Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafafuwa a sama da wayarsa a hannun ta da alama game take yi. Na tsaya a bakin kofar ina kallon su, zuciya ta a wuya na.

Ya dago kai yana kallona "Baby. Kin tashi" ya miko min hannu. Ban amsa ba kuma ban je ba sai bata rai da nayi. Yayi min sign da hannunsa "what?" Na kara hade rai nace "Ummi, ban wayar nan" sai ta juyo ta kalle ni sannan ta kalle shi shima tare da fara shagwaba.

Na jira in ji abinda zai ce sai naji yace "ki bata mana, ko baki ji abinda tace ba?" Maimakon ta mika min sai ta mika masa, ya karba ya miko min, ban karba ba nace mata "tashi ki je waje" ta zumbura baki tana kallon sa, and I half expected yace kar ta fita amma sai naji yayi shiru har ta tashi ta wuce ni ta fita tana kunkuni, nabi bayanta da kallo sannan na tura kofar.



Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Episode Seventeen: The Visitors*

Ya ajiye wayar a gefe sannan ya nuna min kan cinyarsa, "come Baby, zo ki fada min waye ya taba min ke da tsakar ranar nan" na tafi naje na zauna a inda ya nuna min, na kwantar da kaina a kirjinsa sannan nace "wannan yarinyar, bai kama ta take shigowa dakin ka har ta kwanta akan gadon ka ba"

Ya dago da fuska ta yana kallona "wai Ummi? But why? She is like a sister........" Nace "like a sister, not a sister. Matsayin ta shine kanwar kishiyar Mama. Babu dangantaka ta jini ko kadan a tsakanin ku" sai yayi murmushi "kishi, kishi, kishi, I feel honored" na ture shi. "Ba kishi bane ba gaskiya ce. Dakina ko gadona duk zata iya shiga ta kwanta amma gadonka ba gurin zuwan ta bane ba. Ba ita ba ko su Mufida da kuke ciki daya dasu bai kamata su zo su kwanta akan gadon ka ba ko da ace baka dakin ballantana kuma kana nan sannan kai ma kana kwance akai"

Ya mayar da kaina kan kirjinsa ya kwantar "shikenan, sorry Baby, ba zata sake shigowa ba tunda ba kya so. In ba kya son ta zauna a gidan ma yanxu sai in kai ta gida tunda ba gidan ubanta bane ba" na dago kai "a'a ni bance ka mayar da ita gida ba, in nayi haka Aunty ba zataji dadi ba, kawai dai ina son boundary a tsakanin ku, bana son yadda kake bari tana taba ka a duk lokacin da tayi niyya dan kai ai ba muharramin ta bane ba kuma shaidan babu zuciyar da baya shiga even the purest of hearts"

Yace "Allahu Akbar. Ya ustaziyya Hauwa'u"

naga alamar wasa yake so ya mayar da maganar, na mike "eh naji ni ustaziyya ce. Ka tashi kayi sallah" na fada half hopping inji yace min yayi amma sai naga ya mike ya shiga toilet, na kalli agogo, almost three o'clock na rana amma bai yi azahar ba.

Ni a gidan mu na saba maza masallaci suke tafiya, in ba wani uzuri mai karfi ba da wahala ki ga wani yayi sallah a gida amma Umar sau da yawa a gida yake abarsa, a gidan ma wani lokacin sai nayi ta tuna masa musamman in yana wani abu sai yace sai ya gama.

Na danga chanji a lamarin sa da Ummi, ya kan cire hannun ta daga jikinsa in ta rike shi ko kuma ya matsa in ta zauna a jikin sa, sai kuma na lura gidan duk ya ishe ta duk tana ta kunci kwana biyu bayan nan ma tace tafiya zatayi gida.

Umar ya siyo mata doguwar riga da takalmi ni kuma na bata mayafi da kayan kwalliya muka kaita gida, amma sai twins suka ki zama suka ce  biyo mu zasuyi mu dawo gida.

Sai naga Mama ta bata rai "ku kun fiya rikici wallahi. Kawai dan kuje su saka su wahala ba kunyi kwana goma a can ba? Shi yana aiki ita tana karatu waye zai zauna daku a gida? Ita kuma Ummi da zata zauna daku din tace ba zata koma ba ya kuke so suyi daku?"

