Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dago yana kallon Rukayya (Momy), suna hada ido ta tafi ya zama daga ni sai shi a dakin.“Safiyya bude idonki.”Ban yi musu ba na bude sai dai na kasa dagowa na kalle shi.“Ki yi shiru ki bar kukan nan kar kanki ya yi ciwo.”Na ce, “Abba don Allah ka gayan gaskiya ta wace hanya ku ka haifi ni.”Kai tsaye yaban amsa da cewa ‘Safiyya ta hanyar aure muka same ki.” Na kara cewa, “To me yasa ka ki karBata a matsayin ‘yarka?”“Safiyya ki kaddara haka Ubangiji ya shirya, kuma ba mu isa mu wargaza shirin Ubangiji ba ya riga ya tsara haka za ta faru a gare mu in har kin yarda da lamuran Ubangiji to kar ki dau wannan kaddara ki mata mummunanar fassara, ki dau hakan wata jarrabawa ce da Ubangiji ya yi miki.”“To yanzu me ye matsayina a wajenka? ”Ya dan yi dariya, sannan ya ce, “Tun farkon ganinki a matsayin kawar Rukayya Allah ya zuban kaunarki a lokacin da ki ka bata na shiga tsantsar tashin hankali ni kaina wnai lokacin na kan tambayi kaina me ye yasa na damu da batan ki? Ashe ban sani ba ke ‘yata ce.”Na katse shi, ‘Abba ka yarda yanzu ka karbe ni a matsayin ‘yarka
Baba ta daina yi min gori.”“Tunda na ganki zuciyata take gayan duk abin da Rukayya ta haifar min nawa ne sharrin makiyanmu ne ya raba mu, na yi neman Rukayya na rasa sai jiya Allah ya hada mu. Safiyya nayi matukar farin ciki da Allah ya ban ke, zan baki kulawar da duk wani uba yake bawa ‘yarsa. Na rasa in da zan saka zuciyata don murna abin da na fitar da ran samun sa yau ga shi Allah ya ban.”Da sauri na ce, “Abba kannena nawa?”“Safiyya ke daya Allah ya ban, k...”Kan ya karasa Alhaji Nasiru ya shigo, yana ganina a zaune fuskarsa ta fadada da murmushi ya karaso da sauri. ‘Sannu Safiyya kin tashi.”Na dan sunkuyar da kaina na ce, “Dady na tashi,ina Khalifa?”‘Khalifa
yana gaishe ki, dazu ya zo kina barci, kuma lokacin zai wuce Bauchi kin san ya samu aiki a can Bauchin.”Na ce, “Allah ya sanya alkhairi Dady, ina su Hassan?”Cikin mamaki ya ce, “Wa ye ya gaya miki Umma ta haihu?”Na dan yi murmushi sannan na ce, “Imran ne ya gayan har ma ya kai min su na gani lokacin da ku ka je nemana can Lagos din.”‘Kai wannan yaron bai kyauta ba, a haka kamar na zai aikata haka ba.”Abba ya ce, “Daman shi mutum ai ba ka san in me ye yake zuciyarsa sai Allah, amma ni ina ganin bai kamata mu bar shi a hannun court ba, kawai a karbo shi mu yi abin mu cikin sirri ba sai an fantsamawa duniya ba, kuma ko don iyayensa sai a rabu da shi tunda Allah ya kubutar da ita.”Dady ya ce, “Ni kaina na so haka, amma mahaifiyarsa ta ce abar shi alkali ya yi masa hukuncin daidai da laifinsa, don dazu muka yi waya da mahaifinsa, shi ma haka ya ce a rabu da shi.”Ya dan juyo wajena, ‘Safiyya ya aka yi ya dau...” Da sauri na ce, “Abba bana san hirarsa don Allah ku bar fadan sunansa, Allah zan iya mutuwa.”Ina fadar haka na saka kuka.Daddy ya ce, “Ki yi hakuri Safiyya ba za mu kara hirarsa a gabanki ba, ki bar kukan nan kar su Hassan su zo su ga Antynsu tana kuka.”Yana fadar haka na yi shiru ya juya wajen Abbana yana murmushi, sannan ya ce, “Alhaji Mukhtar zan je gida ina tunanin kuma ba zan dawo asibitin nan na tadda
ku ba, na ji yana anjima zai sallame mu tunda ta farka.”‘Haka ne Alhaji Nasiru na gode da kulawar da ka bawa Safiyya bakina ba zai iya fadar godiyar a wannan lokacin ina fatan zuwa har gida don....”Kan ya karasa ya katse shi.
