Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takardun hannunshi yyi yace hannu zaki saka anan amatou kallon papers din Tai sannan ta Kalli yayan nata tana son qarin bayani, gyara zamanshi yyi sannan yace wire house ne nai reserving Daya a Kano Daya a Katsina cikin wire house din baba, shine nake so na Baki Daya ki zabi duk wanda kika xaba, girgiza Kai ya fara yi tace bani da abunda zanyi da wire house Yaya na yafe Maka duniya da lahira tunda dadewa sbd bani da wata riba ma idan ban yafe maka ba, Maryam CE ban sani ba itama zan nemar maka yafiyarta, Amma we are okay Alhamdulillah hade Rai yyi yace kinji nace Ina Neman opinion dinki?? Girgixa Mai Kai tayi tace kayi hqr Yaya idan na ansa ma bansan yadda zanyi dashi ba, amatou kadara ce wata Rana zatai miki amfani ko abu kika tashi Yi me muhimmanci Baki da yadda zakiyi ai xaki iya dagawa ki siyar Yaya kayi hqr Dan Allah kayi amfani dashi nidai bana so , duk yadda yyi ta ansa qi tai Yi ma umman naku magana mikewa amatou tai ta kira umma rabi, zama sukai akan tabarma yai mata bayani gidan ajiyar abinci ne yake so ya Bata taqi amsa shine yake so umma rabi ta saka baki, bazai iya ce mata gadonsu ya cinye ba shine yake so ya dan rage Wani Abu ko zai Dan ji sassauci, kallon amatou umma rabi tayi tace ba'a haka amatullahi, ba'a Maida hannun kyauta baya wannan aikin shedan ne ai , umma rabi ni wlh bansan ya zanyi dashi bane idan ya bani, nace Miki ita kadara lokacin amfanin ta tasowa yake ki karba ki ajiye a babu yadda zatayi bazata iya musu ba Kuma tunda sunfi qarfinta yace wanne kike so ?? Na katsinan ko na kano??duk wanda kike so zan Baki Amma ba matsala zan Baki na katsina tunda naga kuna da relatives a can bazaki rasa Wanda zai na Dan duba Miki wajan lokaci zuwa lokaci godiya yai ma umma rabi ta miqe ta koma cikin parlor anan yake cema amatou zai koma, Yaya ka tsaya ka ci abinci mana saura kadan murmushi yyi kawaii yace karki damu amatou yau nake so na koma Kano insha Allah hijab ta Sako ta CE ma maamaa ki fito yaya zai tafi miqewa tai daga zaunen da take a kitchen tace baxai tsaya yaci abinci ba ??yace sauri yake, fitowa tai daga kitchen din suna sallama da umma Rabi tace wai Ina Farrah ne umma??? Tana daki tun dazu tai bacci, bacci Kuma azahar ta kusa, sai Kuma tace bari mu rakashi umma, to sai Kun dawo, bin bayan Mahmud tai da sauri Dan har ya fice a gate, ta qaraso sun Dan fara gaba Maryam ta fito tana qoqarin gyara hijab dinta MOTA ta hango dalleliya mota ta sha kwana ranar Nan ta ga Dr Hammad ya ajiye su amatou a shago hakan yasa ta San cewa shine murmushi tayi, tunda ya karyo kwana yake kallonsu suna tafiya a jere kana ganinshi kaga babban mutum, garin kallonsu ya nemi kaucema titi da sauri ya ja sitiyarin motar tashi Mahmud yace subahanallahi Dan kusa suke sosai Maryam da ta qaraso kusa dasu sai a lokacin Kuma Hammad ya ganga, sauke ajiyar zuciya Maryam ta Kalli Mahmud tace Yaya ku gaisa da VC dinmu gun farrah yake zuwa Yana San Yara sosai kallonta Mahmud yyi yace VC dinku Kuma??? Eh Amma Bai Dade ba dan baifi 2weeks ba Yana da kirki sosai, tana fadin haka ta qarasa gurin motar Wanda yaqi fitowa sai kallonsu take amatou na gefe Yana kallon yadda take cilla ma Maryam harara baisan me Maryam din take fada ganin ta taho ya bude MOTA ya fito tun da ya fito mahmud ke inspecting dinshi from head to toe physically dai bashi da wani aibu sai dai shi Hali a zuciya yake ba a fuska ba Amma dai yyi Mai kama da nutsatstsen magidan ci 😂 Maryam na qarasawa tace Ina kwana doctor, murmushin qarfin hali yyi yace anty maamaa kin tashi