Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a qalla zai Kai mata qwaurinta ta saka mata Dan armless atamface a jikinta sai igiya da aka daure a baya still itama kanta Babu kitso sai parking, kama hannunta amatu tai bayan ta saka mata takalmi suka fice, suna fita qofar gida wata mota tana parking a qofar gidansu dauke kai amatou tai Dan bata san motar ba suka fara qoqarin wuce ta, Bude qofar da akaine yasa suka Dan qara matsawa zasu zagaye Amma ganin Wanda ya fito daga motar yasa ta dakatawa Farrah da Bata San me ake ba ta daga Kai ta kalleta sai Kuma ta juya ta Kalli inda take kallo Shima kallonta yake tafi kyau a cikin hijab nesa ba kusa Saka mayafi sai yafi mata kyau a cikin gida amma badai waje ba she look so beautiful dukda baiga complete fuskarta ba Amma ya sani, Jin Farrah a jikinshi yasa ya sunkuya ya daga ta sama ta hau kyalkyala dariya tace uncle Ina ka tafi dariya yyi yace ke zan tambaya Ina kika tafi naxo nazo bakyanan sai na ganki a Wani waje kina bacci zaro idanu tayi tace nake bacci?? Gyada mata Kai yyi, to ai da ka tasheni sai na ganka dariya kawai yyi ya Kalli amatou Dake tsaye tana twisting hannunta kallonta ya cigaba dayi sai Kuma yace ina zuwa?? Da ita yake Amma Farrah yake kallo amatou wadda ta gama qare mai kallo a sace xatai magana Farrah tace shaloon zamu kallon amatou yayi yace shiga mu tafi, Dan kallonshi tayi sai wani sunnar da Kai take tace ai ba nisa yanzu zamuje, da wani irin dakakken murya yace shiga nace sum sum ta wuce ta bude GABA ta shiga, BAYA ya Bude ya zaunar da Farrah ya Bude mata biscuit ya Bata sannan ya rufe qofar ya tada motar suka bar unguwar tana nuna mishi direction din har suka Isa bakin shagon kallon area din yai wajan it looks little bit safe cikin jama'a ne Amma Kuma Babu hayaniya a wajan ganin wajan a bude yasa ya juya ya kalleta Ashe yasa lock ita kuma ta kasa magana, kallonta yyi ganin yanda ta wani ta kura kana gani kasan a matse take da ta fice gaba daya tabi ta nutsu kuma ya San dalili, murmushine ya subuce mai sai Kuma ya dauke Kai ganin zata juyo ta kalleshi, Farrah na baya tana aikin cin biscuit, kamar me rada tace Dan Allah Dan Bude min na fita kamar da lock a qofar, sai da yai da gaske sannan ya danne dariyar da ta so kwace mai so ta iya ladabi haka, juyowa yyi ya kalleta kamar bai San me yake faruwa ba sai Kuma yai unlocking qofar budewa tai ta juya tace Farrah sakko, ba inda zata rakani zatai, kallonshi tai kamar zata ce wani abu sai Kuma ta tuna ko tace ma is useless Hakan yasa ta fita ta rufe qofar Farrah ta hau yi mata bye bye, murmushine ya subuce mata ta Maida mata da bye bye din hada ido sukayi ta dauke Kai ta juya ta shige shagon Maryam da tuntuni take gulma da sauri ta ko ma kan doguwa sofa din shagon tana Dan Sosa Kai hade da murmushi, ko kallonta amatou batayi ba tace Dan iskanci da ba kowa a shagon kika zauna Baki wuce gida ba?? Maryam tace wlh ko 10 mnts banyi da gama kitso ba Amma yau kwata kwata mutum uku ne, Jin haka yasa suka zauna ganin har 5 ba kowa Kuma su Farrah Basu dawo ba yasa tace tashi mu wuce gida Maryam tace to farrahn fa?? Dan harararta tai tace a Ina kika san na fito da farrah Dan Sosa kai tayi tace kafin ki shigo kamar muryarta naji, qara harararta tai ko kunya bakiji ba kina qarya, dariya Maryam kawaii tai suka tattara suka wuce gida zama sukai tana ta contamplating abunda zatai can dai ta janyo wayarta ta tura message din da zata tura ta ajiye wayar.....




