Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guda uku bisa alkawa da cewa indai bukatarka
ta biya zaka karbi addininsu. Ni dai azatona zasu yarda da
wannan sharadi, kaga kenan koda karfin addinin su bai yi
aiki ba na jarumtkarka zai yi, baza kayi biyu babu ba".
Sa'adda Sarki Sahibul Hairi yaji wannan batu na Bawa
Haluf sai ya cika da tsananin farin ciki, bao san sa'adda ya
rungnmeshi a kirjin sa ya na cewa, " Gaishe ka ya babban
Bawana, hakika ina mutukar kaunarka sabo da hikimarka
da kaifin kwakwalwarka. Na yi maka alkawari indai na
cika burina zan 'yntaka, kuma na maisheka waziri na mu
cigaba da tafiyar da mulki tarw a birnin Misra".
Koda Bawa Haluf yaji wannan batu, sai shima ya cika da
tsananin farin ciki ya kama godiya
Kashe gari da safe aka kawowa su sarki Sahibul Hairi mai
mai kyau da na garta. Bayan sun kimtsa cikinsu sai Imam
Sadik ya Shigo cikin dakin da aka saukesu tare da wani
badakore a bayansa cikin shigar fararen kayan yaki na
sulke. Badakaren ya nade kansa da rawani idansa kadai
ake gani. Duk da cewar gashin kansa a daure yake a
gadon bayansa, kuma a rufe cikin rawani kasan cewa
Allah yayi masa baiwar gashi mai tsawo. Badakaren ya
rataya zabgegiyar takobi a bayansa, kuma kafafunsa a
sanye suke da dogwayan takalma na farin kirgi masu
madaurai. Kai hakiki shigar Badakaran ta yi kyau, amma
ko kadan babu wata alamar kirar sadaukantaka a jikinsa.
Koda sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf sukayi arba da
idanun Badakaren sai kirjin su ya kama sabo da kwarjini
kyawawn idanun Badakaren. Duk su biyun sai suka aiyana
a zuciyarsu cewa ina ma ace wannan Badakaren mace ne
hakika da anyi kyawu irin wanda babu kamarsa a duniya.
Ya yin da Imam Sadik ya shigo sai ya zauna daf da su
Sarki Sahibul Hairi.shi kuwa wannan bada karen sai ya
koma gefe guda ya tsaya kikam kamar gunki ko
kyakkyawan motsi baya yi.
Imam Sadik ya dubi sarki Sahibul Hairi cikin fara'a da
murmushi ya ce, "ya kai wannan sarki babban namiji,
kayi sani cewa yau nea zanyi bankwana da ku,domin ku
cigaba da yin tafiyarku, amma bayan mun warware
matsalar da ke dake tsakaninmu, shin yanzu ka amince
zaka karbi addininmu ko kuwa a'a?".
Sarki Sahibul Hairi ya yi gyaran murya, sannan ya ce, "
mun amince zamu karbi addininku, amma bisa sharadi
gida. Sharadin shi ne, ina so kununa min cewa zaku iya
taimakamin naje Boka Shamzabul Azwas na dakko
yarinya Alfila 'yar uajan sadauki Awaisu na fito daga ciki a
raye kuma lafiya da karfin Ubangijinku, sannan ku kaini
inda sadauki Awaisu yake ku tolastashi koda zaiki ko ya
yaudareni bayan na bashi 'yarsa akan mutafi neman 'an
mata uku wadanda zan aura na zamo Sarkin Sarakai, nayi
alkawari in dai kuka yi mini haka zan karbi addininku bil-
hakki"
.SA'ADDA SARKI SAHIBUL HAIRI YA ZO NAN A ZANCENSA
SAI IMAM Sadik ya yi murmushi mai nuna yarda sannan
ya ce, "ya kai wannan sarki, ka sani cewa Ubangijina ya
sanar dani duk abin da zaaifaru tsakaninmu tun ka fin ku
zo wannan birni namu mai Albarka, sabo da haka na
amince da dukkan sharadanku bisa dalilin hakan ne ma
nazo da wannan Badakeran nawa domin na gabatar da
shi a garwku sabo da shine zai zamo wakilinmu, wato
shine abokin tafiyarku. Da izinin Ubangijin gaskiya zai iya
yi muku duk abin da ya gagareku ya yin wannan
gagarumar tafiya. Amma ku sani cewa wannan
Badakaren nawz baya magana, amma duk abin da zaku
fada yana ji kuma zai iya mzgana da kai kamar yadda
bebaye ke magana da hannu. Duk abin da zai faru a
tsakanin ku kada ku matsashi, kuma kada kuce zakuyi
masa dole, domin zaku sha mamaki. Tabbas dan hakin da
ka raina shi ke tsone maka ido. A yanzu haka wannan
Badakaren nawa ya futo sa shirinsa na yin wannan tafiya
tare da ku, kuma na sa an tanadar muku guzuri.
