Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hirar mu.

Da yake ana fara da wuri wajen azahar har an gama nawa, sai duk suka fita palo ana yi musu a can ni kuma na zauna anan dan bai gama bushewa ba bana so a bata min shi. A lokacin ne kuma aka turo kofar aka shigo, na daga kai muna kallon kallo ni da Yaya Jamila.

Ta rame sosai, duk da glasses din idonta amma naga ramar ta. Gabana ya fadi sanda ta cire glasses din, nayi saurin sauke ido na kasa ina jin wani irin kunyarta a raina. "Amarya kin sha kamshi" ta fada tana karasowa kusa dani. Ta zauna tana dan taba kunshin hannuna daya fara bushewa "yayi kyau sosai. Allah ya sanya alkhairi" nace "ameen. Ya su gwoggo?" Tace "lafiya lau. Ya angon naki?" Sai nayi shiru na kasa amsa mata.

Tace "zuwa nayi muyi magana Jidda. Ina so in tabbatar miki da cewa ni banji haushin ki ba ko kadan, tunda ba wai kwace Faruq kikayi daga gurina ba, sanda yace yana sonki baki san yana zuwa gurina ba dan haka baki da laifi for falling for him. Baki da laifi. Kuma banji haushin ki da kika ki fasa aurensa bayan kinsan abinda yayi min, I would have done the same thing da ace ni ya zaba. I love him so much that I would have done the same thing"

Ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannayenta "na san da kika gaya masa abinda Umman mu tace karyata wa yayi, dan baya son ya sirka soyayyar ku, baya son ya bata kansa a idonki. Watakila ma cewa yayi bai ma sanni ba. Watakila cewa zaiyi bai taba yi min magana ba. Tunda abinda yake pretending kenan tunda abin ya faru. Kuma nasan kin yarda da shi dan nasan idan ni ce nima zan yarda da shi saboda son da nake yi masa"

Ta dago kai tana kallona tace "watanku nawa tare? Bana jin kun kai shekara daya tare, imagine yadda kike jinsa a ranki. Imagine ace kun shekara uku a haka. Imagine yadda zaki ji shi a ranki then. To haka nake sonsa, haka ya saka min sonsa a raina. Then imagine rana daya yace shi baia taba saninki ba, yayi cutting duk wani link da yake tsakanin ki da shi."

Ta fara murza hannayenta. "Tun ranar da ya dawo dani daga dinner din abokinsa dana raka shi, ina shigowa ina duba chats dina naga video din sa dake wai shine mijin da zaki aura. Na gaya wa Umman mu, da sassafe ta zo ta fada a gidan ku, I guess ke kuma kika kira shi kika gaya masa, tun ranar yayi cutting dina off tamkar wata used and unwanted rag, yayi blocking number dina, yayi blocking dina a duk social media accounts dinsa, hatta abokinsa Bashir shima yayi blocking dina. Ni ba zan tilasta masa ya aure ni ba but I just want him to tell me why, at least ai na chanchanci in san dalilin da yasa yayi min haka ko? At least ya kalli idona ya gaya min cewa all those years dama karya yake yi baya sona, ya kalli idona ya gaya min baya sona, ni ko karya ce ma ya shirya ya gaya min a matsayin dalilin da yasa ba zai aure ni ba at least zan san cewa yana da dalili ba wai kawai yayi shiru ba"

Ina kallon wawayenta yana diga a kan hannunta. Ta saka bayan hannun ta ta goge idonta "na san ya riga ya gama tsaraki, na san duk abinda zan gaya miki ta bayan kunnen ki zai bi ya wuce ba yarda zaki yi ba, ni kuma ba ni da wata shaidar da zan nuna miki tunda ko na hada ki da kawayena sun tabbatar miki da magana ta zaki iya daukan hakan a matsayin hadin baki dan in rabaki da shi kamar yadda nasan ya riga ya dora ki a kan hakan" ta danyi murmushin takaici "kullum in zanyi mana hoto sai yace baya so, har tsokanar sa nake in ce yana da 'photophobia' sai yanzu na fahimci dalilin da yasa baya daukar hoto da ni, dan yana tsoron kar irin wannan ranar ta zo in samu abinda zanyi proving gaskiya ta da shi. Ina da hotunan sa amma shi kadai ba tare da ni ba, and I guess they won't probe anything"

Na girgiza kaina a raina ina kin yarda da maganar ta dan idan da akwai abinda Umar yake so to hoto ne, kusan kullum sai yayi mana hoto ni da shi a school ko a hanya ko a gidan mu. Musamman in nayi kwalliya ko inshi yayi.