“Haba Alhaji Mukhtar me ye abin godiya ni na dau Safiyya kamar ‘yar da na haifa, duk abin da na yi mata na yi don Allah.” Sannan ya juyo wajena ya ce, “Safiyya gidan Ummanta ki za ki tafi ko gidan Abban naki za ki tafi?”Kan na yi
magana Abba ya ce, “A’a gidana za mu tafi ta dan kwana biyu ko?”Na dago da sauri na ce, “Abba ina san ganin Ummata fa, ka bar ni in kwana daya sai mu tafi gidan naka.“Duk abin da kike ina so, bari li kita ya sallame mu sai na kai ki ” Na dan yi murmushi na ce, “Na gode Abbana.”Daddy ya ce, ‘Ni ba za ki zo ki kwanar min ba.”Ban yi magana ba sai kaina
da na sunkuyar. Abba ya ce, “Kai ma za ta zo ta yi maka kwana biyu ko don Khalifa.”Tare suka fita. Suna fita Rukayya ta shigo.‘My Sister kuna ta hire da Abba kin manta da Rukayya?‘Lah Momy ban manta da ke ba, hasali ma babu abin da yake raina sai ke da Sadiyya.”‘Tana ina na ba ta hakuri? Na san na muku laifi. Momy a yi min afowa ba zan kar...”Kan na karasa ta katse ni da cewa, “Baby bana san tuna baya abu ya riga ya wuce komai sai labari. Sadiyya ta je gida wanka tun jiya muna nan muna kukan mun ga samu mun ga rashi ga baby ta dawo kuma za ta gudu ta bar mu.”Na dan yi murmushi, ‘Ga ni Momy insha Allahu muna tare.” Na dan yi shiru.“No baby, Doctor ya hana ki tunani.”‘Momy ba tunani nake ba, ai tunani ya kare na ga Abbana.” Na dan girgiza kaina.“Momy don haka muke kaunar juna tsakani da Allah ashe Momyta ‘yar uwata ce ta jini, Momyna kuma Antyna, Kawun Momyna da ya nunan kauna tun kan ya san wace ce ni yake nuna min kauna har ya yi min kyautar da bazan taba mancewa da ita ba.”Na sauke numfashi sannan na tambaye ta cewa “Ina Ummata?”
“Ai tunda ki ka farka Umma ta tafi gida tare da Sadiyya, Abbana ya tafi ya kai su gida.”Kan na yi magana Abbana ya shigo tare da Doctor ya tambaye ni abin da yake damuna, na gaya masa babu abin da yake min ciwo sai idona da kaina da suke ciwo.”Magunguna ya rubutan sannan ya sallame mu. Muna kokarin shiga mota Abban Rukayya ya shigo, ya ganmu a tsaye tare da Momyna
tana min hire sai kokarin sani dariya take. Ya karaso fuskarsa dauke da dariya.“Na ji dadin ganinki haka Safiyya, Hajiyata na ta dokin ganinki amma can za mu tafi ko?”ta ce, ‘Abba, tun da ta dawo nakc ta lallaba ta yarda mu je gidanmu wai ita sai gobe, yanzu wajen Umma za mu kai ta.”Ya ce, ‘‘Wai haka Safiyya?”Abba ka yi hakuri ina bukatar ganin Ummata.'’ Na juyo wajen Momy na ce, “Haba Momyna ki ban na ga Ummata kwana daya kawai zan yi musu na taho wajenki, shi kenan na dawo nan bar abada.”
Ta juyo da sauri tana dariya.“Abba ka zama shaida Safiyaya za ta dawo gidanmu.”“To na zama shaida.”Sannan muka tafi har kofar
gidanmu Abana ya kai ni (da yake Momy ta bi Abbanta). Ya yi parking. Har na ziro kafa ta zan fito na ji muryarsa.“Safiyya zan
je nadawo mai ki keso na taho miki da shi?” Na girgiza kai.“A’a ki min magana bana san girgiza kai, in kuma wani abun ne yake damunki ki fadan yanzu mu koma asibit, bana san ganinki cikin damuwa.”Na dan yi dariya, sannan na ce, “Babu abin da yake damuna Abba, zuciyata cike take da tsantsan farin ciki, yau gani ga mahaifina farin ciki ne yake hana ni magana.”‘To in har kina farin ciki da kasancewa ta mahaifinki ki gayan abin da ki ke so na kawo miki anjima.” ' Da sauri na ce, “Abba ka kawo min kayan dadi.” tare muka fito daga cikin motar ya bude but ya firfito da manyan ledoji har guda hudu, daidai lokacin Kado ya fito daga cikin gidansu yana ganina ya saki baki cikin sanyin murya na ce Kado don Allah zo ka dibar min mu shiga. Ya dawo da saurinsa suka gaisa
da Abbana ya dibi kayan ya shiga na juyo wajen Abba na ce.“Abba bara ka shiga ku gaisa da Baba.”“Hum Safiya ina jin nauyin abin da
ya faru tsakanina da Baba, amma na san ke za ki zama SANADIN ganowar komai ki gaishe ta har Umma, anjima in na zo zan shiga mu gaisa. Yana fadar haka ya koma mota.Na shiga gidan tare da sallama, muka yi karo da Baba tana kokarin fitowa na dan yi murmushi. Ina kuma za ki gani na zo?” Ta sa dariya.“Ba zan iya zama ba sai na ganki, lallai da na yi wa gidansu yaji.”Na hango Hassan yana tafiya a jikin bango na karasa da sauri na daga shi.“My boy ina Ummanmu?”Kamar ya sani ya kama yi min dariya, na juyo wajen Baba wadda ta biyo baya na bakinta yaka sa rufuwa.‘Ga Hassan nan kamar ku daya babu abin da ya raba ku.”Da sauri na ce, ‘A’a Baba ni da Abbana
nake kama babu abin da ya raba mu, Hassan ko da Umma yake kama.” Na shiga cikin dakin tana zaune tana ba wa Hussaini nono, na karasa gabanta na tsugunna, Baba ta yi saurin fita ba. “Bara na kawo wa bakuwa abinci mai jaki, sanna na zo mu gaisa.”Na dan yi dariya na ce,
Umma an tashi lafiya.”‘Lafiya, ya jikin naki?”“Na ji sauki daman ciwon tunanin Ummata ne.”‘Inda kina tunani ba za ki tafi ki bar ni ba har tsawon shekara daya.”“No Umma ki yi hakuri ke daya zan bawa hakuri, Baba kora ta ta yi na san ba ta damu da rashina ba, ke daya
ki ka shiga damuwa, ki yi min afuwa don Allah ki yafc mini.”“Daman na riga na yafe miki, kuma ma tafi yarki ta zama SANADIN na haduwarki da mahaifinki.”Na dan yi dariya, na zauna a kusa da ita, Ina zama su Baba Magajiya suka shigo.Sai wajen karke hudu gidan ya zama shim, sai ni da Umma, sai kuma su Hussaini da suke wasa. Na jawo ledojin da Abbana ya ban na hau duba dogayen riguna kala-kala, sai mayuka da kuma
mayafai har ma da takalma masu matukar kyau Na nuna wa Umma.Ta ce, “To ki tashi ki yi wanka ki kara jin karfin jikinki.”‘Yanzu zan tashi bara na gama shiryawa su Hassan kaya,”Baba ta mi ke da saurinta, “Bara na kai muku ruwan.”Ina fitowa Momy ta yi sallama. Bayan sun gaisa da su Baba ta juyo wajena…



🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/21/2016, 8:47 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 💘WAYE SANADI?💘

8⃣5⃣
💘💘💘 💘💘💘
💘💘💘 💘💘💘
💘💘 💘💘
💘 💘
💖MUH'D*ABBA*GANA💖
www.MuhdAbbagana.blogspot.com





Tare fa da Kawu muke ya tsaya gaisawa da Malam ina jin yanzu za su shigo...Kan ta rufe baki Malam ya yi sallama suka shigo tare da Abba Tunda suka shigo yake raba ido ya ga inda zai hange ni. Baba ta yi saurin shimfida tabarma Bayan
sun gaisa shiru ta biyo baya sannan Umma ta leko suka gaisa.‘Baba duk wani abu da ya faru ya wuce don Allah Alhaji Muntari ya yi min bayanin abin da duk ya ja haka, kuma ga shi tun kafin a je ko’ina Allah ya bayyana gaskiya, kuma Allah ya yi wa
Rakiya sakayya akan kishiyoyinta tun a duniya wanda su suka biyo ta Rasa suka dasa kiyayyar Rakiya da abin da za a haifa a zuciyarsa, ga shi tun kan a je ko’ina Allah
ya nuna masu ikon sa, yau gashi gaskiya ta bayyana, ko me ya faru a baya ya zama tarihi, a yafi juna. Wanda ma ya halice mu muna masa laifi ya yafe mana ballantana kuma junanmu. Ina fatan komai ya wuce tunda shi ma ba yin kansa ba ne.”Baba ta dan sauke numfahsi ta ce, Allah ya yafe mana gaba daya, mu dama fatanmu Allah yasa ya gane gaskiya.”Abba ya jima yana ba wa Baba hakuri, sannan ya fito tare da malam, Rukayya ta ce, “Ki taso yau yawo za mu sha.”Da sauri Baba ta ce, “Au ba za ku bar mini ita ta dan kwana biyu ba.”Na ce, ‘Baba
ba kwana za mu yiba, na gayawa Abba zai bar ni na kwana biyu, ina ta dokin ganin Ummata, amma ta ki mu yi hira gara na san Abbana ba zai ki hira da ni ba. Amma Baba ko dan ke mu kwana muna hira.” Rabu da ita Safiyya irin wannan bakar mara kunyar ce ta yi min babban SANADI, kuma da ba kya nan tana kwana da hotanki tana kuka.”Umma ta dago da sauri muna hada ido ta sunkuyar da kanta muna dariya muka fita da Momyna. Sai da muka jira Abba suka gama magana da Malam, sannan ya taho wajenmu. Na tsugunna har kasa na kara gaishe shi, hannunsa yasa ya dago ni yana murmushi ya ce,“Ai dama mun gaisa ko?”
Na ce, ‘Eh Abba, amma in mun dada gaisawa baba wani laifi.”Na juya wajen Momy na ce, “Momy ina son mu
je wajen Daddyfa.”Lallai Baby ba ki san yawon da za mu yi ba, yanzu ba, yanzu haka Yakasai za mu daga nan mu je Hotoro, sannan mu je Sharada gidan Abba.”Sauran yawo kuma Abba zai bar mu mu jo tunda kawu ya ban mota.”Na dan sanya fuskata, To yanzu yausihe za mu gidan su Sadiyya ‘Ki bari zamu sa rana,
yanzu Hotoro za mu fara zuwa gidan Inna Binta.” Da sauri na ce,wa cece haka?”“Ke Yayar Kawu ce, ni kakata ce ke kuma babarkice Na dan yi murmushi na ce, “Abba kana ganin duk a yau za mu gama zuwa gidan da Momyna ta lissafo?“Insha Allahu za mu gama zuwa, dukka ninsu suna zimudi su ga diyar kaninsu. Yanzu Hotoro za mu fara zuwa, sannan mu je cikin gida (Yakasai).”tunda muka dau hanya Abba yake ba mu labarurruka masu dadi da ban dariya. Babu abin da muke ni da Momy sai dariya har muka karasa, ya yi parking a kofar wani madaidaicin gida.
