Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

💘WAYE SANADI?💘

8⃣6⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Haba Momy bai kamata a ce kin bar Imran cikin wannan halin ba, ni zan yi shaidar dan uwana
ba zai aikata wani mugun abin ba a kan yarinyar ba.”“Ki yi min shiru! Ina tunanin duk halinku daya kana min maganar banza, yaro ya zubar min da mutunci a gaban jama’a bai ji kunyar Allah ba ya dauke ‘yar mutane mahaifiyar yarinyar nan har nan garin suka zo kuma tare da shi ake fita nemanta. Allah ya tsinewa irin son da yake mata, shi kansa Alhajin ya ce kar na kuskura na karbo shi.”Yusuf ya dan goge gumin da ya yi wa fuskarsa sallama ya dan sauke numfashi ya ce, “To ai Momy Malam ya je har gidan da ya boye yarinyar ya kuma daura musu aur....“Ban gane ba?” Ta furta da sauri.“Ina nufin ita yarinyar matarsa ce, malam kakanmu ya je da jama’arsa an daura musu aure da ita.”Stop! Yusuf ban san maganar banza Imran ya yi aure ba
mu sani ba, lallai ya daukowa kansa...”Wayarta ta hau kara ta yi saurin dagawa. Tana gama wayar ta juyo wajensa.“Gobe Abbanku zai dawo, jikin Alhajin Sabon gida ya motsa.” Tana fadar haka ta mi ke ta shiga daki.Ya mike jikinsa a sanyaye ya fito daga falon, suka ci karo da Khadijah
tana tsugunne babu abin da take sai aikin kuka. Ya karaso wajenta da sauri.“Lafiyarki Khadijah ki ke kuka?”Ta dago fuskarta cike da hawaye, kan ta yi magana ya kama hannunta suka shiga cikin dakinsa. Suna shiga ya zaunar da ita a gefen gadon. Ya tsugunna a gabanta.“Sister ki bar kuka na san kina tausayawa dan uwanmu halin da ya shiga, ina ganin kuka ba zai zama mafita a gare mu ba.”Cikin shashshekar kuka ta ce, “To yanzu yaya haka za a bar shi bara A je a karbo shi ba. Wallahi Yaya bai tsare Safiyya don ya cutar da ita ba, sai don ya taimake ta. Amma bai kamata Momy ta rabu
da shi ba.”“Khadijah ba laifin Momy ba ne kin san irin kaunar da Momy take wa Imran Dady ne ya umarce
ta da yin haka.”Na ce, “Yaya ga shawara.”“Yauwa kanwata na san yanzu za ki nemar mana mafita ina sauraranki.“Yaya ka taso yanzu mu je wajen Malam mu yi masa bayanin halin da ake ciki, na san.”
Kan ta karasa ya rike hannunta suka fita.

*** **** **** ***

Karfe takwas Malam ya shigo gidan, na fito daga daki muka gaisa na mike zan koma ya kira sunana. Na juyo ya ce, kije abbanki ya zo ku je unguwa, daman na riga na gama nada kayana tuuda yau kwanana biyu a gidanmu.Baba ta ce, “Malam ka ce ya shigo mana.Kan ta karasa Umma tana jin Baba ta ce ya shigo ta mike ta yi cikin dakin. Bayan ya shigo sun gaisa Baba ta ce, ‘Ya maganar yaron nan.”Abba ya ce “Mun yi waya da Babansa ina tunanin gobe zai dawo, kuma zai sauka a nan garin, in ya sauka gobe zan zo na debe ku gaba dayanku mu je har gidan kakanin yaron tunda a ranar za a yo ballensa.”Allah ya kai mu ai gara a yi ta ta kare.”Ya mike suka fito tare da Malam, na juya ina kallon Umma na ce, “Umma zan tafi, amma ba zan dade ba saboda bana san na yi nesa da su Hassan, tunda na ga Umma ba ki damu da ni ba.”Ta dan yi murmushi, sannan ta ce, “Suma su Hassan ba sa san ki yi nesa da su.” Ta dan yi shiru tana kallon Baba, sannan ta juyo wajcna a hankali ta ce.“Yaushe za ki dawo?”Da saurina na ce, “no in ba kya so na tafi ki gayan sai na yi zamana.”Ta girgizan
kai tare da kallon Baba. Na ce, “Umma ki daina kallon Baba in ba kya so na tafi to na leka na gayawa Abba na fasa bin sa na fi san zama a hannun Ummata, tunda tun farko tafi kaunata, shi din bai rike ni a lokacin da nake bukatar kulawarsa bar aka yi min gori ana kora ta.”Baba ta dago kai tana dariya, sannan
ta ce, “Ni ban kore ki ba ke ki ka kori kan ki. Kin bar babanki a tsaye yana jiranki.”“No Baba ba zan tafi ba, Umma ba ta san na tafi na bar ta.”‘Ke bana san shashanci, ma za dauko kayanki ki bi mahaifinki.”Ta juyo
wajen Umma ta ce, “Ke kuma ce miki ta yi in ta tafi ba za ta dawo ba da za ki hana ta bin mahaifinta?” Umma ta ce, “Baba ba hana ta na yi ba, ita ce ta tsaya.”Na dauko jakata ina dariya na ce, ‘Umma kar ki damu
gobe insha Allahu zan zo na ganki.” Ina fadar haka na fita Yana jingine jikin motar ya zubawa kofar gidan ido, Yana ganin fitowa ta ya hau murmushi har na karaso na tsugunna na kara gaishe shi. Yasa hannunsa ya dago ni.
Ai mun gaisa Safiyya, shiga mota mu je.” Na zagaya na shiga.Muna tafe yana min hira har muka karasa gidan.
Ya yi parking kusa da wata sabuwar mota ‘yar karama mai kyau na duba bayanta na ga an rubuta Picanto, ya
zagayo yana taba motar, sannan ya miko min key.“Abba na mene ne?” Na ce da shi ina kallonsa.“Ga shi nan ki gayan wadda ki ke so sai a canja miki.”Nama rasa bakin magana saboda tsabar farin ciki.“Safiyya na ga kin yi shiru ko ba ta yi miki ba?”Na girgiza kai na ce, “Abba ta yi min, na gode Allah ya kara budi.”“Me ye abin
godiya Safiyya ke ‘yata ce zan iya yi miki abin da ya fi haka.”Yana fadar haka ya shiga ciki na bi bayansa.
Baba Binta tana zaune a dakinta tana sauraran rediyo na shiga ta dago da saurintn cikin mamaki.‘Oho ni Binta
yanzu Muntari ka yi sammako ka dauko ta kamar bazaku kara haduwa ba.”Na karasa kusa da ita na gaishe ta, ta amsa tare da tambayar Ummata na ce tana nan kalau tana ma gaishe ki.“Ina amsawa.’ Ta juyo wajen Abba.“In ce ko
kana idar da sallah ka tafi don ni kwata- kwata ban ga fitarka ba?”“A’a Yaya na leko kina barci shi yasa ban
tashe ki ba.” Ya mike. “Bara na karya na fita.” Yana fadar haka ya fita daga dakin.Baba Binta ta juyo wajena,
Maza Safiyya je ki madafi ki daukar masa kayan karyawar ki kai masa.Na mike na fita ina mamakin aikena da ta yi tunda ni dai ban san ko ina ba a cikin gidan. Na fito na tsaya a falon ina tunanin inda zan nufa da zai kai ni kicin.
Na bude wata kofa da na ganta kusa da dakin Baba Binta. A zatona shi ne kicin din, sai na ga akasin haka. Ashe wani hadadden daki ne wanda daga gani kwanan nan aka hada shi don komai sabo ne a ciki. Na kai kallona kan lafiyayyen gadon da ya sha gyara. Kai duk haduwar dakina na gidan Alhaji Nasir sai na raina shi da na ga wannan dan iya tsaruwa dakin ya tsaru.Na kai kallona kan tafkekiyar Plasma din da ke like a bango ga carpet ya malale dakin babu abin da ke tashi a dakin sai sassanyan kamshi. Na yi saurin janyo kofar na rufe sakamakon motsin da na ji. Na juyo na hango Abba ya fito daga wani dan karamin waje kamar gida hannunsa dauke da tire na karasa na karba. Kai tsaye dakina sa ya nufa na bi bayansa moka shiga. Kai duk haduwar dakin da na gani sai na raina shi da na ga wannan ya ninka shi kyau da tsaruwa. Na karasa inda na ga dinning
table na aje. Abba ya yi cikin dakin ni kuma na samu waje na zauna. Bayan kamar minti sha biyar ya fito ga dukkan alamu ya yi
shirin fita ne ya karasa dinning table din ya zauna, sannan ya juyo wajena ya ce.‘Safiyya ki taso ke ma ki karya mana.”Na ce, “Abba na koshi na yi break fast tun a gida.To taso ki min hira na ga duk kin ki sakin jikin ki ko ba kya san rabuwa da Umman taki ne?” Na yi shiru ina murmushi.“Ki zo nan ki zauna.Ban yi musu ba na taso na zauna, sannan ya hada tea ya fara sha. Na san kin fi son Ummanki da ni ko?” Na dago da sauri ina girgiza kai na ce, “Abba kai ma ina son ka sosai ina farin ciki da ka zamanto mahaifma.”‘To na gode Safiyya.” Ya dan yi shiru yana kallona. Sannan ya sauke numfashi.‘Safiyya me zai hana ki zame min
SANAD1N dawowar Ummanki gare ni.”Na dago kaina da sauri muka hada ido na yi saurin dauke kaina.‘Safiyya ba kya so Ummanki ta dawo
gare ni, kin fi san ta koma gidan Alhaji Nasir ko?”Da sauri na ce, ‘Wallahi Abba na fi so Umma ta dawo gidanka ko a mafarki bana fatan ta koma gidan Alhaji Nasir.”“To za ki shige min gaba.Na daga masa kai ina dariya.‘Yauwa Safiyya Allah ya yi miki albarka.”
Na ce, ‘Amin Abba Kin san Kawun ki (yana nufin Abban Momyna) ya shirya muku tafi kc da RuRayya? Nima ,.uma na shirya muku tafiya to amma wannan yaron da ya zo da wannan maganar ya dakatar da mu don da tuni yanzu kuna Dubai.Na ce, “Abba me ye ruwansa da tafiyarmu?”‘Uhm! Safiyya ke matarsa ce a yanzu yana da hakki a kanki, don haka ba za ku tafi ba har sai ya sake ki.“To don Allah
Abba ka je yau ka takura masa sai ya sake ni, ni bana son sa, ko me sunansa bana so. Allah Abba ko zai mutu akan sona ba zan so shi ba.” Ya zama dole ya sake ki gobe mahaifinsa zai zo da ni da ke har ma da Baba da Malam Mado za mu je can gidan a yi ta ta kare.”
Na ce, “Yanzu Abba shi kenan na zama bazawara? Ina fadar haka nasa masa kuka. Hankalin Abba ya tashi ya hau lallashina.
Wa ye ya ce miki kin zama bazawara? Ai babu abin da ya shiga tsakaninku ko? Kunya ta kama ni na yi saurin sunkuyar da kaina,
sannan na daga masa kai.“To har yanzu ke budurwa ce aurc kawai aka daura muku, kuma shi za a warwarc. Kin ji share hawaycnki mu
je na nuna miki dakin ki.”Na mike ina goge fuskata muka fita. Dakin da na bude dazu na ga Abba ya bude muka shiga na tsaya ina kallonsa cikin mamaki.“Safiyya ga dakinki ina fatan ya yi miki?”Ina dariya na ce, “Kai Abba ya yi min kyau sosai, amma ina tsoron kwana ni daya ba zan dinga zuwa dakin Baba na dinga kwana ba, ko kuma kasa Momy ta dawo mu dinga kwana tare zan fi jin dadi. In ta
zo anjima ba zan bar ta ta tafi ba.”Ya fita ya shiga dakin Baba sannan ya dawo dakin ya mikon kudi.“Ga shi ko za a kawo talla in kin ga kina so sai ki siya.”Bai fi minti goma da fita ba Momy suka zo tare da Sadiya. Da gudu na taso na tare su na fada jikin Sadiya ina murna, har muka karasa falon ina jikin Sadiyya. Muka zube kan kujra ina dariya na ce, “Sister...” Sai kuma na yi shiru. Momy ta ce, Ki karasa mana.”Na dan yi murmushi, “Momy babu abin da zan ce.Sadiyya ta ce ko so ki ke mu gaya miki halin da Imran ya...” Kan ta karasa na katse ta cikin shagwaba na ce.‘Allah in ki ka kara yi min hirarsa zan gayawa Abba, ko Abba na gaya masa ban san hirarsa
Allah zan iya mutuwa.”Ina fadar haka nasa mata kuka.“Lallai yarinyar nan Kawu ya shagwaba ki daga magana za ki sa mana kuka, bara na tuna miki wani abu a karshen wasikar da ki ka samin a jakata.”Sadiyya ta ce, “Kwarai Rukayya tuna mata.”Momy ta ce, “Ki ka ce ki min jaje Momy zuciyata ta kamu da ciwon son Imran na san lokacin da ki ke karanta wasikar nan na yi nisa da barin binin kano, ki bawa
Imran hakurin rashina kuma ki gaya masa sakona ta....” Kan ta karasa na rufe mata baki.“Momy bana so Allah zan hada ki da Baba.” Na shiga kwala mata kirata fito da saurinta tana tambayata lafiya? Tana ganin momy ta tsaya.Momy ta ce, wato yar tsohuwa shi ne ki ka shagwaba yarinyar nan daga mun yi mata magana tasa mana kuka?”Ta karaso tana harararta, sannan ta kai dubanta ga Sadiyya.“Kin ci sa’a
kina tare da bakuwa, amma da sai kin ga yadda ake daka bera.”Na ce, “Baba har bakuwar suke min kuma ita bakuwar ma kishiyarki ce budurwar
Yaya Salim ce.” Tana dariya ta ce, “Ki ce kishiyata ce ta biyu ni har gida. To da me ki ka zo ko dan kin ga na bar miki ragowata to gayan da me ki ka zo da fada ko da neman sulhu?


🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/23/2016, 10:30 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

8⃣7⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.c


Sadiya dai ta kasa magana sai dariya. Ta zamo daga kan kujerar da take zaune suka gaisa da Baba. Momy ta ce ‘“Yar tsohuwa ko karyawa ba mu yi ba muka taho ganin Safiyya mun zo tana mana kukan shagwaba wai ba ta san hirar mijinta.Na nanata kalmar mijinta na ce wa ye mijin nawa?Baba ta ce, “Kin ga ‘yata rabu da su kar su bata miki rai .” Sannan ta juyo
wajen Momy.“Ba dan ke zan kawo muku kayan karyawa ba, sai dan kishiyata, ta san nima na iya girki.”Tana tafiya na ja hannun Sadiyya ina cewa, ‘Zo ki ga dakina.Tunda muka shiga ba mu muka fito ba sai da Abba ya dawo wajen karfe hudu, dukkanmu muka shiga cikin dakinsa.Yana ganin Rukayya ya rike baki cikin mamaki ya ce, “Kuna ina ban ji hayaniyarki kina
wahalar min da yayata ba?”Ta dan yi murmushi ‘Kawu muna dakin Safiyya tana ta zuba mana shagwaba.”Ya ce, “To ai Rukayya, Safiyya rainan ku ce, ku ne ku ka koya mata shagwaba, na ga kanwar taku saurin kuka gare ta, ko Sadiyya?”Momy ta ce, “Lah! Ni Kawu ban da saurin kuka ko da ina yarinya bare kuma yanzu sai dai Sadiyya.” Da sauri Sadiyya ta ce, “Kar ki min sharri Allah Abba ita ta shagwabata da muna school, ko laifi ta yi ba ta yi mata fada.”
Na karasa gabansa na yi masa sannu da zuwa. Bayan mun gaisa ya juyo wajen Momy. Da fatan duk kin hado kayanki?”“Kawu na fasa dawowa nan.”Na yi saurin dagowa ina kallonta,
Abba ya ce, “Saboda me? Gaskiya Kawu in na dawo kullum sai mun dinga fada da Safiyya ga
shagwabar da ta tsira magana daya ta sa ma kuka.Na yi saurin tsugunna a gabanta na kama hannunta.“Don Allah ki yi hakuri ki dawo Allah na daina kukan, kuma ba za mu dinga fada ba.”
Haka ko a school ki ke cewa kin daina min laifi, kuma ki kara zan kwana daya in na ga kin canza shi kenan.“Eh na yarda, ke ma Sadiyya don Allah ki dawo nan gidan duka mu hadu.”
To zan dawo, amma ba yanzu ba.Na ce, “To yaushe za ki dawo?Tana dariya ta ce, “Sai na gayawa Baffana in ya bar ni zan dawo.Abba ya mike.“ko zamuje kuga motoci Muka biyo shi har gate ya umarci mai gadin da ya bude masa wasu motoci biyu da suke lullube yana bude su na
ga irin tawa ce da ya nunan dazu.Ya ce, “Dazu na bawa Safiyya key din ta, ku kuma ga taku.”Momy ta yi wani tsalle ta dire gaban Kawu ta ce, “Kawu da gaske ka canjan mota?” Ya daga
mata kai yana murmushi. Sadiyya ko ta ma kasa magana ganin abin take kamar a mafarki yau
ita ce SANADIN Safiyya ta yi mota.“Allah na gode maka.” Ta zube gaban Kawu tana masa godiya.

WASHE GARI


Misalin karfe sha biyu, Abba ya dawo lokacin mu da Momy muna dakin Baba. Mu kai
masa sannu da zuwa ya ce maza ku taso mu je tun dazu Alhaji Nasir yake min waya.Na ce,
Abba ni wallahi bana san zuwa kawai ka je ku da Momy.Ya dan hade fuska “Ban san shirme, Rukayya ta ce maza taso.” Na mike da sauri na shiga dakina. Daman lokacin doguwar riga
ce a jikinmu iri daya mu da Momy na dauko wani karamin hijabi fari nasa muka fito har ya fitar da motar da za mu hau.Kai tsaye Dorayi muka nufa muka dau Baba da Malam Mado,
na so Umma ta bi mu amma ta ki haka muka tafi.Har muka je cikin Nassarawa Abba ya yi
kiran Alhaji Nasir ya gaya masa inda muke. Bai fi minti uku ba ya zo muka tafi. Tunda
muka shiga gate din gidan kirjina yake ta harbawa da sauri da sauri. Motoci sun fi goma a cikin gate din muka fita. Alhaji Nasir ya yi mana jagora har wani tafkeken falo. Ganin takalma rututu, jikina ya bani da mutane a falon. Momy ta matso kusa da da ni cikin rada ta ce.
Me ye haka ne ki nutsu fa.Daga bayanmu Baba ta ce, “’Yar nan ni kaina na kasa nutsuwa.”
Muka shiga falon Abba da Alhaji Nasir suna gabanmu. Mutane ne kusan su goma a cikin falo
kamar an ce kalli gefenki na hange shi ya hada kai da bango. Kallo daya za kai masa ka hango
muguwar ramar da ya yi ga uban baki kamar angoga masa bayan tukunya idansa duk sun kumbura
kamar mai ciwon ido.Na ji an kama hannuna na juyo da sauri muka hada ido da Khadija, fuskarta
dauke da murmushi, na yi saurin zama a kusa da ita. Abba ma suka samu waje kusa da wani tsoho
wanda ban manta ba har da shi aka daura aurcna da Imran. Inda na zauna a nan su Baba suka zauna.
Malam kuma yana tare da su Abbana. Kanmu na kasa muka gaisa da kowa.Dakin ya dan yi shiru, Malam
Khalil ya ce, “Ku dan yi hakuri Salisun ya shiga ciki fito da Alhaji Dahiru.” Yana maganar yana
kallon Abbana.Abba ya ce, “Babu komai, muma ai kun yi jiranmu.” Aka shiga falon tare da sallama.
Idonsa cikin idon Baba cak ya tsaya bai yi gaba ba, kuma bai juya baya ba, daga bayansa Alhaji
Salisu ya ce.‘Abba mu je mana ko kafar ce ta tashi?” Cikin rawar murya ya cc, ‘Maza ka kirawo
min Hajiya.”Muryarsa da Baba ta ji nc yasa ta dago kanta da sauri, ba ita ba hatta Malam Mado
sai da ya dago kansa yana kallonsa.Yusuf ya mike da sauri ya riko hanun kakansa ya kai shi kusa
da mallam kalil haryanzu idonsa yana kan Baba ita ma din hakance ta kasance da ita. Har yanzu
Baba da malam Mado suna kallonsa Ni kam ban san me ye yake faruwa ba kaina na kasa.Malam Khalil
ya ce, “Alhaji Dahiru lafiya ko ka san su ne?“Ni ko na san su farin sani.”Malam Mado ya ce, ‘Muma
mun sanka bakin sani, tunda ka yi mana SANADIN barinmu mahaifarmu. Ina dan mu da ka gudu da shi.
Kalaman shiga kunnuwanmu. Daidai lokacin Alhaji Salisu ya shigo. da Doctor Khadija da kuma Hajiya,
ga kuma Aysha a bayansu.Malam Mado ya kara tambayar Alhaji Dahiru “Ina dan mu ko ka siyar da shi.”
Muryar Alhaji Dahiru tana rawa ya ce, “Ban saida danku ba sai rayuwarsa da na inganta masa har ya
zama abin alfaharinku. Ga danku ya shigo.” Ya nuna masu Alhaji Salisu da hannu.Da sauri ya karaso
gaban Alhaji Dahiru. Abbana ya ce, ‘Malam ya ku ke magana a baibai ne, kuma muna bayani dukkanmu kun
saka mu cikin rudani.”Dahir (Yayan Imran) ya ce, ‘Alhaji Suf....” Kan ya karasa Alhaji Dahiru ya ce,
Don Allah ki musu bayani ke kadai ce za ki musu bayanin da za su gane abin da ya faru.” Yana maganar
yana nuna Baba.Ba ta yi musu ba ta ba su labarin abin da ya faru a takaice. Baba tana gama ba su labarin
Alhaji Salisu ya ce, “Abba da gaske ba kai ka haife ni ba?”Ya daga masa kai idonsa cike da ruwan hawaye,
sannan ya ce, “Salisu ga mahaifiyarka.” Ya nuna Baba.“Na san a labarin da ta bayar yanzu na san dukkanl
kuna tuhuma ta me yasa akan me yasa na dauko shi? Na yi haka ne don na inganta rayuwar ya samu kyakkyawar
kula da ilimi uwa-uba kuma da kaunarsa da ta shiga zuciyata a lokacin ina cikin radatfin rashin haihuwa.
A lokacin mun fi shekara goma da aure, amma Allah bai ba mu haihuwa ba. Bayan zuwan Salisu da shekara biyu
Allah ya ba mu kyautar Yusuf kwanansa daya ya mutu, ba mu kara samun haihuwa ba sai da Salisu ya cika shekara
goma sha biyar muka haifi Khadija.Daga ita Allah bai kara ba mu haihuwa ba har kawo yanzu. Tare suka tashi
da Salisu. Duk wani abu tare muke musu har kawo yau da Allah ya bayyana su Baba. Ina fatan za ka yafen boye
maka gaskiya da na yi a da wanda a ‘yan kwanakin nan da jikina ya matsan nakc shirin gaya maka gaskiya ko da
ta Allah za ta kasance a gare ni gudun rikici To sai ga shi cikin sauki Allah ya kawo iyayenka.Malam Khalil
yana girgiza kai ya ce, “Ikon Allah ya fi ga haka, dole Imrana ya kaunaci Safiyya ashe kanwarsa ce Ni kam saboda
tsabar mamaki nama kasa dago kaina zuciyata cike da mamakin Baban Imran mutumin da na tsana a rayuwata,
mahaifinsa shi ne yayan Ummata. To yanzu me ma tsayin sa a wajena? Maganar Hajiya Amina ce ta katse min
tunani. Na dago da saurina, fuskarta cike da murmushi ta ce, “Tunanin me ki ke Abbanki yana kiranki Na kai
dubana wajen da Abbana yake zaune na ga ban gan shi ba, ta ja hannuna har gaban Alhaji Salisu na tsugunna
a gabansa kaina na kasa na gaishe shi.Daidai lokacin Abba ya shigo a she waya ya fita ya amsa. Alhaji dahiru
ya ce, Yanzu kam matsalar Imran ta zama ta gida. Kai muktar kai ne mahaifin Saflyya don haka kai ne za ka duba
abin da ya gudana tsakaninsu.”Abbana ya ce, “Maganarta gaskiya ce ni kam zan zamo uba ga Imran, kuma na tabbata
Rukayya (yana nufin Ummata) za ta goyi bayan danta, amma kafin haka muna so mu ji daga bakin Malam me ye gaskiya
radan a kan aurensa da Safiyya shin kai ne ka daura kamar yadda ya gaya mana?Malam Khalil ya ce, “Tabbas nina
daurawa Imran aure da Safiyya.”Hajiya Amina ta ce, “Malam kalin ta yarda a daura musu aure ya mata alkawarin
da an daura zai sake ta?” Doctor Khadija ta ce, “Ni ina ganin duk abin da ya faru a baya a tsakaninku ki ture
shi Safiyya, Imran yana kaunarki ki tausaya masa

Please Login or Register in order to submit comment