Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne wai washegarin bikin mu" ya juyo da sauri tare da mike wa zaune "ni kuma da kika rufewa kofa fa, on our first night, ki ka saka na kwana akan kujera" na sunkuyar da ido na kasa ina jin nauyin laifina "kayi hakuri please"

Ya danyi shiru bai ce komai ba, but ina jin idonsa a kaina. Sai kuma naji yace "okay let's make a deal, kina so in yafe miki ko?" Na gyada kai. Yace "then earn it" na dago kai "earn what?" Yace "yafiyar. Ba a yin komai for free ai ko? Do something sai in yafe miki" nayi sensing wayo zaiyi min, na juya ido na nace "me zanyi in yi earning forgiveness din?" Ya jawo ni daga hannun kujerar na fado kan cinyarsa, nayi kokarin mikewa da sauri "na shiga uku" ya zagaye ni da hannayensa yana kara jawo ni jikinsa "baki shiga uku ba Baby girl, not yet"

Na cigaba da kokarin mikewa tsaye, he tighten his grip dole na hakura na sauke ajjiyar zuciya ina kallon sa nace "to me zanyi a yafe min din?" Yayi murmushi, his first smile of the day "kiss me" na bude ido "what? Ya kashe min ido "simple. Kiss me, sai in tabbatar da gaske kina sona akwai kwakwkwaran dalilin da ya saka kika rufe min kofa".

Na girgiza kaina da sauri amma kafin inyi magana sai ya rigani yace "either you kiss me or I kiss you. Choose one" ya fada yana daidaita fuskarsa kusa da tawa, idonsa akan lips dina.

Na saka hannayena biyu na rike fuskar sa sannan na tura ta baya ina dariya "wait wait wait. I will do it" yace "uhum, yanzu kika yi batu" nace "amma kasan dai ina jin kunyar ka ko? You have to close your eyes"

Yace "okay. No problem" ya rufe idonsa har da kara jingina da jikin kujera yana relaxing, na tsara ina karewa fuskar sa kallo, ban taba kallonta so close to me ba sai ranar and sai naga tafi kyau up close, murmushin sa yana kara mata kyau,

Yace "waiting........."

Nace "ban yarda da kai ba gaskiya, kana kallona ta kasan idonka, ya bude idon yana dariya "na rantse bana kallon ki" na harare shi "ba wani nan, ban yarda da kai ba"

Sai na saka hannu na cikin hijab dina na ciro dankwali na sannan na ninke shi yayi kauri na daga shi nace "rufe idonka, sai na daure maka sannan zan tabbatar baka kallona"

He obeyed and closed his eyes, ni kuma na daure masa idon da dankalin har na cije lebe dan in tabbatar ya dauru sosai, yayi dariya "mugunta ko?"

Sai dana chuchchusa na tabbatar ba zai ganni ba sannan na kyale shi. Sai kuma na tsaya ina kallon sa, ina kallon lips dinsa da suka yi curving yana murmushi and I felt so tempted to kiss him, for a second a thought I was going to, amma sai na ture hannunsa da suka saki a kan cinyata na tashi da sauri zan fita da gudu, sai dai ko taku biyu ban yi ba ya damko ni da hannu daya ya dawo dani jikinsa, then with one move ya juya zaman mu na koma nice a kan kujerar shi kuma ya bini da jikinsa, then with the other hand ya cire daurin da nayi wa idonsa.

"Gotcha"

ya fada yana dariya "yarinya kin mutu murus, ni zaki yaudara twice? Dama ance ko shaidan yana tsoron mata gashi daa jiya zuwa yau kin nuna min sau biyu" na fara karkarwa, ina jin nauyin sa kamar zai rugurguza kashina. "Na shiga uku, wayyo Umma, dan Allah kayi hakuri ba zan kuma yaudarar ka ba"

Yace "ai ba uku kadai kika shiga ba, tara kika shiga, uku sau uku kenan" ya fada yana rabani da hijab dina, na sake pleading, "dan Allah ka rabu dani" yayi wani murmushin da ba zan iya fassara ma'anar sa ba sannan yace "zan rabu dake if you ask me again in the next two hours"

Na bude baki zanyi protesting ya mayar min da magana ta zuwa cikina ta hanyar rufe bakina da nasa, na fara kokawa a hankali ita ma kokawar ta kare na koma nayi lakwas, falling inti his spell, abinda yake ta burin gani tun jiya sai da ya gani din ya tabbatar ba karya nake yi masa ba sannan bar forbidden place din amma wannan bai hana shi exploring other places ba, na barshi ya kama ni yayi leading dina to places, the places that I never knew existed sai da ya nuna min and gladly showed me around.