Mrs Maan
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: ~*Amatou*~ 🧕🏻

~happiest birthday jannatuna 🥰🙌 Allah ya qarawa rayuwarki albarka, ya Kuma doraki a tafarkin dai dai~



12

Dr Hammad Yana tfy Farrah sai surutu take mai Yana biyeta message ya ji ya shigo wayarshi zaro ta yyi daga aljihun rigarshi, ganin wadda ta turo message din yasa da Dan mamaki ya bude message din fada Mai Tai cewa sun bar shago ba ya Taho da ita gida murmushi kawai yyi beyo reply ba ya cigaba da tuqinshi shurun da yaji farrah tayi ne yasa ya kalleta ta madubi, bacci tayi riqe da chocolate a hannu, cigaba yai da tafiya Yana kama hanyar unguwarsu amatou, daukan waya yyi YAI dialing numbern ta ba jimawa ta daga tai sallama, amsawa yyi can ciki da Wani irin stern voice yace kizo ki dauketa hadiri ya taso to tace a hankali, miqewa tai daga zaunen da take daga ita sai umma Rabi Maryam tana ban daki, tace umma rabi ina zuwa, to sai kin dawo, fita tai bayan ta zura qaton hijab,Yana ganin ta fito ya fito daga motar a hankalin ya rufe sannan ya Dan daga kai hadiri ne sosai a sama yai bakikkirin ga iska a hankali tana kadawa me sanyi yasan yanzu ba lokacin magana bane Amma maganar tana bala'in cinshi a Rai kuma Bai tunanin zata Daina damunshi har sai ya fitar da ita, kallonshi tai ta sunkuyar da Kai shi wannan sussunkuyar da kan dariya yake he just miss the naughty and brave amatou, jin maganar ta yai tace Ina farrahn?? Dan gyara murya yyi yace tana nan Amma kafin ku dauketa I want to ask 1 or 2 questions gabanta NE ya fadi sai Kuma tace tam, kallonta yake sosai tam din da tace she sounds so childish Jin yyi Shuru ta dago Kai zatace Mai ruwa za'a fara fa suka hada Ido dauke Kai yyi sai Kuma ya juyo ya kalleta yace me kuka je yi a Abuja Kuma su waye na ganku tare and gidan wa kukaje?? A lokaci daya ya zubo mata su kamar dama jiran opportunity yake ya fitar dasu, a ranta ji take kamar ta dago tace mishi Ina ruwanka ?? Amma Ina asuwa ta CE ma VCn su haka yanzun ma Nema take ta bashi haquri ita da take lallaba rayuwarta Ina ita Ina fada fadanma Kuma VCn su,Bude Baki tai sai ta rufe Bata San wacce tambayar zata fara amsawa ba, he was so nervous zuciyarshi sai bugawa take da sauri kamar ya shiga zuciyarta ya duba abunda zata ce mai , cikin sanyin murya tace gidan uncle dina ne and the guys are my cousins and they are my in-laws gwiwarshi ce tayi sanyi yana koma BAYA sai Kuma ya kalleta da sauri yace kikace in-laws dinki?? Are still married?? Girgiza Mai Kai tayi yace then ex in-laws dinki dai yanda yai magana da Dan haushi yasa ta kalleshi idanunta sun ciko da kwalla, tace they are my in-laws cuz barraq is still my husband, sai kiyi kuma ai hala baki zuwa islamiyya shiyyasa Bata san sanda ta harareshi ba ai sai ka sakani tunda banayi,murmushi yai ya dauke Kai, sai kuma ta kalleshi marairaice tace sir Dan Allah ka daina pushing Dina Ina Maka rashin kunya kaji ?? And kayi haquri wadanda nai Maka a baya kaji?? Ya ilahi shine abunda kawaii ya iya furtawa he was looking at her straight in the eyes dauke abunka da tsohon tuzuru dauke kai yyi da sauri cuz he can't take it shi dai idan zata cigaba da magana a haka beyi alqawarin controlling din kanshi b Dan bazai iya ba Hakan yasa ya juya da sauri dama Kuma an fara Dan yayyafi, yace come and take her an fara yayyafa bin bayanshi tayi Jin be amsa mata