Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Babu islamiyya, zuciyarshi ce ta qarfafa Mai gwiwa akan cewa SUNA saloon din wata qila Basu ji Kiran nashi ba ko Kuma duk sunsa chargy zuwa anjima Daya daga cikinsu zai kirashi, wucewa inda zaiyi yyi gidan childhood friend dinshi ne su ukune suka taso tare da sulaiman ko shekara uku beyi da rasuwa ba yanzu saura su biyu sosai abdurrahman yaji dadin ganinshi sai tsiya yake mishi yaqi aure gashi shi yaranshi hudu, dariya Dr Hammad yyi yace karka damu mama taban deadline din 6months idan ban kawo ba zatamin auren dole, wata dariya Abdurrahman ya kwashe da ita yace kace na fara shiri zanje bikinka da boys dina dukkansu wato iskanci zakamin ?? Karka damu nima nayi 'ya Dan hararar wasa YAI Mai yace dake yaran daga sama suke fadowa ?? Dariya kawaii sukayi suka cigaba da Hira sai kallon wayarshi yake Amma Shuru suna cikin hirar ma sai da ya qara dialing numbern Amma Shuru abdurrahman yace ya dai man?? Lfy dai ko?? Girgiza Mai Kai yyi kawai yace bakomai qarfin Hali kawai take ganin magriba tayi yasa suka miqe a toilet din parlor Hammad yai alwala shi Kuma abdurrahman ya shige ciki tare suka fito da matarshi Hammad yai mata sallama Dan daga can zai wuce, GABA yyi Yana qara dialing numbernsu Nan ma shuru ba a daga ba gaba daya hankalinshi ya gama tashi Hakan yasa bayan sun fito yai ma abdurrahman sallama ya wuce gida, sallama YAI ma mama yace may be da sassafe na wuce zaria zan Dan yi wasu abubuwa, mamatace gobe Kuma?? Bazaka bari sai jibinba knan qa zauna ka qara duba abubuwan da na fada maka girgiza Kai kawaii yyi yace mama Idan akwai wadda kike ra'ayi ki fada ni Banda matsala amma indan ta nine mama Akai kasuwa daquwa tai mishi ya Dan sa dariya Allah mama,miqewa yyi yace bari in dauko jakata, na fito yana fitowa yai mata sallama ya nufi gidan yayan babanshi be taba haihuwa ba so yana riqe yara Saida Hammad ya girma sosai sannan ya daukeshi ya maidashi gabanshi so Yana da daki a gidan sosai matar wadda suke kira da maman lawcoast tai farin ciki da ganinshi fada tai tayi mishi yaqi hidda mata yyi aure yace insha Allah za'ayi mama baban Kam kaca kaca yai mishi yana fadin duk laifinshine da ya barshi haka haquri yyi ta bashi har suka shirya suka cigaba da Hira sai wajan goma yaga kiran Maryam baby shiri ya miqe yai ma baban sallama ya fita Yana dialing numbern Maryam daga wa tai murya can qasa kamar ta Wanda yai kuka tace likita ina wuni gaban shine yace rass.........



Mrs maan 🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: ~*AMATOU*~🧕🏻
(The single mother)


