Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaso yayi hira da wayar. Na juya kaina gefe cikin bata rai da tura baki sai naji yace "yes! Wannan yafi kowanne kyau" na harare shi nace "zan koma ciki in ka gama hirar Allah ya kiyaye hanya" yace "shshsh, in kina motsi zaki bata hoton" na kalleshi ina lura da cewa wayar saitina take "wai hoto kake yi min?" Yace "har da video, kinga na samu na rage dare, ina waya dake ina jin muryar ki kuma ina kallon hoton ki, na zama dan gata. Baki ga yadda suka yi kyau ba lemme show you"

Sai ya taso ya dawo kan hannun kujerar da nake zaune akai ya zauna, naji wani iri sosai duk da jikinsa bai taba nawa na amma kamshinsa ba wai kamshin turaren sa ba a'a kamshinsa ya shige ni sosai, ya fara nuna min pictures dina daya dauka yanzu yana min dariyar yadda na tura baki sanda ina fushi, har da zooming bakin, nasa hannu na rufe screen din wayar da sauri shi kuma yana dariya, sai kuma nace "ka tashi ka koma gurin ka" ya gyara zama tare da yin ajjiyar zuciya, "nan yafi dadi, amma ya na iya da abinda yafi karfina? Tunda an bani umarni dole in bi"

Amma bai tashi ba sai daya dauke mu pictures tare kuma ni kaina nasan munyi kyau sosai together, da ace babbar waya ce dani da tabbas sai nayi dabara na karba ko dan nima in samu hoton da zaike debe min kewarsa in bama tare, sai ya mike ya koma daya kujerar ya zauna tare da yin tagumi da hannu daya yana kallona nace "wannan kallon fa? Ba ka samu pictures ba sai kayi ta kalla" ya girgiza kai "wata goma nake lissafawa, anya kuwa ba zanje in yi wa Abba kuka ba?" Nace "kuka kuma? Akan me? Sai kace ba namiji ba? Kai fa kace ko shekara nawa ne zaka jira" ya shafa kai "yes, haka nayi tunani, but after looking at those lips gaskiya akwai matsala"

Naji wani iri, nace "ka bari dan Allah. Kaga kana bani kunya" yace "bani abata" nace "me?" Yace "kunyar" nayi dariya, sai yace "kinga, gwara in fada miki ita wannan kunyar taki ina sonta sosai kuma tana birgeni sosai amma duk ranar da za'a kai ki gidana to ki tabbatar kin ajiyeta a bakin gate, inzaki fita unguwa sai ki dauki kayarki ki tafi da ita, in kin dawo sai ki sake ajiye ta, dan ni a gidana babu wani abu mai kama da kunya da zai kasance tsakanina da matata" na makale kafada "naki din, ni har cikin gida har kuma cikin daki zan shiga da abata" yace "ko kin shiga da ita ma zan kwace ta in jehota ta taga".

Muka yi dariya gabaki daya, sai naji nima a raina ina hango ranar, ranar da zan zama matarsa shi kuma zai zama mijina, but kafin nan ina son clearing wani abu a tsakanin mu tunda ina ganin shine dalilin da yasa ake zance dan a fahimci juna. Abinda ya jima yana taba zuciyata akan sa.

"Yaya Doctor, dan Allah ina son jin labarin relationships dinka na baya" naga fuskar sa ta sauya da mamaki yace "my past relationships? But why?" Nace "na taba jin kace you were in some relationships kafin ni, sannan kuma Mufida mentioned something like that. Shine nake son ji"

Ya gyara zama yana dan shafa sajensa kadan kamar mai tunani sannan yace "kafin in ganki, abinda zan iya kira da relationship dana taba yi I think guda biyu ne. Ta farko she is my second cousin. Lokacin da nake kokarin tafiya India Mama was like "ba zaka tafi babu aure ba, gwara ayi maka aure sai ka tafi da matar" irin dai abin nan na iyaye mata. So, lokacin bani da budurwa sai ta haɗa nida wata yar cousin dinta. Yes, na jejje gurinta zance but ni a raina gaskiya ina zuwa ne dan in faranta ran Mama. At the end kuma sai na samu Abba ya goya min baya yace ba za'a yi min aure ba sai lokacin da nake so, sooo, sai nayi tafiya ta kawai"

