Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abba ya sanar masa kuma ya roke shi ya bar ni inje, Abba ya bari kuma yayi min fatan alkhairi. Da ranar tazo ma Umar din ne yazo dauka na, na shirya cikin sabuwar abaya ta maroon da Aunty Afia ta siya min, light make up tunda exam zanje, sannan nayi rolling mayafin abayar, amma dana kalli kaina a madubi sai naga nayi kyau sosai fiye ma da yadda na saka ran zanyi, sai dai na lura cikar kirjina ta bayyana sosai kuma veil din iyakacin kafada ta ya tsaya min, wannan yasa na samo bakin medium veil na yafa akan kafaduna ya sauko ya rufe kirjina. Sannan na dauki bakar jakar da na saka duk takardun da ya gaya min in tafi dasu a ciki.

Na fito ina kallon Umma ina saka ran ta kora ni tace in saka hijab amma sai naji bata ce komai ba, wannan ya tabbatar min da shigar tawa tayi dai dai. Na hau nayi wa Abba sallama sai ya hada ni da Amira yace mu tafi tare.

A waje muka samu su Umar, tare suka zo daukar mu shi da abokinsa Bashir, a ranar na fara ganin Bashir. Muna fita ya bude min baya na zauna yana ta bina da kallon dana tabbatar na birge shi ne "da motar da mai motar duk naki ne" ya rada min yadda Amira ba zata ji ba, Bashir yace "gulmar me ake yi ne? Kai fa dan iska ne" sai Umar yayi dariya ya koma gaba ya zauna Bashir yana tuka motar, "in ni dan iska ne kai kuma ai shege ne" suka sake dariya, sai naji ban ji dadin yadda suke zagin junansu a matsayin wasa ba, to ko haka maza suke tasu abotar?

A hanya ne Umar yake cewa "Baby ga abokina, ko kuma in ce oga na. Shine mai private clinic din da nace miki ina yiwa aiki, kuma senior na ne tun a school sannan kuma yana da ruwa da tsaki a cikin duganarwar makarantar ku shi yasa nake ta bragging cewa baki da problem, dan haka sai kike yi masa ladabi. Sunansa Bashir Ibrahim" nace "ina kwana Malam Bashir. Sannu da hidima fa, an gode" ya gyara mirror din motar zuwa kai na yace "da baki gaishe ni ba sai da kika ji zancen faduwa exams?" Nayi murmushi "lah ba haka bane ba fa" yace "kuma bana son Malam din nan, ki ce Bashir direct dan Malam yana saka ni inyi feeling kamar tsoho especially in ina tare da kyawawan yara irin ku" Umar ya saka hannu ya mayar da mirror din dai dai sannan yace "au kai da daukan ka kake yi yaro? Ai chus ne kai".

Haka suka cigaba da hirar su suna tsokanar juna har muka je makarantar. Ni kuwa duk na bi na tsure. Muna tsayawa Bashir ya fita, Umar ya juyo ta bangare na yana min magana a hankali "hey ba wahala fa, am sure zaki ci kinji Baby na?" Na gyada kai, tashin hankali na shine kar inje in fadi inji kunya a gaban saurayi da kuma abokin saurayi. A haka Bashir ya dawo ya kawo min attendance sheet nayi signing sannan muka fita gabaki daya suka rakani har kofar hall din da zamuyi test din sannan suka koma bakin bishiya suka zauna jira na.

Kusan duk tambayoyin da aka yi mana na san amsoshin su dan haka ban wani samu matsala ba alhamdulillah. Bayan mun gama muka yi submitting tare da photocopies na credentials din mu sannan muka fita. Ina fitowa na hango Umar ya mike sannan ya taho muka hadu a hanya bakin sa har kunne, "from the way da kike ta smiling nasan tayi sauki sosai" na gyada kai, yace "alhamdulillah" Bashir ya karaso tare da Amira a gefensa suna tambayata ya paper din, "alhamdulillah, tayi sauki sosai" Bashir yace "wow, ban taba jin wanda yace pretest tayi masa sauki ba sai ke, lallai ke din ta daban ce, and I think this calls for a celebration ko ya kace Faruq? Ya kamata mu tafi dasu mu danyi celebrating mu sha ice cream"

Sai naga fuskar Umar ta chanja yace "uhmm, I don't think so" Bashir yace "why not?" Umar ya danyi murmushi yana shafa kai yace "bana son muyi laifi a gurin Abba. Gwara mu mayar dasu gida kawai" Bashir ya sake cewa "Abba a ina zai san inda muka je? Ai bai san yaushe suka gama ba kuma ma the day is still young ba wai dare ne yayi ba" Umar ya sake girgiza kansa fuskar sa ta fara nuna alamar bacin rai "no, gida zamu kai su direct".

