Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan hango sadiy ko momy naji an rufe min ido momy ko sadiya ta bude tana dariya kallon me kike ku nake nema littafi ta zaro take karantawa, momy kema kina karatun littafi?? baby labarinsa aka ban momy meye a cikin littafin uhumm baby bazan iya baki labari ba zan so ki karanta baby ban taba ganin rayuwa irin wannan ba zan baki ki karanta momy ya sunansa?
bayan ta juyo tace da ita "πŸ’sireenahπŸ’"baby so nake kawai na karanta na 3 naji karshen matar da yayanta.
ya rage saura kwana uku su umma su tafi ina daki umma ta shigo nana kizo alhaji yana kiranki tare muka fita muka tarar dashi yana zaune a falon umma, safiyya kinga saura kwana uku mu tashi shine nace zaki zauna ko zaki tafi gidan kaka kan mu dawo? zan zauna sai a dauko kaka ta tayani zama kuma muma sauran sati hudu mu tafi lagos, Allah ya kaimu karatu yazo karshe kudi ya zaro gashi ki rike a hannunki na karba
ranar da suka tafi ina school ban samu damar raka su ba ina dawowa na tadda kakz a,a yar tsohuwa kin sha A/C har kin fara mulmulewa zaki fara halin naki koh kinga abar magana yanzu ina abinci na ba wani musu ta nuna min.
khalifa ya shigo muna cikin hira maryam ta shigo yaya kazo inji momy okey ina zuwa. muka ci gaba da hira ji mukayi an banko kofar kai dan wulakanci ana kiranka shine kake zaune wajen wannan kwadayyayun tare suka fice aiko ranar kaka ta rantse ba zata kara kwana gidan ba babu irin magiyar da khalifa bai mata ba amma taki haka dole ya kaita gida, ina daki naji sallamarsa har ka dawo daga kai tsohuwa yar rigima babu wani rigima sai gaskiya kuma wallahi in daddy ya dawo sai na gaya masa yanzu nana zaki iya kwana ke kadai to me zai sameni? shikenan safiyya zanje nayi sallah yana fita momy su ta shigo kina ina makira? nayi saurin fitowa ta cigaba da cewa to wallahi abinda zan gaya miki ki fita daga harkar dan in kina ganin uwarki ta cinye zuciyar alhaji toke kinyi kadan ki cinye tasa...........


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[9/25/2016, 2:57 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

3⃣5⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–




murmushi na saka zahra'u ni safiyya a golar gida nafi karfin danki kece kike kishi akan danki har kike tunanin ko auransa zanyi umma kuma da kike maganar ta cinye zuciyar mijinki ladabi da biyayya ta fiki ina fadar haka nayi daki.
tun da ga ranar ban kara ganin khalifa ba yau ina kwance naji shigowar message dagawa nayi tare da budewa 'please safiyya kin ban dama na kiraki mu gaisa na rasa ya zanyi bana so na kira ba tare da amince warki ba. naku muhammad I salis. muhammad na kara mai mai ta sunan kwata kwata na manta dashi filashin nayi masa ba,ayi mintu biyu ba ya kira "Assalamu alaikum naji sansanyar muryarsa ta doki kunne na safiyya kin amince na dinga kira muna gaisawa kau nifa na mance da kai sai ka tuna min waye kai bakin ciki ne ya tunkare zuciyarsa da kyar ya iya hadiyewa tare da cewa ni kam kinga bazan taba iya mancewa dake ba koh? sosai ma kuwa kina lafiya ya karatu? lafiya klau karatu mun godewa Allah safiyya ni baki tambayeni ya karatuna ba, meye ruwana sa karatunka kaga maganar ta isa haka zan kwanta, bai kamata ki kwanta haka ba cikin mamaki nace saboda me? ki tashi ki roki ubangiji bukatunki ko ki daura alwala ki kwanta.' okey na gode
ina cikin sallah naji wayana na kara bayan na idar nayi addu'o'ina na dauko littafin da momy ta ban na karanta "MASOYINA HAR ABADA" na mrs umar. ina cikin karantawa wayata tayi kara na daga, na zata kinyi barci ga karatu nan zan sa miki, to na gode ina saurara muryar sudeis naji cikin suratul rahman tun ina bi har barci ya dauke ni muryarsa naji safiyya iya nan kika iya? firgit na bude idona cikin wata rikitacciyar murya nace ka kashe kar kudinka ya kare wata irin ajiyar zuciya ya sauke kiyi addua sai na kashe kan ya kara wata magana na katse wayar.
washe gari umma ta kirani mun jima muna hira muna cikin waya naji sallama juyawa na momy ne tare da farida na hango tare muke karatu da ita yar katsina ce da gudu na taro su. yanzu baby ke kadai kike kwana momy ya zanyi umma ta tafi ta barni na juyo wajen farida yaushe kika dawo ina kuma tsarabata uhum suppy kin fiya ban haushi kudi kawai na karbo kin san saura sati daya mutafi.
sai bayan isha suka tafi na gama shirya tsaf zan kwanta naji karar wayat sai da ta kusa katsewa sannan na daga' na zata kinyi barci yanzu nake shirin yi dai okey safiyy wai me kike karantawa ne?? da sauri nace meye ruwanka da abinda nake karantawa, laifi ne dan na tambaya?? to ba zan fada ba".