"Ita kuma ta biyu was my colleague a India, sunan ta Zuwaira tare muka yi karatu. Kuma farkon haduwar mu we thought something can work out between us but daga baya sai muka fahimci muna da banbancin halayya kuma ba zamu daidaita ba, sai muka rabu muka cigaba da friendship kawai, and we lost contact bayan mun dawo Nigeria, na san dai ta samu aiki yanzu but ban san a ina ba but am sure tayi aure by now"

"To bayan dawowata kuma sai Mama ta kuma tayar da maganar Hafsa. Su wai ashe suna ta jira ne in dawo a cigaba daga inda aka tsaya, a lokacin ne kuma na fito na gaya musu gaskiyar cewa batayi min ba ba zan iya auren ta ba. Nan fa akayi ta magana wai na yaudare ta and stuffs like that. At the end akayi mata auren huce haushi da wani cousin din mu, I heard ma wai ta haihu. Shikenan" ya karasa yana murmushi.

Na gyada kai cikin fahimta, case din Hafsat shine abinda Mufida tayi referring to as broken heart(s).

Yace "now your tone, akwai samarin da ya kamata in sani?" Na girgiza kai zuciyata daya "babu, babu kowa sai Umar Faruq" yace "nooo, don't be like that mana, ina wannan dan gajeren gayen nan dana gani a nan ranar nan" na dafe kai, ni na manta ma da musa sai yanzu. Sai na bashi labarin Musa na kuma tabbatar masa da cewa na sallame shi, yace "now, mu biyu muka rage wa junan mu kenan ko?" Na gyada kai "Allah ya bamu ikon rike amanar juna".

Umar ne ya tsaya min akan komai na registration dina, tun daga kan biyan kudi har sauran abubuwan da ba'a rasa ba wanda suke buƙatar wanda zai tsaya maka da kuma siyan littattafai da sauran abubuwan bukata na harkar karatu, sannan kuma ya dauki kudi masu kauri ya bani saboda transport zuwa makaranta. Ni a lokacin duk sai kunya ta ishe ni duk da ba ni na roke shi ba amma nasan ba alhakin sa bane ba yayi min wannan hidima tunda ba a daura mana aure ba an dai kawo sadaki kawai.

Sai naki karba, shi kuma yayi fushi daga baya yazo ya ajiye min kudin yayi tafiyar sa. Har da siyayya sutura yayi min wai zuwa makaranta yana kashe kayan sawa. Duk irin wadannan abubuwan su suke kara hura wutar kaunarsa a zuciya ta har nake jin sa a matsayin wani babban jigo na rayuwata. Kuma wani karin abin burgewa a tare da shi shine duk wannan hidimar da yake yi min bai taba fada wa mutanen gidan su ba ballantana inji tsoron wata rana zasu iya goranta min. Dan da ace ya fada da sai Mufida ta fada min ko da cikin hira ne ba wai da sunan gori ba. Sun san dai shi ya samo min makaranta amma basu san shi ya biya kuɗin ba.

Na fara zuwa makaranta successfully bani da wani stress tunda duk abinda ake bukata ina dashi ga kuma yan chanji a jaka ta. Challenge din dana fara fuskanta shine na samari, babu ranar da zan fita in dawo ba tare da wani ya tsayar dani yayi min magana ba, ko a hanyar zuwa ko a dawowa ko kuma ma a cikin makarantar. Sai dai amsa daya nake basu a koda yaushe "ni matar aure ce".

Wadannan kalmomi sai suka zauna min a bakina har ya zamanto bana mistake dinsu, kuma kasancewar duk babu wanda ya sanni a school din. Wannan yasa kowa ya dauka da gaske ni din matar aure ce har wani girma na musamman ake bani harda masu kirana da Aunty, ni kuwa in amshe abina😂. Kuma shigar mutuncin da nake yi ita ta kara fentin karyata. Kuma yawan ganina da suke yi da Umar sai yasa duk suka tafi a cewar shine mijina, ni kuma naji dadin hakan sai na cigaba da zura su suna tafiya.

