Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin zaria suke dinki amma yarinyar ta matsa su kai cikin kaduna kuma maamaa tana ganin dinkunanta suna bala'in yi mata kyau dukda dai suma telan nasu ya iya amma kana gani kasan ba kwarewarsu daya ba,ya karbi numbern maryam yace zasuyi waya dan ya fada mata kudin hakan kuwa akai 13k yayi musu dinki su biyu 5k kowa farrah kuma 3k a ranar da maaman ta fada mata kudin dinkin tasha fada sosai sai da tayi dana sanin kaiwa dinki cikinky kaduna amatou tace me xanyi da dinkin 5k ga na 2500 ko 3k dina yafimin rufin asiri bansan wane iyayin yasa kika jajjabo dinki a kaduna ba kwana maryam tai ta wuni tana fushi dan dakyar umma rabi ta bata haquri gskyr ta ce duk sallah babu inda suke zuwa suna cikin gida zadai suje idi wanda anan bayan unguwarsu akeyi kuma zasuyi tuwan sallah kowa yaci ya qoshi basu da maqota balle su kai musu opposite dinsu ne ma a lokacin aka fara gyara daga gani bayan sallah za'a tare a gidan, kallon kayan kawai amatou takeyi tace wannan wane kayan ne?? Dan har ta manta dasu ma tunda ta bata ATM ta tura mai kudin ta dawo mata dashi kota kansu bata qara biba balle tasan ta amso ko bata amso ba ba tare da maryam ta damu ba tace kedai kisa mana lace dinnan ne dai da na kai dinki daga shi tayi gown ce kusan zance pencil ce me balloon hand, zama akai akayiwa dinki biyayya sannan akai ma lece din bauta ya tsaru yyi kyau sai a lokacin taga kamar ma ya musu arha tunda ko a da ma dinkunan da ake musu suna yara yana kaiwa 5k din kasa kunne maama tayi taji ko zatayi complain amma shuru kake ji dinkin babu wani hayaniya a tattare dashi amma yyi kyau spray ta fesa oud ne mai qamshi amma ta cikin jikinta kawai kake jin qamshin amma ko yaya ta danyi nesa da mutum bazaka ji ba dora humrarta tayi yar duri sannan ta saka rigar ta juya ma maama dake ta kallonta baya tace saka min zip din shuru maryam tayi dukan ta tayi tace dalla zugemin zip mana washh maryam ta fada tana sosa gun tace anty mimi wlh karki zauna a gaba juyo tayi tace ban gane ba tace kinsan Allah sai doctor ya sakar mana sitiyarin mota dan haka wlh baya zaki shiga ba daukan dan braight red jambaki tayi ta miqa mata ba musu ta ansa dan ita ma ta fara zama interested da abun sakawa tayi ta dauki kwalli ta saka maama tace kinyi azkhar?? Girgiza kai tayi tace yawanci five nakeyi tace to zauna kiyi bari na tattare dakin kafin kace me ta tattare dakin ta gyarashi kayanta ta dauko zata saka ita kam wani light brown cotton yard ne akai mashi dinkin a shape amma yyi mata kyau, sai tayi mai adon black ita kuma ,ciro ma amatou hill sandal tayi yyi kyau black sai back vail ta bata sakawa tayi ita kuma maama tana saka mata siririyar sarka golden da dan mitsitsin dan kunne tun bayan rasuwar barraq bata qara ganinta tayi kwalliya haka ba kullum cikin simple dressing take infact ina ma suka ga lokacin yin wannan?? Su ba biki suke zuwa ba ba komai ba ko conference din da tayi presentation da tai kwalliya bata kama qafar wannan ba kallonta kawai maama keyi she is truly beautiful masha Allah, nifa bana son kallo kin sani ai dariya maamaa tasa tace to kuwa ki shirya suna tsaye sai ga farrah ta shigo an taje mata tsefaffen kanta an gyarashi an saka mata band din kayan, durqusawa maamaa tayi ta rungumeta ita ma tayi kyau sosai sai kuma ta dagota tace zo nan zama tai ta saka mata kwalli sannan tai dressing mata idon da baqi yyi kyau idanun suka fito sukai manya tubarkallah masha Allah sai ta dan saka mata jan baki itama sama sama hakan yasa yai mata kyau, amatou