Ta mike tsaye tana mayar da glasses din idonta. "Gwara in tafi kar in bata miki mood dinki kanwata, sai dai da ace zuciyata kawai Faruq ya karba a gurina da zan iya healing with time, but ya karbi abinda ba zan taba iya dawo dashi ba komai dadewar danayi ina healing, abinda mijina kawai ya kamata in bawa amma na bashi saboda dadin bakin da yayi min na cewa shi din ai shine zai aure ni dan haka babu komai"

Na dago ido da sauri ina kallon ta zuciyata tana bugawa da karfi a kirjina, idanuwana kamar zasu fado a gabanta. Ta gyada kai tana kallo na "yes my dear sweet cousin, I gave him myself" na toshe kunne na da hannaye na ina girgiza kai na "not another word, bana son ji, bana son ji" sai tayi murmushi tace "da ace abinda na fada miki zaiyi destroying Faruq ne shi kadai da tabbas loudspeaker zan saka in sanar da kowa, amma zaiji destroying dina ne fiye da shi, wannan yasa ba zan gaya wa kowa ba sai ke daya zaba akaina, dan ki san irin mijin da zaki aura. At least na rama in my own small way"

Sai ta kama hanya kamar zata fita sai kuma ta juyo tace "na san baki yarda ba. Amma watarana zaki yarda. Zaki fahimci cewa auren Faruq is not a blessing to you but a curse". Sannan ta bude kofa ta fita

Na sauke hannayena daga kunne na duk da cewa basu yi amfanin komai ba dan naji duk abinda ta fada. Na fara girgiza kaina "she is lying" nafada a fili. "Karya take yi!" Na maimaita ina jin kamar ana gasa masara a kirjina. "Tana so ta bata min rai ne kawai, tana so ta bata mana auren mu ne kawai. Saboda bai aure ta ba shi yasa take son tahana shi aure na nima" na cigaba da sambatu ni kadai.

But what if she is saying the truth?
Wani bangare na ƙwaƙwalwa ta ya tambayi zuciya ta? What if da gaske Umar yayi abinda tace yayi din. Me ya kamata inyi a wannan stage din? Me ya kamata inyi? In ce na fasa aurensa? Can I even do that? Idan ma kuma na iya yi Abba da Umma zasu yarda?
Idan kece a matsayina mai zakiyi?

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Episode Thirteen: The Wedding*

Tana fita Farhan ta shigo, kallo daya tayi min ta taho inda nake da sauri tana dafa kafada ta "me tace miki? Ni banga shigowar ta ba wallahi sai fitar ta na gani, wani abin ta gaya miki?" Nayi saurin girgiza kai na duk da masan kamanni na kadai sun isa su tabbatar mata karya nake yi. Sai dai maganar gaskiya ba zan iya gaya wa kowa maganar nan ba not even Farhan, kuma nasan sanin hakan ne ya saka itama Yaya Jamilar ta gaya min, wannan kuma ya saka zuciya ta ta cigaba da gaya min cewa karya take yi.