Amma duk da haka ban fita ba a gurin Umar. Yana yawan gaya min cewa yana da kishi amma ban tabbatar ba sai da na fara zuwa school, duk yabi ya saka min ido, da farko ma cewa yayi nikab zan ringa sakawa sai da nanuna bana so sannan ya hakura. Amma in dai har na sake ya ganni da namiji to kuwa ya saka ni a gaba da tambaya kenan a karshe kuma sai yace "babu ke babu shi, dan iska ne" na kan yi mamaki "dan iska kuma? Me yasa kace haka? Ka san shi ne?" Sai yace "ban san shi ba amma yadda ya saka ki a gaba yana washe miki baki ya nuna min cewa akwai wani abu a zuciyarsa. Please promise me ba zaki sake kula shi ba" a haka ahaka sai daya cancelling fiye da rabin mazan ajin mu daga list din wadanda zan ke kulawa.

Amma ni ban damu ba, tunda dai naga baya so sai na ke kokarin ganin cewa bai ganni da mazan ba, ba wai dan na yarda da abinda yace na cewa yan iska ne ba sai dan ina so in faranta masa. Kuma dama ni kula maza is not my thing, sai idan ya zama dole.

Ina shiga makaranta na kara wayewa na kara gayu fiye da wanda nake da shi a da, Farhan cewa tayi har kyau na kara, ni kuma nasan na kara son Faruq na kuma kara shakuwa da shi. Dan yanzu kusan kullum sai na ganshi tunda school din mu bata da nisa da office dinsa, duk sanda yake free kuma ya kira yaji ina free sai ya shigo ko da briefly ne munyi magana ya fita, ko kuma ya siyo min snacks ya kawo min yace kar inji yunwa, wani lokacin kuma idan lokacin tashin sa yazo dai dai da lokacin tashi na sai ya dauko ni zuwa gida.

A irin wadannan lokutan ne yake bani labarin an fara hada masa lefe a gida. "Aunty tace wai ta karbi kwangilar lefen" yayi dariya "ita shegen son kudi ne da ita, ni kuma nace a'a bana son a bata, tace wai buƙulu nake mata nace naji ɗin" nace "to me yasa ba zaka bar mata ba? Waye baya son kudi?" Ya daga kafada "ni nafi son mu hada kayan mu tare ni da ke. Komai mu siya wanda muke so ba wanda wadansu suke so ba. Matata yar gayu ce kuma I trust her choices" na sunkuyar da kaina ina murmushi "kuma shikenan sai kace musu ni zan siyo?" Yace "why not? Ni fa bana takurawa kaina saboda ina jin kunyar wani, ni gaskiya in kika cire Umma da Abba to few people nake jin kunya fa"

Nace "banda ni?" Yace "especially you. Saboda me zanji kunyar ki? Someone that I will share everything with in the future. Including toilet" na rufe fuskata ina dariya "lallai ma, wallahi toilet biyu za'a yi naka daban nawa daban" yace "sai in bar nawa ai in dawo naki" nace "key zan saka in ke rufewa ai. Ni ba zaka ga toilet dina ba" yayi murmushi yace "amma na tausaya miki, irin sosai dinnan cos you have no idea yawan abubuwan da zamu ke sharing, toilet is among the least important, we will share a bed, a bath, and a toothbrush"

nayi saurin chanja topic "maganar Aunty da lefe, ina ganin da ka barta kawai tayi kaga ba zata ji dadi ba in ka hana ta, ka barta tayi ko ba duka ba ta siyo wadansu. Misali laces, tunda yanzu tana Lagos zata iya siyowa tare da sarkoki tunda sunfi kyau da saukin kudi a can. Zata iya ta turo maka sample ta waya sai mu zaba din tunda kana so mu zaba, in tazo nan kuma sai ta sayi atampa da materials da abaya, shima sai mu zaba ta waya. In yaso kayan kwalliya sai mu siya tare, ya ka gani?" Yayi murmushi fuskar sa tana nuna jin dadin sa "hakan yayi sosai. Wannan ya kara nuna min cewa nayi zabe mai kyau na uwar yaya na mai hankali da sanin ya kamata" daga nan kuma hirar sai ta koma kan yayan da zamu haifa.

