Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

je gurin cikin cikin fara'a da tsokanar juna. Wani irin farin ciki nake ji a zuciya ta musamman in na juya na kalli mutumin daya ke zaune a kusa da ni, mutumin da duk juyi na ina jin idonsa a kaina hannu na kuma a cikin nasa. Sanda muka tsaya ne bayan Bashir da Farhan sun fita ya kara matsowa kusa dani

Na matsa ina zaro ido shi kuma ya kuma matsowa har sai da na makale a jikin kofa ina zare ido, ya saka hannu yana shafa side din fuska ta a hankali "I feel like stealing you right now, in yiwa motar nan key kawai in tafi dake somewhere inda babu wanda ya sani bare ya dame mu. What do you say? Mu tafi?" Na girgiza kaina da sauri. Ya matso da fuskarsa kusa da tawa har ina jin hucin numfashin sa a fuskata, idon sa cikin nawa, nayi saurin rufe nawa idon dan sam bana son abinda nake gani a nasa idon, zuciya ta tana kokarin balla kirjina saboda bugawar da take yi "why?" Ya fada can kasa "me yasa ba kya son in sace ki mu gudu?" Na hadiye yawu sannan nace "saboda bai dace ba" yace "dama a tsakanin mata da miji akwai abinda bai dace ba?"

Na ce "ba tsakanin ni da kai ba, tsakanin mu da mutane" yace "ni ina ruwa na da mutane, ni matata kawai na damu da ita" nayi shiru ban sake cewa komai ba saboda bana jin ko na bude bakin magana zata fito saboda dan yatsan sa da naji ya sauka akan lips dina yana zagaye su "open your eyes" ya fada da alamar dariya a muryarsa, ga girgiza kai na tare da kara rintse ido na da karfi, yace "open your eyes nace ba close your eyes ba" "uhm uhm" nace tare da sake shigewa cikin kujera ina kara tattare jikina a waje daya. Yayi dariya "wai cikin kujerar zaki tsaga ki shiga?"

Na gyada kai. "Saboda me?" Na nuna shi da hannu na da yake free, sai ya kama shi shima ya rike sannan ya dora shi akan kirjinsa "kinji yadda take bugawa? Kinji yadda zuciyata take bugawa? Just for you" naji ya saki hannuna ya bar shi a kirjinsa sannan naji saukar nasa hannun akan nawa kirjin "bara muji naki bugun zuciyar"

Na bude ido na da sauri tare da yin yar karamar kara a lokaci daya ina ture hannunsa, ya tuntsire da dariya, na harare shi ina kokarin bude motar in fita ya riko hannuna "sorry baby kawai zanji ne ko zuciyarki ta fi tawa bugawa da karfi" na kara masa wata hararar tare da murguda baki "only in your dreams" na fada sannan na bude kofa na fita, ya fito shima ya tsaya kusa dani yana gyara min rigata da veil dina sannan a hankali yace "kar Allah ya kawo abinda zai kara min tsahon gobe, I know these 24 hours will be like 24 years to me"

Amma addu'ar sa bata karbu ba dan ana tsakiyar dinner din naji alamar period dina tazo, bayan an tashi kuwa ina zuwa gida na tabbatar da zuwan nata. Naji dadi sosai dan har da yar karamar rawa nayi a toilet, duk da dai nasan kwana biyar ne kadai zata yi ta tafi amma at least nasan zan dan huta in huce gajiyar biki a kwanakin, sai dai kuma bansan yadda Umar zai dauki abin ba. Nayi murmushi ina lissafo yadda reaction dinsa zai yi idan na gaya masa bani da tsarki.

Ranar kam mutane kadan ne sukayi bacci a gidan, duk kuwa da cewa an debo gajiyar dinner amma haka kawai sai aka bude chapter akan rayuwar aure da ire-iren kalubalen da yake ciki, anayi ana jefo min nasiha a ciki tare da dabarun zaman aure, wannan a gare ni shi ya zamanto kamar fadan da akeyi wa amare, kuma babban abinda na dauka a cikin fadan shine hakuri wanda aka nuna min cewa shine jigon komai.