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[9/25/2016, 4:07 PM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

3⃣6⃣
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–




shi kenan safiyya na dai kusa dawowa nazo na ga nana safiyya. baka da hankali kan yayi magana na katse wayar.
yau ya rage saura kwan biyu mu tafi umma kuma gobe zasu dawo duk wani kayana dazan bukata na hada su har ma na zubasu a boot.
yau tsakar dare zasu sauka gobe da safe suna gida na gama duk wani shirina zan kwanta dauki nake gari ya waye naga ummata rediyo na na kunna ina sauraran karatun alkur,ani har bacci ya daukeni cikin barci naji kamar mutum a bayana hannu na kai na taba bayana nayi ba komai dan haka naci gaba da barci na can kuma sai naji kamar ana shafan jikina firgit na tashi na hau dube dube banga komai ba, tsoro na ya kamani, da sauri na nufu kofa zan fita ji nayi an dauke ni cak an cilla gado kan nayi ihu naji an toshe bakina kan na dago naji an danne ni, cikin wata siririyar mury naji magana'yau zanyi maganin rashin mutuncin da kike na keta abinda kike tinkaho karfina na saka na shiga ture shi na kasa ganin yana neman yi min babbar illah naji wani irin karfi yazo mun yunkurawa nayi iya karfina na tureshi nayi saurin mikewa jikina yana rawa kokarin fita nake naji an rungume ni iya karfina na kama naman wuyarsa na ciza ba shiri ya saken, ji nayi ka fata ta bugi cup din glass ba wani bata lokaci na dauka yan kara matsow na buga masa har sanda ya pashe, wata mahaukaciyar kara ya saka bashiyi ya zare sakata ya fita a guje, da sauri na kunna fitila nayi saurin rufe kofar gani nayi bakin kofar ya bachi duk da jini, a wajen na tsugunna ina kuka waye wannan? wake shirin cutardani? burina gari ya waye umma ta dawo wallahi sai mun bar gidan nan ta gama auren.
ina zaune har gari ya waye buga kofa nakeyi kamar za a balla na tashi da sauri na bude, ji nayk an zabgan wani mugun mari a gigice na dago ina kallonta. hajiy ce babar alhaji nasiru zo ki bar gidan nan karuwa Allah ya tona asirinki. a razane na dago kai tsawa ta dakan zo ki bar gidannan yau Allah ya tono asirinki shegiya karunwan ban.......kan ta karasa na daga hannu iya karfina na zabga mata mari tare da hankada kofar na mayar na rufe naci gaba da kukana
umma naji tana kiran sunana nayi saurin budewa ina ganinta na fada jikinta ina kuka umma kizo mu bar gidan nan Allah kin gama auren, tunda kin kashe auren dole ki fadi haka nana baki kyauta min ba meyasa kika fadi haka? nana kin kawo saurayi gidan nan har kuka kwana da abba ya ganki shine kika dau abu kika fasa masa a kai safiyya me yasa kika mari babar alhaji?? karon farko da umma ta ba kiran sunana kai na shiga girgiza mata nama kasa magana dakyar na iya furta umma karki min haka kin fi kowa sanin halina, wallahi sharrin abba ne shi ya shigo dakin da da..... maganar hajiyar mukaji kuzo ku bar gidan baya sake ki ba? kuma ki saurari kiran kotu keda karuwar yarki yunkurawa nayi na kanga dady ya rikeni a hankaki naji muryarsa kiyi hakuri safiyya nasan shari abba yayi miki, zuciyata tana gayan ba zaki taba aikata haka ba komawa nayi daki na dauko jakata hannun umma naja muka fita tunda muka shiga mota nake kukan bakin cikin sharrin da abba ya kullamin..
a bangaren umma tunanin ya zasu kwashe da kaka take, har kofar gida ya kaimu na zaro dari biyar na mika masa kana na zaune a zaure taga shigowar umma da murta ta tashi rakiya saukar yaushe ganim hawaye na bin fuskarta yasa tayi shiru lafiya kike ku..... bata karashe ba taga shigowa na ina jan akwatun umma sai yanzu umma taji kuka yazo mata haka zaki zo kina kuka farar takarda ta mika mata babah alhaji ya sake ni. jawaf tayi ta zauna yanzu rakiya sai da shaidaniyar yarki ta kashe auren nan. inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, na shiga uku ni safiyya wannan yarinyan kin gama asara ai wallahi gara da alhaji muntari bai karbi cikinki ba in da ya karbeki a matsayin yarsa da bakin cikin kine zai kashe shi. umma ce ta taho da gudu zata rufe mata baki tayi saurin dokw hannunta taci gaba da cewa kuma wallahi ba zaki zauna a gidan nan ba sai dai ki nemi wajen zama inda kika raba yata da gidan aurenta to wallahi ki tafi waje ki nemi ubanki kalmar da ta dinga yawo cikin kunne na kenan ji nayi numfashi na yana neman daukewa kan umma na nufa da gudu.......

