Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wahalar samu ba"

Na dauke kaina gefe ina jin tamkar garwashin wuta ya dauka da hannun sa ya saka min a zuciyata. Wasu hawaye masu zafi suka taho min nayi sauri na hadiye su amma sai naji tamkar sun kara min zafin da yake kirjina. Wato wasa kawai yake min da hankali tun jiya. Tun jiya ko kuma tun kafin muyi aure?

Tabbas ya san su, ya san wacece wannan Zuwaira din, shin amma abinda ta nuna min akwai a tsakanin su menene gaskiyar wannan maganar? Sai naji ba zan iya zama a gurin ba dan sosai nake so inyi kuka. Na tashi na shiga kitchen na turo kofa sannan nayi kuka na silently, still maganar Yaya Jamila tana sake tugging zuciya ta. "I gave him myself" na girgiza kaina da sauri. "No, please God no"

Na jima a kitchen din sannan naji motsinsa ya taho, na dauko albasa na fara yankawa duk da babu amfanin da zanyi da ita, ya turo kofar yana kallona "Baby zan dan fita amma bazan jima ba zan dawo, zamu hadu da Bashir ne" ya danyi dariya "kinsan mutumin yana ta kokarin ya shiga daga ciki fa, to gidaje zan taya shi dubawa" ban kalle shi ba kuma banyi dariya ko murnar cewa Bashir zaiyi aure ba dan sam hankali na baya gurin maganar sa, I was in no mood for that.

"A dawo lafiya" na fada shortly, hoping zai fita ya barni da hawayena, amma sai naga ya karasa shigowa "are you okay?" Ya fada cikin concern. Naji kamar in kikkifawa kyakykyawar fuskar sa mari amma sai na dauke kaina na cigaba da yankan albasa ta. "Lfy ta kalau fa. Kaje kawai a dawo lafiya" sai ya ja kujera ya zauna. "In ba kya so in fita na fasa, zan kira shi ince ya sake booking dina next time. Yanzu Baby bata so"

Na juyo ina kallon sa, sai kuma ya mike ta karbe chopping board din da yake hannuna ya ajiye a gefe "ji albasar nan yadda tasa idon ki yayi ja? Me zaki yi da ita wai? Ba naga akwai abinci ba zai ishe mu har dare? Please ki je ki zauna ki huta in wani abun kike so daban ki gaya min sai in taho miki da shi a waje" na wuce shi ina cewa "okay. A dawo lafiya to"

Ban tsaya a falo ba na shige cikin daki. Ina dakin naji tashin motarsa and for the first time tunda muka yi aure sai naji ina tambayar kaina inda zashi, naji ban yarda da abinda ya gaya min ba a matsayin gurin da zashi. Ko gurinta zai tafi? Zuwairan?

Na bude kofa ta na shiga nasa dakin, kayan suna nan a inda na barsu, na dauka na sake duba aljihun amma yanzu babu takardar a ciki. Ya fita da ita. Kuma na tabbatar zuwa zaiyi ya yar da ita dan na tabbatar mantawa yayi ba yar da ita din ba tun dazun.

Na ajiye kayan na sake komawa dakina na kwanta ina shafa cikina. What is happening?

Ban kuma tayar masa da maganar ba shima kuma bai kuma yin maganar ba, nayi kamar na manta amma abin yana cikin raina kullum dashi nake kwana da shi nake tashi. Burina kawai in san wacece ita in kuma sam dalilin da yasa yayi min karya yace bai san ta ba.

A haka har hutun mu ya kare na koma school na shiga third year dina wadda kuma ita ce final, one month into the semester ne mukayi first wedding anniversary din mu, a lokacin kuma cikina kadan ne bai karasa wata takwas ba. Ya girma sosai yayi nauyi ga lafiya dan kullum abin cikin cikin tsalle tsalle yake kamar wanda yake filin ball.

Sosai Umar yayi celebrating dina ranar anniversary din mu. Ya cika social media da kalaman soyayyar sagare ni ni kuma na biye masa na shiga nima nayi ta mayar masa da amsa yan'uwa da abokan arziki suna ta taya mu murna.

