu attack kamar na yau, har na fara tunanin ma na rabu da asthma.

Farhan ta saka hannu tana share min gumin da ya hadu da hawaye ya wanke min fuskata. "Breath Jidda. Ki kwantar da hankalin ki don't panic just breath" na girgiza mata kai da sauri dan dan karfin da nake dashi ya kusa karewa amma har yanzu na kasa kai iska hunhu na. Ta juya tana kallon kofa "Umma!" Ta sake kira, as if kiran shi zai saka ta ga abinda take nema.

Sai kuma naga ta sake ni ta hau kan katifar da muka kwana da sauri tana hargitsa shimfidar, can sai gata da waya ta a hannun ta, na fahimci abinda take son yi, Umar take son ta kira, nayi kokarin girgiza mata kai dan har zuciya ta bana bukatar taimakon sa, tun ina yarinya nake asthma kuma nake samun sauki ba tare da shi ba kuma yanzu ma haka zanyi in gama.

Ta dawo inda nake kwance da sauri ta kama ni ta mikar da ni zaune sosai tana kokarin kirkirar murmushi "babu komai Jidda, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru misunderstanding kawai aka samu am sure misunderstanding ne. Just breath please" na rufe ido na ina gaya wa kaina cewa misunderstanding ne, maybe ba Umar dina bane ba, maybe mai kama da shine, ai akwai masu kama iri daya a duniya right? Musamman tunda ba ido da ido suka ganshi ba a video ne.

Ina jinta ta saka hannu cikin rigar bacci na tana balle min bra dan ta kara taimaka min wajen numfashi, na jingina kaina a kafadarta ina jin numfashin yana fara shiga hunhu na.

A lokacin ne Umma ta shigo dakin da sauri hannunta rike da blue inhaler ta, ta dago kai na tare da saka min ita a baki sannan ta matsa sau biyu. Na mayar da ido na na rufe ina jin sanyinta a makogwarona zuwa kirjina kuma ina jin airways dina suna clearing numfashi na yana kuma daidaita.

*Saurayin Jamila ne, shine wanda zata aura* na tuna da maganar gwoggo Habibah.

Na dago kai ina kallon Umma, hawaye yana bin idona nace "Umma wai da gaske ne? Da gaske Umar ne saurayin yaya Jamila?" Ta zauna a kusa dani tare da kara mika min inhaler ta, na dauke kai gefe ina so inji ta gaya min cewa ba haka maganar take ba ji ne banyi dai dai ba. "Ki nutsu ki mayar da hankalin ki guri daya, ki kwantar da hankalin ki ki dawo da lafiyar ki jikinki kafin kiyi kokarin neman sanin wani abu da ba zai amfane ki da komai ba" na mayar da kaina kafadar Farhan, bansan me Umma take nufi da maganar da ba zata amfane ni da komai ba a yayin da ake magana akan mijin da zan aura, wanda nake da niyyar spending the rest of my life with, wanda nake saka ran zai zama uban yaya na. Shin bani da right din sanin komai a kansa?

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Episode Eleven: The Denial*



Wahalar da nasha a attack din dana samu yayi exhausting dukkan karfi na, hakan yasa duk da halin da zuciyata take ciki sai da bacci mai nauyi ya dauke ni a jikin Farhan.

Sanda na tashi ni kadai na ganni a dakin, daga alama rana ta fito sosai

Na mike zaune nayi salati tare da dafe goshina, ko kadan ban manta abinda ya faru ba duk da cewa ganin shi nake yi kamar a mafarki, ina tunawa da yadda Abba yayi biris da maganar yayi kamar ba wani abin da za'a yi doguwar magana bane ba a kansa, na kuma tuna da hukuncin da ya yanke a karshe, wai Umar zai iya auren mu mu biyu ni da yaya Jamila in dai yana son haka shi bashi da problem. Na mike tsaye da sauri dan tabbas ni ina da problem da haka.

