Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

deputy president din ku ba ?? Kallonta kawaii amatu take sai wata zuciyar daga gefe takejin cewa gsky take fada tabe baki tayi aikuwa abunda ya faru knan bayan ta gama girgmki ta dauko kayan kitso ta bama amatu comb ta taje gashinta kamar xatai kuka ta taje Kanta sai Kuma ta juya ta Kalli Maryam din wai maamaa nida ba gashi xanje innuna ba meye sai anyi wani kitso, karbe comb din Maryam tai sannan tace bakisan yadda kitso ke maki kyau bane kina son yima wani amma ke bakyaso a taba miki gashi, kitso me bala'in kyau tai mata ya fito da fuskarta tai wani irin kyau na ban mamaki, bayan ta gama taje ta dauko lalle kasancewar amatu na bala'in son lalle yasa batai musu ba ta sa mata a yatsunta guda goma,Wajan qarfe 2 ta cire saboda sallah yayi wani irin jaa dan tana da cin lalle umma rabi tace ko kefa amatullahi bakiga yanda kika fito sak mace ba wlh murmushi kawaii tai, washe gari da safe ta tashi tai duk abunda zatai Dan 10 za'a fara Maryam ma tsaf ta shirya ta shirya farrah sunyi bala'in kyau duk dogayen riguna suka Saka Dan koyayane basa rasa kayan fita kunya ta Amatou red ta Maryam brown sai ta Farrah itama kids gown me bala'in kyau ja ita ma amatou Bata do zuwa da ita ba amma ganin maryam ta matsa yasa ta kyale bayan sun shirya ta kallesu tace kuyi azkar, gyada kai Farrah tayi suka koma gefe sunayi kafin ta qarasa shiryawa, black sneakers dinta ta saka tana bala'in son gayu kawaii dai bata da wannan gatanne yasa ta hqr rolling tayi tai kyau sosai ta kalli kanta a madubi sauke idanunta tai still kwalla na ciko idanunta, in har zata Kalli kanta a madubi sai ta tuna gwagwarmayar da tai a rayuwa tun tana yar qarama Koda yaushe sai zuciyarta ta karye idan ta kalli kanta she is too young for all these itama da zata samu Wanda zai kula da ita so take Wanda zata Dora kanta a kafadarshi tai kuka kamar mijin barraq lokacin da ta aureshi Yana tausayinta Yana gatata ta kamar kwai, sosai yake shagwaba ta Amma within shot period of time komai ya faru ya qare kamar mafarki, juyawa tai ta fice ba tare da ta bari zuciyarta ta karye ba dan hakan ba qaramin butulci bane ga Allah tunda idan ta kalli rahamar da Allah yai musu sai ta gode ma Allah tunda ba kowa yaima wannan rahamar ba , ba kowa yaima baiyar dakiya da qoqari da Neman na Kai ba da Allah yaso da yanzu wani labarin ake ba wannan ba Amma Allah ya tsaresu ya karesu kuma, fita tai ta samesu suna ta dariya ita da Farrah mu tafinku," umma rabi mun tafi, to Allah ya bada sa'a amatullah Allah ya taimaka, suna fita suka nemi a daidaita sahu,,,,
Babban hall ne dake iya daukan mutum dubu goma dake cikin makarantar ABU Zaria amatou bata tashi fargaba ba sai da suka shiga hall din dukda daruruwan mutane da suke hall din Amma Basu cikeshi ba basarwa tai suka shige Dan ana dab da fara Taron, ammaa da ta hangosu tun daga nesa da sauri ta taso tayo gunsu OMG amah Ina kika samo me bala'in kama dake she is sooo cute tubarkallah Masha Allah qanwarki ce??? Ta fada daga durqushen da take gaban farrah,murmushi kawaii amatou tai ba tare da tace komai ba, hi cutee how you??? Ammaa ta fada cike da iyayi irin nasu na yaran yan gayu, kallon Maryam Farrah tai gyada mata Kai tayi Dan Babu Wanda ya taba mata turanci a waje beside Maryam sai kuma mamanta, a hankali tace am fine daukanta tai suka miqe tare tana kallon maryam tace hi sister sai kuma tace wait ta juya ta Kalli amatou sai ta kalli maryam, lallai amah Baki da kirki wlh kina da qanne masu kyau ko irin introducing dina bazakiyi ba kodan na manta ke bakya yadda da kowa ta fada a zuciya tana juyawa tare da Farrah a hannunta Maryam sai dariya take musu janyota amatou tai tace am sorry ammaa ai there is nothing much to say shiyyasa kikaji ban fada miki but am sorry meet my little sister Maryam maamaa and then sai ta nuna Farrah