Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka hijab dinta suka fice mazan suna ta Hira a parlour har baban Maryam na cikinsu SUNA ta chapter Abdurrahman ne kawai Bai wani cika sa musu baki ba, dakin amatou suka shiga dai dai nan wayar amatou tai ringing ganin ammaa ce yasa ta daga ammaa tace ya sunan unguwarku na kira maamaa Bata daga ba da bazan kiraki ba tunda naga ke bakya Sona kamar yadda nake sonki, dariya kawaii amatou tayi tace ba haka bane sabuwar unguwa Zaki CE bari na ce ma maamaan ta zo ta taho dake to tace sannan ta kashe wayar, Mami Ina zuwa Dan Allah tana fadin haka ta tafi parlor maamaa Ammaa ya kiraki Baki daga ba kije ki taho da ita, laaa wayar na daki tana chargy bari na dauko , tana fitowa ta kalli khalifa tace aboki zoka rakani mana, miqewa yyi yace to muje Khalil yace ku jirani nazo na ga garin zaria tare suka fice gaba daya, amatou Kuma tana shiga daki ta koma inda take zaune da farko ta durkusa Mami ta Kalli umma rabi tace Rabi naji dawainiyar da kike da yarana wanda mu ya kamata muyi mun gode sosai Allah ya Saka da alkhairi dukda dai kamar yiwa kaine Allah ya Saka da alkhairi ya bar zumunci dama abunda yasa nace ta kiraki shawara ce dukda kwanaki nayi ma amatullahi maganar naga kamar maganar batai dai dai da ra'ayinta ba Hakan yasa na bar zancen,gaban amatou ya Fadi, ba wai Dan Ina so na kwace farrah ba, ba Kuma wai Dan abunda ya faru ba sbd bawa baya kaucewa qaddararshi, dalilin dayasa nake rokon a Bada ita Kinga na farko zata samu ilimi me inganci daga islamiyya har Boko a Abuja sannan amatullahi zata fi maida hankali tayi karatu dukda dai na San kina Nan amma kamar hankalinku zai Dan fi kwanciya idan yaso sai tana zuwa hutu idan anyi hutu,amatou tasan bazata taba yi mata musu ba this time around, Hakan yasa cikin sanyin murya tace to Mami ba matsala, kin tabbatar Baki takura ba amatou??? Girgiza Kai tai tace bakomai Mami Nagode Allah ya Saka da alkhairi, umma rabi tace Allah ya qara girma gabannin za'ai azahar mazan sukai Alwala baban yace mami ta shirya idan sun dawo zasu wuce, alokacin amatou ta hada kayan farrah da ta fada ma maamaa bade tace komai ba Amma sarai amatou tasan da maganganu a bakinta, ta hada Mata wasu kayan ta bar su anan tunda Farrahn zata na zuwa hutu, da suka tashi tafiya 20k Mami ta bata ta ba umma rabi 5k sosai tai godiya baban kuma 100k ya bata sannan ya bama ammaa wadda daga shigowarta suka Saba da kowa barinma khalifa na mata na mata abdurrahman kam Bai kula su ba baban yace cema abdurrahman ya karbi account numbernta to yace ya kalleta sannan ya Kalli amatou dake gefenta dauke Kai sukai a tare sannan yace zo muje madam takawa sukai suka fita a parlorn ya miqa mata wayarshi yace ta saka mai, bayan ta saka mai, yyi saving ya qara miqa mata wayar kallonshi tayi tace me zanyi?? Qasa qasa yace numbern waccan me surutun Zaki bani yar dariya kawai tayi ta saka mai, GABA Daya suka fito musu rakiya, abdurrahman ne a jeep din babansu yake jan mamansu da babansu a baya, khaleel a MOTA Daya Dan Babu Wanda yake iya shiga motarshi Dan ba ruwanshi da wace kalar hanyace yaita tsala gudu a wannan dinma sai da baban yai mai warning, farouq da khalifa Wanda asali rigima sukai Khalil yace shi zai jasu suka Sam sai DAI su raba mota hakan kuwa sukai, laluben idanun ammaa abdurrahman yyi sai da suka hada Ido da ITA ya kashe mata idanu Wanda harta dauke kai sai Kuma ta juyo da sauri tana kallonshi for the first ya sakar mata murmushi tare da alamun zai kirata irin kallon waya baka numberta tai mishi ya Kalli amatou da sauri sai Kuma ta kalleshi ta dan murguda Baki murmushi ya qarayi yana kallonta kawaii tayi mishi sosai barin layin sukai su amatu suna daga masu hannu kafin su juya su shiga gida......