Daya dawo gida daga office kuma sai gashi ya kawo min golden necklace da sabuwar laptop a matsayin anniversary gift, naji dadi sosai na makalkale shi ina ta murna sannan muka shirya muka ci kwalliya muka fita yawo. Muka je gidan mu muka je gidan su, sannan muka je KFC (Kano fried chicken) muka yi dinner da wata fried rice din su na yasan ina so sosai, daga nan muka je see sweet and bakery muka sai ice cream muka hau baranda din su ta can sama muka sha muna hira iska tana kadamu, renewing our love for each other.

Bayan mun gama kuma muka siyo kayan ciye ciye muka dawo gida, a gidan ma kuma I let him celebrate in his own way, duk da dai nauyin da nayi yanzu ya saka yana dan rangwantamin dan lokuta da yawa ma yakan barni inyi baccina kawai amma ranar sai daya karba.

Washegari na tashi da ciwon jiki, activities din jiya suna tambaya ta ga kuma gajiya da Umar ya tara min da daddare. Tun da nayi sallah na lallaba na koma na kwanta ina jinsa yana ta shirin fita amma na kasa tashi, yazo gabana ya durkusa yana leka fuskata "hey Baby" na dan yi masa murmushi yace "yayane" na bata rai "ba kai bane na ka saka min ciwon jiki" yayi murmushi yana gyara min gashin fuskata ya kwaikwayi magana ta "ba ke bace ba kika yi kyau da yawa" na murguda masa baki yayi dariya.

"Akwai school fa" na juya baya na "ni ba zanje ba" ya ce "it is okay. Kiyi kwanciyar ki nima ba dan ina da abubuwa da yawa ba da ba zan fita ba, da zama na zanyi in yi jinyar baby na" na juyo "no, kaje kawai. Na san in na huta sosai shikenan" ya girgiza kai yace "bayan kin huta kuma sai kin ci abinci ai" na tura baki ya kama lips din, "yes, sai kinci abinci. Let me get us something mu ci"

Sai ya tashi ya fita, na juya na koma baccina zuwa can naji shigowar sa, ya tashe ni na zauna sannan ya jawo mana table ya dora mana plate din indomie da ya dafa mana da kwai ga kuma tea, dama ya iya dafa indomie sosai dan sau da yawa in dai ita zamu ci to shi ne yake dafa mana. Muka cinye tas muka sha tea sannan na koma na kwanta, har da kawo min robar ruwa kusa dani wai ko zan nema ba sai na tashi ba, sannan yayi min sallama ya fita.

Yana fita nakoma bacci na, bacci mai nauyi wanda ban farka ba har kusan karfe biyu, shima kuma nepa ne sula dauke wuta zafi ya tashe ni, ina farkawa wayata na fara dubawa dan nasan ya kira kuma naga two missed calls din sa, nayi murmushi na kira shi bugu daya ya dauka. "Baby na ta tashi daga bacci" nayi murmushi "amma bai ishe ni fa, nefa sun dauke" yace "bara in kira mai gadi ya kunna miki gen" na ce "nooo, baccin ya ishe ni haka ai. Gwara in tashi in dan motsa miki na kuma inyi sallah"

Yace "Okay. Amma kinji dadin jikin?" Na dan yamutsa fuska "har yanzu ciwo" yayi dariya "bana son shagwaba Baby, ki bari zan dawo in yi miki tausa" nace "kayi min tausa ko kuma ka kara min gajiya. Kai ai wayo ne da kai"

Muka jima muna hirar mu sannan muka yi sallama na tashi nayi sallah sannan na koma na kwanta, na dauko waya ta na kira Farhan muka yi hira tana gaya min drama din da a ke tayi a social media har screen shot din kalaman da mukayi da Umar ake yi ana sharing. Nayi dariya sannan nace mata bara in duba.

Na bude ina ta replying messages din mutane a WhatsApp, sannan naje facebook shima nayi sai kuma naga friend request da yawa, a ciki na san akwai na friends dina da har yanzu bamu hadu ba.