Farhan ta zauna a kusa dani tana dafa ni, "me tace miki Jidda? Menene zai bata miki rai haka a lokacin bikin ki?" Na danyi gyaran murya dan magana ta fito daga makogwarona da nake jinsa a toshe "babu abinda tace min, kawai dai maganganu ne irin nata akan wai yadda Umar ya yaudareta and other stuffs" Farhan tayi tsaki "na sani dama, na san sai ta tayar da maganar a bikin nan wallahi kuma gashi gobe a gidan su za'a yi kamu yadda zasuyi ta fadar maganganu ita da yan uwan ta, ni wallahi da an chanja venue din gobe ma" sai ta mike tayi hanyar fita "bara inje in gaya wa Aunty Afia"

Kamar zan hana ta kuma sai na barta dan ina son in samu quietness din da zanyi magana da zuciyata. Zuciyar da naji tana tsatstsagewa gunduwa gunduwa. Na saka yatsuna na kuma toshe kunnuwana da har yanzu suke amsa amon maganar ta "I gave him myself" na runtse idona tareda girgiza kai na. "Karyar banza" na fada a fili. "Karyar wofi" na maimaita. "Muguwar ƙatuwar karya" na fada da dan karfi tare da yin jifa da pillown da yake kusa dani, a dai dai lokacin da Aunty Afia ta bude kofa suka shigo tare da Farhan "shashancin me kike yi haka Jidda?" Ta fada tana kallona. Na sunkuyar da kaina ina jin numfashi na yana fita da sauri "babu komai Aunty" ta rufe kofar "babu komai kike jifa da pillow?" "Babu komai" na sake fada ina jin hawaye yana tahowa idona.

Sai ta karaso ta zauna a gefe na Farhan ma ta zauna a daya side din, haka suka yi ta tambaya ta amma naki gaya musu komai, it would have created a scandal idan na fada ko da kuwa anyi finding out cewa karya ne to kuwa wasu ba za su yarda cewa karya ne ba.

Haka ranar na karasa wuni a daki, duk wanda ya ganni da safe sannan ya ganni bayan zuwan Yaya Jamila tabbas zai fahimci chanjin yanayi a tare da ni, wadanda suka san abinda yake tsakanin mu sunyi guessing ita ce silar chanjin mood dina, wadanda kuma basu sani ba sai suke tsokana ta da cewa ko har ma fara tunanin rabuwa da gida ne.

Tun bayan tafiyar Jamila Umar yake ta kirana a waya, ina jin wayar kuma nasan shi yake kira amma ko kallonta banyi ba ballantana in dauka, kawai bana jin zan iya yi masa magana yanzu duk da cewa kaso casain na zuciyata yana gaya min cewa karya tayi masa dan ta rama abinda take tunanin yayi mata, but duk da haka sai naji ina bukatar break from him. Daga karshe dai dole ya hakura ya daina kira

A haka har aka watse daga taron, har akayi magrib, ina yin sallar na koma na kwanta akan sallaya ta na rufe idona kamar mai bacci duk da ba baccin nake yi ba kawai dai bana son ake yi min magana ne. A haka naji wayata ta cigaba da ruri na kidan da na saka musamman saboda Umar, sai a lokacin na tuna da cewa munyi alkawarin zai zo yaga kunshina yau da magrib. Na mika hannuna na dauko wayar sannan ba tare da na ko kalli sunansa ba na katse kiran sannan na kashe wayar gabaki daya na cusa ta a kasan pillow na, a raina ina jin bazan iya ganin sa ba har sai na goge wani dan digo da nake ji a zuciya ta na cewa Jamila gaskiya ta fada.

Naji an murda kofar dakin an shigo, na daga kai ina kallon Farhan da ta shigo da plate din abinci ta ajiye a gaba na tana magana kasa kasa duk da bana jinta amma na san mita take yi akan yadda banci abinci ba tun rana.

Wayarta tayi kara ita ma, ta daga tana murmushi "ango kasha kamshi" nayi saurin kallonta dan na fahimci da wanda take magana. "Wallahi ka ganta nan tun azahar a kwance" "eh Yaya Jamila ce tazo, bamu san me ta gaya mata ba shikenan mood dinta ya chanja take kwance" "ta tafi tun dazu, tana zuwa ko five minutes bata yi ba ta fita" "a'a dan Allah kar kaje gidan su, kaga yanuwan mu ne fa, wannan ma sabanin da aka samu so muke a gyara shi" "okay gata" ta fada sannan ta dora min wayar a kunne na.