He took us out of this world, to cloud eleven, ya dawo damu and then decided to go back again. A hanya ne naji kamar ana buga kofa a cikin kaina, I decided to ignore it amma sai aka sake bugawa, this time har da kiran sunana akayi da dan karfi, and I finally came back to my senses sannan ne ma nayi realising what was happening. I realized situation din da muke ciki sannan na fahimci wani ne a bakin kofar falon da muke ciki yake knocking kofar yana kiran sunana, after some seconds na fahimci muryar Mufida sai kuma naji kamar ba ita kadai ba ce ba.

Cikin azama nayi kokarin raba shi da jikina, shi bai ma san me akeyi ba daga dukkan alamu, a tattara karfi na gabaki daya na ture shi baya sannan na zame daga kasansa na koma bayan kujera na buya "na shiga uku" ma fada ina rufe bakina da hannu na.

Shi kanshi bansan da wanne ido zan kalle shi ba ballantana kannensa da suke kokarin shigowa falon. Na kalli jikina, realising daga bra ta har rigata sunyi disappearing, I couldn't believe I let him see what he saw, and do what he did "Na shiga uku" na maimaita ina kokarin jan skirt fina zuwa sama amma yaki cooperating
jin haushin zuciyar data bani shawarar saka riga da skirt.

Naji yayi kokarin magana daga kan kujerar, muryar sa taki fitowa sai da yayi gyaran murya sannan yace "waye ne wai anan?" Naji muhibbat tace "yaya Doctor mune, ni da Mufida" yayi tsaki "go away! Me kukeyi anan ne wai" Mufida tace "Mama ce ta aiko mu"

Ya sake tsaki "go away I said, ko baku gane turanci ne yanzu kuma? Don't let me come out there in same ku a gurin nan" muhibbat tace "breakfast ne fa Mama tayi muku tace a kawo muku"

"Ku ajiye anan ku tafi"

Suka yi shiru duk su biyun, duk I can sense basu tafi din ba, sai Mufida tace "to yaya ina son magana da Jidda fa, akwai abinda zan nuna mata" yace "in kuka bari na fito na same ku a gurin nan sai na yanka namanku na cinye"

Nayi murmushi ina daga bayan kujera, sararsa kenan yace zai yanka mutum ya cinye. Ina jin motsin su suka tafi sai kuma naji karar tashin mota da bude gate, nayi mamakin yadda akayi bamuji shigowar su ba.

Shiru ya biyo bayan tafiyar su, ni in ta leke ta gefen kujera ina son inga inda hijab dina yake, dan shine kadai zai taimaka min a halin da nake ciki, ina kuma fatan kar umar ya zagayo bayan kujerar ya ganni.

Can na hango hijab din da nisa, babu yadda za'a yi hannuna yaje inda yake. Me zanyi ne kuma yanzu......

Option dina daya shine in roke shi ya miko min. Amma da wacce fuska zanyi masa magana?

Na danyi gyaran murya kadan "yaya Doctor?" Naji shiru bai amsa ba duk da na tabbatar in yana falon zaiji, to ko ya fita ne ban sani ba? Na kara daga murya na kira shi, wata zuciyar tana gaya gaya min ko ya koma bacci ne, amma anya kuwa? Na kuma kira "Umar?"