16

Cikin qarfin hali da dakewa yace maamaa lfy qalao alhamdulillah sai Kuma ya kasa daurewa yace I hope all is well, muryarta na rawa tace likita Farrah muka nema muka rasa cike da mamaki yace Farrah kuma? Garin yaya ?? Dama tana fita ne?? Maryam taja hanci sannan tace wai fa suna zaune a parlor da umma rabi taji qarar MOTA a qofar gida to duk sun zata Kaine shine fa farrahn ta fito qofar gida shikenan shuru Shuru Bata dawo ba to ita ta dauka tare kuka fita saida muka koma gida umman take mata bayani shine take cewa ai bama ka gari ko dazu da safe kunyi waya dafe goshi yyi yana fadin hasbunallahu wa'ni'imal wakeem innalillahi wa'inna ilaihirraju'un yanxu ku kuna Ina ?? Tace gamu a police station keda wa? Dukkan mu harda umma rabi ok bata wayar, wa?? Anty Mimi ?? Eh Bata toh tace sannan ta miqe daga inda take ta qarasa inda amatou take tace anty mimi likita yace in Baki wayar, amatou da idanunta sukai sutum sutum sunyi jawur hancin Nan yai ja ta Kalli wayar kamar baxata karba ba sai Kuma ta karba ta Kara a kunne a hankali yace hello?? Shuru tai idanunta suna cikowa da hawaye Dan idan tace zata bude baki to kukane zai fita maimakon magana, for the very first time a rayuwarshi yace AMINATOU?? Cikin rawar murya tace umymm Shuru yyi yace kiyi haquri kinji?? Hawayen da take riqewa ne suka gangaro sai ya fashe da kuka shuru kawai yyi ya dafe goshi Yana karanta addu'a a zuciyarshi Amma kafin kace me idanunshi yyi ja, katse wayar yyi ya miqe tattara kayanshi yyi ya fita sadab sadab ya bar gidan tare da cema me gadi yace ma masu gidan Kiran gaggawa akaimin shiyyasa gida ya nufa da zai iya wucewa ba tare da yaima mahaifiyarshi sallama ba da yyi Amma bazai taba iya Hakan ba balle Kuma tafiyar dare ce yana tsananin buqatar addu'arta duba da yanayin tsaro da yyi qaranci akan hanyoyin, har Mai gadi ya kwanta yaji horn Bude qaramar qofa yyi Hammad ya rage hasken fitilarshi Dan me gadi yaga cewa shine yana Gani kuwa ya rufe qofar tare da bude babban gate din danna Kai cikin gidan yyi yana saukowa ya nufi me gadi yace Hamisu karka kwanta yanxu zan fito to yallabai Yana fadin haka ya juya ya shiga cikin parlorn sannan ya wuce bangaren maman Yana Jin surutu a dakin Yan Matan Bai kula ba nufi dakin maman kwankwasawa yyi sai da yai ta uku sannan maman ta tambaya waye Dan ta fara bacci qasa qasa yace mama nine Hammad?? Na'am mama shigo tace Dan Riga ce doguwa me kauri a jikinta ta bacci sai hula shigowa yyi Yana kunna fitilar dakin da mamaki take kallon shi tace lafiya DAI ko dan kana kallon fuskarshi kasan ba qalao ba qarasawa yyi ya durqusa qasa gefenta yace mama zaria nake son zuwa kallon agogo tai da sauri taga sha Daya da minti tace yanxu Kuma me ya faru?? Shuru yyi Bai San ta ina zai fara ba yace mama wata yarinya ce kin sanni da Yara muka Saba da ita to Ina zuwa in dauketa muje yawo mu dawo to shine wai yau taji qarar MOTA a qofar gida ta dauka nine shine fa ta fita to tunda ta fita har yanxu ba'a ganta ba tunda wadda suke tare ta dauka fita mukai naita kiransu Basu daga ba sai yanxu qanwar maman yarinyar take min bayani maman tace yar waye ?? Su waye su? Dan Sosa qeya yyi yace maa it's a long story zan maki bayani insha Allah idan komai ya dai daita yanxu sallama nazo nai miki tace Muhammad a wannan tsohon Daren zakace zaka tafi Zaria ?? Babu inda zakaje idan ka je ma Babu abunda zai canja sai dai ayi ta addu'a Allah ya bayya nata Dan haka ka bari sai gobe idan yaso sai kayi sakko 6am sai ka tafi kallon mama yyi ba zai iya mata musu idan ya turje ma sai ya tafi zaije ya Bata biyu ne Daya bata gyaru ba tunda bata so din kawaii yace to