Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki ke barci haka.Na dan yi murmushi, ‘Lafiya kalau Baba. Na tsugunna muka gaisa na tambaye ta Abba ya fita? ‘Ai tun karfe takwas Muntari ya fita ya je can gidanku, su kuma su Rukayya sun fita da yayan Imran wai za a kama wajen da za ku yi party.”
Na mike “Baba bara na je wajen Ummnata.“To ki gaishe su.Na koma daki na dauko key din motata na fito. Kwata-kwata bana jin dadin zuciyata na daure na fita . Ina daidai Gadon Kaya an tsayar da mu
na dan sauke glass din motar na yi kiran mai saida dabino na zaro dari biyu na mika masa.Ina zuwa kofar gidanmu na tarar da motar Abbana na karasa na yi parking cikin gidan Malam Mado na yi babu kowa
a gidan sai auta. Na tambaye ta ina Baba Magajiya ta ce ta shiga gidanmu, na shige cikin dakinta na
yi kwanciyata. Na jima a kwance auta ta shigo.Yaya Safiyya ana kiranki.Na ce, Wa ye yake kirana?
Abbanki ne. Na mike da sauri na fito. Yana kofar gidan na karasa gabansa.Abba gani.Ya dago yana kallona? Me ya hana ki shiga gidan bayan tun dazu ke nake jira? ‘Abba shiga na yi mu gaisa.”
Okey na je mun yi magana da Alhaji Salisu kan maganar tarewarki, kuma na san in kin shiga za ya
tambaye ki ra’ayinki na ce kin amince, kar ki shiga ya tambaye ki ki yi magana akasin tawa.Na ce, Abba zan gaya masa kamar yadda ka yi min ummurni kuma rashin shigowata in ta bata maka rai ka yi hakuri. Na mike na shiga cikin gidan tare da sallama muka ci karo da Hussaini yana kokarin fitowa, na dauke shi ina dariya. ‘Boy yana ga ka kara girma mai Umma take ba ka?
Na ji muryar Baba ta ce, “Yana girma ne don ya bi ki ku tafi Lagos zaman aure Na juyo da sauri ina kallonta. Na dan yi murmushi na ce, “Ni da ke zan tafi ba da Hussaini ba.“Ni Allah yasa in na
je ma abude min kofa.” Na dan yi murmushi na tsugunna muka gaisa. Na shiga falon tare da sallama.
Dady Imran ne shi kadai a zaune sai Hassan da yake kan cinyarsa na karasa gabansa na tsugunna na ce, Daddy an tashi lafiya? Lafiya kalau Safiyya, ya mutan gidan? Na ce, “Duk suna lafiya suna ma
gaishe ku.Na dan yi shiru ina wasa da hannun Hussaini.“Yanzu muka gama maganarku da Abban nake ya
yi min maganar tarewarki to shi ne na ce sai na ji ra’ayinki don ba zan yarda a kai ki ba in har baki amince ba.” Na kara sunkuyar da kaina.‘Ki yi min magana kin amince?” Na daga masa kai. Ya dan yi murmushi, Allah ya yi miki albarka.” Ya mike.Bara na je mota na dawo ki shi ga ku gaisa da su. Yana fadar haka ya fita.Na mike na shiga cikin dakin Momyn Imran ta juyo tana kallona
fuskata cike da murmushi. Na karasa gabanta na tsugunna muka gaisa na juya wajen Umma na gaishe ta kanta na kasa ta amsa. Dady ya kira Momyn Imran ta fita na karasa gaban Umma cikin taushin
murya na ce, “Don Allah Umma ki taimaka ki koma gidan Abbana, ki yi hakuri da abin da ya faru
a baya. Abbana yana son ki yana kaunar ki dawo ku ci gaba da zama, kuma na san ke ma kina sonsa kin ga na amince zan zauna da Imran tad ago da sauri tana kallona tace, Da gaske kike?


🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/25/2016, 5:22 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

9⃣0⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Na daga mata kai.“Umma na amince zan zauna da danki, don Allah ke
ma ki amince ki koma wajen Abbana kan....Kan na karasa Momyn Imran
ta shigo hannunta dauke da hotona ta miko mini.“Ga shi in ji Daddynku ki zabi wadanda suka yi miki gobe zai tafi can Lagos din kin ga sai a
siya a can.Na ce, ‘Momy ki zabar min da kanki na san za ki yi min zabi mai kyau.Ta dan yi dariya ta ce, “Ni daman na riga na zabar miki.” Ta mikon wasu hotona guda biyu na karba kaina yana kasa na karba. Iya kyau saitin kayan gadon sun yi na mika mata hotunan.Na ce, “Momy sun yi kyau.”
Ni na san za ki yaba, ina fatan Allah ya zaunar da ku lafiya ya tsare ku daga shairin makiya.” Baba ta amsa da amin.Barrister Amina ta mike “Bara
na je Nassarwa. Bayan fitarta ya rage da gam sai Umma, Baba da Dady. Abbana ya shigo gidan tare da sallama, Dady ya leko suka shigo tare na mike na koma daki ya rage daga Baba sai Abbana da Daddy. Abba ya ce.‘Yanzu muka yi waya da Imran yake tambayata na gaya muku kun amince.Dady ya ce, ‘Amincewar ‘yata ita ce amincewarmu na tambayi ‘yata kuma ta amince gobe ma za mu tafi gyara dakin ‘yata. Ya mikowa Abba hotiman da Momy ta zabar min kayan daki.“Ga kayan da ‘yata ta zaba ina fatan kai ma zabinta ya yi maka. Abba ya dan yi murmushin jin dadi. ‘Sun yi kyau. Allah ya taimaka har zan yi waya Nasiriyya ka gan ma huta da jigilar kava kan ku tafi na kawo kudin sai a siya a can.Abba ya dago fuskarsa ta nuna alamun rashin jin dadin maganar da Abba ya yi. “Yanzu don zan wa Safiyya siyayya shi ne
za kace za ka ban kudi na siya, ina tunanin Safiyya’ ‘yata ce tunda yar kanwata ce zan iya yi mata komai ba tare da na bukaci tallafin kowa ba.Abba ya dan girgiza kai ‘ban fadi haka da wata manufa ba wallahi Safiyya 'yarka ce halak-malak, ni daman kara zan yi da kuma gudunmawata amma tunda ba ka bukata na yi wa dana gudunmawa.
Dady ya ce, “Gara dai ka yi wa dannaka gudunmawa ka kuma hada da jan kunnensa ya kular min da ‘yata sosai don ba zan laminci ya dinga cutarta ba, ni kam zan yi shaidar ‘yata na san ba ta da matsala.‘Bara na shigarwa mijina. zan ba da shaidarsa
wajen hakuri sabanin kishiyar tawa da take sarkin rashin hakuri.Abba ya ce, “Alhaji Salisu nima ina da muhimmiyar magana da za mu yi. amma sai bayan mun gama da su Imran
amma kafin lokacin na san barristcr Amina za ta gaya maku ina fatan za ka shige min gaba.
Dady ya dan yi murmushi ya ce, “Tu jiya Hajiya take gayan kuma mun yi magana da Baba har ma da Malam duk sun amince dari-bisa-dari. Kuma mun yi magana da Alhaji Nasir shi kansa ya gayan cewar ya hakura da Rukayya, ya bar maka in har ta amince za ta koma gidanka. Don haka yanzu aikinka dava ku sasanta kanku da ita, amma ina fatan za mu bar wannan maganar sai bayan mun gama bikin ‘yata.Washe gari su Momy, Dady da YayarDahir-suka koma
Lagos don shirin biki, kuma ranar Aysha ta zo hutu daga Zariya. Tana zuwa gidan Doctor Khadijah ta yi wa Yusif waya suka fita dauko ta,suna fita Sadiya ta zo. daki ta shigo na dago ina kallonta. Ta dan harare ni ta ce Malama ki yi waya tun dazu nake kiran wayar Rukayya ba a daga ba sai Abban Yusrah ya kira yake tambaya s kuna gida.Na ce, “Wa ye Abban Yusrah? Tana murmushi ta ce, “Yaya Salim. ‘Uhm! Allah ya sauwake muku.Ta karaso kusa da ni
ta ce, “Amarya kin sha kamshi, ya na ga sai wani kyalli ki ke, kina kiba?“Kina zagina kawai inda auren soyayya zan yi to in kin fadi haka ba zan karyata ki ba, amma ana shirin auran mutumin da na tsana a rayuwata ina batun kiba da kyau baya ga tarin rama da kuma tashin hankali.”
