Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki shiga. Ina tunanin saura sati biyu ya dawo. Kana sa ne da tafiyarmu Kano rana ita yau?" "Au Momy ranar Monday za a fara shari'ar?" "Ranar Monday za mu fara, har Khadija ta gayawa Aysha za mu zo Kano da kai dazu muka yi waya da Hajiyar sabon gida sun fara damuna yaushe za mu taho." Yana dariya ya ce, "Nima shckaran jiya na kira nake tambayarta ina tsohon mijinta na
ce ta gaya masa in dai na zo Kano sai na karasa shi, tunda ya ki ya mutu mu ci gado.""Hum maza Abbanku ya ji kuna fadar haka, shi bazai so ya mutu ba."'Allah Momy ya dade shi da Malam."'Ai ka dawo kaina, to tashi ka fita. Kai da yan uwanka kuncinye uwata, shi ma malam din cinye shi za kuyi Ya mike yana dariya."Momy sun sha miya gara su mutu."Kan ta yi magana ya fita da sauri.Babu abin da ka ke ji cikin dakin sai
sautin kukana, ina can a karshen gado. Yau kusan .kwana biyu ban ga Imran ba. Duk wata dabara da zanyi don na bar gidan nan na yi, amma ban yi nasara ba. Tun jiya nake fama da zazzafan zazza6i ban da karkarwa babu abin da jikina yake sai kuma sautin kukana da yake tashi.Ya turo kofar tare da yin sallamaduk tsananin
kiyayyar da nake wa muryarsa a duk lokaci. da ya yi sallama saina amsa masa a zuciyata. Ya karaso gefen gadon ya
zauna. Hannu yasa ya janye bargon ganin fuskata sharkaf da ruwan hawaye cikin kidimewa ya ce."Safiyya me ye ya
sa ki kuka?"Ban iya bude baki na yi magana ba saboda azabar da kaina yake. Hannu yasa ya dago ni da nufin na zauna,
kwata-kwata babu karfi a jikina ganin ina kokarin komawa na kwata yasa ya yi saurin kwantar da ni ya kai hannunsa zuwa kaina cikin tashin hankali ya furta."Ya Salam! Sannu Safiyya."Ya yi saurin mikewa ya fita, na bi
shi da kallo ido cike da hawaye. Bai fi minti biyu ba ya dawo."Daure ki sha magani za mu yi Magana mai muhimmanci Ban yi musu ba na kar6a na sha. Flask din da ya shigo da shi ya jawo ya dau plate. Tuwon shikafa ya zubo ya miko min. Nan ma ban yi musu ba na kar6a, rabona da wani abu mai nauyi tun ranar da ya tafi. Ina gamawa
na ji wani nannauyan barci ya kawon ziyara.Kamar a mafarki na dinga jin muryarsa yana karatun Alkur'ani, na bude idona a hankali na hange shi kan sallaya kan-shi a sunkuyc yana kallon Alkur'ani cikin zazzakar muryarsa yake karanta suratul Nisa'i. Na yi yunkurin tashi don shiga toilet ya dago yana kallona, muna hada ido na zabga masa harara na shiga toilet.Wanka na yi na dauro alwala, yana ganm fitowa ta ya mike daga kan sallayar, ina idarwa
ya juyo wajena. Cikin taushin murya ya ce."Safiyya ki sauraran don Allah za mu yi magana, ina fatan za ki nutsu ki saurari abin da zan gaya miki."Yana magana yana kallona, na yi saurin dauke kaina gefe. Ya ci gaba da cewa."Ina fatan abin da zan gaya miki za ki yarda da shi, kuma ni a zuciyata zan gaya miki gaskiya ne, har ga Allah in kuma na miki karya ina fatan Alltah ya miki sakayya a yanzu-yanzu ga kuma Alkur'ani mai tsarki zan dafa. Kin san dai hukuncin wanda ya yi rantsuwa da Alkur'ani har ya dafa shi.""Kai!" Na yi saurin katse shi cikin tsawa na ce."Ka cikan kunne fa ka fadi tatsuniyar ka ka tafi, ga shi dai a fuska kamar ba azzalumi ba.""Ki bar kirana da azzalumi har a zuciyata haka nake babu zaluncin kowa a raina. Bana zaluntar ,kowa ba kuma na kaunar na zalunci kowa. Ke ma a yau