Washegari akayi yini anan gidan mu, da magriba kuma kamar yadda aka tsara aka zo aka dauke ni ina kuka zuwa gidan mijina bayan dogon fadan da Abba yayi min a kan biyayya da miji

Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


Episode Fourteen :The Wedding Night

Gidan Umar yana rijiyar zaki, flat ne madaidaici dai dai karamin family. Falo ne madaidaici, a cikin sa akwai kofofi guda uku, daya zata shiga da kia guest room mai hade d guest toilet, daya zat shiga da kai dining room wanda ta cikinsa zaka shiga kitchen, a cikin kitchen din akwai store da kuma dan karamin dakin yan aiki sai kuma kofar da zata fitar da kai backyard, daya kofar kuma ta falo zata shiga da kai corridor din da daki na dana umar suke kallon juna.

Komai na gidan ni dai zance yayi min, dan Umar yayi iyakacin kokarin sa gurin tabbatar wa yayi komi dai dai da zamani sannan nima iyaye na t nadu bangaren sunyi matukar kokari gurin zub kayan da suka dace da gidan, komai yaji sai san barka sai kuma fatan alkhairi.

A falo su Aunty suka ajiye ni akan kujera, suka zauna suma ta hira da barkwanci da yan gidan su Umar waɗanda suka zagaye ni suna ta tsokana ta da neman lallai sai sun bude min fuskata, ni kuma na kankame mayafina na kuma takure a jikin aunty ina karasa sauran kukan da ban gama ba, tsoro na Allah tsorona su Aunty su ce zasu tafi. Ai kuwa basu wani jima sosai ba suka fara shirin tafiya haka suma yan uwan Umar banda su Mufida da suke a matsayin kawayena, nan na sake bude wani sabon babin na kuka kawayena suna ta tsokana ta.

Farhan tace "munafuka, Aunty ganin ku ne fa ya saka take wannan abin, bara ku gani yana zuwa zaku ganta tana ta zagba masa murmushi, idan da zaku ce tazo ku tafi tare da ita cewa zata yi ba zata bi ku ba" Mufida tace "wallahi kuwa, kukan munafurci ne. Kuma wallahi in yazo naga hakorinki a waje sai nayi miki hoto na nuna wa kowa ya gani" yaya Hudallah tace "kar ku takura mata, wa yaki auren soyayya? Auren soyayya ai dadi ne dashi. Kana son mijinka shima kuma yana sonka me yafi wannan dadi?"

Maryam tace "ballantana miji irin yaya Doctor. Gaskiya Jidda tana daga cikin mata masu saa a duniya. Ta samu miji ga kyau ga kudi ga tarbiyya ga ilimi uwa uba kuma gashi yana balain sonta"

Sai hirar da juya ta koma akan irin dacen da nayi da miji, duk a kokarin su na making me feel better kuna naji dadin sosai dan ina so inji ana yabawa Umar. A haka sukayi ta zame jiki suna tafiya.

Bayan sun tafi ne na dan bude fuskata da kumburarrun idanuwa na, Farhan ta matsa min wai lallai sai na sake wanka ni kuma naki yi tunda da zamu taho bayan magrib sai da nayi wanka kuma yanzu bayan ishai sai in sake wani? Sai kace kwaduwa? Banyi wankan ba dai amma na dan gyara fuska ta, sai kuma barin turare da Mufida tayi min a jiki kala kala ta ringa fesa min a kowanne loko na jikina, suka hadu suka gyara gidan fes suka kuma saka turaren wuta a ko'ina yadda daga ni har gidana duk kamshi muke yi, sai kuma zaman jiran angwaye.

Anan falo muka zauna jiran su, su Mufida su uku, Farhan da Aira, Maryam, sai kawayena na school of nursing su uku. Angwayen ba su zo ba sai tara da rabi, kamar yadda muka yi tsammani classy abokan sa bisa jagorancin Bashir su suka rako shi, tun daga waje muka jiyo hayaniyar su daga dukkan alamu tsokanar sa suke yi, muka yi sauri muka shirya Farhan har da kara rufe min fuska tana tuna wa sauran kawaye irin kudin da zasu karba a matsayin na siyan baki.