Ganin musu yana kokarin sarke wa a tsakanin su yasa na ja Amira muka tafi gurin mota ina bata labarin irin questions din da aka bamu. Mun dan jima muna tsaye kafin su taho, sai na lura kuma tension din tsakanin su was no longer there, kafin mu shiga mota Bashir yace "I must comment to you Jidda, ke ce mace ta farko data sace zuciyar abokina, ya saba sace zuciyoyin mata amma shi ba'a taba samun wadda ta sace ta sa zuciyar ba sai ke. Hope zaki rike min shi da amana" na kalli Umar da yake tsaye yana ta zabga murmushi nima na mayar masa sai yace "ana baki amana ta baki ce komai ba" na sunkuyar da kai na sannan nace "na karba, na kuma gode" "nine da godiya" ya fada da dariya a muryarsa.

A Oasis naga sun tsaya sannan suka yi excusing kansu suka shiga, few minutes suka fito da ledoji suka dawo muka karasa gida, bayan sunyi packing ne Umar ya bawa Amira ledojin hannunsa, ta karba yayin da ni kuma na bita da harara, yace "tunda ta harare ki kar ki bata ko dandane" tace "ai kuwa tunda ka fada ba zan bata ba, ni da Farhan zamu cinye"

Bayan ta shiga nima ban jima ba nayi musu doguwar godiya su kuma suka yi min fatan nasara sannan na bi bayan ta.

A falon Umma na tarar an baje ledojin da Amira ta shigo dasu, har da yaya Tahir da Abbah kowa ya dauki burger da ice cream. Ina shiga Abbah ya fara tsokana ta "ka ga likita matar likita, kina tafiya allura tana zuba"


Ga masu son siya zasu iya turo kudin su #300 zuwa wannan account din

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai su turo evidence of payment zuwa wannan number din ta hanyar WhatsApp
08067081020

Wadanda basu da account kuma zasu turo MTN recharge card na 300 zuwa wannan number din 08067081020

Please banda kira, WhatsApp only


*Episode Nine : Engaged*

Soyayya muke yi da Umar mai ratsa zuciya da ruhi, Umar baya iyayin kwana uku ba tare da yazo gidan mu ya ganni ba haka nima duk inda ya kwana biyu bai zo basai inji ko abinci ma baya tafiyar min sosai.

Cikin kankanin lokaci duk jama'ar gidan mu da wadanda suke cikin gidan da kuma wadanda basa ma gidan a lokacin amma sun san labarin Doctor Umar saurayin Jidda, a lokacin na kuma fahimtar abinda ake kira da yan'ubanci dan kiri kiri Hajiya da yayanta suke nuna rashin jin dadin su da irin saurayin da na samu, a inda ita kuma Umma take sakin bakinta tayi ta mayar da magana a duk lokacin da aka jeho mana ita. Amma wannan sam bai taba amintakar mu da Farhan ba, su suna harkokin su mu muna namu.

A bangaren Umar shima a yanzu duk yan gidan su sun san da zama na kuma sun san abinda yake tsakanin mu, dan ranar nan kawai sai ga Mama ta kira Umma a waya wai ta kira ta su gaisa, haka Aunty ita ma ranar nan ta kira. Mufida ma yanzu ta fahimci yayanta da gaske yake dan haka ta saki jiki da maganar musamman yanzu da suka gama hutunsu a Lagos suka dawo Kano Umar ya samu damar yin amfani da ita wajen yin waya dani, ya kansa ta kirani in karbi wayar mu gaisa sai yace in rike wayar kar in mayar wa da Umma sai shi kuma ya kira ni da layinsa.