TO BE CONTINUE SOON!!!!


MUHD ABBA GANA
09039016969

πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[9/30/2016, 11:48 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

σΎ °σΎ ΄
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–



Kan na karasa babata tareni wani irin mari ta sabgan nan take wajen yayi ja iya karfinta baya baya naji nake nayi saurin dafe bango cikin wata irin murya na furta umma gayan gaskiya me maganar babah take nufi akaina ban da uba sai yanzu naji wani marayan kuka ya zomin umma tambayarki nake gayan gaskiya ni din shegiyace ban da uba? tana kuka tace nana kina da mahaifi wallahi ke ba shigiya bace nana matsala aka samu har mahaifinki ya ki kar.........karki karasan labarin bakin ciki na yarda ni din shegiya ce, wayyo Allah na umma na barki har abada ba zaki kara ganina ba cikin kuka umma tace nana karki guje ni ki tsaya ki saurari maganar da zan gaya miki wallahi kina da ub.....kuka yaci karfinta ta kasa karasawa na juyo ina kallon babah dakyar na iya bude bakina na furta na gode babah da wannan mummunan labarin na kuma ji dadi gayan matsayina da kika yi yanzu nasan wacece ni din ina fadar haka na juya har nakai bakin kofa naji muryar babah zonan safiyya.

nayi saurin juyowa ina girgiza kai wallahi babah bazan kara shigo miki gida ba zanje nayi rayuwata ni daya ina fatan ubangiji yayi gaggawar daukar raina na huta da wannan bakin cikin na juya ina kallon umma wanda take tsugunne tana ta faman sharman kuka kan babah ta kara magana har na fice koh ganin gabana ba nayi kawai saka kafata nake ba tare dana duba ba ji nayi an taka birki zuro kai akayi daga cikin adaidaita sahu haba baiwar Allah tunanin me kike har kika hau titi sai lokacin na kula kan titi nake karasawa wajensa nayi tare da cewa malam tafiya zakayi yace ehh ina zaki B.U.K shigo muje tunda nashiga na hada kai da gwiwa nayi gaba da kukana. hajiya ciki za,a shiga? naji maganarsa muje ciki har bakin dakinsu farida ya kaini na zaro kudinsa na basa, ita daya ce a dakin tana duba kittafi taji shigowata tayi saurin dago kai suppy daga ina da san.... hawaye data gani a fuskata shi ya hanata karasawa.
karasawa nayi na zauna akan katifarta safiyya lafiya kike kuka?? babu irin magiyar da farida ba tayi ba akan nayi shiru nayi mata bayani, har ta gaji cikin fushi tace tun dazun nake lallabaki kiyi shiru ki min bayani meye yake faruwa kin ki kigayamin kin fi rabin awa kina kuka tunda ba zaki gayan ba bara na kira ruky ki gaya mata ta dau wayarta ta fita.
ba,a fi minti talatin ba suka shigo tare da momy gatanan ruky tun dazun nake lallabata tayi shiru taki momy tayi saurin dagoni ganin yadda fuskata ta kumbura yasata gigice safiyya dukanki akayi na girgiza kai ina kuka to mota ne ya bigeki na kara girgiza mata kai hannuna ta kama muka fita motarta muka shiga baby kin fa tayar min da hankali ki gayan meyake faruwa.
A fusace farida tace me kika dauke mu maciya amana tun dazun muke miki magiya ki gaya mana meye yake faruwa kin ki ki zauna ki tayi ta bude motar ta fita.
momy ta juyo tana kallona baby yau na ga matsayina ashe duk momy da ake gayamim a bakine zan tafi gida ganin ina kokarin bude motar zan fita tayi saurin rike hannuna zauna safiyya bana son ki gayamin damuwarki bara muje na sauke ki a gida, cikin dashewar murya tace momy bazan koma gida ba na bar gida har abada baki ta rike tana murmushi baby har yanzu ke din yarinya ce to yanzu ina zaki kwana kan gobe mu tafi? nima ban sani ba muje gidan mu momy ki bar....karkice komai nasan wannan kukan bai barki kinyi break ba taja muka tafi Al'amin restauranta muka nufa ita daya ta ta dawo da take away shigowa tayi to bude maza cinye mu wuce momy bazan iya ciba hannunta tasa ta debo bara nayi miki ta yara haaaaa babyna" cikin dabara naci abinci sosaiπŸ™„.

baby har yanzu baki min magana ba sai ajiyar zuciya kike kin tayar min da hankali har farida tayi fushi bara muje chemis su dubaki.

school muka koma ta samu waje tayi fakin baby bara naje wajen prof adam. na daga mata kai dai da taga nasha maganin sannan ta fita bayan na koma nan take barci ya dauke ni dab da magariba na farka, momy na hanga a gabana tana waya tayi saurin juyowa tana murmushi baby kin tashi na daga mata kai tun dazun nake jiranki kitashi momy me yasa baki tasheni ba? gara ki tashi da kanki ruwa ta mikomin na fita na yi alwala nashi sallah tare muka kwanta ina jin munsharin momy tunda na kwanta na fada duniyar tunaniπŸ€”.


πŸ…°bbagana hausa novels @ faceebook.
[10/1/2016, 10:53 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

