Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qamshin turarenshi da ta shaqo yasa ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya share hawayen take amma kamar ana tunkudosu, sallama yyi ciki ciki kamar ana mishi dole malam haruna ya amsa dan ya girmi hammad kawai dai tsohon banzane dan harda furfura akanshi dr abdullahi da duk ya dan rikice yace barka da safiya rankai dade, ko kallonsu beyi ba ya qarasa gaban amatou dab da ita ya sa hannu a aljihu ya zaro handki yasa yatsu biyu ya dago fuskarta share kata fuska yyi tas harda hanci ta dago tana kallonshi ya mata kallon ki daina kuka yana gamawa ya juya ya kareta gaba daya da bayanshi lumshe ido tayi cuz they are so close and she feel protected, sun saki baki suna kallon abunda yakeyi, ya kallesu yace pardon my manners amma inaso naji ko tayi wani laifin ne?? Gaba daya kame kame suka fara dan basu tsammaci abunda zai fara tambaya ba knan malam haruna ya daure yace dama nace ma abdullahi hawayen munafurcine daga magana sai yarinya ta fara kuka me aka mata tambayarta fa kawai abdullahi yyi ko yarinyar da ya gani a gunta yar tace shine ta hau kuka shikenan daga nufinta da alheri sai ta saka ma mutane da sharri shifa abdullahi taimakonta zeyi tunda yaga bazawara ce yace zai aureta amma sai wani wulaqantashi take ya tabe baki yace ni ban sa musu baki bama dama kuma kiran da yyi mata nan dan na tayashi shawo kantane, idan ka kalli hammad bazaka so qara kallonshi ba yana da wani irin rashin damuwa duk inda bacin rai yake to bazaka ganshi ba amma karka kaishi bango anan ne zaka ga the other side of him, addu'a kawai yake a ranshi kuma yana kare musu kallo especially malam haruna da yake a babu babu zai bashi shekara goma amma baiji kunyar kallon idanunshi ba ya gilla mai qarya amatou dake bayanshi was shocked jin qarya qiri qiri, matsawa yyi daga setinta ta bayyana a gabansu ya kalleta strictly yace ke kika ce mai kina so ya taimaka miki ya aureki sbd ke bazawara ce da sauri ta girgiza kai tana share hawayen dake gangarowa a fuskarta, ba tare da ya kallesu ba ya sa hannu ya kamo tsintsiyar hannunta dr abdullahi yabi hannun nashi da kallo suka fice dan dr hammad bai tsammanin idan ya bude baki zai musu ta dadi sannan baya so yyi musu a gaban amatou suna fitowa yace muje a hankali take tafiya tana share hawayenta sai da suka zo wani dan corridor babu mutane a wajan ya jinginar da ita a bango yana qara share mata idanun murya qasa qasa yace meye na kukan kuma?? Fashewa da kuka tayi juyawa yyi ya bata baya instead of rungumeta da yyi niyyaryi yace mimi dan Allah kiyi haquri karki sani yin wani abu daban sai kuma ya juyo har a lokacin idanunshi da dan ja bai jin dadin kukan nata gaba daya ya dan dagota yace ko so kike na rungumeki na rarrasheki da sauri ta girgiza kai yace good to maza share hawayen naki to tace sannan ta karbi handki din ta goggoge idanunta juyawa yyi yace muje to, gaban mota ya bude mata gaba daya a darare take ganin idanun mutane dayawa akansu dama anxo ana ta qishin qishin din gulma harda masu tambayarta wai ita qanwar VC ce ba yadda ta iya hakan yasa tace musu eh, to yau kuma anga ya bude mata mota ko me za'a ce oho zagayowa yyi ya shiga motar ya kunna karatu a ranshi yana tunanin it is high time for him to act up against dr abdullahi dama ire irensu ganin ya nufi gate yasa tace muna da lectures 1:30 ya kalleta yace zaki iya zama?? Gyada mishi kai tayi juyawa yyi tace dan Allah ka kira wayata tana hannun ammaa bai ce komai ya zaro wayar yana dialing numbernta