Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gari ya waye na tafi school. umma ce ta turo kofar ta shiga tana hararata sannu mara kunya 'umma me kuma nayi? ban sani ba wallahi nana in baki canja wannan mugun halin naki ba bazaki taba jin dadin rayuwarki ba ace mijin mamanki ya zama makiyinki mutumin nan burinsa ya kyautata miki amma dai dai da rana daya baki taba masa godiya ba, tsakaninki da shi sai harara kamar sa'anki."


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[7/7/2016, 8:31 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣1⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–


www.muhdabbagana.blogspot.com



ihun data ji na saki ne ya sata katshe maganar "dole ne sai na gode masa wallahi in dai sai nayi masa ne kar ya ban ni kawai ki mai dani dangin babana,tunda ke bakya kaunata ina maganar ina hada kayana "ki mai dani dangin babana, ita ce kalmar da take yawan yi mata ciwo a cikin kunnenta ganin zan fita daga dakin yasa tayi saurin rike hannuwana "nana yanzu ban isa nayi miki fada ba to tunda haka ne nayi miki alkawarin duk abinda zaki bazan kara yi miki fada ba kiyi hakuri ki zauna tana fadan haka ta fita, washe gari karfe tara da rabi na shirya cikin farar doguwar riga me adon duwatsu tayi min kyau sosai takalmina milk colour high hills na jawo durowa na dau glass dina fari siriri na dora nace yau dai bara na dau wayata. na fita dakin umma na fada cewa zan tafi makaranta gashi inji daddy ya shigo kina barci dubu biyu ta mikon na juya na fita kai tsaye wayen motata na nufa sai daukar ido takeyi me kyau 2007 fara sol maryam na hanga tana jiran direba na shiga na bata wuta na tafi nayiwa maryam bye bye wata uwar harara ta zabgan nayi mata murmushi na fita jina nake cikin nishadi mara misaltuwa in da muka saba daukar sadiya nan na tsaya na san tana hanyar fitowa. waya tace naji tayi kara alamun shigowar message ne suka shigo har guda uku, nana me yasamu wayar taki tsawon kwanaki a kashe dayan kuma akace: nana duk inda kika shiga cikin duniyar nan ba zaki guje min ba mutum baya gujewa kaddararsa muna tare har abada wani kuma yace; ni nasan muna tare gara ki tsaya ki fahimce ni duk inda kika shiga imran mai nemo kine. ganin sadiya a sanyaye na bude na fito zuciyata cike da tunani baki ta saki tana kallona har na karasa "meye haka kin wani saki baki sai kuda ya fada miki sufy kice yau ke kike jan motar to ko ban dace ba no wallahi ban taba ganin macen da take jan mota tayi mata kyau ba sai ke gaskiya kin dade fitowa fa darajarmu a B.U.K kinga kinzo mu tafi lokaci yana tafiya muna shiga kira ya shigo wayata sufy kina jin calling "sady lamarin wannan me kiran nawa yana bani tsoro ban gane ba "wrong number yayi ta kirana nafa gaya masa wrong ya kira amma kullum sai ya kira har kiran sunana yake abinda matukar mamaki kuma yana tsoratani".


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[7/7/2016, 8:31 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣2⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–


www.muhdabbagana.blogspot.com



kin ga message din shi bayan ta gama dubawa ta dago tana girgiza kai gaskiya shawarata kawai karki kara gayawa mutumin nan magana inkina son kanki da arziki dai anyo ko mutum ne kibi a hankali dan ya rabu dake duk lokacin daya kiraki ki daga kuma kar kice zaki masa rashin kunya "sadiya wallahi har tsoron wayar nake ni kawai yarda ita zanyi na huta ke waya gaya miki in kin yar kin huta a yani duk inda kika shiga kuna tare kawai kawai ki dau shawarar dana baki shikenan sadiya na gode tunda muka shiga makaranta ake kallonmu duk inda muka shiga nuna mu ake har mukayi parking muka fito sufy kallo ya dawo kanmu duba ki ga mutumin naki na juya ina kallon ina ta nunan saifu na hange shi zaune da abokinsa duk suna kallonmu muna hada ido ya sakarmin murmushi ya dagan hannu fuska na hade hannuna biyu nayi masa umbola naja hannunta muka tafi muna shiga class sakon m.yusuf ne ya same mu na same shi a office sadiya zaki raka ni gaskiya kawata bbu inda zani kawai kije ki dawo bani wayarki nayi game ban koyi sallama ba na shiga in da kai tsaye nace "gani" nana safiyyya mukhtar ki zauna mana ina da abinyi to nana ina maganar mu ta kwana ban dau maganarka a bakin komai ba tunda ba ita ce a gabana ba ina na riga haba ka amsa bana sonka dan ba soyayya nazo yi ba nana saffiya nima bance muyi soyayya ba aure nake so muyi sannan ina sonki please ki taimaka ki karbi soyayyata kanan......... kan ya karasa nayi ficewata sadiya na tarar akan mota na har kin fito? to kwana zanyi wallahi sadiya zan rufe idona na zabgawa malamin nan rashin mutunci,ki dai bi a sannu tun dazu nake kiran number taki shiga sai yanzu......"Assalamu alaikum sunana sadiya dawa nake magana ke baki san dawa kike magana ba gaskiya ban sani ba a a towa kike nema? ina neman wanda yake kiran kawata nana safiyya inji meye nufin shi a kanta sannan imran salis,ni dan nigeria ne karatu ne ya kaini america zan kira momyna kira wrong number bazan boye miki ba ina son kawarki taki tsayawa muyi magana ta fahimta kullum sai fada sai zagi ki taimaka ki shawo kanta".gaskiya ka dau babban aiki dan kuwa bauddaden hali gareta musamman akan maza amma ya akayi kasan sunanta??


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[7/7/2016, 8:44 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣3⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–


www.muhdabbagana.blogspot.com


ran da muke waya da ita kanta kashe naji wata ta ambaci sunanta shine naji nana safiyya bata da kawa ni daya ce kawarta nace maka wani irin hali gareta? ita fa yanzu.ta daukeka a matsayin aljani kafa bata tsoro sosai" yauwa sadiya naji dadin wannan labarin kuma zan so ace kin boye mata cewa baki sanni ba karki nuna mata kin yi waya dani kuma dan Allah kici gaba da tsoratar da ita kanni aljanine sannan ina so ki dinga gayan wani abu daya faru akanta wanda kike ganin zata kara tabbatarwa ni aljanine shikenan imran zan yi maka kokarin okey na gode sadiya nafi wata uku ban ji wayar aljani nan ba wanda a wannan lokacin shekara ta biyu a makaranta yau muna zaune da sadiya da kuma sabuwar kawarmu mai suna rukayya wanda nake kira da momy waya ta tayi kara nasa hannu na dauka na shiga uku sadiya aljani ya dawo waye kuma aljani? inji rukayya to kinga ki nutsu ki daga to sadiya ya zance kiyi masa sallama hannu na yana rawa na daga cikin shakewar murya nace salamu alaikum kamar na fashe da kuka ya amsa wa alaikissalamu wata zazzakar muryace ta amsa nana saffiya ya gida ya karatu nasan yanxu kina makaranta ko? sufy kinyi shiru kimin magana Dan Allah ka gayan waye kai kana tayar min da hankali "sunana imran kuma gaskiya ni aljanine kar kuma kice zaki ji tsorona zan dinga kiranki karki tunanin kubuta daga tarkona yana fadan haka ya katse, sadiya naga ta kaina kuna jin maganar da yake fadan wai kr meye haka kiyi abinda nace miki dan ku rabu lafiya ko class ban koma ba nayo gida lafiyar ki nana? umma kaina ke ciwo Allah ya sauwake to kije ki kwanta na shigo miki da abincinki ina shiga na kwanta ina ta tunani naji wayata tana kara cikin dauri na daga nayi sallama. ke baki iya gaisuwa ba ya fada cikin wata katuwar murya kayi hakuri yanzu zan gaisheka daman ke bakya gaida kowa koh hantar cikina ta kada waye ya gaya maka? kina tunanin waye ya gayan ko? karki manta ni fa aljanine karkiyi mamakin ganina zabura nayi na mike ina kallon dakina dan Allah yanzu kana ganina?


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[7/7/2016, 8:44 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣4⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–