σΎ °σΎ ΅
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–Β©




me yasa umma ta min haka taje ta hanyar banza ta samu cikina ya zanyi da raina meyasa ban bari abba ya aikata abinda yaga dama dani ba, na rama abinda umma ta min ji nayi kaina yayi wata irin sarawa nayi saurin dafe kaina tare da kiran sunan Allah,me yasa tun da ban taba tunanin ina dangin babana suke ba tabbas maganar babah gaskiyace inda da uba duk daya mutu ai yan uwansa zasu iya zuwa su ganni ko ita ta kaini in gansu meye dalilin boye min gaskiya umma koh Alhaji muntari shine wanda suka hadu da umma ta haifeni? wani irin kukane ya kamani momy tayi saurin tashi lafiya safiyya kike kuka? kai kawai na girgiza mata ta matso kusa dani tare dafa kafadata cikin sanyin murya tace haba safiyya kina abu kamar ba musulma ba duk wani tsanani yana tare da sauki kiyi hakuri ki tashi ki kaiwa ubangiji kukanki wallahi na tabbata in har kika mika wuya kika gaya masa abinda yake damunki na tabbata zaki ga komai yazo miki da sauki ki tashi kiyi sallah ki kai kukanki wajen ubangiji kai kawai na daga mata na shiga toilet na dauro alwala kwana nayi ina kaiwa ubangiji kukana.
karfe takwas muka fito dakin hajiya muka shiga bayan mun gaisa tace har kun shirya?? mun shirya kin san takwas da rabi zamu tafi ai tun dazun Alhaji ya fito baku tashi ba kuyi maza ku karya kan ya kara saukowa tunda muka zauna na shiga rijiyan tunani.


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[10/1/2016, 11:17 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

σΎ °σΎ Ά
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜ πŸ’˜

πŸ’–MUH'D*ABBA*GANAπŸ’–




momy tace maza ki ci abinci kan abba ya sauko momy bana jin yunwa bakin ciki ya cika zuciyarta okey kin jawa kanki hajiya tace sai kin gaya mata meye yake damunki haka na dinga turawa kamar madaci
saukowa yayi yana kiran rukayy tayi saurin amsawa da cewa tunda zun abba muke jiranka au abun ya koma karya saukowata uku baku tashi ba.
dakin hajiya muka shiga ta jima tana yi mana nasiha tare da bamu addu'o'i sannan muka kama hanyan makaranta.
mun jima yana yi mana nasiha a cikin motarsa sannan muka fito dakin farida muka shiga bamu jima da shiga ba wata yarinya rashida ta shigo ana kiran safiyya muktar nayi saurin dago kai rashida wa yake kirana? alhaji nas...' karki karasa sunansa rashida kince masa ina nan? ta girgiza kai cewa nayi bara na duba toh kice masa bana nan cikin mamaki momy tace saboda me? momy bana son ganinsa kwata kwata in kika matsayan naje wajensa Allah kema zaki rasani, bazaki kara ganina ba. shi kenan ya isa ta juyo tana kallon sadiya fita kice bata nan rabuwarku da ita tun ranar jumma'a . yana tsaye a jikin motarsa ta karasa dady an tashi lafiya? ina safiyya? cikin mamaki me hade da tashin hankali yace bata zo nan ba? au dady na zata ita ka kawo rabona da ita tun friday. ba ita na kawo ba nemanta nake tun jiya ido ta zaro dady me yayi zafi nema a jalloh haka. babu amma don Allah yanzu ina kike ganin za,a sameta? gaskiya dady ban sani ba saboda ita safiyya bata da kawaye ni daya ce kawarta sai rukayya kuma muna tare da rukayya toh kina ganin zata iya tafiya lagos da kanta? nima yanzu nayi tunanin hakan tun jiya wasu suka fara tafiya yafi minti biyar bai yi magana ba can ya numfasa tare da cewa sadiya ga wannan in har kin jeh kun sameta ki bata kuma ki ban lambarki in kin sameta kin min waya dan Allah ya miko mata karamar farar jaka toh dady insha Allah da mun hadu zan bata.
dakin ta shigo tare da mikamim leda gashi a fusace na dago sadiya ce masa ki kayi ina nan? auntyn masifa cewa yayi in mun hadu a can na baki farida mikomin ledar karba tayi tasa a jakarta tare da zabgan harara.

karfe goma mota ta daukemu a bangaren umma kuma.........


πŸ…°bbagana hausa novels @ facebook.
[10/3/2016, 8:15 AM] πŸ’–Γ„bbΓ₯-GΓ£Γ±Γ’πŸ’–: πŸ’˜WAYE SANADI?πŸ’˜

σΎ ±σΎ ·
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜πŸ’˜ πŸ’˜πŸ’˜
πŸ’˜

Please Login or Register in order to submit comment