lfy?? Dariya kawai tai Dan haka yake kiranta Wani lokacin tunda Farrah ma haka take kiranta tace yayanmu ne nace mai zaku gaisa tunda Kun hadu, wani abu me kama da relief ne ya ziyarce shi genuine murmushi yyi yanxu Kam yace sure, why not?? Gaba Maryam tayi Yana biye da ita suka qaraso ya miqa Mai hannu a mutunce suka gaisa amatou da ke gefe sai kallonsu kawaii take bama su ba particularly Hammad a da tana ganin tsayin Mahmud yau DAI sai Taga Ashe gajerene hada idon da sukai yasa da sauri ta dauke Kai sai kuma tace ina kwana sir murmushi kawai yyi be amsa ba ance babba babbane Dan haka Mahmud na lure da komai Dan ya girme ma doc Hammad ko a ido dukda yasan Shima Hammad ba yaro bane, Maryam tace Farrahn ma bacci take tun dazu yace habba ?? Ba damuwa sai na dawo gobe tunda nasan zaku islamiyya an jima ko?? Gyada mishi kai tayi qara gaisawa yayi Mai sallama ya wuce, a hankali suka cigaba da takawa Shuru GABA Daya sukai sai Kuma ya Kalli amatou kana ganinta kasan tunani yake yace amatou??kallonshi tai da sauri sai kuma tace na'am yaya,a yanda na ganku sosai nake alfahari daku kunsan meyasa?? Girgiza Kai sukai a tare," yace sbd baku zubar da mutuncin ku ba ya Kalli amatou yace ke kina babba kuma wadda ta taba aure naji dadi fiye da tunaninki da baki zubar da mutuncinki ba sbd shine kima da darajarki ta diya mace haka zalika maamaa tashen girma baisa ta kauce ma hanya ba dukda nasan harda contribution dinki kin qoqari ba kadan ba hatta khadija(Farrah) Banga alamun Rashin tarbiyya a tattare da ita ba sannan kuyi hqr da na gaza muku a matsayin yayanku Kuma Banga laifinki ba amatou da kika qi yadda ki zauna a gurina a karo na biyu ba Dan Allah ku cigaba da riqe mutuncinku, sannan game da mutane naga unguwar taku babu mutane sosai amma Ina so ku kula da Wanda zakuyi mu'amala dashi kunji ko??? Gyada Kai sukai amatou tace insha Allah, sai Kuma yace shi wannan VCn naku kika ce gurin Farrah yake zuwa?? Gyada kai Maryam tayi tace wlh Yaya haka kawai Allah ya hada jinin su da farrah sai ya taso tun daga Kaduna ya ganta, yace A Kaduna yake ?? Ta girgiza Kai tace da a Abuja yake sai aka dawo dashi nan gyada Kai yyi sannan yace Kuma Kikace gun Farrah yake zuwa ?? Maryam tace eh, murmushi kawaii yyi bai ce komai ba ya juya ya Kalli amatou yace kika CE level nawa kike???tace 4 ya ce maamaa Kuma 2 ko?? Tace eh to Allah ya Baku sa'a gaba ki dayanku Allah Kuma ya qara tsareku da tsarewarshi, a tare suka amsa hannu amatou tasa ta tsaida Mai a daidaita sahu, shiga yyi amatou tace a gaida kowa da yakowa yace zasuji insha Allah sannan ya fada ma me adaidaitan tashar da zai kaishi Qarfe hudu sukai waya da Mahmud akan ya Isa lfy godiya amatou ta qara Mai ko babu komai naka nakane ba qaramin cikin farin ciki suke ciki shekara biyar Babu Wani nasu da ya taba zuwa Dan ya gansu, ran Monday amatou da wurwuri ta Farka bayan tayi sallah ta nufi kitchen ta Dora musu abinci Dan basa barin wanke wanke ya kwana Hakan yasa Babu kwano ko Daya me datti tuwo miyar kukar da umma tai musu ta dumama ta Dora ruwan tea baqi Wanda yaji citta da kanun fari da girfa Sai bakwai da wani Abu ta gama ya shiga tai wanka ta fito umma rabi ce ta fito ta fara gidan ita kuma, umma ina kwana?? Cewar amatou dake rataya jaka abayanta Basu tashi ba ko??? Umma tace babu Wanda ya tashi ai kamar maamaa tace Basu da aji sai sha daya, ok to shikenan ni na fita ta fada tana kallon baqin agogo Dake hannunta sosai tayi kyau doguwar Riga ta saka A shape ta dora madaidaicin mayafi tun daga saman Kai Wanda bata sa dan kwali ba hula kawai ta saka wadda zata dace