ta kalli kanta a madubi tace maamaa bamu zaqe dayawa ba?? Ba wani zaqewa anty mimi so kike a rainaki ?? Kuma ba shigar banza mukai ba wlh kinyi kyau idan kina so ma sai ki yafo mayafinki daga saman kai ba wani abu bane haka kuwa akai dake yanayin daurinta laure ce ta shigo tace likita ya zo yana parlor miqewa sukai mama ta karbi wayarta ta zura a aljihun rigarta suka fice tun daga nesa hammad ya fara leqe dan ya hango gefen fuskarta amma bai tabbatar ba ko ita dince maama na gaisheshi wlh beji ba kwata kwata gaba daya kallon amatou yake she is totally a changed person bada ban daga cikin gida zasu shiga mota ba kuma sai sunje gidansu sannan zasu sauka da babu abunda zaisa ya barta taje ko ina a haka ba she is too precious to be seen like this by everybody dai dai kanshi yaji mama tace ikon Allah Hammad ana gaisheka fa da sauri ya juya ya kalli maamaa dake ta dariya kamar ranta zai fita shafa kai yyi yace anty maamaa muje mama bari mu dawo qin yadda yyi ya wuce gaba ba saida maama tayi gaba tana ma mama sallama amatou tabi bayanta shi kuma ya kama hannun farrah suka fice bai yadda ya dauke idanunshi daga kanta ba lips dibta looks more delicious today...


Mrs maan🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: *AMATOU*🧕
(The single mother)

25
Suna fita maama ta tura amatou baya ita ta shige gaba ganin dagaske zancen nata ya fito kallon maryam yai ya cilla mata hararar wasa yaso ta zauna a gaban nan yanda duk bayan second daya ya juya ya kalleta sai kuma ya kalli reverse mirror a saitinshi take hakan yasa ya saki wani murmushi maama dake dariya tace an gudu ba'a tsira ba nidai a bari a saukeni farrah ta dafa kujerar da yake zaune ta baya tana fadin uncle ina zamu?? Yar dariya yyi yace gidan grandma?? Tace grandma irin ta nan gidan?? Tayi min wanka ta taje mun kaina bude ido yyi yace ita grandma din?? Gyada mai kai tayi tace kuma tace sunanta grandma dariya kawai yake amma idanunshi na kan amatou da kana ganinta kasan she is uncomfortable kamar harda mixture of narvousness kallonta kawai yake Allah ne kawai ya kaisu lfy horn yyi aka bude mai gate, din hade tafin hannunta tayi ta damqe su a tsorace take wani irin kallo yake jefa mata dukda bata dago ta kalleshi ba, kallon compound din yyi yaga motoci dayawa a compound din wanda da safe daya zo gidan babu mota biyu ya gabe yasan ta qannenshi ce da suke aure a kt second to the last born dinsu ce kawai aka kaita maiduguri parking yyi ya fita daga motar ya zagaya ya bude mata a kunyace tafito tsoro yasata delay da tasan abunda zaiyi knan bazatai delay din fitowa ba kunya takeji idan taga yana haka yanda yake treating dinta is something da yake sa zuciyarta narkewa and hakan yana sa ta na dan samun hope a zuciyarta unlike before da tayi giving up komai sai dai taci tasha ta rayu these days idan ta tuna hammad tana jin zuciyarta cikin farin ciki da annashuwa nauyin dake zuciyarta taji ya dan ragu kadan fitowa tayi a hankali hills din da ta dan sa yasa ta zo dai dai shouldernshi har kanta ya dan gota they made a perfect match, daga can wajan qofar parlourn maamaa ta tsaya tana kallonsu kamar ta sace ta gudu, farar shaddace light brown shaddace jikinshi simple dinki babu komai tayi mashi kyau dis time around ta kai mishi har qauri dan ta zarce ce hannunshi da black cufflinks da black wrist watch sai black ta kalmi hularshice kawai dark brown amma sai kyalli yace jerowa sukai da sauri maama ta sauka tace likita dan aramin wayarka kafin mu shiga zaro ta yyi kawai daga cikin aljihu ya miqa mata daga