Shawarata a gareku ko kuma ina ce dokar da zan kafa
muku ita ce, kada ku kuskura ku yi wani abu da jibanci
tsafi a cikin wannan tafiya taku muddin kuna tate da
wannan Badakaren nawa, idan kuwa kuka yi din zaku iya
halaka ko ku shiga mugun hali. Idan kunne ya ji gangar
jiki ta tsira. Daga wannan furci nake muku bankwana sai
kun dawo wannan birni namu mai albarka bayan cikar
burinka".
Lokacin da Imam Sadik ya zo nan a jawa binsa sai sarki
Sahibul Hairu da Bawa Haluf suka ji kamar tatsuniya ya ke
musu amma a zahiri basu nuna hakan ba. Nan take suka
fito gabaki daya daga cikin wannan gida na masaukinsu
sarki Sahibul Hairi.fitowarsu ke da wuya sai suka ga gaba
daya mutanan birnin sun taru a waje guda.
Koda fitowar sarki sai jama'a suka taho da yawansu suna
yi wa Badakaren murna tankar wanda ya sami mulkin
duniya. Koda ganin abin da ke faruwa sai mamaki ya
kama sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf. Sarki Sahibul
Hairi ya dubi Imam Sadij ya ce, "me yasa mutanan ka
suke taya wannan Badakaren murna"?
Sa'adda Imam Sadik ya ji wannan tambaya sai ya yi
murmushi sannan ya ce, "Abin da yasa kaga jama'ata
suna wa abokin tafiyarku murna shi ne,sun san cewa zai
tafi JAHADI ne, wato daukaka kalmar Ubangijin
Musulumci. A ka idar addininmu duk wanda ya mutu a
cikin wannan tafarki sai ya sami babban rabo a wajan
ubangijin musulumci, don haka gaba dayanmu muna
kwadayi da sha'awar ina ma ace mune wannan
badakaren".
Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi da Bawa
Haluf cika da tsananin mamaki irin imanin wadannan
mutane a bisa Ubangijinsu.
Bayan su sarki Sahibul Hairi sun yi bankwana da su Imam
Sadik sai abokin tafiyarsu, wato Badakaren ya zo gaban
Imam Sadik ya tsaya daf da shi suka kurawa juna ido.
Kawai sai hawaye ya zubowa jowanne daga cilin su a
lokaci guda. Nan take suka rungume juna suna kukan
zuci, kai da gani kasan cewa akwai shakuwa mai karfi a
tsakaninsu.
Daga can sai suka saki juna. Badakaren ya nufi inda su
sarki Sahibul Hairi ke tsaye daf da Aljani Dabarus yana
waigyen Imam Sadik cikin alamun damuwa kamar ya
fasa tafiyar. Sauran jama'ar gari sai suka kurawa
Badakaren isanu gaba dayansu daga mai zubar da
hawaye sai mai kwalla. Ai'amarin da ya kara jefa su sarki
Sahibul Hairicikin tsananin mamaki kea nan, suka
tambayi kansu a cikin zuciyarsu. wai shin wana irun
matsayi wannan Badakaren yake da shi ne a wannan birni
harda kowa zai shiga damuwa da bakin ciki sabo da kawai
zai yi wannan tafiya? A kan wanne dalili Imam Sadik zai
zubar da hawayansa a lokacin da suke bankwana?
