Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

momy yunwa bakeji toh waye zai fita a wannan darwn ga take away dinda imram ya siyamana nima shi zanci na kwanta.

sai karfe uku na fito daga dakinmu kai tsaye na wuce cikin makaranta sanye nake da doguwar riga baka na nade fuskat da dan mayafina babu komai a hannuna sai book guda daya muryar momy naji daga bayana tace sai yanzu akaga damar zuwa class din? kuka kama hanya koh jirana kunkiyi, keh dakika tsaya shiritanki shine zamu jiraki? kai momy kefa aunty nace kuma abba yace ki dinga lallabani'zan lallabaki ko dan darajar yaya imran kai momy har yafi abba matsayi? ba haka nake nufi ba kowa da matsayinsa.


karfe biyar wayata ta hau kara ina dubawa labar na wayar imran ne na ajje can wata zuciyar ta tunamin alkawarin da nayi masa nayi saurin daukan wayar


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[10/31/2016, 8:36 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

5⃣7⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
09039016969

www.MuhdAbbagana.blogspot.com


safiyya kina lafiya? can kasan makokorona na amsa da lafiya kuna cikin makaranta ne? na girgiza kai kamar yana ganina baki ban amsa ba ina tambayarki, bana girgiza kaiba to ai safiyya kin san ba ganinki nake ba ballantana na ga kin girgiza kai kiyi hakuri ki ban amsa ni ina hostel momy kuma tana cikin makarant su dasu farida shi kenan amsar da kake so na baka. shi kenan kanwata nima gaya miki zanyi nazo mu gaisa ina jiranki cikin makaranya da fatan kina sane da alkawarinmu na zuwa muna gaisawa yana fadar haka ya katse nabi wayar da kallo.

wannan mutumin zai dinga fakewa da nayi masa alkawari ya takurawa rayuwata gaskiya sai na taka masa birki, hijabi nasa na na fito yana zaune cikin motarsa tunda na tawo ya kasa dauke idonsa akaina babu wata kwalliy a fuskata amma hakan ta masa wani irin kyau mai makantar da zuciya gabaki daya, yana yin komai na yana burgeshi ya Allah ka mallakan safiyya ya furta a hankali tare da lumshe ido ta karaso fuskanta a hade.

jin alamun an tsaya a ganansa yayi saurin bude ido yan murmushi muka hada ido nayi saurin dauke idona"safiyya ki shigo mana? nan ma ya isa sauri nake ina aiki a daki fitowa yayi daga cikin motar ya dawo kusa dani sanye yake da kananun kaya wanda suka dace da kallar fatar jikinsa, tunda bazaki shigo ba ni na fito sai na tsaya kusa da kanwata. da sauri nace wacece kanwar taka?? safiyya man koba kanwata bace? gaskiya ni ba kanwarka bace saboda me kika ce ha? ni daya ummana ta haifa banda yaya bare kanne to aii ummance ta haifen kinga na zama yayanki ko babu kara, kan na bashi amsa wayarsa tayi kara yayi saurin zarota daga aljihunsa hello khadija ya akayi? sun jima suna hira sannan sukayi sallama ya juyo wajena yace wata kanwatace yae rigima wai na dawo gida bata gaji da ganina ba.

nace to ka koma mana nima na gaya maka aiki nake, in gaisuwane kazo yi mun gaisa bari na tafi ina san ganin momy zan zauna na jirata ki tsaya muyi dan hira kafin tazo.

nafa gayamak aiki nake ka rabu dani in kanaso muci gaba da gaisawa to duk abinda na gaya maka karkace zaka gyaran koka takuramin ina fadar haka najuya na tafi.

yana tsaye cikin mamaki yaji sallamar momy imran yanzu kazo? yayi saurin juyowa yana kallonta aunty momy na juma ke nake jira harm safiyya tazo mun gaisa, aunty momy naje wajen mallami nayi masa bayani to shine yace nazo da ita.... momy ta dago kai da sauri hmm imran kasan inzamu to safiyya bazata taba yarda muje ba "ai aunty momy baki tsaya na gama gaya miki ba, yana gayan haka nace mallam baza ta taba zuwa ba. wani rubutu ne ya bani nakai mata in ya kare sai na dawo 'imran bansan wani irin godiya zan maka ba nasan kanason safiyya tsakani da Allah ina maka fatan Allah ya baka safiyya amin aunty kasan wani abu imran? ya girgiza kai tunanin yadda zann mata ta dinga shan rubutun nake nima nayi tunanin haka dan na hango taurin kan safiyy za a sha wahala kan ta amince.