A hankali nake bi nake zabar wadanda na sani ina accepting wadanda ba sani ba kuma ima rejecting har nazo kan wani suna daya dauki hankali na. "Zuwaira Abdulkadir (Zuzu)" Gaba na ya fadi, na danna kan profile picture dinta ya bude min and there she is, kallo daya nayi wa hoton na gane ta duk da cewa ta sha kwalliya kamar wata amarya ranar bikinta.

Na shiga profile dinta farkon abinda na fara dubawa shine friends dinta, and Umar Faruq Dikko was listed as our mutual friend. Na lumshe idona na bude ina jin zafin karyar da yayi min yana sake dawowa. Nayi ta dubawa cikin posts dinta wadanda mostly akan tallan saloon din ta take yi sai pictures dinta da take yawan sakawa da sunan yin tallan kwalliyar da take yi. A kowanne hoto tana samun 1k+ likes da kuma hundreds comments. But a iyakacin dubawa ta banga na Umar ba.

Na dawo kan friend request din data turo min, ina duba options din accept and reject da facebook suka bani, na sani cewa kamata yayi inji rejecting in wuce gurin amma zuciyata tana son sanin wacece ita kuma menene alakar ta da mijina da har yayi min karya akan ta duk da takowar da tayi tazo har gida na.

Sai kawai na danna accept. Sannan na fita daga facebook din na ajiye wayar na tashi na fara gyara gida na da tun safe ban gyara shi ba. Da yake babu datti, nan da nan na gama na gyara ko ina fes na saka turaren wuta sannan nayi wanka na fito nayi sallar laasar. Ina idarwa na sake ganin missed call dinsa, na kira shi back ya na tambaya ta jikina nace masa na warware, duk na jishi agajiye sai yace min tun safe bai zamu zama ba ya gaji sosai gashi akwai wani aiki da zasuyi yanzu, amma yana gamawa zai taho gida. Daga haka muka yi sallama.

Na shiga kitchen na dora abinci sai ma dawo palo na kunna kallo, ina yi ina shan fruits dina ina kuma duba girki nahar na gama na kawo dining na ajiye, a lokacin ne na sake dauko wayata da niyyar duba ko an sake turo min wasu congratulatory messages din, sai tunanin sabuwar facebook friend dina ya zo min, sai na bude messanger ta na fara duba can.

Ina budewa kuwa na ga sako daga gare ta,

"Hi"

Na jima ina duba wa, wata zuciyar tana gaya min inyi ignoring wata kuma tana gaya min in amsa dan in samu amsar tambayoyi na. Sai nayi replying

"Salam"

Two seconds sai gata online, ta turo min

"Amarya ya kike? Ya unborn?"

Sai naji haushin kaina dana kula ta in the first place, har nayi niyya fita daga chat din sai ta sake turo min message

"Ina angon? Ko yau ma har yanzu yana office. Lol"

Naji raina ya fara baci. Na bata amsa

"Inda yake, da kuma abinda yake yi ba abinda ya shafe ki bane ba"

Sai ta min reply

"Really? Ko da kuwa inda yake din gida na ne kuma abinda yake yi shine bacci akan kirjina?"

Naji wani abu ya daki zuciyata har wani duhu ne ya ratsa ido na. Na dafe kaina ina kokarin dawo da tunani na gare ni sai ta sake min magana

"Ya kika yi shiru? Ko babu amsa? Ya gaya min ai ce miki yayi zai shiga surgery sai anjima zai dawo. Ko ba haka yace ba?"

Hannuna yana rawa na rubuta mata

"You are lying. Kina so ne ki bata shi a gurina dan ki samu abinda kike so daga gare shi. Karya kike kuma. Kinyi kadan ki hada ni da mijina. Na san shi, nasan abinda zaiyi da kuma wanda ba zaiyi ba kuma abinda kike fada yana daga cikin abinda na san ba zaiyi ba"

"Really? Kin tabbatar kin san shi? For how many years? Bana jin kinyi sama da shekara biyu da sanin sa. Ni kuma yanzu shekarun mu takwas tare da shi. Ko quarter din abinda na sani a kansa ke baki sani ba wallahi. Kuma bana jin har abada zaki sani"

Kafin in gama karantawa in gama fahimta wani sakon ya shigo, sai wani, sannan wani, haka tayi ta turo min messages.