Na danyi murmushi "babu wahala ai Mama, gobe sunday bani da school shi   kadai ne zai fita, jibi kuma in zamu fita sai mu biyo mu ajiye su anan tunda hanyar mu ce"

Ta bata rai. "ba wani hanya, lokacin da zaku bata gurin shigowa da su ai yaci ace kunyi wani abun. Kuma keda ba ke ce mai driving ba ai ba ke ce zaki wahala ba"

Sai naja bakina nayi shiru amma bana jin dadin yadda yaran suka yi kamar zasuyi kuka. Ga Aunty tana Lagos a lokacin. Na daga kai na kalli Faruq da yake ta danne danne a waya kamar ma bai sannan maganar da ake yi ba. Na dan dungure shi da kafata. Ya kalle ni sai na marairaice masa. Ya juya ido sai kuma ya mike yana saka wayar aljihu yace "su taho mu tafi, monday din sai mu dawo dasu"

Muna tsaye a bakin gate muna jiran maigadi ya bude mana gate sai ga bakuwa munyi, Maryam kawata. Tun da ta doso motar take washe baki tana kara sauri, nima nayi mata murmushi sannan na daga mata hannu ina nuna wa Umar ita "ga Maryam nan, kawar mu ni da Mufida, ka gane ta?" Sai naga ya dauke kai kamar bai ganta ba sannan yace "eh" tana karasowa ga mamaki na sai naga ta zagaya ta window dinsa

"Yaya Doctor sannun ku da dawowa, ashe na kusa in daki gurbi na kusa in tarar ba kwa nan" sai naga ya nuna ni da yatsansa "kamar kinyi batan kai, ga kawar taki can" sannan sai ya daga mirror dinsa.

Sai naji a raina banji dadin abinda yayi mata ba, duk da ita ma rawar kanta yayi yawa ina ita ina zuwa window dinsa tayi masa magana in banda neman magana? Ni ce kawarta kamar yadda ya fada, guri na tazo dan haka ni ya kamata tayi wa magana.

Kafin ta zagayo window na mai gadi ya bude mana gate, Umar bai jira komai ba yaja mota ciki sannan yace da mai gadi ya rufe gate. Shi kuma mai gadi bai san tana waje ba kawai ya tura gate ya rufe.

Nayi sauri na bude kofa na fita sannan na tafi na bude mata karamar kofa. Na tarar ta hade rai kamar zata fashe "mijin ki dan wulakanci ne" na girgiza kai. "Kiyi hakuri kawata, wallahi bashi da wulakanci kawai dai ina jin a gajiye yake ne" na kama hannun ta "zo mu shiga ciki" ta zare hannun ta daga nawa "ni ba zan shiga ba ballantana ya kara wulakanta ni, sai anjima"

Ta zare hannun ta daga nawa ta tafi ranta a bace, sai naji banji dadi ba. Tabbas yayi mata wulakanci amma ai laifin ta ne rashin kamun kanta ne ya jawo mata. Kuma a ganina ai tunda gurina tazo babu ruwan ta da abinda Umar yayi mata musamman tunda na fito har waje na bata hakuri.

Na juya jiki a sanyaye na koma gida. A  palo na tarar dasu sun baje shi da twins yana raba musu abinda muka siyo a hanya. Na wuce su na dauko kayan su daga guest room na shiga dashi cikin bedroom dina, tunda Ummi ta tafi gwara su dawo kusa da mu.

