Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwana gidanka kamar dada karan tsanarka a raina ne, na ga kana wani rawar
kafa da ni, to tun wuri ka fita a hanyata zan zo gidanka don zaman wacin-gadi zuwa lokacin da za ka gaji ka sake ni. Tun farko ban 6oye maka ba, na tsane ka, bana sonka, bana kaunarka, ba kum Wata mahaukaciyar tsawa ya dakan ba shiri na cire wayar a kunnena na ji muryarshi. Nima na tsane ki, bana sonki, kina so ki samin ciwon zuciya ne za ki sha azaba muddin ki ka shiga hannuna Yana fadar haka ya katse wayar.Tunda gari ya waye muka je muka gaisa da Abba
nake cikin dakin har karfe bakwai, lokacin da za mu tafi dan Lagos gidan Imran. Baba Sadiya ta
shiga da saurinta.“Wai Muntari hirar mai ku ke haka ta shirya mu tafi.Abba ya mike “Ina kara mata fada ne, Safiya ku je bara na yi wanka sai a kai ta can dorayi wajen Rukayya daga nan sai mu wuce filin jirgi.karfe uku muka sauka a Lagos motoci hudu daga gidan su Imran aka turo da su. Tun da muka taso babu abin da nake sai aikin kuka, su Baba Laure suna rarrashina har sun gaji sun yi shiru. Su Momy daman ba su zauna a kusa da mu ba. Kai tsaye gidansu muka nufa wanda yake cike da yan biki, tunda ita yau take nata bikin.Su Baba na hutawa suka tafi ganin dakin amarya. Hajiya Amina
ta shigo fuskarta cike da murmushi ta karaso gabana.“Haba ‘yata me ye abin kuka ko ba kya san zaman
Lagos? Na girgiza kaina. Ta kara cewa, “To ba kya san zama da Imran ne?” Na kara girgiza mata kai.
To ki yi hakuri ki bar kukan nan kar kanki ya yi ciwo in ba kya so a kai ki can ki gayan sai ki yi zamanki a nan, in kuma kewar gida ki ke? Na daga mata kai. tayi murmushi Ki yi hakuri nan ma kamar
gidanku ne duk abin abinda da imran ya yi miki ki zo ki gaya mini, ki kwantar da hankali ki sawa ranki kamar kina tare da iyayenki Na daga mata kai.‘Yauwa Safiyya ki yi shiru duk sati zan zo na ganki, haka Alhaji ma.” Ta mike. “Bara na kawo miki abinci.karfe goma aka sada ni da gidan Imran da yake
bictoria Island. gida ne mai kyau madaidaici, plate house mai dauke da yalwar farfajiya, wanda aka kawata
da kyawawan shuke-shuke. Daga shigarka kyakkyawan falo ne mai zurfi dan kuwa sai ka taka matattakala
kafin ka sauka ciki. A nan ne kuma duk wata mahada take. dakunan barci guda biyu kowanne dauke da
toilet da kitchen wanda aka yi mutukar kawata shi da kayan ado. Bayan gidan madaidaicin lambu ne mai mutukar kyau da ban sha’awa.Tun bayan tafiyarsu Momy nake aikin kuka, ga shi gidan abin tsoro unguwar shiru. Tsoro ya cikan zuciya na ci kuka na gaji sai faman sauke ajiyar zuciya nake. Sai karfe goma sha biyu ya shigo gidan, ya shigo dakin tare da sallama. Ya karaso gabana ya zauna kusa da ni, shiru kowa da abin da yake sakawa a ransa.Ya daure muryarshi na rawa ya ce, “Safiyya ki bar kukan nan kar kanki ya yi ciwo.Kamar ya zuga ni na bude wani shafin sabon kukan. Ya yi jugum yana kallona, kwata-kwata tsoron yi mata magana yake don haka ma ya zamewa rakiyar abokan nasa ya taho shi daya do kar ya sha kunya.
Ya rasa yaya zai yi da kaunar Saffiya duk abin da take masa baya rage kaunarta a ransa, sai ma karuwa
da take a zuciyarsa. Ya dago ya tsura mata ido ya sauke kakkarfar ajiyar zuciya duk da sanyin A.C din da ya sanyaya dakin bai hura shi hada gumi ba. Ya daure karo na biyu ya ce.Don Allah ki yi shiru in ba kya san ganina yanzu zan bar miki dakin. Na shigo na ga lafiyarki ne.” Ya mike tsaye.Ga abinci nan kar ki kwana da yunwa, Allah ya tashe mu lafiya.” Yana fadar haka ya fita daga dakin. Jikina ya yi sanyi da kalaman Imran, tun ranar da ya yi min tsawa na fara shayinsa, musamman in na tuna maganarshi ta karshe da ya ce za ki sha azaba in ki ka shigo hannuna.Na mike da sauri na rufe kofar dakin da nake. Zama na yi a gefen gadon ina kallon kayan da Imran ya zube a gabana, haka barci ya dauke ni daidai da mayafin jikina ban
cire ba iya gajiya na gaji. Kusan kwanana uku ban samu cikakken barci ba, don haka mai nauyi ya dauke ni. A hankali na ji ana bubbuga filon da nasa kaina na bu?e idona muka ha?a ido, fuskarshi cike da murmushi ya ce.
Ki yi ha?uri na tashe ki gani na yi lokacin sallah yayi Na dan hade fuska ina harararsa. Na mike zaune. Na ce, Shi ne za ka bugar min kai.” Ya zaro ido yana murmushi, “Duka kuma Safiyya akan me zan da ke ki? Ki yi
hakuri ba zan kara tashinki ba, su Momy sun zo yi miki sallama kina barci, Hajiyr Momy ta ce kar a tashe ki har sun tafi.Ban san lokacin da na mike tsaye ba, ina kallonsa bakina na rawa na ce, “Sun tafi da gaske? Kalli agogo karfe nawa?’ Na daga kaina da sauri. karfe takwas har da kwata, kuma so Momy karfe bakwai za su
tafi. Ji na yi ruwan hawaye yana bin fiiskata. Shi kenan Momy sun tafi bamu yi sallamaba , yaushe zan kara ganin su su tafi sun barni a hannun mutumin da na tsana a rayuwata.‘Me ye abin kuka ne wai ba ki da wuyar kuka? Kina so ruwan hawayenki ya kare da an kwana biyu za mu je Kano, ki je ki yi sallah lokaci yana tafiya.Yana fadar haka ya fita daga dakin.na shiga toilet na yi wanka, sannan na dauro alwala bayan na idar na dauko jakata na debo kayan kwalliya, na mi?e na bude kwabata na dauko wata atamfa mai ruwan ganye wanda aka yi mata
dinki mai kyau, bayan na zira na ?arasa gaban mudubi domin daura dankwali, ya bude kofar ya shigo sanye yake da farar T. Shirt mai adon zanen ananun taurari masu ruwan toka tare da sanyi da shudin jeans. Ya fito sosai angon nasa. Muka hada ido ta mudubin na yi saurin dauke kaina ya karaso fuskarshi cike da murmushi.



🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/28/2016, 9:52 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

9⃣5⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Kin tashi kalau?” Na daure na daga masa kai.Ya dan tsayar da murmurshin fuskarsa
ya ce, “Wai Safiyya ciwon baki ki ke?” Na dago muka hada ido.Na yi shiru ya dan
daga murya “Ki yi min magana mana sai na dinga yi miki magana sai dai ki dagan
kai ko kiyayyar da ki ke min ce ta hana ki magana.Nan da nan idona suka ciko da hawaye.‘Shi kenan kar ki min kuka bana bukatar maganarki taso mu je ki yi break.
Na bude baki dakyar na ce, “Ni na koshi.Bai yi magana ba ya juya ya fita ya dawo dauke
da kayan breakfast ya dire a gabana.Ki ci abinci ko na yi wa Abba waya na ce tun
jiya ki ke kuka na baki minti goma kar na dawo na ga ba ki ci komai ba.” Yana fadar
haka ya fita na bi bayansa da kallo. Kamar ina cin madaci haka na dinga tura break fast din, ya shigo yana amsa waya sai dariya yake har ya gama ina kallonsa ta gefen ido ya juyo wajena.Ki taso mu je ki ga yadda gidan naki yake. Yana maganar yana kokarin kama hannuna na mike da sauri (kamar wanda aka tsikarawa allura). Ina kallonsa cikin
fushi na ce.Ka fita a rayuwata babu ruwanka da zamana a gidan nan, ina tunanin tun farko ban maka nauyin bakina, to wallahi bara na gaya maka in har ba ka fita daga rayuwata ba
za ka rasa ni har abada. In kuma kana ganin ba zan iya ba to don Ailah ka ci gaba da shiga lamarina babu ruwanka da ni, gara tun wuri ka yi harkarka na yi tawa. In kuma kana ganin za
ka gayawa Abbana to Bismillah.Wallahi Imran duk ranar da ka hada ni da Abbana sai na gudu na bar ka in ya so ka fadi ka mutu.Ya dago idonsa wanda suka canja launi daga fari zuwa
ja. Muryarshi a sarke ya ce, “Na gode Safiyya za kuma ki san Imran dan halak ne.Yana fadar
haka ya juya ya fita yana dafa bango na bi bayansa da harara, a zuciyta na ce Allah yasa ka mutu ma karewar ma bakin ciki.Ina cikin dakin har wajen karfe sha biyu, sannan Khadijah ta zo
tare da su Khalil. Na fito da sauri ina muma zuwansu na ji duk wata damuwa ta kau daga zuciyata. Khalil ya ce, “Anty ina Yaya? Kan na yi magana ya fito idanuwansa boye cikin siririn bakin glass
fuskarshi cike da murmushi yana kallon kannansa.Sister na yi tunanin sai kin kwana biyu kina barci,
saboda gajiyar biki.Ta danyi dariya‘Kai yaya Imran dazu ma da su Anty Sadiya suka zo yi maku sallama ina wanka shi yasa ban biyo su ba.Ya zauna kusa da Khalil “Brother ya ka kwana?” Ya jima suna hira da su Khadijah ni kam hankalina yana ga wayar Khadijah.Ya mike, ‘Sister tunda kuna nan bara na je gida in na dawo sai ku tafi.” Ya mike ya yi cikin dakinsa. Bai jima ba ya fita hannunsa rike da key ya tsaya
a gabana. Kudi ya doran a cinya na.Ga shi ko za ki bukaci siyan wani abu, zan kai dare akwai komai a kicin.” Yana fadar haka ya fita.Yana fita na sake da su Khadijah tare muka shiga kicin muka yi girki, Salim ya fita ya siyo mana filet-filet din C.D har da na cartoon. Na yi farin ciki da ganin Tom & Jerry. Sai karfe takwas, sannan Imran ya dawo . Na shiga daki na debowa su Khadijah turaruka har da kudin da Imran
ya bani, duk na hada na ba su. Har bakin motar Imran na karaso, Khalil ya ce.Anty ki shigo mu tafi tare sai ku dawo.Na danyi murmushi na ce, Zan zo Khalil ka gaida su Momy.Ina shiga ciki na zarce dakina na shiga toilet. Wanka na yi na canja kayan jikina zuwa doguwar riga, na dan gyara fuskata na fito falon na shiga kicin ragowar
abincin da muka yi na zubo na dawo falon na saka cartoon din da su Salim suka siyo na dawo na zauna a kujerar ina cin abinci ina kallona. Ina kaunar Tom & Jerry don haka tunda na san nake dariya, kwata-kwata ban ji shigowarsa
ba, don hankalina na ga kallo, sai shigewarsa na gani na dan rage dariyar da nake bai fi minti goma da shiga ba ya
fito sanye da jallabiya ruwan toka. Hannunsa rike da jarida ya shiga kitchen jim kadan ya dawo. Na ji muryarsa.
Safiyya ina abincina? Takarda na yago a jikin memo na yi rubutu kamar haka: banyi girki da kaiba kar kuma kayi
tunanin zan dinga girki da kai' Ina gama rubutawa na mika masa ya karba da sauri ya karanta. Yana karantawa ya juya cikin kitchen din ina jin kiciniyarsa da tukunya. Har ya dafa Indomie ya fito duk ya hada gumi. Ajiyewa ya yi kan kafe ya koma ya dauko robar ruwa da silba tare da cup har ya zauna ya mike ya kara karfin A.C, sannan ya dawo ya zauna. Duk abin da yake ina kallonsa ta gefen ido haka shi ma ya fara cin Indomie yana kallon carloon din .
Ya gama ya debe kayan ya mayar kitchen ya dawo ya zauna kan kujera yana duba jaridar da ya ajiye.Har wajen karfe goma ina falon, haka shi ma sai da na ji barci ya kama ni sosai sannan na mike na shiga dakina na mayar da kofa na rufe.
Na bude durowa na dauko rigar barci na sa na haye dandashen gadona na ja kyakkywan bargona mai tare da laushi na lullube kaina barci mai dadi ya dauke ni.Haka zaman mu ya kasance da Imran har tsawon sati daya babu mai shiga harkar kowa.
In zan yi abinci sai dai ' na yi iya cikina, wata rana ma in har na dafa ruwan shayi shi kenan ba zan kara girki ba,
sai dai kayan sha na kwanwani. Haka shi ma Imran in ya dawo ya kan shigo ya girka abin da yake so. kullum ya fita sai
ya zube min kudi ko zan bukaci wani abu.Yau da yake weekend ne imran yana gida, don tunda na dafa tea na yi shigewa ta daki. Ina karyawa na shiga toilet na yo wanka har na gama shiryawa ina daure da tawul. Ina gama shiryawa na dawo kan gado na yi kwanciyata. Na rufe idona kamar mai yin barci, na ji ma a haka na ji kamar ana min tafiyar tsutsa a tafin kafata na bude
idona da sauri na ce.“Me ye haka? Ya dago kansa a firgice yana kallona, na yi saurin jan bargo na rufe jikina. Idona cike da hawaye na ce, “Me ye haka za ka shigo min daki kana taban jiki? Ya mike jikinsa ya yi sanyi, “ki yi hakuri ni kaina ban san
na aikata haka ba, kuma ko da na sani ban aikata haramci ba, na shigo na gaya miki anjima Momy za ta zo Yana fadar haka ya
fita daga dakin.Na mike na zura. kayana na fito, babu kowa a falon. Na nufi kicin don shiryawa Momy abinci. Har na gama bai fito ba. Ina gamawa na koma daki na kara shiryawa. Ina shirin fitowa na ji sallamar Momy na fito da sauri ina mata sannu da zuwa fuskarta cike da farin cikin ganina ta zauna. Na zauna 'kusa da kafarta ina gaishe ta ta amsa tare da tambayar lafiyata.
Na mike na kawo mata ruwa. Mun jima muna zaune ta ce, “Ina Imran din? Na ce, Momy yana daki. Ta ce kira min shi. Na mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na nufi dakinsa dan tunda na ke ban taba shiga dakin ba. Na shiga tare da sallama yana zaune ya hada kai da gwiwa ga dukkan alamu ya yi zurfi cikin tunani, na karasa gabansa. Ka zo Momy ta zo.” Na fada har sau biyu, amma bai
dago ba. Na kira sunansa ya d’ago da sauri yana kallona cikin mamaki. Na yi saurin kauda idona na juya zan fita na ji ya ruko hannuna,
na yi kasa da murya ina harararsa na ce.Me ye haka? Allah zan hada ka da Momy. Bai saki hannuna ba sai ma jana da ya yi har zuwa gefen gadonsa. Na zauna tare da sunkuyar da kaina yasa hannunsa ya dago fuskata muryarshi na rawa ya ce. Gayan Safiyya ba kya sona, yanzu
nan zan sake ki ki je ki auri wanda ki ke so. Mu je Kano gaban Abba ki gaya masu ke ce ba kya sona.Na zaro ido kamar zan su fado na ce, Momy na jiranka fa. Ya hade fuska.‘Ba maganar Momy muke ba, ki gayan matsyina in kuma baki gayan ba to wallahi yanzu zan gayawa Momy abin da Ki ke min gara kowa ya ya san irin kiyayyar da ki ke nuna min, zan wa Abba waya yanzu na gaya masa.idona ya ciko da hawaye na
ce, Don Allah ka yi hakuri ka bari ta tafi zan gaya maka.Ya mike Mu je. Har na kai bakin kofa ya yi kirana na juyo da sauri ya ce,
Haka za ki fita da hawaye a fuskarki? Na yi saurin sa hannu na goge har na juya zan tafi ya kara kiran sunana.Ki tsaya mu fita tare. Tare muka fito ya karasa gabanta yana murmushi.Momy sannu da zuwa.Sai karfe uku.Momy ta tafi yana fita raka ta na shige daki na kulle
kaina ina jin shi da ya dawo yana ta buga kofar tawa ya ji ta a rufe.Abu kamar wasa sai da muka yi kwana uku ba mu hadu da Imran ba Kullum
ina jin fitarshi zan fito tafasa ruwan shayi na dau duk abin da nake bukata na yi shigewata daki.Yau ina jin fitar Imran na fito don
tafasa ruwan tea kamar yadda na saba, daga ni sai rigar barci iya gwiwa don na san babu kowa a gidan sai ni kadai. Na zuba wanda zan sha a cup ragowar na zuba cikin flaks ma tsaya ina firfita wanda zan sha na juyo zan fita. Yana tsaye jikin kofar kitchen din fuskarshi
a hade na ji wani irin tsoronsa ya cikan zuciya wanda ya yi SANADIN subucewar kofin shayin daga hannuna, duk ya zube a kan kafafuna.
Wani irin azababben zugi ne ya ratsa sassan jikina ban san lokacin da na saka kara ba tare a runtse ido na..



🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/29/2016, 9:11 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

9⃣6⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


durkushe a wajen. Ya karaso da gudu yana salati, hankalinsa ya yi mutukar tashi. Sannu Safiyya garin yaya ki ka saki shayin a kafarki? Nama kasa magana sai ruwan hawaye da yake bin fuskata kamar an bude famfo. Cak ya dauke ni ya fito da ni daga kicin din, har zuwa dakinsa ya dire ni a kan gadonshi ya jawo kafar yana min addu’a
muryarshi kamar zai yikuka ya ce.Ki yi shiru in Allah ya yarda ba za ta tashi ba, ki dinga kula Cikin kuka na ce, Ba kai ne ka tsorata ni ba ka sa na zubar da tea din a kafata, ga shi sai zafi take min.ki yi hakuri ba nufina na tsorata ki ba, na tsaya ne dan na ji daiilin takura kanki da ki ke a daki.Na ce, “To me yasa ba ka min sallama ba, dan na san kana tsaye...,Kukan azabar da kafafuna suke ya ci karfina na kasa karasa maganar.
Ya dafe kansa Kin yi shiru don Allah na ji na yi laifi ki yi hakuri don Allah bara na dauko
miki kayanki mu je asibiti.Na daga kaina ina kallonsa na ce, “Ni ba za ni asibiti ba, kawai ka kai ni wajen Abbana, tunda kai ba ka kaunata ka tsorata ni na ko ne a kafa, Allah sai na gayawa
Dady. Ya zaro ido waje Haba Safiyya me ya kawo rashin kaunarki, kin san ni din mai kaunarki ne tsakani da Ailah ke ce ki ke nunan kiyayya, in kuma ki ka gayawa Dady ya yi min fada to nima zan
gayawa Abba abin da ki ke min. Ki yi shiru yawan kuka in mutum ya kone to ko ba ta yi niyar tashi ba in har ana Kuka zai tashi (Amma fa a cewar Imran).Na ce, To kai ni wajen Abbana, in kana so nayi shiru. zaro wayarsa. Bara na yi kiransa na gaya masa in ya ce mu zo to sai mu tafi yanzu kira daya ta shiga, ya daga suka gaisa Imran ya ce, ‘Abba, Safiyya ce ta ke kuka sai na kwo ta Kano shi ne na ce bara na gaya maka in ka ce mu zo sai mu taho yau. Ban san me ya ce masa ba na ga ya mikon wayar. Na karba ina shashshekar kuka na ji muryarsa.Safiyya akan me ki ke kuka sai kin zo kin gan ni?”