musu yatsa tayi tace a bani one minute please i cant let this moment slide kafin suce komai ta dan matsar da amatou jikinshi, kabar da hannunta tayi tadan harareta kashe mata ido daya tayi sannan ta hau step din ta fara yi musu hotu tace to ku taho kasancewar da dan hasken rana yasa hotunan sukai masifar kyau har suka wuce suka shiga cikin parlorn tana musu sai da taga zasu shiga sannan ta zira wayar a aljihu ta ja hannun farrah suka shige ciki duk a bunda suke raudah tana ta leqensu ta window gidan a cike yake kowa na son yaga matar hammad har yan matan su safeeya Aisha sai yau ta dawo mama taso maidata tunda ba'a isa ayi mata fada ba amma ganin mutane yasa bata ce mata komai ba tsayawa amatou tayi ta kasa shiga juyo wa yyi ya mata alamun da ta shigo dukda tai parlorn nan tap yake abunda ya bashi mamaki harda hajiya gwaggo tana zaune ta kwama gilashi irin na ido dinnan baqi ta tsufa sosai sai mamul mamul take da baki wucesu maamaa tayi ta shigo da sallama amatou ta biyo bayanshi zaka ga dai alamun mutum amma baka isa kace ko waye ba gaba daya parlorn suka zuba musu ido duk yanda amatou bata tsoron idon mutane yau sai da jikinta ya hau rawa dukda bata daga ido ta kallesu ba amma tasan akwai idanu da yawa akanta wasune suka amsa sallamarqtake a ranta tana cewa to su mutanen gidanne haka ko kuma gayya akayo mana, kallon maamaa da farrah kawai suke ganin da fara'a ta qarasa duk sun dauka itace banda aisha da ta san cewa wannan bace kallon hammad kawai take dayake tafiya a hankali bakinshi yana dan motsi daga alamu magana yake mata ita ta hango mutum a ta bayanshi qarasowa sukai jin gwaggo na cema maryam zonan kishiya inga dame kika fini har ya hangoki kowa mamaki yake ganin maryam ko raudah bata kaiba dukda yanayin jikinsu kusan iri daya amma kasan maamaa yarinya ce dariya kawai maryam tayi tce ba ni bace gata can tana boyewa ita gaba daya juyawa sukai kowa jira yake yaga vazawarar da hammad zai aura murmushi yyi sannan ya dan matsa amatou ta bayyana sai wasa take da yatsunta a hankali ta dan dago ta kallesu ta sunkuyar da kai a hankali ta durqusa zata kunce igiyar ta kalminta yace let me help please da sauri ta girgiza kai a tsorace tace zanyi ganin yanda ta tsorata yasa ya barta sunkuyawa tayi ta qunce takalmin mama na zaune tana kallon ikon Allah itafa ta zata zataga wata me idanu a tsakar kai idan banda kamar da amatou take tsananin yi da farrah cewa zatai qaryane ba ita ta haifeta ba sai yanzu ta fahimci dalilib dayasa hammad ya dage kan cewa ta fara ganin amatou kafin ta yanke hukunci yammatan kuwa tamkar ruwa ya cinyesu haka sukai a cikin parlorn idanun aisha tuni suka kada sukai jaaa ita bata tsammaci kyan da zaleena take zuzutawa ya kai haka ba qirjinta ta kalla wanda a duniya shi yake tsokale ma aisha ido ko namijine ya gudu bai santa to sai ta dauka cewa sbd rashin nono ne yasa suke qinta a nata mentality din ko wanne namiji mayen breast ne, yaya sai murmushi take ita dai ta yadda da yayanta gashi kuwa bai bata kunya ba bayan ta gama cire takalman ta daukesu ta kaisu gefe daya sannan ta qarasa parlorn gaba daya a rude take she just try to keep calm amma manyan wajan sosai suka fahimci haka, gaban ajiya gwaggo ta qarasa daidai qafarta ta durqusa wannan dabi'arta ce tun a gidan barraq bata taba jin dadi ta gaisar da babba daga nesa sai da ta gaisheta gwaggo da baburarren bakinta da wasu haqoran suka fice tana mata tsiya, lallai muhammadu da abunda ya gano shine ya yadani hammad kam sai bin amatou yake da kallo anty yahanasu ta tabo yaya tana