Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki, bakin da zuwansu ya zamanto tamkar opener ta wami phase na rayuwar aurena. Bakin da zuwansu ya zamanto tamkar budar ido a gareni akan kaddara ta.

Ranar monday ne, Umar ya fita tun sassafe and he told me that he is going to be late saboda yana da wani surgery da zaiyi late evening a asibitin Dr Bashir. Dan haka tun rana nake kwance inata bacci na har sai da laasar tayi sannan na tashi na shiga kitchen nayi masa dinner dan ni ba wani cin abinci nake yi ba har yanzu.

Bayan na kammala girkin kuma na shiga nayi wanka na nutsu na shirya masa kwalliya irin wadda nasan yana so sannan na fito na dan gyagygyara gidan duk da dai kafin ya fita ya gyara ko'ina wai dan kar in tashi ince zanyi bayan ya tafi. Na dauko freshener na fesa a duk gidan sannan na samu guri na zauna na kunna kallo ina kuma chatting a waya ta, ina ta dariyar yadda ake zabga drama a WhatsApp group din Maman Maama novels, wanda Aunty Halima ta bayar da number ta aka saka ni kwanakin baya.

Ina yi ina duba agogo, magrib ta gabato sosai amma har yanzu shiru. Nayi tunanin kiransa kuma sai na fasa, bana so in kira shi yana tsakiyar aiki musamman in surgery ne.

Ina nan zaune naji tsayuwar mota sannan akayi horn, na tashi na leka ta window ina jin dadi a raina amma sai naga bakuwar mota ta shigo, bakar Panadol extra, na tsaya ina kallon motar har tayi packing sannan naga wasu mata su biyu sun fito.

Ban san su ba, ban taba ganin su ba sai a ranar. Suka fito suna karewa gidan kallo sannan daya tayiwa dayar magana suka yi dariya amma banji me suka ce ba. Sai kuma naga sun rufe kofofin motar sannan suka doso cikin gidan. Naga daya tayi gefe, sai dayar ta kamo hannun ta "ke kamar an chanja entry din fa. Kinga kofar nan"

Ina kallon su har suka zo sukayi knocking sai na saki labulen da nake tsaye a bayansa na zo na dube musu kofar. Suka shigo dul su biyun idon su a kaina Kamar yadda nima nake binsu da kallo.

Kyawawa ne duk su biyun, kuma kallo daya zakayi musu ka fahimci duk inda budewar ido ta kai to nasu idon yaje gurin. Sun sha kwalliya tun daga sama har kasa daya daga cikin su ta sha kitson attachment wanda akayi shi da colored zare kuma ya sauko har kan kafadar ta. Da maka makan glasses a idanuwan su. Banbancin su da kedarai kawai a fuska ne amma ba'a yanayin jiki ko kuma shigar da take jikin su ba.

Na fara tunanin su waye wadannan? Ni dai bana jin na san su a yan'uwa ko abokan aikin Faruq dan yanxu kusan duk collique dinsa na sansu saboda zuwa office dinsa da nake yi.

"Sannun ku da zuwa" na fada. Mai attach din ta sauke glass din idonta kasa tana kare min kallo tun daga fuskata zuwa kyakykyawan cikina daya fara girma. Sannan kuma tabi falon da kallo tana yamutsa fuska.

Dayar ce ta amsa min "yauwa amarya. Sannu da gida" na matsa baya ina nuna musu gurin zama. "Bismillah. Ku shigo ku zauna" suka biyo bayana suka zazzauna still suna ta kallon falon, irin kallon wulakanci din nan.

Naji abin ya taba zuciyata. Who are they? Daga gani sun girme ni nesa ba kusa ba, dan haka a ka'ida ni ya kamata in gaishe su amma sai naji na kasa gaishe su din. Na tashi na dauko musu lemo da ruwa na kawo musu bagansu. Dayar tace min "mun gode amarya" na dan yi mata murmushi kadan sannan na zauna.

"Ban gane ku ba fa amma" na fada hoping zasu fahimtar dani sai mai attach din tace "mai gidan yana nan ne?" Naji raina ya fara baci. Nace "baya nan. Yana office" sai naga sun kalli juna sun kwashe da dariya. "Su office manya" suka kuma wata dariyar. Yanzu raina ya kai kololuwar baci.

