Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a can lambuna na
wajan gari, yau da duku-dukun safiya naje na daukosu na
sanyasu a jikina, sannan na taho fada.
Ina mai tabbatar maka da cewa duk yawan nan naku na
banza ne, domin ba za ku oya hallakni ba. Yanzu kun rufe
kofofin fadae gaba daya babu wanda zai kawi mini dauki,
kuma babu wanda zai kawo muku. Ni da ku kowa
karfinsa da sihirinsa ya kwaceshi."
Koda gana fadin haka sai Aminul Has ya gyara tsayuwa ya
ruke sandarsa da hannu biyu.
Cikin tsananin firgita da taurin rai Waziri ya dakawa
dakarunsa tsawa ya ce, "Su afkawa Aminul Has su yi
gutsun-gutsun da sassan jikinsa".
Nan take kuwa dakarun suka yi ca! A kansa tamkar an
ajiye kwayar dawa a tsakiyar gidan tururuwa.
Nan fa fadar ta hargitse da ihu mazaje, karafkiyar karafa,
domin Aminul Has ya zamo tamkar shaidani a cikinsu.
Duk inda ya kai duka da sandar hannunsa sai ka ga ya
bazar da sama da dakaru biyar. Kuma take suke zama
gawa ko shurawa basa yi.
Shi kuwa idan suka sari jikinsa sai kaji kara kal! Tamkar
sun sari dutse. Wani lokacin idan suka yi masa rubdugu
suka lullu6eshi suka danneshi kasa da ya yunkura sai ka
ga ya taso sama ya tarwatsasu tamjar an jenyesu da
kugiyoyi.
Koda dakarun suka ga Aminul Has baya jin sara da suka
kuma sai bankesu yake tayi suna ta mutuwa, sai suka fara
rugawa da gudu izuwa bakin kofofin fadar da nufin su
bude su gudu.
Koda Aminul Has ya fahimci hakan sai ya kwaci kwari da
baka a hannun wani Badakare ya rinka harbo wadanda
suka ruga jikin kofofin suna fadowa kasa matattu.
Babu abinda zai baiwa mutun mamaki face irin tsananin
zafin naman da Aminul Has ke amfani da shi wajen harbo
dakarun, domin a cikin dakika biyu yana iya dana kibiyoyi
arba'in cikin bakansa ya harbe mutum arba'in din.
Kafin a jima Aminul Has ya kashe sama da rabin Dakarun
da ke cikin fadar.
Koda ganin wannan al'amari, sai cikin Waziri ya duri ruwa
suka fara tunanin hanyar da za su bi su tsira da
rayuwarsu.
Abin da ya fara fado musu a rai shi ne suma su shmmaci
Aminul Has su ruga su bude kofa su fita. Amma kuma
samun nasarar yin hakan abu ne mai hadari, domin zafin
naman Aminul Has ya wuce tunaninsu.
A wannan lokaci Waziri da manyan mukarrabansa sun
6oye ne a bayan karagar mulkin.
Nan fa suka fara tattaunawa a tsakaninsu. Waziri ya dubi
mukarraban nasa ya ce, "Hakika bokanmu ya yaudaremu
kuma ya cucemu, ashe bai samu ikon sato ababan

dogaron Aminul Has ba?".
Koda jin haka sai galadima ya ce, "ai ba yauda rarmu ya
yi ba, shima an shammace shi ne. Ni kam a tawa
shawarar kada mu ce zamu yi yunkurin gudu, kawai mu
fito mu yakeshi da iyakar karfimmu da dai mu mutu
ragwaye ai gwara mu mutu mazaje.
Ina tabbatar muku da cewa a yau dai dayanmu ba zai
tsira da rayuwarsa ba.
Don haka dukkamu burinmu da shirinmu ya rushe, kawai
mu fita mu yi kundumbala mu tari kaddararmu".