Wadannan tambayoyi ne wadanda basu san amsar su ba.
Amma sai sarki Sahibul Hairi ya kudurce a ransa cewa
nan gaba sai ya san amsoshinsu
Ba tare da bata lokaciba su sarki Sahibul Hairi,Bawa Haluf
da Badakaren suka hau bayan aljani Dabarus suka zauna.
Shi dai Badakaren a can gefe daya ya zauna, bai kusanci
su sarki Sahibul Hairi ba, har Aljani Dabarus ya yun kura
zai bude fuka-fukansa, sai Imam Sadik ya tsaidashi ya
dubi sarki Sahibul Hairi ya ce, "in mai yi muku tuni da
kada ku manta kuyi tsafi muddin kuna tare da
Badakarena, yin hakan zai iya kaiku ga halaka ju shiga
mugun hali."
Sarki Sahibul Hairi ya ce, "lallai zamu kiyaye da wannan
umarni naka."
Take aljano Dabarus ya sake yunkurawa bude fuka-
fukansa yai sama, kafin kiftawar ido ya luluka a can
kokoliyar sama. Koda Badakaren ya leko kasa ya hango
birninsu da jama'arsu sun zamo 'yan mini-mini kamar
kiyasai, sai hankalinsa ya dugunzuma, baisan sa'adda
hawaye ya subuto masa ba, domin gani yake kamar har
abada ba zai sake dawowa birninsu ba bare yaga
jama'arsu.
Sai da sa'a uku ta shide suna tafiya a sararin samaniya
sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suna ta hirarsu amma
shi Badakaren ko kallansu bai ba bare ya nuna ra'ayinsa
bisa abin da suke tattaunawa, kuma tunda aka fara tafiyar
ba abinda ya ke yi face jan wata tasbaha yana ta lazumi
abinsa. Da yake a wannan lokaci ana zabga rana su sarki
Sahibul Hairi sun sha ruwa a kalla ya kai sau bakwai,
amma shi Badalaren ko sau daya bai bukaci ruwa ba.
Wannan al'amari ba karamin mamaki ya baiwa sarki
Sahibul Hairi ba, har ma sai da suka yi tseguminsa suna
cewa, "wai shi wannan Badakaren wana irin mutun ne
shi? Anya kuwa mutin ne? Babu mamali aljani ne ya yi
badda bani"
Lokacin da Dabarus yaji tsegumi nasu Sarki Sahibul Hairi
sai ya bushe da dariya sai ya ce, "ya shugabana ai tabbas
wannan Badakaren mutun ne dan uwanku,domin inda
aljani ne yana kusantata zan gane, amma a cikin mutanan
ma shi daban ne."
Haka dai suka ci gaba da surutansu har suka sake shafe
sa'o'i ukun. A tsawan wannan tafiya Badakaren bai yi
wata bukata ba facelazumi, sallah sa nafulfuli kuma a duk
sa'adda zai yi sallah ko nafula sai ya kwance farin mayafi
a kugunsa ya shimfida shi a kan aljani Danarus sannan ya
hau kan mayafin sannan ya yi ibadarsa, kuma ko yaushe
alkibla yake fuslanta.
Bayan cikar sa'a shida da fara tafiyar sai sarki Sahibul
Hairi ya yi wa aljani Dabarus umarni da ya sauka su ya da
zango. Ba tare da bata lokaci ba aljani Dabarus ya bi
uamarni ya sau ka kasa ya dure a cikin wani tafkeken daji
mai tarin bishiyoyi, koramai da kwzazzabai iri-iri. Nan
take sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka kafa tanti,shi
kuwa Badakaren ko kallansu bai yiba bare ma ya tayasu
aikin kafa tantin. kafa tantin ke da wuya sai Bawa Haluf ya
je ya samo itatuwa ya hada su waje daya ya kunna wuta,
suka zauna a ganwutar suna jin dimi kasancewa a
wannan lokaci ana muku-mukun sanyi a wannan nahiyar
da suke. Shi wannan Badakaren nan sai ya koma gefe
daya ya yo zaman sa a kas y dakko casbaha ya kama
lazumi. A dai-dai wannan lokaci ne sarki Sahibul Hairi ya
fuskanci cewa wannan guri da suka yada zango, sansani
ne na wadansu mucizai iri-iri barkatai, gasu nan a kwance
ko ina babu adadi. Wasu manya wasu kananu, kafin kace
me tuni mucizan sun kewa ye harabar wajen gaba daya.