nake zaton na wanke kaina daga zargin da ki ke min na Azzalumi."Murmushin da ke kan fuskarsa ya bace, ya sauke numfashi kamar wanda ya tashi daga barci. Ya fi minti uku bai yi magana ba, can ya Kara sauke numfashi karo na biyu ya ce."Safiyya na rantse miki da girman Zatin Allah ban aikata abin da ki ke zargin na yi miki ba."Da sauri na dago kai cikin sarkewar murya na ce, "Ban gane abin da ka ke nufl ba, kana nufin ka ce ba ka yi min fyade ba?'Ya dagan kai cikin dakiyar zuciya ya ce, "Ban miki komai ba Safiyya, wallal ban aikata abin da kike zargina da shi ba. Abun da ki ka ga ya faru lokacin da kika farka na yi haka ne don a tunanina za ki yarda ki aure ni sai na ga hakan bai sa kin amince za ki aurc ni ba,don haka na gaya miki gaskiya in "Kan ya Rarasa abun da yake san fada na katsc shi da cewa.Imran wa za ka mayar mara hankali."Na yi murmushin da ya fi kuka ciwo.Kar ka mata imran ba da 'yar shekara sha uku kake magana ba, da 'yar shekara ashirin da biyu ka ke magana. Na taka matakin jami'a har na yi gogayya da
irinku, dadin bakinka ba zai maka wani amfani ba gara ka hakura na riga na barka da Allah, ina fatan ya yi min sakayya da gaggawa ka"Na san ba za ki yarda ba, bara na yi miki rantsuwa ta karshe."Hannunsa ya daga ya dora a kan
Alkur'anin da yake gabansa, sannan ya ce, "Na rantse da girman Zatin Allah Safiyya ban miki fyade ba, idan kuma na
yi miki Allah Ka gaggauta saka miki don girman Ka."Yana fadar haka ya dauke hannunsa daga kan Alkur'anin ya ci gaba
da cewa, "Ki yi tunani Ssafiya ya za a yi a cc na kusancc ki ba ki ji wani canji a jikinki ba?" Ya mike tsaye.
"Ki zauna ki nutsu ki yi tunani babu wata 'ya mace in dai kamilalliyar yarinya ce da namiji zai kusance ta ba ta ji wani canji a jikinta ba, in kuma za ki yi tunani na kusancc ki ba kya cikin hankalinki, amma kin san in har kin tashi
za ki ga alama. Ki gayan tsakaninki da Allah in kin ji wani canji ko wata alama ta hakan ya faru, ni kuma na yarda ki min duk hukuncin da ki ka ga ya dace da ni. Zan karBa zan kuma amsa laifina a yi min duk hukuncin da ya dace da ni."Yana fadar haka ya fita ya bar ni cikin sanyin jiki da fadawa cikin zuzurfan tunani. Me yasa ban yi tunanin haka ba? Ya aka yi Imran ya fi ni hangen nesa? Me yasa kwata-kwata ban yi tunanin haka ba? Tabbas abin da Imran ya fada gaskiya ne babu yarinayr da za a kusanta ba ta ji wata alama ba, kuma ni kaina na san haka. Me yasa ban yi tunanin ba? Kai tsaye na bawa kaina amsa da cewa tashin hankali ne ya hana ni tsinkayar hakan babu wani canji ko alama da na gani a jikina. Akwai lokacin da na yi tunanin haka, arnma zuciyata ba ta ba ni goyan baya ba, don haka na cire tunanin bincikar wani yanayi a jikina ba. To me ye manufan sa na nunan ya kusance ni? Me hakan yake nufi? Me ye dalilinsa na tsare ni a nan gidan?
"Tabbas Imran bai kusance ni ba."Na furta a fili tare da sakin wata siririyar dariya wadda ni kaina ban san ta fito ba. Allah na gode maka da…..to be continue soon!!!