tace meet Farrah sai ta danyi Shuru sai Kuma tace my daughter, da sauri ta kalli amatou tace like serious haka zamanmu dake yake ?? Babu komai mene Dan kince min kina da aure?? Da sauri Maryam ta katseta tace chill sister she is not married yanzunnan sai ta ja hannunta ganin yanda amatoun ta sunkuyar da Kai tana murmushi Amma ita maryam ta san wane kalar murmushi ne, tace kuzo mu nemi front sits dan naga anty mimina dakyau," Maryam ta fada Dan ta kautar da zancen da suke aukuwa gaba gaba suka nema din ammaa sai kallon amatullah take bakinta fall da tambayoyi da kuma tausayinta she never thought ta taba aure ballantana har tai Mata tunanin bazawara ma basu taba Wani personal hira ba ganin amatoun bata taba Wani personal magana da itaa in fact da naci ma suka fara shiri da ammaan dan ita bata da shariya barin ma idan yanayinka ya mata shiyyasa take son amatou din dukda akwai 'ya 'yan manya a class dinsu masu ji da class da Kuma gayu kwata kwata Bata shiga cikinsu kafin kace me manyan baqinnan duk sun qaraso dai dai kune Basu qaraso ba hakan yasa aka fara tsit kakejin hall din hakan ya qara bama amatullah tsoro she has never been before more than 1000 people head girl ce ita da tana sec school so tana so many speach suna zuwa wasu schools din Amma bta taba tsayawa gaban mutane dayawa haka ba, jin hannun maamaa tai a jikinta kallonta tai murmushi sai taji Dan qarfin gwiwa a hankali aka fara gudanar da taron Wanda babu dadewa aka kira Amina garba isma'il a hankali ta miqe cike da nutsuwa a zuciyarta tayi hamdala da take saka sneakers ba wasu takalmi me tudu ba Dan a yanda takejin ido ko flat shoe ne zata iya hardewa tana jiyo wasu suna hailing dinta Wanda batasan ko su waye ba amma tasan tabbas dasu ammaa dab da zata hau stage taji gwiwarta tayi sanyi jikinta ya mutu, addu'a ta nemo ta farayi Bata tsammaci haka abun zai zo mata ba, tana daga Ido sai idanunsu suka hade dai dai shigowa casual kayane a jikinshi kaftan da hula sai labcoat a sama ya rataya stethoscope a wuya, code na dressing din guest of honours din knan a tare suka dauke kai, ta qarasa wajan mic din tai stabilizing kanta cike da nutsuwa ta fara addressing kowa cike da smartness da Kuma cikin tsarkakken ingishi da ta fara magana his heart stops for a bit kafin ta cigaba da aiki bai fahimci ya tsaya da abunda yake ba sai da ya dawo hayyacinshi qara dagowa yyi ya kalleta sai Kuma ya sauke idonshi ya cigaba da duba presentation din da zaiyi data gama tafin da Akai ya fi na farko dan ta tada qura class president dinsu was so proud Dan DAMA can yayi trusting capabilities dinta yasan performance din kowa a shekaru ukun da sukai Dan Wani lokacin Wani lecturer din yana sashi recording test ko assignment wani lokacin assignments din Yan ajinsu yana kwana a hannunshi and Yana going through kawaii DAI Bata da shiga mutanene Kuma Bata Saka kanta a komai be san Kuma meyasa ba Bata taba zama a extra lectures haka ko kuma yanda wasu suke bin Yan level 4 ko 5 su koya musu Abu bai taba ganinta ba dayawan matan ajinsu zaginta suke suna ganin girman kanta but yasan ba girman Kai bane Amma su bazasu fahimci hakan ba, zama tai a sit dinta sai Kuma a hankali ta duqa ta Dora kanta a kujerar Dake gabanta she feels like she wants to cry Bata San meyasa ba tayi tayi ya riqe hawayenta ta kasa a hankali ta bude jakar Maryam ta dauko handki Amma ce ta leqota ta gani tai tana share hawaye a hankali abun ya Bata mamaki Amma sai Bata ce komai ba hada Ido sukai da Maryam sai ta Nuna mata ita da Ido sun kuyawa tai taga abunda take da sauri ta janye Farrah dake qoqarin leqawa a hankali tace Mimi bacci takeji bari ta kwanta Dan tasan idan taga tana kuka yanxunnan itama zata saka kuka ta dade tana kuka sannan taji dama dama ta dago abunka da farar mace Nanda nan idanunnan sukai luhu luhu hancinta yyi jaa, idanunshi yaji suna mai