Ina dakin ya shigo babu sallama kamar yadda ya saba sai kamshinsa ne ya sanar da ni shigowar sa. Ya tsaya a bayana ya zuro hannayensa ta cikina ya jani jikinsa, ya saka fuskar sa a wuya na yana goga min sajensa a fuskata. Na saka hannu na kare ina dariya "ka ga duk zaka min scratches a fuskata"

Yayi dariya "au haka ma zaki ce? To bara in miki scratches din abinda yafi fuska" ya juyo da ni yana goga fuskar sa a kirjina" na fara ja da baya ina dariya "wannan ai chakulkuli ne" yace "chakulkuli? Bara in nuna miki yadda ake chakulkuli" sai ya zura hannunsa a rigata ya fara yi min ni kuma ina dariya ina ture shi nace "ka daina, kaga bamu kadai bane a gidan, akwai yara"

Ya bata rai "in zasu takura min sai in mayar dasu gidan ubansu. Haka kawai ban ajiye ba ba za'a takura min ba" ya fada yana shafa mara ta "saura wata tara da kwana goma ki haifa min baby mai kama da ke" nayi murmushi "ni nafi son mai kama da kai. Kuma tun kafin a samu cikin har za'a fara lissafin ranar haihuwar sa?" Yace "eh mana. Yau za'a samu. You are ovulating and I am going to get the shot today" na rike fuskar sa "insha Allah" yace "insha Allah"

Sai daga baya ne muna cin abincin dare yake cewa "kawar taki kuma bata shigo ba?" Na bata rai "bayan ka wulakanta ta" shima ya bata rai "waye yace tazo tayi min ihu aka?" Nace "magana ce fa kawai tayi maka. Ina laifin wanda ya kula ka?" Ya ajiye chokalin hannunsa "I was accused of being too open just few days ago, yanzu kuma ana accusing dina of wulakanci. Which way should I go please"

Nayi shiru bance komai ba, ina jin a raina kamar nayi masa ba dai dai ba, sannan nayi wa kaina alkawarin ba zan sake tayar da maganar ba. Shi miji na ne dan haka ko cewa yayi kar in sake kula Maryam then I won't have any other option then to obey.

Bayan mun gama ne muka koma palo na kunna wa twins cartoon sannan na dauko littafi na ina karatu, shima ya fito ya bude laptop yana danne danne. Jimawa kadan na tashi na tashi afnan da ta fara bacci na kaita daki na na kwantar  da ita na dawo na tarar ya rufe computer din ya dauki wayata yana danne danne.

Na zauna a kusa shi ina leka cikin screen din wayar "me kake min a waya?" Ya zagayo da hannunsa daya ta side dina sannan ya kwantar da kansa a wuyana muna kallon wayar tare yace "am trying to make you social. Ke har yanzu kifin rijiya ce" na kwanta a jikinsa sosai "wai kana nufin social media? Na dauka ba zaka so ba shi yasa ko gwadawa ban taba yi ba dan nasan halin mijina da kishi"

yayi dariya "gaskiya ne wannan, kishi kam ina da shi sosai, amma ai yanzu na riga na samu Jidda dan haka bani da wani insecurities. Kuma dan ina kishin ki ba zan hana ki cigaba ba, ta hanyar social media ne zaki yi growing ki san me duniya take ciki beyond abinda yake gaban ki. Kuma it is a chance for you to meet and make friends. Ni kuma I don't have problem with that as long as friends din ba maza bane ba kuma as long as ba zan ga pictures dinki suna yawo ba"

Ya fara kokarin bude min facebook account, yace "ya sunan ki?" Na lakuce masa hanci "sunana Hauwa Umar" yayi murmushi ya rubuta "Doctor Hauwa'u Umar" na bude ido "am not a doctor" yace "you are matar doctor, dani da occupation dina duk naki ne ranki ya dade"

Sai ya nemo hoton Afnan da Affan ya saka su as profile picture dina sannan ya fara nemo mutanen da muka sani yana tura musu friend request "Daga haka zaki ke haduwa da wadanda kika sani, za'a ke turo miki friends of friends a matsayin people you may know" ni dai ina ta jinsa ina gyada kai, naga ya tura wa Mufida request kuma nasan zan samu friends dina ta hanyarta.

Ya bude min WhatsApp shima, nan da nan naga contacts dina duk da suke WhatsApp sun bayyana a take kuma nayi wa monitor din ajin mu magana nace ya saka ni a group, dan dama ina missing abubuwa sosai dan yawanci duk ta can ake making announcements.