Ba shiri Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka dakatsalle
suka haye kan bishiya, sai da suka kure can karshan
bishiyar sannan suka sami nutsuwa. Dama bishiyar masu
irin santsin nan ne, macizan ba za su iya tafiya a kan su
ba.
Shi kuwa Badakaren nan ko kadan bai yi gezau ba da
ganin mucizan, sai kawai ya cigaba da karanta 'yar
addu'o'insa, mucizan kuwa sukai ta kewa ye shi aka rasa
guda daya wanda zai kawo masa hari. Bayan Badakaren
ya gama lazuminsa, sai kawai ya kwanta bisa buzunsa, ya
kama barci tamkar ma babu ko mai a kusa da shi.
Mucizan suka kare zaryarsu a gefan Badakaren sannan
duk suka watse suka bar wajan. Dyk abinda ke faruwa su
sarki Sahibul Hairi suna makale a kan bishiyar suna kallo,
dan haka suka cigaba da tsananin mamakin yadda akayi
wadannan mugan mucizai suka kasa yiwa wannan
Badakaren komai. Bayan tafiyar mucizan ne sarki Sahibul
Hairi da Bawa Haluf suka sakko daga kan bshiyar suka
tsaya a kan Badakaren suna masu mamakinsa. Bawa
Haluf ya bubi sarki Sahibul Hairi Sai ya ce, " ya
shugabanani ko zan so naga fuskar wannan takafarin
barde mai ban al'ajabi. Wai shin ma sabo da me ya rufe
fuskar tasa garemu?
Sarki Sahibul Hairi ya ce, " ni kaina na kagu naga irin
fuskarsa, amma tunda barci yake yanzu mai zai hana ka
ya ye rawanin da ke fuskar tasa?".
Koda jin haka sai Bawa Haluf ya ce, "kwarai kuwa, adin da
ya kamata ke nan ayi".
Kai tsaye ya kai hannu da nufin ya ye rawanin. Caraf! Sai
yaji Badakareb ya cafke hannunsa ya matse da karfi. Sai
da tsananin jin zafin rukon da ya yi masa bai sa'adda ya
kwallara ihu, kuma ya saki fitsari a wando. Badakaren ya
bude idanunsa yana mai nuna Haluf da daya hannun
nasa cikian nuna alamun yi masa kashedi. Cikin rawar
murya Bawa Haluf ya shiga wana yanayi yana bada hakuri
Shi kauwa sarki Sahibul Hairi sai ya tuntsure da dariya da
yaga Bawa Haluf ya saki futsari a wando. Ya yi
kyakayatawa da dariya kamar ba zai daina ba.
Koda Badakaren ya saki hannun Bawa Halufa sai Haluf ya
rugo da gudu izuwa bayan sarki Sahibul Hairi ya boye
tamkar zomo ya ga kare yana yiwa sarki Sahibul Hairi
rada a kunne ya ce, " ya shugabana tabbas wannan ba
mutun bane, domin da danke hannuna ji nayi kamar zai
rugurguza min kashi.
Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi ya sake
bushewa da dariya a karo na biyu ya ce, " kai tabbas
wannan Badakaren mutun ne, amma sadauki ne na
gaske. Kar ka damu, wata rana zamu kara ni da shi domin
na jarraba iyakar sadaukantakarsa."
A wannan daji su sarki Sahibul Hairi suka kwana sannan
kashe gari suka sake hawa kan aljani Dabarus ya tashi da
su sama aka ci gaba da tafiya. Sai da suka shafe kwana
arba'in da daya suna tafiya, su sauka nan su tashi can.