"Baby na" ya fada da muryar sa data taba zuciyata da already take cike da kishirwar samun kulawa da kuma assurance daga gare shi.

"Why Jidda! Me yasa zaki bar yarinyar can ta shiga kanki haka? Me yasa zaki bar ta ta bata miki daya daga cikin mafi girman ranaku na rayuwarki? Wallahi baby da ace nasan Jamila zata kasance sanadiyyar zubar digon hawaye daga idon ki wallahi da ko hanyar da ta bi ba zan bi ba ballantana mu hadu. Da ko iska ba zan bari mu shaka a atmosphere daya ba"

"Abinda take so kenan Baby, so take ta hana mana farin ciki a cikin ranakun farin cikin mu Jidda. Kar ki bata wannan satisfaction din dan Allah. Kar ki hana kyakykyawan murmushin ki bayyana akan kyakykyawar fuskar ki akan abinda ni na riga na gaya miki cewa karya ne"

A hankali nace "doctor baka san me tace min ba ai ........" Yace "shshshsh, bana son ji, at least not now. Kin san sai yaushe nake son ji" na girgiza kaina kamar yana kallo na, sai yace "sai rana ita yau, a lokaci kamar yanzu, muna zaune a falon mu kina kan cinyata ina baki kaza a baki, a lokacin zaki bani labari then we will laugh over it and let it go" kawai sai naji murmushi ya subuce a kan fuska ta, nace "bana son kaza, sai dai tsire" yayi dariya "to zan baki tsiren kaza" nayi dariya nima "ni tsiren tsire nake so" yace "kin san me? Come down and tell me wanne kala kike so, kuma ki nuna min wannan kyakykyawan kunshin and in yayi min akwai kyautar da na taho miki da ita"

Na cire wayar daga kunnena na mike ina murmushi na shiga toilet na dan gyara fuskata sannan na fito na saka turare, Farhan ta saki baki tana kallona har na gama sannan tace "oh Allah, su soyayya manya, tun dazu fa muke fama ni da Aunty amma mun kasa samun abinda cikin seconds shi ya samu. Me ya gaya miki?" Na harare ta "ina ruwanki? Abin sirri ne"

Yau ma a motar sa na same shi na bude na shiga, ya lumshe ido ya bude yace "kamshin ki kawai ya warkar min da duk wata damuwa" nayi murmushi "muryar ka kadai ta warkar min da duk damuwar da take cikin zuciyata" yayi saurin kallona da budadden ido "wow, for the first time in history yau Jidda ta fada wa Umar abinda yake ranta" na rufe ido "practicing na fara, practicing yadda zan kula da mijina" ya saka hannunsa a seat din baya ya dauko wani karamin box a saka a tsakanin mu "bana bukatar ganin kunshi kafin in bada gift. Wannan maganar kadai ta ishi a bayar da tukuicinta"

Ya bude ya dauko sabuwar waya babbar harka exactly irin wadda take hannunsa ya miko min "a new phone for my new bride" na saka hannu biyu na karba ina bude ido "Abba fa yace karama zan rike" yace "sanda kina gidan sa ba, yanzu kin dawo gidan Umar" na mayar masa da kayarsa "zan je gidan Umar dai banje ba ai" ya dawo min da ita "yanzu kina gidan Aunty, gobe zaki je gidan gwoggo, jibi zaki zama matar Umar. Ni banji sunan Abba a ciki ba" na langwabe kai shima yayi irin yadda nayi "please amarya ta, kinga na gaji da saka kannena suna dauko min hoton amarya ta gwara ita ta dauko min da kanta. I don't want to miss out on anything. Duk wankan amarya ta ina so in gani"

Na dauki wayar ina juyawa "Nagode, Allah ya......." Yace "nayi miki charging, kawai sim card zaki saka" na kunna sannan na nemo camera nace "let's snap the first selfie"

Ko sunan Jamila bamu ambata ba........

