Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amin. Duk suka mike Imran ya ce na taso na raka su, ina harararsa na ce, โ€œKafata Suna fita na yi cikin dakina ina kuka, wanda na rasa dalilinsa. Ya dawo daga rakiyarsu ya ga bana falon don haka ya shigo dakin. Ganin ina kuka ya karaso da saurinsa yana tambayar abin da ya sani kuka. Ina kuka na ce, Allah sai na hada ka da Dady, na ce ka kawo โ€˜yan matanka gidan nan kun hadu kuna ta yi min dariya, suna hararata tun da za ku fita ka faman ciwona. Cikin mamaki ya tsaya yana kallona sai da ya ga na fito da wayarshi zan kira ya yi saurin rike hannuna ya karbe wayar na ci gaba da kukana. kusa da ni ya zauna ya zuban ido yana kallon ikon Allah ganin ban da niyar daina kukan ya ce. Safiyya ko da โ€˜yan matana na kawo bai ci ki yi kishina ba..



๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[12/31/2016, 9:46 PM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

9โƒฃ7โƒฃ & 9โƒฃ8โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


ke da ba kya sona ba kya kaunata. To me ye ruwanki da abin da zan yi, kuma wadannan matan da ki ka gani aiki ne ya hada mu duk cikinsu babu wanda maganar so ta hada mu ko da zan yi soyayya da su ba su yi kalar matan da nake so ba. ke daya ce kala ta burin rayuwata, tunda na mallake ki babu gurbin kowa a zuciyata. ki yi shiru kar kanki yayi ciwo ki sawa zuciyarki ke daya ce matar da imran zai yi har karshen rayuwarsa.Ya kawo hannu zai gogen hawayen fuskata na yi saurin kawar da fuskata.ki je ki yi sallah kin ji kira. Zan fita masaliaci, na ga Safiyya shiri take nema da ni. Ya karasa maganar cikin dariya Na bi bayansa da kallo zuciyata cike da mamakin canjin da na samu a zuciyata. A ciki ta yi matukar, karuwa da kaunar Imran, na yi shiru ina ne marwa kaina mafita. Bayan na yi sallah na fito na tadda Imran a kicin yana kiciniyar dafa Indomie ya juyo yana kallona Har kin idar? Na daga masa kai. Ya dan yi murmushi To kin roki Allah ya sa miki kaunata? Na yi shiru ina kallonsa na karaso falo na zauna.Na tambaye ki kin yi shiru? Na ce ni ban yi ba.Ya girgiza kai Shi kenan ni kuma kullum in na yi sallah ina rokon Ubangiji ya sa'miki kaunata. Za ki
ci Indomie na dafa da ke? Kunya ta kama ni ganin ga ni ni a zaune mijina yana kicin zai dafa abin da zai ci har ma yana tambayar ya dafa da ni. A zuciyata na ce shi wai ba ya fushi da mutum Tunanin me ki ke yi, ko kafarce take zafi? Na ce, โ€˜Ta daina zafin tun
dazu. Ya ce, Ai gara ta daina zafin ko dan na fita aiki. Na dafa miki Indomi ko na zo na
yi miki take away? Na girgiza masa kai.Wai ke bakin ki yana ciwo ne, ni ba magana nake miki ba ne ke ma ki bude ba ki ki yi min magana Na ce, โ€˜To na koshi fa.Ya hade fuskarsa me ki ka
ci da za ki ce kin koshi ko kina bukatar na yi miki dure ne? Na dan hade fuska ina harararsa na ce, Me ye haka ne? Tun daga ranar na dan sake da lmran in dai muna zaune a falon muna hira sama-sama, amma kusan rabin hirar ta mu fada ne. Duk wata kulawa yana ba ni har tsawon wata uku babu abin da ya shiga tsakaninmu tunda hirar da za mu yi ta minti goma sai mun yi fadan minti takwas
hirar minti biyu. Amma imran ya dau laifin. Shi kam kuilum burinsa mu zauna lafiya A wannan lokacin su Baba suka lafi Adamawa gaba dayansu har Alh. Bashir ni da Imran kawai ba mu je ba, babu irin magiyar da ban yi wa Abbanmu ba kan na zo kano mu tafi tare, amma ya ki. Haka na hakura na sauke fushina akan imran wanda har kawo yau da suka dawo fushin nake da shi.Duk wani dan uwanmu da yake Adamawa tare aka
taho da shi Kano. Kuma a can aka mayar da auren Momy da Abba har su Dady duk suna Kano. Tun bayan da na yi sallar Asubah ban ji motsin Imran ba, wanda kullum bayan ya dawo daga masallaci sai ya shigo dakina ko in zai tafi amma yau shiru har zuwa lokacin fitarsa ban ji motsinsa ba. Bayan na yi wanka na fito na shiga kicin na hada tea, wayata ta yi kara na fito da sauri na dauka na ji muryar Dadyn lmran na tsugunna kamar
yana gabana muka gaisa yake tambayar ina imran ya kira wayarsa ba a daga ba? Na ce โ€˜Dady ya fita ne kuma ya bar wayar a gida. Ina gama karyawa na dawo falon na kunna kallo na dau wayata na yi kiran Momyta muka
yi hira. Har sha biyu Imran bai fito daga dakinsa ba.ina kallon kofar dakin, amma shiru. har karfe takwas
na dare hankalina duk ya tashi in na yi kamar in shiga dakin na ga lafiyarsa sai kuma na fasa tunda ni duk
zamana a gidan sau biyu na taba shiga dakinsa lokacin da shayi ya zubar min a kafa sai kuma Momy da tasa na yi kiransa.Na mike jikina sanyi kalau na shiga dakina, bandaki na shiga na yo wanka har na yi shirin barci
na kwanta na ji na kasa barcin burin zuciyata sanin halin da imran yake ciki. Babu abin da idanuna suke sai gani fuskar imran na mike da sauri na saka hijabina. Ina zuwa bakin kofar dakin na tsaya ina tunanin shiga kan kwakwalwata ta yi tunanin komai na ji muryar imran cikin mawuyacin haii yana kiran sunan Allah. Ai ban san lokacin da na danna kaina cikin dakin ba. Duk da rashin wadatar hasken da yake dakin za ka iya hangen murkususun da yake a kan gadon. Na karasa gadon da sauri na dago kansa, gabaki daya fuskarsa ta canja, ya ma kasa bude idonsa ya kalle ni, sai faman cije baki yake. A rude na ce. imran ba ka da lafiya? Me ye yake damun ka? Ina maganar hawaye yana zuba a fuskata. Bai samu bakin yi min magana ba sai hannuna da ya kama ya dora akan marar shi, na dauke hannuna da sauri sakamakon shokin din da ha ji a jikina. Na ji muryarsa
a shake Don Allah Safiyya ki kira min Abbana na mutu a gabansa, ki taimakan zan mutu, ga wayata can don Allah ki yi kiransa. Ina kuka na ce, Ka yi hakuri Imran ba za ka mutu ba, don Allah kar ka mutu ka bar ni, ka yi kiran Faisal mu je asibiti ka san Abba suna Kano.Jin shiru bai yi magana ba na kama girgiza shi ina kiran sunansa amma shiru. Hawayen da yake fuskata ya dauke cak tsabagen razana da tsoro suka ziyarci
zuciyata. kar dai Imran ya mutu. Na shiga uku! Yaya zan yi da rayuwata? Hannuna yana karkarwa na dora a kirjinsa kan na dauke na ji muryarshi kamar a mafarki ya kira sunana Na amsa da sauri tare da dago kansa na dora a cinyata, duk da babu haske cikin dakin na san ni yake kallo Muryata na rawa na ce, "Ta daina ciwon?
Muryarshi kamar mai rada ya ce, Ba ta daina ba Safiyya zuwanki ma ciwon karuwa ya yi, na daure ne don kar
na daga miki hankali ban san kina kuka. Na ce, Imran in har ina ganinka a cikin halin rashin lafiya idanuwana ba za su daina zubar hawaye ba, ka taso mu je asibiti don Ailah kar dare ya yi ciwon ya matsa maka.โ€˜Safiyya na je asibiti sau biyu kuma sun bani iya taimamkon da za su iya bani kiyi min adduโ€™a Allah ya ban lafiya marata ta matsan da yawa Ina kuka na ce, Don Allah mu je asibitin ko Faisal mu kira ya kai mu. Ina maganar ina kokar in daga shi naji ya rike hannuwana ba zan koma asibiti ba safiyya kece maganin ciwona ki tausayan halin dana shiga na rasa wane laifi nayi miki kika tsane ni na rasa me zan miki ki kaunace ni yanzu da nake ciwon nan zan
so Allah ya dau raina ko don na huta da kiyayyar da ki ke min Ki daina kuka farin ciki za ki yi zan mutu na bar ki ki huta. Ina so ki rike a ranki Imran mai kaunarki ne, kaunata tsakani da Allah na kaunace ki tun kan na ganki, kuma tun kan na ganki na yi wa kaina alkawarin zama da ke cikin ko wane yanayi, sai na yi rashin dace Safiyya babu
wanda ta tsana a rayuwarta kamar Imran. Na rasa wane gagarumin laifi na yi miki da ki Yayi shiru yana sauke numfashi.
Na ji ya kara matse min hannu sosai ga dukkan alamu mararce ta motsa masa, na kifa kaina a kirjinsa. Ka yi min afuwa Imran waliahi ina kaunarka, in ka mutu ban san ya zan yi da rayuwata ba, tun ranar da na fara ganinka nake kaunarka don Allah ka yi hakuri kar ka mutu ka bar... Kuka ya ci karfina na kasa karasawa. A hankali ya dago fuskata.Safiyya
da gaske kina kaunata Na yi saurin maida kaina kirjinsa Don Allah ki gayan kina kaunata tamkar yadda nake kaunarki? Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya wadda take fal da tunani โ€˜Wash! Allah na Ya furta a hankali. Da sauri na ce, Ciwon take ko? Kan na rufe baki na ji ya rungume ni a kunnena ya radan 'Safiyya ke ce maganin ciwon marata, ina
fatan yau za ki kawo agajin gaggawa don ceto rayuwata. Yana maganar yana kokarin cire hijabin da yake jikina. Muryata na rawa na ce, Imran ka bari Ya dan tsaya daga kiciniyar cire hijabin yana lalubar hannuna ya dora a kan kirjinsa.
Shi kenan Safiyya ba kya so na warke na bari ba zan taba neman hakkina ba ba tare da amincewarki ba. Ya dago ni daga kan kirjinsa Na gode da kulawar da ki ka ba ni a yanzu, ki je dakinki ki kwanta Allah ya tashe mu lafiya Na marairace ina rike da hannunsa na ce Ba zan iya tafi na barka ka kwana kai daya ba, kada marar ta tashi
No Safij'ya kije dakinki zamanmu tare kamar kara ciwon ki ke, ki tausayan mana ko kina so na mutu? Na girgiza kai. To kin amince mini? Na yi shiru zuciyata cike da tsananin tsoro. Ya dan shafa bayana tsigar jikina ta tashi na yi
saurin rintse idona.Kin yi shiru Safiyya kin amince za ki kawon agaji? Idanuwana na rufe na daga masa kai ya sauke wata kakkarfar ajiyar zuciya.Na gode Safiyya tashi mu je mu yi sallah, don neman albarkar wannan daren.Tare muka
shiga toilet muka dauro alwala. Bayan mun idar ya mike ya fita, ni dai ina zaune a inda ya bar ni tsoro fal zuciyata ya dawo. Na barki ke daya naje rufe kofa ne.Na daga masa kai Ki zo ki kwanta Safiyya Ban yi masa musu ba na taso.
Ya ja bargo har zuwa kanmu.


Tun karfe uku Imran bai rintsa ba tsabar farin ciki ne ya cika masa zuciya ya hana shi runtsawa tun bayan daya lallaba Safiyya ta yi barci. Kaunarta tare da tausayin wahalar da ta sha su suke maza zarya cikin zuciyarsa.


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[1/1, 5:22 PM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

9โƒฃ9โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Safiyya ta bar mishi tarihin daren da ba zai taba gogewa cikin zuciyarshi ba. A hankali ya zare ta daga jikinsa ya jera matasai kamar jaririya ya shiga toilet ya tsarkake jikinsa ya haye kan sallaya don nuna godiya ga Ubangijinsa. Har aka yi sallar Asubah bayan ya idar ya mike a hankali ya shiga toilet ruwan zafi ya hada mata sannan ya dawo ya dauke ta cak sai cikin bahon wanka. Na saki wata wahalalliyar kara ina kokarin mikewa ya yi saurin rike ni. Ki zauna Safiyya za ki ji dadin jikinki. Na yi shiru idanuwana yana zubar da hawaye saboda azaba, sai da ruwan ya fara sanyi sannan ya sake ni ya kara hada min wani dan tsarkake jikina ya fito. Zanin gadon ya canja, ya shiga dakina ya daukon farar doguwar riga. Lokacin na fito ya karaso da sauri fuskarshi dauke da murmushi. Na dauke kaina na mika masa hannu cak ya dauke ni ya dire a gefen gadonsa. Safiyya fushi ki ke da ni? Na girgiza kai. To me yasa ki ka dauke kai da na shigo ba kya son ganina ko? Na ce, Ka ban rigar nasa ina san na yi sallah Da kansa ya sa min rigar. A zaune na yi sallar. Bayan na idar na juyo wajensa yana zaune a gefen gadon ya zuba tagumi ya ji muryata ina gaishe shi, da sauri ya amsa yana murmushi na ce ya jikin? Safiyya ciwon naki ne tunda kuma kin kawo min agaji na riga na warke Na kwantar da kaina kan kafet ya taso da sauri ya dauke ni har kan gadon. Na runtse idanuwana tare da takure jikina ya kwanta a bayana cikin taushin murya ya ce. Ki saki jikinki Safiyya babu abin da zan miki Na girgiza masa kai idanuna suna fitar da hawaye, na ce, Ni dai ka raka ni dakina ba zan kara kwana a nan ba. Ya juyo da fuskarsa hannu yasa yake gogen hawayen fuskata. Ya jima
yana lallaba ni kamar yarinya har sai da barci ya dauke ni. Karfe bakwai Imran ya farka kai tsaye kicin ya nufa ina jin fitarsa na mike na yi cikin dakina ba tare da ya ji motsina ba. Yinin ranar Imran ko gate bai je ba yana like da ni duk wani motsi da zan yi idonsa yana kai. Daidai da sallah ranar a gida ya dinga yin ta. Bini-bini ya tambaye ni lafiya
ta. Kyakkyawar rayuwa mai cike da dandasheshiyar soyayya muka shiga shimfidawa tsakaninmu da Imran, bana tunanin zan kaunaci wnai abu kamar yadda nake kaunar dan uwana kuma mijina Imran, wanda duk wata kulawa ya dauke ta ya dora a kaina. In yana office ba ma minti goma ba tare da mun ji muryar juna ba, bare kuma weekend. Har ya yi hutunsa ya gama bai zama lallai ya leka gate ba, in har ba lambun gidan za mu shiga ba. Daidai da girki tare muke yi
har raba girki muka yi. Za mu hada break tare da rana na yi ni kakai da daddare ya girka.
Har shara da gyaran dakunanmu tare muke yi A cewarsa baya san โ€˜yar aiki Zamanmu mu biyu ya fi dadi. Wanki ne kawai ake fita dashi. Rayuwarmu cikin farin ciki Har tsawon wata shida lokacin muka yi bautar kasarmu ba tare da wata matsala ba, Imran ya shiga nema aiki, kuma a lokacin aka tsaida bikin Rukkayya (Momyna) da Yusuf, Sadiya da Salim. Na yi mutukar farin ciki. An tsaida lokacin bikin wata shida masu zuwa. A lokacin cikina yana wata uku babu wanda
ya san ina da ciki da gani sai Imran har muka yi laulayinmu muka gama. Duk wata kauna yanzu Imran ya dankawa cikin da yake jikina. Duk wanda ya kalle ni ya san na canja, na yi kyau iya kyau na gani a fada ta ko ina na fita haka Imran.

Tun karfe bakwai muka shiga kicin ni da Imran domin tarar bakin Kano wanda tun jiya da yamma suka sauka babu irin lallabawar da ban ma Imran ba kan ya bar ni na je na musu sannu da zuwa ya ki. Karshe ma sai da ya lallaba ni na yi barci ya fice ya yi musu barka da zuwa sai farkawa na yi na gan ni rungume da filo.tunda na yi sallar
Asubah ban koma ba, nake kicin nake shirin tarar su Abbana burina na ga Ummata da kannena. Ganin na zage ina aiki Imran sai tsokana ta yake. Sai karfe sha biyu muka gama komai. Na shiga toilet don shiryawa, haka shi ma Imran ya fito sanye cikin lallausan yadi ruwan toka wanda ya dace da kalar fatarsa. Ya shigo muka hada ido ta mirrow ya sakar min tsadadden murmushinsa. Ban yi kasa a gwiwa ba wajen mayar masa da murmushin da yake dimauta shi Ya karaso ya tsaya a bayana muna kallon juna ta mudubi ya dan yi murmushi yana shafa bayana, cikin shagwaba na ce, Ka yi min wayo ka shirya shi ne ka zo ka takuran kasa na kasa shiryawa ko? A yi min afuwa ranki ya dade Maman
Safiyya ina jiranki a falo. Yana fadan haka ya juya da baya ya fita. Sai da na gama shirina tsaf na fito yana zaune ya zubawa kofar dakin ido na fito sanye cikin shadda ruwan kasa. Ya mike da sauri Barka da fitowa. Zuwa na yi na zaunar da shi, sannan na zauna a kan cinyarsa na
sarkafo wuyansa da hannu daya dayan kuma ina shafa kyakkyawan sajensa da yi wa wadatarciyar
fuskarsa kawanya. Ya lumshe ido yana murmushi na ce, Don Allah mu je tare taho da su. Kan ya yi magana muka hangi motar Abba ta shigo gate din gidanmu, na mike da sauri zan fita ya rike hannuna, mikewa yayi ya dan kama kunnena cikin wasa ya ce, Bana hana ki gudu ba kina so ki
dinga wahalar min da Safiyyata ko? To zan miki hukunci na karshe Na ce, Don Allah ka sake ni kar su shigo su gan mu Yana dariya ya ce, Me ye dan sun gan mu? Ai yana da kyau su ganmu dan su ga shaidar kaunar da mukewa juna. Yana kiciniyar goya ni Baba ta fara shigowa na yi saurin zillewa na karasa gabanta cikin kunya Bava barka da zuwa Ina maganar ina kokarin kama hannunta. Tana dariya ta ce, Lallai amarcin yayi karfi haka kika kara girma ga dukkan alamu an kusa sauka
Daidai nan su Ummata suka shigo tare da Abba da sauri na saki hannun Baba na dau Hassan ina dariya,
imran kuma ya dau Hussaini su Malam mado suka shigo na rasa ina zan saka kaina dan farin ciki Yini suka yi a gidanmu har sai karfe biyar muka fito tare da su har gidan su Imran, sannan muka dawo.
Satinsu Umma daya, sannan suka koma nan ma na yi nacin Abba ya yarda na bi su amma ya ce sai bikinsu Momy haka na yi hakuri, amma kullum cikin zuciyata burin lokacin nake. Zamanmu ya dora cikin kyakkyawar
fahimtar juna da zaman lafiya. Haka iyayensa tunda suka fiiskanci ina da ciki Momy kullum cikin aikon da kayan da mai cike take bukata, duk kuma kwana uku sai ta zo ta ga lafiyata har gida Doctor take zuwa ta yi min awo.Lokacin da cikina ya yi wata takwas kullum muna tare da su Momy ta waya muna shirin-shiryen biki. Cikin lokacin duk wani shiri ya riga ya gama kankama, wata kawai muke jira ya kama mu sha biki. Wanda watan bikin ya yi daidai da watan haihuwata. Tun cikina yana wata takwas Baba take san na taho gida.


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[1/1, 8:46 PM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

1โƒฃ0โƒฃ0โƒฃ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜
๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com

Mun sauka Kano ranar da za a yi dinner sai da na fara zuwa gidansu Momy da Sadiyya, sannan na tafi gidan Baba. Duk inda na sa kafa nan Imran zai sa tasa har muka tafi gidan Abbana. Na yi matukar farin cikin ganin Ummata. Bayan na gama cin abinci ina tare da Hassan Imran ya shigo dakin da nake Safiyya amaryar Imran kamar yau aka yi tamu dinner ana hararata tare da takan 'yanyatsu Na ce Me ye haka kai kai ka fiya tuna baya, wacce irin kulawa ce bana baka? Ya zauna kusa da ni, ki yi hakuri Safiyya Abba ya hana zuwanki dinner. Na dago da sauri kar ki damu mu yi zamanmu nima babu inda za ni, mu yi zamanmu mu yi tamu dinner mai tarin lada. Na dan yi murmushi Nima bana jin dadin jikina tunda za mu taho marata take ciwo Ya mike da sauri, 'Ban san shirme baki da lafiya tun safe baki gayan ba, ta so maza mu tafi asibiti cikin sirri kamar unguwa za mu, tunda daman da kayanmu a mota Ban yi musu ba na bi bayansa muka fita, don nima marar tawa dada takuran take. Ya yi kiran Doctor Khadijah ya tambaye
ta tana asibiti ko gida? kai tsay asibitin Nassarawa muka nufa. Awa biyu da zuwanmu cikin iko na Ubangiji na haifi yarinyata mace. Imran ya rasa inda zai saka kansa saboda farin ciki. Ya shigo dakin hutun ina zaune na zubawa bayna ido cikinso da kauna. Duka awarmu biyar a asibitin muka fito tare da dankareriyar kyautar da Ubangiji ya yi mana Iokacin da muka shiga gate din gidanmu Abbana ne a zaune su da Abban Imran Lokacinda Abba ya ga na fito dauke da yarinya a hannuna bai san lokacin da ya mike tsaye ba Dadyn Imran ya ce Kai Imran yarinyar wace ce? Ya karasa yana dariya ya ce, โ€œDady โ€˜yar Safiyya ce daga asibiti muke ta haihu Duk wanda aka gayawa haihuwata ba karamin mamaki
yake ba, haka โ€˜yan party da suka dawo. Ina gani aka tafi aka kai Momy da Sadiya gidajensu. Ba mu yi wani gagarumin taron suna ba sai walima da muka yi. Baby ta ci sunan mahaifiyar Imran Amina. bayan na yi arbain na koma gidana wanda ba mu da nisa da Rukayya illa Sadiyya da take Kano. Zaman da kauna muka shiga shimfidawa. Aminatu ta taso cikin kulawa da soyayya daga kowane bari


Alhamdulillahi.

Nan na kawo karshen wannan labari nawa mai suna *๐Ÿ’–Waye Sanadi?? ๐Ÿ’–*

*SADAUKARWAR: Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana*


GAISUWA TA MUSAMMAN A GAREKU

๐Ÿ„Raheem Jega
๐Ÿ„Baby Afreen
๐Ÿ„Hajiya Zahra B.B
๐Ÿ„Abdul mr smile
๐Ÿ„Abdulaziz A.A J
๐Ÿ„Mrs Bilkisu
๐Ÿ„Kurratulayn
๐Ÿ„Herleematus Serdeeya
๐Ÿ„Billy gero
๐Ÿ„mrs

Please Login or Register in order to submit comment