Marar attach din tace "dama munzo ne mu ganki kuma mu gaishe ki. Mu kuma yi miki Allah ya sanya alkhairi tunda ba'a gayyace mu biki ba sai a media muka ji. Allah ya kawo kazantar daki amma bata rashin shara ba. Though mun fara ganin alamun kazantar dakin tana hanya" ta fada tana kallon ciki na.

Mai attach din ta juyo itama ta kalli cikin ta tabe baki "in dai akan wannan aikin ne ai sai dai a bashi number yabo ta kasa. Shi din gwani ne ta wannan bangaren"

Na mike tsaye, ina jin wani irin zafi araina "please in ba zaku fada min ko ku su wa ye ba kuma ku fadi abinda ya kawo ku gidan nan ba you can take your leave please"

Suka mike a tare, mai attach din ta tako zuwa gaba na ta tsaya tana tauna cingam "kamar yadda kawata ta fada munzo ne mu ganki mu kuma ga dakin ki. Kuma mun gani. Dama na gaya masa zanzo mu gaisa but ya dauka da wasa nake masa shi yasa muka zo da yamma hoping ko zamu same shi a gida dan in tabbatar masa ba da wasa nake ba, but ashe yana 'office' kamar yadda ya gaya miki. Nevertheless, zan bar masa sako"

"In yazo ki gaya masa Zuwaira tazo ta kawo muku ziyara tare da fatan alkhairi. Zancen su waye kuma mu idan kin gaya masa haka sai ki tambayeshi shi zai fi kowa yi miki bayanin ko wacece ni"

Sai ta juya gurin kawarta "ko ba haka ba kawata?" Sai suka tafa, kawar tace "naso ace mun same shi wallahi, naso inga idon sa, munafukfuk" suka sake dariya sannan wadda ta kira kanta da Zuwaira ta duba agogon hannun ta "mu tafi haka, na bar clients suna jira na, kin san akwai amarya da nace miki zanyi wa gyaran jiki yau" kawar ta harare ta "kema munafuka daya, ko dai katoton client ne yake jiran ki? Tunda ance bai dawo daga 'office' ba" suka sake dariya sannan suka kama hannu suka fita.

Suka bar ni a tsaye tamkar gunkin da aka sassaka......

*One more free Episode*


*Episode Eighteen : Zuwaira*
Tun da suka fita ban iya komawa na zauna ba. Ji nake yi tamkar na hadiyi tabarya dan wani dogon abu ne ya tsaya tun daga makogwarona har zuwa kafafuwana.

Dan cikina naji yana ta tsalle kamar wanda oxygen dinda na ke shaka bata isar mu ni da shi.

Kwakwalwa ta tana ta kokarin assessing maganganun su amma zuciyata taki bata dama dan bugawa take yi da tsananin karfin da har cikin kunnuwa na nake jin karar bugun ta.

Babu abinda nake so inji irin amsar su waye wadannan kuma menene fassarar maganganun da suka zo suka yi? Sunce suna min fatan alkhairi amma ko kadan banga fatan alkhairi a tattare da su ba. Me suke fada akan Umar? Me suke fada akan mijina?

Motar su bata jima da barin gidan ba naji shigowar ta sa. Ya bude kofa ya shigo fuskar sa da murmushi "sorry Baby, na barki kina ta jirana ko?" Sai ya daga ledar hannun sa yana nuna min "wannan agwalumar sai da na zagaye Kano kaf kafin in samo miki ita, shi yasa ban dawo da wuri ba"

Sai a lokacin na tuna da cewa na bashi sakon agwaluma. Nayi kokarin hadiye wannan dogon abu sannan nace "sannu da zuwa dear" sai ya bude min hannayensa. Come and give me a hug now, don't just stand there like a statue"

Na yi kokarin takawa amma sai na kasa, sai ya ajiye ledar shi ya taho ya saka ni a kirjinsa ya rungume tare da kissing saman kaina. "Kinyi kyau sosai Baby" ya sunkuyo yayi kissing ciki na. "Hey there little Jidda. Kina ta jiran Daddy ko?" sai kuma ya dago fuskata "what's wrong. Yana ganki wani iri ne" sai ya saka hannunsa a wuyana yana testing temperature dina. "jikin ki yayi zafi, are you sick?"