Sai dai suna shigowa Umar bai bi ta kan kowa ba ya doso inda nake gadan gaban, ina jin kawayena suna retaliating, Mufida har da zuwa gabana ta tsaya tare da rike kugu, yana zuwa ya saka hannu daya ya ture ta gefe sannan ya saka hannu biyu ya kama nawa hannayen ya mikar da ni tsaye sannan ba tare daya jira komai ba ya jawo ni zuwa kirjinsa ya rungume.

Ina jinsa ya sauke sassanyar ajjiyar zuciya yana kara matse ni a kirjinsa, sannan a hankali yace "welcome home Baby" naji murmushin da Farhan take cewa zanyi yazo fuskata sannan a hankali nayi rising hannayena da suke sides dinsa na hade su a bayan sa tare da cewa "thank you dearest". Sannan na lumshe idona ina shakar daddadan kamshin sa.

Ihu da sowar yammata da samarin ne ya saka ni bude ido na, sai kuma na sake shi ina kokarin ture shi cikin jin kunyar su. Ina jin Farhan tana cewa "munafuka na dauki hoton ki ai sai na nuna wa Aunty da Umma" na juya side din ta ina yi mata alamar roko. Umar ya sake ni shima sannan ya rike hannuna muka juya muna kallon su, kusan kowa da waya a hannun sa yana daukar mu hoto, a raima mace na shiga uku shikenan za'a ga hoto na a rungume a jikin namiji, sai wata zuciyar ta tuna min cewa namijin ai miji na ne kuma Umar dina ne and I felt I don't care, the whole world can see it.

Yace "what are you guys still doing here? Na dauka kun tafi ai. Thank you thank you thank you, but your presence is no longer needed, a gaida gida" Bashir yace "in baka kore mu ba dama ai baka cika Umar Faruq ba. To babu inda zamu je in muka ga dama ma anan gidan zamu kwana ko ya kuka ce guys" Mufida tace "aa banda kwana dai, za dai a bamu kudin siyan baki sannan a kaimu gidajen mu bayan an gode mana ba wai an kore mu ba" Bashir yace "wannan duk mai sauki ne, zamu kai ku har gida kuma zamu sallame ku, amma mu dai kam tunda wannan angon ya wulakanta mu kuma ya kore mu to anan gidan zamu kwana. Ko ya kuka ce?" Sauran abokan suka fara amsawa da eh, duk suna kallon Umar cikin tsokana.

Sai ya daga kafada "okay, no problem, ga dakin baki can ga kuma palo nan wanda bai samu guri ba sai ya kwanta akan carpet. And please in kun gaji da zama zaku tafi make sure you close the door. Sai da safen ku"

Ya juya ya doshi hanyar dakunan mu hannunsa cikin nawa, ni dai duk kunya ta ishe ni kamar kasa zata tsage in shige ciki. Har mun kai bakin kofa sai ya juyo yana kallon Bashir. "Na bar kaji na a mota, bring them please. And in ka kawo be a good boy and knock on the door sai ka ajiye a bakin kofa ka tafi" ina jin suna ta dariya yayin da Bashir yake babatun Umar bai isa ya aike shi ba,ni dai ban dago kai na kalle su ba dan bana jin zan iya kallon idon su amma su ko a jikin su. Kawayena ma duk babu mai cewa komai sai dariya da suke yi.

Muna shiga corridor din ya mayar da kofa ya rufe sannan ya jingina da jikin ta yana kallo na. Na harare shi. "Kaga ka sa naji kunyar abokan ka ko, ka bari mana minti nawa ne zasuyi su gama su tafi?" Yace "rabu dasu wadannan, tun yamma suka saka ni a gaba da tsokana wai ba sabanba nima yau zan shiga daga ciki, wai na kasa rufe baki saboda doki, shine nima na nuna musu tabbas dokin nake yi" ya saki hannu na ya rike fuskata yana kallon ido na "ina dokin kasancewa da matata" na ja baya ina kallon sa ina murmushi, sannan na juya da sauri na shiga daya daga cikin ɗakunan da suke gurin duk da bansan ko na waye a cikin mu ba. Na zauna a bakin gado tare da sake lullube fuskata ina jin mixed feelings a cikin zuciyata.