Na ce, ‘Abba shi ne ya tsorata ni na kone a kafa, yanzu wajen sai zafi yake min.” Na karasa maganar cikin kuka. To ki yi hakuri insha Allahu nan da sati biyu za mu zo tare da Ummanki, ga ta ma ku gaisa duk su Hassan sun yi kewarki suna gaishe ki..Na ce, Ina amsawa. Abba ban Umman.Ya mika mata muna gaisawa na ji tana kokarin mika masa na ce, Umma ba ki yi min sannu ba, yanzu Imran ya kona ni a kafa.Ta ce, ‘To Allah ya kiyaye gaba ki gaida Imran din Tana fadar haka ta mikawa abba wayar. Na mika masa wayar ya karba yana murmushi. kan na yi magana wayar sa ta yi kara ya zaro ya daga, sun jima suna hira da Faisal na mike zan fita ya rike hannuna ina za ki Safiyya? Na ce zan je dakina na shirya. Kin ga ki shiga toilet ki yi wankan sai na debo miki kayan.Na ce, “Ni fa yunwa nake ji. Ya mike da sauri. “Bara na hado miki shayin ki yi zamanki, ba zan ma fita ba jinyarki zan yi.Da kansa ya hado min break fast bayan na yi wanka ya kawo magunguna ya bani. Na mike zan fita.“Ina zuwa? Ban kalle shi ba na ce, Falo za ni.Tare da shi muka fito ya kunna mana kallo. Kowa ne minti sai ya kalli kafata ya ga ko za ta tashi cikin ikon Allah ba ta tashi ba. Muna falon misalin karfe shida wayar Imran ta yi kara bayan ya gama amsawa ya juyo yana kallona. Kin ji gasu Faisal nan da abokanan aikinmu za su zo duba ki Kan na yi magana muka ji muryar Faisal yana cewa, Mu shigo ko mu koma? Imran ya mike da sauri yana dariya ya bude musu suka shigo. Maza biyu ne duk na gane fuskarsu sai kuma ‘yanmata guda uku. Kallo daya za ka yi musu ka san an gogu a duniya. Cikin isa suka shigo suna raba idon inda za su hange ni. Na dago kai muka hada ido ina dan murmushi na ce, Sannunku da zuwa.Jikinsu a sanyaye suka karaso falon ba su tunanin za su gan ni haka ba, dukkansu sai da suka raina kyan da suke ta da shi. Zuciyarsu ta cika da mamakin gani na tare da hassadar kyawun da Allah ya zuban. Imran ya dawo kusa da ni ya zauna yana kallona ya ce, Safiyya wadannan matan abokanan aikinmu ne, ga Fadila, ga Maryam, sannan ga Sakatariyata Aliya.Na dan yi raurmushi na ce, Sannunku ya hanya? Suka amsa, Ahmad ya ce, Amarya ya kafa, ya kamata ki doka cup din a court bai san a kafar Barrister Ya dauka ba har ya sa abokinmu fashin zuwa aiki. Na dan kalli Imran ina murmushi na ce, Ahmad ai ba zan zama cikakkiyar Barrister ba ka bari sai na yi bautar lasa da na gama har case zan maka a court. Muka dan yi dariya.Nafisa ta ce, Amma Imran kanwarka ce ko? Yana murmushi ya ce, “Me ki ka gani Nafisa?Aliya ta ce, “ku na mutukar kama sosai. Fadila ta ce, Wallahi kamar har ta yi yawa, ga shi kun dace da juna. Tana maganar tana kallona Imran ya zage sai faman hira yake da ‘yan matan. Ina ta'satar kallonsa amma kwata-kwata hankalinsa baya kaina sai dariyarsa ka ke ji, na ji duk zaman wajen ya gundire ni kamar na mike na shage Faisal ya mike, Amarya za mu tafi Allah ya kara sauki Na amsa da

Please Login or Register in order to submit comment