Daga saman kujerar naji yace "Yes, Baby" na daga kai a tsorace, ya leko da kansa ta saman kujerar harda yin tagumi da hannun sa yana kallona, nayi kara tare da dunkule wa a guri daya, "na shiga uku" na fada da karfi, yayi dariya, "wai sau nawa zaki shiga uku ne daga wayewar gari zuwa yanzu"

Na kara dunkule wa covering as much of my body as I can. "Dan Allah ka daina kallona, dan Allah ka bani hijab dina in saka" yace "a nawa? Na gaya miki yanzu an daina aikin banza. A nawa zan dauko miki hijab din?" Nace "dan Allah ai nace"

Sai nji ya sauka daga kan kujerar yana cewa "tunda kika ce Allah ai kin gama komai yarinya" ya dauki min ya miko min, sai kuma na kasa mika hannu na in karba, "kar bi mana?" Ya fada yana min murmushin mugunta, hawaye ya tarar min a ido "dan Allah ka ajiye a kasa, sai ka juya bayanka, ko kuma ka tafi dakin ka, ko ka tafi koma ina ne please just don't look at me"

Ya ajiye "shikenan cry cry Baby. Na tafi in dai Umar ne" sai dana tabbatar ya shiga corridor din da bedrooms din mu suke ya rufe kofa sannan na dauki hijab din na saka. Jikina har rawa yake yi. What have I done? Wannan abin kunya da me yayi kama?

A hanya na tsince tarkacen kayana da singlet dinsa, sannan na tafi dakina da sauri na rufe kofa na jingina da jikinta ina mayar da numfashi, sai kuma na kama zabga murmushi kamar tababbiya, na rufe idona tare da rungume kayan mu a kirji na ina bitar duk abinda ya faru, so shameful but so good.

Toilet na wuce na gyara jikina sannan na dawo dakin na mayar da kayana na kuma gyara dakin duk da ba wani gyara yake bukata sosai ba.

Yunwar da nake ji ta saka ni sake fitowa a raina ina fatan ba zamu kuma haduwa ba, na wuce na bude kofar palon sannan na dauko kayan abincin da na gani a gurin, na tuna da su Mufida ina lissafin abinda zasuyi tunani a matsayin dalilin da yasa Umar ya hana su shigowa.

Na shigo da kayan na wuce dining na jera su sannan na dauko abubuwan bukata a kitchen na kawo. Sai dana tabbatar komai ya kammala sannan na zauna na hada tea sannan na zuba chips da kwai dana gani acikin abincin da aka kawo na faraci da sauri saboda yunwar da take kwakular cikina, sannan kuma ina fatan in gama kafin dodo na ya fito.

Tunanin sa ya saka ni murmushi na rasa son sa nake, tsoronsa nake ji ko kuma kewarsa nake yi. Duk loma sai na daga kai na kalli hanyar da nake saka ran ganin ya biyo,amma ban san ko so nake ya fito din ko kuma bana so ya fito. A cikin satar kallon gurin da nake yi ne naga ya bude kofar ya fito, na kware da tea din da nake kurba.

Nayi saurin dauke kaina daga side dinsa amma image dinsa ya tsaya min a rai na. Wando ne a cikin sa three quarters da sleeveless riga, fuskar sa tayi fresh kamar wanda ya shafa hoda, gashin kansa yana kalli daga alama gyara shi yayi. But duk wannan bai ko kama kafar kyawun murmushin da yake kwance akan fuskarsa ba.

Ban yi magana ba har ya karaso ya zauna a kujerar kusa da tawa, na mike da sauri zan chanja guri sai ya saka hannayensa a waist dina ya jawo ni zuwa cinyarsa. "Na shiga uku" na fada ina kokarin sake mikewa. Ya dawo dani tare da cizon earlobe dina, nayi kara ina rike kunnen "in kika sake motsawa sai na kara miki wani, ba kuma lallai nan zan ciza ba next time"

Na murguda masa baki "wallahi sai na rama, dani kake zancen" yace "zanso kuwa inga ranar da zaki rama din. Sai dai ki rame ba dai ki rama ba" ya fara wasa da hannun sa a jikina cikin tsokana. Yace "ki rama in zaki iya"

Na shagwabe "yunwa nake ji dan Allah. Ka barni inci abinci please" ya jawo plate din dana zuba yace "same here, nima yunwar nake ji"

Muka ci abincin sosai, a plate daya, tea ma nawa ya shanye min nace sai ya biya ni sai ya hada mana wani muka sake sha tare, and I found that kunyar ta dan ragu bana jin kamar zan mutu.