Mu muka fara shiga. Momy ta yi wani loko tana k walawa Baba Laure kira, ni dai ina bin ta a baya. Tana shiga falon suka ci karo da Sagir (Jikan Baba Laure ne). Ta dan rage fara’ar fuskarta suka gaisa. Ya juyo wajena kur ya kuran ido, na ja dan siririn tsakin da yasa ya dauke idonsa daga kaina.Momy ta ce, ‘Kafa tsare mana hanya muna son shigewa fa.”Ya dan yi murmushi yana shafa kansa, ‘Sorry Barrister, na dan tafi tunani.” Yana fadar_haka ya juyo wajena na daure na ce.“An yini lafiya?” Ban saurari amsar da zai bani ba na shiga falon.Muna shiga ta cafi sunana (Ban yi mamakin jin ta ambaci sunana ba). Na karasa gabanta na zauna kamar na yi magana, ta ci gaba da cewa.
Duk wanda ya kalle ki ya ga jinin Muntari, ga shi nan kin debo shi kin kuma debo mahaifiyarki, ke har ma wannan berar kuna kama.” Tana maganar tana nuna Rukayya da take kwance a gadonta.Ta ce, “Kai Baba tsohuwa da ke har kin san kama?”Ina dariya muka gaisa. Momy ta ce, “Bara na yi kiran Kawuna...” Kan ta karasa suka shigo tare da Sagir. Mun shagala muna hira Momy ta mike ta ce,Kawu ka mance muna da tafiya mun tsaya biyewa ‘yar tsoh uwar nan, sai zuba
mana rikici take yi, in kuma ba kya rikicin tsofa to ki lissafan uku uku sau uku da rabi.”Tana dariya ta ce, “Ni dai yau ba zan biye miki ba, bare ki wahalar da ni yau. Ina murna da zuwa ‘yata ke kam bana maraba da ke.”‘Au! Haka ki ka ce?” Da sauri ta ce, “Na fada.”“Shi kenan zan ga me Kara kawo miki ita.” Da sauri na ce, “Baba ko ba ta rako ni ba na san hanya zan dinga zuwar miki da kaina har sai kin gaji da ganina.”“Ni kam ba zan taba gajiya da ganinki ba.” Sannan ta
juyo wajen Abba.“Amma dai barinsu za ka yi sai gobe? “Za dai ta zo ta kwanan yanzu za mu je Yakasai da can Sharadan.” Har waje sai da ta rako mu, Sagir ya miko min katuwar bakar leda.“Kanwata ga shi in ji Baba.” Nasa hannu na karba.Muna zuwa Yakasai gida ya rude da murna. Sai wajen karfe shida muka ta no tare da Baba da sadiya, don ita kam ta ce dole ta je ta ga ummanta.Sharada muka nufa na ga mun tsaya a get din wani tafkeken gida. Wani Buzu ya taso da saurinsa ya bude get din gidan tare dayi mana barka da zuwa abba ya Karasa rumfar ajiye motoci ya yi parking, muka fito,A hankali na cewa Momy, “Wannan gidan wa ye?”‘Gidan Kawu ne ”Gaskiya gidan ya burge ni, don iya haduwa ya hadu. Muna shiga babban falon gidan muka tadda kakar rukayya baba binta wanda suke gida tare da abbana Tana ganin shigowarmu ta mike da sauri ta nufa wajena tana faman
washe baki.“Lale marhabin da Safiyya. Allah mai iko ai ko a hanya na ganki zan iya bada shaidar ke ‘yar Muntari ce. Ina Rakiya
mahaifiyarki baiwar Allah?”Na karasa muka zauna. Ta kara tambayata, “Ina Rakiya? Bayan mun gaisa Abba ya mike ya shiga Bangarensa.
Rukayya ta ce, “Wato Kakus kin manta da ni ko?” Baba Sadiya ta ce, “To ba dole mu manta da ke ba muna ta sabuwar ‘yarmu.”
Baba Binta ta ce, “Ke ki ke ma ta ita, wata bera daita.” ‘Okey na yarda ni din bera ce, amma bari bera ta tambaye ku in dai ku ka ban amsa ni na san kyautar da zan muku Ni dai ina zaune ban da dariya babu abin da nake yi. Momy ta ci gaba da cewa, “Ku gayan arba’in da hudu a tara da sha uku da kuma rabin arba’in da uku.”Baba Sadiya ta ce, “Ni kam yau ba za ki wahalar da ni ba, z a ki fara lissafin abin da ba zai kirgu ba.”Baba Binta ta ce, “Kin ga Halima (Sadiya) rabu da bera ko saurayi ba ta da shi.”Na dan juyo wajen Momy na ce, “Momy ina san zan yi fitsari.” Ta mike muka shiga barin da Baba Binta take.Sai karfe bakwai muka taho daga gidan Kai tsaye gidan Momy muka nufa, Tun kafin mu karasa yin parking Hajiya ta fito, ina fiitowa ta rungume ni.Tana rike da ni har muka karasa falon, na dan zamo daga kan kujerar da nake muka gaisa. Momy ta ce, “Hajiya kin kasa magana sai kallonta ki ke?” Ta dan yi dariya, ‘Farin ciki ya cikan
zuciya nama kasa magana, sai Allah mun gode maka.” Ta shiga kiran Salim ya fito da saurinsa. Yana ganina ya tsaya cikin tsantsan mamaki,
sai kuma ya hau dariya.Baba Sadiya ta ce, ‘To shashasha haka ake murnar kasa mu a gaba kana dariya?” Ya juyo wajenta da sauri, ya dan tabe baki ya ce, “Yau ma kin zo biko na ne, na ce na sake ki saki dubu, bana auren yanzu an daina yayanki sai yarinya sabon jin....” Dukan da ya ji a bayansa shi ya hana shi karasa abin da yake bakinsa. Ya juya da sauri sukayi ido hudu da Abbansa ya matsa gefe da sauri
yana shafa keya.Abba ya ce, “Wato ka sa min mahaifiya a gaba kana mata dan biki.”“No Abba soyayya fa muke.” Ya juyo yana kallon Baba Sadiyya
ya ce, “Darling ki gaya masa don Allah ba soyayya muke ba?”Tana dariya ta ce, ‘Gaskiyar na karfen muna maganar zuwa hoto ne ka zo kana dukar min maigidana. Dukkan mu muka sa dariya.Sai wajen karfe takwas muka fito daga gidansu Momy. Dakyar Momy ta yarda na taho mu da Baba Sadiya. Ina shiga soron gidanmu na jiyo hayaniyar Baba na karasa da saurii Tana garina, tace Yauwa ga yar halak.” Ina shiga falon na hangi Alhaji
Nasir tare da imran sai ‘yan sanda biyu da suke bayan Imran. Baba ta ce, “Zo nan ki zauna daman maganarki muke,”Na ce “Baba tare muke da Abbana Yauwa maza ki yi kiransa ya shigo,”Bayan sun shigo na mike zan shiga daki Abba ya dakatar da ni na dawo na zauna kusa da kafarsa.‘Baba me ye yake faruwa ne?” Abba ya tambaya. Baba ta ce, “Wannan shashashan yaron ne ya zo mana da wata magana wai Safiyya matarsa ce don an daura musu aure a can inda ya tsare ta.”Cikin fusbi Abba ya ce, “Kai ba ma son iskancin banza, don ka ga mun rabu da kai ba mu dau matakin Boye mana