qaiqayi zuciyarshi na kwadayin wani abu Amma shi kanshi be San mene ba, kawaii scrolling tab dinshi yake amma bawai dan Yana karantawa ba tunaninshi Yana Wani wajan Amma baisan Ina bane a hankali ya dago ya fara lalube a cikin hall din be dadeba ya hango abunda yake tunanin shi yake nema Amma bashi da tabbas tunda ta sunkuya kasa dauke idanunshi yyi yana kallo ta gefen damanta ta sunkuya ko magana tai mata ko kuma yayane oho sai ta hannun hagunta da take dauke da yarinta itama ta sunkuya kallon yarinyar ya qarayi sai kuma yaga kamar waccan din yake kallo Amma mini version dinta dauke Kai yai dasauri Yana shafo bayan wuyanshi Maida idanunshi wajan yai dai dai Nan ta dago if he is not mistaken kamar idanunta sun canja irin na Wanda yyi kuka, Yana daganan zaune Yana gulmarta shi kadai ba tare da ya Ankara ba Yana cikin gulma da shiga abunda ba ruwanshi Akai presenting dinshi as DR. HAMMAD IBRAHIM MASKA as a presenter a hankali ya miqe Yana watsar da tunanin da yake ya qarasa jikin mic din cike da karsashi da kuma qwarin gwiwa, a hankali ya fara presentation din cike da ilimi kana ji kasan yasan me yake yanayi Yana throwing questions ana amsa mai har ya gama bayan ya gama ba dadewa aka tafi break Dan schedule din har 4pm sai da ya gama harhada abunda zai hada sannan a hankali ya fara Yi masu sallama Dan Yana da Wani conference din a abuja da zaiyi attending fita yyi ya nufi inda ya parker walpepiyar motarshi da sai walqiya take age dinshi zai Kai 38-39 a qiyasi kana ganinshi kasan yaji Boko Kuma boko at jishi har zai bude mota suka hada ido da Farrah Bata Saba da Maza ba Bata sansu ba shiyyasa duk Wanda zai wuce ta kusa dasu take binshi da kallo wannan ganin yayo wajansu yasa take ta kallonshi, murmushi yyi ya Bude seat din BAYA ya ajiye kayanshi kafin ya qaraso ita da Maryam ne kawai a tsaye Amma da amatou sun tafi ladies zasuyi fitsari, qarasowa yyi gabansu cikin muryarshi yyi sallama Yana kallon Farrah ya miqa mata hannu Allah ya halitta Mai son Yara kullum gorin family dinshi knan yaqi yayi aure balle ya samu ya ranshi and he just fell in love with the little angel da ya matso kusa da ita tana da kyau sosai ganin yadda take kamar tana tsoronshi yasa yadan durkusa gabanta gaishe dashi Maryam tai ya amsa yace nazo Aron baby murmushi Maryam tai tace gata idan zata yadda, janyo hannunta yyi ganin ta taho ya sa hannu ya dauketa sai murmushi yake me kyau Maryam taita kallonsu se ka rantse da Allah shi ya haifeta kodan suna farare dukkansu oho, matsawa yyi jikin motarshi ya dorata a bayan motar yace hello angel kallonshi kawaii take yace ya sunanki??? Tace Farrah yayi murmushi yace Farrah ?? Which class are you ?? Buda mai hannu tai alamun bata sani ba Dan zare manyan idanunshi yyi alamun mamaki yace Baki San class din da kike ba?? Tace ai bana zuwa makaranta da Dan serious face haka yace why??? Shuru tayi kafin tace mimi tace sai ta tara kudi sannan zata sani but Ina zuwa islamiyya kallonta kawaii yake yace and who tot you English ??? Juyawa tai ta nuna Maryam dake kan concrete din qasan bishiyar tana kallonsu Dan Bata jin me suke cewa juyawa yyi ya kalleta sai Kuma ya juyo yace is she ur?? Sister ?? Bude Mai hannu tai alamun Bata sani ba tace anty maamaa nake ce mata tare muke da Mimi da ita da umma rabi with much interest yace Ina babanki to ?? Baze saki a makaranta ba?? Bude hannu tai tace waye babana?? Da bala'in mamaki yake kallonta kafin yace komai ammaa tai sallama ta gaidashi zata dauki Farrah kallonta yyi sai Kuma ya Kalli farrah he don't feel like ya barta ta tafi haka dan haka yace baza'a a ramin ita ma for 30mnts haka?? Shuru ammaa ta danyi sai kuma tace to sir bari na tambayi mamanta sai ta juya ya bita da kallo jin tace mamanta tun kafin ta qarasa ya fahimci wacece maman nata sai ya Kai kallonshi sannan ya juyo ya Kalli Farrah yace.......