momy ta hau dariya karka samu damuwa imran yanzu zanwa abba waya nayi masa bayani. kai naji dadi kin iya kawo shawara bari naje gidan kanwarmu ta damu na dawo kisan nima dan gatane kamar safiyya na au har ta zama taka? momy ba kekika bani ita ba.

ina kwance ta shigo hannunt dauke da jakar rubutu kan nayi mata magana tace yanzu muka gawa waya da abba, amma koki kawo da gudu mugaisa ke nima ba hira mukayi ba turo abonkisa yayi ya kawo mana rubutu. cikin mamaki nace rubutu kuma? ta daga kanta tare da nunamin jakar hannunta. to ce mai kikayi bamu da lafiya? kewa yayi na tsari ne saboda mutane kuma bamu san zuciyarsu ba na hau dariy gaskiya abba yana sonmu da yawa, gara ana taimakawa da rubutu saboda mayu irinsu saifu da .....sai kuma nayi shiru ta dago kai ta harareni da kuma wa?? momy ba wani abu zance bafa.



πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/1/2016, 9:10 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

5⃣8⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com

karya kike kinaso ki karasa da imran koh? lah momy ai shi baice yana sona ba, kawai gaisuwa kawai muke kinga shi ba maye bane. oho miki dai wallahi ki iya kanki, zan iya momy amma ba yanzu ba. sadiya ce ta shigo yanzu muka hadu da imran zai fita nace har an gama soyayyar Allah sadiya bakya ganewa waya gaya miki soyayya muke?

ana gobe abba zaizo bayan mun gama waya na mike na shiga toilet bayan na shirya na juyo ina kallon momy nace"momy zanje unguwa tayi saurin dago kai ina kika sani da zaki unguwa? kai momy me kika daukeni ina tare da oniya tana nunamin gurare kuma yau nidaya zan fita nayiwa hajiya tsaraba na bana abba ya kai mata.


**** **** **** **** **** **

Rakiya!! Rakiya!! ta shiga kwala mata kira tayi saurin fitowa tana daura dankwali 'gani babah' gani nayi lokacin zuwanki asibiti yayi baki fito ba kin ta sana'ar taki" yanzu nake shirin fitowa ina gyara kayanmu dana wanke ne dana gama zan tafi.

bara naje nayi barka kanki gama, tana maganar tana yafa mayafi bayan fitarta baifi minti biyu ba naji sallama na amsa tare da fitowa ina karasawa mukayi ido hudu dashi nayi saurin juyawa zan koma naji muryarsa babah tana nanne? a ciki na bashi amsa na shige cikin kallon fuskarsa babu abinda ya karan sai bakin ciki ina shiga daki na zauna wani irin hawaye ya zubomin wannan auren ba karamin ya karamin ba face bakin ciki tunda sanadin sa na rabu da farin cikin zuciyata, wayyo Allah na safiyya ina kika shiga kika barni da tunanin ki a raina bazan taba farin ciki ba muddin bakya tare dani, a wani hali kike shin tana raye tsahon wata uku ban sata a idona ba nayi saurin kauda tunani tana raye tabbas jikina yana ban safiyya tana raye ki dawo gareni na miki bayanin da zaki gamsu wallahi safiyyata ba shegiya bace kizo na gaya miki gaskiyar waccece ke,
kuka yaci karfinta tafi minti biyar tana kuka jin muryar babah a waje tan gaisawa yasa tayi saurin tashi ta fada ban daki, wanka tayi ta fito babah zan tafi ta zaro kudi ta mika mata ki biya ta bakin asibiti ki siyomin kayanmiya. tana fitowa bakin titita samu mota ta shiga ta zauna kusa da wata yarinya wayartane tayi kara tayi saurin dagawa hello aunty na dawo can kuma tace a,a tun jiya na dawo na baro su lafiya. ta kara cewa aunty zaman lagos da dadi karatu yazo gangara sai dai innazo zaki sha labarin karatun safiyya umma tayi saurin dago kai tana kallon yarinyar, ita kuma ta cire wayar da ke kunnenta tana dariya nan take umm ta shiga tunanin tata safiiyan.
hajiya ba a nan zaki sauka ba? tayi saurin kai dubanta kofar asibiti ake ta zaro kudi ta mika masa ta shige cikin asibiti.