Ina jin sa yashigo dakin, ya jima a tsaye yana kallona sannan ya karaso ya zauna a kasa a gaba na tare da dora guiwowin hannayensa guda biyu a kan guiwowin kafafuwana yayi tagumi da hannu bibbiyu yana leka fuskata. "Ni ka daina kallona, so kake sai ka gano muni na" ya lumshe ido ya bude "muni fa kika ce? A jikin ki Jidda babu wani abu mai kama da muni in ma da akwai ni Umar ban ganshi ba" nayi murmushi ina jin dadin maganar sa, tabbas Umar yana da baiwa mai yawa amma iya magana musamman a gare ni tana daga cikin manyan baiwar sa.

Na gyara mayafina ina kara bude masa fuskata sannan wani tunani ya fado min, wata tambaya da na jima ina yiwa kaina 

"Why me?"

Yace "what?" Na daga kafada "in nufin you can marry any other Lady, why me? Me yasa ka zabe ni?"

Sai naga yayi mamakin tambayar tawa, yace "ke zanyi wa wannan tambayar Jidda, you can marry any other guy because you have everything needed, why do you accept me?"

Na juya ido na "I asked the question first Mr, answer me first"

Sai ya mike yayi kneeling a gaba na yadda fuskokin mu suka daidaita da juna sannan yana kallon cikin ido na yace "I don't know. I just saw you and know that it is you. Farko muryarki na fara jiyo wa kina gaishe da Mama a school dinku and I felt like ba zan iya cigaba da rayuwa ba sai na ga fuskar ki, I turned my mirror and saw you and I felt like bazan iya cigaba da rayuwa ba sai na sanki, and when I did manage to get to know you I felt like bazan iya cigaba da rayuwa ba sai na aure ki. And here am I thankfully married to you and feeling like my life is finally complete, feeling like kamar bani da wani sauran buri kuma sai fatan cikawa da imani. Buri dai kam na duniya Jidda na gama samunsa. Now tell me, me yasa da nace ina sonki ki ka karbe ni"

Naji kwalla ta kawo idona, I hate wannan saurin kukan nawa wallahi amma haka halitta ta take kuma nasan ubangiji yasan dalilin da yasa ya halicce ni a haka. Na saka bayan hannu na a hankali na shafa sajen sa ina jin wata sabuwar soyayyar sa tana kara shiga cikin zuciyata.

Na tuno da wani baiti na wata waka dana taba ji somewhere duk dabazan iya tuna sunan wakar ko a inda na ji ta ba

*Have you ever love someone so much that looking at them makes you cry?*

Sai naji na fahimci dalilin hawaye na.

Na ga ya lumshe idonsa yana feeling hannuna da yake shafa fuskar sa. A hankali nace

"Because I love you. Bansan dalili ba so don't ask me, I just know I love you tun second din dana ga idonka ta cikin mirror kana kallona, har zuwa yanzu da kake matsayin mijina, and I am pretty sure that I am going to take your love with me to my grave. Wannan shine abinda na sani, bayan shi ban san komai ba"

Sai ya saka hannun sa ya rike hannuna da yake kan fuskarsa ya jawo shi a hankali zuwa kan lips dinsa sannan ya manna min kiss a tsakiyar palm dina, ya bude idonsa da naga sun juye zuwa irin na yan shaye shaye sannan yace

"And I love you too Baby"

Nayi sauri na karbe hannuna daga gurinsa sannan na goge shi da sauri a jikin cinya ta, ina jin sakon kiss dinsa yana tafiya tun daga hannun nawa zuwa duk wani bari na jiki na har inda ma ban taba tunanin zai je ba.