sannan ya miqa mata waya kallon sunan tayi yasa "sweet soul😍" Karawa tayi a kunne a ranta tana tunanin bayan foxy wani sunan knan ya saka mata ranar da ta duba meaning din foxy kunya ce ta rufeta sosai kamar yana gabanta, qara kira tayi jin ammaa bata daga ba sai a na biyu ta daga tare da sallama muryar amatou da taji ne yasa ta riqe baki qasa qasa tace wayar tashi ya baki ki kira?? Murmushi kawai amatou tayi tace kina ina?? Tace kin ganni a masallaci naga shabiyu da rabi tace ok ganinan zuwa tana fadin haka ta katse wayar tace saukeni anan tana masallaci juya kan motar yyi ya nufi masallacin da ita har qofar masallacin ya kaita ta miqa mai wayarshi tace nagode sosai, yace duk randa ya qara kiranki you have to call me first kafin kije kinjini?? Gyada mai kai tayi a ranshi yasan dole yasa tint kallon yyi yawa kuma kana gani kasan she is uncomfortable sarrounding din yyi a ranar amatou sai da ta matsu ta tafi gida sbd kallo irin ana gulmarkan nan da ta juya sai dai taga sun hada ido da mutane ammaa tace amma wannan anyi yan iska gulmar taku ma qara mace kuzo ku fuskanci mutum shine suna gama lectures ta samu ta sulale ta bar school din ranar friday hammad ya ba zaria zuwa katsina gdan wan babanshi yana gaba tar mai da abunda ke tafe dashi suka hau murna yace ya sanar ma waliyyanta zasu zo neman aure, ba musu ya amsa ya fice ya nufi gidansu da aisha ya fara cin karo a ranshi yace kinyi kadan ki bata min mood hakan yasa da fara'arshi ya qarasa parlorn inda mama ke zaune ya durqusa qasa ya gaidata muhammad yaushe rabo yar dariya kawai yyi yace wlh mama sai a hankali aisha zubo mai abinci da sauri yace na qoshi mama good news nazo miki kallonshi tayi yace baba yace na sanar ma waliyyan mimi zasuzo neman aure dan bude idanu tayi tace dgsk? To aini bansan wacece ba ka tabbatar da halayyarta?? Murmushi yyi yace mama kallo daya zakiyi mata kiji kina sonta kinsan marigayi alhaji garba isma'il mai kano tace me wire houses dinnan koba shiba yace exactly yarshi ce tace kamar a kano suke zaune ko?? Gyada kai yyi yace eh shuru yyi yana tunanin ya fada mata cewa ta taba aure yasan mata da daukar abu amma dole ya fada mata tunda hakkintane ta sani and he loves her heart and soul he isnt after her pussy shi kam hakan yasa yace mama???....



Mrs maan🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: ~*Amatou*~🧕
(The single mother)


24
Kallonshi tayi ya dan sosa qeya yace itace maman yarinyar da ga bata kwanaki kallonshi takeyi kamar bata fahimci me yake son ya fada ba tace ban gane ba gabanshi na faduwa yace maa wannan yarinyar data bata kwanaki har na bata waya kikai mata jaje?? Itace za'ayi abun da ita daquwa ta mai jin yana wata magana tace muhammad yi min bayani dallah dallah yanda xan gane dan gyara zama yyi yace eh mama ta taba aure 6years back shekararsu guda da mijin ya rasu ya barta da ciki amma mama wlh baxaki taba cewa ta taba aure bama balle kice ta haihu kuma yarinya ce yanzu kwata kwata she is 25 marainiya ce and wlh kallo daya zakiyi mata kiji kina sonta tana da nutsuwa sosai ita da qanwarta, Aisha dake zaune tana jinsu ta kasa kunne taji ya fadi sunanta complete tana da qawaye dayawa a ABU and tasha giggilla musu qaryar cewa ai new VC dinsu zata aura saurayinta ne, kallonshi kawai maman take tace kai yanxu muhammad auren farko bazawara zaka fara da ita ina laifin ka fara da budurwa idan yaso sai ka qara da ita rasa inda zaisa ranshi yyi yace mama wlh tafi wasu yan matan sau dubu yana sane ya fadi hakan kuma saqonshi ya isa inda