ba, sunkuya wa yyi ya dauko farrah janyo hoodie jacket dinshi yai dake kan kujerar me zaman banza mantata yai a motar jiya, juyawa yai ya miqa mata Farrah making sure Basu taba juna ba garin kuje ma Hakan DAI still hannunsu ya hadu, da komawa baya yai farrah tana neman faduwa Dan Bata riqeta da kyau ba, wayyo Allah, shine abunda ya subuce a bakinshi kallonshi tai taga ba ita yake kallo ba sai gyare gyaren rigar da zai rufa ma farrah kawai yake bayan ta gyara mata kwanciya a jikinta ya rufa mata rigar tashi ya Kalli gefen amatou yace zaki iya kaita kuwa ?? Gani yake kamar ta mata nauyi, eh zan iya ta fada tana Dan Nishi dan da gaske Farrah tana da nauyi juyawa yyi yace wait, dauko leda yai guda Daya ya miqa mata juyawa tai taqi karba, yace karki qara taku ko daya anan ki tsaya ki amsa yanda yai maganar ya Dan Bata tsoro ga kuma farrah da ta gama sakin nauyin a jikinta ga yayyafi sai qara qarfi yake juyo tai kamar zatai KUKA sir Dan Allah kayi hqr miqa mata YAI a bbu yanda zatayi ta amsa yace good girl and we will talk over the phone akan sabon sunan Nan da kika samin zata Mai godiya yace oya Maza kar ruwa ya jiqamin yarinyata, juyawa tai ya wuce gida a ranta tana fadin wai yarinyarshi ko a Ina ta zama tashi oho, shiga mota yai yana sauke ajiyar zuciya, Saida ya danji dadai kafin ya tada motar ya wuce gidan da ya dawo a cikin zaria wanda federal government ta bashi, umma rabi ce ta miqe ta karbi Farrah ta wuce daki da ita ta kwantar da ita, kamar jira ruwa yake su shigo aka tsuge da ruwa Maryam ta kalli hannun amatou da ke riqe da hoodie din Dr Hammad tana zaune daga inda take tana jiyo cologne Mai tafe da qamshin turare aunty Mimi Ina Kuma Kika samo riga??? Kallonta tai da sauri Dan ta tafi tunani qamshin ya bala'in Yi mata Kai bama ita ba duk wanda zai shaqi qamshin rigar sai yayi masa dadi, miqewa tai tace rufe Farrah Akai da ita tana fadin haka ta wuce daki, murmushi kawaii maamaa tayi tana hango Wani chemistry Wanda tana addu'ar Allah yasa suyi balancing, miqewa tai ta shiga dakiinta ta kwanta dan basa sallah dukkansu, itama amatou kwanciya tai ta kunna data Wanda tunda ta tashi yay Bata kunna ba waya bata dameta ba Whatsapp ta shiga gaba Daya cousins dinta sun mata magana ta Whatsapp tai masu reply dukkansu sai Ammaa da suka fara hira da ita, can wajan 9 time din harta gaji ta sauka Dan ammaa Bata gajiya har mita take mata ta rage, kirane ya shigo wayarta, dubawa tai Dr Abdullahi ne a Fili tace yau kuma ?? Daga wa tai ta Kai kunne tare da sallama, Shuru taji kamar baza'a amsa ba sai kuma ya amsa, ya kike??tace,Alhamdulillah shuru sukai, sai Kuma yace baki iya gaisuwa ba ko??rolling idanu tai sai kuma tace ina kwana, in kwana??? Yanzu kika tashi daga bacci?? Tace uhmmm daga bacci na tashi na dauka safiya CE Dr abdullahi dake zaune a dakinshi dan a Kano family dinshi suke sai weekend yake zuwa musu, ya riqe baki tsantsar rainin wayo CE a maganarta , yace ni zaki raina ma hankali?? Amatou tace uhmm rainin hankali Kuma likita ?? A a wlh ni kawai gsky na fada maka amma idan kaji haushi kayi hqr, GABA Daya maganar cike da rainin hankali take Hakan yasa kawaii ya datse Kiran wayar kallon wayartan tayi Dan tana waya kamar taji alamun kira, Dr Hammad ne, tura wayar tai kasan pillow ta kasa baccine Amma da tuni tayishi, kamar wajan 30mnts sai gashi ya kira dagawa tai ganin