"In nace miki nasan komai a kansa ina nufin komai, nasan cikinsa na san kuma wajensa. Gidan da kuke zaune a ciki ma ni na fara zama a cikinsa, shekara ta guda har da watanni a cikin gidan kuma zamansa nayi, sai da zai tafi India ne ya nema min wani gurin na tashi saboda zai bar gidan a hannun iyayensa"

"Ya tafi da alkawarin idan ya dawo zamuyi aure"

"Bayan ya dawo ya kama aiki ya fara kokarin settling down ya kuma tara kudin auren, kawai kuma daga baya sai ji nayi wai yayi aure"

"A lokacin munyi fada sosai. Na dauka ma mun rabu har abada dan munyi wajen six months bamu ga juna ba"

"Sai daga baya kuma sai gashi ya dawo da kansa, you should see him begging me to take him back,daga dukkan alama ya rasa abinda yake samu daga gare ni agurin ki"

"A lokacin kuma ya gaya min dalilin da yasa ya aure ki"

"Ba wai sonki yake ba, kar ma ki saka haka a ranki cos you are nothing special to him. Sha'awar ki yake yi tun sanda ya fara ganin ki. Ya kuma kasa samun abinda yake so a gurin ki shi yasa dole ya aure ki dan ya kashe kishirwar sa"

"Yaso ya samu time sosai da ke a waje, dan ya ja hankalin ki har ya karbi abinda yake so shi yasa ma har ya nema miki makaranta amma baban ku yace aure zai miki a lokacin, saboda ya karbi kudin fansho yana so yayi miki kayan daki da shi kar su kare ya rasa yadda zaiyi"

"Yes, shi ya gaya min wannan"

"Ya kuma gaya min cewa yana gama biyan duk bukatun sa da ke zai aika ki gidan ku muyi auren mu. Amma sai naji shiru, kullum karyar yau daban ta gobe daban"

"Shi yasa naje gidan ku ranar nan dan inga whats holding him"

"A lokacin ne naga cikin jikin ki. Sai na fahimci plan din ki kenan na rike shi, kina ganin in kika haihu da shi ba zai iya rabuwa da ke ba albarkacin yara"

"A lokacin ne kuma naga rubabbun kayan dakin da akayi miki da kudin fansho"

"Yes, yayi fadan me yasa naje gidan sa, amma I guess fadan iyakacin na fatar baki ne dan ba zai iya rabuwa da shiga in between legs dina ba"

"Dan haka ki sani cewa Faruq nawa ne ni kadai. Gwara ki tattara ki kara gaba tun kafin ya tsofar dake ki rasa wanda zai kwasa in kin fita"


Ban san sanda na fita daga messenger din ba, na fara neman number din Umar hannuna yana karkarwa, so nake kawai ya dauka in tabbatar da cewa karya take yi cewa yana tare da ita a yanzu, in na tabbatar da haka to zan tabbatar da cewa karya take duk sauran maganganun ta.

Wayar ta fara ringing har ta katse babu amsa, na sake kira, na sake kira duk shiru. A hankali nake cewa "pick up Umar pick up" amma umar bai yi picking up ba.

Sai naga message ya shigo min da bakuwar number

"Shshshsh. Stop calling him Baby Dove. Na gaya miki bacci yake yi. Ya gaji sosai a office shine ya taho guri na ya sauke gajiyar sa sannan yake bacci"

Baby Dove shine sunan da yayi saving number ta dashi a wayarsa.



Anan muka kawo karshen free pages na wannan littafin Jidda. A yanzu ne kuma battle din zai soma.

Shin ya zata kwashe tsakanin Umar da Jidda? Menene makomar aurensu?

Ku biyo Maman Maama dan it is going to be a long ride dan ba'a ma fara wasan ba.

This is going to be one of the best novels da kuka karanta.

This is the novel I want to be remembered with........

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment