Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita. Don haka nake so na ji gaskiyar abin da ya faru da ita."Na dago ina hawaye na ce, "Wallahi Abba iya gaskiyata na gaya maka, a ranar da za ta bata sai da muka yi fada muka shirya a lokacin kuma duk akan ta ce ba za ta koma Kano ba, muka yi fadan bayan mun shirya muka fita da sadiya shine dawowarmu muka tarar bata nan bayan na dawo ne na duba jakata shine na tarar da wasikanta da sauri yace yanzu ina wasikar? yana wajen hajiya ya juyo wajenta kan yayi magana ta mike bata fi min ti biyu ba ta dawo dauke da farar takarda mai dauke da rubutun nana safiyya bayan ya gama karantawa, ya dago kansa yana murmushi ko wanan takarda ta ishe mu shaida in ya ishe shida in yaso alhaji nasir yaje can ya nemo WAYE SANADIN batan yarsa kan ya karasa salim ya shigo bayan sun gaisa da abba ya ce ke kuma sarkin daukar magana me
ya saki kuka ko kina tsoron haduwarku da manta sabo (alkali) ne? ya dan yi murmushi maganin kwashe-kwashen kawaye kenen kallo daya zakayi masa kasan yana cikin tsantsar farin ciki,


***** ***** ***** ***** *****
shi daya cikin mota sai faman murmushi yake ji yake kamar anyi masa bushara da gidan aljanna ya karya kan motarsa ya shigo layin gidan mallam kalil tun daga kofar gida ya hango manyan motoci ya karasa ya yi fakin. ya shigo tare da sallama malam kalil yana ganin shigowarsa
ya hau murmushi ya karasa har kasa gabansa ya zube bayan ya gaishe shi ya juyo wajen mutanen da suke gaban kakansa tsoho mai ran karfe kaki ka mutu araba mana gado ko sai kaga jikokin imran naka ne?




πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[12/14/2016, 5:44 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

8⃣2⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–




'Dan albarka za ka fara halin naka koh, ya mutanen gidan da fatan kowa lafiya? "Duk lafiya sun a ma gaishe ka."'To madallah ya kumu yarinya da jiki?" 'Hum, malam ta ma ji sauki."To, mana godewa Allah.

"Ya mike muka shiga ciki babu kowa sai tarin almajirai. Cikin dakinsa muka shiga cikin nutsuwa na Kara gaishe shi, ya amsa shiru ya biyo baya. Na daure na ce, "Malam an yi min aikin?"Ya dan sauke numfashi yana kallona, sannan ya fara magana. "Imran na dau tsawon kwana biyu ina maka aiki, kuma babu abin da nake gani sai tarin
alkhairi mai yawan gaske, amma fa bayan an sha wuya tare da riginginmu komai
zai zama tarihi."Yana murmushi ya ce, "Na gode Malam. Sannan ya gaya masa yadda
suka yi da Safiyya. Ya jima kan ya yi magana ya sauke numfashi.'Imran kana ganin in aka daura maka aure ba tare da sanin Salisu ba, ba zai haifar maka da matsala ba?" Ya yi saurin cewa, Wallahi Malam babu wata matsala da za ta faru, ka ga shi Dady baya gari, kuma su iyayenta sun ce in har gobe ban turo waliyina ba za su
bawa dan uwanta. Don Allah ka taimakan ina so da ya dawo sai ka gaya masa. "'Har yanzu kai yaro ne Imrana, ba ka san ya rayuwa take ba, ka je ka Iallaba iyayenta zuwa nan da kwana uku, ka ga kan sannan su "Dahiru sun zo sai mu je tare da su a daura maka auren."Ya kara tausasa murya ya ce, "Ni dai Kawu ka
taimakan kar na rasa ta, kasan yaya Yusuf bai yi aure ba, sai ni kaninsa."Shi kenan gobe ka zo mu je sai a daura auren in ya
so daga baya kwa yi bikin."Cikin murna na dago ina godiya na zaro dubu hamsin.
'Malam ga sadaki.""A'a ka bar abin ka ka yi wani abun ni zan bada sadaki a matsayin gudummawata."Yana fitowa daga gidan Malam kai tsaye cikin kasuwa ya nufa duk wani abu da ake zubawa a lefe sai da ya siya sai da ya cika akwati set shida nan take ya biya kudin aka zuba masa a but, ya taho zuciyarsa fal da faiin ciki.Ya shigo
tare da sallama, na dago fuskata a hade, kallo daya na yi masa na maida kaina. Ya karaso kusa da ni."Safiyya zo mu je falo ki ga wani abu."Ban yi musu ba na biyo shi zuwa falon. Akwatuna na gani har guda shida.'Safiyya ga kayan lefe nan na yi miki."Na dago da sauri na ce, "Ban gane ka yi minkayan lefe ba, ni da da an daura mana aure
za ka sake ni ko ka mance da haka?"Yana murmushi ya ce, Na san da haka wannan lefan na yi ne kawai don na faranta miki ko ba ky...."Kan ya karasa na katse shi da cewa, 'Bana bukatar kayan lefen ka burina gari ya waye a daura mana aure ka sake ni."Ina fadar haka na juya ciki ya biyo bayana da kallo fuskarshi dauke da murmushi.