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Episode Ten: Jamila*

Haka siyayyar lefen ta kasance, hatta boxes tare da shi muka zaba Aunty kuma ta siyo, komai sai abinda nake so abinda na zaba sannan zai yarda a saka in kuwa ta sayi wanda ban zaba ba sai yayi mata tijara ta sake wani. Farko in yana mata haka sai inga kamar rashin kunya, daga baya sai na fuskanci akwai wasa sosai a tsakanin su kuma na fahimci ita ce take musu wasan dan ni kaina ta kan kirani a waya ta tsokane ni.

A haka aka hada lefen, kamar yadda na fada kayan kwalliya tare muka je muka siyo da Mufida da Farhan, a lokacin na ga uban kudin da ya kashe a iyakacin kayan kwalliya kawai, sai na fahimci lallai dole samari suji tsoron lefe dan ba karamin aiki bane ba.

A daren ranar ne bayan mun dawo gida mun yi shirin kwanciya sai ya kira ni a waya kamar yadda ya saba duk dare, "Aunty ce ta aiko ni, tace in tambaye ki size din pant da bra" na rufe ido na da sauri kamar yana kallo na "kai dan Allah" ina jin shi yana dariya, "ni dai dan aike ne, amsa kawai za'a bani sai inje in bayar ni ma" nace "ba wani nan, Aunty ba zata yi maka wannan tambayar ba ai tana da number dina zata iya tambayata ko kuma ta saka Mufida ta tambaye ni"

Yace "Allah da gaske nake fa, ta tambaye ni nace ban sani ba tunda ni ban taba gani ba sai dai ta cikin hijab, ta cikin hijab kuma ba gane girman nake yi sosai ba amma dai ina ganin kamar suna da dan girma haka....." Na katse shi "ka ga ka daina, zan kashe waya fa wallahi in baka daina ba" yana dariya yace "sorry Baby. I am just curious, dan Allah ki gaya min size nawa ne, babu wanda zan gaya wa daga ni sai ke"

Nace "kuma kace Aunty ce ta ke tambaya" yace "ni ne nake tambaya. I just want to know" nace "ai kuwa ba zaka sani ba" yace "kar ki rantse dai, only time will tell. In dai size ne kwana nawa ya rage in sani, ba size ba har shape da texture duk zan sani, in auna abina da kai na......." Banji karshen maganar ba na katse wayar tare da tura ta kasan pillow na na kuma rufe kunnuwa na da hannayena amma ban daina murmushi ba. Da gaske zai sani? Duk wannan abinda ya fada zai faru ko? Na shiga uku.

Ina jin wayar tana ta ruri amma ban daga ta ba dan nasan shine har saida ya hakura ya daina kira.

Shigowar Farhan ya dawo dani daga tunanin abinda zai faru a ranar da Umar yake magana akai, ta zauna a bakin katifa tana jujjuya wayarta a hannun ta amma hankalin ta baya tare da ita sam. Na mike zaune ina kallon ta. "Har yanzu bai kira ba ko?" Ta gyada kai kawai ba tare da ta kalle ni ba tace "bai kira ba kuma wayarsa bata shiga. Ina jin yayi blocking dina ma" na jinjina kai kawai sannan na koma na kwanta dan ban san abinda zan ce mata ba.

Kamar yadda komai yake tafiyar min dai dai haka komai yake tafiyar wa Farhan ba dai dai ba. Na farko kuma mafi muni shine yadda Sulaiman ya juya mata baya lokaci daya tunda ta sanar da shi cewa Abba yace ya fito maganar aure, farko sai yace shi bai san yanzu ne za'a yi auren ba dan bai gama sanin ta ba yana so a kara masa lokaci su kuma fahimtar juna, ta nuna masa cewa ba wai a lokacin za'a yi ba za'a dauki watanni kawai dai ana son in da gaske yake ya turo magabatan sa ayi magana.