“Kin ga ni ba wanann maganar ce a gabana ba, kin san ba kya sonsa me ye ki ka amince za ki
zauna da shi? Wallahi Safiyya ki ji tsoron Allah kar ki cutar da imran. Ina baki shawara ki gayawa Abba na tabbata ba zai miki aurcn dole ba, kar a yi abin da zumunci zai zo ya yi rauni, maimakon ya kara karfi tun kan abu ya yi nis..Da sauri na katsc ta da cewa, ‘Sadiyya ina son Abbana bana son ya rasa Ummata, in har ban amince na zauna da Imran ba, to na tabbata Umma ba
za ta ta6a yarda ta dawo wajen Abbana ba. Ni kaina na rasa laifin da Imran ya yi min nake masa kiyayya haka.Haba Safiyya, Imran dan uwankine ya zama yaya a gare ki, ya kamata ko ba kya sonsa ki bashi kyakkyawar kulawa. Imran na kaunarki tsaka ni daAllah ya kamata ki cirewa ranki kiyayyarsa, ki maida ta kaunarsa. Ke in ma ba za ki saka kaunarsa ba to kisa tausayinsa ki bar ganin kulawar da
iyayensa suke baki kiga kamar don kin nuna ba kya kaunar dansu ba za su damuba.Na dago kaina ina kallonta.
Shi kenan Sadiyya zan yi yadda ki ke so. Na fadi haka ne don mu bar hirar ni kam ta gudire ni banga shigwar dadin bakin da zai sa ni na kaunaci imran ba a zuciyata na kudiri ba zanyi sati biyu a gidansa ba tare da bakin cikin abinda nake masa yasa ya sake niba, muna dakin momy suka dawo aysha ta shigo da gudunta tana kiran sunana na dago ina murmushi aysha sannu da zuwa ta fado jikina tana dariya khadija tace sai na gayawa yaya imran nace aysha zata balla cinyar anty safiyya Na mike na kama hannun aysha zo muje ku gaisa da abba naji shigowarsa muna fitowa muka ci karo da hajiya hassana (mahifiyar rukayya) na karasa wajenta da sauri nayi mata sannu da zuwa ai bazan amsa ba fushi nake dake tunda zuwa daya ban kara ganinki ba ina murmushi nace ayi min afuwa hajiya yau n ace zanzo ta danyi dariya ko dai angon ne ya hana zuwa? Na tsugunna muka gaisa aysha ma suka gaisa sannan ta shiga dakin baba mu kuma mukayi cikin dakin abbana.


🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/27/2016, 10:03 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

9⃣1⃣ & 9⃣2⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Gadan-gadan su Momyn Yusuf suke shirin biki haka su Abbana, har mun fara ba? Can ma Nassarawa haka suna shirin bikin jika Imran mai masoya da yawa. Yau Momynsa ta taho daga Lagos tare da tawagar ‘yan uwanta da kuma kayan lefe, wanda ya zama kaso
uku ga tun na farko da Imran ya ban ga Alhajin Nassarawa shi ma ya ha?a nasa ga kuma na Abbana, haka duk aka hadu aka kawo gidanniu kaya na ban mamaki, tun kan su kawo Hajiya (Mahaiiiyar Momy) ta gama yi min tanadin duk wasu kaya da zan saka tun da farkon bikin har zuwa karshe?.Ana gobe za a fara biki sai kusan karfe tara muka shigo gidan a gajiye tun safe muka fita kunshi da gyarna gashi. Duk wannan yawan tare da Yusuf da Salim muke
yinsa ni dai ido ne nawa, don zuciyata cike da mamakin ina lmran ya shiga. Abu daya na fuskanta kullum sai sun yi waya da su Sadiya barin ma ?annansa su Khadijah wanda komai tare muke yi,Muna shigowa muka zarce dakinmu, Salim ya tsaya a falon wajensu Baba Sadiya
yana aikin nasa (tsokanarsu). Muna shiga na fa?a kan gado tare da fadin. “Wash! Allahna Sadiya ta dan harare ni ta ce, “Sai ka ce wadda ta yi aikin wahala."Momy ta ce, “Kya ma tashi da mun yi sallah za mu tafi kar6o aikin dinkunanmu.” Na zaro ido waje na ce, “Da waza ku karbo ?inkin? Aysha ta ce, “Da Anty Safiyya.Da sauri na ce, “Ai wailahi sai dai
in ba za ku sa kayan ba, ni kam babu inda zan ?ara fita.’ Na dan juyo ina kallon Khadijah wadda take ta shafa kunshin kafarta. Na ce, “Khadijah ko ke ma za ki kar6o dinkin? Ta kama girgiza kai “Hum Anty na gama fita ni da fita sai gobe, in za mu tafi dinner, tunda nake ban ta?a gajiya irin ta yau ba, ita daman Aysha ta saba tafi haka tunda ita ma ‘yar kano ce.” Momy ta kalli su Sadiya ta ce, “Bara na yi sallah sai mu je don sun san sun kama komai a hannunsu.” Ta mi?e ta yi cikin bandaki.Bayan fitarsu muna zaune da Khadijah muna cin
abinci babu abin da take sai yabon UMMIN BABA mai kunshi take. Ni dai dariya kawai nake mata na dago kaina ina kallonta. hadijah baki taba kunshi mai kyan haka ba ne?Ta ?an yi
murmushi, ‘Allah Anty ban ta?a yin mai kyansa ba, sai wata ran da na zo Kano muna biki aka yi kiran RUMA kawar wata ‘yar uwarmu ce ita ma ta iya ?unshi, har yaya Imran ya ce in dai a yi aure zai dinga kawo matarsa ana yi mata. ?azu ma da muka yi waya na gaya masa kunshinki ya yi kyau shi ne ma na dauki tafin ?afarki a hoto na tura masa.?an na yi magana ta mi?e ta shiga bandaki. Tana shiga wayarta ta yi ?ara na yi shiru ina sauraran muryar Imran tana karatun Al?ur’ani
mai tsarki cikin taushin murya wanda khadijah ta yi recording din ta kuma dora a ringin tone nata, har ta katse Kadija bata fito ba. Aka kara kira karo na biyu na ji muryar Khadija tana cewa. ‘Anty Safiyya ki daga.” Ba don raina ba na daga wayar na kara a kunnena. Na yi shiru ina sauraren mai zai ce.“My sister ina ta kira baki daga ba ko aikin tsaran lafiyar NANAH ne ya hana ki dagawa?”na ce, ‘khadijah tana toilet. ’ Cikin sauri ya ce, “Safiyya ce? Na daga masa kai kamar yana kallona. Kin yi shiru Safiyya kina lafiya?” Na dai yi shiru na yi shiru ina sauraran muryarsa na kuma kasa katse wayar. ‘Safiyya ki yi magana ko ba kya jina? “Ina jinka mana.” Ban san lokacin da bakina ya
furta haka ba.Na ji sautin dariyarsa. Safiyya kina nan kalau, ya su Abba? ?an na yi magana Khadijah
ta fito na yi saurin mika mata wayar.“Hello Yaya.”Da sauri ya ce, 'A’a Khadijah ina Safiyyar?”
Ta kwanta barci ne ‘Sister ban san karya.‘Allah yaya da gaske nake yau mun gaji da yawa.Okey kara mata wayar a kunne zan mata magana Ta karaso wajena ta karan wayar a kunne na ji muryarshi mai cike
da tarin sanyi.“Safiyya ki karbi wayar mu yi hira ga abokaina na duk suna gaishe ki suna dokin gobe ta yi su ga tauraruwar Imran.” Ya ?an yi shiru ya ji mai zan ce shiru babu maganata.
