Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–



magajiya kin kyauta kinyi yanda ranki yake so kin kori jikarki kin kuma jefa yarki cikin bakin ciki me ki kayi kan wani dalili naki na banza waya gaya miki saffiya ce ta kashewa rukayya aure daman can Allah yayi aurenta zai mutu baki tsaya kinji abinda ya faru ba kika bata yarki a idon yarta cewar mallam mado, mallam kayi hakuri raina ne ya bacu dan ranki ya baci sai hankalinki ya gushe, ke yanzu zaki iya rantsewa safiyya bata da uba? kin bata yarki kan zigar shaidan kinga kin nunawa safiyya uwarta tayi yawon duniya to har sunanki kika bata ke din ina uban rakiyar ta taba ganinsa? ko ta taba ganin danginsa to kinga kema zata dinga miki ayar tambaya. ya juyo wajen umma wadda take ta faman share hawaye rakiya ki kwantar da hankalinki ki mikawa ubangiji lamarinki na tabbata safi....' sallamar alhaji nasir ce ta katse masa maganar bayan sun gaisa da mallam ya juyo wajen umma rukayya har yanzu baki bar kukan nan ba baki ji maganar da likita ya gaya miki ba? tayi saurin goge fuskarta babah tace me likitan yace mata? lokacin da muna makkah tayi zazzabi har ta kwanta shine muka je asibiti likita yake gaya mata tana dauke da juna biyu.

a razabe babah ta dago kai tana sallati yanzu kaima sai dai kaga tana da ciki shine ka saketa wato kai ma kana so ka mata sharri kace ba naka bane?? cikin mamaki ya dago kai babah wani ya tabawa rukayya sharri?? kar kimin mumunar fassara ki kaddara aure na da rukayya Allah ne ya kawo rabuwarmu rabuwarmu ba zata hanamu karbar kyautar ubangiji da yayi mana ba ina so...... maganar maganar mallam ta katse masa abinda yake so ya fada Alhaji har yanzu babu labarin safiyya?? wallahi mallam duk inda nasan zan sameta naje nasa an duba amma shiru ita kanta kawarta sun sauka a lagos din tace babu irin nemanta da ba tayi ba har wasu makarantun taje bata ganta ba. umma ce ta kara fashewa da kuka.
sallama tayi har wajen sau uku taji shiru dan haka ta shiga daki ina zaune nayi nisa cikin tunani har ban san lokacin da hawaye yake bin fuskata ba har ta karaso kusa dani hmmm saffiya Allah ya kyauta miki wallahi in wata cutar ta kamake ke kika saiwa kanki kin zauna kina tunanin banza momy ta fada cikin fishi nayi saurin dago kai na ta cigaba da cewa mutum baya jin nasiha tunda muka zo garin nan yau sati daya kullum kina daki baki da aiki daga kuka sai tunani damarki ta karshe in kinki ki mayar da hankalinki kiyi karatunki wai ma me kika dauki kanki?? da ubangiji ba zai saukar miki da kaddara ba? wallahi kinji na rantse in har baki cire wannan halin ba zamu yi fada ta mike zata fita nayi saurin riketa momy kiyi hakuri ta juyo tana hararata me kika min da sanyi hakuri sakarmin hannu na fita momy kiyi hakuri zan gaya miki abinda yake damuna amma bisa alkawarin zaki boye min sirrina ina zuwa tace kofar ta rufe ta dawo kusa dani ina sauraronki.


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[10/3/2016, 3:59 PM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

๓พ ฑ๓พ ฎ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969



nan take na bata labarin abin da ya faru tunda ga shigowar Abba dakina har kawo sakin da Alhaji nasir ya yiwa umma muka dawo gida har karshen maganar. yanzu baby kan wannan yar matsalar kike tada hankalinki? cikin kuka nace momy wannan ce yar matsala rashin ubane karamar matsala? safiyya ke din baki da shedar da zaki gaskata haka umma tana ki tsaya ki saurareta kawai shedan yana ingizaki kika tawo kika bar mahaifiyarki cikin wani hali me yasa baki tsaya sauraran maganar babah din ba, fuskanta cike da hawaye na dago kaina momy me zan tsaya naji daga wajensu momy a lokacin nan in har na tsaya na cigaba da sauraran maganar babah zuciyata zata iya bugawa wallahi a yanzu nafi bukatar mutuwa momy bana fatan na kara ganin ummata momy ina ji cikin zuciyata kamar na shiga duniya na rama abinda umma ta min.
saffiya har yanzu ke din yarinya ce ke yanzu kina ganin in kin shiga duniya umma kika cuta? toh ina kina tunanin haka ki daina wallahi kanki kika cuta ke baki tsaya kin saurari maganansu ba. kina ganin Allah ba zai kamaki da laifin tayar mata da hankali da ki kai ba ki duba irin sonki da umma take miki amma....nayi saurin kaste ta momy ai don tasan bata da gaskiya ne shi yasa ta nuna min so da kauna kuma wallahi duk ranar dana gama karatuna saina shigar da umma kara ta nuna min ubana na ganshi ko waye ne s....kan na karasa momy ta dakan tsawa waike baki da hankali ne in kin kai umma kara wa kika tonawa asiri ki, zaki zo kiyi na dama ta cillo farar leda ga sakonki da dady ya bayar a kawo miki kuma wallahi in baki shiga hankalinki ba zanyi waya na gaya masa muna tare naga mutum ne kamar kafiri baijin lallashi ๐Ÿ™„ kuma ki dauka kiga meye a ciki. akan dole na karba na bude kudine rafa biyu yan dubu-dubu sai kuwa wasika ta dada daure fuskarta karanta mana cikin kuka nace momy bana son jin bayaninsa don Allah ki rabu dani bazan karanta ba.
wallahi sai kin karanta in kuma har baki karanta ba karki kara tunanin kinsan wata rukayya ta mike zata fita na riketa momy karki gujen dan Allah bari na karanta da kanta ta warware ta miko min dole na dora idona kan rubutun nasa.
"safiyya me yasa kika yankewa kanki irin wannan hukunci da zaki zo kina nadama wallahi safiyya nasan sharri abba yayi miki please safiyya ki dawo kin daga mana hankali ummanki tana cikin damuwa don Allah ki dawo garemu ki rungumi ummanki da yan biyu da zata haifa miki " wata irin zabura nayi umma zata haifa min kanne? wani cikin shegen tayi umma kin cucen kin cuci abinda zaki..... bakina naji an buge shi yasa ban karasa abinda nake son fadaba ta mike a fusace banza mara hankali tana fadar haka ta juyo zata fita kai na naji yayi wata irin sarawa wata irin kara na saka wadda ta dawo da momy da gudu dai dai lokacin sadiya ta shigo tare suka karasa kaina momy ta hau kiran sunana a gigice safiyya!! safiyya!!. safiyya!! sadiya sai faman jijjigani take nan take na saki ajiyar zuciya maganar momy na dinga ji sama- sama.
bude idona da zanyi zafi nakeji kamar an zuba borkono kin tashi naji muryar sadiya na daga mata kai dakyar na iya bude baki nace sadiya ruwa nake so momy ce ta mikon ruwan nayi kokari na tashi na zauna momy kirjina ciwo yake min sosai ina magana ina dafe kirjina wanda kamar zai fashe sannu baby gobe maje asibiti sadiya ta mike rukayya bari naje daki tana fita momy ta dawo kusa dani baby sannu na daga mata kai baby fushi kikeyi dani?? a,a momy tunani nake yaushe nayi barci ta hau dariya muna hira na juyo naga baby tayi barci sai munshari take. nan take na tuno wasikar Alhaji nasir momy ina tausayawa alhaji nasir umma ta cece......tayi saurin katseni kibar maganan na dago idona wanda ke cike da hawaye momy bazan iya cire maganar nan daga zuciyata ba, baby waye muhammad?? ya bugo miki waya yayi daga nace baki da lafiya duk ya tashi hankalinsa sai kira yake tayi baby shine sirrikin nawa?? momy banfa sanshi ba kawai kirana kawai yakeyi a waya to koma dai waye ni dai na yaba da hankalinsa harma kuma nace na bashi keh' ido na zaro waje momy ban san shiba fa ban taba ganinsa ba momy tunda kika min haka bazan kara daga wayar saba, ta mike kinga abar maganar taso muje kici abinci ba wani musu na mike dan yunwane ya timermireni wanda zai iya kashe ni. wani restaurant muka shiga bayan mun gama muna fitowa momy ta mikomin wayata kirashi yaji muryarki ko hankalinsa zai kwanta zan bude baki hannu ta dora kan lebeta karba nayi tare da kiransa" hello safiyya muryarsa ce ta doki zuciyata ya jikin naki na amsa tare da cewa naji sauki ganin zamu tafi nace masa in na koma daki zan kira kasamin karatu sai anjima. yayi saurin cewa safiyya karki katse a hasalce nace a kanme baran katse ba ina fadar haka na katse muna shigowa cikin makaranta muka hadu da saifullahi momy tace saifu saukar yaushe rukayya jiya muka tawo yanzu muka rabu da sadiya take gayamin safiyya bata ji dadi ba ya juyo wajena sannu safiyya ya jikin naki ko kallonsa banyi ba balle na amsa masa nayi gaba momy kamar zata nutse don kunya.