Mrs maan🥰😘
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: MrsMaan✨: ~*Amatou*~🧕🏻
(The single mother)



19


Suna shiga amatou tana kallon Amma da murmushi tace what was that??? Dan Sosa kai ammaa tayi tace what was what? Uhmnym kwayi bayani daga ke harshi din dariya maamaa tayi tace wlh nima Ina kallonsu suna magana da Ido Ashe haka yaa abdurrahman din yake kana ganinshi seme seme ashe shima A ne ammaa tai Dan murmushi tace da farko I tot he is kind of weird maamaa tace ai ni da a wajene naga Wani me irin halinshi zance wlh girman kaine, amatou tai murmushi tace he is so nice and caring idan ka zauna dashi ka fahimce shi sai kuma tai murmushi tace Babu abunda ya rabasu da barraq kawaii dai barraq yana da fara'a sosai Jin muryarta ta fara rawa yasa ta miqe ta tafi daki gaba Daya suka bita da kallo ammaa ta kalli maamaa tace baban Farrah?? Gyada mata kai kawai, she is also missing him sosai and yanda amatou is so pained and traumatized is understandable bawai Dan basa missing din iyayensu ba amma they lost them when they are young especially ita but barraq da girmansu da wayonsu ya kyautata musu ya qaunaci amatou ya kula da ita fiye da tunanin mutum rana daya suka rasa shi dole suji ciwo and har yau tun bayan ranar da barraq ya rasu ta fara labour ta haihu Bata taba ganin amatou tayi kuka ba, batasan ko tanayi a boye ba, Shuru ammaa tayi Bata ce komai ba, amatou tana shiga daki ta zauna a gefen gado ya dafe goshinta, Bata so tayi kuka barraq addu'arta yake buqata ba kukanta ba dan ta kauda tunanin a ranta ya sa ta miqe ta daura towel a ta shiga wanka tunawa tai Ashe Babu ruwa a container din toilet dinta Dan tap din cikin toilet din ya lalace daukar medium bucket tai ta fito dakin qaramin 2yard hijab dinta light blue Wanda da baqar abaya take hadashi ta dauka ta dora akan towel dinta ta fito suna zaune a parlor Dan Ammaa tai cheering mood din su din yasa Ammaa ta saki Baki cike da iskanci tabi amatou da kallo amatou kamar ance ta juya suka hada Ido harara ta jefa mata tace malama wannan kallon fa?? Subahanallahi anty Mimi?? Wlh da Ina da babban yaya namiji baxan bari wannan kayan ya barshi ba kam Dan Yasin sai mun kada Dr Hammad , amatou ta harareta tace shi din meye dina Dr hammad din?? Dariya Maryam tasa qasa qasa tace waya sani wannan Abu a duhu, Wani deadly kallo amatou ta jefa mata da sauri tai zipping bakinta, Ammaa tace oho kin fimu sani ai, shuru amatou tai mata Dan bata iya musu ba ta debi ruwan da Dan yawa tai wankanta ta fito shiryawa tai ta fita gidan taji tsit,leqawa dakin Maryam tai taga babu kowa a dakin Hakan yasa ta leqa dakin umma rabi zaune ta ganta kan sallaya tana jan carbi sosai ta bata tausayi ta Saba da Farrah sosai zatayi kewarta,amatou tace umma su maamaa sun fita nee?? Eh ta leqa kina wanka sunje kasuwa su dawo, ok kawai tace ta wuce daki ta kwanta ganin qarfe biyu da rabi Wani Abu taji Yana Dan damunta a rai a hankali ta janyo wayarta ta duba Babu miss call ko Daya sai na Dr abdullahi da tai blocking numbernshi Bata taba yadda su a hadu yanzu a school and lokuta da dama idan ya ritsata Dr Hammad ke kwatarta a hannunshi Bata San ya akai yake sanin Dr abdullahin ya kirata ba , share kiranshi tai tayi dialing numbern da take so tai dialing sai Kuma kawaii tayi saurin katsewa ta kwanta akan pillow ta lumshe ido shuru tai tana tuna halin da ta shiga jiya da daddare Bata fatan Allah ya qara nuna mata irin wannan daren, Kiran wayarta yasa ta bude ido ta jan yo wayar ganin me kiranta yasa ta gyara kwanciyarta, tare da amsa kiran cikin sanyin murya tai sallama, Dr Hammad Dake cikin office dinshi ya lumshe Ido he just miss her voice da deep voice dinshi ya amsa yana jinginar da kanshi jikin kujera yace ya