nuna mata hammad da ido murmushi kawai tayi lallai an mai babban kamu dukda bata ga laifinshi ba dan tana hango alheri a tattare da amatou insha Allah miqewa tayi ta qarasa gaban mama ta durqusa ta gaisheta amsawa kawai take tana alajabi ita mamaki abun yake bata wai farrah yar tace sosai take ganin nutsuwa na tashi a tattare da ita wannan ai baxata taba hadata dasu aisha ba dama wasu yan matan dake cikin family din nasu gaisar da anty yahanasu da yaya tayi suka amsa cikin fara'a yaya ta miqe ta qaraso wajan ta zauna a kujerar gefen amatou tana miqa ma farrah hannu tace masha Allah ni ga wadda nake so a bani nan yayana ya dauki uwar ni ina son 'yar kafin wani yace komai hammad yace ban baki ba dariya suka saka dake suna wasa da hammad yasa tace kai yaya kaima ka jira a baka mana sai ka hanani tukunna ta fada tana dora farrah a kan cinyarta sosai yarintar ta burgeta ba kuma wani abuba gayun da akai mata shi ya bala'in burgeta ga kamar mamanta sak tasan kuma maamaa ma suna da alaqa da su dan ga kama nan kawai dai ita baqace amma baqin me sheqi hakan yasa ta ita ma ta bada nata kalar kyan ko ruwa qinsha amatou tayi gaba daya ta qagu su tafi wani abun haushin aka kawo kaza maamaa sai da ta baje taci kayanta ba fulako taci ta qoshi yaya ta bama farrah dan kadan taci tace ta qoshi maamaa ta kora da sanyayyar hura abunta sunayi suna hira maamaa ce ke amsa mata su rauda tuni sun tafi daki aisha kuwa dama ta nemi maboyar kuka gwaggo ce ke jan amatou da hira sai dai tayi murmushin yaqe, tashin da mama tayi ta je daki yasa yana ganin ta tafi ya taso ya qarasa gaban amatou ya durqusa sbd zaune take a kan carpet qasa qasa yace you are uncomfortable ko?? Da sauri ta girgiza mai kai yasan kara kawai tayi mishi, yace are you sure ?? Gyada mai kai tayi yace to shikenan , gwaggo ta dago sandanta wato ni ka raina ko?? Kaga uwarka ta miqe yayi yar dariya yace au ashe kuna parlor to tunda mama ma ta tafi daki na dauka kunbar parlorn anty yahanasu sai uhm da uhm uhmn takeyi wato duk kyan takalmi sai an takashi ita bazata taba yadda hammad ke wannan rawar qafar akan mitsitsiyar yarinyar da batafi sa'ar mami ba yanda yake kamar bashi bane wanda suke bala'in jin tsoro sai wajan 6 suka babar gidan, yaya kamar jira take su kebe da mama tace.....


Mrs maan 🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: ~*AMATOU*~🧕
(The single mother)

26
Tace maa kinga abunda nake fada miki ko?? Ko kinga aibun wannan?? Maman tace uhmm ai zamani ne yazo da haka dukda dai baka shedar dan mutum kar muje boye halinta take, murmushi kawai yaya tayi tace ni kuma ko mama anawa tunanin idan har boye halinta ta so yi abunda zatayi shine zata sako hijab ne har qasa cikin siffar saliha dan ace ita saliha ce idan kuwa tayi niyyar kwalliya kamar yanda wannan tayi to zaiyi wahala idan baki gane ba ko yayane sai ta nuna wani halayya a shigarta misali ko kiga attatch ko chewing gum ko abun hanci kingane irin wannan tunda ba abune marar kyauba amma mu anan idan mutum yayi wani abu makamancin haka to za'ai mishi mummunar fahimta ne,mama tace naji nima bakiji na kusheta ba idan alheri ce a gareshi ina fatan Allah ya basu zaman lfy idan kuma ba alheri bace Allah ya kawo mishi hanya mafi sauqi ya rabu da ita, rungumeta tayi tace ameen mama insha Allah ma alherice ta burgeni sosai barin nutsuwarta kana gani babu algus nan suka cigaba da hirarsu, a ranar babu wanda yasan sanda aisha ta bar gidan tana zuwa gida ta tafi gurin mamanta dakinta tace mummy da yaushe daddy zai dawo kallonta tai tace ya'akai?? Naga