ina sallah ta shigo bayan na idar na juyo ina kallonta momy ya naga kina hararata laifi nayi?? baki min laifin komai ba kawai burgeni kika yi da kika iya rashin kunya tana fadar haka ta mike ta fita.
washegari na tashi babu wata damuwa a tattare dani tasowa nayi nazo wajen momy . momy fishi kike dani na gaisheki kinyi shiru ta dago fuskarta a hade wato baki san abinda kika min ba koh? momy gaya min Allah zan gyara ta dan saki fuskarta baby kowa yazo yace yana sonki sai kin wulakanta shi haka zaki zauna ba zakiyi aure ba tun muna kano ki kewa saifullahi rashin mutunci me kika fishi ina kallon wayarki an kira yafi a irga kinki dagawa kina abu kamar baki da ilimi ki gayamin me......kukan da taji nasane yasa bata karasa abinda yake bakinta ba.



๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[10/3/2016, 5:03 PM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

๓พ ฑ๓พ ฏ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969




cikin kuka nace momy kinyi niyar cimun mutunci waye zai aure shegiya momy karkisa zuciyata ta buga please karki kara min maganar aure babu tunanin aure a raina ballantana yanzu da nasan matsayina nasan waccece ni koda ina son saifullahi ko muhammad sunfi karfina momy koda yanzi aure sai dai nasamu dan uwana shege na aura umma ta cuceni ta cuci rayuwata kullum ina jin haushin kaina me yasa ban bari abba ya cimma burinsa a kaina ba......kuka ne yaci karfina jikin momy yayi sanyi sosai ta tsunguna a gabana kiyi hakuri kibar kukan nan yau satin mu hudu tunda mukazo kullum kina cikin kuka haba baby kamar ba musulma ba tafi awa tana lallashina tare da nasiha. bayan munyi break muna rufe daki sadiya tazo ina kuma zaku kuke kokarin rufe daki zai kai baby asibiti tako kwashe da dariya wannan uwar zaki kai asibiti to wai ke din ina kika sani da zaki fita wata kawatace zata rakamu. na zaro ido momy kawa kikayi tace kwarai kuwa ko ban isa nayi kawa ba amma musulmace? meye ruwanku kiyi hakuri momy to ya sunan kawartamu muna cikin magana wata shirgegiyar bakar mata mai sa kukan dare ta nufo wajanmu kannan nata yaci karin gashi daga ita sai wani mini siket da farar riga nida sadiya muka bita da kallo har ta karaso muka gaisa na juyo wajen momy' momy wannan ce sabuwar kawar tamu? kai ta daga tana harararta.

da sadiya mukaje asibitin karfe biyu mua fito tare da ita muka shiga daki na juyi ina kallonta kawata baki gayamana sunanki ba ta juyo tana murmushi oniya okinwa ke kumafa ina dariya nace nana saffiya mukhtar suna mai dadi ina son irin sunanku amma kin burgeni kina da kyau sosai kuna kama da rukayya sosai amma ke kanwartace? juyiwa nayi ina kallon momy tana waya maganar oniya ce ta dawo dani ina son muyi kawance ina son inga inda kawaye kyawawa duk cikin makarantar nan ban ga me kyanki ba zakiyi samari da dami dariya nasaka oniya kin ban dariya tace me nayi na baki dariya? maganar ni din bana kula samari kuma oniya aikin fini kyau, kina zagina ne kawai dazun da muka fita ake miki magana don ma kar muji me zakice sai ku juya baki, safiyya duk wanda kikaga yayi min magana cewa yake na shigar dashi a wajen ku musamman ma ke.
mun jima muna hira sannan ta tafi gida na juyo ina kallon momy nace momy yunwa nakeji a hasalce ta dago sai na zama abinci ki cinye kwanciyar ta tayi ta shareni.
har wajen karfe uku tana barci wayarta ce ta tasheta tana tashi ta juyo tana kallona na kwantar da kaina daya bari, bayan ta gama wayar ta shiga toilet tayi wanka ta dauro alwala bayan ta idar ta mike kizo muje wajen abincin ban ko kulata ba na mike muka fita. ban garen umma kuma......