yake so, yace nutsuwa hankali kamun kai duk babu wanda bata hada ba mama tace yo kai dama me ka sani a rayuwa yaudararka dai zatayi zawaran yanzu da sai addu'a har zakace wani abu idan zaka canja zani ka canja zani idan kuma ba haka ba kana aurenta babu dadewa sai ka nemi wata a cikin dangi ka aura banason shashanci kallon mama kawai yake babu ko blinking idanu, yace mama ki bari ki ganta tukunna, ko na ganta ma babu abunda zai canja ni bazan hanaka auren wadda kakeso ba amma zaka qara da wata abokanka nawane suke da mata biyu yanxu?? Dan haka mun rufe wannan zancen miqewa aisha tai sum sum sum ta wuce dakinsu, hammad kam kallonta kawai yake can ya sunkuyar da kai bai san me zaice ba shi a tunaninshi ma kasancewar amatou baxawara bai taba damunshi ba bayajin ya damu yasan dole zai samu yar matsala da mamanshi amma bai tsammaci haka abun zai zo mai ba kuma bazai bijire mata ba, hakan yasa yace to shikenan maa tunda haka kikeson, Aisha na zuwa daki ta zaro wayarta tai dialing numbern zalina tana shiga aka daga zalina tace shegiya ina ta zuci zucin in kiraki wlh maqaryaciyar banza da wofi ke har yanxu bazaki daina halinki na qarya ba kika sa ina ta bazawa cewa handsome new VC dinmu dan uwansu qawata ne shi zai aureta ashe qaryar banza ce kinga budurwar shi kuwa kambala' i wlh ta ninka ki kyau sau goma Aisha da take ji zuciyarta zata fashe tace ke wlh ba da wasa nake ba ina jin itace bazawarar da yazo yana fada yanxu wlh yanzu haka asiri ta mai zalina tace wace bazawarar?? Gaskiya ba dai wadda na gani ba ke kinga kyau?? Dan ma duhun kai yasa kullum cikin hijab take amma wlh ta hadu ranar a bainar jama'a naga ya bude mata mota sai lallabata yake wlh zuciyata tai melting ina ma nice da rumour din da aka farayi akace qanwarshi ce amma wlh kana gani kasan yana sonta sosai, aisha tace wlh to bazawara ce yanxu ya gama fadama mama ina gidan su fa zalina da shegantaka tace shegiya kedai bazaki daina halinki, Aisha tace wlh da gaske nake miki jin tasa serious tune a muryarta yasa zalina ta gane da gaske take tace idan yace zai aureta b abun mamaki bane amma ace bazawara ce?? Isha bakiga abunda na gani bane au ni nama manta qanwarta tana kitso a cikin hostel kuma naji ance suna saloon a cikin kasuwa bari zan binciko nima na kashe kwarkwatar kunnena aisha tace yawwa leena ta shiyyasa nake sonki dayawa dan Allah ki daina tsoratani da kyanta zuciyata zata fashe dariya zalina ta ce wlh bazan miki qarya ba to ko qanwarta da take baqa kina fara wlh bazaki kara da ita ba kuma wlh yayar tafi qanwar kyau Aisha tace nidai sai anjima ina jiranki daga haka tai shuru tana zaune a dakin, raudah dake kwance a qasan carpet tana bacci tun shigowarta ta farka tana jin wayar da tai juyowa tayi tace me kike cewa ne?? Tasowa aisha tayi tace kinji wai yayanki aure zeyi kuma bazawara zai aura rauda ta tashi zaune tace bazawara kuma?? Duk yan matan duniyar nan ya tsallake su ya je kan bazawara?? Aisha ta tabe baki tace kema dai kya tambaya idanunshi bai ganine?? Wayarta ta zaro ta kira babbar yayarsu mace wanda a yanzu ita take bin hammad wanda na tsakiyarsu tun suna yara ya rasu tana dagawa tun kafin ta ce komai tace yaya wai kinji yaya bazawara zai aura tsaki yayartata taja tace u're very stupid baki iya sallama ba baki iya gaisuwa ba?? Tura baki tayi tace ni wlh na manta ne kinji yaya zai bata mana budget duk burin da mukaci na bikinshi, yayar tace so what if bazawarace?? Sai me?? Kema zaki iya zama bazawarar nima haka kowa ma haka ba fata muke ba suma da suke zauwaran