ya da ka yiba shi ne za ka zuwa da mutane da maganar banza. To uban wa ye ya daura muku auren? Wallahi ka yi sa’a na rabu da kai ne darajar mahaifiyarka da Alhaji Nasir ne. Dube ka a haka kamar mutumin kirki.”Ya dago fuskarshi cike da ruwan hawaye, muryarsa na rawa ya ce, “Abba na san na yi muku laifin da na cancanci duk wani hukunci, kuma wallahi ban boye Safiyya don wani abu ba, sai don in ceto ta daga fadawa mugun hannu. Ina kaunarta tsakanina da Allah, na rantse da girman Allah Safiyya matata ce saboda kakana ya daura mana aure kuma ku tambaye ta ga ta nan da amincewarta aka daura mana aure.” Ya juyo gare ni.Kaina yana kasa, amma jikina ya ban ni yake kallo. Na ji muryarshi ta doki zuciyata. “Safiyya ki gaya
musu gaskiya tsakaninki da Allah ke ba....” Kuka ya ci karfinsa ya kasa karasawa.Falon ya yi shiru babu abin da ka ke ji sai ajiyar zuciyar Imran. Abbana jikinsa ya yi sanyi da jin kalaman Imran. Baba Sadiya ta kalle ni ta ce.“Safiyya ki fadi tsakaninki da Allah shin da aurensa a kanki?”Na yi shiru
har sai da Alhaji Nasir ya kara tambayar, sannan na ce, “Na san an daura mana aure da shi, amma bisa sharadin da an daura zai sake ni na taho Kano.” Na dan yi shiru. Abba ya ce, “Ki yi magana mana, to me?”“Abba tunda aka daura nake nacin ya sake ni ya ki har zuwa ranar da na taho.”Baba ta ce, ‘Yanzu dai
kenan da aurensa a kanki?” Kafin na yi magana Abba ya ce, ‘To kai Imran mun yarda an daura muku aure, to kuma ga shi ta fada kun yi bisa sharadin za ka sake
ta, don haka ya zame maka dole a yanzu ka sake ta Ya hau girgiza kai. “Abba ba zan taba sakin Safiyya ba ko da za ku dau raina, ina fatan na mutu a mijin .
Safiyya. Ina sonta tsakanin da Allah, kuma ita ma tana sona.Na dago da sauri na kalle shi cikin sa’a muka hada ido nayi saurin dauke idona. Na ce, “Allah ni karya yake min bana sonsa bana kaunarsa, mai sonsa ma bana sonsa.”Baba ta ce, “Ni kaina bana fatan ki auri wannan ' mugun kuma ko ta tsiya sai ka sake ta.”Baba Sadiyya ta ce, ‘A dai bi komai a sannu kar mu yi shishigi a lamarin Alla..”Kan ta karasa dansandan da yake bayan Imran ya ce, ‘Lokacin ka ya yi magana suka mayar da ankwar da take hannunsa Na juyo wajen Abba da sauri na ce, “Don Allah Abba kasa ya sake ni kar ya tafi. Kar ki damu kanki
Safiyya ya zama dole ya sake ki. Alhaji Nasir ya ce, ‘In ma bai sake ta ba Court ya raba auren Har sun kai bakin ksofa Imran ya juyo fuskarsa cike da
hawaye ya ce, “Dady ina fatan samun goyen baya daga wajenka, amma kai ka fara shigowa da maganar court, to wallahi ban ga court din da za ta raba auren....’Kan ya karasa ‘yansanda suka hankada shi waje



🅰bbagana hausa novels @ facebook.
[12/22/2016, 9:51 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖:

Please Login or Register in order to submit comment