Daga nan kuma sai ya bani wayar ya mike "gobe ki karasa, duk wanda kike so ki bude ni na gaji bacci nake ji" na karba sannan na gyara kwanciya ta a space din daya tashi "ba sai gobe ba ma, yanzu zanyi, am so eager to meet secondary school friends dina" ya karbe wayar, "bakiji abinda nace ba? Bacci nake ji. And I am sure going to take that shot kafin inyi bacci"

Na langwabe kai shima yayi irin yadda nayi, dole na fasa abinda nace zanyi din muka rufe komai muka kwantar da Affan wanda shima yayi bacci sannan muka tafi dakinsa na kuma bashi dukkan kulawar dayake bukata.

Daga auren mu zuwa yanzu na fahimci Umar yana da yawan bukata, amma sai na jingina haka da dokin amarci da ake cewa maza suna yi sannan kuma na dage iyakacin iyawa ta nake biya masa duk bukatun sa a duk lokacin da ya zo min dasu. Ba zan saka shi a layin masu tsananin bukata ba duk da yana da yawan bukata dan baya fashin dare, kuma ko da rana ne ma musamman in muna gida kuma mu kadai ne to fa sai yayi amfani da damarsa. Ni kuma a kokari na na ganin na faranta masa kamar yadda shima yake faranta min sai na dage ta wannan bangaren, duk tsoron da nake dashi na ajiye shi a gefe tunda yanzu babu sauran zafi, kunyar ma kuma na fara rageta dan shi ko shafi daya bai karanta ba a littafin kunya. Babu ruwanshi da wai wani kashe fitila and don't even try to say a lulluba da bargo. Shi ko a ina yake son abinshi anan zaiyi kayansa ko da kuwa kitchen ne ko toilet, yakance "gidana ne kuma matata ce, a barni in shana"

Watan mu biyar da aure na samu cikin Yasmin, ranar da Umar ya fara gane ina da ciki lokacin ko missing period banyi ba amma yana taba kirjina yace "Baby we are pregnant" na harare shi "ta haka dama ake gane cikin?" Ya saka matsawa "sosai ma. Wallahi akwai. Come lemme confirm" sai ya kwantar dani flat yana mammatsa mara ta, nayi dariya "Doctor Faruq. Idan ma akwai cikin fa bai yi wata daya ba kenan, how on earth can you feel it" ya kalle ni "shshsh, stop talking and relax. Kina magana ne da Doctor Umar and am not your average doctor" ya kara dannawa expertly da thumb dinsa can kasan marar,sai kuma ya danyi kara kadan "Jidda, wallahi akwai. About four weeks. How did I miss this har yayi four weeks ban san da shi ba"

Sai ya dauke ni ya fara zagaye dakin yna hajijiya dani har muka fada kan gado. Zan iya cewa ban taba ganinsa cikin wannan farin cikin ba dan haka kullum nake fadar cewa bai taba son wani abu ba kamar yadda yake son Yasmin.

Sai daya gama murnar sa sannan ya dauko kaya ya fara kokarin saka min,ya fasa kuma abinda da yayi niyyar yi. Na karba ina karasa sakawa shima ya dauko nasa "ina zamuje?" Na tambaye shi "gwara muje mu ga lafiyar ta, ko lafiyar sa, ko lafiyar su" nace "tun yanzu?" Yace "me kike tsammani? Yar doctor da nurse ce fa" nace "ne fa" ya kuma cewa "ce fa. Ni nafi son girl. Kyakykyawa kamar ki" ya fada yana jan kumatu na.

Asibitin Doctor Bashir muka je. Ranar ne na fara shiga asibitin muka zarce office din da yake a matsayin na Umar, ya nuna min kujerar marasa lafiya na zauna shi kuma ya zauna a kujerar sa. Sai kuma yayi waya aka kawo masa sabon file. Tana fita ya hade rai ya tambaye ni "full name please" nace "Umar Muhammad Gidado" sai yayi murmushi. 

Ina ganin shi yayi ta cike cike a jikin form din sannan ya dauko takarda ya saka aciki ita ma yayi ta cike cike a jiki, duk abinda ake tambaya ya sani, yace "so nake in bude miki file the normal way yadda ko bana kusa nurses din nan zasu iya duba ki" na gyada kai. Information din patient yana da amfani dan gudun samun matsala.