Koda jin wannan batu sai hawayen takaici da bakin ciki ya
su6uto daga cikin idanun Waziri, kawai sai ya kurma ihu
ya mike tsaye sannan ya zare takobinsa ya ruga izuwa kan
Aminul Has. Koda Aminul Has ya hango Waziri ya
durfafoshi gadan-gadan da mugun nufi, sai Aminul Has
ya daka tsalle sama ya kai masa wawan duka da sandar
aka. Take kan Waziri ya rabe goda biyu tamkar an 6are
gyada, ya sulale kasa matacce.
Koda ragowr mukarrabansa suka ga abin da ya faru akan
shugabansu, sai suka kara firgicewa, suka kasa fitowa dga
bayan karagar har dai Aminul Has ya gama kashe
dukkunin dakarun dake cikin fadar.
Lokacin da ake ta wannan gumurzu a cikin fadar, jara'ar
gari sun yi cincirindo a kofar fada suna ta jiyo ihun
daharu a ciki, gashikuma kofa a rufe take an ki budewa.
Al'amarin da ya tabbatar da cewa lallai akwai
makarkashiyar da ake shiryawa a kan harkokin mulki.
Da yawa daga cikin jama'ar gari sai suka yi tsammmanin
cewa ana ta kashe dakarun sarki Aminul Has ne
makusanta a gareshi da kuma shi kansa Aminul Has din.
Abin da basu sani ba shi ne, kishiyar hakan ce take
faruwa.
Bayan Aminul Has ya gama kashe dukkanin dakarun da
ke cikin fadar ya zamana cewa duk inda ka duba ba abin
da za ka gani face gawarwakin dakarun da kuma jinimalemale a kasa sai ya dubi 6angaren da kargar milki take ya
ce, "ya ku makarraban Waziri, ku fito daga ma6oyarku ku
yi mubaya'a gareni ku nemi gafara, idan har kuka yi
alkawarin cewa ba za ku sake ha'intata ba ni kuwa zan yi
muku rai, kuma na barku a cikin majalisata."
Koda jin wannan batu sai mukarraban Waziri sukai tsurutsuru suka kasa fitowa sabo da tsoro. Tunaninsu shi ne,
suma zargin cewa Aminul Has so yake ya yaudaresu.
Cikim rada daya daga cikinsu ya ce, "mu amince da tayin
Aminul Has, akwai abin da na shirya a zuciyata".
Koda jin haka sai gaba dayansu suka fito daga ma6oyar
tasu suka nufi inda Aminul Has yake suka durkusa a
gabansa.
Kawai sai suka kama tuba suna neaman gafara, harma
suna kuka suna cewa, "ai Waziri ne ya yi musu dole suka
bashi hadin kai".
Ya yin da Aminul yaga yadda suka marairaice sai

tausayinsu ya kamashi ya ce da su, "su mike tsaye ya yafe
musu."
Su duka suka mike tsaye suka kama murna da godiya.
Aminul Has ya juya da baya ya nufi babbar kofa ta
shigowa fadar da nufin ya budeta.
Cikin shammata daya daga cikinsu ya dauki mashi a kasa
ya duge sandar da ke hannun Aminul Has ta fadi kasa can
gefe daya.
Koda ganin haka sai su duka suka afkawa Aminul Has da
nufin su hallakashi, domin a zatansu idan daya tare da
wannan sanda ta hannunsa ba zai iya tsinana komai ba.
Nan fa suka rufeshi da rubdugun sara da suka, har suka
saishi kasa. Sai dai ko kadan makaman nasu basu yi tasiri
a jikinsa ba, don fatar jikinsa ko kwarzanewa bata yi ba
bare ya sami babban rauni.
Cikin tsananin fusata Aminul Has ya yunkura ya taso
sama ya watsar da su su duka suka zube kasa, kafin su
yunkura su sake afka masa tuni ya hausu da naushi da
bugi hannu da kafa. Duk wanda ya yiwa naushi daya a
fuska sai ka ga jini na tsartuwa a hancinsa da bakinsa,
kuma nan take ya fadi kasa matacce, sabo da karfin
naushin ya wuce misali.
Kafin cikin dakika dari da ashirin babu dayansu a tsaye ko
a zaune rayayye.