Soyayyar Umar mai dadi ce, irin mai tsayawa a rai din nan ce, kalaman sa masu dadi ne dan zan iya cewa Allah yabashi baiwar tsara kalamai yadda duk wanda aka gayawa sai sun shige shi kamar yadda kullum suke shiga ta.

Kamar yadda Umar yayi min alkawari haka ya tsaya kai da fata, da karfinsa da lokacin sa da kuma aljihunsa wajen ganin yayi min securing admission a school of nursing, har Allah ya taimaka aka samu din. Sanda aka samu da kansa ya dauki takardar ya kuma dauki mota ya tafi office din Abba yaje ya kai masa, Abba yayi murna sosai ya kuma saka albarka. Sai kuma Umar ya sake rokonsa wata alfarmar daban "Abba nace idan babu damuwa idan kuma ka amince ina roka mata alfarmar ta fara rike waya, saboda harkar makaranta idan babu waya a hannunta karatun ba zai tafi mata dai dai ba, saboda yanzu ma in taje registration dole akwai inda za'a bukaci number din ta kuma......." Abba ya daga masa hannu "na sani, nasan duk wadannan tsarikan. Doctor Umar kana son Jidda ne zaka aure ta?" Umar ya sunkuyar da kai yana shafa keya, sai da Abba ya maimaita tambayar sannan ya amsa "eh Abba haka ne" sai Abba yace "to in ka koma gida ka turo min magabatan ka muyi magana da su".

Yana komawa gida nima ya aika aka kirawo ni "banyi niyyar aurar dake a yanzu ba Jidda, niyya ta sai shekara mai zuwa zan aurar daku ke da yaruwarki, kuma har yanzu ina kan wancan niyyar sai dai dole a danyi wani motsi dan bana son ki fara makarantar nan haka kai tsaye, gwara ko babu aure ace da baiko" ya miko min admission letter din tare da yar karamar Nokia phone. Na saka hannu biyu na karba, ya cigaba "kin samu makaranta ga takarda nan dazu Umar ya kawo min,ga kuma waya nan dan zaki bukace ta a hidimomin shiga makarantar, sannan kuma sanda ya kawo min na gaya masa nace ya turo magabatansa dan muyi magana dasu" na kasa cewa komai dan na kasa tantance menene nake ji a zuciyata.

Ya cigaba "ina fatan dai har yanzu shine zabin da kike dashi a zuciyar ki? Ko kin chanja?" Na girgiza masa kai a hankali. Ya daga hannunsa "shikenan, tashi kije, zaki iya amfani da wayar amma da sharadin in har na kama ki da laifin yin amfani da ita ta wata hanyar da bata shafi karatu ba to ba wayar kadai zan karba ba har makarantar zan hana zuwa".

Nayi godiya sannan na tashi na sauka kasa ina jin wani iri a raina.

A falon Umma na same ta ita da Amira na ajiye mata kayan hannuna a gabanta sannan nayi mata bayanin duk abinda Abba ya gaya min. Ta dauki takardar tana dubawa, fuskarta tana nuna jin dadin samun makaranta "kai! alhamdulillah, Allah mun gode maka. Kai wannan yaron Allah yayi masa albarka. Hausawa dama sunce juma'ar da zata yi kyau tun daga laraba ake gane ta wannan jumaar alamu sun gama nuna mana mai kyau ce insha Allah. Allah yasa kin shiga a saa shi kuma da ya tsaya Allah ya saka masa da alkhairi".

Farhan kuma wayar ce tafi daukan hankalin ta "wow, mun samu waya. Bara in zo in kira Man" na kwace wayata "ke rufa min asiri, Abba yace zai kwace in dai nayi wani abu wanda bai shafi makaranta ba" ta harare ni "shima Abba neman magana yake yi kawai, in dai har ba'a kira Doctor da wannan wayar ba ai bata cika waya ba".