ba zabar hakan sukai ba Allah ne ya tsara hakan kuma shi yaga abunda ya gani tunda shi dai ba yaro bane dan haka ki kama kanki tun kafin ya jiki ranki ya baci tana gama fadin haka ta katse wayar tura baki raudah tayi tace ni dama tsautsayine yasa na kiraki me bi ma yayar sun ta sake kira bata daddara ba tana dagawa wannan karan tace anty yahanasu ina wuni tace lfy qalao auta ya gida?? Rauda tace gida ba lafiya anty yahanasu kiji wai yaya hammad bazawara zai aura anty yahansu tace to me akayi da zai auri bazawara?? Tace anty yahanasu bazawara fa? Tace ita din ba mutum bace?? Kinga? Wlh ki kiyayi kanki ni ba ruwana tana gama fadar haka ta yanke wayar wadda raudahn take bi ne kawai ta biye mata sukaita jimami ita ma din dai bata wani zurfafa ba amma dai bataji dadin hakan ba, mama na parlor bayan hammad ya fice maimuna wadda ita sauran yan gidan suke kira da yaya har first born dinsu dake kaduna har hammad sbd kowa haka yake kiranta ta kira maman dagawa tayi bayan sun gaisa tace to mama wlh kijama raudah kunne ta kiyayi kanta da yaya muhammad tasan halinshi tsaff mama tace uhm miya faru?ina ruwanta da matar da zai aura? Ba shi ya gani yaji yana so ba sannan shi zawarci ai ba option din mace bane sai dai idan bata da wani zabin shuru maman tayi tana jin ta tace to ita waye ya fada mata?? Naga ko minti talatin beyi da fadamin ba yanzunnan ya fice kuma suna daki sai kuma ta tuna da Aisha tana parlorn suka fara magana ta dauka hankali gareta da ta basu waje ashe gulma ta tafi kaiwa bari maimuna zan kiraki to tace sannan ta kashe wayar ta miqe ta nufi dakin suna nan qasan carpet sai gulma suke suna kushe tun basuga matar ba maman ta shigo ta bata rai tace Aisha juyowa tayi da sauri tace wane banzan haline wannan munyi magana da muhammad zaki kwashe kije kina fada ma mutane sai kuma ta kalli rauda tace kinga ki kiyayeni ina ruwanki da wadda zai aura kuma shi qannen nashi iyayenshi da zaki kai qararshi kinhmga raudah ki kiyayeni wlh bansan iyayi da gulma ke kuma aisha karki qara min irin haka na dauka ganin muna magana yasa kika miqe ashe gulma ce ta ciyoki kika taso ita raudahn me zatayi bata rai aisha tayi ta hade rai ta tsani ai mata fada ita fa a rayuwarta saida maman ta musu tass sannan ta juya ta five tana fita a dakin aisha ta hau hada kayanta a cewarta gida zata tafi raudah tace dan anyi mana fada shine kikai zuciya? Aisha tana hada kayanta tace anyimin fada dai ke wani fadan akai miki?? Kuma ni ba dan shi zan tafi ba dama ina son zuwa gida ta gama hada kayanta ta dora black kimono akan riga da wandon da ta saka ta yafa mayafi ta fito tana zuwa parlor tace mama zan je gida dama ina ta so inje mama tace Allah ya kiyaye a gaida mutanen gida dan bata ga dalili dan tayi ma yaro fada ya yi zuciya sannan ta zauna tambayarshi me ya faru ba, aisha tace zasuji ciki ciki ko kallonta mama bata qara yi ba tana hada kwadon ramarta sai tayi maganinta idan ta sake dawowa, washe gari hammad yaje gidan baba yai mai bayanin abunda mama tace murmushi kawai yyi yace mata sai a hankali to ba matsala ai sai ta nemo maka sai a hada gaba daya ko kuma kai ka duba ko a dangi ko kuma a waje, sunkuyar da kai yyi yace sai dai ita kam ta duba wadda tai mata dariya kawai yyi yace ja'iri kai auren ma arreas za'ai maka shafa kai kawai yyi anan suka ci abinci tare tun da haka sukeyi tun yana yaro,anan gidan ya kwana washe gari sunday yace zai koma mama tace to yaushe zaka shiga ka duba wadda kakeso kallonta yyi yace mama ki duba wadda tai miki kawai ba matsala ranshi