Bayan mun gama yayi min scanning, kuma abin da ya bani mamaki shine four weeks din da ya fada sune dai muka gani, wannan ya kara tabbatar min da cewa umar yasan aikin sa.

Wani abin mamakin kuma shine sai da muka san da cikin sannan na fara laulayi. Laulayi sosai nake yi sam bana iya cin komai musamman ruwa sai dai insha fruits, su kadai ne abincina. Gashi kuma a lokacin muna cikin exams din first semester of second year din mu. Umar harda daukan emergency leave danya kula dani, sannan ya gaya wa Mama ta aiko Mufida wadda a lokacin ta fara zuwa buk dan ta zauna tana taya ni aiyukan gida. Tunda babu nisa daga gidan mu zuwa makarantar ta, wani lokacin ma da kafa take karasa wa.

Nayi tayi masa mitar me yasa ya gayawa Mama "yanxu kasa zanyi ta jin kunyarta wallahi" ya yamutsa fuska "kunya? Menene abin kunya a ciki? Ji nake kowa sai da akayi cikin sannan aka haife shi. Kuma wannan abin da mukayi aka samu cikin nan kowa ma in ta shiga daki da mijin ta tana yin abinta" na ture shi na mike "Umar kafi karfina, na sallama wa duniya kai. Zancen Mama fa muke yi"

Sai yayi dariya kawai. Shi babu wanda ya bari. Ai kuwa kunyar nayi taji dan kullum sai ta kira ni tambayeni ya jiki, haka na lallaba na gama exams din, sai dai kuma dan hutun namu bashi da yawa fifteen days ne kadai muka yi muka koma school second semester second year. A lokacin na dan rage laulayi, Umar ma kum ya koma aikinsa amma dai ba wata lafiya ce dani sosai ba dan haka karatun wahala yake bani sosai, sannan kum babban tashin hankali na shine wannan semester din posting biyu ake yi, psychiatric posting inda za'a tura mu dawanau sannan kuma da orthopedic posting shi kuma za'a tura mu dala.

Da na saba duk sanda za'a yi posting into general wards Bashir yana taimaka min a tura ni nan AKTH inyi zama na a gurin Umar yanzu kuwa dole mu raba gari. Ina ta lissafin yadda zanyi coping a asibitin mahaukata ga kuma ciki ina fama da shi. A haka har muka gama theories aka yi posting din mu na dauko takardar posting din na kawo wa Umar.

Yana zaune yana aiki da computer dinsa na mika masa takardar "anyi posting din mu dazu. Gashinan, an kaini dawanau" na fada ina jin hawaye yana zuwa ido na. Sai ya dago kai yana murmushi, na dauke kai ina jin haushinsa sai yayi dariya "wa yaga Jidda tana fama da mahaukata" sai na fara kukan sosai "ni dai ba zan je ba. Haka kawai in wani ya kwace ya dake ni kuma fa. Kasan dai bani kadai bace ba ko?" Na fada ina hoping albarkacin cikina zai ce ba zanje ba.

Sai ya rufe system din yayi folding hannunsa yana kallona "to ya kike so ayi Madam? Karatun ki ne ya kama da haka kuma kika sani ma ko a can zaki yi aiki?" Na bude ido "wallahi ba zanyi aiki a can ba. Chafdi, wallahi sai dai in fasa aikin gabakidaya" yayi dariya "ke kam wannan akwai farar kura. Come here" sai na taso nazo na zauna a jikinsa na saka fuska ta a wuyansa ina jin dadin kamshin sa.