idanunki sunyi ja, ta xauna gefen gado tace mummy transfer nake so zuwa ABU zaria, kama baki mummyn tayi tace ke dai wahala bata isheki ba shi hammad din zaki bi zaria?? Girgiza kai tayi tace ba shi zanbi ba wata zanbi na koya mata hankali aisha nifa banson fitina wacece kuma me tai miki?? Turje qafa ta farayi tace mummy nidai zan fada miki daga baya kinji yaushe zai dawo?? Tabe baki mummyn tayi tace nasan bayan magariba zai shigo, abunka da masu hannu da shuni within 3weeks aka gama komai ta koma Abu sai dai level 300 take ita gida aka kama mata dan cewa tai bazata zauna a hostel ba yyi mata qazanta hakan kuwa akai aka nema mata unguwa mekyau aka kama mata gida ba kusa suke da su amatou ba, ta bangaren amatou kuwa ranar baba ya kira akan farouq zai zo ya daukosu dukkansu semester tayi xafi amma bazata iya ce mishi hakan ba sai tace mishi to ranar friday farouq yazo har umma rabi suka tafi da tace baxata ba farouq yace harda ita baban yace suka ko kama hanyar abuja Allah ya kaisu lfy, gidan tuni ya cika a abdurrahman ne kawai bai qasar da daddare baban ya kira amatou ita kadai, zama tayi tana jin fargaba, kallonta yyi yace aminatou yanxu dai nasan ke ba yarinya bace dukda ba wani shekaru gareki so ina so in gambayeki, tace to baba yace akwai muhammad da yazo neman izinin nemanki nan to sun kirani suna so suzo nace su bani lokaci dan naji ta bakinki kin amince?? Haushine ya turnuqeta wato shi hammad haka akeyi itafa bata taba cewa tana sonshi ba bata taba amsa mishi cewa ta yadda zata aureshi ba wancan neman izinin fara nema ne ai he is surpposed to ask her first kafin yace zai turo, yace inajinki idan baki yadda ba bbu wanda zai miki dole sai dai zan miki tuni a matsayina na uba a gareki aure ba qaramin mutunci yake ja ma mace ba kuma duk inda kika je kina da mutuncinki da darajarki kuma yin aurenki shi zai nuna cewa kin yadda kin amince da taki qaddarar nayi bincike sosai yarone mai hankali da nutsuwa nama yi mamaki da akace har yanzu baida aure farkon ganina dashi ban dauka cewa tuzuru bane kina buqatar kulawa ita mace daraja gareta ba'a barinta haka sakaka qofofin rahamar ubangiji suna da yawa idan baki samu wannan ba zaki samu wata a gaba amma idan zan baki shawara karki bari ya kubuce miki dan naga yana sonki sosai amma idan bai kwanta miki ba zan baki goyon baya dari bisa dari, shuru tayi yace aminatou ina sauraronki ko na dan baki lokaci?? Gyada mai kai tayi a hankali yace to daga yau zuwa gobe da daddare sai ki yanke decision tace to nagode baba Allah ya qara girma tana fadin haka ta miqe ta fita maamaa ta qagu abun ya zama official duk abunda ake ciki hammad yana sanar mata kamar wani abokinta bai taba tsammanin zai sake da yarinya qarama haka ba duba da baya sake ma qannenshi dukda basu da raini rauda kuwa tashi kawai tai taga ana tsoronshi shiyyasa ta bi sahu amma abu bai taba hadasu ba a ranshi yana ji may be da ya sake musu suma baxasu rainashi ba sosai maryam take ganin girmanshi duk abunda yace mata to tamkar yankan wuqane kuma zasuyi wasa da dariya abunsu, maamaa tasan dalilin zuwansu amma ita amatou bata sani ba sai da baban ya sanar musu lokacin da aka kira amatou suka hau gulmar da khalifa wanda ke gefenta suna hira, amatou na shigowa parlorn maamaa sai kallonta take ganin ta hade rai ta nemi waje ta zauna ya sa maamaa ta nema ma kanta lfy, hammad ya kira maamaa satar idon amatou tayi ta miqe khaleefa ya kalli amatou yace madam me baba ya baki be bama dan auta ba?? Dariya ya bata sosai tace ai na karbe maka matsayinka