babu dadi amma tausar kanshi kawai yake tace to masha Allah ina da wata a raina dukda na san gwaggo zata yi mita tace na dauko a dangina kai kace baka so a dauko maka daga maska dan haka akwai safeeya da suka zo kwana ki yar gidan isyaku qofar qaura kaje ku daidaita naga tana da hankali kuma bata da matsala kallonta kawai yake yace mama yanxu bazaki bari kiga amatullahin ba?? Kallonshi tayi tace meyasa kake insisting na ganta yace maa idan kika ganta zaki fahimci abunda nake fada yanzu wlh bansan ya zan kwatanta miki ba fault dinta da zakice kawai shine ota bazawarace amma apart from that bata da wani matsala mama tace ka zauna da ita ne da kake shedar ta haka??? Girgiza kai yyi yace ko kadan ina dai zuwa gidansun akai akai kuma ina ganinta koyayane a 5months din da mukai zatayi presenting din wani hali dariya kawai maman tayi tace lallai muhammad baka san wacece macen ba amma ba matsala ka kawo min ita na ganta cikin sanyin murya yace to shikenan insha Allah zanyi qoqari dan naga tazo mamanta 'yaryar mashi ce muhammad ba wai cewa nayi bata da asali ba tunda ka fadi babanta ansan yar asalice kawai dai kai dinne bana so ka fara da bazawara nafison ka fara da budurwa tukunna yace to xaki bari idan kin ganta sai kiyi deciding?? To shikenan idan n ganta din sai naji, da murna yace nagode sosai mama Allah ya qara girma kallon yanda ya ke murna take what is so special about yarinyar?? Sai taji she cant wait ta ganta, few days later maman ta kira maimuna a waya taxo gidan take mata bayanin abunda ke faruwa kallon maman kawai take ta kasa cewa komai sai kuma cikin sanyi murya tace mama?? Ba questioning dinki zanyi ba amma what is so special about auren budurwa wata budurwarma fanko ce bata iya komai ba sannan maa yace miki mijinta rasuwa yyi zata iya yuwa da ace me tsawon kwana ne da har yanzu tana tare da mijinta tace na sani maimuna amma auren fari ya auri bazawara?? Tace mama kinsan waye hammad tunda kikaji yace ita din may be da abunda ya gano, kuma yanzu duk yarinyar da kika cusa mai bazai ga mutuncinta ba kuma bazai sota ba mama wannan hadin zai iya sawa yaya hammad ya fada halaka yau da ace shi ya gani yace yana so kinsan cewa zai iya adalci tunda har yana sonta amma matar cushe?? Bata da wani daraja a idanunshi dan Allah mama ki janye wannan abun kawai ki musu fatan alkhairi yace ran asabar zasu zo ko?? Gyada kai kawai maman tayi tace ki bari idan kika ga alamun rashin tarbiyya ko budewar ido sai kice ya auri wata balle nasan yaya bazai taba zuwa inda babu tarbiyya ko kamun kai ba sbd tsanarsu da yayi dan Allah kiyi haquri mama gyada kai kawai tai tace to shikenan Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lfy amma idan bata min ba dole zai auri wata gyada kai maman tayi tace insha Allah mama karki wani damu kuma idan zaki nema mai ma banda safeeya ko aisha nasan aisha kinsan halinta na safeeyane dai ya qaru kima janye zancensu gara a nemomai a maska very simple and local wife yazo ya wayar da ita ya saka ta a makaranta amma ina fada miki yan matan yanzunnan sai a hankali kam to Allah ya nuna mana, randa hammad yaje yake sanar ma da amatou zai kaita wajan mamanshi cewa tai bazata ba yace baki yadda dani bane?? Girgiza kai tayi tace gani nake kamar bai dace ba yace to kuna da yan uwa a cikin katsinan sai kuje can idan yaso sai nayi maku kwatance tace akwai amma ni bansan gidajensu ba tunda tun ina yarinya rabona da gidajensu kuma basu nemeni ba wasu ma tun bayan rasuwar mama ban qara ganinsu ba yace to how about mu tafi dake