Yace "za a yi musu magana a gaya musu ga halin da kike ciki, and they won't let you anywhere near dangerous patients kinji. Akwai wanda na sani a gurin munyi buk tare da shi kuma yana da say sosai a gurin, already har munyi magana dashi tunda nasan dama can za'a kai ki kuma he assured me cewa babu problem, zai yi miki hanyar da ba sai kina zuwa kullum ba ma. Kin ga kin samu chance din hutawa ma for four weeks kafin nan kun kara kwari ke da baby"

Naji dadin maganar sa sosai sai na kankame shi "Nagode sosai my sweet husband. Allah ya bar mu tare" sai kuma na dago kai ina kallon fuskarsa na bata rai cikin shagwaba "amma yanzu shikenan ba zamu ke fita tare muna dawowa tare ba. Kuma ba zan ke ganin ka da rana ba"

Ya shafa fuska ta "waye ya gaya miki? Dawanau din ai ba zata yi min nisa ba indai kina can. Zancen fita da dawowa kuma already nayi solving wannan problem din" nace "how?" Yace "I bought you a car" na bude ido shi kuma ya kashe min nasa idon "a Rav4"

Na mike da sauri sai ya jawo ni ya dawo dani jikinsa yana dariya "don't even try that" cikin zumudi nace "da gaske dear?" Yace "eh mana. I wanted to give it to you a matsayin gift din cikin nan amma Allah bai yi ba, bata zo da wuri ba sai this weekend zata zo insha Allah. Probably tomorrow"

Na kankame shi ina hawaye "Nagode Nagode Nagode" ya dago fuska ta "dama a haka mata take godewa mijinta?" Nace "to me zance?" Na nuna lips dinsa "a kiss will be very much appreciated" nayi murmushi sannan na dora bakina akan nasa.

Two days after that kuwa motar ta iso, and it was much more than I expected dan tayi min kyau sosai, red color wacce tayi matukar dacewa dani. Gidan mu na fara zuwa da ita na nuna musu, gabaki dayansu suka fito kallon motar har da yan unguwa ma sai da suka fiffito. Ba a cikin yaya matan gidan mu ba, har cikin mazan nice na fara mallakar mota kuma lafiyayyiyar mota irin wannan.

Sosai kuma naga rashin jin dadin hakan a idon Hajiya "wannan mota haka? A ina ya samu kudin siyawa matarsa wannan mota? Anya kuwa Alhaji ba za'a binciki inda yaron nan yake samun kuɗi ba. Dama likitoci suna samun irin wadannan kudaden?"

Abba yace "suna samun kudi mana, kuma misali shi ai iyayen sa suna da arziki dan haka bashi da nauyin su ko na yanuwan sa a akan sa sai nauyin iyalinsa kadai"

Har cikin gida Abba ya shigo da Umar Umma tayi masa godiya, shi kuma yana ta sussunne kai, a raina nace kamar gaske dan nasan babu wata kunya da yake ji.

Bamu jima ba muka tafi, kuma tun a ranar ya kaini...............na fara gwada driving duk da cewa duk basics na driving din na sani dan nakan kunna motarsa a gida har reverse na iya in fitar da ita daga gate. Dan haka koyon tuki baiyi min wahala ba kuma sai Allah ya taimake ni bani da tsoron titi nan da nan na dara driving da kaina duk da cewa sai da Umar ya makala min 'L' saboda tsautsayi.

Kamar yadda ya fada haka ce ta kasance a dawanau din da aka tura ni, sun daga min kafa sosai kuma har wani girma naga suna bani, sun ganni fes fesga galleliyar mota ina hawa. Satin mu hudu a can aka mayar damu asibitin Dala orthopedic muka sake yin wasu four weeks din sannan muka koma school muka yi revision sai kuma exams.

Amma wannan karon sai aka samu akasi na fadi courses har biyu, abinda ban taba yi ba tunda na fara. Kuma hakan yana da nasaba da cikina da sam sam baya son karatu daga na dauko littafi na fara karatu to kuwa sai dai azo a tashe ni ina bacci.

Inda Allah ya taimake ni suna bada grace na two weeks mutum yayi resitting papers din daya fadi, in still baka ci ba sai kayi repeat, in kuma kaci sai ka wuce da yan ajin ku. Kuma Umar ya taimaka min sosai wajen karatun dan shi yake zama da kansa yana karanto min yana yi min vayani dan in ya barni da littafin bacci zanyi. A haka da taimakon sa da na ubangiji na samu naci exams dina ta wannan semester din. Daga nan aka yi mana hutu.

A cikin hutun ne nayi

Please Login or Register in order to submit comment