Yadda ya nuna concern dinsa sai naji ya taba zuciyata. Karyar banza ma suke yi wadancan mutanen a kansa, har zasu saka inyi tunanin daga wani guri yake ba daga inda yace min ba, daga wani mummunan guri. Na girgiza masa kai "no am fine. Kawai dai mood dina ne bana jin dadinsa" ya sake ni "ahh. The mood swings. Me zanyi ne in cheering dinki, ga agwaluma nan dai na siyo miki, in still baki ji dadi ba in nayi wanka sai in fita dake yawo. Ko muje gidan Aunty Afia ko gidan yaya Mubaraka duk wanda kika zaba"

Na je na dauki ledar daya ajiye ina jin kamar babu abinda na tsana irin agwaluma. Na ajiye nace "na gode. Ga abinci nan a dining zaka ci ko a nan" na nuna jikinsa "bara in yi wanka first. Ko zaki zo ki taya ni?" Ya fada yana kashe min ido. Na sunkuyar da kaina bance komai ba. Yace "not in the mood right?" Sai yayi ajjiyar zuciya "yaya dan Adam zaiyi da ransa tunda yayi wa matarsa ciki dole ya dauki hakurin duk abinda zai biyo baya"

Ya wuce ni ya shiga corridor.

Na zauna akan kujera ina rungume ledar agwalumar daya siyo min a kirjina. Ina sake tambayar kaina suwaye bakin da nayi dazu? Su waye su da har zasu zo su saka min shakku akan mijina? Har suna dariyar cewa nace yana office, har suna making jokes with it, making me think yana wani gurin da bai dace ba ashe shi ni ya tafi nemo wa abinda nace masa ina so. Sai naji banji dadin yadda nayi masa ba.

"Karyar banza" na fada a fili, sai maganar tawa ta tuno min dawani memory na last time da na fadi wadannan kalmomi. Lokacin da Jamila ta same ni a daki ranar kunshin biki na, naji kunnuwa na suna dawo min da kalamanta dana tura su na boye a deepest part of my mind.

"Karyar banza" na sake maimaita wa ina kokarin hada memory din maganganun ta dana wadannan matan in tura su zuwa inda na fito da natan yanzu. Amma sai suka ki tafiya, suka tsaya suna zagaye a kwakwalwa ta.

Na ajiye ledar nabi bayansa na tarar har ya shiga wankan sai na bishi toilet din na tsaya a bakin kofa ina kallon sa yana cire kaya. Ya langwabe kai "please ki zo ki taya ni mana. I will cheer you up i promise you. Duk wannan mood din zan chanja shi" naje na karasa balle masa buttons din rigarsa sai ya fara kokawar cire min tawa.

Na rike rigar "ni fa nayi wanka na wallahi" yace "wanka ai baya yawa, sake wa zaki yi" na fara mita "kai wallahi sai ka saka mutum mura kayi ta saka mutum wanka kamar wani kwado" ya karasa cire rigar sannan ya jani cikin shower ya hadani da jikinsa da hannu daya daya hannun kuma ya kunna shower dashi, ya sunkuyo dai dai fuskata yace "I will warm you up" sannan ya hade bakin mu......

Sai daya tabbatar ya karbi dukkan abinda yake so ya karba sannan muka fito daga toilet din, ina ta mitar ya sakani na jika gashina bayan da kyar na samu nayi drying dinsa dazu. Shi kuma as usual yana ta lallaba ni. A karshe ma sai ya dauko hand dryer dina yace zai yimin drying gashin.

Na zauna a gaban madubi yana min drying gashin ni kuma ina shafa mai, sai nayi masa maganar baƙin sa.

"Dazu kayi baƙi dear" yana cigaba da abinda yake yi yace "nayi baƙi ko munyi baƙi? Su waye?" Nace "oho. Nima abinda nake so ka gaya min kenan" ya dakata da abinda yake yi muna kallon juna ta madubin, his face looked tensed.

