Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halin da ya shiga haka.Shi ma Yaya Dahir ya ce, ‘Kanwata ina da
yancin zabar miki miji don haka na zaba miki yayanki a matsayin miji ina fatan ba za ki ban kunya ba.”
Na daure na yi murmushin da bai kai zuci ba ganin yadda kowa yake ta magana. Ni dai kaina na kasa. Safiyya ya
ce babu wanda zai wa ‘yata auren dole ya zama dole Imran ya sake ta a yanzu-yanzu.Tunda suka fara magana bai
daga ko idonsa ya kalle su ba sai yanzu da ya ji maganar da mahaifinsa ta furta ya juyo a razane ya dago kansa.
Idonsa fal da ruwan hawaye, yana kallon fuskar mahaifin nasa ya kara kwatsa masa tsawa.“Maza ka sake ta kamar
yadda ki kai bisa sharadi?” “Ba zan iya ba Dady ba zan taba iya budar baki na saki Safiyya ba ku bari in ciwon
sonta ya kashe ni Dady ko a mafarki bana fatan bakina ya furta kalmar da za ta batawa Safiyya rai bare ta kai
mu...”Kan ya karasa Alhaji Nasir ya katse shi da cewa, “Ka yi shiru da bakinka Imran insha Allahu babu wanda zai
raba ku da matarka taso mu je waje ka ji.Bai yi musu ba ya bi bayansa.Kiran sallar da aka yi ne ya tashi kowa. Muna
fitowa daga falon na bi bayan Abbana ya juyo da sauri Lafiya Safiyya? Sai da na waiga na ga babu kowa a bayana sannan
na karasa gabansa na fara kuka. Ya dago fuskata.‘Me ye ya saki kuka, muna cikin farin ciki za ki bata ranki? .Cikin
shagwaba na ce, “Ni fa Abba bana son sa Allah in kuka auran shi zan iya mutuwa.”“Kin ga ki bari in mun je gida ma yi
wannan maganar, yanzu ki shiga ciki ki yi sallah.”Ni dai ba zan koma ba gida zan tafi ka ban key din motarka.”“To ita
Rukayyar fa....” Kan ya rufe baki ya hango tata taho inda muke. Ta karaso.“Kin dagan hankali ina ta nemanki ashe kina
wajen Kawu kamar zai gudu.Abba ya ce, Kin ganta tana rigima har da kuka wai sai ta tafi gida.‘Uhum Kawu na dago ta fa
bara mu je gidan kawai.
Ya zaro key din motarsa ya miko mana.Na ce, ‘Abba wajen Ummata za mu.Muma yanzu za mu taho.Muna fita daga gate din gidan
muka hangi Yusuf (yayan Imran) ya daga mana hannu muka tsaya na juyo ina kallon Momy kan ya karaso na ce, ‘Me ye
na tsayawa dan ya daga mana hannu?' Ta juyo tana harara ta sannan ta ce, “Saboda ya cancanci na tsaya masa ne.
Kan na yi magana ya karaso fuskarsa dauke da murmushi sai na ga suna matukar kama da Imran.Ya na ga za ku tafi ba
za ku tsaya mu tafi tare ba?” Ya karasa magana yana kallon Momy.Ta ce, “Amaryarku sannan ‘yar shagwabar Abba ce ta
ce sai mu je ta ga Umma.Ya dago yana kallona.‘Kanwata ba za ki kira angon naki ya kai ki ba, kin san yayanki cikin
damuwa. Ina fatan za ki tausaya masa Ya juyo wajen Momy.ina son mu yi magana ga shi kun fito, in babu damuwa ina
bukatar number wayarki. Bayan ya karbi number ta ya zagayo wajen da nake ya yi kasa da muryarsa ya ce, “Kanwata
ina fatan za ki shigar da ni wajen Antyn taki a hada mu a sha biki.” Yana fadar haka ya juya cikin gida.
Na juyo wajen Momy ina murmushi na ce, ‘Ina fatan ya samu karbuwa.Kai tsaye ta ce, “In har Imran ya samu karbuwa
a wajenki to nima Yusuf ya karbu.Nan da nan na hade fuska har muka karasa ban Kara yi wa Momy magana ba. Tana yin
paking na fito, ina shiga muka ci karo da Hassan na yi saurin surarsa ina dariya.“My Boy ina Umma da Hussaini? Kai
masa wayo kana gudu ka bar shi yana fama da rarrafe ko?” Ya wangale baki yana dariya. Na karasa ciki yana hannuna.
Umma tana jin sallamata ta dago da saurinta muna hada ido ta mayar da kanta kasa na karasa gabanta na rusuna na ce,
Umma mun yini lafiya Ta ce, ‘Lafiya kalau. Ina ki ka baro su baban?” Kan na yi magana Momy ta shigo. Umma ta kara,
tambayarta ina su baban? Momy na dariya tace su baba suna can gidan cikin farin ciki yanzu ma zasu taho nace umma
yunwa nakeji ta mike bara na kawo muku abinci tana fita momy ta dawo kusa dani fuskata a hada tace: wallahi safiyya
kije tsoron Allah me imran ya miki kike masa wannan muguwar kiyayyar ina guje miki ranar da imran zai rama abinda kike
masa kin san a yanzu ko zaki mutu ba za a raba aurenku da Imran ba. Ina baki shawarar ki janye wannan kiyayyar da ki
ke wa Imran ta baki don na san zuciyarki ba haka ba ne zan iya bada shaidar kina mutukar kaunar Imran ina fatan za ki
taimaki kanki ku zauna lafiya da mijinki tunda yanzu magana tarewa za a yi mu....Kan ta karasa na katse ta da cewa,
In ke ce Abbana ko Ummata sai kisa na zauna da shi.” Ina fadar haka na sa mata kuka. Ta dago tana harara.‘Dan kin ga
in kin yi kuka ina lallaba ki to yarinya ki yi kukan jini, wallahi ba zan lallaba ki ba, kuma insha Allahu sai Allah
ya zuba miki kaunar Imran a zuciyarki, kina ab....Shigowar Umma ce ta hana ta karasawa ina mike ina kuka na yi cikin dakin,
Umma ta bi ni da kallo cikin mamaki.Momy ta ce, “Allah Umma, Safiyya ba ta san gaskiya duk wanda ya ga Imran sai ya tausaya
masa, ‘yan uwanshi sai lallaba ta suke amma ta ki kula kowa karshe ma Kawu ya fito zai sallah ta biyo shi tasa masa kuka sai
mun tafi gida shine ma fa yanzu muka taho, kuma Umma an gano baban Imran din shi ma dan baba ne, ita ta haife shi tun yana yaro
ya bata. Kin ga Imran ya zama yayanta ga zum...Kan ta karasa suka juyo hayaniyar su Baba, yanzu ma gaba dayansu suka taho.
Abbana, Alhaji, Nasir, Alhaji Salisu, Dahiru, Yusif, Doctor Khadija, Imran, Hajiya Amina, Khadija, Malam Mado Baba ga kuma
Malam Khalil.Umma ta bi su da kallo cikin mamaki har suka gama shigowa. Umma ta bi kowa da gaisuwa, Alhaji ya kalli Malam
Mado ya ce, “Baffa wannan ce kanwar tawa.” “Ga ta nan kanwarkan kamarku daya babu abin da yarabaku.Doctor Khadija ta ce,
Tun farkon zuwanta nake gayama tasunakama da ‘ya’yana.Malam Khalil yace, “Ina matar tawa ne ina ta raba ido ta fito mu yi
sallama?”Momy ta ce, “Malam tana cikin daki kanta ne ke ciwo ina tunanin barci ta yi.Yace, “Allah yasawake, ga wannan kiba
ta tayi shirin tare wa bazan kuma zuwa ba sai ranar da za a kai min ita.” Yana fadar haka muka sa dariya.Ya jima yana nasiha
mai ratsajiki tare da wa’azi, sannan ya mike bayan yayi wa kowa sallama Dahir ya mike yazo gaban Baba yana murmuishi, yace,
Kaka ban gaji da ganin ki ba barana kaiMalam filin jirgi.” Bayan fitarsu Umma ta mike ta yi cikin daki, hakaAbbana tare da
Alhaji Nasir sukafita, sannan Doctor Khadijah ta tafigida, domin girkin tarar maigida da ‘yarta Aysha wadda take karatu a
ABU. Ya rage daga Malam sai Abban Imran da Hajiya Amina, sai Malam Yusif, Imran, Khadijah sai kuma Momy.Abban Imran yace,
Baffa sai mu yi shirye-shiryen zuwa can Adamawar.Yusif yace, “Don Allah Dady mu tafi gobe, daman ina san mu dinga zuwa wani garin.”
Malam yace, ‘Dukkanmu zamu hadu mu tafi, in munzo mu hudu sai da shanunmu za mu koma mun zama da yawa.Hajiya Amina ta ce,
Kan mu tafi sai a yiwa Aysha waya ta tafi, don dukkanmu za mu tafi.Dahir ya yi sallama ya shigo yana kallon inda Imran yake
zaune kusa da Baba ya zauna sannan yace, “kai me ye haka dukka bi katakura kanka, baka san nan gidan ka bane kana tare da
matan ka biyu tsohuwa da sabuwa Baba ta ce, ‘Ai kaine mijina ni bazan iya kishi da takwara ta ba gara damatarka.Imran yadan
yi murmushi yana kallon fuskar Momynsa, sannan yace brother bana jindadin dadin jikina ga kuma fushin da su Dady suke da ni,
don Allah Malam ka sa baki suyi hakuri su daina fushi da ni, kalli Momy sai harara ta take ya zanyi da raina duka biyu nikam
bazan bi su mu koma Lagos ba a wajen ka zan zauna har sai kun ban matata Safiyya.Malam yace, “Kama daina maganar Safiyya, tuni
Safiyya ta zama taka lokaci kawai za a tsayar mu yibiki. Abbanka in har yana farin cikin ganin mahaifiyarsa to ya daina fushi
da kai, ita Hajiyar in tana taya shi farin ciki to za ta daina fushi da kai.Barrister Amina ta yi murmushi sannan ta ce,Wallahi
Malam ina matukar farin ciki da samunku a matsayin iyayen mijina gaskiya, a da na yi niyyar daina fushi da I mran don duk cikinsu
shi ne dan lelena, bayyan nan safiyya matsayin yata yasa bazan daina fushi da shi bahar sai Safiyya ta yafe masa, kuma in har ta
ce ba ta san zama da shi to ya sake ta shi ne kawai zai sa na daina fushi da shi.Dady yace, “Kin yi daidai Amina nikaina bazan yiwa
yata auren dole ba, in ba ta son sa dole yasau wake mata. To gayan wanda take so na aura mata? Ya dago idonsa cike da rowan hawaye
yana kallon Dadynsa muryarsa narawa yace, “Don Allah Dady karkayi min haka wallahi Safiyya tana sona kunyar ta fada take kuma kutambayi
kawarta.Baba ta ce, ‘Ai kaine mijina ni bazan iya kishi da takwarata ba gara da matarka.



🅰bbagana hausa novels@ facebook.
[12/24/2016, 9:44 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

8⃣8⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Sai karfe takwas muka fito za mu tafi har Khadijah, Momy da Dadyn Imran za su kwana gidan Baba,
Doctor Dahir ya tafi Nassarawa. Mu kuma Yusif da Imran za su kai mu a motar Dadynsu.Tun da muka
shiga Momy da Khadijah suke hira, Imran kuma da Yusuf ni daya ce na yi shiru. Yusif sai tambayata
yake lafiya? Muna shiga gate din gidan kan motar ta gama parking har na fice, Khadijah ma ta biyo
bayana.Imran ya juyo yana kallon Momy fuskarsa cike da damuwa ya ce, “Rukayya anya ko za mu sami masauki a gidan nan, duba ki ga irin kallon da Safiyya take min.Ta dan yi murmushi, sannan ta ce,Kar ka damu Imran za mu shigo ciki.Ni kam ina shiga muka yi dakin Baba Binta suna tare da Abbana, na yi sallama muka shiga. Baba ta ce, “Yar halak yanzu muke maganarki an kusa shirin bikiniku.”
Khadijah ta karasa gaban Abba suka gaisa. Na ce Baba kanwata ce fa.Ta dan yi murmushi, Allah Sarki Muntari ya ban fari ciki ai da an gan ku an ga ‘yan uwana. Momy ta shigo tana harara, baba ta ce,
Ke kuma lafiyarki kin shigo kina faman zare ido.“Kin ga ni ba zan miki magana ke goyuwa ki ke da bayanta.” Ta juya wajen kawu ta ce, “Dan Allah Kawu ka fadi gaskiya.” Shi dai murmushi yake ya
dukar da kai.Kawu tare muke da su Imran su biyo mu za su kwana tunda muka shigo take harare-harare, yanzu muna shigowa gate kan a karasa parking ta fice inda tsautsayi ta fito za ta iya faduwa ta ji ciwo fa Abba ya hada fuska yana kailona wannan gangancin kina harara, to wa ye ki ke harara duk motar yan uwanki ne.Baba ta karashe da cewa, “Bare kuma har da mijinki maza Rakiya ku shigo da su.” Na dago da sauri ina kalion Baba.Abba ya ce, “Baba rabu da Rukayya ta huta ita ta jc ta shigo da su.”
Na yi saurin dagowa ina kalion Abba nace, “Abba ni zan shigo da su.Ya Kara hade fuska, “To da da wa nake maza ki shigo da su.” Na mike na fita.Suna tsaye a jikin mota na karasa ina kalonn Yusuf, kwata-kwata na ki kalion inda Imran yake. amma ina ji a jikina Imran yana kallona. Na daure na
saki fuskata na ce. Yusuf ku shigo.Kanwata muna shirin juyawa ne." Na dago kaina ina kallonsa na ce,
Saboda me za kujuya? Ya ban amsa da saboda bamu samu fuska a gurin kanwarmu ba, tunda muka tawo taki
kula kowa, kin ga gara mu juya. Na dan yi murmushi.Kaina ke ciwo Yusuf, amma yanzu ya warke zan maka hira har sai ka kore ni.Cewa za ki yi za ki mana hira sai mun kore ki tunda ga Imran ko? Na dan juyo na kalle shi cikin sa’a muka yi ido biyu na ko zabga masa harara, sannan na juyo wajen Yusif ina girgiza
kai Ban kula da mutum a kusa da kai ba Ina fadar haka na juya tare da cewa Abba na jira Yusuf ne ya bi bayana shi kam Imran yayi shiru yana tsaye saboda bakin cikin da ya cika masa zuciya. Wanan wacce irin kiyayya Safiyya take min haka? Ya ya zan yi da son wadda ba ta sona? Ya Allah ka kawo min d'auki,
wannan masifar bar ina...“Imran! Imran!! Imran!!!” Ya ji muryar Abban Safiyya yana kiran sunansa. Ya dago kansa da sauri kamar wanda ya tashi daga barci ya yi saurin tsugunnawa yana gaishe shi. Abba
ya dafa kafadarsa cikin tausayawa ya ce, “Haba Imran kai da ka ke namiji bai kamata a ce ‘ya mace tana
saka kana zubar da hawaye ba, kar ka kuskura Safiyya ta ga hawaye a fuskarka za ta raina ka. Bara na
gaya maka daga yau ka rabu da Safiyya kwata-kwata ka fita a hanyar ta.Ya dago da sauri bakin shi na rawa
ya ce, “Please Abba kar ka raba ni da Safiyya in ka raba mu ban san ya rayuwata za ta kasance ba, don....Hannunshi ya kama muna falo suka wuce tare da Abba, har dakinsa suka shiga. Kan Imran na kasa Abba ya ce, Imran bana nufin in raba ka da Safiyya, kuma na fi kowa murna da ka zama mijinta. Alhaji Nasiru ya gayan
kwanan nan ka dawo daga karatu, shin ka samu aiki ne? Ya ce, “Na samu Abba tun washe garin da na dawo a U.B.A Bank, kuma kwanan nan na karasa ginin gidana a Bietoria Island To masha Allahu abin da nake so na ji daga bakinka kenan. Don haka in har ka s hirya rana ita yau safiyya zata tare a gidanka. Don farin ciki bai san lokaein da ya mike tsaye ba, ya yi saurin zubewa gaban Abba yana godiya Me ye abin godiya Imran?