A palon Umma na same ta a zaune da kayan abinci a gabanta, daga dukkan alama bata dade da gama breakfast ba, babu kowa a tare da ita dan nasan Amira tana school. Na zauna a gefenta cikin matsanancin sanyin jiki, ta bini da kallo har na zauna sannan tace "ya jikin?"

Na gyada kai kawai ina jin babu isasshen yawu a bakina balle in amsa mata, ta dauko flask din gabanta ta zuba min kunu sannan ta miko min "ungo ki sha" na karba na ajiye a gabana ina zagaya dan yatsa na a rim din kofin sai ta fara magana

"Nasan kinji maganar da gwoggon ku tazo da ita, farko ni ma kamar yadda hankalin ki ya tashi haka nawa hankalin ya tashi akan maganar amma kuma da baban ku ya sauko ya yi magana sai naji hankali na ya kwanta" na dago kai da sauri ina kallon ta sai tace "ba wai na yarda da maganar sa bane ba ko ina goyon bayan abinda yace ba a'a ina nufin na fahimci abinda ya faru.

"Jidda ke yarinya ce amma duk da haka nasan zaki fahimci cewa namiji ba mijin mace daya bane ba, da wahala ki ga saurayin da yake da budurwa daya, bance ba'a samu ba amma da wahala, haka zalika shima mai auren da wahala ki ga wanda bashi da wata budurwar kuma, haka Allah ya halicce su shi yasa ya basu damar auren mata har hudu in dai zasu iya"

"ba abin mamaki bane dan Umar yana soyayya da ke kuma da Jamila a tare, watakila nufin sa ya aure ta bayan ya aure ki, kuma ba zamu ce yana da laifi ba akan hakan tunda addini ya bashi dama, amma abinda nafi tunani nima kamar babanki shine bai san dangantakar da take tsakanin ku ba, bai ma san kunsan juna ba. Sai dai abinda ban yarda dashi ba a maganar babanku ita ce na cewa zai iya hada ku, kamar yadda Habibah tace ba zata bar hakan ta faru ba ni ma ba zan bar hakan ta faru ba dan tabbas zai iya raba zumunci a tsakanin ku"

"Dan haka yanzu tunda Allah yasa lokaci bai kure ba sai mu dauki mataki, ki dauki waya ki kira shi kice kina son ganinsa, in yazo ki tambayeshi game da Jamila ki kuma fada masa dangantakar da take tsakanin ku sannan ki tabbatar masa da cewa ba zaku zauna kishi ba, ki bashi dama ya zaba ko ita ko ke. Idan ke ya zaba to ki tabbatar masa cewa iyayen Jamila ba zasu bashi ita ba indai ya aure ki, tsakanin sa da ita sai dai mutunci a matsayin ta na yaruwarki. Idan kuma ita ya zaba to ya janye maganar aurenki ya kuma aiko a karbar masa kudinsa da sauran kayansa, ke kuma Allah ya baki wanda ya fishi alkhairi".

Na gyada kai na da sauri ina yadda da hukuncin ta, amma kuma wani bangare na zuciyata yana cike da tsoro "what if ya zabe ta? Zan iya rayuwa babu shi anya kuwa?"

Na mike da wayata a hannu, sai Umma ta dakatar dani tare da nuna min kunun data zuba min, na zauna na shanye ina bata fuska kamar mai shan magani, ina gamawa na dauki waya ta na koma dakin mu. Missed calls din Umar na gani har guda biyar a dai dai time din daya saba kira na kullum dan yaji yadda na kwana.

Nayi dialing number din sannan na saka a kunne na. Seconds biyu ya dauka

"Hey Baby"

Na lumshe ido na na bude ina jin muryar sa tana taba zuciyata. "Hi" na fada da muryar da naji kamar ba tawa ba.