Ba'a chanja vanue din kamu ba kamar yadda Farhan da Aunty suka nema. Sai dai Aunty ta hana ni tafiya gidan kamun da wuri sai da aka gama shirya komai a can mu kuma muka gama komai a gurin kyalliya sannan muka tafi, muna zuwa kawai zama muka yi aka fara gabatar da taron. Tun kafin mu zo already yan uwan Umar sunzo gurin, sunyi ankon su mai kyau kamar yadda nima nawa yanuwan suka yi nasu ankon.

Ni kuma shigar farar atamfa nayi mai adon green leaves, riga da aka yiwa pattern da ganyayyakin a wuyanta sai plain zani wanda da kyar aka daura min shi dan ba iya daura wa nayi ba😃, sannan kuma akayi min dauri mai kyau da dankwalin atampar, sai kuma aka lulluba min zani guda na atampar aka rufo shi har fuskata.

Gwoggo Habibah ce ta fesa min turare bayan Aunty ta biya kudin kamu cikin barkwanci da raha, sai da aka gama min barin turare sannan aka cire zanin da aka lulluba min aka cigaba da daukan pictures tare da chashewa.

Duk yayan gwoggo Habibah sun zo kuma dasu akayi komai banda Jamila ita kadai ce ban gani a gurin ba kuma nafi kyautata zaton bata gidan ma gabaki daya. Yayan gwoggon kuma sune suka dauki nauyin refreshment da duk aka ci a gurin kuma suka bayar da soveniers na turaren wuta, lalle, da hair brush.

Da daddare akayi kamun ango shima a can gidan su, bayan an gama ya kira ni yana ta mita "duk sunbi sunyi min wanka da nono, wata kakata ce tayi ta zuba min nono aka dama haushi na take ji ban auri jikar ta ba" nayi dariya "ayya my dear, sorry kaji?" Yace "dariya ma kike yi ko? Don't worry duk wannan karnin a jikinki zan goge miki shi jibi in Allah ya kaimu".

Friday da safe na dawo gidan mu, da azahar kuma aka daura aure na da Umar Faruq. Da yake babu nisa da gidan mu da masallacin da za'a yi kuma suna amfani da loudspeaker dan haka kusan a kunnena akayi komai, ana shafa fatiha gidan ya rude da guda da hargowar taya murna. At the same time kuma waya ta ta fara rurin kira daga angona amma naki dauka na saka ta a silent na kwanta na ja bargo na rufe har kaina ina jin wani iri a jikina, na rasa gane murna nake yi ko kuma akasin haka, wani irin feeling da babu wanda zai gane sai amarya a ranar da aka daura mata aure, wani irin feeling da yake tabbatar min da cewa am no longer Maijidda yar Umma da Abba, I am now Jidda matar Umar, and that tittle comes with a lot of responsibilities duk da dai a lokacin bansan girman responsibilities din ba.

Har yamma jikina a sanyaye yake, har aka fara shirin tafiya dinner. Da wuri muka fara shirin saboda Abba ya ja kunne sosai akan kar ayi dare, anan gida na shirya banje gidan kwalliya ba saboda tun kafin ranar Umar ya nuna min baya so "bana so mutane su taya ni ganin kwalliyar mata ta, ni kadai nake so in gani, ba dan su Bash sun dage ba ma ni bana son dinner din gabakidaya"

Wannan yasa Farhan ta dan gyara min fuska ta lightly sannan ta taya ni na shirya cikin kayan da ya dinka mana ni da shi, doguwar rigar yadi torquis blue, wadda ta bude daga kasa sosai sannan ta kwanta tana jan kasa daga bayana. A inda ta kwanta din anyi adon pink roses. Aira ta daura min head sannan suka taimaka suka yafa min pink veil din daya dace sosai da pink roses din bayan rigata, tun daga kan head dina kuma ya rufe har kirjina stylishly ba kuma tare daya bata kyalliyar ba sai ma kara mata kyau da yayi.

Gaba daya hankali na baya kan yabon da nake ta saku daga gare su da kuma pictures din da already suka fara daukana. Ni hankali na yana kan ango na wanda tunda ya zama nawa ban bar kaina naji muryar sa ba duk kuwa da kiran da yake ta rangada min, haka nan kawai naji kamar ina jin tsoron sa. Nasan duk abinda aure yake nufi kuma I thought na shirya amma sai yanzu da na riga nazo gurin sannan na fahimci ban shirya ba ashe.