kamar zata tsinke tai sallama, amsawa yyi cikin stern but cool voice dinsa, Shuru sukai dukka sannan yace ehen.. Ina jinki a Ina na samu sabon suna ??? She zai ce dawa kike waya?? A hankali tace eh mana ba Kai VC dinmu bane ?? Dariyar cikin qirji yayi yace shine kike cemin wani sir??? Spare me please ni banson wannan sunan, tace to me zance ? Ki Nemo Wani abun Amma Banda sir Kam, sai Kuma tace to likita, yace likita Kuma?? A a likito ba likita ba Yar dariya tayi Shima yai murmushi yace kisan dai Wani suna amma ba wannan ba, tace to Yaya kaga yayanmu ma Yaya Mahmud nake ce mai kuma shine first born dinmu babbane sosai harda furfura yake da ita, sosai Hammad yake enjoying hirar tasu hakan yasa ya gyara kwanciyarshi cikin bargon da take cuz bata taba maganar Wani nata ba yace yayankune ?? Tace eh manah bakasan muna da manyan yayyu ba ?? Su 7 Yaya Mahmud ne kawai namiji sauran duk matane sunyi aure,uhmn to ke yaushe zakiyi auren ?? Tab ni na gama aure ai Farrah is enough for me murmushi yai akai fuskarshi Amma kwata kwata Bata San yyi ba yace haka zakiyi zama alone kuma independently ?? Shuru tai sai Kuma tace UHM am okay with my life and am not doing anything bad, baisan ya akayi ba can qasa yace dont you need a life partner da zakiyi depending akanshi kinfiso kina mace kiyi ta Shan wahala ?? Tace meye abun wahala?? Karatun ko fita saloon ?? Saloon din da ba kullun muke zuwa ba sai weekends yanxu NE ma da su maamaa Basu koma Hutu ba take zuwa during week days, Amma ni am ok with my life, murmushi kawai yai yace let me tell you something da ke kanwata ce ko Kuma Ina da iko dake you will not go out kina hustling akan neman kudi, I will keep you at home provide all ur needs sannan nayi addu'a Allah ya kawo Miki wani mijin kiyi aure, tabe Baki tai tace Kaine ke wannan tunanin ba wasu ba sannan aini na ce ma na gama aure I love barraq and am ok to die with his love alone, kamar daukewar ruwa haka ta jishi har numfashinshi Daina ji tai Hakan yasa ta Kalli wayar taga Bai kashe ba tace hello?? Dan gyara murya yai yace Ina jinki, me kika ce?? Tace ni bance komai ba , ajiyar zuciya ya sauke yace meyasa Baku zauna da yayanku ba kinyi BUK?? Haka Allah ya tsara mana, sai Kuma tai shuru, yace ko kuma Kika tsara ma kanki?? Tace Babu zancen haka, haka Allah ya qaddara mana idan mutum Bai nuna interest akanka ba ai bazaka mishi dole tho dai ni na zabi hakan for some reasons, zancena ya fito knan for what reason kika zabi Hakan??? Shuru tai taqi cewa koma yace Ina jinki,tace not today but some other day may be na fada maka bai qara cewa komai ba sukai Shuru a haka bacci ya fara fusgarta,tace sai da safe bacci nake ji, yace yau kika fara bacci muna waya?? Bata qara cewa komai ba ta fara bacci har sai da tai Nisa Jin mood dinshi Yana canjawa yasa ya kashe wayar ya gyara kwanciya Yana adjusting kanshi ta cikin bargo, ya rufe idanunshi tun Yana tunani har bacci ya dauke shi shima,,,,,kusan 3weeks da zuwansu Kano sai ga kiran Mahmud Wanda sai da ta daga sannan ta gane shine yace mata yana so yaxo Zaria zasuyi magana me muhimmanci tace ba matsala sai yazo washe gari da wurwuri ya baro Zaria maamaa ce ta taho dashi ta kawo shi har gida sosai ya yaba hankalin amatou Kuma yaji dadin ganin da babba a gidan nasu sosai yai ma umma rabi godiya sai da suka kebe da amatou sannan ya kalleta yace.....