kike?? A hankali tace lafiya qalao alhamdulillah har tayi Shuru sai Kuma tace dazu shine ka tafi Baku gaisa sosai da babana ba, Shuru yyi jin tace babana sai Kuma yace babanki mahaifi?? tai murmushi tace a a yayan babana ne da mukaje gidanshi abuja last time, ohhh I see so they are all ur family, tace yeah , yace that's great Ina babyna?? Lumshe Ido tayi sai taji kamar da biyu yake cewa babyn cikin yar dakewa tace sun tafi Abuja tare, da sauri ya bude Ido ya zauna sosai yace me zatayi a Abuja ko zata dawo daga baya?? Tace a a ta koma can da zama da mugun mamaki yace kamarya ta koma can da zama da can meyasa Basu dauketa ba ko Kuma Basu riqe ku gaba Daya ba tunda kince yayan babanku ne and am very sure uwa Daya uba daya suke meyasa suka barku Kuna ta gararamba a matsayinku na mata?? Sai yanzu suka san da farrahn basu San ya ya rayu ba Basu san ta Yaya kuke ciyar da kanku ba kawai rana tsaka a karbeta ? Kuma kika barsu suka dauketa?? Shuru amatou tayi tana sauraronshi, shikam dafe goshin shi yyi that's what has been eating him up tun safe he is Soo angry da yaga motocin da suka hau sannan he remember qaton gidan dayaga sun shiga ranar Nan it shows they are wealthy Amma sukai abondaning dinsu tho dai baisan for how long ba Amma yasan sun dade babu Wanda ya waiwayesu, sauke ajiyar zuciya yyi yace am sorry murmushi amatou tai tace bakomai yace saboda abunda ya farune suka tafi da ita?? Amatou tace mami tace zata samu karatu me kyau acan both western and Islamic knowledge yace school din da aka sakata Bata da kyaune ?? Da sauri tace not at all tana da kyau Dan sosai Farrah take improving haka islamiyyar da muke ma is very good kawai dai haka tace min and dama tayi requesting karbanta last time ban yarda ba to bazan iya mata musu ba this time gyada Kai yyi kawai but he is so angry kwata kwata Gani yake ba'aima amatu adalci ba Dan sunsan sunfi karfinta ne sukai mata wayo ta hanyar da baxata iya hanawa ba Amma idan tsakani da Allah ne they can take them all along amma without any hasitation suka bar Yan matan su kadai again without realizing how dangerous this world is, they are so exposed to danger gasu mata sannan suna zaune su kadai a gida ji yai aikin ya fita a ranshi tattara takaddun yyi ya miqe ya dauki jakar laptop dinshi ya fice messengern shi Dake zaune akan kujera yana cin abinci da sauri ya rufe abincin zai miqe, Yi xaman ka malam sama'ila tafiya zanyi, to rankai dade Allah ya kiyaye yace sai Allah ya kaimu gobe,Yana fadin haka ya kama hanyar parking lot din admin block din yywajan motar shi yyi ya shiga hanyar gidanshi da ke cikin quarters Yana zuwa wanka yyi ya shirya cikin qananun kaya kaya black sweatpants Dan riga red and black he look so takeaway and sexy his figures are all out tun daga kan broad shoulder dinshi zuwa flat abdomen dinshi dukda dai babu wani six packs Amma wajan flat yake farar fatarshi tayi fresh gashi ya kwanta akan hannunshi expensive smart apple watch dinshi ya saka shima black ya Saka sneakers dinshi me kyau baqi da fari sosai yake tashin qamshi p cap ya dora ya debi keys dinshi da wayoyinshi ya fice daga gidan kaduna ya nufa a lokacin Yana Isa ana Kiran sallar la'asar masallaci ya nema yai sallar la'asar sannan ya fito ya nufi restaurant din dayake siyan abinci ganin Yan mata da samari a wajan yasa YAI requesting VIP table kuwa can aka Kai shi yaci ya qoshi yasha ruwa ya DAU coke dinshi a hannu yaje reception ya sallamesu Yana Jin ido akanshi ya basar ko juyawa beyi ba yazo zai Bude mota yaji ance HI juyawa yyi yaga kyakkyawar budurwa Amma irin matan Nan ne masu qiba sosai tasha black abaya yasa tai wani irin haske bau kana ganinta kasan ta kusa 30 years inma ba kaiba knan dauke Kai yyi bayan ya qare mata