"What's up Baby. Naji muryar ki wani iri ko yanzu kika tashi daga bacci?" Na girgiza kaina kamar yana kallo na ina jin hawaye yana kawowa ido na, nayi kokarin boye emotions dina nace "lafiya lau. Kana ina?" Yace "ina office, nayi ta kira dazu ai kina ta bacci ko? Are you sure you are okay?" Nace "ina so ne in ganka yanzu, if you are free, akwai maganar da nake so muyi" ya danyi shiru sannan yace

"Baby, is everything okay?"

Sanyin da yayi min maganar da shi ne ya saka hawayen da nake rikewa suka zubo, can he really do it? Yana dating dina yana dating wata kuma daban? Ko da bai san yaruwata bace ba amma still.......

"Lafiya lau. Kazo kawai zamuyi maganar in kazo" "are you crying?" Ya tambaya, sai naji hawayen ya sake ballewa "oh my God, gani nan zuwa yanzu. I am about to go into surgery but zan ajiye yanzu in taho...." Na katse shi "no.. lafiyar patients dinka tafi duk wata maganar da zamuyi, ka gama kawai sai kazo" yace "wa? Ba dai ni Umar din ba, Jidda tana kuka kuma zan iya surgery? Ai tabbas zanyi barna ne a ciki. Ba emergency bane ba scheduled cs ne, zata iya jira inzo in ganki in dawo ko kuma wani doctor din yayi taking over amma ni ba zan iya ba Baby, not when you are crying"

Sai ya kashe wayar, na dora ta akan kirjina ina jin bugun zuciya ta yana vibrating a jikin wayar "can he really do it?" "Will he chose me?" Na tuna Yaya Jamila, zuciya ta tana lissafo min yawan abubuwan da ta fini, kusan ta fini komai da wayayyen hadadden namiji kamar Umar zai so a gurin matarsa.

Na tuna da wayar da take raba dare tana yi sanda muka je gidan su, da wa take waya? Umar?

Ina nan a zaune Farhan ta shigo dakin, ta zauna tana ta yi min labarin abokin mijin yaya Hudallah da take kokarin hada su "kinga katon cikin sa kuwa?" Ta fada tana dariya, daga dukkan alamu so take ta saka ni dariya amma ganin bani da niyyar yi sai ta fita ta bani guri.

Bata jima da fita ba ya kirani "ina waje" ban amsa ba na kashe wayar sannan na tashi na wanke fuskata a tsakar gida sannan naje dakin Umma na saka kwalli, bana so yasan how much nayi kuka a kansa. Amma gyaran fuskata bai yi komai ba wajen gyara zuciyata, dan a tsorace take sosai, ko wannan ne zai zamo gani na karshe da zanyi masa? Menene makoma ta idan na rasa Faruq? Har na fito daga dakin kuma sai na koma na dauko wayar Umma na fito da ita a hannu na.

Yana mota bai fito ba, har na fito daga cikin gidan bai fito ba nasan kuma hakan yana da alaka da saurin da yake yi dan lokuta da dama in yana sauri yakan zauna ne a mota.

Na zagaya na bude kusa da shi na zauna. Yana sanye da kayansu na doctors, wannan ita ce ranar dana fara ganinsa da kayan kuma sai naga kamar sunfi yi masa kyau akan kowane kaya, sai naga kamar yafi yi min kyau akan kullum.

But he looked worried.

"My God! Da gaske kuka kike yi Jidda" na girgiza kaina, trying so hard not to continue crying. Sai na dauko wayar Umma na bude sannan na nemo hoton Yaya Jamila na nuna masa direct nace

"ka san wannan?"

Na lura da yadda yanayin sa ya chanja a lokaci daya, sai kuma naga ya dawo dai dai sannan ya karbi wayar daga hannuna yana kara kallon ta kamar mai tunani sai yace "Jamila ko? Jamila something......na manta second name dinta" sai ya miko min wayar "a ina kika santa?" Na karba still ina kallon yadda yaki hada ido dani yana kallon waje, duk damuwa da seriousness din fuskarsa sun tafi, he looked uninterested"

"menene a tsakanin ka da ita?" Na sake tambayarsa. Ya juyo yana kallo na kamar mai mamakin tambayar sannan yace "wai wannan yarinyar? Ni kuwa menene hadi na da ita? Wani abun aka gaya miki? Is that the reason da kike kuka?" Nace "I will be the one asking the questions, and you will be the one answering" sai ya sara min kamar yadda ake yi wa masu khaki yace "yes ma" na lura gabakidaya ya mayar d maganar wasa.