Ina fatan za ka rike Safiyya da amana ko babu aure tsakaninku Safiyya kanwarka ce. Ina kuma ba ka hakuri
kan abin da Safiyya ta ma a baya kar ka ce za ka rike shi a ranka.‘Abba ban taba rike abin da ya faru
tsakaninmu da Safiyya a raina ba, kuma...." Ya dan yi shiru.Abba ya ce, “Ka yi magana mana ko a kara lokaci ka yi shirin ka? Da sauri ya ce, “A’a Abba na gama shirina gobe ma zan tafi Lagos din, daman maganar su Dady nake tsoro.” Abba ya dan yi murmushi, “Kar ka damu gobe zan je na samu Dadyn naka za
mu yi maganar, kuma duk wani shiri da za a yi za a yi shi cikin ‘yan kwanakin a yi komai kowa ya huta, kar ka damu kanka fatana ka rikc Safiyya da amana kanwarka ce ni kuma ita daya Allah ya ban ina fatan za ka zauna da ita tsakanin da Allah.‘Wallahi Abba na maka alkawarin zan rike ta tsakani da Allah, ina kaunar Safiyya tsakani da Allah ba zan taba cutar ta ba. Zan kuma yi hakuri da duk abin da za ta yi min har zuwa lokacin da za ta kaunace ni. Imran safiyy tana kaunarka kuma nan gaba za ka ga haka.”Ya mike “Na gode Abba bara na je falon mu gaisa da Baba.” Ya fito fuskarshi cike da annashuwa. Khadijah ta ce, “Brother lafiya ka ke jin dadi kai daya? Ya juyo da sauri dan bai san ya shigo falon
ba suka hada ido da Khadijah “Uhm! Sister kawai zuciyata ce cikin farin ciki shi yasa ki ka ganni haka, raka ni dakin Baba mu gaisa.” Kwata-kwata bai kalli inda Safiyya take ba, abin da ya bawa Yusuf mamaki, haka Momy. Khadijah ta mi ke suka shiga cikin dakin.Khadijah ta ce, ‘Baba ga imran din ya zo gaishe ki tare kuma da ban hakurin abin da ya faru a baya, bar ma kuma da kokon bararsa.” Ya tsugunna a gabanta suka gaisa.“Komai ya wuce a wajenmu tunda abu ya faru a rashin sani, mu kam mun riga mu baka.Ya kara sunkuyar da kansa kasa yana godiya, hannunsa ya zura cikin aljihunsa ya zaro rafar dari biyu ya dire mata. Sannan suka fito falon.“Anty Momy yunwa nake ji.“Tun dazu abinci yake jiran ka a dinning table, kai daya mukejira.Na mike da sauri na je dinning table din na na debo nawa na dawo na
zauna. Yusuf ya juyo.Kanwata ya kika debo naki ke daya? Na dan tabe baki na ce, bana sakewa a dinning gara nan.Momy ta ce. “Ku tashi mu je ku rabu da ita.Washe gari har wajen yamma ban ga Imran ba, sai Yusuf
da Khadijah. Muna falo su Momy suna hirarsu. Wayar Yusuf ta yi kara ya zaro da sauri ya daga.Hello Brother
ka sauka?" Ya dan jima suna wayar sannan ya ajiye. Khadijah ta ce, “Ya sauka?‘Tun dazu ma ya sauka wayar
shi ce ba caji.Jibi za ta taho kun san abin ya zo a korarran lokaci? Momy ta ce, “Nima jiran Sadiya nake
mu yi shirin da za mu yi kar lokaci ya kure, sai ta waya nake gayawa kawayenmu.Karfe tara har na kwanta,
Abba ya yi kirana na shiga dakin tare da yin sallama. Bayan na zauna Abba ya ce, “Safiyya kin yarda da ni a matsayin mahafinki?” Na daga masa kai.“Yauwa Safiyya kuma kin san duk wani uba nagari ba zai kai ‘yarsa
inda za ta wulakanta ba. Yana burin samar mata miji nagari, wanda ya yardada nagartarsa, ya kuma yarda da Addininsa. Kuma kina sane da cewa duk; abin da Allah ya zaba maka zai zama alkhairi a gare ka.” Na kara
daga masa kai.‘To Safiyya Allah ya zaba miki Imran a matsayin mijinki na aure, ina fatan za ki karbi zabin
Ubangiji da kuma abin da nake so.Na dago a razane, muryaryata a sarke na ce, “Abba kana nufin ba za ka raba auranmu da Imran ba? Cikin karfin zuciya ya ce, “Ba zan ja da abin da Ubangiji ya kaddara ba amadadin hakan ma ranar Lahadi za a kai ki gidansa kin ga sai ki yi bautar kasarki a can. Ina fatan ba za ki ban kunya ba
a matsayina na mahaifinki?Na dago fuskata cike da hawaye na ce, ‘Abba ba zan taba ba ka kunya ba, zan maka
biyayya, zan zauna da Imran ba don ina son shi ba, sai don na faranta maka.Ina fadar haka na sunkuyar da
kaina na fara kuka.Kar ki yi kuka Safiyya, na fasa hada ku tunda ba kya so, shi kenan kin zabi mutuncina
ya zube kuma kin za6i na rasa Ummanki?Na dago kaina. “Ka yi hakuri Abba zan yi maka biyayya bana so ka rasa Ummata na maka alkawarin zama da Imran ka yi hakuri in na bata maka rai. Ina san kasan cewar ka tare da Ummata zan yi duk abin da ka ke so don na faranta maka.” Na yi shiru ina ajiyar zuciya Shi kenan Safiyya Allah ya yi miki albarka, sai ki je ki sami Rukayya ku yi duk shirin da za ku yi.


🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/25/2016, 4:32 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

8⃣9⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Ya zaro kudi cikin lokar gadonsa.“Ga dubu dari biyu ki rike kin ji ko za ki yi
wata bukatar in ma sun muku kadan sai ku gayan.Nasa hannu na karba. Har wajen
karfe goma ina dakin Abba yana min nasiha mai ratsa jiki, sannan na flto babu kowa a falon don haka kai tsaye na yi cikin dakina.Tuni Khadijah ta yi barci sai Momy da take waya. Ina shiga ta dago tana kallona na karasa cikin dakin, na samu gefe na zauna, Ina zama na ci gaba da kukana, Momy ta katse wayar ta matso kusa da ni ta yi kasa da muryarta kamar mai rada ta ce.“Don Allah Safiyya
ki nutsu ni wallahi ban taba ganin mutum irin ki ba, haka kawai don masifa ki tsani mutum ban ga laifin da ya yi miki ba, duk abin da za ki yi yanzu Imran ya
zama dan uwanki da Ummanki da mahaifinsa uwarsu daya ubansu daya. Yanzu don Allah
ba za ki ji kunya Khadijah ta farka ta ga kina kuka akan ba kya son dan uwanta ba?
Haba Safiyya ya kamata Imran ya ci darajar Ummanki don Allah ki daina nuna masa kiyayya haka. Kalli irin kaunar da iyayensa suke miki, kalle irin soyayyar da kanwarsa take miki, ta bar iyayenta ta taho wajenki amma duk ba ki ga wannan ba. Ni ban ga mummunan
laifin da Imran ya yi miki ba da har ki ka daukar masa wannan matakin ba, ya kamata ki kai kukanki wajen Ubangiji ya yi miki zabi mafi alkhairi ba ki zauna kina kuka ba.Na dago fuskata idanuwana duk sun kumbura na ce, “Ni Momy na rasa ya zan sarrafa zuciyata taso Imran in....Ta katse ni da cewa, Baby kina kaunar Imran kuma nan gaba za ki yarda da abin da na gaya miki. Na bude baki zan yi magana ta katse ni, ‘Mu bar maganar nan yanzu shirin biki za mu yi don maganar da muke da Yusuf kenan ki ka shigo.Na dago ina harararta.“Ni babu wani shiri da zan
yi don ta nima kada a yi komai ga kudi in ji Abba. Ina mika mata na haye gado na kwanta. Tunda na yi sallar Asuba na koma na kwanta har wajen karfe tara ina kwance, hayaniyar Salim ce ta tashe ni na dago ina kallonsa.‘ Amarya kin sha kamshi.Na dan harare shi na ce, Ka zo ka katse min barci za mu hau court, ni ba amarya ba ce, Sadiya ce amarya.Ya sa dariya Da kin ki da kin so dole mu kira ki da amarya. Ni da kin taimaka kin yi wa Kawu magana a hade
bikin da nawa da kin ga gama min komai.Na ce, “Ka ga don Allah ni ka rabu da ni ban tashi ba,
ka je tsohuwar matarka tana kiran ka.Ya juyo yana dariya har ya kai bakin kofa ya juyo. Ki fito muyi shirye-shiryen party.” Na daga masa kai.Sai karfe sha biyu na farka, gidan shiru.
Na yi wanka na fito na nufi dinning table na yi break fast, sannan na shiga dakin Baba.
Yanzu nake shirin shiga na ga lafiya

Please Login or Register in order to submit comment