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[12/11/2016, 8:27 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

8⃣0⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–



Ka tsare ni a hannun wannan azzulumin na mike da sauri na shiga toilet. Sai bayan sallar Magriba ya dawo ina zaune ina karatun wani littafi tun na Momy ne. Zama ya yi a kasa, kwata-kwata ban dago kai na kalle shi ba. Hannu yasa ya karBi littafin ba tare da na ga tahowar hannun sa ba."NI NA YI kaina?" ya furta a hankali bayan ya kalli bangon littafin."Shi kuma haka sunansa yake, ba ni labari me littafin ya kunsa kinji kanwata Na dago fuskata cike da murmushi, abin da imran bai taba gani
ba gani yake kamar a mafarki ya yi saurin rufe ido tare da budewa. Kan ya dawo daga duniyar mamaki ya ji maganata cikin taushin murya na ce.'Imran na yarda da abin da ka fada ka yi hakuri zargin da na yi ma don Allah."Saboda tsabar mamaki ya ma rasa bakin magana. Na kara cewa, "Ka yafe min Imran." Kur! Ya zuban ido ya ma kasa magana. nan da nan raina ya baci na yi kamar na tashi na shake shi don tsananin kiyayyar da nake masa na dai daure zuciyata don cinma burina."Ka yi min magana ka yafe min don Allah."Cikin sarkewar murya ya ce, "Sa...fi...yya.. da gaske ki ke kin yarda da abin da na fada miki, kin daina zargina?"Na daga masa kai."Na gode, na gode Safiyyata."Na mike tsaye, "Ka bude min na tafi."a daura mana aure don cika burin zuciyata, na yi miki alkawari da an daura mana aure zan sake ki. Kin ga na cika burin zuciyata ana daura mana zan sake ki, ki koma gida.Kin ga rana ita yau za a fara shari'a, ki yi wa Momy sakamakon alkhairi ki yarda na aure ki kin san in har aka aka fara zaman court za a yankewa su Rukayya hukunci ba akan hakkinsu ba, ki dubu soyayyar da Rukayya da Sadiya suka
nuna miki har ma da iyayensu, ki yi musu halarci, ki yarda a daura mana aure, ki je ki ce su daga fushin
kuliya, ki yi tunani na gaya miki da an daura mana aure zan sake ki ki tafi Kano. Na baki kwana biyu ki yi tunani."Yana fatfar haka ya kwanta a wajen da nake tsaye na tsugunna ina kuka.Me yasa Imran ya yi min haka? Yaya
zan yi da raina? Ba zan iya auran Imran ba da na aure shi gara na zauna ban yi aure ba, in kuma har ban auri Imran ba za a yankewa Momy hukunci ba a kan laifinsu ba? To yaya zan yi? Ba ni da wani zabi da ya wuce na yarda a daura mana aure da Imran tunda ya yi min alkawarin da an daura mana aure zai sake ni.Na dago ina kailon Imran idona cike da hawaye na ce, "Ka rantse min da girman Allah da an daura mana aure za ka sake ni?"Ya yi saurin dago kansa."Na yi miki alkawarin da an daura mana aure zan sake ki, abin da ya sa ma na nace sai an daura mana aure kin ga ina yawan rantsewa akan sai na aure ki, to in kuma ban aure ki ba zan zo na yi kaffara, amma kin ga da an daura mana ban da kaffara sai na sake ki ki je ki auri SAIFULLAHI tunda shi kike so ba IMRAN ba. So..."Kan ya karasa na
katse shi."Duk ba wannan maganar ce a gabana ba, tun farkon hadu warmu na gaya maka bana sonka, bana kaunarka, .
ka hakura ka cire ni a ranka.""Hum Safiyya tun yaushe na cire ki a raina ki ban amsa kin amince a daura mana aure?"Na daga masa kai, daga kan nawa ya yi daidai da zubar zafafan hawaye daga idona. Ya mike zumbur kamar an tsira masa
allura yana dariya."Gaskiya na yarda da kaunar da ke tsakaninku da Rukayya, insha Allahu gobe za a daura mana aure."Na yi saurin cewa, "Kuma goben za ka sake ni?" Ya dagan kai.


