Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasamu abba? ganin ta daga hankalinta tace karki rada hankalinki ranar daya je wajenku hanyar dawowa shida direbansa sukayi hatsari amma basu ji wani ciwo ba yanzu ma dan yana barci ne da saina bashi ku gaisa. cikin kuka tace hajiya ya za ayi ace sunyi hatsari baiji ciwo ba? gobe zanzo naga jikin abba haba rukayya na gaya miki baiji ciwo ba kiyi zamanki. Allah hajiya sainazo tana fadar haka ta katse wayar kukantane ya tasheni momy lafiya kike kuka? ta juyo wajena sadiyy abba sunyi hatsari wani irin zabura nan take na mance da ciwon kaina na hau kuka mundi rabin awa muna kuka babu mai bawa wani hakuri muna jin wayoyinmu suna kara bamu ko kallesu ba.

sadiya ta shigo da gudunta tana sariya ganin halin da muke ciki yasa tayi saurin tsayawa sisters lafiya kuke kuka? cikin sanyi jiki ta karaso gaban momy aunty rukayya lafiya kuke kuka keda kike babba a cikinmu mune zamuyi haka kiyi hakuri dan Allah kiyi shiru kun dagan hankali dakyar ta iya bude baki tace sadiya abba nane yayi hatsari what? ta durta tare da mikewa daga tsugunen da tayi aunty rukayya yanzu yana ina? yana kano kuyi hakuri momy gobe saimu tafi muga jikin nasa, tafi minti biyar tana lallashinmu sannan mukayi shiru.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/8/2016, 8:01 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣2⃣

πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


waya tayi kara a fusace na daga mallsm ka rabu dani ina fadar hama na katse, naci gaba da kukana sadiya ta mike bari na gawaya farida bayan fitar ta momy ta kalleni ki bar kuka dazu kika gama kukan ciwon kai, cikin dasj
hewar murya nace momy kizo mu tafi yau ta girgiza kai yamma tayi ki bari gobe mu tadi shigowar sadiya ce ta katse maganar aunty ruky kizo inji imran" momy tace ki goge fuskarki muje koh.
yana tsaye jikin motarsa sanye da bakar jallabiya kanshi babu hula muka karasa cikin rudewa ya tare mu rukayya yaushe abban yayi haysari? cikin saekewar murya tace wallahi imran ban sani ba tun ranan daya tafi bamu kara waya ba sai yau na kira wayarshi naji hajiya ta daga shine take gayamin ta karasa maganan cikin kuka. kiyi hakuri ya dago fuska cikin damuwa kuyi hakuri kukan bashi da amfani gobe sai muje a ga jikin nasa yanzu bari naje airport nayi mana bukin momy tace na gode imran bari na dauko kudi muje ta juyo tana kallon sadiya kan tayi magana imran yace 'wane kudi zaki dauko rukayya gani kawai ku shiga mota muje ita dayan yar uwanku ba zata bane? duk na duba ban ganta ba muje kawai, har mukaje muka dawo ina kuka fakin daya yi yasa na dago kaina duk sun fita saini daya ina kokarin fita naji muryarsa ya kira sunana cikin kasalalliyar murya safiyya!! na dago kai ina kallonsa kiyi hakuri ki bar kukan nan karki jawa kanki wani ciwon don Allah kinfi awa kina kuka kiyi hakuri kinga gobe zamuje ki ganshi, hankali na tashi in naga kanwata cikin damuwa bare kuma naga tana kuka sai naji kamar zan mutu kiyi hakuri kanwata ki bar kukan nan yana taban zuciya. ya jima yana lallashina sannan ya samu nayi shiru na zaro kafata zan fita naji muryarsa safiyya ki min alkawarin ba zaki kara kukan nan ba , na daga masa kai haba yar kanwata kimun magana naji dadi muryata a dashe nace zan tafi na kwanta. yanzu zakiyi barci? kaina ciwo yake kinga gobe in munje kuka ya kare kiga Abba da umma nayi saurin dago kai bana son kana kiran ummata kana sa zuciyata tana bugawa ka kiyaye ina fadar haka na fita daga motar. farida na hanga tana ganin na fito tayi saurin shigewa na karasa dakin na jiyo masifar farida. har na karasa taba fada ko kallonta ban ba na karasa kan katifa na kwanta bayan ta fita na juyo ina kallon sadiya me kukayi wa farida take fada? rabu da farida rashin mutunci takeji dan Allah ba a gabanku na fita nemanta na gaya mata abban ruky yayi hatsari ba har zuwan imran ban ganta ba duk cikin makarantan nan na duba ban ganta shine tazo tana fada rashin mutunci take ji wallahi dan bana biye mata da sai munyi fada. sadiya ta mike bari naje daki na dauko kayana danni wallahi ba zan kwana a dakin ba, nasan yanzu kwana zatayi tana mita.