Ai kuwa tayi gaskiya dan kuwa da number dinsa nayi activating layi na, sai dana shiga dakin mu na kwanta a kan katifar mu na ja pillow na rungume sannan na kira number dinsa dana dauka a wayar Umma. Bata jima tana ringing ba ya dauka. "Hello" nayi shiru ina murmushi, ina jin dadin jin fitar numfashin sa, "who is on the line please?" Ya sake fada, nace "hi" ya danyi shiru sannan yace "Baby! Is that you?" Nace "nice Doctor" yayi ajjiyar zuciya "Allah ya saka wa Abba da alkhairi. Gaskiya Abba yana sona Allah ya bani ikon mayar masa da soyayyar sa" nace "ameen. Ya kawo min takarda dazu, Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"

Yace "bana hana ki yi min godiya ba? Ni dai fata na in kyautata miki kiji dadi, in dai kinji dadi a ranki shikenan ni kin biya ni duniya da lahira" nayi murmushi ina jin dadin kalaman sa "ya office?" Yace "alhamdulillah, gashi muna cikin sa" "har yanzu baka koma gida ba? Kar fa ka gaji da yawa ka kasa tashi gobe" yace "tunda na samu abokiyar hira ai babu ni babu gajiya, already wadda nake ji ma ta wartsake" nace "haba dai, daga magana?"

"Eh mana, maganar ai ba common magana ba ce ba, maganar matata Jidda ce" nace "yaushe aka daura ni ba'a gaya min ba?" Yayi dariya "an kusa ai, ko Baba bai gaya miki abinda ya gaya min dazu ba?" Nace "ya gaya min" yace "Allah? Amma banji kina murna ba, ni da nake tunanin yau ba zan iya bacci ba saboda murna" nace "nayi mana, kawai dai nayi mamaki ne" yace "nima nayi mamaki, na dauka sai zuwa next year haka sannan zai bani wannan damar amma naji dadi sosai,naji kamar an kara min matsayi ne a rayuwa. Jidda You have no idea yadda nake jin ki a zuciyata dan ko gobe Abba yace inzo a daura wallahi a shirye nake. Ni sai da ya fadi haka ma sannan na kuma fahimtar yadda na matsu kizo gida na, ko dan ina ganin kamar nesa tazo kusa ne?"

Nace "ka daina irin wannan maganar fa, kaga kana saka ni jin kunya" yace "to ki daina sauraron kunya ballantana ki ji ta, ni kawai zaki saurara muryata kawai zakiji banda ta kunya" nayi dariya, yace "har na kira Aunty fa na gaya mata kuma nace ta gaya wa Baba, already am sure ta riga ta gaya masa ma maybe har ya fara hado kan wadanda zasu zo din" na bude baki "da wuri haka? Ai ka bari ka koma gida sai ka gaya masa da kanka tunda yana gari ko?" Yace "and risk the chance of Abba changing his mind?" Nace "never. He never changes his mind. Kuma yana son ka ai" yace "ni kuma ina son yarsa" nace "ohh wato yar sa kake so ba shi ba ko? To sai na gaya masa" yayi dariya "kar ki hada ni da babana"

Haka muka yi ta hira har sai da naji anyi min warning welcome bonus din da aka bani ya kusa karewa sannan nayi masa sallama da cewa "bara in barka haka dan kar patients dinka su jira ka" yace "already ma gasu suna jira, let them wait" nace "wai kana nufin patients suna jiran ka kake hira?" Yace "eh mana, ai sawun giwa ne ya take na rakumi" nace "a'a ka koma gurin su, ai lafiya tafi komai" yace "yes ma, an gama".

Ban jima da ajiye wayar ba naji shigowar message, na dauka na duba naga kudi aka turo min layina na 5k, duk da ban fahimci daga waye ba amma nasan daga shine dan a yanzu shi kadai ne yake da number ta. Na yi murmushi sannan na aika masa da sakon godiya wanda bai yi min reply ba dan ya sha hana ni yi masa godiya a duk sanda yayi min wata kyauta. Amma ba zan iya kin yi masa godiya ba duk da yawan alkharinsa gare ni yafi karfin godiya.

Kunya wata aba ce da ake alakantata da fulani, amma a gidan su Umar zan iya cewa an samu akasi dan kunya tana daga cikin abinda basu sani ba, ko wayewace ta kawo haka oho. Na riga nasan Umar bashi da ita, haka ma Mama dan bayan Umma har ni takan kira wai zamu gaisa, to ban kuma tabbatar da rashin ta idon su ba sai ranar da aka zo neman aurena, Baba ne da kansa yazo tare da kannensa biyu da kuma amininsa guda daya suka zauna a sitting room tare da Abba da Alhaji Saleh babban abokin sa da kuma wani cousin dinsa Malam Umaru. A cikin gida kuma Aunty Afia tazo muka hadu aka shirya wa bakin lafiyayyen abinci da abin sha aka kai musu.