Sarki Aminul Has ya tsaya cak! Ya dubi dukkanin
gawarwakin da ke kwance a cikin fadar, ya ga cewa shi
kadai ne fa ya kashe su sai takaici da bakin ciki ya
lullu6eshi. Nan take idanunsa suka ciko da kwalla, ya fara
zubar da hawaye.
Cikin sanyin jiki ya karasa bakin kofar fadar ya budeta da
hannu daya alhalin sai karti Arba'in sun taru suke iya
budeta.
Koda kofar ta wangame mutanan gari suka yi arba da
sarki Aminul Has suka ga shi kadai ne a raye a cikin fadar
si suka rude da shewa da jinjina. Suka hau yi masa kirari.
Aminul Has ya gadawa jama'a hannu suka yi tsit! Sannan
ya ce, "ya ku jama'ar birnin Misra, ku yi sani cewa
wadannan da na salwantar bada son raina ba ne, domin
su ne wadanda suke son su kawar da mulkin Adalcin da
ake yi muku su shimfida na zalumci. Ni kuwa na yiwa
sarki Sahibul Hairi Alkawari cewa zan ci gaba da tafiyar da
mulki kamar yadda ya saba tafiyar da shi, kuma zan tsare
rayukan talakawa da dukiyoyinsu. Ina fata za ku
gafarcene bisa wannan rayuka da na salwantar, domin da
yawansu suna da nasaba da wasunku."
Koda jin wannan sai wani dattijo mafi tsuma a birnin ya
matso daf! Da Aminul Has ya ce, "ya shugabana kayi sani
cewa wadanda ka kashe ina farin ciki da hakan, domin
mutun baya cika na gari face yana kaunar ci gaban
Al'umarsa. Hakika muna Alfahari da mutane irinka da irin
su sarki Sahibul hairi wadanda suke son talakawa kamar
yadda suke son kansu."

Koda tsohon ya zo nan a jawabinsa sai mutane gari suka
sake rudewa da shewa suka daga sarki Aminul Has sama
suna masu ci gaba da yi masa kirari da jinjina. Duk
wannan abu da ke
faruwa Bokan su Waziri na la6e a can gefe daya yana
cizon yatsa cikin tsananin takaici da bakin ciki, domin
yaga samu yaga rashi.
wannan shine abin da ya faru a birnin Misra bayan Sarki
Aminul Has mai ruke da karagar mulki ya sami nasarar
kawar da makiyansa.
¤¤¤¤¤¤¤¤
SARKI SAHIBUL HAIRI
Al'amarin su sarki Sahibul Hairi kuwa, lokacin da suka
kama tafiya suka iso inda suka bar aljanin da ya kawo su
fadar Boka Shamzabul Azwas sai suka iske wajan wayam
babu wata haliita mai rai guda daya.
Al'amarin da ya mutukar dugunzuma hankalinsu ke nan
suka yi cirko-cirko suna tunanin abin da ya kamata su ya.
Daga can sai sarki Sahibul Hairi ya dubi gimbiya Humaira
ya ce, "ya ke wannan Basadaukiya, yanzu ina dabara? Ta
ya ya zamu yi wannan doguwar tafiya a kasa mu isa can
garin su sadauki Awaisu mu kai masa 'yarsa Alfila domin
ya yi mana jagora izuwa inda 'yan mata uku suke
wadanda zan aura?"
ya yin da gimbiya Humaira taji wannan batu sai tayi
murmushi sannan ta sami wuri ta dubi sarki Sahibul Hairi
cikin untsuwa ta ce, "ni zan iya rokon Ubangijima ya
kaimu can a cikin kwanaki kadan, ti amma yin hajan ba
shi da wani amfani".
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki Sahibul
Hairi da Bawa Haluf da yarinya Alfila, har ma suka kurawa
Humaira idanu.
Sarki Sahibul Hairi ya tambayeta ya ce, "mene ne dalilin
da ya sa kika ce bashi da amfani yin hakan?"