*****WASHE GARI*****

Misalin karfe goma Imran ya shigo ya ci farar shadda har da babar riga fuskarshi sanye da farin gilas,
wanda ya kara kawata fuskarshi. Na dago ina kallonsa har ya karaso ya tsaya a gabana yana murmushi.'Ya dai Safiyya na yi miki kyau ne ki ke kallona?"Na yi saurin dauke kaina, ya
dan rankwafa, muryarshi a hankali ya ce, "Don Allah Safiyya ki yi wanka ki canja kayan nan. 'Babu ruwanka da canja kayana in ka je an daura to ka sake ni na tafi."Fuskarshi cike da
murmushi ya ce, "Ba a daura ba yanzu zan je na dauko su ai a nan za a daura, ki daure ki
canja kayan nan don Allah." Yana fadar haka ya fita.Bai fi rabin awa da fita ba na jiyo
hayaniyar mutane a falon na yi saurin zuwa bakin kofar na leka ta kofar da ake zura makulli. Mutane ne su wajen goma dukkaninsu sun manyanta, ina kallo suka daura aurena da Imran. Wani tsoho mai zaman zabga addu'a yake suna amsawa da amin. Ni kuma ina amsawa da ba amin ba. Aka mikawa wani farin dattijo sadakina. Suna zaune aka dinga shigo rnusu da abinci, bayan sun gama suka fita na koma ina hawaye na zauna.Har wajen karfe goma ban ga Imran ba, duk hankalina a tashe yake ga zazzafan zazzabin da ya rufe ni, ya shigo yana waya har ya gama sannan na dago kaina muka hada ido ya sakar min murmushi."AMARYAkinshakamsh..."Kan ya karasa na katse shi da cewa, "Imran kai fa nake jira."Ya dan rage murmushin fuskarsa."Safiyya jiran me ki ke min haka?"Na Kara daure fuska na ce, 'Ina jiran ka zo ka sake ni, kan..."Dariyarshi ce ta dakatar da ni daga abin da nake son fada na tsaya cikin mamaki ina kallonsa.'Hum, Saffiya kina nufin ni
Imran na sake ki da hannuna? Har abada ba zan taba iyawa ba. Safiyya ke naso, ke nake so kuma ke zan ci gaba da so har zuwa ranar da ban santa ba. Zan kasance jarumin da ka iya fito-na-fito da kowa in har akan sonki da kaunar...."Kan ya karasa na katse shi."Kana nufin ba za ka sake ni ba?"Kan ya ban amsa aka hau kwankwasa kofa, wata irin razana hade da firgicewa ne suka bayyana a kan
fuskarsa. Ya mike jikinsa yana rawa ya leka, da sauri ya dawo da baya. Daidai lokacin aka kara buga Kofar karo na biyu ya karaso gabana fuskarshi ta jike da gumi, na ji muryarshi a hankali."Ki rufan asiri Safiyya ki shiga bandaki yayana ne ya zo da iyalensa don girman Allah ki rufan asiri." Ganin tsantsan tashin hankalin da ya shiga karan farko dana ji tausavinsa. Ban masa magana ba na
shiga bandakin ya biyo ni ya kulle tare da ban umarnin nasa sakata, Ya dawo bakin kofa ya dan saisaita nutsuwarsa, sannan ya bude yana murza ido. Dr. Dahir ya kalle shi sama da kasa, sannan
ya yi magana."Tun dazun muna bugawa ba ka bude ba me ka ke yi a daki ka kulle kanka?"Ya dan kararo muryarshin dole yana shafar kwantacciyar surnarsa ya ce, "Hum wallahi Brother barci ne ya dauke ni. Ina su Abdul-Jalal?"'Suna falo, ka zo ka kai mu gida saukar mu kenan." Ai bai tsaya rufo dakin ba ya fito suka tafi. Suna zuwa gida hira ta barki Hajiya Amina ta
juyo tana kallon Imran."Ka san gobe Rarfe bakwai za mu tafi so nake sha biyu mun taho.'Ina sane Momy."Shiru-shiru Safiyya ta ji Imran ya bude ta ba ta ji ba, ga gidan shiru don haka ta zare sakatar komai zai Faru ya faru. Ganin babu kowa ga kuma kofar dakin a bude yasa ta dan zura kanta falon kamar a rnafarki ta hangi kofarsa a bude har ma tana hangen get din gidan, wanda shi ma kofarsa
take a bade, har ma tana ganin motoci na wucewa. Da sauri na koma na dauko jakata, babhar rigar Imran
na harde ni na yi saurin tsugunnawa na dauke na ji nauyi, na yi saurin zura hannu na a aljihunsa na zaro rafar 'yan dubu guda biyu (Dubu dan biyu) na zuba a jakata jikina na rawa kamar mazari na fita daga gidan. Court ta cika makil illa mutum daya da ake jira Alkali Abdurrahman ya shigo ana take masa baya. wannan lokacin duk wani Bangare biyu sun hadu, Alh Ibrahim, Sadiyya, Rukayya, sai kuma lauyansu Barr M- Shamsu, ilia Alh. Mukhtar da ake jira. Haka bangaren. Alhaji Nasir ga shi ga Umma wadda ta rufe fuskarta da nikaf ga lauyansu Barrister Amina Khalil da dan rakiyarta Imran, wanda ya ki bari su hada ido da su Rukayya. Bayan an gama karantawa Alkali shari'a ya dago ya kalli na kusa da shi suna hada ido ya yi saurin fita. Daidai wannan lokacin Alh. Mukhtar ya shigo, babu wanda ya ga shigowarsa sai Umma, ta yi wata irin zabura, Alh, Nasir ya ce, 'Lafiya?" Ta ma kasa magana sai kai da ta girgiza masa, kan ta dawo daga shoking ta ga abu kamar a cikin mafarki NANA SAFIYYA ta shigo,Ba ma Umma ba duk wanda ya san akan abin da za a fara shari'ar ya gigita da ganinta. Shi kuwa kanwa uwar hadin mutuwar zaune ya yi. Ta karasa ba tare da ta kalli kowa ba har
gaban Alkali, da kansa AIhaji Abdurrahman yace.."Ke ce Safiyya?"Na ma kasa magana sai kai na daga masa."To ina ki ka shiga?"hannu na daga na nuna imran na ce, "Ga wanda ya sace ni."Can na ji muryar
Umma ta kira sunana na yi saurin juyowa ina kallonta ta hau nuna Kawun rukayya, sannan tace, safiyya ga mahaifinki.....



πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[12/16/2016, 8:28 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

8⃣3⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–





*****TUNA Baya*****



ta shigo dakin tare da sallama, ita daya ce a cikin bukar sai wani kyakkyawan yaro da ba zai haura shekara hudu ba, yana ganin shigowarta ya hau murna. Ba ta ko kalle shi ba ta karasa gaban
Yayarta ta tsugunna suka gaisa. Ya taso da gudu ya hau cinyarta, tana kokarin ture shi suka hada ido ta dan daure ta bar shi, yana wasa da awarwariayen hannunta."Yaya za mu tafi fa, in kina da sako
ki bayar na taho miki da shi."Duk kun hadu ne?" Ba ta yi magana ba sai kai da ta daga mata,"Ba ni da sako ga Sale nan ku tafi da shi, shi ma ya ga gari."Ta dan dago da saurinta suna hada ido ta mayar da kanta ta dan yi jim, sannan ta mike."Bara na tafi suna jirana."To ba ki ji abin da na ce ba ne, ga Sale
zai bi ku shi ma ya ga gari.'To yaya na ji ya taso mu tafi.Cikin fushi ta dago kai tare da cewa, "Sofi ki kiyaye ni ki kama hannunsa ku tafi duk abin da zai same shi ya same ku tare, bana san sakarcin banza kamar
ba ke ki ka haifi yaron nan ba, shi ma zai zo ya same...."Kan ta rufe baki ya shigo shi ma gabanta ya tsugunna
kamar mai neman gafara. Suna gama gaisawa ta rufe shi da fada kamar za ta cinye shi, babu abin da yake sai hakuri yake ba ta. Ta dan sassauta murya ta ci gaba da cewa "Ba ka ganin dan uwanka neman haihuwar yake ido rufe amma ku Allah ya ba ku kuna wulakantawa, ku ne iyayensa ku za ku ja shi a jiki har ya gaya muku damuwarsa, to kuna baya da shi ba kwa jan sa a jiki, kuna nuna masa kauna to ya za a yi ya saki jikinsa da ku? In kiwo za ka ka ja danka ku tafi, haka in kasuwa za ki ki ja shi ku tafi, ba kya ganin yadda 'yan uwanki suke jan 'ya'yansu a jiki,Rashin kula shi da ku ke, shi ya ja 'yan uwansa suke dukansa. Yanzu, jiya da ba don na zo lokacin da suke fada da Jauro ba da sai dai a kashe shi a
gabanki kina kallonsa. To daga yau bana san sakarcin banza, ku ja danku a jiki, ku nuna masa kauna da kulaw..."Kan ta karasa
aka yi sallama aka shigo."Lafiya ku ke zaune muna tu fa man tsimayi?""Nina tsayar da su ina musu fada kan sakarcin da suke kan Sale. Yauwa Yaya ki yi musu har da duka sun cancanci haka."Tun da muka fito da Sale a hannuna mutan gidan suke kallona cikin mamaki, nan da nan kunya ta rufe ni bar ma da tsoron maganganun da za su biyo bayan hakan. Haka muka tafi kai nono cikin gari. Magajiya ta matso kusa da ni. Yau yana ganki da Sale?' Ta fada tana murmushi.Na dan sunkuyar da kaina."Hum, Yaya ce ta matsa sai mu tafi dashi."Ta yi daida..Daidai lokacin
muka zo gifta wani katon shagon saida kayan yara muka karasa tare da yin talian nono da sauri mutanen da ke siyayya a shagon suka juyo suna kallonmu bar mai shagon ya bude baki xai yi magana wani hamshakin Alhaji ya ce."Ku kawo mu gani." Yana maganar yana kallon Sale. Muka karasa gabansa tare da sauke kwaryar da take kanmu. Karar waka ta cika dakin muka hau dube-dube, sai Alhajin yasa hannu ya dauko wata katuwar aba baka ya
kara a kunnensa ya hau magana muka tsaya cikin mamaki muna kallonsa har ya gama. Sale ya tafi wajensa da gudu.Baffa ba ni na gani," Ya dauke shi ya dora sa a cinyarsa yana murmushi.'Dan Baffa me za ka yi da waya?' Sale ya ce Wasa zan yi da ita, ban da kayan wasa, baba ba ta sai mun sai dai ta dinga dukana ba ta ma kula ni kullum tana ganin yara suna dukana ba ta hana kowa. kai ma ka yi mata fada kamar yadda su Yaya suke mata.Ya yi shiru yana kallonsu kanta yana sunkuye kunya duk ta baibaye ta.'Ka yi hakuri ni zan sai maka kayan Wasa har ma da na sawa."Sunnan ya juyo wajen umma fuskarsa