washe gari karfe takwas mun gama shiri imran kawai muke jira momy tace wai yau bara muyi break bane? watace tayi kara sadiya ta mikon na daga kanwata an tashi lafiya na amsa da lafiya klau da fatan kun shirya tun dazun muka shirya kai muje jira okey ku fito mu tafi najuyo ina kallon sadiya yazo.
yana zaune a gaban mota ya zuro fuskarsa har muka karaso idonsa yana kanmu fuskarsa dauke da murmushi da suka dada masa kyau hada da kwarjini aunty an tashi lafiya? gani mukayi an bude murfin motar wata kyakkyawar budurwa ta fito fuskarta dauke da murmushi sannun ku ta furta tana kallon imran.
tunda muka shiga mota take hira dan naji kaunar yarinyar a raina. sai dataga jirginmu ya tashi sannan taja motar ta tafi.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/10/2016, 8:12 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣3⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


karfe sha biyu mua sauka a kano momy ta kunna wayarta zata yi kira ya juyo rukayya wa zaki kira? zan kira hajiyane ta turo a daukemu tun kan mu taho nayi way gidan mamam miji...kanya karass wayarsa tayi kara ya zaro ya daga bayan ya gama magana kuzo mu karasa ga motar can mijin mama nane. yana maganar yana nunam mana wata farar honda. mufa asibiti zamu fara zuwa momy ki kira ki tambayi wani asibiti ne ku bari muje gida in mun huta in yaso sai mu tafi. sadiya tacs gaskiya mu fara zuwa can asibitin koya kika gani aunty ruky, ni dai a ganina mu fara zuwa mu hadu tunda dai munzo kano din zuwa can ba zai bada wuya ba. muka karasa wajen motar dureban motan ya fito da sauri ya bude mana sannunku da zuwa gaba imran ya shiga mu kuma muka shiga baya wayar momy tayi kara hello hajiya nazo kano a wani asibiti kuke to shikenan wai suna nassarawa yayi saurin juyowa muma nassarawar zamu kunga babu nisa.

har muka karasa babu wanda ya kara magana muna yin parking yara suka fito da saurinsu su hudu oyoyo yaya ya bude mota ya fita yana dariya hi babies ina momy? mai wayo daga cikin su tace taje aiki to ina ayshata? tana ciki wai fushi take bakazo da wuri ba.
aunty ku fiti mu shiga suna gaba muna bayansu yaran sai surutu suke masa tana zaune ta rufe idonta ya karasa gabanta yana dariya am sorry lovely sister nasan nayi laifi cikin shagwaba tace bazan bude idona ba sai ka goyeni lala sister kinyi girma yanxu bakya ganin inda kika koma ai sai ki karyani ta kara rintse murya Allah bazan hakura ba saika goye ni ko na kira abban salima nace kazo kana dukana karki min sharri hau na goyeki tayi saurin dane bayansa tana dariya ya mike yana zagaya falon to bude idonki, tana bude kamar a mafarki taga yan mata a zaune suna murmushi wata irin wuntsulowa tayi daga bayansa yaran suka hau dariya.