Nace "daya daga cikin su tace min sunan ta Zuwaira. Tace in na gaya maka haka zaka gane kuma zaka gaya min wacece ita"

Ya ajiye dryer din yayi two steps back. In ka kalli fuskarsa zaka dauka fatalwa ya gani. "What?" Ya tambaya his voice deep. Na mike tsaye sannan na juyo muna kallon juna. Na gyara bath robe din jikina ina kara studying dinsa, zuciyata tana so tayi placing reaction dinsa.

"Su waye?" Na tambaya. Ina kallon shi ya hadiye wani abu a makogwaronsa sannan yace "how can I know. Ni da ban gansu ba, you tell me su waye ke da kika gansu" naji mamakin maganar sa.

"Ban gane ba. But you sounded and acted as if ka san su, as if kayi mamakin da nace maka sun zo" ya tako ya dawo gaba na yana kallon fuskata. "Ni ban san wata mai irin wannan sunan ba, ni ko a family da friends dina da kuma abokan aiki na ban san mai irin wannan sunan ba. Yes I was surprised saboda kin ce sun ce zan fada miki ko su waye su so I automatically know sunzo su tayar min da fitina ne"

Nace "but yanayin yadda suka yi magana ya nuna sun sanka Umar. Har magana fa naji sunyi akan wai an chanja tsarin gidan da ba haka yake ba......."

Ya dafe goshinsa, looking frustrated. "They can be anybody Jidda. Zasu iya zama yan leken asiri ko wadansu masu mugun nufin ko kuma su zama one of those girls dana fada miki might be crushing on me, yanzu sunji nayi aure shine zasu zo su gaya miki maganar banza. And you are sounding as if kin yarda dasu haba Jidda. Wacce yarinya ce kuma zata zo tace tasan gidan nan gidan da in ba sisters dina ba bana jin akwai wanda ya taba zuwan sa kafin muyi aure, nima kaina ban taba kwana a gidan ba sai da kika shigo shi"

Na dauke kaina gefe ina lissafa maganganun sa. They sounded real. Zata iya yiwuwa da gaske a cikin masu son nasa ne shine zasu zo da wannan maganar to hurt me.

Ganin maganar ta shige ni sai ya kamo kafaduna. "Did they hurt you?" Na girgiza kaina "not physically" ya hade rai "me da me suka ce?" Nace "just some stuffs about you. Wai ba daga office kake ba. Wai kana can kana jiran ta. And they said something about cikina"

Ya bude ido ya dora hannu akan cikin kamar mai protecting dinsa "me suka ce akan cikin?" Sai yanzu naji dacin maganganun su yana kara kona zuciya ta "na dora nawa hannun akan nasa a saman cikin, hawaye ya silalo daga idona nace "wai kafi gwanancewa ta wannan bangaren, wai za'a iya baka numbar yabo a wajen"

Ya saki kafada ta ya saka hannunshi a cikin gashinsa looking very angry, "damn it" sai naji banji dadin yadda na bata masa rai ba. Dana sani ma da ban gaya masa ba na bar maganar a raina kawai ni kadai tun da dai karya suke yi.

Ya juya ya daki kofa da hannunsa sai kuma ya rike hannun alamar yaji zafi sannan ya bude kofar ya fita. Nayi sauri na nemi kaya na saka a jikina nabi bayan sa. Baya falo, na dawo na duba dakina can ma baya nan har na fara tunanin ko fita yayi sai kuma na leka naga motarsa tana nan.

Ina kokarin tashi inje inyi sallar da naji ana yi a masallaci sai gashi ya sake shigowa daga waje, ransa a tsananin bace kamar ma yafi sanda ya fita bacin rai. Bai ce min komai ba ya wuce ni ya shiga dakin sa ya rufe kofa. Na tashi na bishi sai naji yayi locking kofar dan haka na wuce nawa dakin nayi alwala na tayar da sallah.

Na jima akan sallayar bayan na idar ina ta saka wa da warwarewa. Ina ta so in dai daita tunani na ya tafi a direction daya amma na kasa. Shin menene gaskiyar maganar? Da gaske bai san su ba? Da gaske sunzo ne dan su hada mu? Ko kuma dai akwai abinda yake boye min kamar yadda na gani a fuskar sa a first moment dana kira sunan Zuwaira. Who is she?"