Mrs maan
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: ~*AMATOU*~🧕🏻
(The single mother)
13
Wajan qarfe Tara na dare har sun kwanta kira ya shigo wayarta tsaki tayi kwata kwata Bata Saba da yawan Kiran waya ba Amma kwanan nan damunta ake ganin doctor Hammad ne yasa ta daga tare da yin sallama, amsawa yyi ya karatu?? Alhamdulillah wlh, me kikeyi?? Shuru tai Mai da dai yana fakewa da Kiran farrah Amma ko neman farrahn ya Daina tanbayarta a waya idan Yana son ganinta sai dai yazo ya dauketa suje yawonsu su dawo,tambayarki nake, ba abunda nake kwanciya zanyi, yace ummn so you have to tell me me kikeyi a office dinnan dazu ?? Me yake ce Miki da har sai kinje office dinnan dazu?? Tura baki tayi yana takurata da so many question tace Babu komai kawaii kirana yyi eh ai an fadamin kiranki I want to know cuz bakuyi kama da masu discussing Wani Abu academically ba , nifa kawai kirana yyi Kuma ba wani Abu me muhimmanci yace min ba so just forget it, uhunn Amma you have to be careful,tace insha Allah, Ina babyna??tana daki tayi bacci, ok, Shuru sukai sannan yace yaushe Zaki Sata a school?? Tace an kusa insha Allah, ya kamata dai yanzu ne right time da zatai grabbing abubuwa sosai she is sharp and smart qasa qasa yace just like her mother murmushi NE ya subuce mata, yar dariya yyi see you to ba keba maamaa nake nufi rolling idanu tayi abinda yyi maamaa ai shi yyi ni, eh Amma DAI bake din bace ai dariya kawai tayi haka sukai ta Hira as usual amatou CE tai bacci sai da baccin nata yai nisa sannan ya kashe wayar...
Wasa wasa har yaci wata 2 acikin watannin da mamanshi ta bashi Yana zaune gaban gidan shi qasan rumfa me saman zana yana hutawa mamanshi ta kira shi it is very rare mostly shi yake kiranta and shi kwata kwata ya mance da Wani dead line Hakan yasa yai sallama bayan ya daga wayar, amsawa tayi ya gaishe ta, tana amsawa tace Muhammad inji DAI baka manta da alqawarinka ba?? Murmushi yyi a ranshi sai Kuma yace mama ban mance ba insha Allah zan kawo Miki atoh babu dai fashi idan baka kawo ba zan aura maka wata na dai fada Maka tana fadar haka ta yanke wayar, Saka wayar yyi a aljihu sannan ya miqe parking space dinshi ya nufa ya shiga motar bude Mai gate matashi me gadin da ya samo unguwar su amatou ya nufa dukda he is sure sun tafi islamiyya he is so attached to the girls ya Saba da zuwa wajan Farrah da yamma ko da safe and da daddare Kuma suyi waya da amatou ko ba zasu ce komai ba, and Maryam is like a little sister to him tana bala'in burgeshi a waje inda ba makaranta ba zasuyi hirarsu da dariya yanxu har yawo Suke tafiya a motarshi amatou ta gaji ta zuba musu ido Amma idan suka hadu a school Bata taba rawar kan ta nuna ta sanshi apart from makaranta hakan yasa suke qara burgeshi sosai, parking yyi a qofar gidan yasan tabbas suna islamiyya Amma he can't help it anan ya zauna har 6 tayi lokacin yake expecting dinsu, can ba jimawa ya hangosu duk da kalar hijab iri Daya amatou sanye da niqab Dan ta lura face mask janyo attention yake tunda yanxu ya zama na gayu tun daga nesa yake kallonta ko kiftawa bayayi, nutsuwarta sosai take fita a tfyrta Amma yau sai yaga sanyin jikin kamar yyi yawa, ya fara karantarta da kuma sanin halinta ba tare da ya Ankara ba, Dr abdullahi NE ya fado mai tun maganar farko bai qara yi mata zancen shi ba but kawai qoqarin riqewa yake ko jiya ya gansu a bakin gate shi yana MOTA ita tana tsaye haka yazo ya wuce su Yana addu'ar Allah yasa Bata shiga motar ba, Amma BAYA son shiga rayuwarta ya takura mata she is always saying Bazatai aure ba ita ta gama aure shi Kuma Bai taba gajiya da nuna mata aure mutuncin mace ne bata kama da Wanda suka taba aure jikinta Yana da matuqar kyau bazakce ta taba aure ba ballantana har ta haihu infact shi mantawa da Hakan yake ba damuwarshi bane Hakan and sosai