Duk tsawan wadannan kwanaki su sarki Sahibul Hairi
basu taba ganin fuskar wannan Badakaren ba, kuma ko
wanka ya so yi baya yi a inda zasu ganshi. Koda sun bi
yansa suna labewa sai su nai meshi sama ko kasa su rasa
shi. Shi kansa sarki Sahibul Hairi ya tsorata da al'a,arin
wannan Badakaren, burinsa kawai shi ne wani abin ya
haddasa ya takaleshi da fada su gwabza domin ya gwada
jarumta karsa da tasa.
A ranar kwana arba'in ne cif suka iso dajin da gidan Boka
Shamzabul Azwas yake. Tun daga nesa suka hango
tafkeken gidan wanda girmansa ya kai na wani garin. Nan
fa sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka bude baki suna
kallon gidan cikain tsananin mamaki da al'ajabi tamkar
dan kauye ya shigo burni.
Shi dau wannnan gida an gina shi ne a kan wani tafkeken
tsauni mai tsawo da fadin gaske. Kuma gabaki daya gidan
da wani irin murtokeken kaife aka yi shi tam kara
naekakkiyar dalma. Kai inda mutun zai iya huda ginin da
gatari da sai ya kwana dari yana haka a jikin ginin bai
hudo karshansa ba sabo da kauri.
Da saukar aljani Dabarus kan tsaunin sai ya ja da baya ya
tsaya a can nesa da gidan jikin sa ya kama karkarwa, sabo
da tsananin razana. Shima Bawa Haluf jikin sa ya kama
kyarma, idanun sa suka zazzaro kamar ace kyat! Ya ski
futsari a wando. Shi ma sarki Sahibul Hairi duk da
kasancewarsa mai da kakakkiyar zuciya bai yi yun kurin
komai ba, koda sauka daga kan aljani Dabarus bai yi ba
sai da yaga Badakaren ya sauka ya nufi gidan Gadan-
Gadan sannan ya bi bayansa rike da Gatarin Sihiri wanda
ya dauko a fadar sarki Barusa.
Sa'adda Badakaren ya iso daf da gaban gidan Boka
Shamzabul Azwas sai ya tsaya cak ya waiga baya yana mai
dubam su sarki Sahibul Hairi.
Sarki Sahibul Hairi ya karasa gare shi da suri ya dube shi
cikin alamun rauni ya ce, " dakata a nan indai ba so ka ke
ka halaja ba. Bayan na bude mana kofar shiga gidan nan
sai ku biyo bayana".
Sa'adda Badakaren ya ji wannan batu sai kawai ya yi
murmushi ya tsaya cak a waje daya. Sarki Sahibul hairi ya
je jikin kofar da Bokan sa ya yi masa bayaninta tun kafin
ya zo ya daga Gatarin Sihiri ya sara mata. Karfin saran ya
cika jejin gaba ki daya yana mai amsa kuwa da firgitar da
dukkan tsuntsayen dake kan bishiyoyi da duwatsu suka
tashi sama farr! Ba shiri.
Sa'adda kaifin Gatarin ya hadu da jikin kofar kuwa sai da
tartsatsin wuta ya tashi game da gagarumin hayaki kamar
ana bulbulawa wuta mai.
Bayan hayaki ya tashi sai Sarki Sahibul Hairi ya ga ashe
inda ya sara a jikin kofar ko kwarzane bai yi ba bare ya
fashe. Al'amarin da ya mutukar razana sarki Sahibul Hairi
ke nan kuma zuciyarsa ta karaya, ya dawo daga rakiyar
Bokaye. A cikin zuciyarsa ya ce, "Hakika makaryaci sama
da boka. Kuma duk mutumin da ya sallama imaninsa a
kansu a karshe ingiza mai kantu ruwa za su yi masa ya
fada cikin halaka. Yanzu gashi Bokana ya tabbayar mini
da cewa da wannan gatari ne kadai zan iya sara kofar
gidan nan na shiga. Akan hakan na sallamar da rayuwata
dan dakko gatarin. Na sha bakar wahala da kyar na tsira
da rayuwat a kokarin dakko wannan gatarin, yanzu gashi
wahala duk ta zamo a banza, tun da ga gatarin ba zai iya
cika mini burina ba".