Tun daga nan ya fara ja mata aji, a hankali ya fara zamewa har ya kasance ya tafi ga baki daya. Tun tana boyewa Abba har dai ta fada masa gaskiya shi kuma yayi mata barazanar ko ta fitar da wani ko kuma shi ya fitar mata dan shi lallai tare yake so ya hada mu. A duk sanda ya yi mata irin wannan fadan in ta koma gefe ta kan ce "to ni in ba ni ake so ince ina son kaina kuma in auri kaina ba ban san ya ake so inyi ba, ba sai ance ana so na ba sannan zan ce a fito? Ko kuma mutum zan tara a hanya kawai ince masa ya fito ya aure ni?

Abu na gaba kuma shine karatu, da bata saka ran zata yi karatu ba dan tun mun yara Farhan itace mai son aure ni mai son karatu amma yanzu ganin kullum ina fita inje makaranta ita kuma tana zaune a gida daga kallo sai kwanciya sai ta fara son makarantar itama. Sai dai fur Abba ya shafawa fuskarsa toka yace ba a gidan sa ba nima wanda zan aura ne ya samo min, ita ma ta fito da miji sai ya samo mata. Haka ta hakura, da kyar ya samu ya siya mata waya irin tawa bayan Hajiya tayi kamar zata kona gidan saboda balain ta.

Zancen retire din Abba ta tabbata, sai da ta tabbata sannan ya gaya wa su Umma ya kuma gaya musu niyyar sa tayi mana kayan daki ni da Farhan da wani kaso na cikin kudin pension da aka bashi sannan ya shiga kasuwa da sauran. Amma yanzu da Sulaiman ya gudu sai yace ni kadai zai yiwa har na Farhan din zai shiga kasuwar da shi.

Wannan ya kuma tayar da rigima a gidan mu, Hajiya tace bata yarda ba komai aka siya min sai an siyawa Farhan "idan kuma auren nata yazo babu kudin fa? Ya za'a yi da ita?" Umma kuma tace "to in dai warewa za'a sai a ware har da na Amira itama, ita ma ai komai daren dadewa za'a yi nata auren" nan take rikici ya kaure a karshe Abba yafita ya bar musu gidan, tun suna yi a samansa har suka sauko kasa kowa ta shiga dakin ta amma in wannan ta leko tayi magana ta koma daki sai waccan ta leko ta bata amsa.

A karshe dai bayan cecekuce da fadan da Farhan ta sha a gurin Abba sai Allah ya taimake ta ya ce ya kara mata lokaci dan haka nawa bikin kadai za'ayi yanzu, sannan kuma da aka tashi siyayyar furnitures sai akayi set biyu nawa da nata komi iri daya sai banbancin colors, kayan kitchen manya ma duk bibbiyu aka siya kanana ne dai ba'a siya mata ba nima kuma ba Abba ne ya siya min ba, kudin auren da aka kawo ya bawa Umma suka hada da kudin da suke tarawa suka yo min siyayya ita da Aunty Afia, sunyi min siyayya mai kyau wadda duk kushen mai kushe sai dai yayi hassada. Sannan kuma Abba ya hada min gara dai dai karfinsa.

A haka har watan bikina ya kama, Umar ma kusan duk ya gama shirye-shirye ta ɓangaren sa. Dama Baba already ya siya masa gida a rijiyar zaki tun kafin ya tafi India, dan haka yanzu renovating kawai yayi yan chanje chanjen da muka zauna ni da shi muka tsara. Ban taba zuwa gidan ba amma zan iya cewa babu wani lungu ko sakon daban sani ba a gidan dan hatta fenti ni na zabi kalar da za'a yi.

Bayan an kawo lefe ne kuma sai akayi fixing exact date din da za'ayi bikin, tunda da wata kawai aka saka. A ranar ne kuma na tabbatar da Hajiya bata son aurena da Umar dan kasa boyewa tayi ta kasa fitowa ta tari su Aunty da suka kawo lefe, sai gwoggo Habibah, Aunty Afia, kawayen Umma su biyu da matan abokan Abba su biyu ne suka karbi bakin, sai yan unguwa da suka shigo ciki har da babar Musa da ko a fuska bata nuna rashin jin dadin ta akan kin zaɓen Musa da nayi ba.