Na fara kokarin wayencewa "uhmmm su Mufida ko sun tafi gida? Ya kamata mu duba su" ya danyi gajeren murmushi yana matso da fuskarsa kusa da tawa "I don't know. And I don't care" na matsar da tawa fuskar baya ina zare ido "ni I care. Zanje in duba su, in sun tafi ma zan kira su in tabbatar sunje gida lafiya"

Ya cigaba da matsowa ba tare da yace min komai ba, idanuwan sa akan lips dina, yana yin sa mai cike da rikitarwa. Ni kuma na cigaba da ja baya kirjina yana dukan tara tara a haka har muka hau kan gadon sannan muka tafi har karshen gadon. Sai da naji bayana ya hadu da frame din gadon sannan na far neman next option din guduwa, na duba dama da hagu ina tunanin ina ne zai yi min sauri amma sai yayi sauri ya saka hannayensa a dukkan sides biyun ya tare ko'ina.

A dai dai lokacin muka ji tashin motoci a waje, tare da maganganun mutane, yace "there. Sun tafi, sai kuma me kike so ki sani?" Nace "





Gidan Umar yana rijiyar zaki, flat ne madaidaici dai dai karamin family. Falo ne madaidaici, a cikin sa akwai kofofi guda uku, daya zata shiga da kia guest room mai hade d guest toilet, daya zat shiga da kai dining room wanda ta cikinsa zaka shiga kitchen, a cikin kitchen din akwai store da kuma dan karamin dakin yan aiki sai kuma kofar da zata fitar da kai backyard, daya kofar kuma ta falo zata shiga da kai corridor din da daki na dana umar suke kallon juna.

Komai na gidan ni dai zance yayi min, dan Umar yayi iyakacin kokarin sa gurin tabbatar wa yayi komi dai dai da zamani sannan nima iyaye na t nadu bangaren sunyi matukar kokari gurin zub kayan da suka dace da gidan, komai yaji sai san barka sai kuma fatan alkhairi.

A falo su Aunty suka ajiye ni akan kujera, suka zauna suma ta hira da barkwanci da yan gidan su Umar waɗanda suka zagaye ni suna ta tsokana ta da neman lallai sai sun bude min fuskata, ni kuma na kankame mayafina na kuma takure a jikin aunty ina karasa sauran kukan da ban gama ba, tsoro na Allah tsorona su Aunty su ce zasu tafi. Ai kuwa basu wani jima sosai ba suka fara shirin tafiya haka suma yan uwan Umar banda su Mufida da suke a matsayin kawayena, nan na sake bude wani sabon babin na kuka kawayena suna ta tsokana ta.

Farhan tace "munafuka, Aunty ganin ku ne fa ya saka take wannan abin, bara ku gani yana zuwa zaku ganta tana ta zagba masa murmushi, idan da zaku ce tazo ku tafi tare da ita cewa zata yi ba zata bi ku ba" Mufida tace "wallahi kuwa, kukan munafurci ne. Kuma wallahi in yazo naga hakorinki a waje sai nayi miki hoto na nuna wa kowa ya gani" yaya Hudallah tace "kar ku takura mata, wa yaki auren soyayya? Auren soyayya ai dadi ne dashi. Kana son mijinka shima kuma yana sonka me yafi wannan dadi?"

Maryam tace "ballantana miji irin yaya Doctor. Gaskiya Jidda tana daga cikin mata masu saa a duniya. Ta samu miji ga kyau ga kudi ga tarbiyya ga ilimi uwa uba kuma gashi yana balain sonta"

Sai hirar da juya ta koma akan irin dacen da nayi da miji, duk a kokarin su na making me feel better kuna naji dadin sosai dan ina so inji ana yabawa Umar. A haka sukayi ta zame jiki suna tafiya.

Bayan sun tafi ne na dan bude fuskata da kumburarrun idanuwa na, Farhan ta matsa min wai lallai sai na sake wanka ni kuma naki yi tunda da zamu taho bayan magrib sai da nayi wanka kuma yanzu bayan ishai sai in sake wani? Sai kace kwaduwa? Banyi wankan ba dai amma na dan gyara fuska ta, sai kuma barin turare da Mufida tayi min a jiki kala kala ta ringa fesa min a kowanne loko na jikina, suka hadu suka gyara gidan fes suka kuma saka turaren wuta a ko'ina yadda daga ni har gidana duk kamshi muke yi, sai kuma zaman jiran angwaye.