mama Allah ya kaimu da rai da lfy gwiwa a sanyaye ya miqe yace to mama sai da safe, binshi tayi da kallo sai Kuma ta dauke Ido bazata iya barinshi ya tafi ba, Wanda ke cikin Katsina ma sai dai idan Allah ya kareka balle Kuma ka bi hanya cikin dare gara da safen ya tafi ko bbu komai gari yyi haske akan cikin dare dukda dai rashin tsaron ba ruwanshi da Rana balle dare duk lokacin da suka so tsiyarsu yinta suke, yana fita parlour suka kusa cin karo da Aisha baya yaja bayan ya kalleta sau daya Dan kayan bacci ne a jikin ta Dora Yar top din Amma Bata daure igiyarba hannunta riqe da cup din fura da alama wadda ta dama take shanyewa, zagayeta yyi ya wuce juyawa tai ta bishi da kallo sannan tai kwafa ta wuce, Muhammad na shiga daki ya ajiye kayanshi cire kayanshi yyi well build structure dinshi ya fito gargasa kwance a farar fatar jikin shi, daga shi sai short da singlet janyo wayarshi yyi ya na qara dialing numbern maryam tana dagawa yace maamaa Babu wani labari a hankali tace wlh kaga police dinma sunqi su wani bamu muhimmanci wai ai bamu tabbatar Bata tai ba cikin bacin rai yace Baku ce musu Bata San kowa ba ??? Kuma Bata San ko Ina ba?? Wlh mun fada musu yace miqa mata wayar bama amatou wayar tai yana Jin alamun ta karba yace kina jina?? Tace umm ku wuce gida gobe da sassafe zan dawo insha Allah ,kuka ta fashe Mai dashi to ni ya za'ai in tafi ban ganta ba, a hankali yace kiyi haquri zamanku ba abunda zai qara Kuma Indai bbu babba bazasu saurareku ba kinji?? Gyada Mai Kai tayi tace to qara lallabata yai SUNA gama wayar ta miqe tace umma mu tafi itama hankalinta a tashe duk tayi zuru zuru gida suka nufa dakyar suka samu adaidaita kasancewar dare yyi suna shiga duk suka nufi ban daki Dan Babu wanda yai sallar isha'i a cikinsu cuz sai bayan magrib sukai shawarar zuwa police station bayan sun dawo daga yawon nemanta, suna idarwa suka kwanta Amma Banda amatou tana Nan zaune kan salaya tunanin Kiran Mami tayi sai Kuma taga dare yyi Hakan yasa ta kira Yaya Mahmud ganin Bai daga ba yasa ta ajiye wayar kira NE ya shigo wayarta tasan Hammad NE Hakan yasa daga a hankali tai sallama, amsawa yyi yace kun dawo ?? Jingina tayi da gado ta lumshe Ido tace uhmn yace kiyi haquri kinji?? Komai rubutaccene kiyi ta addu'a insha Allah she is safe hawayen daya gangaro mata ta share tace insha Allah yace kinci abinci?? Girgiza Kai tayi kamar yana ganinta yace kije ki nemi abunda zaki ci sannan ki dawo tace bazan iya ci ba tashi ko kadanne kici Bata San doguwar magana hakan yasa ta miqe shinkafa da miyar kifin da sukayi kafin su fita ta debo yar mitsitsiya tana ci Yana jinta harta gama sannan tace tana zuwa sannan ta kashe wayar Maryam ta tasa akan ta ci abinci sannan ta leqa dakin umma rabi ta leqa ta tasheta akan ta ci abinci cewa tai ita Kam sai da safe zataci komawa amatou tai dakinta zama ta qara yi akan sallayarta Shuru tayi sai Kuma ta janyo wayarta kallon sunan da ta Saka Mai tai tayi sai kwanan Nan tai saving da VC Amma da kawaii numbern kawaii take ganewa dialing tai katse Kiran yyi ganin haka ya ajiye wayar tana ajiyewa ya kirata ta daga lallashinta ya ringayi sosai ta ji dadi sai qarfe Daya Wanda Bai ma San time yaja haka ba sukai sallama, ban daki ta fada ta kama ruwa sannan ta dauro Alwala addu'arta Daya Allah yasa farrah is in safe hand qarfe 3 bacci ya dauketa akan sallaya ana Kiran asuba ta farka alwala ta qarayi taxo tai raka'atainul fijr sannan ta jira ayi sallar asuba Wanda a ta Daya bangaren doc Hammad dakyar ya bari 5 am tayi Dan ashirye yai sallar asuba fitowa yyi mama tai Mai Allah ya kiyaye sannan ya dau hanyar zaria.....


