Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune babah ki gaya min me yake faruwa yau watanmu daya kullum in kuna magana sai kutayin yaren da bana ji meye yake faruwa ki gayamin gaskiya tun da mukazo kullum kina cikin bacin rai dan Allah ki gaya min gaskiya ta dago fuskarta wanda idanuwanta cike da ruwan hawaye tace babu komai rakiya kawai suna fadamin meyasa bamu zuwa musu haba babah me yasa zaki boye min gaskiya in har wannan hausin sukeji yaci ace sun fada mana tare da harshen da zan fahimta rakiya ki bar shiga abinda babu ruwanki.







Muna cikin magana mallam maso ya shigo rakiya ta juyo wajensa dan Allah mallam ka gayamin me yake faruwa, rakiya me kika gani? Ya tambayan yana kallon babah , kullum in babah ta shiga dakin wannan matar sai ta fito tana kuka kuma sai filatanci sukeyi me dalilin? Babu komai rakiya kawai tattaunawa sukeyi.



๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook
[10/19/2016, 9:27 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

๓พ ฒ๓พ ฎ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969

www.MuhdAbbagana.blogspot.com


To mallam yaushe zamu tafi? Rakiya insha Allah gobe zamu tafi ku hada kayanku, da sauri rakiya ta mike dan ita duk ta gaji da zaman garin tana shigowa dattijuwar da take sakar mata fuska ta shigo tana dariya tace rakiya kina murna zaki gudu ki bar mahaifarki? Ta juyo wajen babah yanzu sofi in kin tafi sai yaushe? Nan take babah ta juya baki tayi magana da fillanci rakiya sai kallonsu take cikin mamaki har suka kare maganarsu.






Karshe bakwai suka rakomu tasha, shabiyu daidai muka shigo cikin garin kano mota muka dauko har kofar gida ta kawo mu koda yana zaune a kofar gida yana ganin tsayawar mota yayi sauri tashi tare da karasowa yana dariya sannunku baffa yanzu Alhaji nasir ya bar nan sai muka fara shiga gidan mallam mado habi tace rakiya kin dagawa alhaji nasir hankaki kullum ai sai yazo nan yanzu haka gobe suke shirin tafiya da kado.


Sai da mukayi sallah sannan muka fito karfe takwas mukaji sallamar alhaji nasir lokacin ina sallah sai babah ce ta amsa masa yayi saurin shigowa har yana tuntube sannunku banah kun dawo lafiya? Lafiya klau alhaji ya iyali, lafiyansu klau. bayan na idar na juyo muka gaisa muna gaisawa na mike nayi daki, sai karfe goma ya mike, nabah ina son magana da rakiya har na fara barci naji babah tana tashina kizo Alhaji zai tafi na mike ya fito yana tsaye a sororo na karasa rukkaya in sati biyu sai da akayi wata daya, fuskata a hade nace haka Allah ya tsara, rukayya ya kamata ki fara zuwa awo dan haka gobe zanzo na kaiki na mika masa ledar da babah ta ban na bashi tsaraba.
Ina komawa daki na dauko hoton safiyya ina kallo naji hawaye yana zubar mini kina ina nana ki dawo na ganki kin saka rayuwata cikin matsala ban san wane hali kike ba kina ina nana? Nan dake zuciyarta ta hau rawa tana son tayi kuka.

Washe gari kare tara alhaji nasir yazo muka tafi asibiti nasarrawa, muka nufa bayan yayi parking ya juyo yana kallona fukarshi dauke da murmushi ya zaro kudi ya mikomin karfe sha biyu zan dawo na dauke ki. Bana bukatar ka dawo ka daukeni zan koma da kaina me ka dauken ne babu aure a tsakaninmu meye kuma kake shiga rayuwata fatana na haihu lafiya ka karbi abinka cikin mamaki yace rukayya wani abu na miki kike gayamin wannan munanan kalaman? Bakayi komai ba gaskiya nake gaya maka wani irin kallo kake so ai mana ka riga ka sakeni meye kuma kake bibiyar rayuwata kana so mutane suyi mana mummunar zargi? Na gode rukayya amma karki manta kina dauke a cikina hakkina ne na kula da lafiyarki da abinda yake cikinki, to daga yau bana bukatar haduwarmu ga mallam nan shine wakilina duk wani abu da zaka bamu to ya biyo ta hannunsa na gaji da ganin fuskarka kullum muka hadu sai na tuna yata wadda kukayi min sanadin rabamu da ita". Rukayya daman kalkon da kike min kenan, naji dadi da kika gayan abinda yaje ranki amma nayi mamaki sosai da har kika iya budan baki kika gayan haka ashe zaki iya mancewa da alkhairina a gareki, ban taba zaton haka a gareki ba laifin wani bayan shafan wani uhum daman ance dan adam tara yake bai cika goma ba rukayya wani irin wulakanci da cin mutunci ne safiyya batamin ba, amma albarkacinki bana taba nuna mata damuwata ba wai yau an wayi gari dan wani abu ya faru bisa kaddara ki.......' kan ya karasa ta tari numfashinsa.