Wata zuciyar kuma sai ta ce da shi, "haba jarumi uban
jarumai, kai kuwa daga yin sara sau daya sai ka karaya? Ai
ka cigaba da jarraba balle kofar wata kila kasa mi nasara".
Koda sarli Sahibul Hairi ya ci gaba da saran kofar nan
babu sassautawa, tun yana yi da kuzarinsa har ya sare. A
karshe ma ya fadi kasa yana haki sabo da tsananin gajiya.
Koda ya dago kai ya dubi kofar da yake sara sai takai ci ya
lullubeshi tamkar ya fashe da kuka.
Ba wani abu bane yasa shi takaici ba face ganin cewa har
yanzu ko alamar kwarzanewa kofar bat yi ba. Ba zato ba
tsammani sai suka ji an bushe da wata irin mahaukaciyar
dariya mara dadin sauti wadda ta cika dajin gaba daya,
sannan aka ce.
"ya kai wannan makahon sarki wanda ya haukaceakan
bukatarsa, kayi sani cewa bokan ka ya yaudareka har da
yace maka Gatarin Sihirin sarki Barusa zai fasa kofar
gidannan har ka shiga ka iya rabani da Alfila. Taka sani
cewa duk duniyar nan babu wani mahaluki wanda ya isa
ya shigo cikon wannan gidanawa, walau mutun ko
aljanba tare da izinina ba. Ina mai shawartar ka da
karungumi kaddara, idan ko ka ci gaba da damummu da
saran kofar gidan nan zan gallakaka na hallaka abokan
tafiyarka, ya kasan ce kunyi wahalar banza da tafiyar
banza daga birninku. Don ko a tarihi baza a iya binciko
yadda karshenku ya kasance ba".
Ya yin da kakkaurar muryar ta gama wannan jawabi, sai
sarki Sahibul Hairi yaji babban nadama razo masa, nan
take hawayan bakin ciki ya subuto masa. Kawai sai ya
sako gatarinsa a kafada ya jiyo da baya da nufin ya
rungumi kaddara. Kawai sai yaga Badakaren ya sha
gabansa yana yi masa nuni da ya koma da ya koma da
baya shi zai bude masa kofar gidan su shiga.
Kai tsaye Badakaren ya nufi wannan kofa. Shi kuwa sarki
Sahibul Hairi sai ya tsaya daga baya dan yaga iyakar
karyar Badakaren. Da zuwan Badakaren sai ya dafa kofar
sai ya karanta wata addu'a, sannan ya dafa kofar da
hannunsa na dama. Kamar a bude littafi haka kofar gidan
ta bude wanwar, sai ga hanya zururu izuwa cikin gidan
Boka Shamzabul Azwas.
cikin tsananin mamaki sarki Sahibul Hairi ya rugo da
gudu izuwa gaban Badalaren, shima Bawa Haluf ya rugo
gareshi, suduka su biyun sai suka yiwa Badakaren jinjina.
A sannan Sarki Sahibul Hairi ya wuce kan gaba izuwa cijin
gidan. Badakaren shi kuma ya biyo bayansa, shi kuma
Haluf ya take masa baya.
Suna gama shiga ciki sai kofar ta rufe kanta ta mai bayar
da gagarumin sautin rufewar tamkar an saki katan dutse
daga sama ya fada kan dan uwansa
Ko mai jarumtakar mutun da dakewar zuciyarsa in dai ya
shigo wannan gida na Baka Shamzabul Azwas sai ya ji
tsoro sabo da irin mugwayan halittun da aka tanada a
cikinsa.
Da farko sai da su sarki Sahibul Hairi suka yi tafaiya ta
rabin sa'a a cikin gidan basu hadu sa qani abin tsoro ba.
kwatsam sai suka ga wani jibgegen kare ya duro daga
sama ya sha gabansu. Karar dirar tasa ma sai da ta
firgitasu. Ya yin da ya yi haushi kuwa, sai da hantar
kowanne a cikin su ta kada banda Badakaren nan.