Don Allah Safiyya ki min magana ko na ji dadi.Na ce, “Don Allah ka rabu da ni barci nake ji fa. Ya sauke numfashi da sauri, ‘Shi kenan Safiyya Allah ya tashe mu lafiya na ji da?n hakan ma da ki ka gayan ki yi barci mai dadi tare da mafarkin mijinki mai kaunarki Imran.” Yana fa?ar haka ya katse wayar. Na lumshe ido ina murmushi, Khadijah ta ce, “Anty ki ri?e wayar na yi sallah tunda na ga hirar taku ta yi dadi Na bude idona da sauri na ?an yi murmushi na ce, “Ai mun gama hirar ta ma katse.Gaba ki daya cikin yini daya za a yi bikin a gama sai kuma in mun tafi can Lagos ?n Momy za ta yi nata.

***Washe gari****

karfe sha biyu su Imran suka sauka tare da abokanansa gidan Baba suka sauka. ?arfe shida za a tafi dinner wanda gidan
Abbana tun safe suke bikinsu, ‘yan uwan sa dukkansu sun zo sai faman girke-girke suke. Ni kam tunda na
yi wanka Hajiya (Mahaifiyarsu Salim) ta shirya ni, ni kaina na san na yi kyau. Momy ta shigo da saurinta
tana waya na dago ina kallonta.Me ye haka ne tun dazu ana kiranki, to Abba ya ce ki fito ki yi wa su Imran barka da zuwa Gaskiya Momy ba zan iya zuwa ba Okey bara na gayawa wanda ya turo ni Ta juya za ta fita na yi saurin ruko ta Yi ha?uri Momy bara na zo sai mu je ki raka ni Tare da Momy muka shigo sitroom din tana gaba. Su wajen goma sha biyar ne a zaune, kallo daya za ka yi musu ka san boko ta ratsa su, duk na diririce na rasa
ina zan zauna (Abin ka da wanda ba ta saba shiga mutane ba)„ “Ahmad bawa amaryar ta mu kusa da angonta ta zauna. Na ji wani daga cikinsu ya fada, wanda ya kira da Ahmad ya mike yana murmushi ya karaso gabana,‘Amaryarmu ga waje. Yana maganar yana nunan kusa da Imran.Na dan juyo ina kallon Momy muna hada ido na karasa kusa da Imran na zauna. Gaba daya rabin jikina yana jikinsa, tunda kujera ce mai cin mutum daya. Wanda ya yi magana da farko ya zaro camera a aljihunsa yana dariya ya ce, “Ya kamata mu fara hoto tun annan , don ina ganin kyan da ku ka yi yanzu ba ku yin shi
a wajen dinnar ba Momy ta ce, “Wa ye ya gaya maka ha'ka? Ni kuma ina tunanin in ka gan su a wajen dinner ba za ka gane su ba.” Wani daga cikinsu ya ce, “Gaskiya Faisal ka fara hoto tun a nan saboda ina ganin ba za su kara kyau
kamar na yau ba.Ni dai kaina yana kasa ina wasa da zobunan da suke hannuna. Shi ko Imran kai faman bude hakora yake, ya kuma kara shige min. Sun jima suna hira da Momy har su Sadiya suka shigo. Ana hita na ji muryar imran a hankali ya ce….



🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/28/2016, 10:33 AM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

9⃣3⃣ & 9⃣4⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com


Safiyya kin yi kyau sosai kunshin ya yi miki kyau.Na dan kauda fuskata ya kara
matso da fuskarshi saitin kunnena Don Allah ki yi min magana na ji zazzakar muryarki da take dimauta ni Cikin dabara nasa hannuna a tsakanin jikinmu na
dinga ture Imran, amma ina, ina ture shi zai dawo ya kuma nanike mini. Na dago
ina kallonsu Mommy wanda kwata-kwata hankalinsu baya kanmu hirarsu kawai suke tare da abokanan Imran, na juyo ina harararsa a hankali na furta.Allah zan mare
ka.Ya zaro ido waje kamar za su fado yana murmushin da yake karawa fuskarshi kyau
ya kuran fuskarshi.My lovely wife Bismillah. ” Na daga hannu da nufin na mare shi ya rike hannun ya dora a kan fuskarsa ya dan daga murya yace Bismillah My wife
Momy ta dago tana kallona, haka su Faisal, ban san lokacin da na hau shafa fiiskarshi ba. Ya saki hannuna yana murmushi ya ce Faisal ban da sa ido.” Suka dan yi dariya. Ya
juyo yana kallona, ‘Kin goge mini?” Na daga masa kai ina murmushin dole.karfe shida da rabi su Imran suka kawo motocin da za a dibe mu don zuwa dinner. Tun karfe shida Hajiya Mahaifiyar (Momy) take aikin yi min kwalliya duk ‘yanmatan da za su je an debe su ya rage
daga ni sai Sadiya don har Momy ta tafi.Karfe bakwai na fita mu da Sadiya. Motoci biyu ne a wajen, Salim da Faisal (Abokin Imran) suka taso da saurinsu. Ya take mana baya har muka karasa gaban bakar Hummer Jeep ya bude mana yana ciki a kishingide yana amsa waya jikinsa
ya yi kyau cikin wani lallausan faria yadi, wanda ya dace da kalar fatarsa. Hular kansa irinsu daya da gwaggwaron da yake kaina. Ana budewa ya juyo yana kallona fuskarshi cike da
wani kyakkyawan murmushi na kara hade fuskata ina harararsa. Ina shiga Faisal ya rufe ya
zagayo ya tashi motar. Imran ya matso kusa da ni yana murmushi.‘kanwata kin yi kyau har kin tsorata ni, kishinki ya cikan zuciya har ina ji kamar mu fasa zuwa dinner nan bana san kowa ya gane min kyakkyawar fuskar nan taki.Yana magana yana gogan kafarshi na daga takalmina na danne ta ya saki wata siririyar kara tare da kama hannuna ya rike gam na dago ina kallonsa
nace “Allah in ba ka sakar min hannu ba zan gayawa dady na ce na fasa zama da kai tun jiya ka ke takuran.” yasaki hannun yana dariya.“sorry Sister.Har muka karasa wajen dinner babu wanda
ya kula wani, motarmu na tsayawa su Momy suka taso, Faisal ya budewa Imran, Khadijah ta bude min. kai tsaye ya zagayo barina muka jera dan shiga wajen ya zuro hannu zai kama hannuna na aika masa da wani mugun kallo ba shiri ya wayence da karbar jakata.Sai karfe sha biyu muka tashi tunda muka shiga nake kuka Imran duk hankalinsa ya tashi, sai tambayata yake dalilin kukana. Na yi masa shiru har muka karasa muna yin parking na fita. Ta sitroom na shiga dakin Abba ya dago da sauri yana kallona na karasa gabansa. ‘Lafiya ki ke kuka?’ Kan na yi magana ya mike ya fita suka shigo tare da su Baba Binta. Har wajen karfe daya ina dakin suna min fada tare da nasiha zuciyata ta yi sanyi. Lokacin da na shiga dakin duk sun yi barci. Na shiga na dauro alwala har karfe uku ina kai kukana wajen Ubangiji Allah ya samin kaunar Imran a zuciyata. Wayar Aysha ta hau kara, na mike na dauko, ina kallon sunan Imran har ta zama missed cail. Ina shirin ajiyewa aka kara kira na daga na yi shiru na ji muryarsa.
Aysha wace ce a dakinku take sallah?” Na yi shiru ina jinsa.Hello Aysha ba kya jina? Hello Aysha ba kya jina? Muryata a dashe na ce, Aysha ta yi barci fa. Safiyya ba ki yi barci ba? Na daga kai kamar yana kallona.“Hello Safiyya ki yi magana mana? Na ce, “Ba na daga maka kai ba Ya dan yi dariya har na jiyo sautin dariyarsa ta fito cikin wayar.Ya ce, “Kin ga bana ganinki balle na ga lokacin da ki ka daga kan ba, ko za ki zo mu yi hira? Da sauri na ce, Allah in ba ka fita a rayuwata ba zan fasa zaman da kai, kar ka yi tunanin in na zo gidanka zan kaunace ka,

Please Login or Register in order to submit comment