Bayan mun gama ci ne ya jani muka tafi zagaya gida, muka duba ko'ina kuma a kowanne daki muna lissafin abinda muke ganin zamu chanja da kuma abinda za'a kara dan tsarin yafi kyau, kusan taste din mu duk iri daya ne a duk abubuwa, muka fita har waje and i found spot din dana ke ganin zanyi shuke shuke a ciki, "kamar na'ana'a, lemon grass, Ginger, lemon tsami, tumatur da attaruhu" ya amince sannan ya tabbatar min zai saka a samo min seedlings din sannan kuma a saka min taki a gurin.

Muna komawa ciki na tarar wayata tana ta kara a palo, na dauka sannan na rike baki. "Na shiga uku. Mufida ce, ni ban san me zance mata ba wallahi" ya karbi wayar daga hannuna and without saying anything to me ya amsa kiran "ki daina kiran ta haka, she is busy, sanda take free zata kira ki"

Na dora hannu aka, kafin inyi magana ya riga ni "na shiga uku" ya fada yana kwaikwayon magana ta.

Na dauki pillow zan dake shi ya rike hannun sai na dauko wani da daya hannun shima yayi sauri ya rike da daya hannunsa sai muka fara kokawa, na samu na cije shi a kunne irin yadda yayi min dazu, ya sake ni ya rike gurin nayi masa gwalo na fita a guje ya kamo ni ya hada ni da bango sannan ya matse ni da jikinsa muna haki a tare, sai kuma muka kama dariya.

Yace "Saura kwana uku ko?" Na juya ido na "saura kwana biyar" ya zaro ido "rinto zaki yi min? Jiya fa kika ce hudu yau ba saura uku ba" na tura shi baya "jiya shida nace maka, baka ji bane sosai" nayi kokarin guduwa ya dawo dani "na fahimci wannan yarinyar yawo zata yi min, I will have to be checking daily"

Na langwabe kai "yanzu baka yarda dani ba? Allah in na gama zan gaya maka" ya shafa side din fuskata zuwa wuya na and he kept going down. "In dai akan wannan maganar ne ban yarda dake ba, I lost my trust in you jiya da kika rufe min kofa, na fara kokarin fito da hannun sa daga cikin rigata amma maimakon yayi hakan sai ma ya hade bakin mu.

Da yamma ma an kawo mana lunch, a bakin kofa ta ajiye again sannan tayo min text

"Amarya. Ga abinci nan a waje, mu ajiye har dinner dan ba zan sake muku wani girkin ba. Sannan ga drinks nan inji Mama tace saboda baki, though in bakin sunzo ba lallai ne ku bude musu kofa ba"

Na karanta na mika wa Umar "ka ga abinda ka jawo min ko? Har abada ba zata daina tsokana ta ba"

Tare da shi muka fita muka shigo da abincin, sai muka tarar da cartoons na lemoka kala kala, muka kawo su duk store sannan muka goge fridge din da ko jona shi ba'a yi ba sai yanzu muka kunna muka zuba wasu daga drinks din, sai a lokacin naga kaji na na amarci, Allah yaso sanyi ne babu abinda suka yi, na saka a microwave na dumama, duk abinda nake yi yana makale a jikina, duk inda na dauke kafata a nan yake mayarwa yana yi min hira kuma yana using duk opportunity din daya samu gurin taba ni, in nayi mita sai yace aiki yake tayani, a karshe nace na yafe da tayin aikin amma yaki tafiya, a karshe dai a kitchen din muka yi lunch sannan mukayi wanke wanke, na tafi daki ya sake bina can ma, da kyar na zare shi daga jiki na na shiga wanka.