kallo yace wa'alaikummussalam kunyace ta kamata, tace afwan assalam alaikum amsawa yyi yana Bude motarshi zai shiga yana kallonta yace ya Akai ?? Kallonshi tai cike da wayewa tace ganinka nai nace bari nazo ko zamu zama friends ?? Kallonta yyi sannan yace a wane dalilin ?? Tace Haka kawai naga kamin nace bari na zo muna zumunci dariya sosai ta bashi ya saki murmushi wato ya mata ?? Ko irin kunya da Jan aji ta mata babu yace babu abunda na hada Dake ya za'ai muyi zumunci and ko a musulunci Bai halarta qawance tsakanin namiji da mace ba Dan haka nagode da yi mikin da nayi Amma kiyi haquri Yana gama fadar haka ya dauke dayar qafarshi dake qasa ya rufe motarshi ya bata wuta,kallo tabi motar dashi cike da takaici qawarta ta biyota tana mata dariya KFC yaje ya siyo kazarsu dayawa sannan ya biya ya Siya chocolate chewing gum sweets duk ya kwaso tarkacen mata ya nufi hanyan zaria, Yana shiga garin ya nufi gidansu amatou sai da yaje qofar gidan sannan yai dialing numbernta tana dagawa yace dan leqo mana, a hankali tace to sanan ta miqe daga inda take zaune tana karatu ta nufi daki Dan dauko hijab dinta maroon yai mata kyau sosai kuma har qasa ya Kai mata, har ta sa over sized slippers dinta sai Kuma ta dan tsaya, komawa tai ta dauko silver flat takalminta sannan ta fita ammaa da Maryam sun fice tun bayan sun gama cin abincin da suka dafa ammaa tace ta rakata gidansu amatou tana Jin kunyar ammaa Amma ba'a San ranta suka tafi ba gashi 5 har tayi, tana fitowa ya kalleta ya lumshe Ido she is sooo natural Babu Wani artificial Abu a tattare da ita Dan waigawa yyi unguwar babu kowa a layin sauke ajiyar zuciya yyi ta side din da yake taxo ta tsaya tana wasa da hannunta Dan gaba daya glass din motar a dage yake, Dan sauke glass din yyi kallonta yake sosai maroon hijab din yai mata kyau a hankali ya kai idanunshi kan lips dinta that are wet saboda Dan tsotsarsu da takeyi numfashi ya sauke yana a'uziya a ranshi she is just driving him crazy murya can qasa yace zagayo ki shigo kallonshi tayi sai kuma ta girgiza kai tace karatu nake komawa zanyi, yace shigo nace, a sanyaye ta zagayo sai binta da kallo yake bude qofar tai ba shiri ta lumshe ido sbd sanyin AC hade da qamshin turarenshi Daya bugi hancinta da ya Bude window ta Dan ji qamshin Amma ba kamar yanzu ba jitai jikinta ya mutu shiga tai a darare ta zauna ta rufe qofar kallonta kawai yake Bai taba Jin tsananin buqatar aure irin na yau ba, he is imagining things a wannan lokacin sai yanzu yake qara jin cewa lallai hadari ne mace da namiji su kebe Wanda ba muharraman juna ba, kallon fuskarta yake ta ciji lips dinta naqasa Hakan yasa ya qara zama wet kamar habit dinta ne ya Allah yace qasa qasa ringing din wayarshi ne ya katseshi sauke ajiyar zuciya yyi yana godema Allah Daya ceceshi da sauri ya ware idanunshi da suka qanqance ya zaro wayarshi ganin mamance ya SA ya daga Kiran yana dan gyara murya yace mama Kinga ban kiraki ba ko?? Eh shine nace bari na kira naji har yanxu ba'a ga yarinyar ba?? Yace anganta MAA tun safe Ashe yaran wata unguwar tabi da safe wani mutumi ya kawota, maman tace Masha Allah Alhamdulillah har naji Dadi tun dazu abun yana raina murmushi yayi yace ga mamanta ma ku gaisa, yana fadin haka ya miqa ma amatoun kallonshi tayi ya nuna mata wayar da ido alamun ta karba, cikin sanyin murya tai sallama karkacewa yyi ya Dan Jin gina kadan Yana kallonta, mama da taji muryar yarinya sosai tayi mamaki maman ta amsa gaisuwarta tace Allah ya qara kiyaye kinji tace Ameen Ameen mama nagode Allah ya Saka da Alkhairi ya qara girma, kallonta kawai yake, he is just imagining how this lips will taste ganin shedan Yana qoqarin fin qarfinshi Dan abun yazo mishi ne a kan gaba shiyyasa abun yake neman fin qarfinshi