Manage please


Mrs maan 🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: *~AMATOU~* 🧕🏻
( The single mother)


17

Wani irin sakayau amatou take jinta duk wata damuwa da fargaba Allah ya yaye mata sai dai kawai tunane tunane Ina Farrah ta tafi ?? Ko Kuma waya dauketa a da zuciyarta tafi tunanin ko kidnappers ne suka dauketa Amma da safennan sai taji zuciyarta tana fada mata ta kyautata zato a Hakan kuwa tai imani, miqewa tai shiga toilet brush tayi sannan ta fito kanta da hula Hakan yasa ta fice daga dakin ta nufi kitchen tasan umma bata ci abinci ba Kuma Bata da tabbas din Maryam din ma ta tashi kunun gyada ta dama musu ta kwaba wainar fulawa tai masu ta manja da ta mangyada yar kadan dan maamaa Bata cin manja buruntunta yasa umma rabi leqowa kitchen din Dan juyawa tayi kadan tace umma rabi ina kwana ganin amatou da Dan kwarinta yasa taji dama dama jiya sun bala'in Bata tausayi gashi tana ji cewa laifinta ne da bata bar farrah ta fita ba da duk haka Bata faru ba hakan yasa ta qarasa kitchen din tace Babu abunda za'a taimaka Miki?? Girgiza Kai tayi tace jekiyi zamanki umma wanke wanke ne Kuma Shima saura kadan na qarasa, nace amatallahi kiyi haquri dan Allah nasan duk laifina da ban barta ya fita ba da duk haka bata faru ba, amatou Bata fasa wanke wanken da take ba tace umma rabi kina tunanin wayona ko dabarar mu zai hana abunda Allah ya qaddara zai faru ya faru??? Babu abunda zai canja ko ni ko ke ko maamaa duk a hannun wata take tunda Allah ya qaddara Hakan zai faru bawa baya kaucema qaddararsa zamu cigaba da addu'a da Kuma nemanta in har Muna da rabon ganinta zamu ganta Dan haka karki wani ce laifinki ne, mudai kawai muyi ya addu'a, sauke ajiyar zuciya umma Rabi tayi sosai taji dadin maganganun amatou Kuma ta yarda da abunda take fada din Hakan ya sa tace da izinin Allah za'a ganta cikin qoshin lfy, amatou ya amsa da Ameen tana qarasa kife kwanuka a cikin kwando sannan ta dauko flask din wainar da kunu ta Kai parlor biyawa dakin Maryam tai ta hangota qudundune kan gadonta cikin bargo qarasawa tayi ta yaye bargon Maryam ta juyo idanunta sunyi bala'in ja dauke idanu amatou tayi Bata son ta karya mata zuciya Hakan yasa ta juya tace ki tashi kiyi brush kizo muci abinci kindai yi sallar asuba dai ko?? Ta tambayane kawaii Amma tasan maamaa Bata wasa da sallolinta, kafinta amsa ta fice dan ta hango sallaya daga can lungun gadonta, miqewa Maryam tai ta dauki brush da toothpaste ta tafi toilet din parlorn zama sukai amatou taja gefe tace ku fara ci bari nai waya kallo kawai suke binta dashi barin maamaa da gaba Daya mamakinta take dukda dai idanunta sun kode sun danyi qoqari take ta nuna she is strong while she is not, Mami ta kira ta sanar mata abunda ke faruwa sosai hankalinta ya tashi tace zasu biyo train suzo insha Allah Dan yanxu suna zama a qasar akai akai, bin Kiran Yaya Mahmud tai Wanda tun asuba yaita kwada mata kira bata daga ba, yana dagawa yai sallama amsawa tai bayan sun gaisa ta hau yi Mai bayani sosai tai qoqari gun hana kanta kuka sosai hankalinshi ya tashi yace mata zaizo insha Allah, kashe wayartai ta matsa ta fara cin abinci a ranta tana Jin she really need elders a wannan zancen da zata ita solving problem din da bama zasu ji labarin ba Amma abun yafi qarfinta balle yanda Taga yan sandan jiya sun yi musu tasan Dan Basu ga manya bane, sun rigata tashi Dan GABA dayansu turawa suke a ba yanda zasuyi, bayan sun gama tace ma Maryam su shirya zasu qara komawa police station din qarfe takwas sukayi ma umma rabi sallama suka fita saida amatou ta biya banki ta qara cirar 50k Wanda kwata kwata Bai kai 500k ba yanzu a account dinta hankalinta Kuma Yana kasan ranta, suna zuwa police station din Babu kowa ba dadewa Hammad ya kirata dagawa tai tare da sallama, yace ance Kuna police station, na Ina kuke??? Fada Mai address din tai, ba dadewa sai gashi kallonshi tai ta dauke Kai Dan sosai yyi kyau cikin light blue shaddarshi kana ganin yanda take kyalli kasan me tsadace dinkin half jumper ne da wando sai black takalmi da agogo me kyau Shima baqi qarasowa yyi amatou ta dan ja da BAYA a ranta tana fadin _noooo please not now_ kallonta yake Kuma yaga abunda tai Amma Bai Maida hankali a Kai ba yace me kuke anan bayan ba kowa, maamaa tace jiransu muke suzo kallon police station din yyi yace ku zo muje, kallonshi amatou tai tana so tace Ina zasu amma ta kasa da sauri Maryam ta qarasa ta bude seat din baya ta shiga qarasowa amatou ta bude gaba ta shiga babban police station din garin suka je yace su zauna a mota cikin minti 30 ya shigar da report na missing person Akai komai aka gama a mutunce Dake sunga kudi