Inata qoqarin naga page din ya danyi tsayi



Mrs maan
[9/21, 10:30 AM] MrsMaan✨: *~Amatou~*🧕🏻
(The_single_mother)

5.

Tun daga ranar suka dawo dai dai kullum Farrah tana cikin zancen uncle me mota har sai da amatou tace zata zaneta idan Bata saurara musu da zancen Nan ba sannan suka Dan samu lafiya ta ban gare Daya sosai karatu ya fara yi mata zafi Dan exams din second semester zasuyi a hankali take Dan ramewa sbd stress da ya fara yi mata yawa Dan kasuwarsu ta saloon sosai take ci yanxu tun bayan speech dinta dayawa sun dauki video anan Wanda suke zuwa kitso gunsu sukai ta mamaki sannan suna tura musu customers dan saloon dinsu Babu qarya hakan yasa abun ya fara mata yawa Babu yanda maryam batai ba akan tana hutawa ba Amma taqi abunda kawaii takeyi idan taji ta gaji sai tace Maryam tayi gaba idan yaso ita idan ta danyi bacci ko Kuma ta huta idan batajin baccin sai tabi bayanta a lokacin anyi kusan 2months da conference din Farrah gaba Daya ta manta da Wani Dr hammad normal suke rayuwarsu ,yau umma rabi da Farrah suna zaune da yamma su amatou sun fice saloon dan Sunday bayan Maryam ta yarfa mata kitso mai kyau dakyar ma ta zauna Dan ta tsani a taba mata Kai just like mamanta Almajirine yai sallama yace wai maryam umma rabi tace Maryam kuma ?? Eh haka akace min, kaje kace waye yake nemanta ?? Dan Basu Saba da wannan sallamar ba, ba dadewa ya dawo yace wai dakta maska ne Shuru umma rabi tai sai Kuma kace to batanan juyawa yai ba dadewa ya dawo yace to wai fara tazo umma rabi najin haka tasa Farrah yake so yace sai tayi tunanin ko wanine daga yan uwasu dukda dai lokaci zuwa lokaci dangin baban farrahn idan an samu Wanda yaga DAMA sai ya leqota Hakan yasa ta miqe ta dauki hijab dinta me Dan kyau da amatou ta Dinka mata kala biyu ta saka ta fice ganin qatuwar dalleliyar mota tai sai maiqo take shin an fito daga gidan bayan ya sallami almajirin da dubu daya ya Sako kai ya fito gaba Daya daga cikin motar cike da kwar jini da kamala ganin babbar mata da ta girmeshi sosai yasa ya qarasa ya duqa ya gaidata da fara'a ta amsa tana cewa Kaine me aiken knan Sosa bayan kanshi yace nine farrah nazo gani tun wancan lokacin bamu qara haduwa ba yasa nace bari inzo in ganta umma Rabi Bata fahimci wane lokaci ba sai daga Dan baya abun ya Dan kawo Mata haske sai tace autoo ko kaine kwanaki ka dawo dasu gida ita da maryam murmushi YAI ya gyada Kai yace nine mama,tace to madallah an gode sai dai su amatullahin basa nan suna can shago, Dan kallonta yyi ya dan qifta idanu sai ya fahimci wa take fada yace eh idan farrahn tana Nan Dan Allah zan iya ganinta?? Dan Shuru tayi da dai zata CE Mai bata nan Amma kwarjini da cika idanunshi yasa ta kasa ce fada mishi haka murmushi yai sarai ya fahimci me take nufi Kuma bega laifinta komawa yayi jikin motar ya jingina Yana qara kallon gidan a ido physically gidan bashi da laifi dai dai gwargwado Amma se yaga idan ya kalli gidan ya tuna da yanda suke sai yaga da gidan da su din abubuwane mabambanta guda biyu kwata kwata basuyi kala da Wanda zasu zauna a wannan gidan ba at all, and this woman he can't tell ko mamansu ce ba dan baiga kamar neither Maryam nor ita maman farrahn ba, Yana cikin wannan tunanin yaga Farrah cikin