yake mata kallon yarinya, kwankwasa mai glass yaji anyi yaga Farrah bayanta Kuma maamaa ce, murmushi yasa ya bude motar uncle yaushe kazo?? Dariya yyi yace dazu, nazo kallon amatou yyi bayan ya daga Farrah ya mata kiss a kumatu sai Kuma ya Kalli maamaa dake gaishe shi ya amsa ya karatu ?? Tace alhamdulillah shigewa yaga amatou zatai da sauri yace Mimi ba gaisuwa?? Dan juyo wa tai da Dan murmushin borin kunya tace Ina wuni?? Murmushi yyi yaqi amsawa, yace ya makaranta ?? Lfy qalao tana fadin haka ta shige gida Bata son ta matsa kusa dashi qamshin turarenshi da Kuma muryarshi are driving her crazy sosai take avoiding dinshi sun Saba DAI a waya kodan Bata ganinshi ne oho, Maryam tace Dr bari na shiga ciki am starving wlh kamar anmun yasa murmushi yyi yace princess ma tana Jin yunwa ko?? Gyada kai tayi yace ok to sakko ku je gida zan dawo wani lokacin kinji?? Ban siyo maki komai dariya Farrah tayi tace ai kana siyomin mantawa kayi ko?? Duqawa yyi yace that's my princess Amma next time insha Allah kinji?? Gyada Kai tayi sannan yace kuje bye bye tayi mashi sannan suka shige MOTA ya shiga Jin ana Kiran magariba ya nufi school bayan sai da yyi isha'i sannan ya koma gida da sosai yafi so ya xauna shi kadai bashi da wata damuwa Amma zama da su Farrah yasa yanayinshi yake son canjawa sai yaji zaman shurun na damunshi sosai,unlike before ko a jikinshi, Kiran amatou yyi ba jimawa ta daga dama jiran Kiran take for the pass 2-3months Bai taba missing kiranta ba tun Yana fakewa da Farrah yake nema har ya dawo kan hanya, miqewa amatou tai ganin maamaa tana kallonta kana gani kasan gulma ke cinta so take taji kwakwaf Amma ta kasa sbd basa Wani nunawa a Fili idan sun hadu shiyyasa maamaa ta zama confused to da wa take waya farouq Yana kiranta Shima Amma lokaci zuwa lokaci Amma tasan ba farouq bane tsoron Kiran layin Dr Hammad takeyi bataso ta kira while Bada shi take waya ba, amatou na zuwa kan gado ta kwanta ta lumshe Ido Jin abunda yake tambayarta,girgiza Kai tayi tace nidai babu komai kawaii DAI Yana son kulani Amma bbu komai tsakanin mu, yace to ke Baki son kula shi ?? Shuru tayi sai Kuma tace Nima ban sani ba, hmm kawaii yace sukai Shuru yace in tambayeki, Allah ya sa na sani, meyasa Baki tsayawa idan kin ganni lumshe Ido ta qarayi can qasa tace bbu komai kawaii DAI sai naga idan Ina yawan tsayawa ko yi maka magana zan takura ma ga Farrah ga maamaa making them happy is morethan enough for , yace nifa kawaii tambayarki nai meyasa kike guduwa idan kin ganni kamar Kinga dodo and you have no idea yarana nawa, dan bude Ido tai tace dama kana da aure?? Dariya tambayar ta bashi dariya ya Dake yace a a sai dai idan Zaki zama matar tawa zaro Ido tai tace nii?? Uhmn uhmn am just 25 fa Kai Kam nasan ka kusa 45 koma 50 wata dariya ce ta kwace Mai yace Mimi me kika maidani?? Tsoho?? Ashe dama kallon tsoho kike min?? That a side ma Maza nawa Yan 60 years suke auren yar 20 koma 19?? Balle ni da nake 38 I see no harm in that, Jin shekarunshi yasa amatou tace tabb 38?? Eh mana ko ya maki kadan?? Da sauri tace a a kawaii dai naga barraq was 27 years lokacin da y aureni Amma Kai harka Kai 38 bakai aure ba Shuru taji a wayar kallon wayar tayi tace hello?? Gyara muryarshi yyi yace Ina jiki sai Kuma yace nima idan Zaki samarmin mata ai SE nayi ni ban iya Neman mace ba ban San me zance ba, amatou tace habba dai kana namiji Kuma gaka ga maamaa ka Nemo wadda kakeso am sure she will help you out kasanta da zance da1 iya tsara magana kuwa sai tai Maka campaign dariya kawai yyi yace nafi son nayi campaign Dina da kaina sai kuma murya can qasa yace why don't you be that person???....…





Mrs maan🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: **~AMATOU~* 🧕🏻

(Th_single_mother)

14
Miqa mata

Please Login or Register in order to submit comment