Anan falo muka zauna jiran su, su Mufida su uku, Farhan da Aira, Maryam, sai kawayena na school of nursing su uku. Angwayen ba su zo ba sai tara da rabi, kamar yadda muka yi tsammani classy abokan sa bisa jagorancin Bashir su suka rako shi, tun daga waje muka jiyo hayaniyar su daga dukkan alamu tsokanar sa suke yi, muka yi sauri muka shirya Farhan har da kara rufe min fuska tana tuna wa sauran kawaye irin kudin da zasu karba a matsayin na siyan baki.

Sai dai suna shigowa Umar bai bi ta kan kowa ba ya doso inda nake gadan gaban, ina jin kawayena suna retaliating, Mufida har da zuwa gabana ta tsaya tare da rike kugu, yana zuwa ya saka hannu daya ya ture ta gefe sannan ya saka hannu biyu ya kama nawa hannayen ya mikar da ni tsaye sannan ba tare daya jira komai ba ya jawo ni zuwa kirjinsa ya rungume.

Ina jinsa ya sauke sassanyar ajjiyar zuciya yana kara matse ni a kirjinsa, sannan a hankali yace "welcome home Baby" naji murmushin da Farhan take cewa zanyi yazo fuskata sannan a hankali nayi rising hannayena da suke sides dinsa na hade su a bayan sa tare da cewa "thank you dearest". Sannan na lumshe idona ina shakar daddadan kamshin sa.

Ihu da sowar yammata da samarin ne ya saka ni bude ido na, sai kuma na sake shi ina kokarin ture shi cikin jin kunyar su. Ina jin Farhan tana cewa "munafuka na dauki hoton ki ai sai na nuna wa Aunty da Umma" na juya side din ta ina yi mata alamar roko. Umar ya sake ni shima sannan ya rike hannuna muka juya muna kallon su, kusan kowa da waya a hannun sa yana daukar mu hoto, a raima mace na shiga uku shikenan za'a ga hoto na a rungume a jikin namiji, sai wata zuciyar ta tuna min cewa namijin ai miji na ne kuma Umar dina ne and I felt I don't care, the whole world can see it.

Yace "what are you guys still doing here? Na dauka kun tafi ai. Thank you thank you thank you, but your presence is no longer needed, a gaida gida" Bashir yace "in baka kore mu ba dama ai baka cika Umar Faruq ba. To babu inda zamu je in muka ga dama ma anan gidan zamu kwana ko ya kuka ce guys" Mufida tace "aa banda kwana dai, za dai a bamu kudin siyan baki sannan a kaimu gidajen mu bayan an gode mana ba wai an kore mu ba" Bashir yace "wannan duk mai sauki ne, zamu kai ku har gida kuma zamu sallame ku, amma mu dai kam tunda wannan angon ya wulakanta mu kuma ya kore mu to anan gidan zamu kwana. Ko ya kuka ce?" Sauran abokan suka fara amsawa da eh, duk suna kallon Umar cikin tsokana.

Sai ya daga kafada "okay, no problem, ga dakin baki can ga kuma palo nan wanda bai samu guri ba sai ya kwanta akan carpet. And please in kun gaji da zama zaku tafi make sure you close the door. Sai da safen ku"

Ya juya ya doshi hanyar dakunan mu hannunsa cikin nawa, ni dai duk kunya ta ishe ni kamar kasa zata tsage in shige ciki. Har mun kai bakin kofa sai ya juyo yana kallon Bashir. "Na bar kaji na a mota, bring them please. And in ka kawo be a good boy and knock on the door sai ka ajiye a bakin kofa ka tafi" ina jin suna ta dariya yayin da Bashir yake babatun Umar bai isa ya aike shi ba,ni dai ban dago kai na kalle su ba dan bana jin zan iya kallon idon su amma su ko a jikin su. Kawayena ma duk babu mai cewa komai

Please Login or Register in order to submit comment