doguwar riga marar nauyi sanye da Dan madaidaicin hijab da takalminta very neat tana ganinshi ya ware Mata hannu ta taho da gudu ya dagata ya na rungumeta Yana murmushi su amatou dake tahowa daga nesa suna kallo Maryam tashi Daya ta gane waye while amatou cike da mamaki take kallon abunda ke faruwa idan ta Saka ka a kwandon shara to mantawa take dakai kwata kwata Dan haka bata ganewa waye ba tunda tasan Babu Wanda tai mugun sabo dashi irin haka idan ba maamaa ba, batasan lokacin da tace waye wancan din maamaa?? Tabe Baki Maryam tai tace hala Dr Hammad ne kallonta tai alamun ba dai ta gane ba tace Dr Hammad dai na ran conference Dan Bude idanu tai tare da bada expression din ohhh a fuskarta sai kuma ta hade rai Maryam tana kallonta sarai ta shareta ita bata ga aibun abunba Amma kana magana zata karanto Maka qabali da ba’adi, amatou so tai tana zuwa ta karbi Farrah tace mishi yayi haquri ya daina zuwa Amma data matsa kallonshi tai GABA Daya sai gwiwarta ya sage ta kasa tabuka komai bayan gaisuwa da tabi bayan Maryam tayita qasa qasa kallonta kawai yake Wanda Maryam na ganin haka ta sidade ta gudu cike da Dan murmushi tai ta shige gida suka hadu da umma Rabi da hankalinta be kwanta ba ya fito tana leqensu sai da taji muryarsu sannan hankalinta ya kwanta tare suka shige gidan maryam na fadin yau mutuniyar ko ya zatai kuma to tuntsure da dariya, Amatou dake tsaye ta kasa motsawa sai wasa take da hannunta so take ta karbi farrah Amma ta kasa fada Mai yana sane ya juya ya cigaba da wasa da farrah sai Kuma ya juyo yace na lura rowar yar taki kike min bana satar mutane fa da sauri ta girgiza kai kunya duk sai ya rufeta ta bude Baki zatai magana kawai sai ta fara hawaye da mamaki yake kallonta farrah na ganin haka ta fara qoqarin sauqa tana Kiran mimi kuka kike?? Kana Jin yanda take magana kasan qiris take Jira ta fashe da kukan itama da sauri amatou ta goge idanunta tana murmushi ta durqusa tana kallonta tace kin manta mimi Bata kuka?? Abune ya shiga min idanu irin yanda yai miki ranar nan, gyada Kai tai cike da gamsuwa Bude bayan motar YAI ya ciro kayan kwalamar da ya siyo mata yace zo Farrah juyawa tai ta tafi gunshi ganin leda zai Bata da sauri amatullah ta qarasa ta janyeta ba tare da ta yadda sun hada idanu ba tace a a mun gode wancan ma ya Isa Allah ya Saka da strong voice dinshi yace aini ba le na kawo ma ba ta gyada Kai tace na sani Amma farrah gudan jini nace duk abunda ya shafeta tamkar nawane kallonta kawaii yake Yana kallon bakinta kana ganin yanda take magana kasan a tsorace take abunka da farin mutum fuskar nan tayi jaa janyo Farrah yayi daga hannunta ya miqa mata ledar yace kije gida zan dawo muje yawo kinji??? Gyada Kai tayi tana washe Baki tace nagode Dan ta iya godiya daga haka ta juya da Dan gudunta tana waiwayowa tana mai bye bye daga mata Shima hannu yai Yana dan dariya juyawa yaga amatou tayi a hankali zata shige gida yace ai ban gama Dake ba madam tsayawa tai sai Kuma ta juyo ta dan kalleshi suna hada ido ta sunkuyar da kai qasa tai har mamakin yanda Bata iya hada idanu da shi for no reason, kallonta yake yace what was that? Kallonshi tai Amma ba directly cikin Ido ba tace me fa?? Yace kin fini sani ai na Bata Abu meya