Humaira ta sake yin murmushi a karo na biyu ta ce, "ya
kai wannan jarumin sarki, ka ga dai da farko da muka zo
nan kayi amfani da duk karfin damtsenka da kuma karfin
sohirinka wajen shoga gidan nan amma ka kasa. Ni kuwa
sai gashi na bide maka kofa da taimakon Ubangijina mun
shiga.
Wannan abu da ya faru ya isa ishara a gareka kayi imani
da Ubangijina ko ka rabauta, amma baka yi ba.
Bayan mun fafata kazamin yaki da Boka Shamzabul
Azwas ya sami nasra a kammu ya tsafancemu muka zama
gumaka daga baya kuma muka sake tashi, ni ce na sake
yin gumurzu da Shamzabul Azwas har na sami nasarar
hallakshi da taimakon Ubangijina. Gashi har na mallaki
wannan damara da ke kugunsa.
Wannan abu da ya faru ahima ya isa ishara a gareka akan
ka kar6i addinin musulinci, amma har yanzu baja kar6a
ba.
Shin akan wanne dalili zan ci gaba da yin tafiyata tare da

kai tun da na biyoka ne dama domin na ja hankalinka
izuwa mikakkiyar hanyar da babu karkata a cikinta,
hasken da babu duhu a cikinsa, tafarkin gaskiya, tafarkin
da kau da karya, wato tafarkin addinin musulinci!
Ina tabbatar maka da cewa ni yanzu a nan zan rabu da ku
na kama gabana, in ya so kowa tashi ta fishsheshi".
Koda jin wannan batu sai hankalin yarinya Alfila ya
dugunzuma ainun, ta faka kuka.
Al'amarin da ya mutukar bawa Humaira da su sarki
Sahibul Hairi mamaki ke nan.
Humaira ta durkusa gaban Alfila ta ruke kafunfunta ta
shiga rarrashinta tayi shiru, sannan ta tambayeta ta ce,
"ya ke Alfila mene ne dalilin da ya sa kike wannankuku?"
Alfila tayi ajiyar zauciya ta ce, "ba wani abu bane yasa
kika ga ina wannan kuka ba face na san cewa idan kika
tafi kika barni a nan su sarki Sahibul Hairi ba za su iya
mayar dani kasarmu ba na sadu da mahaifina ba, domin
daha nan zuwa kaarmu tafiya ce ta a kalla wata bakwai
basa rakumi ko doki. Kuma akwai muggan abubuwan
hadari a hanya wadanda ba za mu iya shallake hasarin su
ba.
Ina rokonki da ki taimaka ki ci gaba da tafiyar nan tare da
mu domin nawa burin ya cika".
Sa'adda gimbiya Humaira taji wannan batu, sai tai ajiyar
zuciya sannan ta ce, "ya ke Alfila yanzu idan na kaiki
kasarku kika sadu da mahaofinki za ki yi imani da
addinina?"
koda jin wannan tambaya sai Alfila ta yi murmushi ta ce,
"Ai tun da na ga ma kin sami nasara akan Shamzabul
Azwas na ji na gamsu cewa tsafi karyane, addininki shi ne
addinin gaskiya, yanzu take ina son ki shigar dani cikin
addinin naki".
Da jin haka sai farin ciki ya lullu6e gimbiya humaira. Nan
take ta biyawa Alfila kalmar shahada ta maimaita.
Humaira ta mike tsaye sannan ta dauki Alfila ta goyata a
bayanta.
Humaira ta dubi yarinya Alfila da ke bayanta ta ce, "ya ke
Alfila ki sani cewa daga yau kin zama 'yar uwata, duk
rintsin da za ki shiga sai dai mu shiga tare".
Gimbiya Humaira ta sake juyowa ta dubi su Sarki Sahibul
Hairi da Bawa Haluf ta ce, "ku kuma kun ci albarkacin
wannan yarinya, sabo da haka ku zo mu ci gaba da
tafiya".
Gama fadin haka ke da wuya, sai gimbiya Humaira ta ci
gaba da tafiya dauke da yarinya Alfila, su sarki Sahibul
Hairi suka biyo bayanta cikin jin kunya.