**** **** **** **** **** **

Suna zaune a falon saukar baki suna jiran fitowar Alhaji Nasiru wanda Sadiya ce ta shaida masa zuwansu Alhaji Mukhtar da Alhaji Ibrahim, wanda suka zo yin sulhu tun kafin a je gaban kuri'a kan wata 'yar karamar matsala (amma fa a ganinsu. Batan jarumata Safiyya ne karamar matsala?).

Ya shigo falon tare da sallama fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bayan sun gaisa shiru ya biyo baya, kowa da abin da yake sakawa cikin zuciyarsa. Alh.Mukhtar ya katse shirun da
cewa..............




πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[12/12/2016, 8:51 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

8⃣1⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–




"Alh. Nasiru nine mahaifin su Rukayya yaran da ka shigar court kana tuhumarsu kan Batan 'yarka Safiyya, mun zo ne muyi magana ta fahimtar juna sbaoda bai kamata a ce da kimarmu da mutuncinmu mun je gaban aikali kan wata matsalar da mu a gamnmu in mun zauna mun fiiskanci juna za mu iya maganinta. Don haka muka zo mu yi magana ta fahimtar juna za mu yi kokarin shawo kan matsalar ba saimu je ga zuwa court." Ya dan tsaya ya sauke numfashi. Alh. Ibrahim ya karBa, "Na san ba za ka rasa sanin fuskokinmu ba, kuma bai kamata da kimarmu a idon jama'a a ce mun je gaban court muna karar junanmu ba, gara mu hadu mu yi maganin
matsalar da kanmu."Alh. Nasiru ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Duk abin da ku ka fada haka ne, to amma a inda matsalar take shi ne har yanzu ba ku fadi inda matsalar take ba, kuna ta maganar mu fuskanci juna. In har maganar fuskantar juna ce nima ina son haka, tunda tun farko ni na so mu fuskanci juna mu yimagana cikin mutunci, amma hakan bai samu ba, ranar da na ga hotunan Safiyya a jarida ana cigiyarta na tashi da kaina na je wajen 'yarka Rukayya ta yi min bayanin ya aka yi Safiyya ta Bata, amma kwata-kwata ta kasa yi min magana saboda borin kunya.'Yarku ta munafince ni, zuwana biyu Lagos nemanta, kuma wajensu nake zuwa ita da daya kawar ta Sadiya bayan zuwa kullum cikin waya nake na tambaye su sun ganta, ko sun ji labarinta. Amma sai su ce min suma kullum cikin nemanta suke rana tsaka kuma na ga suna cigiyarta abun ya yi min ciwo. Kuna ganin sun yi daidai? Ya yi shiru yana kallonsu."Gaskiya ba su yi daidai ba, kuma mu ka ga ba mu san an yi haka ba. Sai da muka ce ya kamata a zo gidansu Safiyya a gaya rnusu Batanta, sannan take gaya mana wai tun kafun su tafi Lagos ta bar gida ta ce kuma ba za ta taba komawa ba. Wallahi Alhaji Nasiru tana gaya mana haka muka hau ta da fadan me yasa mu ba ta
gaya mana ba. Kan Alh. Nasiru ya yi saurin katse shi da cewa, 'Wannan duk ba maganar da za a dauka ba ce, ni din
nan a yanzu cikin zargi nake a kan Batan Safiyya, mahaifiyarta ce take zargina da SANADIN Batan Safiyya, don haka