Hakan yasa Nan da nan suka tura report ma qananun police stations din suna hanya Mami ta kirasu kan sun shigo zaria Jin haka yasa amatou ta fara musu kwatancen unguwar da suke ganin duk ta rasa yanda zatai yasa ya miqa mata hannu ganin haka yasa tace Yaya farouq bari ayi maku kwatance to yace mata Hakan yasa ta juyo ta Dora Mai wayar a hannunshi ba tare da ya yarda ta tabashi ba, Kara wayar yyi yai sallama,Dan dum farouq yyi sai Kuma ya amsa, Kuna ta wajan Ina?? Farouq ya fada mai daidai inda suke Hakan yasa yace to ku Jira anan bari muzo yana zuwa motoci uku sukayo Dan harda babansu farouq din bin bayan doctor Hammad sukai a dai dai kofar gidan suka parker amatou ta fito hango gayyar Yara sai namiji babba guda daya sai mace itama babba ce dai dai sun fito daya yaron yace daga Nan gidan naga ta fito ta ganmu muna wasa shine fa ta bimu kallon Farrah kawai amatou take wadda tai zuru zuru kana Gani kasan itama taci kuka maamaa tace kamar Farrah , Farrah ko tana hada idanu da mamanta ta fara qoqarin zamewa tana Kiran Mimi ganin inda take kallo yasa mutumin kallon wajan, sauke ta yyi duk karar amatou yau sai da ta ajiyeta kawai ta durqusa ta Buda ma Farrah hannu tana dariya da gudu Farrah ta qaraso ta fada jikinta yaron da yai magana da farko ya hau murna yace ai dama na fada muku nasan gidansu, qarasowa mutumin yyi ya miqa ma hammad hannu a tunaninshi shine babanta Hammad dake ta kallonsu ko kiftawa Babu sun bala'in burgeshi da kuma bashi sha'awa da sauri ya juya ya miqa mishi hannu farouq abdurrahman khalifa da Khalil sai babansu duk suka qaraso suna musabaha Mami Kuma tana gun su amatou, miqewa amatou tayi bayan Mami ta karbi Farrah tace ku mu shiga cikin gidan Mami , to muje magana Mami tai ma su baba akan su shiga ciki mutumin yace bazai shiga ba gona zai wuce yanzun ma sbd da ya kawo Farrah NE sai da ya samo yaran da yasan daga ina take Dan tare ya gansu jiya tana cikin Yara tana wasa yyi mamaki kwarai Dan yawanci yasan yaran unguwarsu ganin magariba tayi tana ta yawon neman gidan su bata Gane ba har ta fara kuka hakan yasa ya qarasa yai mata magana akan Ina ne gidansu sai dai ta nuna Wani waje tacecan Hakan yasa ya kaima me dakinshi ita dakyar tai bacci tana Kiran sunan mamanta shine fa yau da safe naje na tattaro yaran akan daga Ina suka taho da ita Dan yasan alokacin daga jeji suke shine fa wannan yaron yace yaga daga gidan da ta fito shine nace to yazo ya nuna min Dan da bamu samu gidan ba dama police station nai niyyar kaita sosai baban yai godiya farouq yaja hannun yaran yace suzo su rakashi shago sun kusa su biyar suka bishi kallon matar shi mutumin yace kande Zaki iya komawa gida to tace ta juya baban ya zaro kudi da DAMA a aljihunshi kafin ya qarasa Abdurrahman ya miqa mata 5k karba tai Babu fulako taita godiya Shima mutumin yai godiya miqa Mai Shima abdurrahman yai amma yaqi karba Babu yadda basuyi ba sukai akan ya karba Amma yaqi ya wuce zamewa Hammad yyi dama yana daga jikin motarshi daga gefe tunda suka gaggaisa yaja gefe, bin bayan mutumin yai Mai magana juyowa yai murmushi ganin Hammad ne , Hammad yace Dan Allah ko zan karbi numbern ka?? Mutumin yace babu damuwa sannan ya karanta mai, wane SUNA zan Saka ??? "HASSAN" zaka saka yace to na gode sosai malam Hassan sannan sukai sallama ya juya ya koma wajan motarshi ya ja ya tafi yana mamakin Ashe amatou tana da irin wannan family din suke zaune kamar Basu da gata daidai zai bar layin ya hango Mahmud ya sauka a adaidaita Wanda sosai ya ganeshi Hakan yasa ya parker motar tashi a gefe ya sauka ya nufe shi shima Mahmud ya ganeshi miqa mai hannu Hammad yayi da yar fara'a yace barka da shigowa Maida Mai murmushin Mahmud yyi yace barkan mu dai kwanaki bamu tsaya mun gaisa ba sosai murmushi Hammad yyi yace wlh kuwa Mahmud yace Yama sunan?? Hammad yace Dr Hammad Mahmud yace daga gidansu amatoun kake Bai gane waye amatoun ba Amma yasan DAI Wanda yake magana Akai yace eh wlh naga an ganta shiyyasa zantafi Mahmud da sai a lokacin yake ji yace masha Allah alhamdulillah bari na qarasa gidan to shikenan ngd dga haka Hammad ya shiga mota ya bar unguwar, Mahmud ya qarasa unguwar, ganin motoci dayawa a qofar gidan yasa da Dan mamaki ya qarasa gidan ya tura qofa hayaniya sosai yaji a parlorn alamun DAI a cike gidan yake maamaa ce da khalifa suka fito an aikesu siyan lemuka da ruwa maamaa ta qarasa gurinshi tace Yaya sannu da zuwa Yaya anga farrahn ma dazu babu dadewa khalifa yace to hajiya ki bari mana ya zauna kallon khalifa Mahmud yyi yace khalifa kune Ashe , shafa Kai yyi yace eh wlh Ina kwana amsawa ficewa sukai shi Kuma ya shiga cikin parlorn da sallama......