Shi dai wannan kare girmansa ya kai na katuwar giwa,
yana da kawuna uku. Na daya kan batoyi nae, yana fesar
da wuta kai na biyu irin na mesa ne, yan fesar da dafi. Shi
kuwa kai na uku irin na zalbe ne, yana zazzago wani irin
dogon harshe mai kai fin tsiya kamar zabira.
da ya ke sarki Sahibul Hairi nea a kan gaba, yana ganin
wannan kare mai kawuna uku, sai ya yi wuf! Sai ya daga
garkuwarsa sama, sannan ya daga gataren sihiri da daya
hannun nasa, nan take karan ya fesowa sarki sahibul hairi
wuta da kansa na farko.
.CIKIN ZAFIN NAMA YA KARE WUTAR DA GARKUWARSA.
KARFIN IKAR WUTAR CE TA BANGAJE SARKI SAHIBUL
HAIRI ya fadi kasa can gefe daya. Ka fin ya yunkura ya
tashi kan karen na biyu ya kawo masa sara. Koda ya kare
saran da garkuwarsa sai hakoran karan suka gutsire
garkuwar, duk da cewar ta karfe ce, sai ga shi an wawake
tsakiyar garkuwar an yi mata rami wawakeke. Cikin
dimauta sarki Sahibul Hairi ya yi jifa da garkuwar.
A dai-dai wannan lokaci ne daya kan karan ya zazzago
wannan harshe mai kaifi mai kaifin tsiya ya kawo wa sarki
Sahibul Hairi sara. Sarki Sahibul Gairi ya dada karewa da
gatarin sihiri. Take gatarin ya rabe gida biyu tamkar an
yanka katako da zarto. kuma duk da haka sai da haishin
sai da ya laftawa sarki sahibul Hairi sara a kafada, ta ke
wajan ya dare, jini ya yi tsartuwa. Sarki Sahibul Hairi ya
kwarara uban ihu sabo da tsananin zugin da yaji. A lokaci
guda ya sulale kasa a sume.
Bawa Haluf da ke can baya da ya hango abin da yake
faruwa, sai shima ya sulalea kasa a sume sabo da
tsananin razana ya rage saura badakaren kadai a tsaye a
gaban wannan jibgegen kare. Nan fa suka fara kallon-
kallo. Sai dai Badakaren ya na tsaye a inda yake ko motsi
bai yiba, kuma bai yi yunkurin komai ba. Shima karen sai
ya tsaya cak! Yana jiran yaga irin yunkurin da Badakaren
zai yi. Kai da ganin yadda suka kurawa juna ido kasan
cewa ana shayin juna
Daga can sai Bzdakaren ya far karanta addu'o'i a ransa.
Shi kuwa karen sai ya fara gurnani mai ban tsoro. Ko
kadan zuciyar Badakaren bata yi rawa ba, bare ya ji wani
tsoro.
Cikin shammace karen ya kawowa Badakaren wawan
farmaki da dukkan kawunansa uku. Wato kai na farko ya
feso wuta,na biyu ya kawo sara mai dafi. Shi kuwa kai na
uku ya harbo harshe mai kaifi. cikin tsananin zafin nama
Badakaren ya daka tsalle sama tamkar anjanye shi da
kugiya, ya kau cewa duka harin guda ukun. Duk wajan da
karen ya kawo hari sai kaga ya fashe kamar ansa diga an
hake, kuma gagarumar wuta ta kama wajan.
Durowar da Badakaren zai yi sai ya sauka akan wuyan
karen, ya hau sukarsa da takobinsa ba kakkautawa amma
sai ya ji kamar dutse yake suka, ko kadan tako bin bata
tasiri a jikinsa. Karen ya yi ta tsalle dan ya jeho Badakaren
kasa daga kansa, amma sai abin ya gagara, domin ya
makakkale radau da kafafunsa.
Koda ganin haka sai karen ya fita da gudu yana karo da
gini domin ya watsar da Badakaren. Kai wani lokacin ma
ta cikin gini yake shigewa, sai dai kaga ya fasa katanga
komai kaurinta ya wuce, amma duk da haka duk da haka
Badakaren na makakkale da shi ya ki fadowa
Sai da karen ya shafe sa'a guda yana guje-guje da
bangazar katanga suna rushewa su fado musu a jiki shi
da Badakaren, amma duk a banza.