Nace "menene tsakanin ka da ita?" Yace "nothing really, na santa a buk tun kafin in fita India, she is a friend of girlfriend din Bashir ta lokacin, so in na raka shi gurinta muna haduwa kuma most of the times in zai fita da ita suna tare kuma nima ina tare da shi. So bayan sun rabu ma muna dan gaisawa haka in mun hadu, shikenan...... please ki gaya min mai ya faru?"

Na ajiye wayar a tsakanin mu ina kallon gaba na, trying to think using my head but my heart is already jumping with joy cewa ba wai yana son Jamila bane ba, it was a misunderstanding.....

"Yayata ce" na fada "yar gwoggo Habibah ce...ita ce autarta" ya kalle ni "really? What a small world. Amma menene ya saka ki kuka a cikin maganar? Oh sorry ma, ashe fa kece mai yin tambaya ni mai amsawa" yayi dariya, shi bashi da wani problem.

"Dazu gwoggo Habibah tazo gidan mu da sassafe........." Sai na bashi labarin abinda ta fada na daga dangantakar da tace akwai a tsakanin sa da Jamila. Amma ban fada masa abinda Abba yace akan maganar ba.

Anan ne naga hankalin sa ya tashi "ya salam...... wannan yarinyar sharrin da zata yi min kenan? Yaushe ne muka yi haka da ita..." Na bishi da kallo kawai "ta cuce ni amma wallahi shikenan ta bata min suna a gidan ku" sai yayi kamar zai riko fuska ta sai kuma ya dauke hannun sa yana yarfarwa a gefe "na shiga uku. Wallahi Jidda karya take yi min babu wani abu mai shigen kama da wannan a tsakani na da yarinyar nan, ni ban taba cewa ina sonta ba ballantana har in yi mata alkawarin aure. My God!" Ya fada yana shafa gashin kansa

"Look Jidda, Wallahi karya take min. Look, ban damu da wasu su yarda ko kar su yarda da abinda nake cewa ba, but Please ki gaya min cewa ke baki yarda ba. You think zan yi miki haka? Bayan na same ki kuma Jidda mai zanyi da wata mace kuma?"

Na dauke kaina gefe a kokari nana kara jan zaren aji na, "tace jiya ma kuna tare" ya danyi frowning fuskarsa sannan yace "jiya? Jiya naje dinner ne ta bikin wani friend dinmu" sai kuma yace "ohh I remember seeing her there, sunje a matsayin kawayen amarya mun gaisa haka briefly but it doesn't mean muna tare as in kamar naje 'zance' gurinta" yadda ya fadi zancen kamar wani abun kyama.

Nayi shiru ina assessing maganar sa, ido na akan band dina da yake hannunsa. Ya sake cewa "idan baki yarda ba bara in kira Bashir, zai fada miki komai....." Na girgiza kaina "no need" ya dauko wayarsa tare da cewa "I insist. Bana son ko trace na wani abu mai kama da wannan ya shiga tsakanin mu" yayi dialing number sannan ta saka a handsfree tare da dora ta akan dashboard.

Ina jin Bashir ya dauka "hey namiji" yace "hey Bash. You are on speaker. Ina tare da baby na ne kuma ina bukatar taimakon ka. Please help me clear something out. Ka tuna yarinyar nan Jamila kawar Nafisa ta ka?" Yace "yeah. Na tuna Jamila, me ya faru" sai ya fada masa abinda na gaya masa a game da Jamila

Bashi yace "look Jidda,ba tun yau ba na gaya miki cewa guy din nan ya sace zuciyar yammata da yawa, amma

Please Login or Register in order to submit comment