Allah yaya ba zan yarda ba sai na gayawa momy shine baka gayamin kuna tare da baki ba sannunku da zuwa momy tace yauwa yar gatan imran kinsha goyo kai aunty Allah naji kunya bari na kawo muku ruwa ta mike tana kiran lami. cikin mintina biyu suka cika gabanmu da kayan marmari har kasa suda yaran suka tsunguna suna gaushemu ta juyo wajensa. yaya baka gaya min sunan su ba yana murmushi yace ki gaya musu sunanki dana kannanki suma su gaya miki nasu. ta juyo sunana aysha ta nuna wata yarinya wannan kuma salima ga salim toh ni sunana safiyya wannan kuma sadiya sai kuma aunty mu rukayya. lah yaya kusan irin muryarku daya .

saida mukayi sallah muka tafi har wannan lokacin mamansu bata dawo ba muna gidan ta bugo waya tayi mana sannu da zuwa.

babu wani nisa tsakanin gidan da asibiti muna shiga momy takira hajiya tana ganinmu ta hau murna na gaya muku ba wani ciwo yaji ba kun bi kun daga hankalinku. sadiya tace hajiya dole mu daga hankalinmu abba shi kadai yake zuwa mana yayi hatsari mu kasa zuwa ta juya tana kallon imran yayi saurin zubewa yana gaisheta, momy tace hajiya surinkine saurayin safiyy ne sunansa imran shi ya biya mana mukazo hajiya karya take saurayintane tana murmushi tace an gode, hajiya ba komai .
tana gaba muka shiga dakin tare da yin sallama su biyune a dakin yana zaune a kan gado ba wani ciwo yaji ba illa hannunsa daya da aka dora.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/10/2016, 9:26 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣4⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com



sannu abba ina maganar ina hawaye yayi saurin rike hannuna meye abin kuka safiyya kinga naji sauki, su momy suka karaso su da imran da sadiya suka gaishe shi, momy ta tashi da sauri ta karasa wajen daya mutumin da yake zaune kawu ya jiki maganar datayine ya sa ya dago idonsa muna hada ido naji zuciyata ta buga nayi saurin sauke idona kasa na tsuguna ina gaisheki hannu yasa ya dagonu sannu yata kunzo lafiya? cikin sanyin murya nace lafiya klau abba ya mai jiki? momy ta jawo kujera muka zauna. babu abinda yazo a raina sai tunanin ima nima ina da uba wata irin soyayya ce baran nuna masa ba amma umma tabi ta hanyar da ubangiji ya haramta ta sameni ban san lokacin da hawaye ya dinga zubomin ba, hajiya ta matso kusa dani meya saki kuka safiyya? tana fadar haka kamar ta turani na hau kuka abba yace safiyya meye ya saki kuka ko baki da lafiyane? na girgiza kai sadiya tace wai ke meyasa kike haka kin fi son kullum ki daga mana hankali. shi ko imran yama kasa motsi ya mike jikinsa a sanyaye ya fita dan zuciyarsa zatq iya bugawa in har ya ci gaba da sauraron kukanta waje yayi ya samu waje ya zauna ya rafka tagumi ya fada duniyar tunani meyeke damun rayuwar safiyya?? ita ina nata iyayen? me yasa bata so ayi mata maganar ummanta? meye dangantakarsu da rukayya da sadiy meyasa kullum cikin damuwa da kuka take? tambayoyin da ya kasa bawa kansa amsa kenan koma mene in Allah ya yarda safiyya sain zama SANADIN sanyaki cikin farin ciki nazama SANADIN kawai miki da duk wata damuwarki, nayi SANADIN gyara tsakaninki da mahaifarki, koma meye sai na zama SANADIN gyaruwar rayuwarki ina sonki safiyya son tsakani da Allah tun kan na ganki na kamu da sonki zan soki ko a wani haki kike, ko wacece ke zan aureki na zauna daje insha Allahu safiyya sai mafarkina ya tabbata a kan.... maganar rukayya ce ta katse masa tunani ya dago imran ya ka fito ka zauna anan? rukayya bazan iya zama ina sauraron sautin kukan safiyya ba please rukayya ki gayan meye yake damun rayuwar safiyya, na fuskanci rayuwar safiyya tana tattare da matsla kuma momy nasan kinasane da matsalar kuma kinsan abinda yake damunta ki gayamin dan Allah waje ta samu ta zauna gaskiya imran bazan iya gaya maka damuwar safiyya ba damuwarta ta bani amana kaga in har na gaya maka naci amana kayi hakuri imran bazan iya gaya maka ba amma karka fidda rai ita safiyyar zata gaya maka damuwarta da kanta na fuskanxu imran kana da sa,a cikin mamaki yace rukayya saboda me kikace haka? imran rayuwar safiyya babu abinda ta tsana sama da tsaya tana magana namiji amma gashi rana tsaka kazo ka karya wannan kiyayyarar har ku tsaya kuna hira wani abin ita daya in tana kwance zakaga tana murmushi in na tambayeta dalili sai tace in ta tuna kiranta da kake kanwarka shine yake bata dariy na tabbata gaba kadan zaku shaku da safiyya zata iya gaya maka damuwarta. to yanzu ta daina kuka? tun yaushe tayi shiru yanzu haka ma dariya take kawauna yana bata labari ya saki murmushi momy bara na shiga muyi sallama da abba naje gidan mamana anjima zan dawo tare suka shigo yana fita yaya isha ya shigo (yayan rukayyane) ga dukkan alamu bashi wasa yaje gaban mahaifinsa sun jima suna hira sannan yatafi karfe takwas imran ya dawo hannunsa rike da babban flask bayansa aysha tare da mahaifiyarta lokacin da suka shigo muna waje muna sallah sun jima sannan ta fito aysha tace yay inaso aunty rukayya ya hango sadiya yayi saurin karasaws wajent har kasa ta tsugunna ta gaishesu yace sadiya ina su rukayya? imran yanzu suka fita su da yaya salim aysha tace naso momy kiga me kama dani murmushi tayi tace wata rana zan ganta.