Sanda na fito baya nan, dan haka na samu na shirya a tsanake na tsara irin kwalliyar da na jima ina mafarkin zanyi wa mijina in nayi aure. Ni kaina nayi wa kaina da kaina kyau. Sai dai bansan me nene zai zamo outcome din kyalliyar tawa ba.

Ina fita falo yana shigowa, ashe fita yayi, yayo mana filling gas cylinder, ya siyo kayan tea sannan ya siyo attaruhu da albasar da yaji nace da da akwai da nayi peppe kitchen da kajin da nayi warming. Ya kuma siyo min pad, duk da ban nuna masa ina so ba amma yasan ba zan gaya masa din ba ko da ina bukata.

Ya saki ledar hannunsa yana kallona da sakakken baki, na danyi juyi a gabansa "nayi maka kyalliya. Nayi kyau?" Bai amsa ba sai ya taho inda nake, and he made sure yayi destroying dukkan kyalliyar kafin na kwace na shiga daki na rufe kofa. Ya zo ya tsaya a bakin kofar ya murda handle din sannan yace "dole ma inyi wani abu akan kofar nan"

Washegari kusan wuni muka yi da baki, yan'uwan Mama sunzo da yawan su Allah ya taimake ni su Mufida ma sun dawo dan haka suka taya ni karbar su, na dan samu sassauci daga takurawar Faruq saboda ganin idon mutane ya rage wasu abubuwan amma ba duka ba, bai damu daya rike hannuna ko ya jawo ni jikinsa a gabansu ba, sai dai ni in naji kunya in ture shi ko in matsa.

A lokacin ne naga Hafsat, ex girlfriend din Umar itama tazo har da babyn ta, kuma naji dadin yadda ta sake dani muka yi ta hira ina bata labarin makaranta da yake itama wai da taso school of nursing kuma bata samu ba. Ko a fuskar ta banga wani abu ba, ba dan Umar ya gaya min ita ce ba ma da ba zan sani ba.

The next day kuma yan uwan Baba ne suka zo suma a bisa rakiyar kannen Umar, basu jima ba su sosai suka tafi sai kuma yaya Mubaraka tazo da girls dinta su uku, ta bar su anan guri na ma taje unguwa ta dawo sannan ni da Umar muka je muka kaita gida a motarsa. She is very nice and friendly. 

A wadannan ziyarorin ne na ga yanuwansa sosai, dan da bikin ban wani fahimci kowa da kowa ba. Kuma na fahimci yadda yake faram faram da su kuma suma yadda suke ji da shi, daga dukkan alamu he is everyone's favorite.

Now, kullum Umar yana cikin lissafi "yau saura kwana daya" nace "uku dai, baka ji sosai ba lokacin" ya tabe baki "dan Allah ki gaya min gaskiya, da gaske shida kika ce dama ba hudu ba?" Nace "eh mana, baka ji dai dai ba" ya dafe kai "oh Allah, ni kuma tawa kaddarar kenan, Allah ka bani ikon cin wannan jarabawar"

Nayi dariyar yadda yayi addu'ar kamar wanda yake facing wani mummunan challenge, bayan sosai yake barje gumin sa dan banbancin sa da wanda ya samu full package kadan ne. Ina jin ma da ya samu din da sai yafi rangwanta min.

Ranar da na cika four days a gidan a ranar nayi wanka kamar yadda lissafi na yake, amma ko da wasa ban bari ya sani ba sai ma na saka pad da fatan in ya taba yaji zai hakura. Na kuma buya nayi sallolina ba tare da ya sani ba. A haka muka kwana, washegari kuma sai yace in shirya zai kaini gidan su in gaida Mama da Baba dan zasu koma Lagos.

Na shirya muka je, na kuma samu kyakkyawar tarba a gurin su musamman Mama da ta ringa ririta ni tana loda min kayan ciye ciye. Baba kuma har da tsokana ta wai nayi farin amarci. Dan haka lafiya lau nayi musu yini har magrib, a lokacin ne kuma mistake din ya faru, ina cikin sallar ni kadai a dakin Aunty Umar ya bude kofa ya shigo, ina sallar amma naji kamshin turaren sa nan take zuciyata ta tsinke, ta kuma fara lugude a kurjina.