sallama taima maman ta miqa Mai wayar amsa yyi baice komai ba ya juya BAYA ya kwaso ledojin da suke baya hakan kuma yasa suka zama very close jikin qofa amatou ta dan matsa matsa sarai yaga abunda tai and psychologically yasan mutual feelings ne miqa mata ledojin yyi yace ga abunda Zaki karba, tasan musu dashi ma baida Wani amfani haka Shima Bai Bata kudi ba yasan ko me zeyi bazata karba ba, tace nagode sosai Allah ya qara budi sannan ta bude motar sai Kuma ta sunkuyo ta kalleshi ganin kallonta yake ta sunkuyar da kai sannan tace nagode sosai da dawainiyar da Kai da Farrah Allah ya Saka da alkhairi tabe Baki yyi yace ni na dauka ma cewa zakiyi yaushe zan qara dawowa ai ni na sa kaina ko?? Tace dukda haka nagode yace kiyi hqr ki barni da godiyar nan haka ni gida zan tafi gaba daya ya qagu ta tafi cuz if care is not taken zai iya fizgota cikin motar tace to sannan ta rufe qofar a hankali tana fadin Allah ya kiyaye Saida ta shiga gida sannan ya sauke ajiyar zuciya Yana laluben sassanyar coke dinshi Dan Yana tsananin buqatarta yanxu, sai da ya huce sannan ya kama hanyar gida ganin magariba ta taho parking yyi ya shiga ya cire takalminshi wanka ya shiga yyi sannan ya Saka jallabiya ya dau wayarshi ya sa slippers ya fito waje ya zauna akan wooding chair din Dake compound din danna wayarshi yake a haka aka kira sallah ya miqe ya Isa bakin tap din dake wajan flowers din yana idar wa suka nufi masallaci shida me gadi,,,, bangaren su amatou kuwa wajan 6 sai ga su sun qara dawowa tare ammaa harda yar jakar kayanta gidansu ita kadaice mace yayanta Daya sai qanne Suma Maza su 4 hakan yasa Bata Jin dadin zama cikinsu Kuma ana mata gata sosai da tacema mummynta gidan su amatou zatazo tai kwana biyu Bata hanata ba Dan a gidan babu Wanda be Santa ba, kallon ammaa amatou tayi tace Ina zuwa Kuma?? Tace kwana biyu nazoyi gurin qawata maamaa ko am not welcome?? Riqe baki amatou tayi tace bakiji a bakina ba u're highly welcome kin canja qawa kenan,tace eh na canja maamaa tafi Sona nafison wadda zamuyi ta surutunmu tare bawai Ina zuba ana min Shuru ba ke idan munje school sai Muna qawancen hararar wasa tai mata tace to Nima banayi ko a school din maamaa tace anty Mimi ni qamshi nakeji ki shiga kitchen ki dauko muku Dan da ta kawo kitchenta Kai ta diba ma umma rabi dayawa a plate ta Kai mata sannan ta bar sauran a kitchen qamshin turarenshi ya cika mata ciki dama Kuma Bata wani cika cin abinda ya kawo ba da rige rige ammaa da maamaa suka qarasa kitchen din kallonsu tayi ya girgiza Kai sosai halinsu yazo daya sai gasu da ledojin har na su sweets din maamaa kuma da tray anan suka baje suka CI har amatou tho dai ba wani dayawa taci ba infact ita kunya takeji wai wani ya kawo mata abinci ta zauna tana ci barraq ba daganan ba indai zaizo sai ya cikasu da tsaraba kafin suyi aure amma wani abunma karbewa matar Yaya mahmud take amatou da ya fahimci haka sai take boye masu Wani abun Amma bata taba boye kudi ba a lokacin zata nuna mata sai tace kawo in ajiye Miki shikenan har abada kuma,,,, gidan Mami kuwa Basu tashi ganin tashin hankali ba sai da dare yyi farrah ta saka KUKA a kaita gun miminta da umma rabi da anty maamaanta GABA Daya mazan gidan suka fito suna rarrashinta har baban, har wajan Sha biyu basuyi bacci ba , suna zaune saiga abdurrahman ya fito duk Basu lura da cewa baya Nan ba sai yanxu shikam Yana can yana waya da ammaa ya qarasa hannun Mami ya miqa mata hannu yace come here angel miqa Mai hannu tai ya dauketa ya rungumeta wani ajiyar zuciya ta sauke kafin kace me tayi bacci, Amma tanayi tana kukan cikin bacci sai da ta jera kwana 6 tana wannan kukan tana yadda da abdurrahman din ma daga baya ta Dena ba shiri babana yaCe a shirya a maidata zaria.....