da baby da anty maamaa?? Kallonshi tayi sai ta sauke ido tace to that will be better yace akwai gidan uncle dina matarshi tana da kirki ita ta riqeni bata da yara ko daya sai na kaiku can ku kwana washe gari sai mu dawo, to Allah ya nuna mana ta fada tana wasa da yatsunta a ranar ta sanar ma umma rabi umma rabi tace kina ganin ba matsala?? Tace a yanda nake gani dai ba matsala insha Allah maryam da taji lbrn tace to nameye matsawar dole sai kinje tunda nesa kuke aure fa zakuyi har sai sun gaji da ganinki, su suka sani koma de menene Allah ya nuna mana nidai baxan dagama wanda ya raina min hankali qafa ba wlh, ni ba rigima zamuje yi ba da Allah, na sani kawai ina fada ne dan bazan tolerating nonsense ba, ranar asbar 6 sun bar zaria suka nufi katsina 9 sun isa katsina sai da ya fara ajiyesu gidan baba sukaci abinci sukai sallah sannan suka huta mama kamar zata goya amatou da ta ganta taji dadi sosai daki ta basu suka kwanta sukai bacci ta janye farrah tai mata wanka bayan ta karbi kaya marassa nauyi dan sun taho da na farrah da dan dama sbd gudun qarancin kaya ita ta zauna ta bata abinci taci ta qoshi ta kwantar da ita nan da nan tayi bacci kafin su tashi zuwa azahar mama ta hada musu lafiyayyen abinci sun gama kenan maryam ta taso ganin suna aiki yasa ta karbi wanke wanke mama tace ta barshi maryam taqi sai da ta wanke su tas ta gyara kitchen din maryam tana da wani irin hali yanda kai treating dinta haka zatai treating dinka sabanin amatou itama bata tolerating nonsense amma tana da soft heart wani lokacin sai taga meye ma idan ta rama abunda kai mata?? Sai kawai ta hqr maryam kuwa ba haquri, mai aikin maamaa tana ta mata sannu ganin ta gama gyara kitchen din tayi mopping daki ta wuce ta samu amatou a kan sallaya ta idar da sallah kallonta tayi tace daga ina kike?? Tashi nai na fita shine na gansu suna aiki na tayasu, gyada kai kawai amatou tayi tace farrah bata dawo ba? Eh tana bacci wajan maman leqowa me aikin mama tayi me suna laure tace mama tace ku fito ku ci abinci, maryam tace to nidai bari nayi sallah, wucewa toilet tayi amatou ta zauna a gefen gado dan bazata iya fita ita kadai ba maamaa da ta fito daga toilet tana tsane ruwan dake gashin goshinta tace baki fita ba?? Tace jiranki nake idar mu tafi tunda qasaru zakiyi sai da ta idar kuwa suka fito hajiya maryam ce a kan gaba sai kace wata boss amatou tana bayanta sanye da madaidaicin hijab akan riga da skirt din da suka zo dashi a jikinsu iri dayane da maamaa duk kayan da suka debo iri dayane maaman ce ta hada musu da yamma, wajan la'asar sukayi wanka daukar doguwar rigar farrah tai wanda maroon ne aka hadashi da red net yyi bala'in kyau sosai wani sandal dan dark green maamaa ta fito ma farrah dashi duk cikin kayan da tazo dashi daga abuja ne less din kuwa amatou da farrah kawai suka dinka maamaa tace bata so sbd ita baqa ce bata son maroon ita ta nemi blue a kasuwar yan dameji wanda zaka samu expensive laces amma dameji anan zaka samu 2yards 1yard haka dai su kuma siya sukai suka dinka maimakon su bata wata 13k din ita ma a sai mata sai tace ma amatou zata je cikin kaduna kasuwar en dameji wata course mate dinsu ta rakata dakyar amatou ta barta ta fi da dinkunansu bayan sun siya suka biya shagon dinki dake ya kware a dinki kwatance kawai maamaa tai mishi na amatou da farrah sbd qaramar sallah dake qaratowa amatou ta sai musu dan da wuri take musu kafin kaya da kuma masu dinki suga matsowar sallah su tsauwala komai anan

Please Login or Register in order to submit comment