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ faceebook.
[10/20/2016, 7:57 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

5โƒฃ2โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969

www.MuhdAbbagana.blogspot.com

Tun kan ka aureni na gaya maka halin yata ka kuma yarda ka auren da yata alkhairi kuma kai kayi niyya kai mana tunda nake banta ba tambayarka wani abu ba, dan haka ka bar tunanin kayi mana wani alkairi da kai mun, in kuma safiyya kake tunani kawai alkhairi ka mance cikin sharadun aurena da kayi ta gaya maka duk abinda take so zaka yi mata ka kuka yarda in koh har yanxu wannan sharadin yana nan to duk abinda kayi mata kayine cikin sharadinku dan haka babu wani alhairi da kai mata sai sharudin da yake tsakaninku, mahaifiyarka da danka da kuma mahaifiyata kunyi min babban SANADI kuma rabani da farin cikin zuciyata ta tafi da kiyayyata a zuciyarta nasan halin nana koda zan gaya mata gaskiya ba zata taba yarda ba, duk lokacin da naga fuskarka sai na tuna nana dan haka dan Allah ka taimakamin ka daina zuwa wajena."


Naji rukayya kuma na miki alkawarin har abada ba zan kara zuwa wajenki ba, ba tare da kemeni ba duk kuma nauyin da ubangiji ya dauramin zanyi kokarin saukewa mallam ne ya ban ke dan haka zan dinga komai ta hannun mallam kar kuma ki mance da abu daya har abada ba zan taba zama SANADIN batan safiyya ba Allah yasan zuciyata na rike safiyya kamar yadda nake rike yayana.

Har abada ba zan taba cire cikin wadanda sukayi min SANADIN batan nana ba tana fadar haka ta bude motar ta fita.

File taje ta bude bayan ta gama komai taje tabi layin wadanda za'ayi wa awo tunda ta zauna babu abinda take sai tunani, ji tayi an mata sallama tayi saurin dagowa sannu mama" wata yarinya ce ta fada wadda ba zata gaza shekarun nana ba nace yauwa sannu yata tun dazun ake kiran sunanki nayi saurin tashi wani dakin zan shiga? Ai sun gama sun zaya bakya nab nayi saurin dafe kai yata yanzu bazasu taimaka suyi minba tana murmushi tace karki damu bari na yiwa babban magana sai ta dubaki to na gode ta tafi tana waigena kamar zan gudu abin ya ban mamaki ba tafi minti biyu ba ta dawo.

Mama ki shigo ta dubaki tace dani, muna shiga naga matar ta cire glass din idonta wanda da alama na kara karfin ganine ta hau girgiza kai har na karasa wajenta tana kallona ikon Allah ta furta yarinyarce ta dawo dani daga tunanin da nake momy kinga dan Allah basu kama?? Humm aysha kama sosai kamar an tsaga kara ta juyo wajena kece rukayya nasir?? Na amsa mata, meyasa tun dazun ana kiran sunanki baki amsa ba? Hajiya banji bane tana murmushi tace kina dai tunani shine yasa bakiji ba me yake damunki har akayi ta kiran sunanki bakiji ba , shawara zan baki kina da juna biyu ki rage tunani dan lafiyarki da ta yayanki yawan tunani zai iya kawo miki matsala da kuma barazana a rayuwarki kanwata komaii yayi zafi ki kai kukanki ga ubangiji wanda na tabbata zai amsa miki...........


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[10/24/2016, 8:15 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

5โƒฃ3โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969

www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Cikin sanyin murya nace na gode kuma insha Alllah zanyi amfani da shawaranki.


Ta juyo wajen yarinyar da ta kira da aysha suna hada ido tayi saurin fita. Bayan ta gama dubani na dawo kujera na zauna tana murmushi tace kinga muna ta kallonii koh? Ina zaune aysha tace taga mai kama da dady kamar kanwarsa ni kaina dana ganki nayi mamaki sosai ina son yayana sosai dan haka da naga kuna kama kema sai naji ina sonki a raina" nace haka lamarin Allah yake sai kaga baka san mutum ba amma in wasu suka ganka sai suce kana kama da wani, wanda suke fadan baka sansuba ba ka kuma taba ganinsa ba

ta zaro wani dan kati ta mikamin ga wannan duk ran daki kazo ki dinga nema na ba tare da kin bi dogon layi ba na karba ina godiya mun jima tana ban shawarwari.
Ina fitowa na samu a daidaita sahu na shiga har kofan gida ya kaini babah tana zaune tana kada abu na shigo ta hau raba ido baba me kike kallo ina alhajin da kuka tafi tare ai tunda ya kaini ya taho na karasa na zauna a kusa da ita ta mike bara na miko miki abinci.

Bayan na gama na juyo wajen baba nace nayiwa alhaji magana kan ya rage zuwa kinga babu aure a tsakaninmu bai kamata ya dinga shigemin ba har ma ya dinga kaini unguwa maganar mutane bata da dadi in haka nayi masa magana ga mallam nan shine wakilina tunda daman a wajensa ya aureni duk wani hakkina ya dinga bashi. Babah tayi saurin katse ni kice kin koreshi ya barki da wahala kinyi daidai kin kyauta bab...." kinga yi min shiru har kinda da maganar da zaki gayamin wayasan abinda ki kayiwa alhaji mukhtar ya barki da yarki gashi yanzu ta gudi ta barki shine wannan ma kike so ki cuci abinda zaki haifa, kina ganin nan gaba haka zaki zama mana tashin hankali ina hawaye na dago babu auren na kuma ga kullum yana gidannan zai iya zama matsala ayi mama mummunar zato
Sannu wadda bata so ayi mata sharri ke gak...." kan ta karasa mallam ya shigo naji duk maganar da kuke rakiya tafiki gaskiya tasan meye rayuwa kuma yanzu alhaji nasir ya bar wajena mun gama magana don haka ban san na kara jin kina wata magana mara amfani ya juyo wajena ke kuma maganar da zsn gaya miki karki dora SANADIN batar safiyya a wuyan alhaji nasir ki dora SANADIN batan ta a wuyan magajiya, to inda bata gaya mata wannan mummunar zancen ba babu abinda zaisa tabar gabanki kuma kici gaba da kai kukanki wajen ubangiji har Allah ya juyo da hankalinta ta dawo wajenki.
Ya miko min kudi munyi da alhaji nasir duk wata zai dinga kawo kudin abincinki gashi kuma ya bayar wannan ko bakida lafiya za'a dauka a sai magani sannan kuma da zuwa awo, don haka dukk wata zai dinga zuwa ya kawo.
Ni dai bance komai ba nasa hannu na karba dan basune a gabana ba tunanin yata ya cikemin zuciya.
Ina kika shiga safiyya ki taimaka ki dawo ina maganar cikin zuciyata ashe har ta fito fili maganar babah naji daga baya tace: yanzu ko kunyata bakya ji kike fadar haka? Nayi saurin juyowa babah ba magabar da nayi ta hau salati yanzu bakin san kina maganar safiyya ba? To Allah ya kyauta miki wallahi in baki rage tunaniba, sai ciwon zuciya ya kamaji tana fadar haka ta shiga cikin daki.