Ban san amsar ba, amma kuma na saka a raina cewa tabbas sai na binciko ta na kuma warware kullin data daura min a zuciya ta.

Anan na zauna har aka kira sallar isha nayi sannan na sake fita inga ko ya fito, banji motsinsa ba na dawo na kwanta a falo ina chatting da friends dina, trying to take my mind off duk abinda ya faru, daga baya kuma na mike na hada tea na sha sannan na tafi dakina na fara shirin kwanciya.

Sai da na gama komai na kashe fitila na kwanta sannay kuma na fara jin haushin Umar, me yasa zaiyi fushi da ni kuma? Me nayi masa? No da akayi wa laifi ba ni ya kamata a lallaba ba kuma sai ayi fushi dani a rufe min kofa? Nayi tsaki ya kai cikin charbi, in naji haushin sa sai kuma inji haushin kaina da nake jin haushin sa.

Zuwa can bacci ya fara dauka na sai naji motsin an bude kofa an shigo dakin. Ya kunna fitila sannan ya kashe na hawo gadon ya shigo cikin rufar da nake ciki sannan ya saka hannu ya jawo ni ta baya ya hada ni da kirjinsa, nayi kamar banji shi ba sai ya fara min magana

"Am sorry Baby, na rufe dakina ko? Raina ne a bace bana son zama inda kike kar in miki tsawa ko in gaya miki wata magana marar dadi, shi yasa na rufe kaina sai da na huce tukunna. Kiyi hakuri kinji?" Yayi kissing bayan kunne na.

Nayi shiru nayi kamar banji shi ba. Amma kuma a zuciya ta sai naji na daina jin haushin rufe kofar da yayi. Ya cigaba da cewa. "Dama na taba gaya miki tun kafin bikin mu cewa zamu iya samun matsala irin wannan a gidan nan. Akwai yammatan da ni ban ma sam dasu ba da suke kallon kansu a matsayin yammata nane, while ni kuma ba haka bane ba a wajena, kuma nasan wadansun su dole zasu iya yin kokarin yin wani abu dan su shiga tsakanin mu, bazan iya hanasu ba Jidda tunda bansan plans din su ba amma ke zan iya warning dinki dan ki san da su kuma ki toshe kunnuwan ki da kuma zuciyarki daga dukkan abinda zasu zo su gaya miki"

"Nasan akwai wadanda zasu iya zuwa su yi kokarin hada mu, yes, amma bansan har zasu kai ga fadar maganar da zata saka miki zargi na a zuciyarki ba Jidda. Wannan shine abinda ya bata min rai sosai. Kuma the fact that na gani a idonki cewa kin yarda da abinda suka ce shi yafi komai daga min hankali. How can you believe such a lie?"

Ya fada kamar zai yi kuka. Na juyo ina kallon sa, sai kuma na gyara kwanciya ta na juyi sosai muna facing din juna, na saka hannu ina wasa da sajensa sannan nace "ba wai na yarda da maganar su bane ba akan ka. Ba wai na yarda da maganganun banzan da suka fada bane ba. But I believe somehow akwai sanayya a tsakanin ku. Sun sanka tabbas, kuma sanda na ambaci sunan yarinyar nan sai naga kamar kai ma ka gane ta. I just want the truth shikenan"

Sai ya cire hannu na daga fuskar sa ya fara kokarin mikewa. "Na gaya miki ban san ta ba, ban san taba. Me yasa kuma zaki cigaba da tambayata? Ni da ace nasan su waye da yanzu suna hannun police dan ba zan kyale su ba wallahi" na mike zaune nima nace "well, I can describe them, and their car. Har number din motar na rike" ya juyo da sauri yana kallona duk da cikin duhu ne. Na daga masa kafada "maybe in na bada description din su police zasu iya nemo su"

Sai ya mike bai ce komai ba ya fita daga dakin, har na dauka wani fushin ya kuma yi sai gashi ya dawo da jotter a hannun sa da biro, ya kunna fitila sannan ya zauna a bakin gado.