Mrs maan😍🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: ~*Amatou*~🧕
(The single mother)
20
Kasa haquri Dr Hammad yyi hakan yasa after 2days yaje qofar gidansu amatou yyi dialing numbern maamaa," bayan ta daga ta gasar dashi yace kina gida ?? Tace a a muna shago yace alright bari nazo, juya kan motar yyi ya Isa qofar shagon su amatou yana zuwa ya kashe motar ya fito yana dialing numbern maamaan dagawa tayi yaji alamun bata cikin shagon tace likita ganinan zuwa Amma anty mimin tana ciki,alryt sai kinzo ni ba anty Mimi nazo gani ba gunki nazo, dariya kawaii tai tace to gani nan zuwa kallon shagon yake da takalma a qofar shagon a ranshi yana ayyana idan ba dole ba me zai fito da 'ya mace titi tana neman kudi Dan titi ya dauki wajan dukda dai bbu wani zirga zirga Amma still kasuwa ce, kasuwar da anyone can come yyi musu abunda ya ga dama walau wulaqanci ko Kuma wani abun da kallon title din shagon yyi A&M beauty saloon murmushi kawai yyi how did they came with this idea ba ko wane yaro bane ya taso a cikin kudi Wanda besan zafin neman su Amma ya iya coping da rayuwar Daya tsinci kanshi he is so impressed sosai he wish duk wasu widows can be strong as amatou he wish zasu zama masu zurfin tunani barin ma Wanda suka tsinci kansu a yanayi na rashin gata...maganar maamaa ce ta katseshi juyawa yyi ya ganta ta tattara hijab dinta ta riqe alamun abune a ciki kallonta yyi yace daga ina kike ?? And what's that?? Tace braids dinmu ne suka qare kuma mutane suna Jira shine fa na tafi siyowa yace meye shi braids din ?? Dariya tayi tace attatchment ne amma na rubber idan kaga normal attatch to yawanci christians ne idan suna so kallonta kawai yake yace yanxu ku attatchment din kukewa mutane and kunsan haramunne da meyi da Wanda ake ma?? Sannan kuce kuna neman albarkar sana'arku?? ,Jikin Maryam dinne yyi sanyi sunsan babu kyau infact da farko amatou tace bandashi Amma ita taita insisting suyi sbd sai sunfi ciniki idan sukace zallan kitso zasuyi bazasuyi ciniki ba Hakan yasa amatou ta amince, yace ita anty mimin ita ta saka kukeyi ?? Jeki kirata girgiza Kai tayi da sauri tace a a wlh nice naita insisting ganin yawanci anfi yinshi sai munfi ciniki kallonta yake Banda yaro wa zaiyi wannan tunanin?? Hakan yasa yyi murmushi yace jeki ajiye ki kiramin ita kuzo tare, juyawa tayi a sanyaye ta shiga ciki amatou na stretching kan Daya daga cikin mutanen dake zaune awajen ta kalli Maryam data shigo tace me yake ce Miki?? Girgiza Kai tayi tace yace kizo, tura Baki amatou tayi, ni me zan mishi da yasan ni yake nema ai sai ya kirani ta waya yar dariya maamaa tasa tace nidai ba ruwana saqo na isar idan kinje sai ki tambayeshi, shuru amatou ya mata saida ta gama gyara gashin daga shi har Maryam din suna tsaye

Please Login or Register in order to submit comment