a hade ya ce, "Me yasa ku ke takurawa karamin yaro? Kuna daya daga cikin azaluman iyaye masu wulakanta ya yansu ko?"cikin mamaki suka kalii juna ita da Magajiya, ganin yanda yake fada kamar dansa ya katse musu tunani da cewa, wasu suna neman Β°yaya ido a rufe Allah bai ba su ba. ku ya ba ku kuna wulaRanta su. Ya dan rage murya ya ci guba da cewa.Don Allah ku dinga tattalin 'ya'yanku kuna kula da su, in ba kwa jan su a jiki kuna nuna-musu kulawa sai su shiga wani hali.Na daga masa kai,"Ku zuban na dari uku-uku.Sunnun ya juyo wajen mai shagon."Malam hada masa kuyan wasa da na suwa."To Alhaji." Ya mike jikinsa na rawa
ya shiga hada kayan.Ya juyo wajen mu ya ce, "Ina san na sari shanu a wajen akwai masu siyarwa? Sale ya yi saurin cewa, "Baffanmu yana da su da yawa ka zo mu
je ya siyar ma ni kuma zan bar maka nawa Au kai ma kana da sa? Yaya sunanka?'Sale Ba ku ban amsu ba Mugajiya ta ce, "Ana siyarwa Ya dan numfasa, yana danna
faskekiyar wayar da take hannunsa ya ce "To yunzu ya za a yi na siya, tunda ban san wajen ku ba? baffa ka bi mu mu tafi garinmu, sai ka siya mu tafi gidanka. Hakan ce ta faru har muka gama tallan nono yana yaune a shagon mutumin da muKa yi masa lallar, ya mike ya dan fito bakin shago.'Kun san tafiyarmu ba za ta zo
daya da ku ba. in kuma za ku shiga motata mu lafi to Na girgiza kai na ce Ba za mu shiga motarka ba sai dai mu yi gaba ka bi mu a baya har mu je Sale ya hau kuka Ni dai babah ba zan tafi a kafa ba Baffa zai bi." Yana maganar yana rike hannunsa Magajiya ta jani gefe, mun dan jima muka dawo gabansa. Magajiya ta ce,Mu je mun yarda za mu shiga motar ka Wannan shi ne karanmu na farko shiga mota. Tafi-tafi har muka je garinmu yana ta mamakin mutanen da suke rayuwa cikin wannan surkukin dajin. Mamakinsa ya tsaya cak ganin mun bullo cikin gari duk inda muka wuce yara da manya kallonmu suke har muka karasa. Ya fito yana rike da Sale, Sale haka garin naku yake, gaskiya da wuyar zuwa, kuna shan tafiya. Amma kafarku tana ciwo kam Ya girgiza masa kai tare da cewa Don Allah in za ka tafi zan bika ka sani a makarantar boko Ai ba za su ba ni kai ba in da za su ba ni kai zan yi mutukar farin ciki a ce an bar min kai ka yi karatu mai..Bakinsa ya kasa
karasa abin da yake san fada, sakamakon ganin wasu gungun shanu sun taho farare sol da su kai ka ce gaba dayan shanun garin ne suka hadu. Maza biyu ne ke jan tawagar shanun Suka karaso wajen fuskarsu dauke da mamakin ganin mota cikin garinsu. Alh. Dahiru ya matso ya mika masu hannu don su gaisa cikin dari-dari suka mika masa hannu,
kan ya yi magana Sale ya ce Baffa wajenku ya zo zai sai shano a kasuwa muka taho da shi har ma ya sai min kayan wasa. Bara na dauko masa tabarma Ya zuru cikin gidan da gudu. Bai jima ba ya dawo da tabarma, sun jima suna tattaunawa da su Mado.Cikin gidan kuwa tunda su Magajiya suka bawa yayar mazajensu labrin bakon da suka taho da shi zai sai shanu har ma da siyayyar da ya yi wa Sale. Ta ko rufe su da ruwan fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba har matan gidan taya ta suke haka suka shigo suka same ta, dakyar suka
lallaba ta suka shiga cikin bukkarta. Ta dago tana hararar su dukansu kansu yana kasa.Haka kawai ku dauko mana mutum ba ku san wa ye ba mugu ne dan yankan kai ne muna zamanmu lafiya ki dauko mana bala'i, ni dai ban yarda da shi ba watakila ma irin barayin yara ne, ya gan ku da da yana so ya sace shi har da yi masa siyayya, to wallahi bara na gaya muku duk abin da ya sami Sale ku kuka da kan ku, kuma maza ku gaya masa shanunmu ba na siyarwa ba ne ya bar mana unguwanmu. Yanzu ina ma Salen yake? Bakin Mado na rawa ya ce, Yana wajensa Ta mike da sauri Maza ku taho da shi, kar ya gudu da shi Har matan gidan suka fito waje da gudu, babu mota babu Sale. Ta juyo tana kallon Sofi da Magajiya. Kun ga abin da kuka ja mana ko? To wallahi ba zan koma cikin gidan nan ba in za a shekara dubu sai kun je kun nemo sa, bar mazajen ku ku bar gidan nan ga shanun nan ku dibi naku ku tafi, wallahi duk wanda ya shigo gidan nan a cikinku ba tare da Sale ba sai na KASHE shiSANADIN zuwan su Mado cikin birni Kano kenan.



πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[12/20/2016, 9:06 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

8⃣4⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–

Bakina narawa nace, β€˜Umma Kawun Rukayya, shi ne mahaifina?”na daga kai. Na ji wani irin jiri
yana dibana nayi baya zan fadi, naji an tare ni kannakara sa suma a jikin wanda ya tare ni naji sautin muryar Alkali yana ba da umarnin kama Imran.

Magana na dinga ji sama-sama tare da sautin kukan Rukayyar Momy na, muryar da baza ta taba bace min ba, nayi yunkurin bude idona wanda sukayi min nauyi sosai tare da azabar yaji kamar an zuban barkono, nabude su dakyar idona cikin fuskar Ummana kantana kasa tana sharer hawaye ta jimuryata.β€œUmma me ye kike kuka?”Ta yi saurin dago tana kallona damuwar da take fuskarta ta bace murmushi tayi Ni kaina, ban san lokacin da murmushin ya sauka a kan kyakkyawar fuskataba. Kan ta yi Magana Momy ta dago idonta duk sun kumbura, na bude baki dakyar nace.Momyki bar kuka gani na dawo.”Ina maganar inakokarin kama hannunta, ta yi saurin mikon hannunta, na rike ina mata murmushi ta ce.β€œSafiyya kukan farin ciki nake da Allah ya bayyana gaskiya cikin kankanin loakci, ban zaci haka daga Imra...”Kan ta karasa abin da yake bakinta aka turo kofar aka shigo. Kawun Momy ne ya shigo yana shigowa Hajiya Amina (mahaifiyar Imran) ta shigo, na yi saurin mike ido. Hajiya Amina ta karaso gabana ta dan dafa gefen gadon ta ce, β€œSannu Safiyya.Kai kawai na daga mata, kan ta kara magana wayarta ta hau kara, ta zaro a jaka ta fita. Tana fita Umma ta bi bayanta Kawun Rukayya ya zauna a inda ta tashi.β€œSafiyya bude idonki don Allah.” Na ji muryarsa. Muryata a sarke
na ce, β€œKawu da gaske kai ne mahaifina?β€™β€œKi daina kokwanton haka babu wani kokwanto ke β€˜yata ceta jinina.”
Cikin shashshekar kuka na ce, β€œAbba me yasa ka guje ni lokacin da nake bukatarka ka ki ka tallafi rayuwata
lokacin da nake tsananin bukatar tallafinka? Sai wani wanda ba shi ya haife ni ba ya tsaya ya tallafi rayuwata,
ya yi min taimakon da ba zan taba mancewa da shi ba. Na so a ce Alhaji Nasiru ne ya haife ni, na san ba zan
yi nad....” Kuka ya ci karfina na kasa karasawa.Ya

Please Login or Register in order to submit comment