Ya jima a tsaye yana kallona har na idar, nayi ta jan doguwar addu'a a sujjada ta wai ko zai gaji ya fita amma sai na ji ya ja kujerar gaban madubi ya zauna. Dole na dago na sallame. Na kasa dago kai na in kalle shi sai yace "uhum. Start explaining" nayi shiru yace "kwana nawa kenan?" Na daga masa dan yatsa daya, yace "ban yarda ba, maybe ma tun farko babu" na dago kai da sauri "wallahi Allah jiya ne kadai" yace "jiya da yau" ban amsa ba sai ya mike.

"Ki tashi kiyi musu sallama. We are going home now"

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only

*Episode Sixteen : Ummi*

Kafin in bashi amsa ya bude kofa ya fita, na jima a zaune, na kasa ma yin addu'a dan lugude kawai kirjina yake yi, anya kuwa sauran amare haka suke jin tsoro irin wannan? Anya kuwa ni nawa tsoron bai yi yawa ba?

Amma kuma shima kansa Umar din is not helping matters at all, shine ma yake kara tsorata ni wallahi. Misali yanzu, menene na wani cewa in tashi mu tafi yanzu, making me think of what will happen in munje gidan.

Na tashi na nade sallayar sannan na fara kokarin gyara fuska ta. Aunty ta shigo "ashe tafiya zakuyi Jidda? Yanzu naji Umar ya aiko wai ki fito in kin kammala"

Na dauke kaina gefe na juya idona, wato yasan in ya aiko zasu matsamin in fita tunda yana jira na,amma in ba haka ba ai ya gaya min already kuma zai iya kirana a wata ya sake tuna min.

Na juyo ina kirkirar murmushi, "eh Aunty, tafiya zamu yi" sai ta jani muka zauna a bakin gadon ta sannan ta jawo drawer ta dauko wata leda ta miko min "kinga wannan sister ta ce ta kawo min, sai naga da amare yafi dacewa shine nace bara in baki" na karba jikina yana bani ko menene a ciki, nayi mata godiya.

Sai kuma ta sake karba ta bude tana yi min bayanin yadda ake using. "Kinga wannan ma ance kamar yanzu za'a sha, bara in hada miki ki shanye kafin ku tafi dan in nace in kunje ki sha ba lallai ne ki sha ba" ta fita sannan sai gata ta dawo da cup a hannun ta ta bani ta ce in shanye, ina cikin sha ya shigo dakin yana duba agogon hannun sa, Aunty tace "gata nan zuwa sarkin gaggawa, wannan kai da maye ne in ka kama mutum sai ka kai shi lahira zaka rabu dashi" sai yayi murmushi kawai bai ce komai ba ya fita.

Muka fito palo nayi wa Mama sallama, sai ta bani wata leda ita ma ta gaya min spices ne a ciki na girki, "in akwai wani abun da kuke bukata a gidan ki kira auntyn ku ki gaya mata, kar ki kira gida, shi kuma in kin gaya masa ba lallai ya san inda zai samo muku wani abun ba, a hankali kema zaki san inda zaki samu komai. Na bayar ma za'a yi muku garin kunu tunda yana so, za'a aiko muku da shi" na durkusa nayi mata godiya na kuma yi mata fatan Allah ya kiyaye hanya.

Afnan tazo ta zauna a kusa dani tana yi min rada "Aunty zan biki kinji?" Na shafa kanta nace "maza dauko kayanki mu tafi" sai ta mike da sauri tana murna "mommy ki hada min kayana aunty Jidda ta yarda zan bita" Affan ya mike "wallahi nima sai naje mommy" Aunty ta girgiza kai "kuna da school gobe, ku bari sai da weekend sai kuje kuyi musu two days" Mama tace "da weekend din ma suna da islamiyya, sai dai in anyi hutu" suka fara rikici, sai na rarrashe su da cewa ai an yi hutun sai suje suyi min two weeks.

Sai dana fadi haka sannan suka fara murna, a lokacin ne kuma naji ana maganar Ummi ita ma bata

Please Login or Register in order to submit comment