www.muhdabbagana.blogspot.com



au kin dauka wasa bara na tabbatar kiga shaida da gudu na kara bakin kofa dan Allah kayi hakuri barrister ki nutsu to na nutsu in kina so mu shirya duk safiya ki dinga gaida ummanki da mijinta da kuma abokiyar zamanta kin ji, naji wallahi zan dinga gaishesu to ki tashi kiyi sallah,nima yanzu zan tafi makka zanyi sallah ban san lokacin da bakina ya furta a hirgi zaka? wane jirgi minti biyar zan isa in kuma zaki mu tafi,zubewa nayi ina bashi hakuri dan Allah kayi hakuri yanzu zanyi sallata to da kin idar kije kiyiwa umma aiki ina kallonki kan nayi magana ya katse wayar da sauri na mike nayi toilet ina idar da sallah na mike na fito umma in kina da aiki ki kawo nayi miki cikin mamaki ta dago kai tana kallona umma kinyi shiru zuba min ido tayi"nana ban da aiki ke da kanki yake ciwo na gama komai kije ki kwanta ki huta kamar na saka kuka na juyo na dawo dakina nasan yanzu yana kallona kuma gashi naje tace bata da aiki haka na yini ranan daidai da wanka ma kasa shiga nayi ina tsoron karya ganni ni gashi fitsari ya cikan mara tunda na dawo nake son na kasa tsungunawa nayi, wata zuciyar tace naje toilet din umma nayi imran kinje yana ganinki haka hawaye ya shiga bin fuskata wayata na dauka na kira sadiya sufy ya gida? sadiya ki taimaka min duk motsin da zan aljanin nan yana gani na me kuma ya faru? fitsari ya cika min mara na kasa zuwa yace yana ganina kan tayi magana kudina ya kare wayar na cilla kan gado tana fadawa aka kira da sani na dauka ina tunanin sadiya ce number shi na gani nan da nan jikina ya hau rawa hannu na yana rawa na dauka sufy kije kiyi abinda zakiyi a bandaki zan rufe idona ba zan ganki ba kuma ina ganin bugawa da kikawa sadiya sannan karki kara kirana da aljani ki kirani da imrana sunan da mahaifina yayi min hudu ba dashi dakyar na iya cewa to karki kashe wayar jeki da ita da gudu na mike nayi toilet dan Allah ka rufe idonka zan tsunguna"bara naje london na kai sako kan kiyi amma karki katse min waya minti uku zan dawoπŸ˜‰ cikim murna nace to na gode. washe gari muna zuwa school na fada jikin sadiya hannuna ta kama muka fito cikin motata muka koma har da momina "sufy wai lafiyarki kuwa???


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣5⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–


www.muhdabbagana.blogspot.com



mom kar ki kara gayan sunan nan jiya sai da aljani ya kira ni da haka waye kuma aljani? ta tambaya cikin mamaki kan tayi magana wayata tayi kara lokacin tana hannun sadiya tayi saurin miko min kinga ko shine daman yace duk inda nake yana tare dani jiya har kiran sunanki yayi sadiya kirji ta dafe na shiga uku nana dole kawancen mu ya rabu yanzu dai ki daga nana dan shine kika zo makaranta kina kuka, zan je china nan da minti biyu xan kira ki kan tayi magana ya katse na juyo ina kallon sadiya fuskata cike da hawaye kinji abinda yace naji amma ni kuma bazan karba dan bazan iya magana da aljani ba gara ki ce masa bana nab ko ki bawa momin ki Allah ya kiyaye kinga tafiyata,please sadiya ki rufa min asiri kar ki sa ya kashe ni dan girman Allah ki karba ke baki san halin aljani ba kawai ya sanyen baki da jini kema ina jin sonki yake shi yasa ya kyale ki amma ko rashin kunyar da kike masa a baya da tuni ya kashe ki sadiya na roke ki ki min wannan taimakon in.....kan na karasa ya kara kirana a waya yayi daidai da zubar fitsari abin harya bama sadiya dariya ki bani sadiya yana kallonki dan Allah ki karba ta karba ta daga wace ke magana? kai tsaye imran aljani ya bata amsa to ya kake ya kuma yan uwanka aljanu kuma mai kake nufi da kawata "can kuma ta rafka salati Dan Allah kayi hakuri zata daina kar kamata haka wallahi zata daina ka ci gaba da kira kuna gaisawa to na gode na gode kuma insha Allahu tunda kana ganinta zata daina bayan ta gama ta juyo tana kallona wallahi nana Allah yana sonki amma da tuni sunanki gawa sadiya me nayi masa wau tunda ummank tayi aure kike bata mata rai sannan kakarki bakya ragwanta mata ga mijin ummanki bakya ganin girmanshi "bai isa ya canzan rayuwa ba duk abin da zai min yayi na daina tsoronsa shi din me Allah ya fishi yafi waninsa "ke nana kin san me kike fada yana fa ganinmu, yayi abinda zai yi,nana ki nutsu dan Allah ba zan nutsu ba,ki kaini gida zan kaiki amma ki nutsu kiyi shiru kinga fa mutane suna kallonmu,in bazaki kaini gida ba zan tafi ba zaki kara ganina ba har abada.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.


πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣6⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
09039016969

www.muhdabbagana.blogspot.com


kokarin bude kofar nake tayi saurin rike ni nana dan Allah karki bude bani key din naja mu tafi, sadiya me yake faruwa? naji maganar saifu yauwa saifu taimaka min kakai mu gida nana ce bata da lafiya ya salam ya furta da sauri ya shiga motar sannu saffiya ban iya ce masa komai ba saboda kaina da yake azabban ciwo,sadiya kaina zai cire ki taimakeni ki kaini wajen ummata safiyya kiyi hakuri mun kusa zuwa saifu ya juya yana kallon sadiya komu kaita asibiti 'banso kawai ku kaini gida kona fita saifu dan Allah wai ka kaimu gidan jawo ni tayi jikinta nana gidan zamu kiyi shiru kanmu karasa barci mai karfi ya dauke ni a hankali na bude idona ummata na fara gani a zaune kaina yana cinyarta sannu nana ya jiki? umma naji sauki umma waye ya kawo ni gida? kawarki sadiya da kuma wani,kan nayi magana aka turo kofar aka shigo sannu ya me yake miki ciwo? bbu komai naji sauki Allah ya karo sauki amin, munyi waya dasu suna gaisheki kansu zo "na daga kai umma yunwa nake ji tayi saurin mikewa ta fita kira daya ta yiwa wayar ta shiga hello sadiya kina lafiya lafiya klau imrana ya safiyya maganarta na kira nayi maka okey ina sauraronki "gaskiya imrana ka daina kiran safiyya kana tsoratata yau baka ga tashin hankalin da muka shiga ba a rude yace me ya sameta? take ta kwashe duk yadda abin ya faru cikin damuwa yace to sadiyya ya zanyi ina ganin ka bayyana mata kanka haba sadiya kinfa san halin kawarki kinsan bazata taba karba ta ba to gaskiya ka dai dakata da kiranta ka canja shawara shi kenan sadiya na gode.
washe gari ban je school ba misalin sha biyu sadiya ya ta leko bayan sun gaisa da umma ya juyo ranki ya dade ke fa ake kira da sauri na juyo nace ko dai maryam ke yace dan jiya ma shi ya kawo ki okey kace ina zuwa na juya wajen umma bara naje ki gaishe shi kuma kiyi masa godiya.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[7/7/2016, 5:18 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣7⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–

www.muhdabbagana.blogspot.com


Yana zaune kan bencin sadi na karasa fuskata a hade dai dai lokacin motar daddy ta shigo a,a safiyya ya kuka zauna anan ungo ki bude sit room a dole na karba na bude shiga nayi na samu kujera nayi kwanciyata ganin shiru ban fito ba, ya sa saifu ya shigo, nana kefa yake jira na juyo ina masa irin lalataccen kallo,na zata shima shigowa zayyi bayan ya kai masa ya dawo ya zauna "nana ya jiki? Naji sauki meye kake kirana zuwa nayi na duba ki to kayi kokari na mike zan fita saifu wannan zuwan yazo na karshe a gareka naga kana kokarin shiga min rayuwa ka sauka lafiya. Dan Allah safiyya karki tafi ina son gaya miki wata magana 'saifu na tsane ka sako daya ta hada mu to amma kaci darajar taimakon da kamin jiya ina sauraronka "safiyya kalmar da kika gayan a yanzu ta kara raunana zuciyata amma duk dahaka zan gaya miki ciwon da ke damuna cikin zuciyata,safiyya ina sonki sonki ya dade cikin zuciyata please ki taimakan ki.....' Kan ya karasa na daka masa tsawa baka da tunani saifu me ka dauki kanka dan na baka dama kake so ka wuce goda da iri, to nutsu kaji bana sonka ba kuma zan taba sonka ba na juya zan fita na juyo maganarsa naji bazan daina sonki ba, kuma zaki gane ni din masoyinkine zakiyi nadama sai lokacin da damararki ta kare, ban jima da shiga gida ba sadi ya shigo dauke da manyan ledodi biyu gashi inji bakinki yana kokarin ajiyewa a gabana na daka masa tsawa me yasa ka karbo mayar masa ba,a so, kiyi hakuri ya tafi banza kwadayayye sai kasan yadda zakayi dasu kwashe daga gabana kaine maye kaje kayi taci, sadi yi hakuri ajiye kayan ka tafi bayan fitarsa na juyo ina kallon umma me zaki yi da kayan? Nana kiji tsoron Allah yanzu sadi bai haifeki ba,kike daka masa tsawa. Kan nayi magana kaka ta shigo umma ta mike da sauri ta tarota na juyo ina kallonta na girgiza kai" haka kika kara tsufa dan Allah ki mutu mana" yi min shiru mara kunya bazan mutun ba in raina yana hannunki ki kasheni ina dariya nace bazan zauna a gidan ba kinji abinda ke daya ga kayan dubiya na bar miki tana dariya tace surukin nawa ne ya kawo. in kina sonsa na bar miki bara na tafi islamiya nayi waje.
sati banje makaranta ba ina kwance daga ni sai shimi naji shigowar abba kai tsaye cikin dakina nayi saurin mikewa karsowa yayi yana murmushi zama yayi gefen gado my lovely sister kin kara kyau ya kawo hannu zai taban fuska ban san dana doke hannun ba.

πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[7/7/2016, 5:40 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

2⃣8⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜



Please Login or Register in order to submit comment