Bamu san me suke tattaunawa ba ba kuma musan ne suka yanke ba sai kawai ganin Baba mukayi yazo yace wai in shirya inje in gaishe su. Na rike baki ina zaro ido, Umma tace "ya za'a yi taje ta gaishe su? A ina aka taba yin haka?" Yayi yar dariya, inajin na jima ban ga Abba cikin farin ciki irin na ranar ba yace "surukinta ne yace sai ya ganta zai tafi, ita ce surukarsa ta farko kuma zai jima kafin ya sake wata dan next dansa namiji shekarar sa biyar" Aunty Afia tace "to fa! Wannan kamar ba fulani ba? Wannan ina jin dashi za'a zo daukan amarya" duk suka yi dariya, ga mamaki na harda Abba a dariyar.

Ya fita yana cewa "ku shirya ta dai dan Allah sharp sharp taje ta gaishe su" haka Aunty Afia ta shirya ni tsaf a cikin sabuwar laffayar da a ranar ta kawo min ita tace siya mana tayi mu biyu ni da ita iri daya, ta feshe ni da turare amma bata yi min make up ba sai dan rufe min rabin fuskata da laffayar, da kanta ta fita gurin Hajiya neman Farhan tazo ta rakani amma Hajiya ta hana ta fitowa tace bacci take yi, haka Aunty ta yafa mayafin ta da kanta ta rakani.

Ni dai a lokacin ba zan iya ganewa waye Baba a cikin su ba dan ban dago ido na kalle su ba, tunda na gaishe su kuma sai naja bakina nayi shiru ina jin su suna gaisawa da Aunty sannan suka doddora min kudi a bakin laffaya ta suka fita tare da Abba suna ta hira da dariya. Yanayin yadda suke yi kadai ya tabbatar min da cewa komai ya tafi dai dai. Hakan kuwa Abba ya tabbatar mana bayan ya dawo daga raka su. "Na bayar da Hauwa'u ga Umar. In sun shirya zasu zo a saka rana"

Aunty Afia tace "Allah ya sanya alkhairi to, Allah yasa abokin zamanta ne har abada. Amma ji nake za'a fara bincike akansa tukunna" ya mike "ai ku matsalar ku kenan mata, ku baku san abinda ake ciki ba kuce sai kun shiga cikin magana, tun yaushe nake binciken? Ai sai dana tabbatar nasan duk abinda ya kamata in sani sannan nace masa ya turo din" tayi shiru bata ce komai ba dan ta san ba lallai ta fadi masa mai dadi ba. Yana fita ya kira hajiya "ki gaya wa Farhan itama ta zaba a cikin maneman ta tace ya fito, tare zan hada su nan da wata goma masu zuwa" daga haka ya haye sama.

Aunty ta kalli Umma "wata goma? Why wata goma?" Umma ta daga hannu "Allah masani, ni ban san mai yake shirya wa ba" suka cigaba da hirar su ni kuma na shiga cikin daki na kwanta ina jin mixed feelings a zuciyata. Ina jin Umma ta bawa Aunty kudin da aka bani tace ta tafi dasu ta ajiye saboda abinda yake gaban su.

Ba'a dauki dogon lokaci ba suka dawo suka kawo kudin sa rana, gaisuwar uwa da uba da kuma sadaki gabaki daya. Sun nemi a saka lokaci kadan kamar yadda Umar ya gaya min zai nemi suyi, amma sai Abba ya saka wata goma kamar yadda ya riga ya fada, duk bamu san dalilin sa ba sai da yaya Tahir yayi mana bayani "ina ganin Abba yana son ya karbi pension dinsa sai yayi amfani da shi gurin hidimar auren su" Umma tace "pension kuma? Wanne irin pension bayan baiyi retire ba?" Yaya Tahir yace "yayi, wannan watan yayi, bashi kuma da wani savings da zai ishe shi auren su" Umma ta rike baki tana mamakin halin Abba, yayi retire ba tare da su matan sa ya gaya musu ba sai dai yayansa maza ne kadai suka sani dan shi a tunanin sa yana ganin sune zasu bashi shawara mai kyau tunda sune maza.