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[10/25/2016, 9:16 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

5โƒฃ4โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969

www.MuhdAbbagana.blogspot.com

www.abbagana.blogmr.com

**** **** **** **** ***

waike malama ba kya jin wayarki na karane? na dago fuskata a hade nace ina jinta toh zaki daga bane? momy bana raayin dagawa in kinsan bazaki daga ba meyasa kika bada lambarki? wa nake bawa numberta? wannan dinnan ne da yake kirana wai bashi da sunane? ta fada tana haranta wanda yazo ranan oh muhammad na daga kai, mikomin wayar banyi musu ba na miki mata; Assalamu alaikum, muhammad kana lafiya? lafiya klau aunty momy safiyya bata nan ne? muhammad tana toilet ne ya akayi? aunty momy daman ce mata zanyi yau zanzo mu gaisa ta kuma ki dagawa" kayi hakuri kasan babyn tawa sai na kaita an duba kwakwalwarta ina tunani akwai matsala me yasa kikace haka aunty momy? to muhammad inna gaya mata magana bata yarda ga dan banzan taurin kai, dan haka dole na kaita a dubata yana dariya yace shikenan innazo sai muyi maganar inta fito ki mikamin gaisuwata okey muhammad muna jiranka ka gaida mutanen gida tana gama wayar ta juyo tana kallona banda ruwan hawaye babu abinda yake bin fuskat kan tayi magana na katset momy ni kike cewa banda hankali zaki kaini a dubani koh? kai tsaye taban amsa to kina da hankalinne? na girgiza mata kai na mike zan fita jinayi kamar zan fadi nakai hannuna na dafe kaina da sakin wata razannaniyar kara wannanda harnima ya razanani๐Ÿ™‚.


A hankali na dinga kokarin bude idona naji na kasa hannu na kai fuska naji wani sassanyar murya ta doki zuciyata sannu safiyy.

kin tashi abin kamar a mafarki naji muryan ba shiri nayi saurin bude idona ina kallonsa tare da juyaw ina kallon inda nakw kwance ban wahalar da kwakwalwata ba wajen gane inda nake ba wata asibiti to waye ya kaw....... maganarshi ce ta dawo dani daga tunani sannu safiyya bara na kirawo likita ya dubaki momy ce ta shigo najuyo wajen tare da fadin me ya kawoni asibiti, bakya jin dadine shine na kira muhammad ya kawo mu asibiti inajin haka nayi saurin mikewa ina kokarin saukowa daga gadon ta karaso da sauri"meye haka bakya ganin drip ne a hannunki. na juya ina kallon hannu na kai zan cire naji an rike hannun "karki cire safiyya ki bari ya kare." na zabga masa harara bazan bari ya kare ba meye ruwanka da rayuwata."


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ faceebook.
[10/25/2016, 9:41 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

5โƒฃ5โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969

www.MuhdAbbagana.blogspot.com

na juyo wajen momy nace ce miki nayi banda lafiya da zaki dauko mara hankali ku kawo asibiti ta rike hannuna tana murmushi am sorry nasan nayi laifi a min afuwa. na juyo wajensa kasake min hannu ko nidin ba yar isaka bace irinka nika dakain zan bada shaidar haka amma kiyi hakuri ki bar drip din ya kare kyaji karfin jikinki, dan Allah ki taimaka safiyy yana maganar yana girgiza kai cikin tsawa nace to hannunka ne da ba zaka sakar min ba? to kimin alkawarin bazaki cire ba ki taimaka kanwata. waye kanwartaka? kiyi hakuri don Allah kibar drip din nan momy tace muhammad sakar mata hannun bara na kira abba shi yayi mata magana.
ta zaro wayarta tare da kiransa kira daya a dauka hello Abba bayan sun gaisa take gaya masa tana gama gaya masa ta sa wayar a kunnen naji muryansa safiyya kiyi hakuri ki bari ya kare. abba ce min tayi fah bani da hankali kinga ki rabu da ita ranar monday zanzo amma ki bari ruwan ya rake saiku tafi kinji yat ina kuka nace to abb yayi saurin cewa bana son kukan nan kiyi shiru kar kanki yayi ciwo ina jin ya katse na kaudar da kaina na kwanta momt tace har kun gama banko tankataba na mayar da idona na rufe baby bara naje na samo miki abinci.


ya karaso ya tsugunna kiyi hakuri safiyya me nayi miki kike min haka? ki tausayamin safiyya duk wanda yake nuna maka kulawa bai kamata ya zama abin gudunka ba dan Allah ki tausayamin na yarda bakya sona amma ki amince na zama dan uwanki ki ban matsayin yayanki koh kaninki na miki alkawarin maganar soyayya ba zata taba shiga tsakaninmu ba har abada, dan Allah ki tausayamin duk maganar da yake idona suna rufe sai da naji muryarsa tana rawa yasa na bude idona cikin dabara ba tare da ya gane ba, ji nayi kirjina yana bugawa sakamakon ganin ruwan hawaye a kwance cikin kyakkyawan fuskarsa.