Sai da duk masu tafiya dinner suka tafi aka bar mu a gidan daga ni sai Farhan sai Umma wadda taki zuwa sannan Umar ya kira Farhan yace mata gasu sunzo daukar mu.

Na tashi muka yiwa Umma sallama sannan muka fita. A soro na makale ina lekensa. Yana tsaye a gaban motar dana lura ta Bashir ce, sanye da kaya shigen nawa sai dai nasa sunfi nawa haske sai dai hular daya saka ce tayi duhun nawa kayan, fuskarsa kamar gonar auduga. Sai na ga kamar yau yafi kullum yi min kyau, yau da ya zama nawa sai naga kamar ban taba ganin mai kyawu irin nasa ba. Ina jin Farhan tana yi min magana a kunne amma banji mai tace ba ba kuma nason inji dan bana son abinda zaiyi distracting dina daga kallon mijina.

Ya tako yana kara fadin murmushin sa idon sa yana kyalli zuwa gabana yana ta rarraba ido a kaina yace "WOW. Anya kuwa an taba yin kyakykyawar mace a duniya kamar ki matata?" Na sunkuyar da kai na kasa nace "Nagode mijina" sai ya saka hannu and for the first time tunda muka hadu ya kama haba ta ya dago fuska ta yana kallon idona yace "no, ni zaki kalla ba kasa ba. Dai dai da second daya bana so ki kalli wani abun idan ba ni ba" and I did looked at him kamar ranar na fara ganinsa, bansan second nawa ne ya wuce ko minutes ba dan na shige cikin duniyar idanuwan sa sai da naji muryar Bashir yana magana "to zamu tafi dinner din ne ko kuma anan zamu tsaya ayi ta kallon kuda?"

Umar yace "shut up Bash. Go and find something to do ni na fasa zuwa dinner din ma, amarya ta kawai zan dauka in tafi gida" Farhan tace "impossible. Sai ka kara hakurin cigaba da gwaurontaka na kwana daya, kwana daya kacal"

Umar bai kula shi ba ya miko min hannu "come beautiful" na daga hannuna a hankali na saka a cikin nasa ina jin wani iri a jikina kamar wadda tayi wani abu ba dai dai ba, rike hannu da namiji a titin Allah🙈, yayi murmushi ganin yadda nake ta rarraba ido sannan ya rintse hannun nawa a cikin nasa har da saka daya hannun ya kara rikewa. Muka jera muna tafiya zuwa mota, yace "from wannan karkarwar jikin na fahimci wannan hannun Umar Faruq ne ya fara rike shi" nayi kokarin karbe hannu na ya hana ni, sai da muka je gaban motar ya kuma bude min na shiga sannan ya saki hannun ya rufe min kofa ya zagaya ya shiga kusa da ni. Yana zama ya sake lalubo hannu na ya rike duk kuwa da kokarin boye shi da nayi a tsakanin cinyoyi na, ganin yana kokarin saka hannu a gurin ya saka na bashi hannun da yake nema.

Bashir ya zauna a driver's seat Farhan tana kusa da shi, ya juyo ya na kallona "amarya wato ko gaisuwa babu ko?" Nace "au dama kana nan? Ai ban san da kai aka zo ba. I was busy looking at something special" suka yi dariya shi da Farhan, yace "wato baki ma gan ni ba kenan ko? Shikenan nima rana ta tana nan zuwa duk sai na rama. Na gama shirya wa kaf har kayan da zan saka ranar daurin aure na na dinka, abu daya ne ya rage min, amaryar" duk muka yi dariya nace "ga kanwata nan na baka" Farhan ta juyo ta harare ni "Allah ya sauwake ni kuwa a rasa wanda zai ba da ni sai ke" Umar yace "easy Farhan, yakamata kisan dawa kike magana, she is not your mate now, ta tashi daga just Jidda ta koma Mrs Umar."

Haka har muka

Please Login or Register in order to submit comment