Na tashi zaune daga kwancen da nake nace "wai lokacin retirement dinsa yayi?" Yace "eh yayi mana, tun last year sun dan daga masa kafa ne kawai" Umma tace "kuma idan yayi amfani da pension dinsa yayi wa yayansa aure shi kuma mai zai rike a hannunsa? Na dauka amfanin pension shine mutum ya ja jarin da zai cigaba da rike kansa zuwa karshen rayuwarsa?"

Tahir yace "ai bana jin zai karar dasu duka, dole zaiyi plan for the future, in ma baiyi ba ai yana da manyan yayan da su ya kamata su cigaba da rike shi tunda shi yayi spending all his working years ne wajen inganta tasu rayuwar" Umma tayi ajjiyar zuciya tare da cewa "to Allah yasa. Amma bana jin hakan abu ne mai yiyuwa. In ma zasu rike sai dai su rike uwar su mu kuwa uwarsu ba zata barsu suyi mana komai ba" sai ta dawo da hankalin ta kansa tace "dole ne kai ma ka shiga kasuwa Tahir, ya kamata ka raba karatun nan da kuma kasuwanci dan ka samu ka hada biyu" ya shafa kansa "insha Allah Umma".

A ranar da aka saka ranar yazo shi da Bashir "amaryar mu" Bashir ya fada cikin tsokana. Na rufe fuska, Umar yace "amaryar ku a ina? Ka daina sa mata plural tawa ce ni kadai" yace "okay tun yanzu zaka fara nuna isa a kanta? Wannan in muka je gidan ku a gate za'a ke ajiye mu" yace "au da kana tunanin zaka shiga ciki? Ai a bakin gate zaka tsaya a miko maka ruwa ka sha ka kara gaba, ko kofar falo ba zaka hango ba" na murmusa "ogan naka kake gayawa haka?" Yace " Baby, a cikin asibitin sa ne kadai yake oga na, in muka fito waje ni ne ogan sa yanzu"

Bashir ya gyara zama yana kallon sa da mamaki yace "ta yaya ka zama oga na? The last time I checked ko a school ni senior dinka ne" Umar ya dora kafa daya kan daya yana kadawa yace "ni yanzu an saka min rana, I am one step ahead of you yaro, kai ko budurwar kirki ba ka da ita" Bashir yayi dariya "lallai kai tantiri ne, amma ni na fika tantiranci. Zan baka mamaki dan a cikin satin nan zaka ji an daura min aure, kuma tunda kayi min wulakanci ko gayyatar ka ba zanyi ba sai dai kaji labari"

Nace "a'a ba za'a yi haka ba ogan mu, ina bada hakuri a madadin sa" yace "to kaci sa'a Jidda ta rarrashe ni ta kuma roke ni Allah da annabi na fasa" suka yi dariya tare, Umar yace "kai kam dai ai sai an nada ka bachelor's king na dukkan Kano kafin kayi aure" ya juyo gurina yana nuna shi yace "wannan da kike gani duk girman sa ko budurwa bashi da ita" Bashir ya mike tare da cewa "bara dai in tashi in tafi zance nima tun kafin wannan dan guguwar ya kwance min zani a kasuwa" suka sake dariya sannan suka yi musabaha ya fita.

Shiru ya biyo bayan fitarsa, sai abin ya zame min wani iri dan shiru bata fiya ratsa tsakani na da Umar ba. Sai na dago kai dan inga halin da yake ciki, yana zaune da wayarsa a hannunsa yana dannawa fuskarsa dauke da murmushi, hankalin sa gaba ki daya yana kan wayar da alama abinda yake yi yana yi masa dadi sosai. Sai naji wani abu ya taba zuciyata na tabe baki a hankali nace "ina kishi" bai kalle ni ba still cikin wayar yake kallo murmushin sa yana kara fadi yace "really? Kishin me?"

Naji raina ya kuma baci sai na dauke kai ban sake cewa komai ba, ina lissafi a raina cewa in na kirga goma bai ajiye wayar ba zan tashi in shiga gida in

Please Login or Register in order to submit comment