ni yanzu ba zan iya ce muku komai ba."Alh. Mukhtar ya ce, "Mu ma ba so muke ka ce mana komai ba, ilia muna so ka janye karar da ka kai zuwa court bai kamata a ce mun hau court ba kan matsalar da ina ganin za mu iya maganinta ba tare da mun yi wa kan rnu tirere a gaban dumbin dubatar alumma ba."'Ni kaina zan so hakan, to amma ba nine matsalar ba mahaifiyar Safiyya ce matsala. Safiyya amana ce a gare ni, don haka ya zama dole na tsaya tsayin daka na taimake
ta a kowanne hali take.""Mu kanmu za mu iya taimakon Safiyya, Rukayya tana son Safiyya na yi imanin ba za ta taba cutarta ba, har ma Sadiyya. Don haka muke so kai yi wa mahaifiyarta magana ta yarda a janye karar, sai mu fuskanci maganar nemanta ba wai mu zauna bata lokacinmu a court ba."Zan yi wa mahaifiyarta maganar da muka yi da ku in har ta amince a janye zan so hakan."Shi kenan Alhaji Nasiru mun gode da karbar da ka yi mana, kuma mun ji dadin sauraronmu da ka yi." Har bakin darareriyar motar su ya rakosu,Tana zaune a falon ta rafka uban tagumi ga Hassan a gabanta yana jan kayan jikinta, amma kwata-kwata hankalinta baya wajensa ya tafi ga tunanin NANA SAFIYYA ruwan ranta. Ya shigo tare da yin
sallama har ya Karaso gabanta ya dau Hassan.Rukkayya! Rukkayya!!" Ya kira sunanta.Ta dago a firgice ta gan shi a tsaye, cikin tausayin halin da take ciki ya ce, "Don Allah Rukayya ki bar tunani kar wani ciwo ya kama ki, insha Allahu Safiyya ta kusa dawowa gare mu."Ta daure zuciyarta suka gaisa."Ina Hussaini ne?"A takaice ta ba shi amsa da cewa "Sun shiga gidan Malam tare da Baba."Bayan ya zauna yake gaya mata zuwan su Alhaji Mukhtar. Ta dago tana kallonsa idonta cike da ruwan hawaye ta ce, "Meyasa ba ka tambaye su cewar 'yar tasu ta gaya musu inda ta kai Safiyya. Hawayen da suke cikin idonta suka gangaro
zuwa dakalin fuskarta."Ki bar kukan nan Rukayya.""Duk ranar da ka ga na daina hawayen nan to ranar da na ga Safiyya ne, ranar hawayen zai bar idona. In har kana son farin cikina to ka zama SANADIN dawowar Safiyya gare ni, bana so mu yi wani sulhu gara mu je gaban alkalin.""Shi kenan Rukayya yadda ki ke so xa a yi, ko da sun dawo ba zan Kara sauraran su ba, kawai ma hadu a court,
sai yanzu ma na kula da rainin hankaiin da suka yi mana 'ya'yansu munafukai ne na karshe, zuwana na karshe can Lagos yaran nan suka hadu har kuka suke ya zama ni nake ba su baki ina lallashin su."Umma ta ce, "Ban yi tunanin haka daga wajen yaran ba, ina musu kallon masu hakali da nutsuwa, ina jin dadin haduwarsu."'Hum, daman ba ka yabon dan kuturu sai ya girma da yatsu."Ita Rukayya tana ganina ta rude kwata-kwala ta kasa magana."Haka Sadiyar ma har yanxu ban ganta ba, don ko lokaicin da na raka yaron alkali ya kai musu sammace babanta ne ya leKo tun farko na fi jin haushin Sadiyar Ha ce ranar da na je rnakarantarsu
nemanta ta ce ba ta nan rabon da su hadu tun ranar Jumma'a, kuma alhalin suna tare wai amma yaran nan suka rainan hankali."
"Ni kaina farkon ganina da yaran nan bana tunanin haka daga gare su a fuskarsu akwai alama ta nutsuwa har ma da hankali, ashe a zuciyarsu ba haka ba ne."Har Baba ta dawo yana gidan.

BAYAN KWANA BIYU

Su Alh. Mukhlar suka dawo gidan Alh. Nasiru don jin inda maganarsu ta kwana. Tunda suka tura kiran sa suka ga canji da ya jima bai fito ba, har sun fara tunanin Kara
tura kiransa suka hango tahowarsa yana waya. Har ya karaso bai gama wayar ba, yana karasowa kai tsaye ya shiga falon saukar baki suka bi shi a baya.Bayan sun gaisa shiru ya biyo baya na yan wasu sakanni. Alh. nasir ya katse shirun da cewa 'Kamar yanda na gaya muku cewar zan je na gayawa mahaifiyar Safiyya zuwanku da yadda muka yi da ku, to na je na kuma gaya mata." Ya dan yi shiru yana kallon Alh. ibrahim.Shirun da ya yi ne yasa Alh. Mukhtar dagowa shi ma yana kalonsa, shiru babu wanda ya yi magana.
Alh. Ibrahim ya ce,."To ya ku ka yi da ita rnahaifiyar Safiyyar?"Ya dan yi jini yana saka abin da zai fada, ya dan sauke marayan numfashi tare da daga hannunsa ya (dora akansa yana shafa gashin kansa. Sannan ya fara magana."Gaskiya Alh. Ibrahim mahaifiyarta
ta ki amincewa mu yi sulhu na yi duk iya yina taki yarda ita tana tunanin su suka batar da Safiyya, kuma ko ni kaina ina tunanin
haka, ina ganin abin da zai fi ku je ku kara tambayar yaranku su fadi inda suka boye ta, ni zan yi d'awainiyar. zuwa taho da ita. Ina ganin haka zai fi zama alkhairi a gare mu, in har suka fadi inda suka bar ta, ni kuma na yi muku alkawarin gobe zan yi waya a janye karar."Alh. Mukhtar ya dago cikin fushi ya ce, "Na gane nufinka ka fito ka ce ba a janye karar'ya'yanmu daga court ba kana
magana kamar ta yara, waye ya gaya maka su suka boye yar matarka? Idan kana da shaidar hakan ka fadan mu kuma in har ka ba mu cikakkiyar shaidar da ta nuna su suka boye 'yarka mun yarda ka kai kararmu kowacce court da ke duniya don yanke mana hukunci. Mun zo maka da sul...."Kan ya karasa ya katse shi da cewa, 'Tabbas ina da shaidar da zan tabbatar da haka, kuma ku kanku kun
san 'ya'yanku ba su da gaskiya, don haka ku ke neman sulhu cikin gida ba tare da mun je gaban court ba. Bara na gaya muku gaskiya
ko da babarta ta yarda a janyc kararku a court ni ba zan yarda ba."Alh. Ibrahim ya tari numfashinsa da cewa, 'Mu daman haka muke so mu ji daga wajenku, Allah yana bayan mai gaskiya." Ya mike. "Kawu taho mu tafi."Yana fadar haka ya fita daga falon. Alh. Mukhtar ya mike jikinsa a sanyaye har ya kai bakin kofa ya juyo yana kallon Alh. Nasiru ya dan yi murmushi sannan ya ce.'Alh. Nasiru ba mu
yi tsammanin haka daga wajenka ba, amma babu komai."Yana fadar haka ya fita daga falon.Tunda suka sbiga mota babu wanda ya yi magana
kowa da abin da yake sakawa a ransa, har suka karaso gida a gate Alh. Mukhtar ya sauke Alh. Ibrahim.Tana zaune a falo tana karatun
Alkur'ani ya shigo."Abba sannu da zuwa."Bai amsa mata ba ya hau sama. Jikinta a sanyaye ta mike tana shiga daki ta ji kiransa ta
fito da sauri. Yana zaune a falo har Hajiya, ta karasa gabansa ta zauna muryarta na rawa ta ce, "Ga ni Abba."Ya dago fuska a hade
cikin tsawa ya ce, "Ki gayan gaskiya ina ki ka kai Safiyya?"Wata irin dagowa na yi ina kallonsa, ita kanta Hajiya dagowa tayi.
"Abba ban gane nufin k aba yayi saurin katse ni da cewa, "Tun muna mu biyu da ke ki gayan gaskiya me ya faru da Safiyya?" 'Wallahi Dady ban san me ya faru da ita ba, mun fita da Sadiyya muka dawo ba mu ganta ba sai yanzu da na dawo na ga wasikar da ta yi min cikin Jakarta."Ina maganar ina kuka; Ya juyo wajen Hajiya Hassana ya ce, "Me ki ka sani dangane da Batan Safiyya ki gayan tsakaninki da Allah Cikin rnarnaki Hajiya ta ce, "Alhaji wani abun ne ya faru ka ke wannan tambayar?""Babu abin da ya faru ina so na san gaskiyar inda yarinyar mutane take, kar mu yi wahalar banza a court a zo a tsananta bincike a kama mu da laifi
saboda na fuskanci iyayenta suna ganin kamar ku ku ka boye ta, ko ku ka batar

Please Login or Register in order to submit comment