da rigar Dan dan kwali takura mana yake, ficewa tai daga gidan bayan ta karanto addu'ar fita sai da ta gangara ta fita daga laying sannan ta samu adaidaita SAHU ya dauketa suka tafi, da amma ta fara cin karo a qofar department dinsu, da murna ta tareta Dan tayi missing dinta sai yau ta dawo, ke saida lectures suka fara nisa sannan zaki dawo dariya kawai ammaa tai, Ina babyna ?? Yau dai wlh zaki kaini gidanku na ganta tunda kinqi zuwa da ITA sister maamaa ta turamin hotunanta sosai amma yau dai sai naje na ganta, murmushi kawai amatou tai tace to Allah ya kaimu, Ameen ammaa tace, sai Kuma ta kalli amatou tace Amina nikam sabon VCn Nan kamar nasan sunan amma na rasa a ina dauke Kai amatou tayi tace Zaki iya saninshi mana ammaa tace sunan shi sounds so familiar Amma na manta Ina na sanshi, ni kinga zo mu shige class mu nema seat a farko, tana fadin haka ta jata suka shige class SUNA gama lectures din farko sun fito taga Kiran dr Abdullahi tsaki taja tana dafe goshi ita Bata ga amfanin Kiran Nan ba kullum suna cikin fada Amma baya taba zuciya yace yana so ya zo gidansu Dan bayaso suna haduwa a school anma ta hana shi address dinta shikuma yace sai ya nemo, ammaa tace yadai?? Ta kalleta tace wlh na tsani baqin naci ammaa Dr abdullahin nan ya takuramin Amma tace kawo wayarki kiga kina da data ?? Ena da ita ta week nayi sub Amma tace wannan bazatai mana ba connecting wifi tayi da wayarta downloading true caller tai bayan tayi blocking dinshi a wayar tata tace Kinga ko canja number yyi Zaki San shine ya kiraki ba sai kin daga ba yanzu fa mun rabushi ba lecture yake mana ba, kawaii dai fatana Allah yasa kar ya dawo Miki da physiologyn last semester, amatou tace wlh tsorona knan shiyyasa nake tunanin ko na lallabashi naga result dina kafin na toshe duk wata hanya da zai sameni, ammaa tace ai ba'a dole Kuma inhar bazai lallabaki ba sbd Yana sonki ni banga dalilin takura Miki ba Allah yasa ma ba sha'awarki take ba wlh, kallonta amatou tai tace kamar ya?? Wlh amatou bakisan wasu lecturers dinnan ba some of them suna da kirki Amma wasunsu?? Wlh they are after nothing but ur body bare yanda kike da kyannan tubarkallah Masha Allah gani yake shi lecturernki ne ya nuna yana sanki ta qarfi yyi miki dole sannan ya fara nuna miki qudurinshi, da ya San kin taba aure wlh ni nasan da tuni ya fitar miki da manufarshi kallon ammaa kawai take tana so taqi yadda da me take cewa Amma me?? Wasu kallo da yake mata lokuta da Dan dama yana dawo mata wani lokacin Abu baya kawo Maka a ranka sai an dan baka hint Bata manta ba bayan conference dinnan yake tambayarta wace Farrah ?? Cemai kawai tai qanwar tace dukda kawaii Bata so ya san rayuwarta ne kawaii ta qi fada Mai gsky Amma daga alamu Hakan yyi amfani, Allah ya kyauta to, Ammaa tace Ameen sai ki kula sosai wlh masu mugun abunnan idan suka Saka Abu a ransu to wlh sai sun cin mashi indai ba Allah NE ya kareka ba, cafeteria suka je suka karbi ruwa da lemo suka juyo Maryam suka hadu da ita akan hanya, amatou ta kalleta tace harkin fito?? Tayi dariya bayan sun gaisa da ammaa tace ina fa?? Tun dazu na fito wai lectures din ta koma 9 kina fitowa aka kirani, to kinci abinci ko?? Gyada Kai tayi tace qishirwa nakeji na fito siya sauke jakar bayanta tayi ta dauko pure water guda biyu ta miqa mata ungo ki koma class, anty Mimi to kefa?? Akwai guda Daya a ciki ya isheni ta fadi haka tana zuge jakar, AMINA suka ji daga gefensu varandar da ta sadaka da admin block dinsuce a wajan Dr abdullahi ne a tsaye Yana kallonsu tuntuni yana Kuma Jin me suke cewa, Maryam ganin sabon lecturer dinsu yasa tace Ina kwana sir Ammaa ma tagaidashi cike da Jin haushinshi, Amatou qin gaisar da shi tai kawaii ta wayance da cewa na'am sir, ki sameni a office din yanzu gabanga sosai ya Fadi ganin Bai Dade da kiranta ba taqi dagawa ajiyar zuciya ta sauke tace ku tafi zan taho ammaa tace a a wlh muje na tsaya a bakin office din ai bazai san na rakoki ba kawai idan naji ba dai dai ba zan danno kai cikin office din amatou tace karki damu ammaa insha Allah babu abunda zai iya min, maryam taa kallesu da confusion tace me yake faruwa anty Mimi?? Laifi kika Mai?? Girgiza mata kai kawai tai kiyi wucewarki class, to me kika masa ?? Naga duk kin wani tsorata, ?? Amatou tace nace ki wucewarki class ko?? Maryam tace to wlh sai dai idan anty ammaa zata raka ki indai bazata rakaki ba to sai na biki, yanda ta fada da stubborness yasa amatou ta juya kawai tai gaba bin bayanta sukai suka tsaya baya baya da qofar office din, amatou ta shiga office din Yana zaune akan sofar cikin office din GABA Daya amatou sai taji ta qara tsorata da zancen amatou tace sir gani uhnm na ganki ai, sai Kuma ya nuna mata kujera ganin nesa dashi take yasa ta zauna a darare yace Ina wayarki?? Allah ya rufa mata asiri wayar tana jaka hakan yasa tace tana wajan ammaa kuma tana class wacece ammaa?? Tace qawata Aisha Usman Maruta, gyada mata kai yyi sannan yace meyasa bakya daga kirana ?? Sunkuyar da kai tayi tace ni banga kiran ba wayar tawa tana gun ammaa yace ok ita ta sakani a blacklist knan da sauri amatou tace black list Kuma yace eh tace a a sai DAI ko amfani take da wayar Shuru yyi Yana kallonta kana ganin ta kasan a tsorace take yace meyasa bakison ki saki jiki da ni?? Wasa kawaii take da hannunta dake kan cinya lalle ne a hannunta dukda DAI ya Dan fara kodewa Amma yyi bala'in ma farin hannunta kyau kallon hannun yake sosai Jin yyi Shuru ta dago ta kalleshi Taga Inda yake kallo tusa hannun tayi a cikin mayafinta tabe Baki yyi ni zakiyi ma rowar hannunki?? Karki damu bama hannu ba komai naki zai dawo nawa qarewa banza tai Mai kamar bata ji me yake cewa ba, shikam bayaso a makarantar a gane halinshi Amma sosai yake kwadayinta Bai Dade da samun offer din ba da a asibiti yake aiki ya Maida patients,relatives da Kuma staffs Wanda suka bada kansu abokan hutawarshi Hakan yasa aka koreshi dake Yana da hanya sosai yasa ya samu lecturing anan and he is trying his best to hide his true colour, har ya samu wata yar harka ya level 400 foculty of agriculture tana rage Mai zafi dukda dai ita baqa ce shi Kuma taste dinshi na farar mace ne, Amma baya barin bati tunda ita ta kawo kanta, abunda yasa yake qara lallaba amatou ganin yanda take da nutsuwa sosai bayaso yayi garaje Dan yasan zai iya rasata Bude kofar da Akai yasa duk suka Kalli qofa jiki na rawa Dr abdullahi ya miqe yace welcome sir, ya fada Yana miqa Mai hannu tunda ya shigo idanunshi ke kanta yana hango yanayinta koba komai yanzu ya fara karantar body language dinta, kallonta Dr abdullahi yyi yace na sallameki amina, miqewa tai tace to na gode sir har zata wuce sai Kuma ta Dan kalleshi tace Ina kwana gyada mata Kai yyi Kawai tayi ta kama hanya ta fice ammaa da maamaa ta Gani a gefe suna tsaye Maryam tace alhamdulillah tana dariya amatou tace me kuke Yi anan ?? Maryam tace yo new VC ne yaxo wucewa muka gaidashi yake tambayata me muke anan ni Kam nace Mai ke muke Jira tun dazu amatou ta harareta tace ai kin kyauta Amma zatai magana sai gashi ya fito kallonta yyi fiercely sannan ya juya ya tafi maryam ta riqe haba magana fal ranta juyawa Suma sukai sukai wucewarsu......




Mrs maan🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: *Amatou*🧕🏻
(The single mother)
14
Shuru amatou tai sai Kuma tace na'am?? Bata gane me yake nufi ba kwata kwata, yace nace sannunki yar dariya kawai tai suka cigaba da Hira, a satin ya shirya ya tafi Katsina sbd kiran da mama tai mishi, sallama yyi a parlorn mutanen ciki suka amsa mishi hade fuska yyi tamau ganin cousins dinshi har su hudu said Kuma autarsu raudah da mama, qarasawa yyi cikin parlorn ya durqusa gefen mama yace barka da hutawa maa, Muhammad ka dawo ya hanya?? Yanda take fara'a ne kwata kwata me Gane mishi ba amsa gaisuwar su yyi lokaci daya ya dauke Kai kallon daya daga cikin yan matan tayi tace Aisha dauko Mai ruwa maqewa tai ta nufi kitchen raudah sai Ido take musu akan su tashi su tafi Amma sunqi ganewa Hakan yasa ita ta miqe da sauri zulaihat itama ta miqe ganin Hakan yasa sauran biyun suka miqe suka bi bayansu Suna zuwa daki zulaihat ta tabe Baki tace har yanzu Yaya Hammad Bai canja Hali ba wannan mugun halin Yana nan irinsu ne mace qarama take gwara kansu dariya dukkansu suka saka suka cigaba da hirarsu sama sama suna taba waya, har abinci Aisha ta kawo Mai Dan shiryosu tai a tray ta ajiye gabanshi tace na sa Maka ruwan Yaya Hammad girgiza Kai yyi ba tare da ya kalleta ba yace zan zuba to tace sannan ta miqe ta wuce dakinsu, ya Kalli maman ya maa ina yaran gidan?? Tace gasunan ka koresu Dan takuna fuska yyi yace mama wannan zagada zagadan yammatan zance ma Yara dariya maman tayi tace Ashe kasan Yan matane dama kiransu nai naji ko akwai taste din naka a waennan tunda ka ce rubabbu gwaggo zata zaba maka a maska to ga na cikin katsina,yace mama wannan zancen Kuma?? Naga kince 6months, eh nace 6months kawai dai nayi tunanin tsoron matan kake ne shiyyasa na kawo Maka su dukda Basu San meyasa nace suzo ba, Amma duk wadda ka nuna a cikinsu nasan babu wadda zatayi musu idan muka nema aurenta, rasa inda zaisa kanshi yyi yace maa nace ai zan kawo miki Dan Allah ki bar wannan zancen, tace ni banga alamar zaka kawomin ba hammad ko a can Abujan take?? Kin manta na dawo Zaria ?? A Zaria take ni ban San ya zan fada mata ba a school din take murmushi maman ta saka yar wane gari ce,?? Yace kamar dai yar Kano ce mama ni fa ba yaro bane Dan Allah ki bar komai a hannuna insha Allah kafin 6months din zanje gurin uncle , to Allah yasa Amma ga na gida ai baka tafi waje ba, karki damu insha Allah Zaki sota idan kika ganta batai Miki ba zan NEMA a family din Amma nidai tamin, a a ni ba ruwana indai kana sonta bani da matsala kawaii DAI na gida nai maka sha'awa Aisha dake labe tana Jin komai ta juya tai dakinsu ranta na quna ita take yawan zuwa gidan Amma sai lokaci lokaci take Katarin samunshi a gidan duk wasu hidimominshi ita take karbewa tayi tasan yanzu ma shiyyasa maman ta Saka ta tana bala'in sonshi Amma Bata tsammanin zata zubda ajinta gurin fada mai kamewarshi baya damunta Dan tasan sai dai idan batayi niyya ba, daki ta shige Bata kula kowa ba ta dauki wayarta ta Koma qasa kan Capet ta jefa pillow ta kwanta bayan tayi la'asar ta shiga wanka fitowa tai yawancin su farare ne kwaya Daya CE a cikinsu me Dan duhu ita ma ba wai baqa bace, feshe jikinta da turare tai sannan ta hau shafa manta me kyau da tsada Wanda shi yake qara mata haske ko powder bata Saka ba sai ta goge fuskar da towel Nan da nan tai wani irin fresh da haske tender care ta shafa a bakin Bata Saka kwalli Hakan yasa ta miqe side din wardrobe din da ta shirya kayanta Dan zata Dan kwana biyu Dan daganan zata na zuwa school, jeans ta dauko blue sannan ta dauko pink top da pink touband sakawa tayi kafin kice meye wannan tayi kyau Dan ba Wani jiki gareta ba fesa ma kayan nata turare sannan ya dau chewinggum a jakarta ta jefa a baki sannan ta fice parlor tunda ta fito maman take kallonta sai taji bata ji dadi ba ko ba komai hammad ba muharraminta bane Hakan yasa tana qarasowa maman tace yammatana anyi kyau murmushi kawai aishan tayi ko irin kunyar Nan babu, sai mama tace Amma Aisha kayan nan basu fito da jikinki ba kuwa ?? Naga Maza suna shigowa ko?? Dariyar yaqe Aisha tasa tace maa kinga rigar bata matseni ba gyada Kai kawaii tai Amma bata tunanin zatai tolerating wata improper behaviour a gidanta suje DAI can gidan iyayensu idan zasu barsu suyi sai suyi Amma Banda nan ta barshi a matsayin sai ta qara yin na biyu Hammad NE ya shigo yasan da cewa da wata tana wajan Kuma yasan cikin yammatan gidannan Bai kalleta ba straight mamanshi yake kallo, bayan sun gaisa yace mama hura nake so nasha,nuna mai jug din dake gefenshi tace ga saura nan shiyyasa na rage maka na San zaka nema, miqewa Aisha tayi tace maa bari na dama mai tun da naga akwai a fridge, Jin be ce komai ba yasa maman tace to shikenan ma ya samu ta shan dare , miqewa tai ta nufi kitchen jujjuyawa yai ganin babu dan aike yasa ya miqe ya nufi kitchen a gaban fridge ya sameta baiko kalleta ba ya nufi inda cups suke dauka yyi yazo fita tace Yaya Hammad kaga wannan zata isheka?? Bai amsata ba dukda batada tabbacin ko yaji ko bai jiba, Hakan yasa ta cigaba da abunda take fura me Rai da lafiya ta dama da youghourt me kyau furar taji qanqara, Wani jug din ta damu ta wanke shi ta juye a ciki sannan ta fito lokacin har ya kusa shanye na cikin cup din Daya zuba qarasawa tai ta sunkuya ta ajiye mai jug din da sauri ya canja position din Idanunshi Dan Yana hango Yan miri mirin nonuwanta da suke cikin push up bra, a tsarge ta miqe Dan kwata kwata ta manta ma da yanayin rigarta Dan kallonshi tayi taga shan furarshi yake hankali kwance haushi taji ya kamata gaba Daya nonuwan nata sunqi daukar magani yanzu da sun qara girma ai da yanxu zata San lagonshi, miqewa taga yyi ya Kalli mama yace nifa mama wannan da nasha ta isheni ba gidannan zan kwana bama zanje gidan Abdurrahman insha Allah daga can zan wuce gidan baba aqibu, riqe Baki kawai mama tai Aisha ta juya ta dauki wayarta fuu ta wuce ciki mama tace kai yanxu ai sai kace mata bazaka sha ba Amma yarinya ta hado Maka Abu kace bazaka Sha ba?? Dage kafada yyi yace ni ai ban sata ba mama niyya tayi Nima Kuma banyi niyyar Sha na dama Yana fadin haka yace zan Dan fita mama Amma zan dawo da daddare insha Allah, ba yadda ta iya Hakan yasa tace to sai ka dawo fita yyi yanajin gidan GABA Daya ya isheshi, MOTA yaja yana dialing numbern amatou harta gama ringing ba'a daga ba yaso ya ajiye har sai ta kirashi yaji bazai iya ba Hakan yasa ya qara dialing numbern still dai ba'a daga ba, numbern maamaa ya lalubo yai dialing still dai ba'a daga gangarawa yyi gefen titi, qara dialing numbern Maryam yyi still no answer deep in side him yaji Wani irin rashin kwanciyar hankali ya fara kamashi rufe idanunshi yai yana ta tunani to ko dai suna saloon ?? Basuji ba sanda ya kira? Yau friday yasan

Please Login or Register in order to submit comment