sa kika hana ta karba and what was that cry for?? Da wani yazo wucewa sai yace wani abu nai Miki and kinzo Zaki sa yarinya kuka?? Kasa cemai komai tai yace ehen Ina sauraronki, girgiza Kai tai a hankali tace bazaka gane bane his heart skip again yanda tai magana is a total mess Wani tunani ne ya Kai kanshi da sauri yai a'uziyya Banda besan harta dan fito ba kallonshi tai suka hada Ido ta juya tace zan tafi, yace ai bamu gama ba Ina so ki fahimtar Dani abunda bazan gane ba din idan naji reason ne da zaisa na Daina zuwa sai naji Amma idan Baki fadamin ba zan ta dawowa ne, kallonshi tai Jin abunda yace, a hankali tace Bata Saba ba Kuma bana so ta saba...... Bata Saba me ba ?? Bakinta taji yayi nauyi Bata son cemai Wani Abu da zai ji wani Abu dangane da rayuwarta and indai zata bude baki dole sai yaji Wani bangare, Ina sauraronki," cike da qarfin hali tace '" Bata Saba da ciye ciye irin wannan ba and banaso ta saba bana so watarana ya zamana tana son abun Kuma bani da yanda zanyi na sai mata ba Kuma bana so Wani yazo ya rudeta dashi," yace shine reason din??? Gyada Mai kai tai hawaye ya gangaro kan fuskarta kallonta kawai yake yace kuka baya miki wahala ne?? Juya Mai baya tai tana goge idanunta murmushi yayi yace to naji qorafinki Kuma be karbu a wajena tho dai tunani NE me kyau but Zaki iya dorata akan tasan idan akwai ta gode ma Allah ta karba idan Babu Shima ta gode ma Allah ta haqura and ki koya mata ba gurin kowa zata karbi Abu ba sannan ki cigaba da mata addu'a Babu hijabi tsakanin addu'ar uwa da 'ya Allah zai kareta daga dukkan wasu abubuwa Kuma zai dorata a kalar tarbiyyar da kikeso ta hau yana fadar haka ya zagaya ya qirga kudi ya zagaya ta gabanta ya janyo hannunta a bazata abun ya zo mata hakan yasa tai qoqarin warcewa zatai BAYA Dan they are very close ya damqe hannunta ya Dora mata kudin sannan ya rufe hannun ya juya ya shiga mota da sauri sai da ya kifa kansa a stirring motar na yan mintuna kafin ya tada motar, juyawa YAI ya Kalli gun da barta Bata wajan Hakan yasa ya tada motar yai gaba
[8/20, 7:00 PM] ikhlasyusufyaqub: A tsakar gida amatou ta goggo fuskarta tas Amma har a lokacin jikinta rawa yake cikin sanyin jiki ta shiga da sallama bayan amsawa da sukai ba Wanda yace mata komai farrah ta taso tana nuna mata sweets dinta tana ce mata uncle me mota ne ya kawo mata murmushin qarfin Hali tai tace and did you thank him??? Tace laaa Mimi bakiji ba ?? Ai nace mishi nagode gaba daya kallonta suke ganin yanda take farin ciki da annashuwa Jin zuciyar amatoun zata karye yasa tace bari naje nai wanka kafin magariba kinji?? Juyawa tai ta koma cinyar umma Rabi ta cigaba da Shan kayanta Maryam na tayata daki ta shige ta zame takalmin qafarta ta qarasa bakin gado ta zauna tana tallabe goshin ta ita Bata San ma tunanin me zatai ba na taba ta da yayi ba ya taso mata da tsohon Miki da ya tuna mata barraq ko Kuma na ganin Farrah cikin farin ciki da annashuwa??? Ko ko tunanin mene manufarshi game dasu sai kuma ta tuna maganganun da ya fada mata hannu ta kawo zata share guntuwar kwallar Daya zubo mata ba'a taba bata shawara akan yanda zata tarbiyyantar da yarinyarta ba sai yau hakan yasa taji

Please Login or Register in order to submit comment