Gimbiya Humaira ta ci gaba da tafiya tana mai karanta
wata addu'a ta musamman. Sarki Sahibul da Bawa Haluf
kuwa suka rinka bin bayanta da sauri ba sa yarda ta basu
sata.
Nan fa suja rinka ganin abin Al'ajabi, domin gani suka yi
suna wuce dazuzzuka tamkar walkiya na giftawa.

Tafiyar da ya kamata su yi ta a cikin sa'a guda sai gashi
sun shafeta a cikin dakika sittin.
Haka dai suka ci gaba da wannan tafiya har suka shafe
tafiyar kwana arba'in a cikin sa'o'i kadan
A sannan ne dare ya riskesu a cikin wani dajo mai yawan
manyan tsaunuka da duwatsu.
Kuma a dai-dai lokacin ne hadari ya gangamo, gari yai
duhu, iska ta soma kadawa mai karfi alamar ruwa na
shirin sauka.
Kafin dakika goma karkarfan ruwa ya kece kamar da
bakin kwarya.
Cikin gaggawa suka ruga izuwa cikin wani kogon dutse
suka zauna. Zamansu ke da wuya sai Humaira ta dau wata
karamar butar duma cike da ruwa tayi alwala sannan ta
nunawa Alfila yadda itama za ta yi alwalar, sannan suka yi
sallah tare.
Duk abin da ke faruwa sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf
na daga can nesa kadan a zaune suna kallonsu.
Sarki Sahibul Hairi ya dubi Bawa Haluf ya ce, "ya kai Haluf
kayi sani cewa ina ji a jikina cewa wannan addini na
Humaira gaskiya ne, kuma kaima kanka shaidane bisa
abubuwan da muka gani a zahiri na ban al'ajabi. To
amma inda matsalar take shi ne, ina jin tsoron cewa idan
na kar6i addinin shi ke nan har abada burina bazai cika
ba".
Sa'adda Haluf ya ji wannan batu sai yai ajiyar zuciya
sannan ya ce, "ya shugabana, amma ai idan baka manta
ba Humaira ta gaya maka cewa idan har kayi imani da
Ubangijinta dukkan burin ka zai cika, sabo da me ba za ka
yi imani da shi ba idan har jikinka ya baka cewa addini ne
na gaskiya?"
Koda jin wannan tambaya sai sarki Sahibul Hairi yai shiru
yana sake-sake. Zuwa wani lokaci ya dago kai ya dubi
Bawa Haluf ya kura masa ido na tsawan dakiku, sannan
ya sunkuyar da kansa ya ci gaba da tunani ba tare da ya
ce da Bawa Haluf komai ba.
Tabbas komai na duniya rabone, kuma komai yana da
lokacinsa.
Gashi dai sarki Sahibul Hairi ya gamsu da cewa addinin
Musulinci gaskiya ne, amma kuma ya kasa tankwara
zuciyar tasa ta yarda ta kar6i addinin sabo da tsoron kada
ya yi asarar abin da ya fito nema.
Lolacin da ruwan sama ya ci gaba da tsugewa, sai wata
irin iska mai sanyi ta rinka busowa har cikin kogon da su
Humaira ke ciki ta addabesu.
Ba shiri su sarki Sahibul Hairo suka mike suka kama karyo
tsurarrun itatuwan da ke cikin kogon suka hada
makamashi.
Bayan sun tare ice mai yawa sai suka fara kokarin kunna
wuta ta hanyar goga dutse da dutse, amma sai wuta ta ki
kamawa.
Lokacin da Humaira ta ga sarki Sahibul Hairi da Bawa

Haluf sun jima suna fama amma sun kasa kuma wutar sai
ta dubi Alfila cikin murmushi ta ce, "je ki ki kar6i
duwatsun a hannunsu kiyi bisimilla ki ambaci sunan
Ubangijin musulinci, da izininsa wutar za ta kama."
Ba tare da fargabar komai ba yarinya Alfila ta mike tsaye
taje ta kar6i duwatsun biyu da ke hannun sarki Sahibul
Hairi tare da yin bisimilla kamar yadda Humaira ta koyar
da ita, ta ambaci sunan Ubangijin musulinci.
Gogawa daya tayi akan makamashin sai wuta ta tashi
kamar an zuba mai.
Sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka cika da tsananin
mamaki, jikinsu yao sanyi.
Nan dai suka gewaye wutar su hudun suna jin dumi.
Alfila na zaune daf da Humaira, sarki Sahibul Hairi da
Bawa Haluf na daga can 6angare guda suna fuskantar
juna.
A duk sa'adda Humaira ta dago kai sai ta ga sarki Sahibul
Hairi na satar kallonta, kawai sai ta mike tsaye tsam! Ta
bar gaban wutar ta koma can gefe daya taa shimfida
buzu ta zauna tana mai fuskantar gabas, sannan ta dauki
casbaha ta kama lazumi.
Ba wani abu bane yasa sarki Sahibul Hairi ke satar kallon
Gimbiya Humaira ba face tsananin kyawunta da ya ribaci
zuciyarsa.
Tun ranar farko da ya fara ganinta yaji zuciyarsa ta buga
da karfi, kuma ya rasa dalilin faruwar hakan.
Abin da sarki Sahibul Hairi bai sani ba ya kamu da
tsananin kaunarta da begenta.
Haka dai su sarki Sahibul Hairi suka ci gaba da zama a
cikin wannan kogon dutsen har dare ya yi sosai suka
kama barci.
A duk sa'adda sarki Sahibul Hairi ya farka sai ya ga Alfila
da Bawa Haluf na ta sharar barci abinsu. Ita kuma
Humaira na nan a zaune bisa buzu tana ta lazumi. Wani
lokacin kuma sai ya ga ta mike tsaye ta kama nafilfiloli.
Kai a takai ce dai Humaira bata gushe ba tana ibada har
sai da ta gabatar da sallar Asuba ta jira Alfijir ya keto
sannan ta kwanta ta lullu6e jikinta gaba daya tayi barci.
Lokacin da gari ya waye sosai sai sarki Sahibul Hairi da
bawa Haluf suka farka daga barci suka ga Humaira da
Alfila na ta barci abinsu.
Kawai sai sarki Sahibul Hairi ya dauki kwari da bakansa ya
rataya sannan ya soke takobinsa a cikin gidanta da ke
daure a kugunsa ya dubi Haluf ya ce, "zo mu tafo neman
abin kalaci.
Koda jin haka sai shima Haluf yai sauri ya dauki nasa
kayan yakin suka face daga cikin kogon dutsen suka
nausa cikin daji.
Ba su yi wata doguwar tafiya ba suka hango wata barewa
a can saman wani dogon tsauni da ke nesa da su.
Sarki Sahibul Hairi yai sauri ya dana kwari a cikin bakansa
ya saita barewar, amma sai ya auna ya ga cewa ba zai

sami nasara ba domin akwai tazara sosai a tsakaninsu da
barewar, don haka sai ya yiwa Haluf inkiyar cewa su
lalla6a ta bayan barewar su kusanci tsaunin da take kai.
Cikin sanda suka rinka taku dai-dai a hankali har suka isa
kan tsaunin suka hau a durkushe yadda za su iya hango
barewar ta baya, amma ita ba ta hangosu ba.
Cikin hanzari sarki Sahibul Hairi ya sake dana kwari a
cikin bakansa ya ta6eshi iya karfinsa ya saita barewar a
ciki, sai ya saki harbi.
Kibiyar ta tafi cikin azababban gudu. Koda taje daf da
barewar sai ta tsaya cak! A cikin iska ta kasa huda cikin
barewar.
Ita kuwa barewar sai ta juyo tayi arba da su sarki Sahibul
Hairi, ta kura musu ido kawai. Al'amarin da ya matukar
baiwa su sarki Sahibul Hairi mamaki ke nan, suka mike
tsaye jikinsu a sanyaye suka kasa juyawa da baya, kuma
suka kasa karasawa inda barewar take.
Cikin tsananin tsoro Haluf ya dubi sarki Sahibul Hairi a
lokacin da jikinsa ya kama karkarwa, ya ce, "ya
shugabana waccan dabbar ba barewz bace aljanai ce, zai
fi kyau mu hakura mu koma da baya domin na fuskanci
cewa akwai muggan abubuwa a cikin wannan daji".
Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi ya dakawa
Bawa Haluf tsawa ya ce, "ai ni idan nayi gaba bana baya.
Idan na za ka iya biyoni ba ka tsaya a nan ka ga abin da
zai faru tsakanina da waccan barewar, idan kuma ba za
ka iya tsayawa ba kayi kallo ba to ka koma inda muka
fito".
Koda gama fadin haka sai sarki Sahibul Hairi ya zare
takobinsa ya ci gaba da hawa kan tsaunin ya dufafi inda
barewar take kai tsaye ba tare da shakkar komai ba.
Shi kuwa Bawa Haluf sai yaji kamar ya juya da baya a
guje amma sai ya daure ya tsaya domin ya ga abin da zai
faru.
Har sarki Sahibul Hairi ya isa daf da barewar wannan
kibiyar ba ya harba mata tana nan a tsaye a cikin iska daf
da barewar.
Da zuwan sarki Sahibul Hairi gaban barewar sai ya daga
takobinsa sama ya kai ma ta wawan sara da nufin ya
tsarge jikinta gida biyu.
Ba zato ba tsammani sai ya ga barewar ta rikida ta zama
sarki Barusa rike da takobi yana mai kare saran.
A sannan ne wannan kibiya ta fadi kasa.
Koda sarki Sahibul Hairi ya ga sarki Barusa a gabansa sai
ya ja da baya a tsorace cikin mutukar mamaki ya kasa ci
gaba da kai masa hari.
Sarki Barusa ya bushe da dariyar mugunta ya ce, "shin
kana tsammanin na mutu ne? To ka sani cewa kashe na
mijin kwarai ba karamin aiki bane, duk abin da ke faruwa
ina bie da ku baku sani ba. Yanzu gashi kun je kun sha
bakar wahala kun dauko yarinya Alfila a cikin fadar
Shamzabul Azwas ni kuma zan kwaceta a salim-alim a

hannunku ba tare da na sha wahalar komai ba".
Koda jin wannan batu sai sarki Sahibul Hairi shima ya
bushe da dariya ya ce, "ya akai wannan sarki kayi sani
cewa wannnan mafarkin naka ba zai ta6a tabbata ba don
haka ina mai baka shawara da ka janye wannan manufa
taka ka koma kasarka ka ci gaba da mulki, ka hakura da
iyakar abin da ka mallaka.
Idan kuwa ka zake ina tabbatar maka da cewa za ka iya
rasa rayuwarka".
Ya yin da sarki Barusa yaji wannan batu sai ya sake
kyakyatawa da Dariya a karo na biyu ya ce, "hakika iska
na yawo da mai kayan kara. Tsaya kaji na gaya maka
gaskiyar abin da duk yasa na kasa mallakar yarinya Alfila,
shi ne zai sa kaima ka kasa mallakarta.
Yanzu zan kamaku nayi garkuwa da ku, domin gimbiya
Humaira ta kawo yarinya Alfila, idan kuwa taki sai na
hallaka ku. Sannan na bi sawunta itama na hallakata na
dauke Alfila."
Sa'adda sarki Sahibul Hairi yaji hakan sai abin ya bashi
dariya ya ce, "ya naji kana cewa za ka kama mu kayi
garkuwa damu kamar wanda zai kama 'yan tsaki? Shin
kana tsammanin kamani a hannunka abu ne mai sauki?".
Koda jin wannan tambaya sai Barusa yai murmushin
mugunta ya ce, "yanzun nan kuwa za ka sha mamaki,
domin sanin da ka yi mini na da ne, amma wannan karon
na zama MURUCIN KAN DUTSU, ban tashi fitowa ba sai na
shirya"
.
SARKIN SARAKAI
Littafi Na Huɗu (4)
Part D.
.
Marubucin littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
AA Misau Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa
KAFIN BARUSA YA GAMA RUFE BAKINSA TUNI SARKI
SAHIBUL HAIRI YA KURMAihu ya kara afka masa da nufin
su ci gaba da gumurzu.
Kawai sai Barusa ya nunashi da hannu, take wata irin
murtukekiyar sarja ta karfe ta nannade sarki Sahibul Hairi
tun daga sama har kasa, ta daure shi tamau ya zamana
cewa ko motsi baya iyawa.
Nan fa sarki Sahibul Hairi ya shiga kokarin kwace kansa ta
hanyar amfani da karkin sihiri, amma sai sihirin nasa ya
ki ya yi tasiri. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinsa ke
nan ya tabbatar da cewa ya kamu.
Bawa Haluf dake can kasan tsaunin kuwa koda ya ga abin
da ya faru da shugabansa sai ya juya ya falfala da gudu da
nufin ya tsere. Amma sai ya ga wani katon tsuntsu ya
sauko kasa ya sureshi da 'yan yatsunsa ya mai da shi kan

tsaunin inda sarki Sahibul Hairi ke tsaye a daure.
Koda tsuntsun ya sakoshi kasa ya fado kusa da Barusa sai
shima sarkar sihirin ta kanannadeshi ta daureshi tamau.
Koda faruwar hakan sai sarki Barusa ya bushe da dariyar
mugunta sannan ya rubuta wasika ya mikawa wannan
katon tsuntsun da ya dauko Bawa Haluf.
Shi kuwa tsuntsun sai ya bude bakinsa ya kar6i wasikar
sannan ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka a
cikin gajimare.
Bacewar tsuntsun ke da wuya sai sarki Barusa ya tafa
hannayensa biyu, take gidan dutse ya bayyana akan
tsaunin, sai ga wadansu irin halittu masu kama da
dodanni ba adadi suna fitowa daga cikin gidan dutse.
Sai da suka shafe mintina masu yawa suna fitowa da
jeruwa sahu-sahu sannan suka kare. Lokaci guda su duka
suka yi sujjada ga sarki Barusa.
Barusa ya dubi halittun ya ce, "ku kama wadannan
fursunonin ku shigar da su cikin gidan nan ku jefasu cikin
kurkuku ku kulle.
Shugaban halittun ya ce, "an gama ya shugabana, shin
akwai wani abun bayan wannan?"
Sarki Barusa ya ce, "eh, ina son kuyi gagarumin shirin
yaki, domin nan da wadansu 'yan sa'o'e kadan gimbiya
Humaira za ta zo tare da Alfila, kuma nasan idan tazo za
ta yi kokarin hanani Alfila. Lallai tsakaninmu da ita yaki ne
mai tsanani sai mun yi da gaske zamu sami nasara a
kanta.
Koda jin wannan batu sai shugaban halittun ya kada baki
ya ce, "ya shigabana lallai zamu yi shiri irin wanda bamu
ta6a yin kamarsa ba. Ina tabbatar maka da cewa ko gaba
dayan dakarun duniya ne za su zo su yakemu ba za su
sami nasara a kanmu ba."
Gama fadin haka ke da wuya sai shugaban halittun ya
juya ya dubi wasu daga cikin yaransa su kuma sai suka
kama sarki Sahibul Hairi da Bawa Haluf suka shiga da su
izuwa cikin gadan. Ragowar kuwa sai suka koma cikin
gidan suka yi ta fitowa da makaman yaki. Suka ci gaba da
shirye-shiryen yaki.
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki Sahibul Hairi da
Bawa Haluf bayan sun fita farauta sarki Barusa ya sake
baiyana a garesu tare da sabon hatsabibanci.
A can kogon dutse kuwa, lokacin da Humaira da Alfila
suka farka daga barci, sai suka nemi sarki Sahibul Hairi da
Bawa Haluf suka rasa.
Alfila ta dubi Humaira ta ce, "ya ke 'yar uwata yanzu kuwa
ina kike

1 Comments On SARKIN SARAKAI
avatar
sdeeq

1 year ago

Reply

dan allah babu yadda xanyi download ne

Please Login or Register in order to submit comment