Dan Allah kiyi magana safiyya ko zanji dadi ki gayamin kin amince mu dinga gaisawa.

bansan lokacin da bakina ya furta na amince, yaji maganar kamar cikin barci yayi sauri dago kai yana murmushi safiyya na gode, na gode ya mike da sauri bara na kira likita. momy ta shigo tare dasu sadiya. farida tace yanzu wannan ce mara lafiya? ruky kika wani daga hankalinki haka, na juyo ina haranta sadiya tace sannunki kam nasan ciwon love ne kawai tana kunyar gaya mana amma ba komaii ni zan shigar dake, ban ko mata magana ba.


sallama yayi tare da shigowa shi da wata nurse, ta karaso wajenta bayan ta gama ta fita sadiya ta juyo wajen muhammad tana dariya yau daiga muhammad angon safiyya rike baki yayi yana dariya sadiya bar fadan haka kar kisa ta janye amincewa da mukayi yanzu yana maganar yana kallon agogo dake jingene a sama. karfe takwas ruwa ya kare na azakzali momy taje takirasu a ciremin....



๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[10/31/2016, 8:01 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

5โƒฃ6โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969

www.MuhdAbbagana.blogspot.com


bayan ta gama waya ta juyo waike malama ba zaki bari ya kare ba kin..... kan ta karasa nasa hannuna na cire da kaina, na shiga uku me yasa kika cire na mike tsaye niba ce miki nayi banda lafiya ba kuka kawo ni nan, wai ya akayi kuka kawoni ina barci? abin ya baya momy mamaki ta tabbatar abinda zuciyarta take gaya mata tabbas saffiya tana da matsalar aljannu ina mafita ta tambayi kanta kan ta samu mafita maganarta ne ta katse mata tunani.
momy ya akayi kika daukoni ina barci? toma ya akayi nayi barci kinga bara na kira dr a dubaki tana fita muhammad ya shiga safiyya har ya kare na daga masa kai ina aunty momy ya tambayeta taje kiran likita okey bari nayi sallah nazo mu tafi.


momy ce ta fito bako sallam ta juyo tana kallon muhammad tace gaskiya muhammad ina ganin ciwon safiyya bana zuwa asibiti bane cikin mamaki ya juyo rukayya saboda me kikace haka? nan take ta gaya masa maganganun da sukayi da safiyya ya girgiza kai to momy wannan wani irin ciwone? kan ta bashi amsa ya cigab sa cewa ina ganin tan da mutanen boye, nima haka nake tunani yaceto ina mafita tace kaine zaka samar mana mafita mu din wa muka sani a garin nan? yadi minti uku baiyi magana ba can yaja dogon numfashi shikenan rukayya zanyi duk wani kokari don neman lafiyar safiyya.shikenan muhammad na gode rukayya me abin godiya? muhammad sole na maka godiya yana dari yace aunty momy imran shine sunana na gaskiya ina amfani da muhammad ne dan kada safiyya ta ganeni tace ban gane ba au momy baki da labarin aljani imran da yake kiran safiyya lokacin da kuke makaranta, ta rike baki tana dariya kaine imran aljanin wayar safiyya? kai ya daga amma kaban mamaki kaine mutumin da ya haukata baby gaskiya saina gaya mata anty momy ki rufan asiri karkija a janye alkawarin da aka min. wani alkawarine daban sani ba? na gaya mata babu maganar soyayya tsakaninmu da ita za dai mu dinga gaisawa hmm lallai imran har yanzu baka san wacce safiyya ba bara naje daki kada ayi minu fushi okey aunty momy gobe zanzo hudu na yamma amma kan sannan zanje wajen wajen malami nayi masa bayani.
ina sallah ta shigo toilet ta zarce ta dauro alwala ta fito bayan ta idar ta juyo shine kika wucw bako salkama? to momy dole ne sai nayi sallama? babu sole amma kin masa alkawarin zaki dinga sauraransa ku dinga gaisawa kuma kinsan muhimmancin alkawari to inya dawo wata rana zan masa sallama

Please Login or Register in order to submit comment