sallama tayi yafi sau uku amma shiru don haka ta shigo gidan tana zaune tsakar gida fuskanta shakaf da ruwan hawaye. Rakiyya!! Rakiyya!! ta hau kiran sunanta kamar an tasheta daga barci ta juyo babah sannu da zuwa banji shigowarki ba zuciyarta cike da tausayin halin da yar tata ta shiga tace Rakiyya kuka kike? babah wani irin kuka kuma fuskarta cike da mamaki tare da tashin hankali tace ga hawaye nan a kumatuki....(nima can fuskata ne ciki da raunin tausayin rakiyya)

TO BE CONTINUE SOON!!....

DON'T FORGET HAVE A LIKE ON MY FACEEBOOK PAGE:

๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels.
[10/5/2016, 8:34 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

๓พ ฑ๓พ ฐ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969




kanta karasa umma ta kai hannunta fuskarta wanda kamar an watsa mata ruwa sunkuyar da kanta tayi hakan ya dada tawo da wasu hawaye mazu zafi kan fuskarta har sai da suka taba kasa zama tayi kusa da ita cikin taushin murya babah tace rakiya nayi nadamar korar safiyya daga gidan nan kiyi hakuri duk halin bakin cikin da kike cikii ne yaja miki na rabaki da farin cikinki rakiya ki yafe min dan Allah, baban dan Allah ki daina ban hakuri nice zan baki hakuri in na miki laifi. tana maganar tana goge idanunta wanda ke cike da hawaye rakiya ki rage tunani ki duba halin da kike ciki karki haddasawa kanki wani ciwo munyi magana da mallam ranar laraba zamuje gongola . babah kar muje zasu ce dan muna cikin matsala ne yasa mukazo, sai da mallam ya gayan haka ni kuma nayi tunanin rashin zuwana bazai kwantar da matsalar da take tsakanin ba cikin mamaki nace babah wace irin matsala? hmm rakiya in munje kya gani da idonki mallam yace in munje karmu nuna auranki ya mutu kuma kar muyi maganar batan safiyya zamu nuna tana makarantar kwana, shikenan babah babah bayan fitarki alhaji nasir yazo bai tar da keba yace zai dawo da magariba.
karfe takwas alhaji nasir yazo bayan sun gaisa da babah ta mike bara na shiga wajen mallam bayan fitarta ya juyo yana kallon umma rukayya ina so na tambayeki tsakani da Allah ki ban amsa ta daga masa kai bai damu da rashin bashi amsa da tayi ba yace ki gayan tsakani da Allah ina dangin mahaifin safiyya suke a razane ta dago bata taba tunanin tambayar da zai mata kenan ba kantayi magana yaci gaba da cewa karki boyen komai safiyya bata da uba ne?? cikin kuka taxe wallahi da ubanta to yana ina? in kuma ya mutu ina danginsa? karki boye min gaskiya rukayya in safiyya bata da uba kaddara bata wuce kan kowa ba bata tsaya wata wata ba ta bashi labarin auranta da Dr. mukhtar har sakinta da yayi bayan dawowarta gida ciki ya bayyana akaje aka gaya masa sa duk abinda yace ta kara da cewa wallahi alhaji tunda nake a rayuwata ban taba sanin wani da namiji ba sai shi amma yaxe safiyya ba yarsa bace nayi tunanin zuwan wannan ranar da babah zata gayawa safiyya wannan maganar tun farko nina cuci kaina sa ban bawa safiyya tarb.....kanta karasa ya tare numfashinta karki karasa dana sanin a bata da amfani tun farko kika cuci rayuwar safiyya kina nunawa safiyya so mai tsanani wanda haka yasa kika gaza sauke nauyin da Allah ya dora miki tun tashin safiyya duk abinda tayi bakya taba tsawatar mata ko tayi ba dai dai ba ki mata fada kinga soyayyar da kike mata ta zama cuta gashi yanzu cutar ta zama babba kin kasa maganinta ido ta daga wanda ke cike da hawaye alhaji wace iein cuta nayi wa nana? kin cuceta mana tunda baki sauke nauyin da Allah ya dora miki ba baki taba tarbiyya da duk wata uwa take bawa danta ba.


๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[10/7/2016, 7:51 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

๓พ ฑ๓พ ฑ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜

๐Ÿ’–MUH'D*ABBA*GANA๐Ÿ’–
09039016969



kiyi tunani safiyya macece duk daran dadewa zatayi aure kina ganin akwai namijin da zai aureta bai isa ya gaya mata magana ba, koh ya bata umarni taki bi kuma su zauna lafiy kin san haka ba zata sabu ba. kema ai babah tana sonki ta tsaya ta baki tarbiyya tun kina karamarki in kika yi ba daidai ba ta nuna miki har kika girma gashi kin haihu ke ma meyasa baki taimaki yarki ki nuna mata gatan da aka nuna miki ba. cikin kuka tace Alhaji Allah ya jarrabeni da kaunar nana wadda kukan ya jawo nayi mata Babban SANADI, tun da safiyya ta tashi ba tasan fada ba balle tsawa ko duka, ko babah bana bari tayi mata fada tun abin yana damun babah har ta gaji ta zuba mana ido akwai lokacin da babah tayi wanki nana tazo ta debi kayan ta wasa cikin rijiya shine ranar da babah tayi niyyar dukanta amma na dauke ta na kaita daki ina bata hakurin tsawar da babah tayi mata wanda hakan ba karamin bakantawa babah yayi ba ta biyo mu tana fada karshen kalmar babah dana dau abin wasa yau gashi ta zama gaskiya kull.....kuka yaci karfinta ta kasa karasawa kiyi hakuri kuka bashi da wani amfani addu'a zaki yi, Allah ya dawo da ita. ya jima yana kwantar mata da hankali har sai da yaga ta daina kuka har ya mike zai fita ta tuna bata gaya masa zancen tafiyarsu zuwa Adamawa ba, tana gaya masa ya juyo Rukayya ki bari in kin haihu sai ku tafi toh saboda me? fuskarta dauke da damuwa yace Rukayya ina tsoron ko bara ku dawo ba dan Allah in wani abin kika kulla kiyi hakuri ki kwance kin san ba a san raina na saki ki ba, ina gudun fushin mahaifiyat in Alllah yayi zaki dawo zaki dawo dakina babu wanda ya isa ya hanaki, kaddara daman lokacin rabuwarmu yayi in kika gujen baki min adalci ba, kar kisa abinda zaki haifa yayi marauci. abin har ya bata dariya wallahi alhaji babu wani abinda na kulla a raina za dai muje muyi zumunci tunda mun jima bamu je ba. shi kenan rukayya na yarda dake yanzu yaushe zaku tafi? ranar lahadi zamu tafi to kwana nawa zakuyi gaskiya ban sani ba yayi saurin dago kai in kun tafi kenan babu ranar dawowa? haba dai ba zamu wuce sati biyu ba Allah ya kaimu zan kawo tsarabar da za a kaiwa yan adamawa.
Ana gobe zamu tafi misalin karfe tara Alhaji Nasir ya shigo hannunsa dauke da manyan jakunkuna guda biyu wadda umma zatayi tsara ba tare da kudi masu yawa dan kula da kanta kafin sun dawo.
karfe shida yazo ya kaisu tasha sai dayaga tashin motarsu sannan ya tawo ziciyarsa cike da damusa da kuma tunani, tunda umma suka sauka a tasha take kallon yanayin garin cike da sha'awa mallam mado ne ya dauke su ya shigarda su har kauyensu, maganar mallam mado ce ta katsewa umma tunani tajuyo tana kallom wajen da yayi umurni a tsaya, hango wani dirkekiyar darbejiyan yara jingim a zaune bayanta bukkokine da yawa dukkan su suna zagate da karare.



๐Ÿ…ฐbbagana hausa novels @ facebook.
[10/7/2016, 8:30 AM] ๐Ÿ’–ร„bbรฅ-Gรฃรฑรข๐Ÿ’–: ๐Ÿ’˜WAYE SANADI?๐Ÿ’˜

๓พ ฑ๓พ ฒ
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜ ๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜

Please Login or Register in order to submit comment