Koda ganin haka sai karen ya tsaya cak ya kama a
dungure a kas da murgin-murgin yana danne Badakaren
da nufin ya galabaitar dashi a haka ya kakkarya masa
kasusuwan jikinsa. Amma sai hakan ya zamo a banza
tamkar karawa Badakaren karfi yake domin ji yake yana
kara rukunkumeshi tamkar matsattsaku tamkar ta dafe a
jikin mutun. Inda mutun na nan a tsaye yana kallon
wannan gumurzu da ya bada labarin cewa bai taba ganin
mutun mai juriya,naci,jaruntaka kamar Badakaren.
Lokacin da kare mai kai uku yaga har yanzu fa bai samu
nasara ba, sai ya tsaya cak a waje daya ya shiga wurkila
kawunansa izuwa Badakaren domin ya kai masa farmaki.
Shi kuwa Badakaren sai ya dinga naushin kawunan da
dukkan karfin dantsansa cikin zafin nama. Karfin naushin
ne ya haukata karen ya yi ta haushi mara dadin ji. Kafin a
jima Badakaren ya kumbura fuskokin karen sun duri jini.
Ba shiri karen ya daina gani sosai, idanuwansa duka sun
junbura sun yi luhu-luhu. Take jikin karen ya yi tsami ya
sulale kasa. A sannan Badakaren ya sauka daga kan karen
domin a tsammaninsa ya samo lagwan karen, ashe karen
lambo ya yi.
Koda jin Badakaren ya yunkura, cikin zafin nama ya daka
tsalle sama da nufin ya yi dirar mikiya akan Badakaren.
Hucin iskar karen ce ta doko dodan kunnnan Badakaren
ya farga da farmakinsa, don haka sai shima ya juya cikin
zafin nama ya sunkuya kasa. Kafin karen ya shallakeshi sai
ya ruko kafafuwansa na baya da hannayaensa biyu. Take
ya wujijjiga karen sama cikin iskakai ka ce mage yake
wulwulawa, duj da cewar girman karen ya kai na giwa.
Tabbasa sadaukantakar Baiwa ce, ba girman jiki ba. Idam
mutun ya dubi girman karen kyma ya dubi kankantar
Badakaren sai ya rantse cewar idan karen ya danneshi jo
shurawa bazai yi ba zai zamo gawa. Amma sai gashi
Badakaren yana hajijiya da karen a sama.
Sai da Badakaren ya wulwula karen sau arba'in sannan ya
damfara shi a kan dirkar ginin. Take kawunan karen duka
ukun suka dagwargwaje, jini ya kama malala yana gudu
tamkar an bude ruwan fanfo. A sannan Badakaren ya
koma da baya a guje izuwa inda ya baro su sarki Sahibul
Hairi a sume. Da zuwa sai ya iske sarki sahibul Hairi a
kwance yana nunfashi sama-sama, kuma har yanzu jini
yana zuba a kafadarsa.
Cikin hanzari Badakaren ya daure masa kafadarsa tamau
da wani mayafi, sannnan ya karkata jarkarsa ta ruwa ya
yayyafawa sarki Sahibul Hairi ruwan. Take sarki Sahibul
Hairi ya farfado. Koda ya bude idanunsa yaga Badakaren
a tsaye a kansa kuma a raye sai ya cika da tsananin
mamaki ya ce, "in wannan shirgegen karen yake?".
Maimakon Badakaren ya bude baki ya amsa wannan
tambaya sai ya tashi sarki Sahibul Hairi tsaye ya jashi suka
tafi izuwa inda gawar karen take, yana nuna masa ita. Ya
yin da sarki Sahibul Hairi ya ga irin motsuwar da karen ya
yi, sai ya kurawa Badakaren idanu cikin matukar al'ajabi.
Nan take sarki Sahibul Hairi ya raina kansa, kuma ya raina
duk

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment