Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abun ya tsaya mata arai , Abu taji a hannunta, kallon hannuntai taga kudin Daya bata ne qirgasu tai 20k ne ajiye su tai a qasan pillow Bata tsammanin zatai amfani dashi zata Maida Mai abunshi miqewa tai ta shi wanka ita kadai sai ta zabura Hakan yasa ta gaggauta yin wankan ta dauro alwala ta fito Mai kawai ta shafa ta Saka riga marar nauyi ta fito parlor ta zauna tana jiran a tada sallah, kallonta umma Rabi tayi tace amatullahi Ina so naje mashi kwanan nan hankalina ya karkata kusan shekarata uku banje ba kallonta tai da sauri sai Kuma a sanyaye ta kauda Kai tace to umma Rabi ai kinyi qoqari ma wlh yaushe kike son tafiya da dai wannan satin nake son tafiya umma Rabi ta fada tasan bazasu ji dadin tafiyarta ba Amma tana son taje din ta gano gida sai Kuma tace kuma ya kamata kuje ku gano Yan uwa Suma su ganku tunda kuka daukoni fa Baku qara komawa miqewa amatou tai Jin ana Kiran sallah tace zamuje insha Allah umma ba yanxu ba sai Nan gaba insha Allah zamuje mu dukka Taga haka ta wuce daki ta shimfida sallaya ta da hijab ta tada sallah Maryam da Farrah suna dakinta suna game a wayarta tuntuni Suma Jin ana Kiran sallah yasa ta miqe tayo alwala a toilet din parlor taima Farrah ma Dan dakinta ba toilet Hakan, washe gari da wuri suka fita wajan 8 suna shiga school kowa yai hanya department dinshi sai Kuma Maryam ta biyota da sauri tace anty Mimi juyowa tai qarasawa tai ta ce kudin hannuna ya qare bani da kudi a hannuna sauke jakar bayanta tai ta zuge zip din jakarta ta zari 2k cikin 5k din da jiya bayan ta tashi ta cire a acc. ta Bata tace kici abinci karki zauna da yunwa gyada mata Kai maryam tayi ta juya bawai Dan ta jita ba wani zubin tana riqe yunwarta har taje gida sannan taci abinci shiyyasa ulcer take Bata wahala idan ta tashi kullum fadan amatou knan ita amatou zata ci abinci zata Siya normal sai dai idan Bata da isashen kudi a hannunta Amma ta Bata wasa da cikinta Dan Bata da jimirin yunwa kam, wucewa tai department dinsu tana tunanin doctor abdullahi ne yake da lectures kwanan Nan ya matsa mata bini bini sai ya kirata office yana Janta da hira abun haushi yake Bata Hakan yasa ta shiga ta qofar baya ta nemi seat din baya ta zauna ba dadewa kuwa ya shigo ya fara lectures yanata wurga Ido yaga ta inda zai ganta Amma be gano ta ba sai daga BAYA can ya hangota a baya ai kuwa bini bini ya Kalli wajan Yan class din har sun fara dago shi ilai kuwa bayan fitarshi ya kira class president dinsu suna shiga office din yace mishi Dan Allah Amina zaka Dan Nemo min kace taxo ina da saqon da zan bata Shuru president din yai sai kuma yace to bari na kirata a waya yawwa ban contact din nata ma yafi sauqi ma, ba Dan ran president din yaso ba ya karanta Mai numbern sannan ya Mai sallama ya fice a qofar class ya tadda amatou tsaye da Amma sai wasu few Yan class dinsu Wanda daga baya bayannan suka fara kula su amatou su Basu san ma Bason tarkacen qawaye take ba gata sukai mata da basa kulata yanzun ma ba wani sake jiki tai ba qarasawa yai yace Amina can I talk to you please?? Kallonshi amatou tai sannan tace to gefe suka matsa sannan ya Sosa goshinshi yace na Dan Miki laifi....kafin ya qara cewa komai kira ya shigo wayarta kallon wayar take ganin sabuwar number yasa ta sata a silent sannan tace ina jinka yace no pick up the call I think doc abdullahi ne yanxu yace na kira masa ke nace bari na kiraki a waya shine yace na bashi numbernki, ba yadda zanyi shiyyasa na bashi ganin yanda yake magana a Dame yasa ta kalleshi tace karka wani damu dama nasan ko baka bashi ba nasan watarana zai tambaya,tana gama fading haka ta juya tace sai anjima Karka damu I will handle it,ammm Amina juyowa tai ta kalleshi yace please be careful gyada Mai Kai tai tayi murmushi tace insha Allah sannan ya wuce wajan su amma,,,,Ta bangaren Dr. Hammad kuwa wajan 10 ya baro Kaduna Dan sai yayi kusan 5days kafin ya koma abuja bayan ya iso zaria ya nufi unguwarsu Farrah wannan karan kwankwasa gidan yai ba dadewa umma rabi ta leqo ganin shine suka gaisa yace farrah yaxo Gani babu musu tace to bari na kawo maka ita sannan ta juya cikin gida Farrah wadda tai ma wankaya tana zaune tana Shan tea tace kin gama Shan tea din?? Girgiza mata Kai tai, to ki gama kije wannan mutumin me mota ne yazo da sauri ya miqe tace uncle bari naje na qoshi kafin umma rabi tace komai ta fice daga parlorn tai waje........



Mrs Maan 🥰
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: *~AMATOU~* 🧕🏻
(The_single_mother)

7.
Babu jimawa suka fice daga gidan tanajin tashin motarshi ta dafa goshi can ta miqe ta debo littattafanta ta hau karatu Dan test suke dashi sati me shigowa , lokacin da Farrah suka dawo kusan 11 yau ice cream kawai ya sai mata ya dawo da ita, bayan ya sauke ta a bakin qofa yace turo min miminki gyada Mai Kai tayi tace tam byeee daga mata hannu YAI sai kuma ya miqe ya Kalli agogon hannunshi 1 zaije sallar juma'a can har ya fidda ran zata fito sai gata Koda yaushe she is looking so young and cute gashin fuskarta wanda kana ganinshi sbd hular hijab din Bata matseta sosai ba normal over sized bathroom slippers ne a qafarta dark blue ne a qafarta Hakan ya qara haska fatarta, kallonshi tai tace gani, dauke kai YAI sai ya hade rai yace Baki da Wanda zai miki fada ne ?? Kallonshi tai da sauri tace ban gane ba yace ban sani ba akan me zaki zauna hayaniya da maza a qofar gida ?? Dauke Kai tayi tana rolling idanu Ashe be manta ba tace kamawa tai ai kuma ni ban tabayi ba, maqalewa abunda yake so ya fada ya maqale bakinshi ya bushi the way she roll her eyes is something that he will pay anything Dan ta qara yi, kallonta kawaii yake sai da suka hada ido sannan ya dake yace to karki kuskura ki qara ba mutuncinki bane kome wani yai miki karki kulashi, ciki ciki tace to Jin ta amsa yace meyasa kuke zaune ku kadai?? Ba namiji and naji mum dinku ta tafi Katsina dukda Dan ya tabbatar cewa ba mamansun bace yasa ya Fadi haka dan baiga alamun cewa mahaifiyarsu ce ba,sunkuyar da Kai tayi tace me kake son ji?? Yace so nake naji dalilin da yasa kuke kwana daga ku sai yarinya did you think it is safe for you to sleep alone ?? Yanzu inda yake da security ma ya aka qare ballanta ne ku?? Evil people are everywhere now adays kallonshi tai cikin sanyin murya tace to da wa kake so muna kwana ??? Umma Rabi is our mum's relative and ta tafi ganin gida so no one left except us, rasa me zaice yayi Dan abun yazo Mai a bazata, sai Kuma yace Ina mum din Baku to??? Kallonshi kawaii take Shima haka sai yaga kwalla ta cika idanunta, Sosa goshinshi yai a ranshi yace did I messed up??? Dauke Kai tai tace bata nan, we are all alone, Bai qara cewa komai ba Dan yaga kamar nema yake ya ballo liqi, sai Kuma yace sorry but you have to be extra careful yaushe zata dawo?? Sai tayi 2weeks or so bandai sani ba, alright you should go home and Kuna rufe gida is better a kwankwasa ku tambaya Waye sannan ku bude, Yana fadin haka ya Dan duqa ya zare wayar hannunta ya Saka numbernshi sannan YAI dialing luckily akwai kati yana jin kiran ya shiga wayarshi ya katse sannan yai saving mata da Dr Hammad ya miqa mata wayar yace zanna kiran farrah saura karki Bata Yana fadin haka ya juya ya shige mota, binshi tayi da kallo har yaja motar saida suka hada Ido sannan ta juya ta shiga gida sai taji maganganunshi ya sa mata tsoro jam lock ta Saka sannan ta shige gida, after 2days suna zaune a parlorn babu wuta sun kunna maganin sauro sai lantern ta haske parlorn, amatou na karatu su Farrah da Maryam kuma suna kallo a waya, wayar amatou CE tai qara kallon wayar tayi Tama dauka doc abdullahi ne sai taga suna daban kamar baxata daga ba sai kuma ya janyo wayar a ta daga ta Kai wayar kunne can qasa yai sallama amsawa tai sai tayi shuru, deeply yace give her the phone, rolling idanunta tayi ko Dan pleading dinnan ma babu,ba tace komai ba tace Farrah take ta fada tana miqa ma Farrah wayar juyowa sukai ita da Maryam tasowa tai ta karbi wayar ta Kalli screen din wayar Bata san me aka rubuta ba Amma tasan kirane, karawa tai a kunne tace hello?? helloooo angel how are you?? Tsalle tasa tace uncle kafin kace me sai kyalkyala dariya take Maryam takalleta tace wane uncle din?? Tabe Baki tai tace ki tambayeta mana ko Kuma ki karbi wayar nan da nan Maryam ta dago waye murmushi tayi sai Kuma ya matsa KUSA da ita tace anty Mimi yaushe ya karbi numbernki?? Da sauri ta juyo ta galla mata harara tace ban sani ba din dariya Maryam ta saka, ji tai Farrah na fadin anty maamaa gata nan sai Kuma tace toh ta miqa ma Maryam wayar, karba tai tayi sallama, gaidashi tai, miqewa amatu tai ta shige daki karkade shimfida tai ta kwanta already tayi wanka ji tai wata kalar gajiya na saukar mata Nan da nan kasala ta mamaye ya kafin kace me idonta ya fara rufewa bacci ya dauketa, bata Dade da fara bacci ba taji Farrah na tashinta bude nannauyan idanunta tai cikin muryar bacci tace ya Akai Farrah?? Kizo ki kwanta dare ya fara yi ungo Mimi yace in kawo Miki wayar da mamaki tace waye ?? Karba tai taga haryanzu waya suke sai kuma tarin miscalls da aka Tara mata dubawa tai Taga waye wannan as expected kuwa Dr abdullahi ne sharewa tai tasan rigima ce zasuyi ta tunda yaji tana waya, Kara wayar tai cikin muryar bacci tace hello?? A bazata ya lumshe Ido sannan yace uhmm bakya gaisuwa ko ?? Ba tare da damuwa ba tace inayi ma na, ban ga alama ba, tabe bakiyi tayi tace to Dan bacci take ji while shikam harga Allah godiya kawai zai mata amma sai yaji ya kasa yi balle har ya kashe wayar
Shuru duk sukayi Babu Mai cewa Wani abu while itakam tuni ta koma bacci numfashinta kawaii yakeji kashe wayar yai yayi juyi akan gado yana miqa, daga haka kullum sai ya kirata yace ta bama Farrah wani lokacin farrahn tayi bacci sai su bige da Hira dukda dai sama sama ma hirar tasu Amma sai Sufi awa Wani lokacin har sai amatou tayi bacci Dan indai zata Saka haqarqarinta a kan gado to nan da nan zata ji bacci, fadan da sukayi da Dr abdullahi kuwa Babu kalar fadan da basuyi ba yanxu ta daina tsoronshi ta mugun rainashi, ranar da ya kirata a class tai mai banza be qara marmarin kiranta a bainar jama'a ba tasha masifa ranar acewarshi Dan ya nuna yana sonta ne shine zatai Mai wannan mummunan rainin duk fadan da yake ko a jikinta dan kamar yana magana da dutse haka tai mai tun daga nan yai zuciya ya Daina kulata sosai Amma idan rashin zuciyarshin ya juyo sai yai ta kiranta a waya taqi dagawa bata taba samun carry over ba but tasan tabbas wannan semester sai ta samu a physiology ko a jikinta dukda dai tasan baxata taba Jin dadi ba amma Bata tsammanin zai dameta tunda ba akanta aka fara ba, wasa wasa exams dinsu tazo suka fara exams Wanda ba dadewa bayannan Suma su Maryam suka fara,,,,bangaren doctor Hammad kuwa yakan Dade Bai je gida ba saboda indai yaje gida to Basu da zance sai aure barin mamanshi da kakanninshi sun sashi a gaba sosai ita mamanshi tayi tsammanin ma ko aljana ce ta aureshi Shima Kuma sai da aka fada yake tunanin ko dai gsky ne ?? Dan bazai iya tuna lokacin da yaji sha'awar mace Amma kwanan nan is different yana Dan amsa kida kadan, har abun Yana Dan bashi mamaki Dan baisan dalilin hakan ba, hameeda kuwa class mate dinshi da ta bala'in nace Mai yar jigawa ce shi bata taba Mai ba Dan bata cikin matan dayake so Kuma bata tsarinshi baida burin auren babbar mace me shekaru sama da talatin ita kuwa ta kusa 34 years ita take nace mai Amma Bai Santa tana da tarbiyya da class shi dinne dai kawai Bata Mai ba da naci da komai tasan Huda lokacin suna school yana son Yara Dan babu yara gidansu so duk inda yaro yake Yana nan irin yan qasa da 10years dinnan burgeshi suke duk randa qannenshi suka je gida Shima Kuma yaje to haka zasu daddane shi ta ko Ina harda me zama Saman wuyanshi,,, ba ya so haka ya shirya ya tafi katsina Dan Yana so yaje ya gaida mamanshi tunda sai cigiyar yaushe zaizo take a waya, Hakan yasa ya shirya Amma Saida ya tsaya ta Zaria lokacin su amatu already sun gama exams sai su Maryam tsaraba sosai ya kaima Farrah sai da yaga idan ya sake zeyi dare sannan ya dauki hanyar Katsina Dan Babu nisa, dabda magariba ya isa cikin Katsina 6:35pm yaje gaban gate dinsu kana ganin gidan tsohon Gini ne irin na masu kudi Amma ya Dade, danna kai yyi a gate din bayan an bude mai, horn kawaii YAI ma matashin da ya bude Mai gate din ya wuce can yai parking Dan qaton tsakar gidane sai inda Kai niyyar parking, sallama yai a qofar parlorn hannunshi riqe da ledar yalo,data da Kuma guava da yai ma mamanshi tsaraba Dan yasan tana sansu Bata parlorn ajiye ledar yayi kafin ya shige toilet din parlorn ya dauro alwala, hayaniyar yara ya Jiyo yasan sun dawo daga islamiyya kanan yana fitowa kuwa suka sa ihu sukai kanshi da gudu sun kusa su biyar Saida suka kusa kadashi, wayyo ku bini a hankali mana, dariya suka sa ganin yanda yakeyi da fuska suna qara dane sa, uncle yau ka dawo ?? Bamu ga motar ka ba lakuce hanci ilham yai wadda take yar qanwar shi ce itama yace idonku dai Bai Gani Amma ni mota ta tana waje wadda take yar babbar cikinsu tace kuwa bamu ganta baa, oya kuje kuyi sallah an kira sallah nima masallaci zanje, idan na dawo ma gaisa da gudu sukai can cikin gida suna Kiran mama, masallacin dake qofar gidansu ya wuce sai da Akai isha'i sannan ya shigo cikin gida lokacin mamanshin tana zaune da jikokinta sai yar autarsu a parlourn wadda ita kadai ce batai aure ba, miqewa sukai da murna sukai wajanshi naturally yara na bala'in sonshi, zama YAI a cikin parlorn yana amsa gaisuwa Raudah dake gaidashi, Babu wasa a tsakaninshi da kannenshi amma yanda Yara ke mai har mamaki abun ke ba qannenshi, to ku tsaya na gaisheda mamana mana ihu suka sa suna fadin mamansu ce ba tashi, harararshi maman tai tana musu tariya tace ni banayin maman tunda kaqi kawomin suruka, shafa kanshi yai ciki ciki yace mama gaban yarane fa, raudah na jin haka tasan da ita yake Hakan yasa sum sum ta miqe ta wuce dakinta bakinta alekum, ka korar min yar auta da son girmanka bayan kaqi girman, yar dariya yyi nidai inawuni mama amsawa tai tasan baison maganar bayan sun gaisa tasa aka kawo Mai abinci Dan Taga alamun yunwa a tattare dashi waajan 9 ya kora yaran su kwanta a cewarshi bega abunda yaro yakeyi ba har da zai wuce 9 Bai kwanta ba, kallonshi maman nashi tai maganar da zatai mai me nauyi ce amma Bata tunanin nauyinta zai hana ta tambayarshi Yana Jin idanunta akanshi yasan da magana Amma Bai ce komai ba, Muhammad inaso ka fadamin gsky kallonta ya Sosa goshi ya ce to mama , ka fadamin gsky ko bazaka iya kwanciyar aure bane yasa kaqi yin aure Dan ni banga alamun wasu aljanu ba tunda Nasha Maka turaren su amma banga alamunsu ba, ganin da gaske sarkewar yayi Dan sai tari yake yasa tai Shuru tana kallonshi fura yake sha maganarta ce ta sarqeshi ruwa yake ta kwankwada kafin kace me idanunshi yai ja maganar tazo Mai a bazata sosai kunyace tai bala'in rufeshi ya rasa inda zaisa kanshi Amma bazaka taba ganewa ba Banda mamanshi ce Babu Wanda zai fahimci hakan girgiza Kai kawai yake Amma ya kasa magana miqewa tai ta Isa bayanshi ta fara bubbuga Mai a hankali ya fara lafawa, sai da ya Dena tarin GABA Daya sannan ta tafi ta zauna yana addu'ar Allah yasa ta bar zancen knan amma addu'arshi bata ci ba Jin tambayar data jeho mai, " inajinka Muhammad Kai min bayani sai naji daga Ina zamu fara neman magani girgiza Kai yayi ba tare da ya kalleta ba yace ko Daya mama far duba wacca zan kawo Miki din insha Allah ya fada ne kawai Dan ta rabu dashi Amma Bai da kowa a mind dinshi, tace indai matace ni baka da matsala idan dai matar aurence akwai su dayawa a familyna ko na babanku sai Wanda ranka ya zaba ga asiya nan yanda take maka hidima nasan idan aka ce ta aureka tsaff zata yarda yace yo mama wannan yarinyar nide ki barta ni Bata min ba ki bari zan zabo Miki taste Dina Kuma nasan Zaki so abunda nake so gyada Kai tayi tace last chance zan baka daga nan zuwa qarshen shekara kai de ba yaro bane balle ka ce zaka zauna doguwar soyayya , baka da wannan lokacin zaro ido yai sai kuma yace qarshen shekara kuma mama?? wata uku fa knan kiyi haquri ki ban 6months ko 9 baza'a Bada ba karka wuce 6 months sai yanxu na fuskanci Ashe abun naka harda iskanci, murmushi yai yana sosa goshi, Jin yanda ya cigaba da MITA ace mutum ya doshi shekara arba'in Amma baya tunanin aure kiyi haquri mamana zan kawo miki yarinya me hankali insha Allah......



Mrs Maan🥰🙌🏻



Mrs Maan
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: : 6.
~*AMATOU*~
(the_single_mother)

Da gudu ta qarasa wajanshi ya dagata sama tana dariya, yace hello cutie dariya kawai take oya zo muje yawo yana fadin haka yasm sata a seat din BAYA ya shiga suka bar unguwar zuwa cikin Kaduna da ita yaita yawo da ita sai can daga baya ya he gidan yayanshi Wanda sai yai zuwa 5 befi yaje sau Daya ba, parking yai a harabar gidan da yake qato kana ganinshi kasan kudi ya zauna musu sallama door bell ya danna few minutes aka bude gaidashi wadda ta Bude din tayi bayan taja baya yar gidan yayanshin wadda suke kira da huda Bata Fi 12years ba Wanda itace autar gidan ta kwalla ihu tana Kiran uncle Dane wa tai jikinshi gata irin tuluqa tuluqan yarannan ne kamar kajin tura a tsorace Farrah wadda yake riqe da hannunta koma baya Dan ta tsorata da ihun, wai huda so kike ki balla ni?? Tace uncle yaushe kazo ?? Ni bazan ballaka ba shine ka daina zuwa ganina ko?? Ba komai nama fasa komawa gidan naka tunda ka Daina sona Kuma ko waya anty hamida ta daina min ta fada tana tabe Baki kamar zatai kuka, neman guri yayi Yana zama bayan ya zaunar da Farrah ganin ta tsorata yace Kinga kin tsoratar da yarinya sai a lokacin huda ta kula da ita, durqusawa tai tace who is she uncu Hammad?? Murmushi yai yace a friend of mine kallonshi tai tace yar friend Dinka ce ?? Ya girgixa Kai yai yace bakiji ba ?? She is my friend oya jeki kiramin mamanki mu gaisa zan wuce daddynku fa Yana nan?? Girgiza Kai tayi tace yaje Katsina amma yau zai dawo insha Allah, ok jeki kiramin ita miqewa tai tace idan na dawo zaka fadamin ina ka SAMO cute angel haka tana fadin haka ta haura sama wajan mamanta ta sanar mata ta sauko babi dadewa maman tasu ta sauko da fara'arta tana fadin yau tuzuru ne a gidan namu knan murmushi kawaii yai yace maman Yara barka da gida, dariya tai tace barka dai, Masha Allah Ina ka samo yarinya haka Masha Allah kaqi kayi aure balle ka haihu sai aukin kwashe kwashen yara zo yammata ya sunanki ?? Ta fada tana kallon Farrah Dake Dan maqale da hannunshi, a hankali yace jeki gaisheta Farrah a hankali Farrah ta tafi tace Ina kwana dariya matar tai bayan ta riqo ta tace Ina mamanki?? Tace tana gida,, sai bayan la'asar suka nufo Zaria a lokacin ran amatullahi yakai maqura wajan Maci idanun Nan sun kada sunyi jawur, bawai dan tana tunanin bazai dawo da farrah bane a a sai dai kawai ita bata son yawon hankalinta baya taba kwanciya dirin motar da taji yasa ta miqe ta Saka hijab ta fita ta zira slippers a qafarta ta fice tun kafin ya fito daga MOTA ya hangota ya qare mata kallo tun daga sama har qasa yai murmushi Farrah tana hangota tace laa ga Mimi , sarai ya gane wa take fada, ya share yace kina son zuwa school??? Gyada Mai Kai tai da sauri yace ok to kunce fita yai Ya kalli amatou yanda ta toge ta harde hannu daga alamu jiransu take, tana ganin ya fito da farrah ta qarasa tasa hannu zata karbeta ba tare da magana ba yaqi bata ita yau a wuya take tun a makaranta Dr abdullahi ya dameta sai ta bashi address dinta and ITA she is not ready for that har kamar yana Neman threatening dinta gaba daya she is confused Bata dan wata wahala da damuwa Kuma ita bazata iya cewa directly ya rabu da ita ba tunda malaminta ne tho dai ya nuna baro baro cewa Bata maraba da sabuwar alaqar tasu Amma yaqi haqura sai ma banzatarwa da yake yana nuna kamar be San me take nufi ba, Dan Allah ka bani ita kallonta yake kawaii yace idan na qifa?? Kallonshi tai tace kamar ya idan kaqi fa ?? Yar kace da zaka qi bani ita ?? Naga de 'yata ce wani scoff yayi a ranshi yana cewa gori ya tashi, Dan harararta yai to me 'ya sai ki Fadi Wanda baida yar, then kaje ka dauke su kana yawo dasu mu Nan mun godewa Allah da rayuwar da muke ba sai munje inda yafi karfin mu ba danne zuciyarta take Bata so tai Mai rashin kunya gaban farrah Amma yanda take magana kasan da tsiwa takeyi farrahn ce dai bazata fahimta ba, sakin mata ita yai a hankali ta karbeta hannunta ne ya shafi Saman hannunshi ba tare da ya sani ba yai saurin sakin farrah, juyawa tai tayi hanyar qofar gida batare data Ankara da meya faru ba, Bude gida tai tace Farrah ta shiga gida Farrah Dake qoqarin yima Hammad bye bye amatou ta hanata ta turata cikin gida yana kallonta murmushi kawaii yake ganin ta juyo ya daure fuska ya dauke kai, qara sowa amatou tai gabanshi ta zaro 20k din da ya Bata ranar Nan ta jefa Mai Tai windown motarshi da mamaki yake kallonta yace mene haka?? Kallonshi tai tace firstly bana buqatar kudin ka nagode Allah ya Saka da alkhairi sannan na roqeka da Allah stop spoiling farrah Dan Allah kayi haquri bana son fitar Nan da kake da ita i understand kana son farrah Amma Dan Allah ka barmu muyi rayuwarmu a yanda ka ganmu we are

Please Login or Register in order to submit comment