Mrs maan🥰😍
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: *~AMATOU~* 🧕🏻
(The single mother)



18

GABA dayansu Where impressed da environment din da suke baban kawai aka shimfida ma sallaya akan carpet din dake tsaka parlorn Dan tas tas yake Farrah na kan cinyar baban da ruwa a gabanshi Dan katan dayawa suka siyo wasu suka Kai kitchen din amatou dai tana daga gefe bata saka musu baki jujjuyawa baban yyi yace Ina Wanda ya taho damu din yake ??? Kallon kallo suka fara Dan gaba dayansu sun manta dashi maamaa tace laa doctor Hammad ne ko ya tafi?? Mahmud yace na hadu dashi zai tafi har mun gaisa, baban ya kalleshi yace wayeshi ka sanshi knan girgiza yace sau daya muka hadu Dan last month nazo kamar lecturer dinsu amatou ne ko?? Da sauri da girgiza kai sai Kuma ta daga kai gaba daya ta diririce kamar wata tambaya Akai mata ganin yanda ta rude Dan gaba daya sun zuba mata Ido hakan yasa Maryam da sauri tace shine new VC dinmu ne gurin farrah yake zuwa murmushi baban yyi yace masha Allah, Basu da wani isashshen kayan abinci balle tukunyar da zasuyi girkin da zai ciyar da garadan hakan yasa Mami yace su barshi, Mami ce ta kira amatou dakinta that is well neat and tidy GABA Daya sai da ta leqa dakunan su ta ganshi tsaff na umma rabine is not well organized dukda dai Maryam ko amatou suna gyara Mata shi tsaff amma abunka da mutumin qauye Kuma babba bazaka rasashi da Dan tarkace Amma tsaftsaf yake da yar madaidaiciyar ka tifa mami sosai ta Yaba ma qoqarinsu da Kuma zurfin tunaninsu duk basusan anyi wannan ba suna can suna moaning rasuwar barraq bbu wanda yabi ta kansu,durqusawa tai gefen Mami tace kira rabin tukunna dan Mami ya girmeta kusan sosai to tace sannan ta fita ta leqa dakin umma rabi GABA Daya a takure suke ita amatou rashin sabo da baqi haka a gidan ita kuma umma rabi Jin dangin baban Farrah ne yasa duk ta tsorata batasan Babu Wanda yace musu ma ita da Farrah bane a gidan balle har suce ita ta barta ta fita kawai cewa sukai mota taji ta fita ta, amatou tace umma Mami tana kiranki, jikinta na Dan rawa ta miqe sosai amatou ta Kalli umman sai Kuma ta qarasa ciki tace umma da matsala ne?kallon amatou tayi ta girgiza Kai, amatou tace idan da wata matsala ki fada idan Kuma zancen cewa kina ganin laifin kanki akan farrah na ce karki damu kanki kuma ni da maamaa Babu Wanda ya zauna wannan dogon bayanin Dan haka ki kwantar da hankalinki, murmushi kawai tayi sannan ta

Please Login or Register in order to submit comment