tuntuni, hira suka hau yi har khaleel umya shigo yace madam kun iso su dai bazasu ce mata anty ba amatou yau data gaji tace wai kuyi ta qaqaba min wata madam ni ku kirani da sunana mana amma kuyi ta wani madam madam khaleel yace wane mu?? Ai respect kawai ko yaya na nan ko baya nan ke din matarshi ce first dota in-law din gidannan ko aure yaya abdul yyi ai a gabanta kike harara ta gallama kwalla ya ciko idanunta dariya yyi yace Allah da gaske nake dariya tasa itama amma me tafe da hawaye shuru duk sukayi hakan yasa ta miqe tace ina zuwa kallon tausayi suka bita dashi, basu taba tado da zancenshi a gabanta ba sai yau so basu san haka take reacting ba, daki ta shige maamaa taji tana fadin wlh ban sani ba, nima dai haka na gani, eh kayi kiran yanxu nikam sai anjima dariya ta saka ta kashe wayar ko kallonta amatou batayi ba yanxu ta fara gani maamaa ta san komai amma bata fada mata, kwanciya tai a kan gado ta tuqunqune qafarta cikin bargo ta rufe ido hawayene suka gangaro mata a hankali yau dai tayi missing barraq sosai tuna sai da ya samu full amincewarta sannan ya aureta dukda cewa yana da damar aurenta koda bata amince din ba vibration din wayarta ne ya dawo da ita zaro wayar tayi tunda tayi blocking numbers din bai qara kira ba ganin dr hammad ne yasa ta daga dan ya kira a daidai, murmushi yyi jin ta daga kuma batayi sallama ba wanda is hardly tayi hakan, sallamar yyi ta amsa ciki ciki, shuru yyi sai kuma yace Allah yasa ba wani laifin nayi ba banza tai mishi yace mimi?? Tace ina jinka, yace laifin nayi kenan to Allah ya baki haquri ki fada min me nayi?? Shuru tayi sai kuma tace baba ne ya kirani ya ke cemin zaka turo ni kuma sai naga bance na amince ba tunda bama ka tambaya ba? Ko a ganinka alfarma zakai min ka aureni tunda ina bazawara?? Ya salam yace tare da gyara zama akan kujerar parlornshi da yke kallon CNN tun bayan dawowarshi sallar isha'i, waye yace miki alfarma zan miki ?? You are too precious for that amatullahi let me tell you something ko aure kikai sau goma indai a yanda kike yanzu haka na sameki ke zakiyi min alfarma ke din aba ce me daraja wanda ba kowanne mace bace take da wannan darajar kuma da kin tambayeni dalilin dayasa ban nemi izininki ba, banji dadi ba da kika ji cewar kamar sbd alfarma zanyi miki yasa ban tambayeki ba nace zan turo iyayena amatou i want you to accept me wholeheartedly and willingly bawai ki amsa min ba while you are always uncomfortable with me nasan bazaki saki ranki ki fadamin abun da ke ranki ba randa naje neman permission gurin baba akan ina so na fara nemanki abunda ya fara cemin shine bazai miki dole ba inje in nemi amincewarki hakan yasa nasan dole zai nemi jin ta bakinki and i know you will tell him abunda ke ranki kinji dalilina daya sa ban fada miki ba and... Sai kuma yyi shuru amatou da tuntuni ta lumshe ido wani sanyi yana sauka cikin ranta qasa qasa tace and?? Shima qasa qasa cikin sanyin murya yace i cant stand being rejected by my first love directly from her dagaske yana daya daga cikin abunda yasa ya ji bazai ji ta bakinta directly ba gara idan ma rejection dinne yaji ta bakin wani abun zai masa da sauqi, sosai amatou taji ba dadi yace amma kiyi haquri idan bakiji dadin hakan ba and insha Allah hakan ba zai sake faruwa ba you know i love you so much ko?? Murmushine ya bayyana a fuskarta can ciki wanda da yana cikin hayaniya ko yaya take bazai iya ji ba tace and i love you too, miqewa zaune yyi yace mimina?? Dariya ta danyi jin yanda ya rikice

Please Login or Register in order to submit comment