basufi minti goma da tafiya ba muka dawo hajiya ta fito kuzo mu tafi tunda ga me kwannan yazo hajiya bari nayi wa abba sallama na shiga tare da yin sallama ya amsa fuskarshi cike da murmushi har kun dawo safiyya? na daga masa kai.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/14/2016, 7:24 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣5⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com




Na daga masa kai har na juyo zan fita abba kawun ya tafine? kwata kwata ban san lokacin da bakina yayi tambayar ba yaje gida tundazun yake jiran dawowarku amma yace gobe kanku tafi zaizo kuyi sallama nace Allah ya kaimu muma zamu tafi yace to saoda safe zakuje can gidan kune? na girgiza masa kai ban san lokacin da hawaye ya taho min ba nayi saurin fita ya tsaya yama kallon ikon Allah meye yake damun safiyya ya tambayi kansa ko rukayyace take bata mata rai Allah ya kaimu gobe zan tambayeta.
ina fitowa na tarar da imran ya dawo nayi saurin goge hawayen fuskata imran yace hajiy ku taho mu tafi, tunda muka shiga mota babu wanda yayiwa wani magana har muka karasa bayan sun fita naji kiran imran sai da hajiya tasa baki sannan na fita yana jingine jikin motar da mukazo sanye yake da kananan kaya wanda sukayi matukar dacewa da kalarsa kanwaya ba muyi sallama ba, to dole ne sai munyi sallama na fada cikim fushi Allah ya bawa kanwata hakuri kana cin darajar alkawarin da nayi maka amma naga kana son wuce gona da iri kana neman takurawa rayuwata tun farko na gaya maka bazan taba sonka ba babu soyayy a tsarin rayuwata tun kan lokacinka ya kure ka kama gabanka kaje ka nemi me sonka bari na fada maka wani magana wallahi imran bazan taba sonka ba daga yau ma mun daina gaisawa na juya zan shiga gida naji muryarsa kiyi hakuri safiyya ban juyo ba ya karasa gabana ya tsunguna dan Allah safiyya kiyi hakuri ki bari muci gaba da gaisawa a maysayinki na kanwata shikenan zamu cigaba da gaisawaa amma wallahi ka kara takuramin har abada ba zamu kara gaisawa ba ina fadar haka na shige ciki.


washe gari karfe sha biyu muka tafi kawun momy da salim ne suka kaimu airport, saida sukaga tashin jirginmu sannan suka tafi.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.


πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣6⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com

**** **** **** **** ****
cikin ikon Allah yau kwanan umma uku da haihuwa. ta sauka lafiya Allah yayi mata kyautar kyawawan yayanta guda biyu duk maza kullum alhaji nasir yana gidan farin ciki har ya rasa inda zaisa kansa har mahaifiyarsa sai da khalifa ya kawo ta ga yara tayi murna sosai. da yake haihuwar gida tayi. Dr khadija da aysha zuka zo wa umma barka, lokacin alhaji nasir yana gidan yana ganin aysha ya dago kai tare da saurin mikewa yana fadin safiyya! safiyya! babah tayi saurin fitowa daga kicin tana kallon ikon Allah ya kara cewa safiyya! aysha tace ba ita bace ni sunana ayaha ta tsunguna tana gaishehi cikin mamaki uace sunanki aysha kuma? khadija tace wajen rukayya mukazo babah tace ku shiga tana ciki suna shiga umma ta hau murmushi sannunku da zuwa aysha har dake kan tayi magana babah ta shigo rakiya kinga wani ikon Allah yanzu don Allah me ya raba yarinyar nan da safiyya wallahi sai da tayi murmushi naga bata da hushirya sai kuma safiyya dana lura tafita tsayai umma tace itace likutan dana gaya miki ina zuwa awo wajenta, suka kara gaisawa da babah ta fita fita dan kawo musu ruwa aysha tace umma karmarku day da wannan ta nun daya daga cikin yaran wanda yake hannun mamanta ta dago kai tana murmushi ta hau dariya mama don Allah bani wayarki na kira yaya imran na gaya masa ta zaro wayar ta mika mata kyaji da shirmemki .

yini sukayi a gidan aysha ta bawa umma imran suka gaisa yayi mata barka, da daddare alhaji nasir yazo bayan sun gaisa sa babah ya shigo dakin tare da sallama na amsa kaina yana kasa ina bawa hyssaini nono ya zauna tare da daukar hassan rukayya ya kira sunana a ciki na amsa don kwata-kwata bana kaunar yayi min magana sai wani rawan kai yake akan yayansa ni yayi SANADIN rabani da tawa yar. maganarshine ta katse tunanin da nake nayi niyyar canzawa su hassan suna ki gayan wane suka kike so ni dai na sawa hussaini "salisu" sunan ubangidana ke kuma ki gayan wane suna kike so a sawa hassan a sa masa sunan baffana "yusuf" ya mikon manyan ledoji guda bity ga kayan nan nasa aka dinko miki yana maganar yana mikewa.
ana gobe suna da daddare dr khadija ta kawo aysha har ma da salima duk zasu kwana da kuma kayan barkansu umma tayi murna sosai zuwan aysha ko ba komai in suna tare da aysha tana debe mata kewar safiyya, wanda bata wuce minti biyar ba tare da tunaninta ba. wayar aysha ce tayi kara tayi saurin dagawa hello yaya imran kana lafiya?
lafiya klau yar uwa.



πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[11/14/2016, 7:58 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

6⃣7⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜
πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


ga safiyya tana so ku gaisa "hello aunty'
aunty kin manxe dani ba kya kirana a waya can barin safiyya tace kiyi hakuri kanwata ban cika kunna wayata ba shikenan aunty na hakura yaya ya gaya miki ummata ta haihu baki min barka ba, an min kanne har guda biyu aysha bai gaya min ba da har suna zanzo lah! aunty kizo daman gobe ne sunan tana dariya tace aysha kinga lokaci ya kure da sai nazo amma ki mata barka duk ranar da nazo zanzo naga kannenmu a,a ba zan yarda ba bara na baki kiyi wa umman barka to a bata inyi mata kada kanwata tayi fushi dani ta mikawa umma waya tana dariy umma ga kawata ku gaisa ta karbi wayar tare da yin sallama kirjin safiyy ya buga da sauri daidai lokacin network ya hau rawa muryar nana ta dauke umma ta mikowa aysha waya tare da gaya mata bata jin magana tayi saurin sawa a kunnent hello aunty hello aunty ba kyaji ne ta katse wayar, ina zaton network yana da matsala nasan zai kara kira sai ku gaisa salima tace umma wannan kamar su daya da khalil aysha tace ni kum nafi ganin kamar su da abdul, da yaya imran kalli irin giransu daya ita dai umma kallonsu take tana dariya daga suce suna kama da wane sai suce suna kama da wani. washe gari karfe takwas alhaji nazo gidan tare da khalifa sai kanin hajiyarsa khalifa ne ya shigo umma da matar malam mado

Please Login or Register in order to submit comment