"Oya fada min duk abinda zaki iya tunawa in rubuta, gobe sai in biya ta police station in shigar da complain, cos zasu iya sama masu yiwa robbers leken asiri. Na kuma gaya wa mai gadi daga yau kar ya sake barin kowa ya shigo sai yazo ya gaya miki waye kuma kin yarda tukunna"

Na gyada kai sannan na fara zayyana masa tiryan tiryan duk abinda zan iya tunawa na daga kamannin su da kuma motar da suka zo da ita da kuma maganar da suka yi. A karshe nace "kamar daya daga cikin su tana yin gyaran jiki na mata. Dan naji tayi magana mai kama da haka. Kuma kamar shago ne da ita da take yin aikinta a ciki" sai na ga ya dan ajje biron ya dan dage goshinsa kadan sai kuma ya sake dauka ya rubuta abinda na fada.

Sai da ya gama ya ajiye takardar, ni kuma na dauka na tabbatar ya rubuta duk abinda na fada sannan nace masa "baka ci abinci ba, kar ka kwanta da yunwa bara in kawo maka nan kaci" ya girgiza kai "no, kiyi kwanciyar ki kawai, zanje in ci" ya sauka daga kan gadon kamar zai fita sai kuma ya juyo yana min murmushi "but don't sleep fa. Ki jira ni inyi miki tatsuniya" na gyara kwanciya ta "tatsuniya bayan wacce kayi min dazu? Nagode Allah ya saka da alkhairi" ya marairaice "mutum dai zaiyi bacci ai zai so a lallaba shi ko?" Na girgiza kaina. "Ni zan iya lallaba kaina"

Washegari da zai fita ni da kaina na dauko takardar na saka masa a hannun sa "kar ka manta" ya saka a aljihunsa "ina sane ai. I will never forget"

Sannan ya sunkuya gaban cikina "bye bye little Jidda" na juya ido na "ko kuma little Umar ba" ya daga yana dariya "kar kiyi wa kanki wannan fatan. I wasn't that cute sanda ina yaro dan lukuti ne da dan mitsitsin hanci da baki, duk kumatu ya cika fuskar" nayi dariya "zan so in ga pictures din ka" ya zaro ido "ko da wasa ba zanso ki gansu ba, salon ki ce kin fasa. Ai da na girma a haka ko da na tabbatar baki ce min yes ba" na girgiza kai na. "Sanda na fara sonka ban ma kalli fuskarka ba. Bana jin kuma ko wanne kama zan ganka da ita a lokacin zata chanja abinda naji a zuciyata a game da kai. Besides, lukutayen mutane are cute"

Ya bata rai "kar kisa in fara hada kiba dan kike ce min cute fa" sai muka yi dariya tare. Forgetting about all the tensions na jiya.

Sai dai ban manta ba, yana dawowa ya cire kayansa na duba aljihun hoping inga babu takardar but it was there, exactly yadda na ninke ta daga alama ma ko bude ta ba'ayi ba. Na tsaya da ita a hannu na zuciyata tanayi min zafi, me hakan yake nufi? Dama bashi da niyyar reporting din kawai ya shirya min karya ne? Dama kamar yadda nayi tsammani already ya santa, bashi da niyyar bincikar ko wacece ita" na ajiye rigar da sauri na tafi zanje falo gurinsa amma sai zuciyata ta tunamin wani abu. In naje ma zai iya ce min mantawa yayi, ko kuma ya sake shirya min wasu kalaman. Ni kuma yanzu so nake in tabbatar idan har da gaske ya sanya din.

Na mayar da takardar inda na ganta sannan na ajiye kayan kamar yadda ya ajiye su na fita, na tarar dashi a falo suna wata da Mama, suka gama ya bani nima muka gaisa tana tambayata saukin jiki. "Akwai wasu magungunan gargajiya na yarabawa, in zan dawo zan taho miki dashi suna taimaka wa mata sosai musamman in ciki yayi nauyi da kuma lokacin haihuwa" nayi murmushi kawai ina jin dadin yadda take damuwa da ni da cikina.

Bayan na ajiye wayar ne nace masa "ya zancen zuwa gurin police din kuwa? Kaje ?" Bai kalle ni ba yace "naje, can na fara zuwa kafin ma in karasa asibiti, sun karbi takardar kuma sun tabbatar zasu binciko min su, sunce babu matsala musamman tunda akwai plate number din mota ba zasu yi

Please Login or Register in order to submit comment