Washegarin ranar ne kuma da daddare muna tsakar gida tare da su yaya Tahir da sai a lokacin suke ganin kayan sai Mufida ta kirani a waya tace in tura mata number din Yaya Tahir zata turo masa wani video da suka hada mana ni da Umar. Na tura mata, babu jimawa kuwa ta turo masa. Video ne mai dauke da pictures dina da nasa da kuma pictures din mu tare da kuma picture din iv din daurin aure da ta biki wadanda bansan ma an bugo ba, sai kuma hoton akwatinan lefe na, tare da background music na wakar

"Ko rana da wata sun daina haske, gimbiya ta sai ke, soyayyar mu har abada................"
(Ban iya rakar ba, kowa yayi da kansa. Lol"

Video din yayi kyau sosai kuma ya kayatar, a take yaya Tahir ya dora a social media kuma ya tutturawa yan'uwa da abokan arziki ya kuma tura wayar Umma itama, duk da dai ita ba social media din take ba.

A ranar sai na samu kaina da tafiya dakin mu da wayar Umma, ranar Umar bai kirani ba kuma ban damu ba saboda munyi waya da magrib kuma ya gaya min yana busy da dare, sai nayi amfani da wannan video din wajen debe wa kaina kewar sa, nayi playing and re playing yafi cikin carbi, kuncina har ciwo yake yi saboda murmushi. Ina jina kamar wadda tafi kowa sa'a a rayuwa, kamar wadda tafi kowa dace da saurayi kuma miji insha Allah. A haka bacci ya dauke ni bayan nayi running down battery din Umma.

Kasancewar bani da tsarki a lokacin da kuma dadewar da nayi banyi bacci ba ya saka nayi dogon bacci har gari ya waye, cikin baccin ina ta mafarkin ana bikin mu da Umar kuma an gayyato hamisu breaker yana ta yi mana wakokin soyayya a wajen bikin. A cikin taron bikin ne naji muryar gwoggo Habibah tana kuka, sai kuma naji muryoyin Umma dana Hajiya suna ta magana sama sama amma wakokin da ake yi a gurin ya hana ni jin abinda suke cewa.

Maganganun nasu ne naji yayi karfi, ya wuce karar wakar har ya ratsa mafarkin da nake yi. Na farka a firgice ina salati tare da murza idona, babu Umar babu yan biki babu hamisu breaker amma still akwai muryar gwoggo Habibah kamar tana kuka kuma akwai muryoyin su Umma suna tambayar ta abinda ya faru.

Na mike da sauri ina salati, Allah yasa ba wani abu ne ya samu wani a dangi ba, na tafi taga na leka sai na ga gwoggo a zaune a kafar benen Abba, su Umma kuma a tsatstsaye. "Habibah me yake faruwa? Wani abun ne ya samu wani a cikin yaran?" Inji Hajiya.

Umma tace "kiyi magana gwaggon yara duk kin tashi hankalin mu" gwoggo Habibah ta ce "ina Yaya? Ina son ganin sa, wannan auren na Maijidda dole a fasa shi, wannan yaron da aka bata ba yaron arziki bane ba" sai naja da baya kadan, zuciya ta tana tambayar ƙwaƙwalwa ta "wacece Maijidda? Bani bace ba ko?" Amma kuma na san Maijidda daya ce a dangi, ni.

Hajiya tace "haba? Yanzu naji magana, to alhamdulillah da aka sani tun yanzu tun kafin azo ayi dana sani. Ni dama tun farko yaron nan bai kwanta min a raina ba" Umma ta ja da baya kamar yadda nayi sannan tace "me kike cewa ne gwoggon yara? Waye ya gaya miki? Wani abun kika ga yayi ko kuma wani ne ya gani ya gaya miki ke kuma kike fada?"

Gwoggo Habibah ta dago kai tace "ba gaya min akayi ba Aisha, ni

Please Login or Register in order to submit comment