tafiya take amma ba sosai take ganin gabanta ba, babu abinda yake ranta sai tunanin safiyya har ta kusa karasawa dakin taji muryan asha mama sannu da zuwa nayi saurin juyowa ina murmushi, aysha antashi lafiya? lafiya klau mama. ina maman taki tana gida cewa tayi nazo na tafi dake gidanmu yau ba zata samu zuwa aiki ba, nama dade da zuwa harna fito saina hangeki.
banyi musu ba na bita muka tafi dan na riga na saba da ita kusan yanayinsu daya da nanata illa wannan bata da taurin kan nan gata kuma da hakuri sabanin nana. babu wsni nisa tsakaninsu da asibitin muna tafiya tana jana da hira har muka karaso gidansu, wani falo ta kaini bai kyan tsari mama ki zauna bara na kira momy ina zama ta kwalawa yar aikinsu kira lami ki kawo ruwa anyi baki tana fadar hak ta hau bens wanda mattatakalarsu take cikin falon da nake zaune. tana hawa wata budurwa ta shigo hannunta dauke da tire an dora lemun kwali da ruwan roba sai wani kofi mai kyau............



πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/2/2016, 9:00 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

5⃣9⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


sannu da zuwa hajiya yauwa sannunki ta ajiye har ta juya ta dawo dan Allah hajiya na tambayeki abin ya ban mamaki amma na hadiye nace Allah yasa na sani. muryar a hanki kamar tana tsoro kar wani yaji abinda take san fada tace dan Allah kema irin mutanen nan ne da ake nunawa a talabijin naga kuna kama kum gashi kinsa hakori ance daman a garin ake sawa nace daman a wani gari ake ganinsu a talabijin? da sauri tace naji aunty aisha tana cewa makka abin ya ban dariya nace bi ba,a makka name ba na dai taba zuwa sau daya' ta hau dariya amma wallahi kuna kama babu abinda ya rabaku dasu keda alhajin kegos shima kamarku daya kan ta sake wata magana taji saukowa tayi saurin fita tana dariya.
ta karaso fuskarta a cike da nishadi sannu da zuwa kina tare da lami tana miki shirme koh? bance komai ba illa murmushi muka gaisa kin ganni yau bana jin dadin jikina ba zan samu damar zuwa ba shine na tura aysha ta taho dake dan karkizo bana nan.

nim de yau banzo da wuri ba, tace bari na shiga kitchen tunda ta tashi na fada tuniyar tunani har ta dawo ta hau kiran sunan.

rukayya!! rukayya!! nayi saurin dago kaina kamar wadda ta tashi daga barci ta zauna kusa dani haba rukayya me kika rasa kikeso ki jawa kanki wata cutar, kullum kina cikin tunani ki tuna kina da ciki kullum in an auna miki jininki baya sauka sai kara hawa yake, ki cire tunanin komai a ranki. me yake damunki? duk wanda ya kalleki ba zai ga alamun damuwa a tare daka ba' tayi kasa kasa da murya wallahi rukayya in wata ta gaya miki halin da take ciki sai kinga ke a aljanna kike.
na numfasa tare da goge fuskata likita matsalat ta zarce yanda kike zara lik....kan na karasa tayi saurin cewa sunana khadija dahie ta fadi hakan ne dan na daina gaya mata sunan danake kiranta dashi. murmushu nayi mata kawai sannan naci gaba da cewa Dan Allah in bazaki damuba ina so na miki wata tambaya tace Allah yasa na sani dan Allah aysha yarkice ta cikinki? karkiyi mamakin tambayan kokiji haushin amsar ki nake jira gaskiya aysha ba yata bace yar yayanace uwarmu daya ubanmu daya danayi aure na jima ban haihu ba dan haka ya barmin ita har kawo yanzu da nake haihuwa inada yaya hudu duk suna makarant to yanzu khadiya in aysha ta bata yaya zakiji a ranki? ta dafe kirji tare da zaro ido ai sai na kusa mutuwa Allah kada ma ya nunamin wannan ranar" khadiya yata ce ta bar gabana yau tsahon wata uku me yasa ban mutu ba? na tsaya ga yawaita tunani ta dago kai cikin tausayawa rukayya ya akayi tabar gabanki? kan wani dalili ne wanda ya zama sirrina khadiya ita daya na haifa sai wannan abinda yake cikina. gaskiya rukayya dole ki shiga cikin damuwa amma kiyi hakuri duk wsni tsanani yana tare da sauki, insha Allahu zata dawo gareki rukayya me yasa baku kai gidan radio ba kinga ba bata tayi ba ita ta tafi da kanta lokacin ya rage saura kwana daya ta tafi lagos karasa karatu au karatu take? tana karatu mana shekara uku tana zuwa jami,a to rukayya bakya tunanin koh tana can tana karasa karatun me zai hana kisa abbanta yaje can legos din ya dubo koh tana can, babanta ya mutu kuma wanda nake aure kan mu rab...." yanzu baki da aure? na daga mata kai yasa kawarta ta dubuta tunda sukaje take nemanta har wasu makarantu taje bata ganta ba nasan hakin safiyya tana da wani irin zuciya in dai ta fadi abu saita aikata nayi imani inda muka rabu tana cikin wannan halin zayyi wuya ta dawo gareni ko safiyya bata rantse ba indai tace ta bar abu to ko ta barshi har abada bare kuma ta rantse nariga nayi rashin safiyya babah da abba sun min SANADIN rabuwa da yata" bata san lokacin data furta haka ba cikin mamaki dr khadija tace suwaye? babah da Γ‚bba



πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/3/2016, 8:43 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣0⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


nayi saurin dago kai dan kwata-kwata ban san na furta hakan ba khadija bari na tafi. a,a ki bari na gama abinci nayi zaton yini zaki yi.

sai karfe uku na fito daga gidan khadija ina shiga na tadda babah tana shara ni magajiya, rakiya kin daga hankali baki taba dadewa haka ba nayi murmushi nace babah yau akwai mutane kuma malaman lafiyar bata zo da wuri ba shiya sa kikaga na dade na jawo kujera na zauna ban jima da zama ba jummai ta shigo harkin dawo rakiya? ehh hajiya na dawo.


**** **** **** **** ****

A hankali yake rukin motar cikin nishadi ya shigo cikin makarantar , kamar ance juyo bayanka ya hangi mata sanye da likaf tana nunawa wasu samari motarsa yana kokarin ya dawo baya wayarshi yayi kara ya duba cikin screen my Dady dan haka yayi saurin dagawa bayan ya gama wayar ya juyo yana kallon wajen da yaga an nuna motarsa amma babu kowa a wajen, kai kawai ya girgiza yayi gaba. yana karasowa ya tadda momy ta fito a,a aunty momy ina zuwa? bansani ba na gaya maka ka dinga kirana da rukayya in ba haka ba zamu samu damuwa yan dariya ya fito daga motarsa sanye yake da rantsatsiyar farar shadda ta kamfanin chetex kanshi babu hula sai lallausan bakin gashinsa da yasha gyara sajensa kwance luf a kyakkyawar fuskarsa, bakin ya riga ya saba amma zanyi kokarin gyarawa bari na kira maka safiyyar tana fadan haka ta juya ciki tare muka fito momy tace imran bari naje cikin makaranta wajensu sadiya minti uku.

wai safiyy baki iya gaisuwa ba? ban iya ba kuma ba zan koya ba' kiyi hakuri kanwata ki mayar da wukar kar a yanka yaya imran, murmushi nayi ina kallonsa abin kamar a mafarki yau safiyya tayiwa imran murmushi insha Allah daga yau harara ta kare. kanwata mun wuni lafiya? ba gani ba wai ma me ya dawo da kai ina ba jiya kazo ba? dan kuma na baka dama shine kullum sai ka zo" kai kanwata abin harda kari jiya banzo ba ina zaton tun ranar da abbanmu yazo muka gaisa sai yau na dawo. waye abban naka? kan babba kana karya kiya saida kazo har naki zuwa mu gaisa saida momy kuka gaisa, yana dariya yace kinga aikin bawa kanki amsa dana zo naki fito mun gaisa ba sai da momy muka gaisa, har na zo mata da budurwata suka gaisa naso ki ganta kiga yayanki koh ya iya zabe" na dago kai ina hararansa wsi kai wacece kanwar taka?? safiyya ce kanwar imran Allah ya kiyaye na juya zan tafi naji muryarsa hab yar kanwata kiyi hakuri naci darajar umma nayi saurin juyowa ina kallonsa ji nayi hawaye yana taho min nayi saurin tsungunawa, ya karaso da sauri fuskarshi dauke da tashin hankali ya tsuguna safiyya lafiya kike hawaye? nan take nasa masa kuka ya shig tsananin tashin hankali meya same ki? wani abinne yake miki ciwo? ni na bata miki rai? dan Allah kiyi shiru ki gayamin kaina girgiza mass to me yasa ki kuka? imran ummata na tuna to kiyi hakuri gobe tunda weekend ne sai muje kano kiyi kwana daya na girgiza kai ina kuka ba zani ba!! bazani ba!! ina fadar haka na mike cikin hostel ya tsaya sororo cikin mamaki har momy ta dawo yan a ganka kai daya ina safiyyar? hum momy lamarin safiyya yana bani mamaki cikin rashin fahimta tace ban gane ba, imran meye yake faruwa? muna hira daga nace mata dan darajar umma shine ta samin kuka, na tambayeta tace ummar ta ta tuna daga nace gobe zamuje taga ummanta shine fah ta hau kuka tana bazata ba tayi saurin shigewa ciki. yayi saurin bude motarsa ya dauko mata jakar rubutun, momy ga rubutun zan kiraki an jima naji me yasa kuka."



πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/4/2016, 8:32 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣1⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


karka damu imran lamarin safiyya sai addu'a momy hankalina ya tashi sosai bana so naga tashin hankalin safiyya please rukayya ki lallasheta kar kanta yayi ciwo yana fada fuskarshi cike da damuwa. ta shigo dakin ta samen na hada kai da gwiwa ina kuka ta karaso da sauri ta dago kaina safiyya me haka? ta fada cikin rudewa cikin dashewar murya nace momy umman ' to ba imran yace zai kaiki ba kince bakya so me kuma za,a miki? cikin kuka nace momy bana iya barci kullum ina cikin kewar umma amma bana fatan na kara ganinta, momy ya zanyi? hmm safiyya wallahi kiji tsoron Allah mahaifiyarki kike cewa bakya fatan ki kara ganint kan wani banzan tunanin ki da bashi da amfani.

na dago ido duk sun canza kala saboda kukan dana sha yanzu momy bakya tausayin halin da nake ciki, ya zanyi da rayuwata, momy banda jigon rayuwata, banda mahaifi dan Allah ki gayan momy ya zanyi da rayuwata gashi bana fatan na kara ganin umma duk wani bakin ciki da nake ciki itace SANADI, me yass tabi hanyar da Allah ya haramta ta haifeni ki gaya min ina zansa rayuwata? nasha gaya miki in har zaki daka ta zuciya wallahi zata kaiki ta baroki, na gaya miki baki da shaidar da zaki tabbatarwa kanki ke shegiya ce in kuma kina da ita ki gayamin, momy kakatace ta gayamin to kakarkice ta haifeki?? na girgiza kai meyass baki saurari ummanki ba ? momy in na tsaya zuciyata zata iya bugawa kinga babban kuskure da kikayi kinga safiyya mu tafi a baki da uba kin isa ki canzawa kanki kaddara?? na girgiza kai to tunda kinsan da hake me yasa kika kasa cinye jarrabawar da ubangiji yayi miki kina abu kamar ba musulma ba, ko me umma tayi miki baki da abinda zaki saka mata, safiyya kiyi hakuri ki barwa Allah komai zakiga komai yazo miki da sauki. to momy ya zanyi? wa zai aureni banida uba? baki da shaidar da zaki tabbatarwa kanki baki da uba ki bari mu koma kano kiji bayanin da umma zatayi miki in har baki gamsu ba sai ki dau matakin da zaki dauka. kaina naji ya sara nayi saurin dafe shi tare da kiran sunan Allah cikin sarkewar murya nace' momy kaina zai cire ki taimakamin ta maso kusa dani tare da cire hannuna daga kaina sannu kiyi hakuri bara na kama miki a hankali naji rage zafi, barci ya soma daukana ta mike ta tsiyayo ruwan rubutun da imran ya kawo mata, ta shafa a fuskanta sai lokacin ta tuna da katin wayar data siyo ta dago tare da sawa daman abbanta zata kira taji yaje gida kira daya tayi aka daga hello abba' muryar hajiya taji bayan sun gaisa tace hajiya ina abba? kanta bata amsa taji ana cewa ya jikin Alhaji usman din "hajiya abbane bashi da lafiya? waye ya gaya miki? hajiya yanzu naji ance miki ya mai jiki kigayan me

Please Login or Register in order to submit comment